Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yi masa ya same wuce hankali, domin ko auren Sadiya bai kashe wannan kudin ba, sannan kudin sa da ke accout yayi shirin siyan wani gida ne da aka yi masa tallansa can kasan su a sabuwar unguwa da ke nan unguwar Mu'azun. Ya kalli Usman ya ce aboki ni fa ba zan iya biyan wayan nan kudinba. Usman ya ce, to ka kirata ta fada musu baza ka iya yin al'ada ba. Ya kalli waliyin ya ce a kirata. Sai suka ce ai su al'adar su ba a magana da amarya sai su waliyanta. Usman ya ce to su basa yin wanan al'adar sadaki kawai zasu biya. Sauran suka ce sam ai tunda ta haihu a tasu al'adar yin biki dolene, kuma abubuwan al'ada dole ne, domin ita mai albarka ce mai haihuwa ce, sannan ba dama ya ce ya fasa tunda ta haihu. Shi da Usman suka kalli juna a ran shi ya ce lallai ya debowa kanshi ruwan dafa kanshi. Usman ya ce kawai ka basu inya so sai ka sai fili bana son a samu matsala. Nan dai ba da son ran shi ba ya amince bayan sun fita suka tafi banki in da ya ciro kudi suka dinga yi masa lissafi yana ba su, nan fa suka ce jibi za su yi hutu, suka amince a haka. Ni kam ko da suka dawo bai fada min ba gurin Anty Abida na samu labarid Usman ke fada mata, na ce shi dai ya sani can da yawarsa. Idanu na zuba ina kallonsa yau da na ga yanzun yana dan zakewa tare da rawar kai, sam ban zata ba, ya sa a yi gyaran gida. An yi fenti na kwashe kayan yarana daga dakin da ta zauna tunda nan za'a sa ta, ya ce da ya so canza min gado,amma in yi hakuri ko daga baya ne. Yaba ni dubu talatin,na yara ashirin na karba na aje tare da cewa mun gode. Na dauki waya ta ina dannawa ya ce, Wai Sadiya akwai wani laifi da nayi makine?na kalleshi' Me ka gani? Ya ce, Na ga tun jiya da na zo ba wata fuska a gurinki?Na maida kaina ga kallon wayata,sannan na ce, Akwai abin da ban makaba daga cikin wanda na saba yimaka?Yace, A'a,kin min komai MY CHOICE, sai dai ni na gane kamar ba ki da walwala. Na ce, Ba ka yi min komai ba. Ya ce, To anjima zan tafi, Na ce, Allah ya kai mu. Har ya kai bakin kofa na ce, Au! Na manta in fada maka an dauke ni amma ba aprimary ta nan unguqar Ma'azu ba, ta can Tudun wada. Ya tsaya yana kallona, nima shi nake kallo don son jin ta bakin shi,a zuciyata ina cewa yanzun dai a ce ya hana ni, tabdijan! Da sai ya ji magana. Tamkar ya sani sai ya ce na san kina zaton zan hana kineko? Ai ba ni da yanda zan yi tunda na rigana yi miki alkawari,amma ki sani raina baya so. Ban ce kala ba na ci gaba da danna wayata shi kuma ya fita. Ban tabbatar da cewa ina da kishi ba sai da lokacin auran ya gabato,wallahi ko abinci kasa ci nayi duk datausar da Aisha ke min da kuma Anty Abida dan ganin na kwantar da hankalina, amma na kasa, bana bacci sosai duk da cewa bana nunawa Yaya damuwata sai dai shi duk lokacin da muka yi waya sai ya yi min korafin in daina damuwa in kwantar da hankali,To kurum nake ce masa, amma zahirin gaskiya zantukansa ma soya min rai suke yi. Ana gobe daurin aure zasu tafi can Lagos din ina kallo shi yana ta shige da fice yana shiri,an zuba sababbin dinkuna an sai Huluna da Takalma sai ina mamakin mutumin da na dinga shan kan shi da kyar shi ne yake zumudi. A fili na ce Allah yasa abin ya tsaya nan. Ya fito cikin shiri ina kwance kan gadon yara ya ce 'My Choice mun shirya,na dago na kalle shi, yayi matuqar kyau cikin Shadda Wagambari Blue shar kaladaya da hularsa mu hadu a banki, kamshinsa ya cika gidan, kishi ya kama ni mai tsanani,na kau da kai gefe. Ya ce, 'My choice yaya ne? Ban tanka masa ba sai zuciyata ta ce gwada shi ki gani da yake cewa in na ce ya fasa zai fasa,in ya so duk ma abin da zai faru to ya faru. Ya tallabo fuskata. 'My Choice, yaya ne? Na ce, 'Ni fa gsky na sake tunani a kan wannan auran, gaskiay ina tsoron abin da zai biyo baya. Zai fi kyau a barshi. Zumbur ya mike tsaye daga russunawar da ya yi, na kalle shi ga mamakina fuskarshi daure, ya ce, 'Me ki ke nufin maidani? Karamin mutum? Kin sa mun yi magana yanzun kuma kizo ki ce ke kina jin tsoro, ya kamata ki fadi haka ne tun kafin yau, sai dai ki yi hakuri,mamakida tsoro suka sa na kasa daina kallonsa sannnan ga hawaye yana ta zuba tamkar an bude famfo, na girgiza kai tare da sauke ajiyar zuciya,sai kuma ya zauna kusa da ni tare da dafa kafadata. My choice bana nufin cutar da ke kece kika karfafani kika nuna min yin auran nan shine mafita, to me zai sa yanzun ki bijiro min da wani sabon batu bayan aski ya zo gaban goshi? Kuka ya kwace min na shiga rera shi, tsam ya makaleni jikinsa yana lallashina. Sadiya in kin ce baki so wallahi abar shi. Ya ciro wayar shi yasoma dannawa. Bari na fadawa Usman ya kira Yaya Sulaiman ya fada masa cewa nafasa.ina jiyo shigar wayar ta soma ringing a can,da sauri na dago na amshi wayar da sauri na katse. Ya ce, yaya kuma za ki katseki bani in dakatar dasu su daina shiri. Na cecikin shagwabar kuka, Ni fa ban ce ka fasa ba.yasa hannunsa ya dago fuskata,To me kika ce?Na kalli cikin idon shi 'In ka aure ta zaka daina sona? Sai kurum naji bakin shi cikin nawa, minti1muka dauka, sai wayarshi ta shiga ruri,ya sakeni tare da daukar Wayar. Usman ina zuwa. Ya katse ya kalleni. My Choice in na yi rantsuwa bazan yi kaffaraba Ke ce 1 tak nake so, kum na soma son ki ne tun lkcn da kika soma zama mace. Da farko ban fahimci ina sonki bane sai da Usman ya kwadaita mini da nazo iya ta ki sai na samu kaina da kasa hakura, wannan ya tabbatar min cewa ina mutukar sonki,Ke ce zabina, kada ki damu da Mujidat sam ba na son ki hada son ta da naki, Ke ba ita ba in miki ta mahaukaci duk duniya ba wata mace da nake so ko kuma zan sota sama da ke, ki rike wannan a cikin zuciyarki,so 1 tak Ke na ke yiwa shi.,lumshe ido na yi inma karya Yayaya fada min to na yarda don gaskiya maza da ace zasu gane furta son ka ga matar ka komai dadewar aurenku yana susutar da mace komai shekarunta ta ji ta tamkar sabuwa,amma matsalar maza musamman irin na yankinmu ba sa iya cewa matar su suna sonta, ko wasu kalamai na soyayya irin wanda suke yi mata yayin yakin neman aurenta da zarar sunga cewa sun aurenta shi Kenan ta tsufa Nima haka na ji tamkar farkon aurenmu duk damuwar dake cikin zuciyata sai ta gushe, sabida ina son a so ni,ina son a nuna min soyayya, ina son a fada min kalaman so. Nasa hannu a kumatun shi na shafa ina kallon cikin idon shi, Yaya na gamsu da kalamanka, Allah ya tsare hanya gobe zaku dawo? Ya ce, insha Allah ko jibi, tunda da nisa in mun taso da yamma ko da dare sai safe zamu iso. Na ce shi Kenan. Ya mike tsaye, me zan sayo miki a can? Na ce, gdnsu lesuka, in ka siya min zanyi murna. Ya ce insha Allah zan zabo miki masu kyau. Na ce to nagode. Har waje na raka shi. Sai dai duk da haka kasa bacci nayi daren ranar sai damuwa da sake saken zuci. Washe gari kuwa data kasance ranar daurin aure ba zan iya lissafa tashin hanklin da na shiga ba. Da safe kasa zama na yi a gidan na tafi gidan Iya wai don in manta da batun auren amma duk da haka na kasa sukuni, har Iya ta fahimta, sai kurum naji ta ce. Sadiya, hakika kishi wani abu ne mai rai, amma yana da sauki in kin saukakashi, ina son ki nutsu ki rike girmanki. Shawarar da zan baki ki kara zage damtse gurin kyautatawa mijinki kada ki dauki halayen wasu matan masu cewa in miji ya kara aure zasu daina yi masa komai suce ya je can matar da ya auro tayi masa, wannan kuskure ne, don in aka samu wadda ta san hannunta kafin ki samo mijinki sai wani ikon Allah,ki zama a gidanki Ke ce uwar kowa. Ina nufin duk abinda ya taso na kudi ko matsalar lalacewar wani abu a gida Kar ki tsaya jiransa kiyi da kudinki in yaso in yazo kya karba ko yaturo miki, sannan ba'a fata in har sabani ya shiga tsakaninki da ita tunda an ce zo mu zauna zo mu saba, to kada ki sake ki fara kai kara Kinji ko? Na ce, to. Yauwwa sabida in kinyi nazari cikin ya'yanki mai yawan kawo kara duk gaskiyarshi sai kinji haushinsa. Na ce, haka ne. To ki rike hakuri da addu'a ki dinga yawaita karatun Alkur'ani mai girma, ki zauna da ita zuciya1, sannan ga aikin ki ma, ai ni naji dadin barin ki da yayi wannan koyarwar, na ce, nima naji dadi iya, don ina da yara gara dai yanzu da muke mu 2 aikin ya dauke masa matsalolina in ina samu ba sai na jira shi ba, kudin da ya bani ma nawa da yara wai muyi siyayya su dai na Dan sai musu wani abu, so nake in hada jari in dinga saye da siyarwa. Iya tayi dariya tare da cewa, da kyau Sadiyayyena. Haka nayini Iya tana kwantar min da hankali tare da bani shawarwari sai kusan 10 na dare na debi ya'yana ta raka mu har gida, nima na sake rako ta hanya.ina sa hakarkarina a kan gado na dauko wayata nakunna dama yinin ranar kashe ta na yi. Nan fa sakonni suka soma shigowa na yaya sai na Aisha da Anty Abida, na su na soma dubawa. Tanbayata suke ina naje sun zo ba nanan? Na yi dan murmushi, a fili na ce da kun zo gidan Iya ni kam ba zan yi wani taro ba, sai na soma duba nashi,duk kusan yana nuna damuwane akan ya kira bai sameni ba. Sai na karshe da yake cewa sun taso 9 suna hanya, akwai yiwuwar su iso kafin 9 na safe, kuma suna tare da wasu daga danginta dan Allah ta tanadar musu abinci. Kiran Abida ya katse karatun sakon da na keyi, na daga muka gaisa, ta ce min, ina na shige yau? Na ce ina gidan Iya,tace to, ki yi sammakon tashi don mijinki zasuyi shigowar safe ne, nace Anty me zanyimusu?tace karin kumallo mana kiyi zuciya1 kada ki sa kishi ciki, bakin kine, kin kuma san darajar baki a musulunci. Na ce to Aunty zanyi. Tin 4 na tashi na fara firar dankali da nayi sallah kuma na hau suya, har kaji biyu nayi musu farfesu, kwai ma isasshena yi musu kwai da kwai na dafa ruwan tea mai yawa, sannan na gyara gidana nayi wa yara wanka na zabo musu sababbin kaya nima na sheka nawa adon. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Takwas daida na ji tsayawar motoci,gabana ya yanke ya yi wata muguwar faduwa,sai na hau karanta Hasbunallahu wa ni'imal wakil. Na mike na je na bude musu kofa gabana yana ta faduwa,zuciyata tana maimaita addu'a.suka shigo suna yi min sannu, wasun su suna kallona wani iri,amma duk da haka na saki raina ina yi musu sannu da harshen Turanci.Najee na bude musu dakin suka yi sororo a tsakar daki don ga al'adarsu miji ke shiryawa mace daki ya zuba komai, ita kuma iyayenta su yi mata kayan sawa, nan fa suka soma yare, duk da bana ji amma ganin yanda suke magana suna tabe baki na fahimci zancen nasu bana dadi ba ne, naje nasoma fito musu d kuloli. Sai gasu Yaya sun shigo, na kirkiro fara'a ina yi musu sannu da zuwa. Falo suka je suka zauna na gabatar musu suma da abin kari, na kula yaya ya ji dadin yanda na saki jikina na kuma yi musu abin kari.Nan nabarsu nayi daki,bayan Mujidat da danginta sun gama karyawa sai suka samu su Aliyu da Usman suna yi musu korafin ba su ga kmai a dakin ba.Usman ya ce, Mu a nan da kaya amarya take zuwa. Suka ce su kam ba haka ba ne, nan suka fito masa da akwatunan amarya har da na mijin da na Maman shi da kuma na danginsa. Aliyu ya ce shi kenan zai siya daga baya, amma yanzun a kwaso na dakinsa a sa mata,sukace bakomai. Ina dakin nashi ya shigo wanda zuwa yanzun ya zama nawa,ya zauna. Sadiya kin ji wata sabuwa. Na kalle shi, ya ce, Wai ni zan sai mata gado. Na ce, ina zaton haka al'adar su take don mun taba yin zancen da wata 'yar ajinmu da muka yi N.C.E take ba mu labarin al'adunsu, miji ke yin kayan daki kuma sadakin su yana da tsada, amma mace za ta ja jari da su ita ce za ta rike gida,wasu kuma jarin daban miji zaibada, wadanda ba Musulmi ba sun fiyi, Musulminsu kamsai sunyi aure suke tarewa gidan mazajensu,yace,nidai yanzun ya za'a yi? Na ce su zo su dauki wannan gadon. Na tsura masa ido cikin mamaki,sai ya ce, ko ya ki ka gani? Na mike na nufi dakina bayan na ce, Me zan ce kai da abinka. Na shiga dakina na soma kallon dakin ina lissafa yanda zan gyara shi ni da yarana da na bar musu gadona tunda dama katifu gare su. Sai ga shi ya shigo.Haba Sadiya,me zai sa ki yankemin wannan hukuncin? Nazo miki da shawara amma sai ki yi watsi da ni kitaho abin ki? Na ce, Yaya kainefa da abinka kuma ka ba matarka, mene ne laifina dan na taho? Yace, Ok, kije amma ki sani kada nan gaba ki ce na daina kawo miki Shawara,kin sani dai ke ce kurum nake tunkara da duk matsala ta. Shiru na yi dan nasan in hakan ta faru lallai ba zan zama uwar gidaba. Ya mike zai fita na ce, Yaya'' ya dawo,Mene ne? Na ce, Shi kenan ka yi hakuri. Ya zauna tare da kamo hannuna, Nagode da ki ka fahimce ni, yanzun ya ki ke ganin za'ayi? Na ce, Ka ba ta,ni kawai sai naringa kwana a nan da yarana. Ya tsura min ido, To nifa? Na ce, Ba komai ka yi ta kwana dakinta. Ya yi dan murmushi, Har yanzun baki huce ba.Na yi 'yar dariyar yake, Bana fushi da kai. Yace, Zan siyo katifu yau a sa can dakin in komai ya warware zan canza gadajen gidan.Na ce to maimakon ka ba ta tsohon gadon ba gara ka sai mata katifar ba? Amma yanda ka gani, Ya ce na riga na fada musu ne na ce to su dauka bari. In zo in kwashe kayan na wardrobe din. Ya ce, A'a, gado kawai da katifa za ta dauka. Na ce, Shi kenan, Allah ya rufa asiri. Ashe tashin hankali yana gaba,sai lokacin bacci, Mujidat ta kira shi a waya wai tana jin bacci, ya kalle ni muna zaune kan gado,sannan yaci gaba da magana. To ki kwanta mana. Ta ce, Ba dakin ka zan kwana ba? Ya ce, A'a yanzun bani da daki in danginki sun tafi na kwana adakinki. Mamaki da haushi suka cika ni, ga kishi kamar in hade raina, na ce, Kuje dakin naka mana? Yaja tsaki tare da cewa, Don Allah ki bar wannan maganar. Na kwanta tare da juya bayana na rungume yarana bankara sauraron shi ba, shi ma ya kwanta a daya gefen Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Washe gari tun Asbahi suka soma shiri,suna karyawa suka tafi, wata daya ce daga cikinsu kadai ta yi min sallama da godiya, suna kama ina zaton yarta ce dake illorin din, domin nayi dawainiya dasu sosai ta fannin abinci. Ya tsaya da su sun shiga gurin Iya sun gaisa duk da cewa ba sa jin yaren juna, sannan ya wuce dasu zuwa gareji. Ranar ne matan Yaya Sulaiman da su Anty Abida sukayi ta zuwa ganin Amarya. Anty Abida ta yi ta yi min fada wai ya zan sa abu a cikin raina ga shi nan duk na rame, na ce Anty dole in sa a raina, ba za ki fahimci zafinkishi ba, duk irin bayanin da zan yi miki, kuma bana fatan a yi miki ki ji.Anty Abida tace, Ameen,don Allah ina son ki saki ranki. Amarya dai tana daki bata fito ba, da za su tafi na raka su ganin amarya ta ci rigarta da wando na bakin Jeans, danta yana cikin gadon shi ta yi ruf daciki kan gadon da suka kafa tana chatting, a yatsine ta amsa sallamar,sannan aka gaisa,suka yi fatan alkhairi suka fita. Daran ranar ne ya hada mu a falo yana yi mana nasihar zama lafiya, sam ban san me yake cewa ba, ina can gurin tunani. Yau ga shi abin da nake karantawa cikin littattafai ya zo kaina, ji nake tamkar cikin mafarki, ashe dai nima za a min kishiya. Girgiza nin da yayine ya sa na dawo cikin hayyacina,cikin damuwa ya ce, Menebe? Na girgiza kai ba komai. Ya ce, ina tambayar ki game da kwana,na ce, Nawa nawa? Nayi hamma kirkirarra, sannan duk yadda kace. Ya ce, To a bar shi bibbiyu kamar yanda aka fi yi. Na ce shi kenan. Ita dai tana ta jijjiga danta,na sake kirkiro hamma, zanje in kwanta bacci. Ya kalli agogon bango; Da wuri? Na ce, Na gaji ne. Na kalli amarya wadda ta sha leshi kai ya ji gashin doki ya zubo har kafada, na ce, Sai da safe,ta dube ni da 'yar yatsina eh, dama ban jira amsar ta ba na yi tafiyata. TABDI! Daran ranar kasa bacci na yi har zuga ni zuciyata ta dinga yi wai inje in labe inji me suke yi, amma sai na fi karfinta inda na yo alwala na yi ta sallah in nagaji in dauki Alkur'ani nayita karantawa,sai da na yi sallar Asubahi sannan na kwanat. Allah ya taimake ni yarana suna cikin hutun makaranta ne, don haka da na tashesu muka yi sallah sai muka koma. Ban farka basai tara, ina tashi Mama ta tashi, sai da na yimusu wanka sannan muka fito.....zandakata anan zuwa lokaci na gaba,fatan zaku kasance tare dani Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Darajar Yayana3-04 Posted by ANaM Dorayi on 07:21 PM, 06-Apr-16 Under: DARAJAR 'YA'YANA _________________NA ___________HALIMA K/MASHI Tun a falo nasan cewa masu gidan sun jima da tashi,domin ga gurin da aka karya nan ba a kwashe kayanba,na shiga kicin na soyo wayara dankali da kwai, dama ni ban damu in ci wani abuba don bana jin yunwa, na hada musu Tea sannan ni kuma na sha ruwan Lipton, na kwanta ringine ina karanta wani post da Sheik Daurawa yayo a facebook, sai ga shi ya shigo, idanuna basa san kallonshi, ina jin su Kausar suna gaida shi ya amsa tare da sumbatar su a goshinsu su duka, sannan ya zauna bakin gado kusa da ni. My choice,ina ta shigowa kuna bacci da yaranki. Ban tanka masa ba ya ce, An tashi lafiya? A ciki na ce, Lafiya lau. Ya ce, ke kin ci abincin ne? Na ce Um, ya yi shiru yana tunanin me zai ce, ni ko da zai fita ma zan fi so. Sai ya ce, yauwa am, Sadiya jiya namanta ba mu yi magana ba. Ba tare da na dago ba na ce inajinka. Ya ce yanzun wane hukunci zamu dora Mujidat ko in ce ina za mu ajeta? Budurwa ko bazawara? Yana cewa haka na fuskanci nufinshi wato kwana nawa zaiyi, zuciyata ta soma tafasa,amma sai na fara karanta addu'a, na tashi na kalle shi. Mujidat budurwa ce, don haka sati daya za ka yi a dakinta, garabasa ma dazan yi maka ita ce ka gama hutunka kaf a dakinta. Ya ce, a'a ban yarda ba. Na koma na kwanta ba tare da na kara cewa komai ba. Ya amshi wayar hannuna yana cewa. Me ki ke gani ne cikin wayar ki, wanda ya fi ni? Juyowa na yi ina kallon shi,sai da ya gama karantawa,sannan ya ce, Banace kirufe wannan account din ba? Bana son kina hawa facebook fa. Yayi maganar tare da dan hade rai. Nace, To ni menakeyima a facebook din? Daga ganin abin da duniya ke ciki sai post din malamai,sai ko gidajen da akabude dan wayarwa da mata kai. Ya ce, Duk da haka dai na ce ki rufe zan sai miki kasunan wa'azi in namu sun miki kadan, sannan zan baki kudi ki sai littattafai na wayrwa da mata kai din, huldarki da internet din ne ba na so,ban amsaba,shi kuma ya fice. A raina na ce ka zaci abin da kakeyi a internet din haka kowama keyi? Na ajiye wayar batare da na goge ba, sai dai cikin zuciyata na dauki aniyar gogewa,amma ba yanzu ba. Duk zatona da naganta kicin tana girki duka gidan za ta yi, amma sai na ga ta juye kula daya ta nufi dakinta, don haka sai na tashi nayiwa yarana. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Bai shigo gidanba sai Magriba duk da dai ya kirani ta waya da rana yace menadafa? Na ce masa taliya, shi dabagwanin taliya ba ne don haka sai ya ce to bari ya ci tuwon sa gurin Iya. Ya sameni daki ina karanta littafin Hausa, su Kausar suna ta wasa, nan suka tashi suna yimasa oyoyo, na dube shi tare da yi masa sannu da zuwa. Ya amsa,sannan ya zauna. Kin ganni sai yanzun? Na ce, Eh, ina zaton wani aiki ne ma ya taso maka. Ya ce, A'a, wallahi gidan ne sam baya yi min dadin zama duk jina nake a takure, shi yasa naso in sayi wancan gidan ga shi duk na kashe rabin kudin. Dariya ta subuce min cikin zuciya nace ai ba a banza aka kashe ba,tunda aure kayi, ko ba nan kudin suka wuce ba? Shiru ya yi tunda ya san bai fada min cewa kudinsa sun wuce a gurin auran Mujidat ba, sai ma ya dauko wani batun. Yauma baki cemin lesukan nan sunyi kyau ba? Nace, Na fada maka mana, ka dai manta ne ko dai anan kakashe kudin? Da sauri ya ce, A'a ni ban ce ba. Wayar shi ta soma ruri ya dauka, sai na ji ya ce, Ke ina zuwa nafa shigo gidan. Ina jin haka na san cewa Mujidat ce, a raina naji zafi mijina wata ke kira kuma tana da damar yin hakan, jin hawaye na son zubo min sai na mike na shige bandaki tare da cewa, Bari in yo alwalar Isha'i. A dakin Mujidat Aliyu ya zauna idanun shi yana kallon Abdul wanda daga jiya zuwa yau ya soma son dan shi, ita kuma tana kwance rufda ciki tana chating ya sa hannu ya amshi wayar, ta tashi zaune. Honey ban waya ta, muna hira a group dinmune, don Allah.Ya soma danna wayar yana dubawa,can ya dube ta, Har da maza fa na ga kuna hirar? Ta ce, Eh, ba za mu yi hira ba,'yan group din mu ne fa? Ya kashe wayar, sannan ya sa ta cikin aljihunsa, ta ce, Ban gane ba, amma kai ka sai min? Ya ce, Zan sai miki wata da wani sim din yanzun karkashina kike ba zan yarda ki yi hulda da kowa ba,tace Kana nufin har da iyayena,da sauran dangina? Aliyu ya ce, Bance zan hana ki hulda da danginki ba, amma sai na tantancesu.taja tsaki,sannan ta zauna cikin fushi, ya isa gabanta yasa yatsunsa ya damki lebenta, Kar ki sake yi min tsaki sabida yanzun ni mijinki ne yana da kyau kisan darajata. Taji zafin yanda yayi mata, har ta yi 'yar kara sannan ya saki ya kuma fita. Na yi hakuri tare da cijewa gami da kau da kaina game da Yaya da matarsa.Ranar da ya cika sati dayama nace nakara masa wani satin,amma ya ce sam ba ya so. Kafin hutun shi ya kare wani aiki ya taso don haka ya shirya komawa ya kira mu falo ya ce to ni zan tafi. Ya kalli Mujidat. Kada ki sake in dawo inji wata matsala ta faru, sbd in na ga sabon abu daga ke ne. Na dade dasanin wace ce matata,sannan duk abin da ki ke bukata ki tambayeta. Sai abu na gaba bance kitafi ko'ina ba, don baki dakowa a garin nan, kin fahimta ko? Ta turo baki gami da bata rai,sannan ta ce yana yi mata gorin dangi kenan? Ya ce in kin dauka haka to hakan ne. Ya dube ni, Kici gaba da hakurin da nasan ki da shi,sannan ki kama girmanki, kamar yanda kikeyi, inda wata matsala ki sanar da ni,sannan yau kwanana daya a dakin ki tafiyar nan ta taso,ina dawowa zan sauka dakinki in yi kwana dayan da ya rage,sannan in koma gurin ta,nace, to Allah ya tsare ya dawo da kai lafiya. Yara ma ya sallame su, kamar yanda ya saba muka raka shi har mota,har da Mujidat din sabe da danta a kafada,duk da ba ta zo kusa da shi ba. Na ce,baka sallami Abdul ba.nakalli Mujidat, Ki ba Baban shi su yi sallama. Ya ce, A'a, bar shi kawai. Ya tada mota, sam ban so yanda ya yi ba,domin a gabanta ya rungumi sauran yara tare da sumbatar su, fuu! Ta juya ciki, tun kafin ya tada motar,nabita da kallo,sannan na kalleshi. Yaya ka daina haka, yanzun mun zama daya kuma wannan yaron ka ne kar ka gwada bambanci ko ka ce za ka yi kara dan ganin idona na san dai kana son danka,ya tada motar tare da cewa, Na tafi.Na ce Allah ya tsare. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Gaskiya Mujidat ba ta bukatar muyi zaman lafiya yadda take mu'amalarta da yarana amma ni na sawa kaina alwashin sai dai tayi da wani amma badaniba, duk da cewa na san ban girme ta ba,amma a gurina zubar da aji ne in tsaya cacar baki da kishiya,gurin cin abinci dama tun yana nan bai hana kowa yin na shi ba.Da farko na so in masa magana kan cewa ya

Chapter 17 of 25