Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mace mai ciki ta haihu tayi IDDA ko?Ta sake tattaro hankalinta gareni,in an sake ta ba?me ya kawo wannan tunani cikin kwakwalwarki?ta yunkura. Bari in kira likinta nan ina zaton har yanxu b ki dawo cikin hayyacinki ba Gam!nariketa iya! Ina cikin hayyacina,na soma kuka,yanxu ni ba matar shi b ce salati naji Iyar ta saka,sannan ta sake tambayata,saki kuma sadiya?na kama hannunta,kiyimin addu'a in cinye wannan jarabawar.shiru tayi ta kasa magana sallamar shi ce tasani lumshe ido,sam bana son ganinsa kojin muryarsa.Iya ta subule hannunta daga nawa ta fita,kuma cikin fushi,sanan taki ansa sannu da yayan keyi mata.yabita da kallo har ta fita,y iso kaina,na bude ido na kalleshi,kallon tsana,fuskar shi babu alamar nadama yace. Daga ganin yanda Iya ta fita rai a bace,nasan kin fada matane,banso kikayi saurin fada ba,sabida in rufa miki asiri,kamar yanda kikayimin. Duk da halin da nake ciki ban san lokacin dana tashi zaune ba,cikin kuka nace Aliyu bana bukatar rufin asirinka,domin in kaji mutm yana neman rufin asiri bashida gaskia,sai dai bansan mekazoyi nan ba,tunda yanzu ba matarka bace,nayi iddarka ka tafi banason sake ganinka,yace nasan haka zuwa nayi in duba jikin ki matsayina na yayanki kadai kuma uwar yarana,Nace,to nagide,tafi yace yanxu kuwa,sai dai zan miki irin halaccin da kikayimin,har abada iya bazata ta6a jin dalilin sakin ba.nagirgiza kai,dole tasani,don ni zan fada mata,ka tafi bana son ganinka,ka tafi,na jefeshi da filo,Iya ta shigo,Gadanga fita daga nan! ya juya ya fita.tazo ta kamani ina kuka ta rungumeni a jikinta tana lallashina tana bni baki har na hakura nayi shuru. ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Kwana na 2 na dan murmure mutane suna ta zuwa dubani,sunayimin barka,amma kishiyata da yarana shuru bare yaya.tsakanin da da mahaifi sai Allah,zuciyita tana can gurin yan yarana dana tuno su sai inji hawaye yana bin kumatuna,Iya tayi ta lallashjna. Sati na 1 aka sallameni,Usman ne ke tsaye gurin kula dani da biyan kudin Asibitina,sam baiyi mana zanchenba,muma ba muyi masa ba,Anty Abida kecemin wai yayi bakin cikin abunda Aliyu yayine yasa shi jin kunyata.nace rayuwace kice masa ba komai,shida yayi bai ji kunya ba sai shi? Kai tsaye gidan Iya muka wuce,sun bani dana sun mana gargadi banda jagwalgwalonshi. Daran ranar Usman yazo kan batun sunan yaro.Iya ta bamu wuri na mika masa yaron,sannan na zauna muka gaisa,Ya dubeni Sadiya,wallahi nauyi da kunya sun hanani in miki jajen abinda ya faru,lokacin da Aliyu yazomin da batun nan wallahi karkiga tashn hankalin dana shiga,na tabbata an hado sharri ne don kawai a tarwatsaku,hawaye suka soma kwaranya daga idanuwana,na soma magana cikin kuka, Yaya Usman wallahi bansan komai akan abinda Abban Kausar yazo min dashi ba,sannan yaki tsayawa ya fahmci hakan.A tunanina yafi kowa sanin wacece ni,kuskurena 1 daya ce in rufe account dina sai ban rufe ba,wannan kuma mantawa nayi don ina ta kaina bana hawa. Yace,kiyi hakuri ki dauki abin amatsayin jarabta,Allah ya baki lafia,sannan ya raya miki yaronki.wane suna za'ayimasa huduba dashi? nace,ni bani da za6i a sa masa duk wanda yakansance rabonsa. Usman yayiwa yaro huduba da Abubakar,nace sunan babana?yace rabon shine,Iya ta fito daga uwar daki dama tanajinmu tace Allah yaraya Abubakar Saddiku mukace amen. Ta zauna,sannan tace,Usman abinda Gadanga yayi sam bai kyauta ba,ba'a ta6a 6atamin rai b kamar wannan tunda nazo dunia,Sadiyar ce bai sani ba? in ya gaji da zama da ita sai yayi mata sharri? abin da batayi da kuriciyartaba shine zatayi yanxu wai tana bin wani Malami? Murya iya ta soma rawa.Allah zai saka mata insha Allahu.Usmn yace kiyi hakuri Iya,rashn bincike ne kar kiyi masa baki.da sannun gaskia zatayi halinta,nikaina baram baram muka rabu dashi.ina kalln kiranshi dazu ban daukaba, saboda ina son ya san cewa yayi laifi.nafada masa in an bincika za'a gano duk wanda ya shirya wannan sharrin sannu a hankali,mudake aiki da internent muka san computer mun san ana yin irin wannan sharri sai wani can ya bude account din mutm ya kwace yayita aikata sharri ko batsa ko kuma hotunan banza yayita turawa da sunan mai wannan account mutane kuma su zata shne.Inatasan inyimasa bayani lokacin amma yaki'saida y iso gida ya aikata abinda da yasha masa kai,amma insha Allahu komai zai wuce a koma tamkar da.nayi yar daryar takaici tare da cewa ta6di! Insha Allahu hakana bar auren yaya.Iya tace insha Allahu kuwa,nidai dama na guji hakan,amma ganin sun zauna lafiya harda yan yaransu sai na saki jikina,ashe yace tsiyar tana gaba,Usmn yace insha Allahu komai ya wuce,yaba Iya yaron yamike tare da cewa yana zuwa.jim kadan y dawo da manyan ledoji dauke da kayan shayi zuwa su pampers.nace yaya Usman dan Allah kabar dawainiyarnan dani haka,yace haba dai ina abinyake?mukayi gidiya tare da cewa ya gaida Anty Abida da yara,yace zasuji. Washegari da safe wayar Iya na kar6a na kira Anty Abida nace mata kayan sawa na dana Baby za'a kwaso min a gidan Yay Aly.iya tace ai ba kayan sawa ba anjima zan nemi mota komai naki za'a kwasomin tas. Haka kuwa ranar a ka kwaso gadona da kujeru dake falo tare da kayan kicin dina,iya da kanta taje gidan.Mujidat sunata shewa da wadannan yaren nasu,ta shigo da yaran makota da Anty Abida suka kwashe. ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Nace iya kingasu kausar tace a'a suna makaranta. Nasoma kuka,gaskia Iya zan kar6o yarana,wallahi Mujidat bazata iya rikeminsu ba,Iya tce Sadiya! nasan cewa da ciwo inaso ki danne ki kau da kai,musawa Gadanga ido nace shikenan. Cikin 'yan kwanaki duk na rame na kade ba na iya cin abinci sai Iya ta matsa min da fada,sabida tunanin yarana ina son in gansu. Wata rana Aisha ta zo min yini, na ce don Allah ta je ta dubo min yarana,amma tana zuwa gidan an datse shi da kwado,cikin kuka na kira Yaya Usman ina tambayar shi ina yaya ya kai min yara? Ya ce Sadiya ki yi hakuri ya kwashe iyalan shi sun koma Abuja. Na lura baniba hatta Iya ranta ya baci, tace wato ban isa ma yace min zai bar garin ba,shi kenan yayi in dai duniya ce ga shi ga ta nan. Nafi sati ina kukan yarana,sai da Iya ta saka aka yomin rubutu wai na dangana,ni dai duk da haka ban dangana ba. Aliyu zaune a kan kujerar shi ta office,duk da ayyukan da ke gabansa da kuma matukar son aikin shi, ya kasa yin aikin. Baya ya tura kujerar shi ya jingina da bango yana tuna tun daga shigar sa dakin Sadiya zuwa yanda ta zube a sume ya kwashe ta zuwa asibiti,ko da uban shi ya mutu bai yi kukan da yayi saboda cin amanar da Sadiya ta yi masa ba.A fili yake fadin,Sadiya dame na rageki?meye bana miki,me yasa zakibi wanina ina mijinki?Ya kalli saman silin,inasonki Sadiya,saidai bazan iya zama dake ba,ya mike tamkar an tsikare shi y nufi kofar fita,kai tsaye gida ya nufa,kmar yanda ya zata yaran suna zaune guri 1,Mama ta kwantar da kai a cinyar Kausar shima Al'amin ta kafadarta yasa kanshi,ya tsugunna gabansu.Kausar yaku ka zauna anan? ina kayan wasanku? Ta dubeshi da wayayyun idonta,Abba ka taimake mu ka kaimu gurin Momy,kaga Mama kuka ta gama yi yanzu,karya nayimata nace kaje kawotane. Ya rungumesu,nace kuyi hakuri zan kaiku ina Auntynku? Khausar ta ta6e baki,tana ciki.ya dafo fuskar Al'amen ga mamakin shi sai yaga idon yaron biyu yace kunci abinci? Khausar tace a'a bama jin yunwa.yasa hannu ya dauki Mama jikin yarinyar zafi rau ga dukkan alamu bata da lafia. hankalinshi ya sake tashi,ya kira Mujidat wadde ke can kwance kan gado da yaranta tana faman yin sana'ar tata chatting da abokanta,ta tura wayarta a kasan fiilo,sannan ta tashi,yace yaya za'a bar yarannan?tace to ya zanyi musu,suci abinci sunqi,na kunna musu TV sunki,tome zanyi musu? ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Yace ki dauko hijabinki mukai yarinyar nan asibiti,bada son ranta ba suka tafi,,anbata magunguna har da allura,sannan suka dawo.ranar dakinshi yayiwa yaran masauki,Mujidat anyo kwallia anzo dakin miji sai ta tarar da yaran kwance kan gadonsa,ya tasa su ya zabga tagumi,turus ta tsaya,Anan zasu kwana? ba tare da yadubetaba yace eh.tsaki taja sannan ta juya zuwa dakinta,Wannan ta zamar mata baka,kuma tsanar yaran ta ninku a ranta,tana murna ta kashe maciji ashe bata sare kanba,dole ne tayi wani abu akan yaran nan,shikuma sam bai runtsaba yatasa yaran yana kallonsu hawaye na bin kumatunsa,bai san ko na mene neba hawayen,na tausayin yaran ne ko na bakin cikin da uwarsu ta kunsa masa?ckin haka Mama ta farka,Momy kawai take kira,hankalin shi ya sake tashi,zafin jikinta na nan,ya bata magani yasata a kafada,Kausar ma tatashi ta zauna tsakiyar gado tana kallonsu,itama kukan take amma na zuci,dakyar Mama tayi barci,sannan yaje kusa da Kausar ya dafata,'Yata kiyi hakuri kar karkiga laifina,mamanku ce ta jawo hakan,Khausar tace metayimaka Abba?intayi maka laifi ne Abba ka yafe mata,kaji?yaushe zaka kaimu,Anty bata sonmu Abba,yarungumeta,kiyi shuru zan kai ku kinji,amma sai kunyi hakuri kun dan kara kwana 2 kinji?Haka yayita lallashinta har tayi bacci. Hudu daidai aka bukaceshi wurin aikinshi, sakamakon yan fashi da suka shiga wani gida,dole y fice zuciyar shi cike da tunanin yaran.Mujidat kuwa yana fita ta koma gurin dan ta tare da cewa babu wanda zai hanani bacci,tanajin lokacin da Mama ta tashi,tana ta kuka amma matar nan taki fitowa,Khausar ta farka taje ta dora kan Mama a kan cinyarta dan bazata iya daukar taba tana ta jijjiga ta tana cewa yi shiru Mama zan kira miki Momy,in kira miki ita?tayi shuru. Al'amin ma ya tashi ya zauna,kashi da fitsari mama tayi,Khausar ta rasa yanda zata yi gashi jikin Mama y saki,ba zata iya daukarta ba,haka suka tasata suna kuka,har gari ya waye.Khausar ta je dakin Mujidat ta same ta tayiwa danta wanka tana bashi madara,ta ce, 'Anty Mama ta yi kashi. Mujidat ta dalla mata harara, sannan ta ce, 'To ina ruwana? Kije ki wanke mata. Khausar ta dawo da kuka, suka ci gaba da zurawa Mama ido. Fitar Aliyu zuwwa takwas na safe ya kira Mujidat sama da sau biyar yana tambayar yaran, tana fada masa cewa suna bacci har yanzun basu tashi ba. Badon ya kira ta cewa gashinan ba to da zai samu yaran a yanda ya bar su, ko kuma yanda suke. Jin cewa ga shi nan sai ta nufi dakin da gudu ta dauki Maman zuwa bandaki inda ta shiga wanke mata tana yi tana zagi,da ta fito sai da ta rankwashi kan Khausar wai me yasa da ta ji kashin ba ta kai ta bandaki ba? Kausar din da Sadiya ke yi wa wanka yau ita ce da yin wanka da kanta,sannan ta yi wa kannanta. Maama tana ta rawar sanyi, Mujidat dama tun da ta nade zanin gadon ta aje tare da cewa. In ubanku yazo dole ya wanke ko inyardashi. ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Tana hada musu tea ya shigo,duk suna zaune rakube lungun kujera, Mama tana manne jikin Khausar, ya isa gurin ya dauke ta.Mama ya jikin? Khausar ta soma kuka, 'Abba don Allah ka kaimu gurin Momy, kaga Mama bata da lafiya, tayi kashi na fadawa Anty sai ta koreni, kuma har ta dokeni. Ya kalli Mujidat rai a bace, da sauri ta ce, 'Ta shigone ba sallama, da yake ta san tun a gaban uwarsu in sun shigo ba sallama yana korarsu yace suyi. Khausar tace Allah Abba nayi sallama. Nan yashiga ruwan bala'i, ya ce itamafa zai iya rabuwa da ita kan yaranshi, ta soma kuka duk abin da take yi baya gani, ta aje hada Tea din ta nufi dakinta,nan ya hada musu kawai suka sha da kyar, sannan ya shiga gurinta. Ya ce shi dai ya roketa ta duba masa yaranshi amma in har son datace tanaymaasa na gaskene, tsakanin mata da miji nan da nan ya lallabata suka shirya, kuma tayimasa alkawarin lura da yaran.Tun daga ranar sai ta dauki salon da mata da yawa sukeyi,in yana nan ta nuna kulawa in baya nan sai zagi, hantara gami da kyara. Hakan ya sa shi sakin jikin cewa zata rikesu, har ma ya daina yarda da korafin Khausar na cewa ta musu kaza, ta yi musu kaza. Cikin wannan halin ya nemi makarantar boko yasasu, sannan ya samo musu malamin Islamiyya,sai dai sam yaran tamkar kurame ko sun je makarantar basa magana bare karatu,in an tashi break sukan hada kansu guri guda, kallo daya zaka yimusu kasan suna da matsala. Ni kam zuwa yanzun an samu wata biyu rabona da yarana har na dangana da kukan fili sai na zuciya. Haka nan kullum cikin tunanin su da ambaton su tare da yi musu addu'a Allah ya kare minsu. Wani dare nayi mafarki wai Mama ta rasu, tun Asubahi nake kuka, Iya ta yi ta lallashina wai taci ta koshine, duk da haka shida daidai na kira Anty Abida nace tataimakeni tabani Yaya Usman, tabani shi nace, 'Yaya ka taimake ni ka je ka dubo min yarana, ina zaton akwai wadda ta rasu a cikinsu,dan na yi mafarki. Ya ce, Sadiya nutsu ki kwantar da hankalinki. Nace, Yaya don Allah zakaje? To shi kenan zanje jibi ranar Lahadi. Na ce, To yaya na gode. ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ina ajiye wayar ya kalli Abida 'Wallahi ina tausayin yainyar nan kinsan Allah banda ita, wallahi bazani inda aboki yake ba,domin ranar da zai bar garin nan sai da naje na sameshi, ba yanda ban yi ba a kan cewa ya bar yaran gurin uwarsu,sai ya ce shifa sam bazai bar mata yaran shiba,tunda ita iskanci ta zaba,nace masa baka da tabbas, kana yin abu sai ka ce bakaje makaranta ba, wai kuma kana jami'in tsaro, ka gaggauta maido da auranku ta hanyar sake daura wani,domin idan ba matata ba ce nasan cewa ba za ta iyaba. Kin san me ya ce? Abida ta ce, 'A'a. Usman ya ce, Budar bakinsa sai cewa yayi ba zan maida taba,kaima kana da dama bai haramtaba inka shiga layin zawarawa,sai ka aure ta kasata gidanka. Abida ta zaro ido tare da rike haba 'Lallai Aliyu ya dauki abin da zafi. Usman ya ce, Shi duk ya manta abin da ya yi na zaci yarinyar nan za ta tona masa asiri,saboda abin da yayi mata, amma da yake 'yar halak ce. Abida ta ce, In nice Allah saina tona. Usman ya ce mata, Da yawama bazasu shanyeba, ita wannan yarinyar daban ce, amma bazai ganeba sai nan gaba (Nasan dayawanku kuma bazaku iya abin da Sadiya tayiba ko idan kuma da wacce zata iya ta fada muji! Duk da banayiwa kowace mace daga cikin fatan makamacin wannan rayuwar...ANaM) Abida ta ce, Inzaka je muje tare ina son ganin yaran. Yace bari mugani. Har gida Yaya Usman yazo yayi ta lallashina tare da daukar min alkawarin zaije ranar Asabar ko Lahadi, sannan ya ce ya yi alkawarin binciken duk wanda yayi wannan kulli. Cikin kuka nake masa godiya. Haka kuwa ranar Lahadi Anty Abida ta kirani ta sanar da ni cewa gasu a hanyar Abuja,cikin raunanniyar murya nace. 'Anty ki taimakeni in kunje ki kirani mugaisa. Ta ce to. Na san ba kowa zai fahimce ni ba, wasu za su ce na cika kawa zucin 'ya'ya, amma duk wadda ta taba shiga irin wannan halin ina nufin ta rabu da 'ya'yanta, ba wai ta yi tafiyane tabarsu taje ta dawoba, ba wai sunje hutubane, sakinta akayi,sannan aka kwashe mata yaranta dole zata dandana irin abin da naji, ko nake ciki yanzun. Ina ta zaman jiran kiransu. Sha biyu da 'yan mintuna Usman ya kira wayar Alliyu,a ringing na biyu ya daga suka yi sallama a tare, Usman ya amsa,sannan yace, Aboki ina zan same ka,ina Abuja yanzun haka. Aliyu ya ce, Ina office ko zaka karaso? Aliyu ya ce, Shi kenan.Sun sameshi bakin hanya sannan suka karasa gidan.Abida sai kallinshi take duk ya rame suka gaisa, sannan suka isa gidan.kamar kullum yaran suna takure a gurinda suka maida tamkar gurin zamansu,wato gefen kujeru,Mama da Al'amin duk sun jingina jikin Kausar wadda suke ganinta tamkar uwa a garesu,domin itace take yi musu duk abinda uwarsu take musu,in har kaga Mujidat tayi musu wani abu to tabbas mahaifinsu yana gidan. Ko da sukaji sallamar mahaifinsu basuyi wani yunkuri tashi ba don taryarsa.sam Abida har ta zauna bataga yaran ba,Aliyu ya kalli gurin. ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Khausar ku taso mana,yaushe zaku daina zaman gurin nan? Abida ta zaro ido tare da mikewa"Khausar!yaran suka mike da sauri dukkansu suka rugo da gudu tare da rungume Abida sannan sukayi gurin Usman,Aliyu ya cika da mamaki,ya manta rabon dayaga yaran haka suna murna ya nufi ciki kiran matar, Abida duk da cijewar da takeyi sai da hawaye suka soma yimata sintiri,Usman ya kalle ta ya girgiza kai alamun tadaina, amma ta kasa saboda yanda yaran sukayi baki suka rame,gashi ba wata cikakkiyar tsafta,kitson kan su Khausar duk ya tsufa,ba'a ko ganin layin kitson.ta tuna yanda yaran suke kansancewa tsaf cikin tsafta da tsantseni kowa sha'awarsu yake,ta dauki mama ta rungume.Khausar tace,aunty maman mu fa? cikin rawar murya tace,lafiyarta kalau,tace a gaidaku,Al'amin yace yaushe zatazo? Khausar tace,kai sunzo tafia damu ne.ta kalli Usman Uncle ai dai zaku kaimu gurin Momy ne ko?kafin Usman yayi magana,Aliyu suka fito da Mujidat tana sanye da riga da siket na shadda mai ruwan kwai,shikuma yana sa6e da Abdul,wanda aka tsafta ce shi ckin jeans blue da riga ja,sai wani dacin rai takeyi.ta zauna tana gaida su cikin yatsina, Usman ne ya amsa Abida kam ta kasa magana don bakin ciki. Usman yayi mata sako cewa don Allah ta nutsu,sabida yaran sun soma kuka suma.Aliyu ya kalli Mujidat,a kawo musu abinci da abin sha mana,ta tashi can ta kwalawa Khausar kira da sauri ta tapi,sai ga ta da pure water leda biyu da dan kwalin juice,sai kofi 2,ita kuma ta fito da kula yar madaidaiciya. Abida ko ruwa batayi burin shaba,bare abinci,Usman dai ya dan kurbi Juice din da Aliyu ya tsiyaya ta mika masa,daidai lokacin ni kuwa na kasa hakuri nakira layin Abida,ta dauka yanda naji muryarta sanyi kalau,sai na soma kuka,nace Aunty ta mutu ko? Abida tace a'a lafiyarsu lau,bari kijisu. Ta kamo Kausar zoki gaida Mamanki,cikin doki ta amsa tace Momy,nace na'am...'kukan yaki tsaya min,cikin rishn nace kausar.ita ma yarinyar ta saka kuka tana cewa Momy don Allah kizo ki tafi damu,hankalina yakara tashi nace,Khausar kuyi hakuri kinji?ki lura da yan uwanki kinji? Cikin kuka mai tsanani tace,wayyo Momyna! don Allah zamu zo Momy. Abida cikin hawaye sharkaf ta amshi wayar ta rungume Khausar,Sadia yaya zakiyi haka?kinsan zaki kara tadamin hankali ne,kika kirani,nace yi hakuri Aunty,Aunty kibani Al'amin da Mama.tace a'a bazan baki suba dan ganin Khausar tana kuka suma gasu nan sunayi.Khausar ta sake janyo hannun Aunty Abida tana cewa,Momy don Allah kinji Momy!!! Tilas na kashe wayar na dasa sabon kuka,iya dake kallona itama hawayen take sharewa tana cewa "Sadiya kidangana da 'ya'yan nan. Na kalleta Iya kitayani addu'a Allah yaba ni hakurin jure rashin su kinji Iya? Tace to Sadiya ta taso ta kamani ta rungume tana lallashi tamkar yarinya karama. Su kuma a can Aliyu ya kalli Khausar meye abin kuka? Mujidat dake gefe ta tabe baki tare dace " a to" Ta gatsina hanci gami da hararar Abida tana magana kasa kasa Abida tace Kuka ya zamar musu dole wadannan yaran kanana a ce an rabasu da uwarsu? Aliyu na rokeka arziki kayi hakuri ka bamu yaran nan mutafi dasu Uwarsu tana cikin damuwa Yatabe baki Kadan tagani ma kin san Allah bazan bada yarannanba ko zasu mutu daga ita har su,Usman yadagawa Abida hannu alamun tayi shiru sannan yakalli Aliyu Aboki zamu tafi daman munzo ganin yarane,ya dauko ledar gefenshi Khausar yi shiru ga tsarabarku tana sheshshekar kuka ta amsa tana ji da dan nauyi har ya mike ya cewa Abida tashi muje sai kuma ya tuna da binciken shi yadawo yazauna yace Aboki ina son wani taimako daya Aliyu ya kalle shi inajin ka. Yace zaka bani sunan wannan account din zanyi searching zan gudanar da wani bincike Aliyu yaruntse ido wallahi bana son a tunamin komai game da ita ban san tuna account din nan. Usman yace bazan samu ba kenan? Aliyu yakalli Mujidat dauko min laptop dina sun kunna inda suka fito da komai. Aliyu yadauke kai inda Usaman yashiga bincike cikin sa'a akwai lambar kuma ta MTN sannan shima Malam din ya dauki lambarsa haka nan yadauki ta wanda yakawo gulmar wanda yace sunan shi Sulaiman yakulle komai sannan yamike. Mujidat tazaro ido tana kallon Usman cikin zuciyarta tana tsine masa, suka mike suka tafi Abida tana kuka su Khausar na kuka haka aka rabu yaran suka ruga daki suka dora sabon kuka. Mujidat da gudu tashige daki lokacin da Aliyu yatafi rakasu Usman takira layin Jamilu daya dauka yace lafiya? Ina ta kiran layinki kin ki dauka don kada ki bani cikon dubu 2 na koh? Tace zan baka mun tashi daga kaduna ba shirine zan aikowa Anty Ramata zata baka amma kana ganin asiri bazai tonuba? Yayi Tsaki Sungama su hkr Mujidat ta sauke ajiyar xuciya sannan takashe wayar. ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Aliyu yakalli Usaman Aboki na godefa tunda abinnan yafaru banga wani nawaba sai yau ga tunanin Iya a xuciyata bansan ya zan tunkaretaba dan nasan Sadiya ta fadamata abinda nabinne. Usman yayi murmushi, ay Sadiya mutumce wallahi har yazu Iya batasan wancen zancenba kayi mamaki koh? Aliyu yayi ta kallon Usman tunanin cewa zata fada shiyasa ya tattara ya bar kaduna ya maimata bata fadaba? Usman yace ko daya Aliyu yace Uhm duk na zata ta fada. Usman yace shiyasa nace kayi bincike kan wannan laifin dakake zarginta. Aliyu yace tafa aikata laifinnan bazanyi mamakiba sabida shaidan ba rago bane, nima nazaci zan tsinci kaina acikin haka?Usman yace inma gaske ne bazakayimata adalci ba? Aliyu yace adalcin kenan nayi mata na saketa kalau ba tare danayi mata dukan hauka ba sannan banda ta fada na so in ramawa kura aniyarta wato in bar zancen tsakaninmu inkuma dauki nauyin zunubin zagin da za'ayi min na sakinta batare da tayi min laifi b kawai sai ta tona. Usman yace Aliyu kenan bari muwuce Allah yabayyana gaskiya inga yanda zakayi Aliyu yace wahala kawai zaka sha amma gaskiyar ce tabayyana in kalura da hirar data gudana atsakanin ta da malamin. Koda suka tafi ya jima bai shiga gidanba yana mamakin yanda Sadiya taci gaba da rufa asirin shi yayi ta ganin kiran kiran yayunsa. Yaya Sulaiman, Yaya Sani, Yaya Zakari, kai har kawu ya kirashi amma ya ki dagawa nashi ganin asirin shine yatonu zasu kira suyi Allah wadai dashi to shi in ya dauka dabatun sakinnan ze kare kanshi Aliyu Kenan. Koda Anty Abida ta dawo sam bata nunamin cewa yarana suna cikin matsalaba, illa fadan da tayimin na kukan danayi tace shine yasa su kuka. Jin hakan sai na kwantar da hankalina kadan, don har Usman ma yace min kada in damu suna samun kulawa. Haka na dangana sai dai duk na rame yarona kawai ke tafka kibarshi har mukayi kwana 70 nace baxan koma aykiba,Iya tazare min ido dole nakoma yanzun mota nake hawa zuwa gurin aiki dan ban waiwayi motarshiba. Ranar asabar ina zaune a tsakar guda yarona yana cinyata na kifa shi ina karanta dan karamin alkur'ani mai girma suratul Bakara kamshin turaren yaya naji kafin sallamar shi tabiyo baya badon na san mahimmancin amsa sallama ba da baxan amsaba, sannan banko dago kainaba bare nadube shi yayi sallama dakin Iya tana ciki can kan gado don haka bata jishiba shima din be tankaba yashiga dakin. Natashi nagoya dana naja Hijabina a igiya na dauki pose dita da yan canjina napita sai gidan Aysha, taganni hankali tashe tace lafiya har yanzu baki kwantar da hankalinkiba? Haba Sadiya. Naxauna hawaye suka soma zuba daga idona nace ni na hakura Aysha yayane yazo gidan yanxun, wallahi shine yafama min bakin cikin daya cusamin,ta dapani yi hakuri meyace? Nace bamu ko kalli junaba fitowa nayi dan ko ganinshin shi banasan yi. Aysha tayi ta lallashina tana bani hakuri tace kin fadawa Iya shima abinda yayi? Nace har abada baza aji daga bakinaba wannan ya wuce saidai taji gurin wani. Ina gisan har dare sannan suka rakoni ita da Bellonta, itama dai tana tayi min korafin cewa Bello yanzun sai bakin halaye yake shigo mata dasu, ya soma doguwar hira sai yakai sha daya bai dawo gida ba yayi ta 'yan daure daure da fadace fadace. Nace lallabashi zaki Aysha kiji ko kin masa wani laifi ne kar ki dauki fushi da mijinki karamar matsala tazama babba, kar kiyi sanadin dazaki nesanta kanki da yaranki ni na isheki misali Aysha 'ya'ya sune rayuwar uwa kamar yanda uwa take rayuwar 'ya'ya yanxun duk macen da bata tare da 'ya'yanta ina tausaya mata dan na dandani ciwon dataji. Cikin bacin rai nasamu Iya nace, Iya ya ne? Tace Sadiya ina kikaje? Nace gidan Aysha natafi kiyi hakuri banfada miki ba wallahi ganin yaya ne naji bazan iya zaman gidanba shiyasa natafi. Tace baki batamin raiba Sadiya bacin ran Ali ne yaron nan na zata yayi nadama ne ashe zuwa yayi yabani hakuri, nace me kayimin? Ni awa zakazo bani hakuri? Ali banzaci zan sake sakaka a idona ba. Yace sabida me zaki ce haka Iya? Na tafine don ki huce sannan inzo in baki hakuri dan na san cewa babu wanda zai fahimceni ko yabani gaskiya akan sakin danai wa Sadiya duk kuwa da cewa yin hakan ba laifi bane. Iya tace sai na tari numfashinsa cikin gatse nace to dama Ali waya ce kayi laifi? Ko guda banga laifin kaba don ka auri mace kana sonta lokaci guda kuma kaga ka daina sonta ko ta maka tsufa ka sake ta sai ace kayi laifi? Laifin da kayimin daya ne bata min ita da sharri wai tana bin maza wannan kazafi yayi min ciwo sosai domin yarinyar nan har ta gama kuriciyarta a cikin gidan nan kaganta kace kana so ka aura bata taba dauko min maganaba. Iya tace Sadiya yau har nauyin na aje gefe na tsakanin da da mahaifi na tambayi gadanga cewa ko ba budurwa kasame taba? Sai ya sunkuyar da kai nace in ba budurwa kasameta ba sanar dani. Yace Iya duk ba wannan zancen bane ai mutum yakan canza kuma ni fara koyarwar ta dinnan ne ta hadu da abokan banza. Iya tace na ce dakata bata tare dakowa nabanza kai dai ka gaji da ita ka saketa ka kuma hada mada da sharrinka na 'yansanda to kaje Allah ze sakamata ina raye sai naga sakayya sannan 'ya'yanta in kun lura dasu kuda Allah inma kun wulakantasu kuda Allah. Ya kasa magana sannan wai ina jaririn? Nace yana gurin uwarsa ai danaga baka waiwayeshi ba na zata zakace ba danka bane? Yace ni bance ba Iya, yaciro kudi ya aje wai gashi kibata sabida siyan wasu abubuwan na yaro Iya tace dauki kudinka babu abinda muka rasa yayi shiru can ya sake cewa. Ina kara baki hakuri iya nace kai ne da hakuri amma dauki kudinka in ba so kake kaga bacin raina ba,ya dauka yafita.Na sauke ajiyar zuciya nace, Iya na gode dabaki karba ba na sani sosai Iya cewa bashine yayi min sharriba wasu ne daban amma takaicina yanda yakiyin bincike kuma yayarda cewa nice, kobe sakeni ba aure baya yiwuwa da zargi.Iya tace ay na gaya masa nace lokacin

Chapter 20 of 25