Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
nata fadin kayi wauta. Suna tafe shi da Usman shiru babu mai magana saidai shi Usman ranshi Fes yaji dadi komai yafaru a agaban Aliyu. Koda sukaje gidan Usman din Aliyu Yakasa yin tinanin komai,yamaji cewa yakoshi,duk da irin yunwar dayakeji, idanunshi sunyi jazir. Usman yace,"Aboki bisimillah" Aliyu yace,"haba aboki, yakake tinanin zan iya cin wani Abu a halin danake ciki? Don Allah kaima ka ajiye muyi magana." Usman Yayi murmushi, sannan yasake cika cokalinshi ya tura baki yace, "wace magana zamuyi." "Ta Sadiya mana , gaskiya nayi wauta danaki natsaya nayi bincike,kuma saida tace inbincika." Abida dake jiyosu batasan sanda dariya ta subucemataba, saidai taji Aliyu yana cewa "au! dariyama nabaki Madam?" Abida tace, "yanda kake maganar ne yabani dariya." Usman yace, "ai abin dariyarne,ni yanzu bazan saka bakinaba cikin wannan lamarin, Sadiya Alkawari nayimata zanyi bincike ingano masu hannu cikin wannan lamarin kuma Allah ya taimaka nasara tasamu,daga nanma sai can gidan sabida insanar da ita,saikuma mudora daga inda muka tsaya kan maganar auranmu." Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Aliyu yakalli Usman cikin tsananin bacin rai yace,"kai nalurafa ba kasan kawaiciba ko?" Usman yace, "kamar yaya?" Aliyu yace, "wallahi dan kaine kunnuwana suka jure jin kanacewa zaka auri Sadiya." Yamike tsaye,"Wato damacan kanason matata tin muna aure ko?" Usman yace, "sam karkayi wannan tinanin, hasalima ka manta kaine kabani shawara in aureta lokacin danake lallabaka kamaida ita? Kace ai bai haramtaba inna aureta, katuna? Shine kawai mukayi shawara da Abinda,kuma Alhamdulillah zance yasoma bisa...." Aliyu ya harari Usman, sannan yaja tsaki yanufi waje yanacewa, "Kadakatar da Neman aurenka." Usman yace, "Sabida me?" Aliyu wanda yakai bakin kofa, "najanye shawarar dakace nabaka,inkuma kaki ji kada ka zargeni akan abin dazaibiyo baya." Usman yace ," aboki kazo muyi magana a zaune" Tsaki Aliyu yayi tare da bugamusu kofa yayi waje,ranshifa yayi zafi.,dama Habu yagayamishi Usman ke zuwa gurinta duk kwana uku,saidai sam bai tsammaci yanazuwa don sontabane. Yashigo gidanmu inna shirin fita zuwa Isalamiyyar 'ya'yana tada domin inmaidasu, yanda naganshi yashigo a sukwane nadan tsorata.yace, "ina iya?" Nayi masa banza,yashiga daki tare da cewa, "zo Sadiya!" Yayi maganarne cikin taushin murya. Nashiga. Yace, "Sadiya don Allah kinyafemin nayi kuskure,ashe Mujidat ce duk ta kullamiki Wannan Sharrin?" Iya dake cikin daka tace, " Usman yakira waya yayimana bayani yanzunnan,binciken da kakasayi shi yayi kuma Allah yatoni asirinsu." Aliyu yace,"Usman ai ba don Allah yayiba,yayine don manufar kanshi,kuma wallahi Usman inbai kiyayeniba za'ayi danyen aiki"." Iya tace, "kai Gadanga da girmanaka kakeyin wannan zancen,duk taimakon dayayi baka ganiba?" Aliyu yace, " Bansaniba". Yanunani. "Kekuma zanfadamiki wallahi bake bashi." Namike, "baruwanka da rayuwa ta don ni yafimin kai." Iya tace, "sau dubuma,kuma wallahi innaji wani abu tsakaninka dashi Sai ranka yabaci,tsakaninka dashi sai godiya." Yace , "Iya matata fa yakeso,banda cin amana yazaice yanason Sadiya?" Nace, "Ok! Sabida bakasona shikenan kar kowa yasoni ko?inkaga ban auri Usaman ba saidai inbansoba kokuma shi yafasa....." Ban ankaraba sainaga yatasomin zai dokeni,nagudu nayi bayan iya innacewa, "Wayyo Iya zai dokeni" Yatsaya yana huci, "ni kike gayawa zaki auri Usman?" Iya tace , " tafada , hauka kake kadoketa?" Yace, " inna tacigaba da yimin irin wanna zancen bashakka zan jimata ciwo,kuma Usman zaisha mamakin abin da zanyi masa." Nace, "karkaga wani kana dansanda,inkatabashi baza'a barka ba." Yace, "kimin shiru,karkibari inzonan wallahi zan ballaki." Yajuya fuuu! Yafice rai a bace. Nasauke ajiyar zuciya,nace, "wallahi natsorata ban manta da irin fishinnan ba,irinshi yayi lokacin da akayimin wannan sharrin,jikinshi har rawa yakeyi, Allah yatemakeni badan keba da yau naci duka." Iya tace, "tinanina yanzu Usman,ko kiranshi zakiyi yanzu kicemasa inna nemansa?" Nace , "to , bari inkirashi." Tace "kishin banza ne ke cinsa a rai. Nace , " Dama yabar Usman,danni ba auranshi zanyi ba, na fadamasa hakane don kawai yaji haushi.shima Usman din ina zaton dan yaturawa Yaya Haushine yace yana sona." Iya tace, "banda matar shi dake tsakanin ai Usman mijine." Daidai lokacin kiran yashiga, yadaga ,nace,"Yaya Usman wai kazo inji Iya" "Lafiya?" Cikin daga murya. Nace "lafiya,kodai ba kalau ba." "Ko Abokinane?" Nace, "eh, ai yacene wai kace kana sona,a ina yaji?" Nina fadamasa,Kice iya karta damu, ni dashi babu a binda zaifaru,nasan dama dole yayi haka,ni dama hakan nakeso." Nace, "to shikenan,sai anjima" nakalli iya bayan nakashe wayar nace, "yace babu abinda za'a faru." Nandai mukayi ta tattauna zancen. Shikam yaya police yakoma yasake bincika Jamilu ya tabbatar da gaskiyar lamari,sannana yawuce Zuwa Abuja cikin damuwa. A daki ya kulle kan shi yana tinanin tsantsar rashin kyautawar da yayiwa Sadiya,baimasan ya zaiyiba.ya daga waya yakira layin Usman har takatse yana kallo bai dagaba,a karo na biyu ma saida takusa katsewa sannna ya daga. Aliyu yace, "Usama nakirakane ince kafita harkar matata,zan dawo da Ita dakinta." Usman yace, " innaki fa?kawai Mallam ka shiga layi zawarawa nima inna ciki mai rabo Yasamu,kuma banda abunka wannan baikamata yashafi zumuncinmuba." Aliyu yazo iya wuya,ranshi yakai matuka gurin baci,yace, "ok! Haka kace? To shikenan kajira a abin dazai faru." Yakashe wayar yanata kai kawo a dakin,zuciyarshi tagama sakamasa abinda zaiyi,kawai zuwa zaiyi yasa akama Usman, baza'a fito dashiba har Sai anmaida auranshi da Sadiya,inyaso saiyaga da wanda zaija. Mujidat tasauka a garin kaduna kai tsaye unguwar Mu'azu ta dosa,muna tsaka da cin abinci kwanonmu daya da Yayana,tire ne dan babba nazubamana,Danwake mukayi munaci muna hira,Iya kuma tana gefe tanacin sauran Tuwon Masara da Miyar Kuka. Kwatsam sai mukaji sallama,zunbur namike ganin Mujidat nace, "me kikazo yi gidanmu?" Tace, "Ba gurinki nazoba,gurin sirikata nazo." Iya tamike itama,"karki shigomin gida,juya." Su Khausar kuwa tini sun ruga daki sun rufo kofa,nace ," azzaluma kinje kin cutarmin da yara duk da irin taimakon Dana yimiki." Mujidat ta sheke da dariya sannan tace, "kikadai taimaki mijinki,yanzu kuwa nazo na kwance kullin da kukayi ke da mijinki." Nace, "Ina ruwana,yanzu mijinkine ba nawaba,inkinso ki tona,inkinso ki rufa." Iya kawai ta tsaya tana kallonmu tare da sonjin asirin da ake cewa za'a tona." Mujidat ta kalli Iya tace, " Tsohuwar ba zama nazo ba, nazone in fadamiki gaskiya tsakanina da danki." Gabana yashiga faduwa,tamkar in tashi in toshe bakinta kar ta sanar da Iya taji bacin rai,banason 'ya'yana suji abin da ubansu yayi. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Mujidat tace, "Danki Aliyu ciki yayimin tin a Ilori,yace inna yarda dashi zai aureni.Yayi min ciki ya taho, nikuma na biyoshi,shine sukace inyi shiru kar ince haka zasuce mijinane ya mutu yabanni da ciki,kisani Abdul jikankine." Na kalli Iya wadda takasa magana, na iso gurin ta na kamata nace, "Iya zauna karki damu." Iya ta fincike hannuwanta tace,"Sakar min hannu." Ta nuna mujidat "fita tinda kinfadi sakonki." Mujidat tace,"Yanzu kuwa zan tafi burina yacika tinda kinsani." Nace , "To me yadame mu? Saiki fita ai ko?" Ta saka dariya, kidena min korar kare,domin ko bana auren yayanki uban 'Ya'yanki inna da yaro daku." Nace, "naji jeki." Kafin insake magana Iya ta isa bango ta dafa,na isa gurin ta,sannan nadauki wayarta na kira Yaya Usman , nacemasa, "dan Allah kazo in kana kusa,Mujidat tazo ta dagawa iya hankali." A zaton ta Yaya Aliyu nakira,don haka saitafice da sauri.Allah yasa Yaya Usman yana kusa ya iso mukayi ta bata baki. Tace, " Ashe dake za'a hada baki a rufeni?" Nace, " Iya kiyi hakuri, alokacin ko anfadamiki babu abinda hakan zai kareki dashi sai bacin rai." Usman yace, " Iya lokacin abin da zaifaru yariga yafaru." Sai ga hawaye yasoma zuba daga idanunta, tace, "Wato shi Aliyu ko yaushe shi zaidinga sani zubar da hawaye " Usman yace , "sai hakuri iya" "Nagaji da hakuri da laifukan da Yake aikatamin,ya batawa zuri'a ta suna,ya gurbatamin zuru'a yabani mamaki." Kukana ya tsananta,nace, "Iya kiyafemasa." Tace,"kema ai a gurina me laifice balleshi,kike cemin inyafemasa." Usman yaciro wayarsa yakira laying Aliyu, lokacin yagama shirya yanda zaisa a kama masa Usman din domin bazai yuwu a kamoshi batare da wani laifiba,dolene a nemi laifin da za'a joganamasa,kamar kada yadaga layin, saikuma yadaga cikin isa yace. "Malam Lafiya?" Usam yace, "kana inane yanzun?" Cikin jin haushi yace, "menene kake son jin inda nake? Innaso fa ka manta kasan ni." Yace, "kafin in manta nasanka din kazo ga matarka nan tazo ta kunce kullun da Kuke ta boyonsa yanzu haka Asibiti zamu kai Iya." Tace, "daina kiransa Usman, na yafeshi cikin Yayana,ya nemi wata uwar shi ba zuri'a ta bane..." Ta fashe da wani kuka mai ban tausayi. Aliyu duk yaji wadannan kalaman dama wasu,don Usman sam ya manta bai kashe wayar ba,sabida wata irin sheshsheka da Iya tasoma. Yace, "Sadiya dakko mayafinki da nata muje Asibiti." Ta dakko,suka kama iya zuwa Mota. Sai da Sadiya tace zamu bar yaranne ? Sai yaciro wayar tare dacewa, "bari inkira Abida tazo ta kwashesu," a lokacinne yaga bai kasheba don haka sai yakashe,sannna yasake kiran Abida. Aliyu yanata kai kawo cikin ofishinsa gumi yajika rigarsa sharkaf,ya balle duk botiran gaban rigarsa, ana kallon singiletinsa,Sam bazakace da Akwai AC a cikiba. Kiran wayane yasashi isa gurin wayar,kawimishinane ke nemansa wai zasuyi wani dan meeting, a isa ofishin yana balle botiran gaban rigarsa,sai kwamishinan yabukaci daya zauna. Bayan ya zauna be suka gaisa da sauran mutanen daya gani ciki,fuskarsu ba boyayyabace 'yan siyasane na gwamnati me ci a wannna lokacin,wasu masu neman tazarce wasu kuma masu son sababbin mukamai.Aliyu fa ya hade rai sabida ya lura 'yan siyasan nanfa sun raina jami'an tsaro. Wanda suka wakilta yayi magana shine ya gabatar da kudirinsu na Neman goyon baya daga jami'an tsaro,su zama suna bangarensu. Kwamishina ya kalli Aliyu tare da bashi izinin magana. Aliyu cikin isa yace, "Ranka ya dade mu ba 'yan siyasa bane,bazaiyuwu mu cusa kanmu cikin harkar siyasaba,mu jami'an tsarone dole yazama muna tare da kowa ku da 'yan adawarku,bai kamata gwamnati maici dan kawai tana ganin tanada madafan ikon a hannunta tayi anfani da hakan gurin tursasamuba,mun San aikinmu,kuma inshaAllahu in zabe yazo zamu tsay kai da fata ayi zabe a gama lafiya.......zandakata anan Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Darajar Yayana4-04 Posted by ANaM Dorayi on 07:27 PM, 16-Apr-16 Under: DARAJAR 'YA'YANA _________________NA ___________HALIMA K/MASHI Wakilin siyasa yace, " amma mu muke daku tinda muke da gwamnati." Ya kalli kwamishina. "Ranka ya dade kai yakamata kace wani abu,sabida wannan mataimakin naka ya nuna karara baya tare damu." Yace,"zantukanshi suna kan hanaya,sai dai zamuga taimakon da zamuyi muku." Sai suka mike tsaye suna zantuka,wani harda Cewa, " kujerarku tana rawa,domin kunsan akwai nasama daku,kuma su namune inkunce Ku ba namu bane." Aliyu ya lumshe Ido,baiyi wani mamakiba domin yasan su basu da wani buri sai son kansu,amma indai yana nan da yardar Allah sai ya hana ruwansu gudu,zai dawo da martabar 'yan sanda. Bayan tafiyarsu kwamishina ya kalli Aliyu yace, "kamin dai-dai,shiyasa nakiraka." Gida Aliyu yanufa,sintiri yakeyi tare da kai kawo daga falo zuwa dakinshi,yarasa ta ina zaibi kuma wa zaikira yabashi shawara? Yazauna yaciro wayarshi yanabin lanbobin daya bayan daya yanason yaga wa yakamata ya canja abokin shawara madadin Usman. Yaduba har karshe baisamuba,wata zuciyar tace dole dai Usman ne zaibaka shawarar data dace. Tsaki yaja,sannan yabi shawarar zuciyarsa yasoma kiran layin Usman,duk dacewa shi yafi tsana a halin yanzu.Ringing biyu Usamna ya dauka,yace,"Aboki ya akayi?" Cikin tsana yace,"bawani zancen Aboki,nakirakane inji ya jikin mahaifiyata?" Yace,"da sauki,amma zaifi kyau kazo kadubata." Yaja tsaki ,"bayan kaje ka shishshige a gurinta don tabaka matata." Usaman yasa dariya,"Aboki ka aje kishi a gefe guda,muyi magana me muhimmanci, Sadiya allurace cikin ruwa,kaga kenan me rabo kadauka." Aliyu ya runtse ido,jiyake maganganun Usman na sukarsa cikin rai,amma dayake shawara yake bukata sai ya danne yace, "InshaAllahu matatace ni Daya." Yacigaba da Cewa. "Kana ganin inzo gurin ta ko Yaya?" Yace,"zaufi kyau kazo din don kabata hakuri." Yace, "kana ganin inzo yau ko gobe?" "Kabari sai jibima,domin lokacin ta dan huce," inji Usaman. Aliyu yace, "to shikenan zamudinga yin waya." Iya ta tara sauran 'ya'yanata tafadamusu abinda Aliyu yayi,kuma tace musu ba'ita babu shi,tacireshi daga sahun 'ya'yanta,nima da kyar na wanke kaina daga zargin datakemin wai na rufeta. Yaya Sulaiman yakira Aliyu yamasa Nasiha kan abin da yayi,Aliyu yabashi labarin yanda abubuwan suka faru,yakuma yimasa rantsuwar cewa yanzuma yadena.Yaya Sulaiman Yayi masa fadan girma sannan yace yaje yanemi iya gafara,don tadau zafi dayawa.Kwananmu Daya a asibita aka sallamemu,Yaya Usman da sauran 'ya'yanta sunbata kulawar data kamata. Na idar da Sallar La'asar na nufi kitchen domin dafawa Iya wake da Alayyahu sai naji sallamar Yaya, na amsa amma ba lallai yajiba,bankuma kalleshiba nacigaba da harkar gabana.Bakin kitchen din yazo ya tsaya,kamshin turarensa yacika kitchen din,nakalleshi cikin tsana. "Lafiya?" Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Yace, "in ina cikin damuwa da nakalleki sai inji ta yaye." Naja tsaki, "dan Allah kabani guri kaje kaji da kalubalen da yake gabanka." Yace, "Don Allah kitayani bawa iya hakuri nasan zaki iya shawo kanta." Nace, "eh, dama bakasan daniba sai matsala ta sameka wadda kake ganin nice zan iya yima maganinta." Najuya baya. "Malam kaje da matsalarka,Yanzu ni babu wata alaka tsakaninmu dazan iya yimaka wannana arzikin.jeka da kanka,innace mahaifiyarkace?" Ya tausasa murya, "Don Allah kizo muje innason muyi zancen gabadayane harda batun auranmu." Naji tamkar ya watsamin wuta,Nace,"Allah ya kyautamin,." Naja tsaki tankashima bata lokacine,don haka yagaji da surutunsa da banbakinsa ya kyaleni. Inna jiyoshi yanatayiwa iya magana tayi banza dashi,nasaka kujera bakin kofa na zauna,yayi ta bata hakuri,amma kala bataceba,sai datagaji sannan tace, "Don Allah kafitar min daga gida, Innaso insanar dakai tini nacireka daga sahun 'ya'yana, bana koson ganknka." Yace, Don Allah iya kiyi haku...." Ta katseshi, " inkanaso inyimaka baki to kacigaba da zama a cikin dakinnan " Tsam yamike yafito yanufi waje cikin damuwa, baifi minti 5 da fitaba yayomin text wai in yara sun dawo daga Islamiyya inshiryasu zasuje shan Ice cream,tsaki naja na aje wayar gefe. Shida da mintina,suna shigowa yana shigowa, saikace dama yana wajen yana jiransu,jin muryarshi duk yaran sukaje suka makalkaleshi harda Sadeq dake koyon rarrafe,sai daga hannu yake wai dole yagane babansa.Ina Mamakin yaron. Yace, "kuje kucire kayan makaranta kuxo muje shan Ice cream." Yarannan sai suka hau murna da tsalle. Khausar ta nufi iya tana murna tana cewa, "Iya zamu fita da babanmu." Wata tsawa da iya tayiwa Khausar ni kaina saida na tsorata,tace,"Ku tashi sama mana da Baban naku me yadameni?" Karshe dai da kayan makaranta ya tattarasu suka tafi harda Sadeeq. SaKu ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347i Tara saura suka dawo,lokacin sadiq yayi bacci,ni da iya wai har tsaraba yayimana don neman gindin zama. Yanda iya bata kalli ledarba, haka nima nayi saida Iya tafita sannan nace dasu Khausar Su dauka su hada datasu. A daren ne Alhajin nan yasake zuwa karo na uku,biyun ban fitaba,nace ace bana nan,Amma yau sainafita sabida nasan Yaya yana nan,tayiwu yazo zanso ya ganmu. Kwalliya nayi sosai, sannan nafita. Cikin wata dankareriyar Mota yazo sai kamshi Yake,na kwankwasa motar sai gashi yafito daga gidan baya yace, "ranki ya dade yau dai naci sa'ar samunki,amma naji Dadi." Nayi murmushi sannna na rage tsawo nace, 'ina yini?" Yace, "Lafiya kalau," Bayan mungaisa yace, "Mama tana ciki?" Nace, "Eh" "Inna son mugaisa." Tofa!,bani da zabi,dole saidai inkaishi din. Na shiga nagayawa Iya za'a shigo gaidata,tace, "toh" A gaban iya yazube ya gaisheta,itako Iya harda fadamasa cewa; ni marainiyace,dan Allah in aure ya hadamu yarikemata ni amana, saboda na wahala a gurin mijina na farko,shi kam sai yace ,yaji komai game dani, tinda ya ganni yasan innada tarbiyya sabida naki yarda inhau motarshi, mata yanzu da zakaga suna tare mota da kansu wai dan a ragemusu hanya! Yacigaba da cewa, "Sai danasa akaimin bincike akanta, kuma naji sakamako me kyau don haka nashigo da karfina zan aureta." Iya tace, "InshaAllahu, yanzu kaima yakamata insanka." Yace, "Sunana Alhaji Badamasi Yunusa,ni dan asalin jihar katsinane karamar hukumara Bakori,inna nan gwamna road da iyalina,matana biyu,yarana goma,ni ma'aikacine a matatar man fetir dake nan Kaduna." Iya tace, "to shikenan,Allah ya tabbatarmana da alherin dake ciki." Yace, "Ameen." Kan ya wuce saida ya ajiyewa iya daurin yan dari biyar guda daya. Nafito daga uwar daki dan innajinsu,iya tace, "da alama yanada mutunci,nace, "nalura tin farkon haduwarmu." nakoma gurinsa inda yacigaba da yimin zancen aure,shi bayason adauki lokaci,sannan yanason muma muyi bincike a kansa,bayan nan zai turo tinda yanzun mu ba yara bane da zamuyi ta doguwar hira,nace , to! Yabani lokaci nayi nazari da tinanin kafin ya turo din,Yace to yabani,nima haka yacikani da kudi,nayi nayi yabarshi yace Sam; dole nakarba. Yataka zai shiga Mota kenan Aliyu yayimana sallama,shine ya amsa nikam gabana sai faduwa yake. Yace, "Alhaji nazone inyimaka gargadi." Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Alhaji Badamasi yace, "name fa?"tare da dawowa da kafarsa. Aliyu yace," wannan matatace, dan Allah karkasake zuwa." Alhaji Badamasi yadubi gurin danake Yace, "Wannan ne?" Koda bansan meyake nufiba Sai nace, "Eh! Shine Alhajina,shiga motarka kayi tafiyarka sai munyi waya." Tamkar me jiran umarnina sai kurum yashiga mota tare da cewa, "sai kunjini ginbiya." A hankali motar ta silala ta dauki hanyar barin layin. Cikin zafin rai yasha gabana, "wato harma labarina kike bayarwa ko? gani dan iska!" Nace, "Eh!" Nacigaba da tafiyata." Yace kinsan Allah zakijamasa bala'i,zan tono laifukansa inmasa tarko yafada hannunmu,ai nasan shi." Tsaki naja nacigaba da tafiya inna cewa dadinta baka isa kayimasa abinda Allah baiyimasaba. Innashiga zaure shima yashigo, "Sadiya dan Allah tsaya kiji." ya tsare hanyar shiga gidan ya tausasa murya, "Sadiya dan Allah ki rabu da mutuminnan, yawancinsu suna ta'ammali da matan banza." Nasaki dariya cikin izgili Nace, "wannanfa shine shege! Yi da me zina," nanunashi da yatsa, "ashe har kai zaka dinga zargin wani cewa yana bin mata? Kamanta da naka laifin ko? har sakamako ka ajiye." Nayi murmushi, "bani hanya in wuce." Yace, "Naji dai,duk abin da zaki cemin Kice,amma zan nunamiki cewa nidai nine mijinki." Na ratsa ta gefensa na wuce,bansan yabiyoniba sai da namikawa iya kudin inna cewa "nayi-nayi yabarsu yaki." Ta ciro nata tace, "kingansu dami guda, Allah yashi albarka,tinda yafadi inda yake zansa yayanku babban a bincikomana,in bashi da wani aibu shikenana." Kurum sai Yaya yafado dakin, "Dama sabida kudi kike sonshi ko Sadiya? Sannan kuma kisani bazakiyi aureba har sai kin yayemin yarona." Nace, "ina ruwanka dani? Yaro kuma dashi zanyi aure a can zan yayeshi." Yasake daga murya, " kinyi kadan." Da hannu iya tayimin alama wai inyi banza dashi, don haka na shareshi Yakara masifarsa ya nufi waje. Ranar Aliyu yaga tashin hankali,yanzun yanda zai shawo kan Sadiya da Iya yake nema.nikam dan So banson Alhaji,amma zan iya auransa da in auri Aliyu ko Yaya Usman, in anyi bincike zan amince muyi aure kawai in huta. Aliyu fa yadage kullum yana kan hanyar gida daga Abuja,yana gida yana bawa iya baki,ya turo wannna ya turo wancan,rokon gafara har dasu mahaifina. Andau tsawon wata biyu a haka,lokacin zancen aurenmu da Alhaji yasoma nisa,dan batun har yakai Zaria. Yaya Aliyu kam yadan rame duk da juriyarsa. Saifa yadauki wani sabon salon kamun kafa da yaransa,kawai sai mukaga yara sun canja ba kamar Khausar, in Alhaji yazo ta dinga kunci kenan harda Kuka,dana tanbayeta dalili wai inkoma gidan Babanta,ranar har marinta nayi, iya tayimin fada wai indena dukanta,ammafa baza'a komaba. Ko Yaushe zaizo yakwashesu zuwa yawo yanatayimusu hidima. In Iya kuma tayi maganarsa sun dinga kunci kenan,har Mama. Wata ranar Juma'a muna zaune iya taje Masallacin Juma'a Yaya yayomin waya inshirya yabiyamin kujerar maka ni da Iya zamuje,duk da farincikin daya girgizani amma sainace nikam nagode bazaniba zamuje da Alhajina, ( Lallai Sadiya kin burgeni,ANaM Dorayi hhhhhhh) Bantabaji Aliyu yayi babban zagiba sai yau,ya kudundumawa Alhaji zagi, da sauri na kashe waya Yaya Sulaiman yazo da daddare cikin murna yana gayawa Iya wai Aliyu yabiyamusu Hajji shi da Iya da Mahaifina,ga mamakina sainaga tahau murna harma tasoma kiran 'yan uwa a waya, saidai banji ana kiran sunana a 'yan tafiyaba Alhalin ya cemin yabiya ni da iya.washegari makota sukai ta shigowa taya murna iya tana yaye baki, amma da yamma da yazo sainaga tayi kicin kicin,musamman nazo nazauna inji ko zaiyi batun tawa kujerar, sai naga iya ta tubure, "Naji sakon, nagode, amfa kasani karkazata zan hakura da laifin dakayi,hajji kiran Allah ne koba ta hannunkaba indai an kirani Sai naje." Yace, "hakane Iya,innadai neman afuwa,kuma dama kujeru hudune yanzu saura daya shine nace kowakikaga yadace abaiwa? Har na bawa wani sai yace bayaso." Iya tace, "kai wannan wane mara rabone? To kai kajene?" Yace, "a'a zanje wata shekarar,sabida Siyasa datake bullowa a daidai lokacin aikin hajjin,kasarnan tana bukatar Irina." Iya tace, "Allah yataimaka " Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Nashiga daki cikin takaici, bakina ya cuceni,da'ace nasan Iya zatayi saurin yadda da batun da bance banasoba,gashi tace yabawa kawunmu kaninta na Hadeja. Aliyu yasamu sassauci gurin iya da yan'uwanshi sanadin wadannan kujeru da yabiyamusu yanzu burinsa kawai ya shawo kan Sadiya, amma ta yaya bayan tabawa wani dama har ankawo sadakinta. Daya Isa Abuja kai tsaye Office yawuce sai wajen shabiyu yaje gida, abinda yabashi shi mamaki yanda yaga ankulle kofar falon ta ciki maimakon ta waje, yasaka Key yaki shiga sabida akwai wani ta ciki,don haka sai ya kwankwasa don yaga ikon Allah,jim kadan aka bude. Mujidat yagani, tayi kyau iya kyau,kamar farkon haduwarsu, ta rungumeshi; Oyoyo Mijina,ya yakiceta ya tureta yadaga murya, "Wayace kidawo gidana?" Tace, " to inna can zaune bakazoba" Ta nufi ciki ya shiga, ta nunamasa tebur da hannu; " ga Abinci." Yace, "bana ci." Ya nufi dakinshi ta bishi, bandaki ya fada ya watsa ruwa, yafito yayi shirin kwanciya yana hawa gado itama ta fada,Yace, "kifita,kuma nabaki zuwa da safe kibar gida na." Tace, "Gidanmu dai, dan Allah Honey kayi hakuri bazan sakeba." Yace, "kina takama da aurene ko? To ni zan ball....." Ta katseshi ta hanyar manna bakinta a a cikin nasa,hmm Mujidat yar duniya, sai datasa ya manta komai,yashiga shawagi cikin duniyar Ma'aurata. Haka ya hakura ya barta sannan ya dakko mata danta daga inda yakaishi Ajiya bayan taimasa alkawarin bazatasake sabamasaba,kuma zata mutunta kowa nashi. An ajiye lokacin bikinmu nan da wata biyar,lokacin na yaye Sadiq,Alhaji Badamasi nason yin dawainiya damu danma iya tana hanashi,su Khausar sun tsaneshi,har shidakansa ya fahimci hakan,har yataba cemin, meyasa yarananan ko yakirasu basason Zuwa? Nace haka suke basu da sabo. Cikin yan kwanakin da suka biyo baya Yaya banda kyautatawa dangi baya komai,ya kammala gidanshi dankarere yace Iya takoma donshi ba shiga zaiyi ba,namu nada kuma Yaya Sani yakoma. Nadauka Iya zatace a'a,sainaji tace zatayi shawara, Nace, "to iya komawa zamuyi?" Tace, "Eh,ai abinda baifaruba shi ake gudu Sadiya, wanda ya faru saidai a kiyayi gaba.Aliyu yariga yanemi afuwa ta yaya zanyi? Sai addu'a inna nunamasa fushi nane don ya kori gaba yakuma gane yayi ba daidaiba." Nace, "yanzu dai za'akoma gidan kenan?" Tace, "to waye bayason cigaba yarnan?" Natabe baki cikin takaici nace, " to saidai kukoma kubarni a nan, ko kujira in nayi aure ku kuntare." Iya dai banza dani tayi. A raina nace wato da da Mahaifi sai Allah,yanzu iya har tamanta da fishin datakeyidashi. Wata ranar asabar yazo har da Abdul su Khausar suna ta murna ganin dan'uwansu nidai beganeniba yaron,lokacin iya na makota. Yaya Yace, "gabar harda danki?" Nidai ban tankashiba, Allah-Allah neke iya tashigo naga irin warwarar dazataimasa amma tana shigowa sai naga ta hau washe baki. "Ai harda Abdul din kazo." Al-amin yakamomasa hannu, "gashi Iya." Ta daukeshi tanacewa Khausar ta debomasa ruwa a firij,Yaya ya kalleni harda yin wani murmushi,wato inganidai bashi da wata matsala, nima dan inkular dashi nadauki wayata nakira Alhaji Badamasi mukagaisa,nace, "Alhaji zanje unguwa kozaka aiko akaini." Cikin murna Yace, "dole inbar komai inzo inkaiki " Nakalli fuskarshi kamar zai fashe da kuka,murmushi nayi na tashi na hau yin kwalliya, minti shabiyar saiga kiranshi, "Na'iso ranki ya Dade " Nace, "dama kana kusa kenan,to ganinan fitowa." Nadinga yiwa jikina aman tirare har saida ya time,yace,"wai ke ina kike shirin zuwa haka?" Nace, "Sai kaji? Ba matsalarkabace." Ya kalli iya, "haka take yawo kamar mara mafadi?" Iya tace, "shi zata aurafa.".. Nazo fita ina wucewa ina cewa, Iya zanje gidan Aisha,tace, "ki dibarmata kwai." Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ya kara kulewa,sai yatare bakin kofar, "To Koma ki dauki Sadeeq bazakibarshi ya tashi yadinga kukaba." Dariya ke nema ta kufcemin,Nace, "Kasan Allah yayi kukan jini inyatashi nikam bazani dashiba." Yayo kaina, nayi bayan Iya inna fadin, "Dukana to zakayi?" Yace, "bakin rashin kunyar zan buge." Nace, "Aiko daka amsa tanbayoyin Alhaji,domin matsayin matarshi nake." cike da rashin kunya nayi maganar. "Inma matsayin uwarsa kike be dameniba,amma daukarmin yaro aje duk inda za'a dashi." Na kalli iya wadda tinda tayi magana dazu bata kuma yin maganaba, sai nagama dariya take kunshewa dan abin dariya itama yabata. Nace, "kifada masa yadena zargin mijina." Sai naji jifa a kafadata da wayar shi, nashiga uwar daki inna sosa gurin domin naji zafi,bakina bai mutuba innacewa, "Ba inda zanje dashi kome zakayimin." Iya tace, " ina ruwanka da sune? Yaza'ace saitafita da yaro dole?" "Iya amma inyatashifa yanason nono?" Nace, "nawa kake biyana kudin shayarwa?" Yace, "kifadi kudin nonon gabadaya a biyaki." Iya tadaure ta hade rai tace, " to tinda ban isaba kacigaba." Yazauna tare da fadin, "shiyasa tagama rainani,domin kankomai sai a nunamata tafini." "Au, hakama zakace?" Sai kuma cikin sauri Yace,"iya kiyi hakuri." Nidai nafi to na debi kwai kawai nayi gaba. Tin bayan fitata kai yadafe, baisan ta ina zai bullowa lamarinaba,abinda dai yayiwa kansa alkawari shine , bazai taba bari Sadiya ta auri waninsaba,yadogara ga Allah ta hanyar tsayuwar dare tsananta addu'a,Allah baya bacci. Nikam a gidan Aisha inna fadamata yanda mukayi munata kwasar dariya,Aisha tace Sadiya nidai bazangaji da fadamiki da Aliyu kadai kika daceba,shima dake yadace, nace tabdi, ni yanzu nacire batun wani so ko dacewa a cikin raina, nafiso inyi aure inda za'a ga mutuncina,insamu tsabtataccen miji mara aibu,tace ai bari infadamiki Sadiya a wannna zamani da wuya kisamu mara aibu,sai dai wani yafi wani,ni innagudun kar kiyi gudun gara ki afkawa zago, amma shi din kinbincika halinsa? Nace, "iya ta bincika ba matsala" Tace, "shikenan Allah yazaba mafi alkhairi." Aliyu yacewa iya yagama zubamusu kaya a wancan gidan sati me zuwa zasu tare. Iya tace, "Ai nazata sai mundawo aikin hajji anyi bikin Sadiya don batason tarewa a gidan." Yace , "a'a, tafiyarku saura wata Daya da kuntare kawai," Tace, "ko a barshi mutafi daga nan inmundawo lafiya sai musauka a can." Ranar tafiyarsu iya har kuka nayi, nace yanzu ni kadai zan zauna a gidannan sai yara, gashi zandinga tafiya makaranta, iya tace, "bana fadamiki matar kawu Hauwa tana nan tahowaba daga Hadeja tare zaku zauna,in Allah yadawo damu lafiya sai sutafi tare da kawun naku ko?" Nace, "shikenan," Amota Daya Yaya yadaukesu wata kuma aka debi 'yan rakiya, nidai dama nafadawa Alhaji kuma yaturo direbansa yakaini, Aliyu ya hana yaransa shiga motar, nace ohodai. Bayan tafiyarsu Iya da sati daya sai ga yaya sunshigo da Habu, na daure fuska muka gaisa da Habu,dama alokacin zantafi gurin aiki, sai kawai nafita. Aliyu yasa Habu yayi ta jidar kayan yana kaiwa gidansu, irinsu kujeru,TV harma da fringi,Baba Hauwa tace lafiya? Aliyu yace dama zaku tashine,kayan nabaiwa uwar yaron nanne mokatanmu." Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Tace, "harda firingin? Amma danasani na tanbayi firing din innasonshi,Aliyu yace, "inzaki tafi sai insemiki wani" Tasoma godiya yace ai ba komai,nidai addu'ar dazakiyimin Allah yasa Sadiya ta yarda tadawo gurina. Baba Hauwa tace, "Ai dama kanasonta baka yunkuraba?" Aliyu yace, " Ai babu irin yunkurin da banyiba amma yarinyar nan taki yarda dani,yanda kikasan inyi hauka." Baba Hauwa tace, "shikenan zan tayaka addu'a,sannan zan dinga dan cusamata ra'ayi." Yace, "nagode, nikuma zanmiki alkhairin da bazaki mantaba indai kika shawomin kanta." Nadawo naga gidan wayam, yarana da murmushinsu suka tareni da batun wai Abbansu yace yau zamu tashi,tsaki naja tare da cewa dan Allah kukauce kubani guri,raina yabaci daganin hukuncin da Yaya ya yanke, na dinga zaga dakin inna kallon jakunkunan kayanmu a kasa anfito da komai sai gashi yashigo, "kufito Habu yayi gaba damu nikuma zantaho da jakunkunan, ko bata dawoba?" Baba Hauwa tace, "tadawo tana ciki." Yashigo cikin dakin, "Sadiya" nakalleshi cikin bacin rai,har saida yayi in'ina kafinyacemin, "kizo Habu yakaiku" Nace ina? Yace sabon gidanku, na girgiza kai gami da tabe baki, gidanka dai bazaniba.yashigo tare da tausasa murya yace , Sadiya wai bazaki yafeminbane? najuyamasa baya, "wai me zanmikine kiga haskena Sadiya?" na waiwayo na dubeshi, "rabuwa dani kawai za'ayi kadena shiga harkata sai inyafemaka."

Chapter 23 of 25