Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ce iya tazo.Ya ce tana nan?Na ce eh.A zatona zai sake ni amma har fallon mu saida ya zauna sanan na zame na barsu suna gaisawa da Iya.Na kawo masa ruwa da abinci, yace my choice ba zan ci abinci ba, dama nazo ne in dubaki kawai don na kira wayarki a kashe.Nace yanzu aka kawo wuta, ka kuma san batir din baya rike chaji.Ya ce, haka ne.Zan chanja maki wayar ma, Iya ma in sai mata.Tace ni yanzu gadanga in ka hada ni da waya ban san yaya zanyi da ita ba.Na ce, zaki iya mana, mun gode yaya.Yayi murmushi tunkafin a siyo?Ta ce, ai nasan tunda ka furta zaka aikata.Iya ta ce, gadanga kai naga kayi bul ka kara kiba ita ko yar tawa duk ta rame.Ya kalleni, ashe bani kadai nake ganin wanan ramar ba, to ko Asibiti zamuje?Na ce, yaya babu inda yake min ciwo sai muje Asibiti?Yace rama ciwo ne My choice, zasu baki magani.Iya ta ce, ni da na zaci ko rigima kuke.Ya ce, haba dai, ai yar taki tana da biyayya.Iya tayi murmushi sanan ta ce, haka nike so,Allah yayi muku albarka, ya baku yaya na gari.Yaya ne, ya amsa da amin.Tare da dago haba ta.Iya ta ce bari na tafi.Naje daki na dauko dubu daya na ce, iya gashi, ta ce ina kika sami kudi?Na ce, in abokan yaya suka zo suka bani, ko na bashi sai ya ce in ajiye abina.Kuma ni ko katin waya shi ke loda min.Ta amsa tare da ce min Allah ya anfana.Na ce, Iya da kin dan bari sai anjima.Yaya ya harareni ke zakiyi mata aikinta a gida?Na ce, (cikin shagwaba) ba ina kai mata kullum ba, ia yana isarki ko?Ta ce har ma in rage in ba wani.Sai dai duk da haka ina yin girkin saboda almajirai ko yan ciranin nan na mokatanmu.Na ce, har yanzu iya kina ci dasu?Iya ta ce, wanda ka bada shine naka.Nace to ki tsaya zanyi da yawa sai in sa miki.Aliyu ya kawo hannu ya dan mintsineni gefen ciki na, tare da cewa sauran aikin ke zakiyi mata?Iya ta nufi hanyar fita tana fadin Sadiyayyena kina in zauna shiko gadanga korata ma yake.Da sauri kuma cikin dariya ya ce, lah, iya bankoreki ba, nima yanxu zanfita nazo duba ta ne kawai, kuyi zamanku ni bari na tafi. Duk muka sa dariya, Iya ta ce a a yayan nan ni dai naji dadin yanda na sameku haka, fatana Allah ya kauda shedan tsakanin ku.Ta bude kofar gidan ta fita, ya bita nikuma nayi mata alkawarin xuwa inyini in an kwanabiyu.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Bayan ya dawo daga yi mata rakiya ya sameni ina gyara gurin, ya makaloni jikinsa ya dago fiskata.Sarai kinsan abinda ya kawoni, shine kike rokon iya ta zauna ko?Gaba na ya fadi, amma sai nayi yake tare dafadin ba haka bane.Muka nufi dakinsa.Na rasa duk lokacin da yaya zai zo mun da wanan batun gabana ya dinga faduwa kenan.Na kasa sabawa.Ko shi ke sani rama? Oho.Kawaye na duk wace tazo sai tayi zancen ramata, haka Aisha, ta damu da son jin dalili Na dage kan cewa ba ko mai, tunda bai kyautu in fada mata yanayin mijina ba.Munje Asibiti likita shima ya sha mamakin jin banda matsala kuma ba inda yake min ciwo, amma na rame.Sai dai ya ruvuta mana magunguna masu sa cin abinci, amma duk da haka sai a hankali.Wani dare anty Abida ita da Usman sun kawo mana ziyara munata hira, sai Aliyu ya kawo batun ramata, aka danyi zancen har Usman yana tsokanata da cewa ina tsoron kishiya ne ki daina tunani, aboki na naki ne ke daya.Nayi dariya sanan na ce, nasan haka shima yasan haka.Yaya Aliyu yayi dariya.My choice ban maki alkawari ba fa.Na ce, yaya kaima kasan ko bakai min alkawari ba kai nawa ne ni daya.Abida taja ni bed Room dina muka zauna bakin gado, ta kalleni wai me yake damunki? Na ce, ba ko mai wlh.Ta ce, ki fada mun ban sani ba ko zan iya taimakonki.Nayi shiru ina nazari, can nace anty ba ko mai, Allah sai dai ina zaton ko dan yaya yana da yawan buka ta ne?Kin san Allah anty na yaya bashi da hakuri hatta kai da na ganshi ya dawo gaba na ya dinga faduwa ke nan.Ta kada kai zancen ke nan, amma wanan ba abin damuwa bane, da farko ki daina tsorata har gabanki ya dinga faduwa.Kisa haka aikin da ya zaman maki dole, aure bauta ne, in zakiyi sallah gabanki na faduwa?Na ce, a a.Ta ce aikin gida fa? Na ce, a a.Ta ce, wanan ma kisashi cikin dolenki, tunda zama ne ba na kare ba.Gashi baki son kishiya.Tayi dariya sai dai zan fada maki wasu abubuwa da zasu taimakeki, dauko biro da takarda.Na ce, to.Na tashi na dauko memo, ta soma bayani kamar haka: ki samo Dabino,Zuma,Aya, da Cukui zaki maidasu gari ne, sanan ki dinga zuba madara peak da zuma kina sha kullum safe da yamma.Kinji daya? Na ce eh, na rubuta.Ta ci gaba, ki samu,kankana ki dinga yawan shanta har kwallon,na ce gashi kankana bata dame ni ba, ta zaro ido to kuwa ta dame ki, kuma kya iya yanyankata ki zuba mata madara peak ki dinga sha shima har kwallo.Sanan a kai na kan Akuya, ki dafa shi da romo, sai dai bazaki zuba mashi mai ba, maimakon mai ridi zaki zuba da yawa ki cinye ke daya.Haka kuma zaki sami garin dabino ki fasa kwai da madara peak ki juya ki shanye.Nace wai zan iya duk wanan?Ta ce, ki gwada tun gobe zaki sanya ya nemo maki amma karki fada masa dalilinki na son kayan, kawai kice zakiyi anfani da su ne. Kan batun ramarki kuwa, ki canza abin kari, da me kike karyawa?Na ce,Tea ne sai Bread da Kwai, watarana inyi kunu da kosai, ko indomie da kwai.Ta ce ki koma cin dankalin turawa da agada,ko doya da kuma kwai, in da hali harda farfesu.Shayinki kuma ya zama yaji sugar da bota, milo da madara.Ki zuba sosai yayi kauri kisha.Sanan kirinka baccin rana shima baccin yana sa kiba, sanan da daddare kici abinci sosai.Na ce, to anty na gode.Ta ce, ba komai, ke dai kada kiyi wasa, in kinyi su da kyau na tabbata sai kin dawo neman wasu.Ko da yake ban fada maki na tafin hannu ba,kin san hannu yana daya daga cikin mai aikawa da sakonni.In mijinki mai yawan kama maki hannu ne, ki samu zautun ki kwaba da suga ta narke, kullun in zaki kwanta ki rinka shafe hannunki.Sanan ki rinka shafawa a lebunanki, nace to na gode anty sosai.Sallamar yaya ce ta katse mu, ya ce, me ta baki kike ta godiya?Nace abubuwan karin kiba ne wanda zan rinka karin kumallo da su.Ya kalli Abida dama zaki iya wanan taimakon amma kika share mu? Muka sa dariya harda shi.Ya ce, mun gode.Ta ce, ba wani abu bane wanan har da za ayi mun godiya.Kai dai ka dage da siyo wa.Ya ce, in sha Allahu ko su ke nan kudin za a siya, me nene da me nene za a siya?Na ce, na rubuta zan nuna maka.Yayi murmushi, to da kyau, yace kizo, abiki yace zaku biya ta gidan yar uwarki ko?Ta ce, eh, tare da mikewa na shiga dube duben me zan bata, turare na bata mai kyaunace ta kaiwa Ummulkhairi.Ka fin ya dawo da ga rakasu, har na gama rubuta abinda ta ce na rinka karyawa da shi,ya ce agada da dankali sai da safe, nayi godiya da cewa Allah ya kaimu.Cikin satyn na hada duk wani abu da anty Abida ta fada mun, na shiga anfani da su.Kafin wata daya naga canji sosai, yanzu bana wahala da duk dawainiyar da miji na yazo mun da ita.Sanan nasoma cika ina cika kayana gwanin sha'awa.Shi kanshi yaya wani sabon ji dani ya sake ko mai tare muke yi in har yana gida ni dashi mun zama abu daya.Ko tari nayi sai ya tabbatar ba na cutarwa bane, haka nima ina binshi sau da kafa, da ya nuna ra'ayin abu zan masa balle ya ce my choice ina son kaza.Ai in na soma sai ya gundire shi, duk abinda bai so na kiyayeshi har abada.Shinfidar da muka yiwa rayuwar mu ba zan iya bada labarinta ba, kowa yana mamakin mu tamkar mun shafe shekaru goma muna soyayya kafin muyi aure.Muna cikin wata na uku iya ta matsa masa wai sai ya maidani makaranta, form din (N.C.E) ya sai min bada bata lokaci ba na zama daliba a makarantar horas da malamai dake riga cikun.Aliyu ya ce, ya zama dole in nemi avin hawa ko don ke.Na ce Allah ya bada iko.Ba da jimawa ba kuwa ya ,mallaki motarsa dai dai ta talaka.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Don haka bani da matsala sai dai yanayin aikin sa ya ce in ya sami lokaci zai rinka koya mun, na ce to.Ban jima ba na iya mota, sau da yawa ni ke kaishi gurin aiki in dawo, sanan in tafi makaranta.Kai yaya ya nuna mun dukkan gata, a lokacin jini ke babu matar da ta kaini sa'ar zuwa duniya a zamaninnmu. Wata safiya na farka da zazzabi, mura, ciwon kai da sauran su, gashi ranar yaya ba gida ya kwana ba, saboda wani case da ke hannunsa.Bana kiranshi in dai yana wurin aiki, amma shi in ya sami lokaci yana kira na.Ina kudindine a kan gado naji ringing waya ta, da kyar na lallaba na dauko, na daga.Ya ce, my choice kin wuni lafiya?Cikin wata murya na ce, lafiya lau.Ya ce, me ya same ki naji ki haka?Wani dan kukan shagwaba ya subuce mun na ce, zazzabi.Nanfa ya rikice sai gashi a gida bayan minti ashirin.Banyi ko wanka ba ya sani a mota sai asibiti, gwajin farko ciki ya bayyana, murnar da ya Aliyu ya dinga yi ta rinka bani mamaki.Kula da tarairaya ina ganinsu gurin sweet Aly na da iya, cikin ya sa ni yin kyau, duk da na sha wahala kafin yayi kwari.Sanan na bude nayi kiba gwanin sha'Awa.Lokacin da cikin ya tsufa sai kuma na kumbura abin da yayi matukar daga hankalin yaya.Duk da cewa likitan ya ce babu matsala.Cikin haka aka chanja yaya zuwa kogi, ranarda ya zo mun da maganar na sha kuka.Duk da ya zaci dama zanyi rigima bai tsammaci har haka ba.Yayi ta lallashina da cewa, sadiya my choice,ki kwantar da hankalinki.Ai duk matar mai kaki San sanda ko Soja da sauransu, dole ta kwana da sanin akwai yawon zaga duniya.Banzaci zan dade haka ba tare da an canzani wani gari ba.Na shafa cikina yanzu baka nan zan haihu?In katafi yanzu sai yaushe zan sake ganinka?Ya ce da na sami sarari zanzo, na kwanta a jikinshi.Ni dai zanbika sweey Ali kaji yaya na?Ganin yanda na rikice sai ya ce, to shi ke nanmu tafi tare ko? Na ce, to sanan nayi shiru.Ana gobe zai tafi yaje suka hada baki da iya,na zage ina ta hada kaya har yana taya ni, sai ga iya tayi sallama.Na ce, sweet yaya na dubi iya tazo kamar tasan zamuje sallama.Iya ta shigo har cikin daki na, ta kalli kayan da akwatinan ta ce, wanan fa, kwalima ce? Na ce iya kin manta gobe ne fa zamu tafi can jihar kogi inda aka tura yaya.Iya ta ce, zakutafi ko zai tafi?Ina zaki tafi da wanan katon cikin ga kumburi?Na kalli yaya na wanda ke ta aikin jera min kaya na a cikin a kwati.Ni ina kwasowa daga cikin sif.Kin kallona yayi, sai da na ce yaya!Ya kalleni na ce, kaji kuma wai ba tare zamuba, inji iya?Ya ce, eh, a a ai kinji ta ce saboda cikinki na ce, tabdi jan!Ni kam ba zan zauna ba.Iya ta ce, lallai Sadiya ba inda zakije yar dadi muji, ni yanzu ma zuwa nayi in tafi dake.Na saka kuka, iya sororo tayi tana kallona, shi kuma sai ya tashi tsam ya dawo kusa dani.Iya kije gida zan kawo ta.Iya ta mike ai ba wani lallashi ba in zata zo dan ma kada ka sake yi mata karya.Ke ko yanxu ance ki bishi kya je?Na ci gaba da kuka na iya dai ta tafi tana cewa sai kiyi ta yi.Tana fita ya rungumeni, haba my choice ni na lura iya tafimu gaskiya.Ki bari in kin haihu sai muje, ina zo zan tafi dake.Yanzu kinga dole inje in ga yanayin garin.Na ce, yaya dama na san cewa baka damu dani ba, can na san baka sona.Ya manneni a jikinsa, inji wa yace bani sonki?A zaman da mukayi baki fahimci matsanancin son da nake maki ba?Na ce, to me yasa zaka tafi ka barni?Ya ce, ina canne amma na rantse maki zuciyata tana tare dake.Yanxu ni dake bamu san haihuwa ba, gashi yanayin aikina ba na za,ma bane bugu da kari ba mu san kowa ba in haihuwa ta zo maki bana kusa yaya ke nan?Nayi shiru a raina na tabbata haka ne, amma damuwa ta daya, yaya na nasan ba zaka jure zama ba mace ba, don nasan yanayin ka.Ina tsoron matan zamani.Ya ce, au, dama dan wanan ne?Nayi maki alkawarin ba zan kalli wata ya mace da sunan so ko wani abu ba, baki tunabaya ba?Na tsare kaina kuma Allah ya tsareni, ba wanan a raina, nace to ya ya zakayi?Ya ce, azumi mana, ko can shi na tayi ta irin na annabi dauda.Inyi yau gobe in huta, kada ki damu ki kyautata min zato, bani da sha'awar aikata kazamin laifi irin su zina da makamantansu. Na kalleshi na yarda da kai mijina, kuma ni da kai mutuwa ce zata raba mu.Zan jira dawowarka, amma za ka dinga yawan kirana?Yace, kema na yarda ki kirani duk lokacin dakike so, nace to amma dai mu kwana abinmu a nan da safe in katafi sai na tafi nima.Ya ce, sammako zanyi, na ce, eh, duk da haka, ya ce shi kenan, sai muje da daddare mu kai kayanki ko?Na ce, eh. Hakika yaya na sweet Ali ya tafi ya barni da tsananin kewarsa. Kafin ya kai munyi waya yafi sau goma.Haka nan na hakura na saba da kwana ni daya, daran wata lahadi na farka da wani matsanancin ciwon ciki da baya.Kafin in tashi iya yaya na soma kira, ya daga a rude na ce yaya zan mutu ka yafe mun, nayarda wayar saboda ciwon mara da ya murdo min.Kalamaina suka farkar da iya, tazo tana cewa haihuwar ce Sadiya? Yaya ya kashe ya sake kira a rude, iya ta daga ya ce Iya don Allah............Kuyimin hakuri indakata anan zuwa lokaci nagaba sai mudira daga inda muka tsaya,fatan zanga comment dinku rututu,kafin nan nake cewa zaku iya ziyartar blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Darajar Yayana2-02 Posted by ANaM Dorayi on 09:51 PM, 02-Apr-16 Under: DARAJAR 'YA'YANA _________________NA ___________HALIMA K/MASHI Irin tarbar da kikayimin ta mutunci shi yasana boye kalatata,boye kishinki zaifi alheri, sama da bayyanashi don yanda na yi mani bakikaini son mijinki ba, haka na yi imani na fi ki kishin sa,in kina musu lokaci zai tabbatar miki dahaka. Kije kiyi aikinki sannan ki kunna min T.V Na harareta tare da jan tsaki na nufi dakin yaran. Sun gama cire kayan, Kausar tana linkewa, Al'ameen ya ce,'Mama wace ce wannan??? ..... Na ce 'Bakuwa ce, Na kunna musu T.V dinsu, na ce kar su fito sai an kira sallah. Nima na shige dakina na fada kan gado. Maganganun yarinyar sun ratsa ni, har na rasa tunanin dayakamata inyi. Ina buqatar shawara, domin na lura da 'yar iskar matar nan batazo dawasa ba. Wa zan kira don neman shawara? Aisha ko Abida? Aisha ba ta san d wannan zancen ba, bari kawai in kira Anty Abida tunda ta san da matsalar. Ringing na uku ta dauka na ce, 'Anty Abida ya gida da yara. 'Ta ce, Lafiya lau. Na kwashe komai na fada mata, ta cika da mamaki, sannan ta ce, 'Shawarar da zan ba kikar ki bari ta gane lagon ki kar ki nuna fushinki, kuma kar ki kulata kuyi tashin hankali, ballantana ta yi furucin da yaranki za su gane,ki jira zuwan shi muji hukuncin da zai yanke. Na ce, 'To shi kenan Allah yayi mana jagora.'Ameen, Ta ce. Na kashe wayar ina nazarin maganganunta. Ita ko 'Yar Gwari, Mujidat tuni ta ciro wayarta ta soma chatting da abokanta. Murfat ke tambayarta wai yanzuntana ina? Mujidat ta ce tana Kaduna. Murfat tace, 'Ashe muna kusa ni ina Abuja jiya muka zo tare d Alhaji Karimu zai yi meetina na kwana biyu.. Mujidt tace lallai kina cikin kudi, murfat tace sosai ma, abokinshi Alh muslimu ya tambayeki .Mujidat tace yakiranima bandaga wayar ba, kinsan ina ina yanxu? Murfat tace ba kin ce kaduna b? Mujidat tace ina gidan officer Aliyu,Murfat tace kina hauka ne? Zaki je gidansa? sai matar sa ta kasheki a banxa? Mujidat tace ai matar tashi wawiya ce, har ruwa ta bani nasha, bayan na gaya mata cewa mijinta ciki ya min, tace ina baki shawara ki cire cikin nan kixo gurin masu sanki, officer ba sanki yake ba. Mujidat tace , ni inasonshi, zan tsaya nai fada a kanshi, saboda ko nadawo zanta tunanin shine, bazaki fahimta bane saboda bakitaba shiga tarkon So ba, ni kuma na shiga tarkon So mai tsanani.Murfat tace to yaya akayi kika gane gidan?ina kwance Hotel ba lafiya , sai ga wayar direban shi wai Ogafa an canxa shi zuwa Abuja, yanxun haka ya tafi in gaya miki duk sai na rude, take na miqe ina roqon Adewale ya taimakeni , yace sai nabashi kudi, bani da kudi sai dana roki samarina , suma shegu ban samuba sai dana musu alqawarin basu kaina, ina bashi kudin yace naje kaduna zai turo wani dan sanda daga can Headqurter su, yayi Tanbaya kan Aliyu Tukur aka fada masa sunan unguwar su, sannan na nufo Kaduna, nasha wahala kafin na iso, sabida motar dana shiga me arhace, inazuwanan na samu wani dan sanda da Adewale ya hadamu , shima akwai kudin da akayi alqawarin xan bashi, sai daya dafe shi,sannan yayi min jagora zuwa unguwar su Aliyu, nan ya bar ni wai in nemi gidan, wai in mun shig unguwar tare, asirinsa zai tonu, na Adewale ma haka,nadade ina yawo, sannan na samu gidan mamanshi, na shiga bata nan, sai nace a kai ni gidan matarshi, Murfat tace ke yar neman bala'i ce, bari tasa miki guba a abinci kici ki mutu, mujidat tace shi yasa bazan taba cin abincita ba,Murfat tace kidai yi ahankali, garinsu kikazo, tace a garinnasu sai in karbe mijin kuma na zauna lafiya.haka suka yita chat har xwa wani lokaci, Niko munyi sallar magariba har na zubawa yara abinci, 9 da yan mintina yya Aliyu ya iso gida,da ita ya soma cin karo a falo, ckin zafin rai yace me zakiyi agidana?itam cikin daga murya tace goyon cikin dakayi min, abinda naji kenan, na miqe ina kallon yarana,Kausar ce kawai idanta biyu tana yin homework dinta, na miqe na fito da sauri, dai-dai lokacin yana cewa, zan nuna miki kurenki na biyoni gidana yar iska karuwa.nakamashi ina fadin yaya yara fa? itama tace yan iska dai, namijin karuwa. na dafa kaina dan takaici, yar bariki tana zagin mijina da nake girmamawa a gabana, najashi zuwa dakinsa, nace, haba yaya, kamanta cewa kana da yara a gidan nan?dubi yanda yar bariki tazo har cikin gidanka tana zaginka?sabida mutuncinka daka sai da,ai dama haka ne, dukwanda yabar maganar ubangijinsa dole ya fadawa dana sani, da wace rana zaka iya hada yau a gurinka dan bakin ciki? ni dai a gurina babu, ya dago kai ya dubeni, Sadiya nayi nadama sosai wallahi, ba sai ta kanjamau kadai Allah yake kama mazinaciba, in Iya taji batunnan na shiga uku, nasan bazan kara yin daraja ba, kila ma ta cireni daga yayanta, ga wannan matsiyaciyar da alamu fallasa tazi min,nace to yanzu dai nema mata masaukin da zata kwana, in yaso da safe sai mu zauna da ita mu kafa mata sharuda,ya kama hannuna, wadanne irin sharuda za'a kafa mata?kara min haske, sai musa mata sharudan cewa ka yarda zaka amshi dan,amma za'a rufa asirin cewa ba'a son kowa ya ji, dan haka za'a ce mijinta ne ya rasu, iyaynta suka koreta saboda ta musulunta,na tabbata duk wanda yaji haka zai tausaya,to inta haihu sai ta bamu yaron ta tafi abinta,yace wazai rike yaron?nace ni mana, Yya ko ban aure ka ba ai xan rike maka da, bare kuma ina matarka na kasa rike jininka? yadan yi shiru yana nazarin batuna , can yayi dariyar yake yace,Sadiya baki tunanin me mutane zasu ce?in sun gammu da jariri?me zamu fadawa yaran mu? idan sun tambayemu nan gaba? nace ai zamu fada musu dan mu ne, amma bani na haifeshi ba, tunda dama a musulunci bai da gadonka,kaga ba zamu sami matsala ba, ya sake yin shiru, can yace ina ganin fadin gaskiya kawai shine mafita, saboda duk rintsi karya bata kaiwa ko ina baki tunanin cewa nan gaba zata zo nemn danta?kuma asiri zai tonu? nace Allah zai rufa asiri, kai dai da safe mu sameta da batun muji yanda za'ayi.yace shikenan, Allah ya rufa asiri,to yanzu ina zata kwan?ka kaita dakinka,yace a'a, sai dai yara su dawo dakinki, ta kwanta acan , amma bazata kwanar min a daki ba, araina nace yanxun ba, amma da ai tare kuke kwana ma. yace kota kwana a falo? a'a ,bari in kaita dakin yaran.haka kuwa akayi,muka kaita can.Da safe dana kai mata abin kari sai tace a'a, tanada maltina da kuma biredinta, bata cin abincin kowane guri, da kanta takeyi, nace good, sannan na fita.mudai sama-sama mukayi bacci, kuma sama-sama muka karya, duk sai tunani muke, yaya kuwa sai nadama yake, dan dadin da yabi na watanni yaja masa zubewar mutunci na kila tsawon shekaru.misalin sha dayan rana yace in kirata ,muka zauna yara suna makaranta lokacin, ta fito sanye da riga da siket na jeans, kanta babu dankwali, cikinta kuwa har ya turo, ta zauna tana taunar cingam, yaya yace Mujidat dama mun kira kine don mu tattauna dake, shawara ta farko zanbaki dubu dari biyu ki zubar da cikin nan,ta daga masa hannu, ban amince ba ,koda zaka bani duniya da kayan cikinta, inbaka mantaba nafada maka, badan kudi nake tare da kai ba, sonka da kauna ce kawai, kuma cikinnan, (tasa hannunta ta shafa cikin)ribar soyayya ce, taya zan zubar dashi?kawo wata shawarar dai muji,kalamanta sun konan raina tamkar in tashi a gurin,amma sai na shanye.yace to naji, zaki zauna damu ki haihu, amma da sharadin baxaki fadawa kowa komai ba,duk abin dana fadawa mutane zaki tsaya akan haka ne?ta dan yi tsai tana tunani can tace ,zan yarda, amma idan na haihu meye makomata? zan tafi da danne?ko kuwa zan barshi anan?sai lokacin nasa baki , zaki tafi ne kibar yaron a wurina, sai ki tafi abinki,wata ran,xaki iya xuwaki ganshi duk bayn wani lokaci, tayi min wani kallo, tare da yin kwai da cingam dinta kato, sannan ta fasa shi taci gaba da tauna duk muna kallonta, tayi yar dariya, in naki fa? cikin zafin rai Aliyu yace , sai ki tafi da cikinki, danma kin samu zan amsa? nasan uban dayayi miki? tace , ka manta dararen daka yi ta kwana dani?cikin bacin rai yace in baki yarda ba malam kizo ki fice min daga gida kije kiyi duk abunda zaki yi. tace zan fi son haka , dan zama gidan mamanka ze fimin wal-wala, dan haka zan je na fada mata ina dauke da jikanta, ta bani masauki, ni dashi muka kalli juna, yace kije man , zanfi san haka.nace , a'a ,kedai barshi a wancan tsarin,tace in dai har za'a barshi cikin sirri, tonima zan kawo nawa sharadin?Aliyu kam takaici ne ya hana shi daga kai, ban taba ganin shi cikin wannan yanayinba, na takaicida bakin ciki.nace fadi sharadinki muji?tace sharadina sai dai in na haihu zai AURE NI.... kalamanta na karshe suka tafi da numfashina, tsawon kiftawar ido, huhu, nayi nasarar janyo nimfashi na,idanuwana suka futo sukayi jajir, zufa ta ketomin, ta tuntsureda dariya har Aliyu ya dubeta, nima lokacin na dubeta, tace ,ya kika yi saurin firgita?naga keda mijin naki kamar tagwaye, shawarar ku daya, kun burge ni, kuma nasan yana sonki, kuma nima ina san shi dan nasan qualities dinshi, na baku zuwa gobe kuyi shawara. (Uhm!Allah yakayuta,ANaM Dorayi) Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Aliyu ya harareta, Allah ya kiyaye ni Aliyu na aureki,ai ko zan yiwa matata kishiya na nemo mata yar mutunci bake ba karuwar titi,tir Allah ya tsareni, ya miqe, na baki awa daya kibar gidana, ko kuma yan sanda su zo su fita dake, da kyar na miqe kafafuna sunyi sanyi, dakina na nufa don ko ganin gabana banayi,zuciyata tamkar ta faso ta fto,rigijif na fadakan gado, inasan yin kuka amma na kasa, lallai kuka ma rahama ne, tunda idan kayi shi zaka samu sauki, Hannuwanshi naji a gadon bayana, ji nake tamkar ya doramin wuta,zuwa,yanxu nasoma tsanar yaya Aliyu,gaskiya hakurina yana son ya kare, danzan iya danne komi, amma banda batun kishiya ,zan iya hakura ya aureta, amma kuma zan juri zama da ita?(Mata kenan,da kishiyar gida!..Allah ka karemu daga bin soye-soyen zukatanmu.....Ameen.ANaM Dorayi) Birkitonin da yayi shine ya katse min tunanina yace, haba My choice, kada wannan ya dameki, zanyi waya yanxun xa'a turo min yara su tafi da ita, xuwa ynxun ban damu duk duniya tasan cewa na mata ciki ba, ai nima dan Adam ne kamar kowa, ban wuce kuskure ba, nace aika riga ka tafka kuskure,dole ne ka aureta, kuka ya subucemun, naci gaba da magana cikin kuka wane hali Iya xata shiga in taji wannan labarin?ita da ba cikakkiyar lafiya ba, me zaka cewa y'ay'anka ? wadanda tun jiya suka damu dasan sanin wacece wannan bakuwar? y'an 'uwanka, wane idan kake dashi da zaka kallesu?su da sukeyimaka kallon mutunci da kima? ga abokai da sauran mutan gari?kada ka manta, shi fa mutunci madara ne, in ya zube sai dai a kwashi kasa,ka riga kayi abinnan da hausaw ke cewa TSALLE DAYA ME JEFA MUTUM RIJIYA....ya rike kanshi, sadiya na yarda duk wanda ya bar layin da aka ja masa a matsayinsa na musulmi dole yayi nadama mara amfani,danasan abubuwa zasu zama haka da banbi san zuciyata ba ,dam malamai suna gaya mana zuciya wata tsoka ce ajikin dan adam me hadari in kabi sonta sai ka halaka, ya dube ni, yanxu kin yarda? kinaga ba wata mafita sai ta auren ta? nace to inban yadda ba ya xanyi ,nasa masa kuka ina fadin na amince ka aureta, ,kallona ya dinga yi tamkar na zame masa wata sabuwa a sanyaye yace"nasan kin hakura ne saboda ni, amma nasan bakya san kishiya,amma kina ganin cewa nan gaba bazaki damu ba?na runtse ido, zuciyata tana wata irin tafasa nace, batun zan damu ko bazan damu ba a ynzun ba shine mafita ba,na bude jajayen idanuwana ina kallonshi, sai dai ina fatan daga baya ba zka canzamin ba? ya rungume ni, Sadiya kada kiyi tinanin haka kada kiyi fatan haka, ki tayani addu'a Allah ya bani ikon yi miki irin

Chapter 8 of 25