Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fi karfinta inda na yo alwala na yi ta sallah in nagaji in dauki Alkur'ani nayita karantawa,sai da na yi sallar Asubahi sannan na kwanat. Allah ya taimake ni yarana suna cikin hutun makaranta ne, don haka da na tashesu muka yi sallah sai muka koma. Ban farka basai tara, ina tashi Mama ta tashi, sai da na yimusu wanka sannan muka fito.....zandakata anan zuwa lokaci na gaba,fatan zaku kasance tare dani Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Darajar Yayana3-03 Posted by ANaM Dorayi on 12:12 AM, 04-Apr-16 Under: DARAJAR 'YA'YANA __________________NA ___________HALIMA K/MASHI Assalamu'alaikum,akaro na barkatai gani na dawo domin kawo muku cigaban labarinmu ,fatan kuna sane da inda muka tsaya. Yayi shiru. Na ce Hello, kana jina? Eh, kin fadawa Iya ne? Na ce, nanmuka amshi haihuwar tare, Kasan cewa taso ta gano cewa danka ne? Dan yaron yayi kama da kai fiye da duk yaran gidan nan.Da karfi yace Haba dai! Wlh, yaushe zaka zo? Yayi dan tsaki, gaskiya bani da ranar zuwa, zan turo miki kudi kiyi duk abinda ya dace. Nace, zuwan ka yana da muhimmanci, sabida Mujidat zata iya tana komaifa, inbata gankaba. Ya ce, to zan zo kafin suna inkuma dawo Gurin aikina. Nace to saikazo. Na kira auntyAbida na fada mata, haka ma Aisha kawata.Makota duk suna ta shigowa Barka. Su kausar ma nasa sunje sunga baby,na fada musu cewa kaninsune, suna ta murna har da kausar. Aisha ranar datazo barka tana daukan yaron tace, kai Sadiya yaron nan yana kama da Abban kausar. Nace, haka ake ta cewa, dama kin san mutane sun ce in mai ciki tana yawan kallon mutum ta kan haifi mai kama da shi. Ta yi Yar dariyar yake,tare da cewa, hakane kawata.Mai jego kam ina kallon ta sai harara take watso mana. Muna shiga dakina tace, Sadiya anya kuwa ba kanshin gaskiya a cikin lamarin matar nan? Kin san halin mazannan ko dai Dan sa ne? Ki yi hakuri kamarce naga tayi yawa. Nace, hum! Ke dai bari kawata, tsakanina dake nasan amanace, wlh dansane ciki yayo mata, yanzun data haihu zasuyi aure. Aisha amana na fada maki ko iya bata San wannan ba. Aisha ta zabura tare da fadin, kan uba! Lallai Sadiya ban taba sanin cewa Ke sakarya bace sai yau, yayowa wata ciki sannan ki yarda ta zauna maki a gida? Wallahi da ace nasan haka ne in nazo barka shegiya nake,kin ma daure masa gindi kenan gobe ya kara.Na ce, Aisha ki fahimta, uban 'ya'yanane,mijina kuma yaya zanyi? Nawa ganin rufin asirinshi Nawa ne, kuma na yara nane. Ta yi tsaki bana Jin zan fahimceki, in tazo gidan ta koreki kin ga ai sai kiji dadin rufa masa asirin. Na ce, nasan dama bazaki fahimceniba, shi yasa tun farko ban sanar da Ke ba, dan na sanki. Ta dauki yarta tasa a baya,ta suri jakarta da hijabinta, Ni kin ga tafiyata. Na bita ina fadin, "Dan Allah Aisha ki saurareni. Ki tayi ta tafi abinta. Na ce to shi Kenan in kin huce za muyi waya ta ce ni kar ki kira ni. Na dawo daki na kwanta kan gado ina hawaye, in na tuno Yaya zasuyi aure da Mujidat Abin na daga hankalina ya kuma sani kuka. Ranarr da suka cika kwana 5, sai ga Yayakusan 10 na dare, Ni ce ma na bude masa kofa, ya janyo ni jikinsa,ni kaina bansan me yasa jikina yayi sanyi ba kuma banyi wani farinciki da ganinsa ba. Ya dago fuskata, sannan yahaskani da wayarsa, lafiya my choice? Na sa hannu na tare hasken,lafuya mana Yaya mai ka gani? Na karbi jakar hnnunsa tare da cewa sannu da zuwa,bai amsa ba sai dai ya ce, na ganki cool ne, kamar ba kiyi farin ciki da gani na ba. Na ce, bacci na fara. Sannan nayi gaba na bude masa daki ya shiga. Ya zauna bakin gado tare da fadin, na gaji yau Sosai,8 ta wuce na baro Abuja, kuma da safe zan wuce na zone Kawai sabida kin nuna zuwan nawa yana da muhimmanci. Na ce, to Kayi wanka zaka warware. Ya ce to. Kafin ya fito wanka na kawo masa tuwo daman shi nayi a daren miyar zogole. Sai da yaci na fitar da kwanukan, sannan na shiga gurin Mujidat tana zaune da waya tana chatting, na ce, ya kamata fa ki dinga bacci. Ta ce, ba zan yi hira da kawayena ba? Na ce, kuyi tayi, akawo yaro babanshi yazo. Ta kalli yaron sannan ta kalleni, ya yi bacci. Na Isa gurin yaron na dauko shi, ban tsaya jiranta ba na kai shi. Aliyu ya mike tsaye zumbur likacin da ya kalli yaron duk yadda Sadiya Ke bashi labarin kamannin shi da dan bai zaci har hakaba. Ya kalli yaron kusan minti 1, sannan ya miko mini tmkr yana tsorace,na maida hannuwana baya. Kayi masa addu'a kamar sauran yaran ka duk dadai baka samar da shi ta hanyar da shari'a ta amince ba, sannan ka yi masa hudu ba,ya daga murya rikeshi mana Sadiya. Na juya na fita. Abin mamaki sai ga Mujidat labe tana lekenmu, na tsaya turus ina kallonta, ita ma ta yi tsuru-tsuru na ce, a'a dama kina min labe? Ta soma Sosa kai, sai kuma ta shiga borin kunya, kin zo kin daukarmin yaro ba dole inbiba? Na ce, kina zargin zan cutar miki da yaro ne? Yaya ya fito ya mika mata yaron "ungo yaron ki kar ku tada min da yara suna bacci. Ta amshi danta ta tafi, ni kam a gurin na tsaya na ma rasa tunanin da zanyi, tun yanzu kenan kafin a daura Auren? Shi kam bai so yanda ya yi ba kada ma mu tada masa yara suna bacci, maimakon ya gargadeta kan cewa Kar tasake yi min labe, bai yi hakan ba sai ya shige abinsa. Ni kam dakin yarana na nufa amman ko zama ban yi ba sai ga kiranshi, sai da wyrta kusa tsinkewa sannan na daga. Meyene? Yace, zomana,sai da na dan bata lokaci, sannan na je. Kai kawo na samu yana yi a cikin dakin, ina shiga ya nufo ni ya kama hannuwana. Sadiya asirin da muka rufa zai tonu sabida kamannina da yaron nan ya dauko,ina ganin gara mu fadawa Iya Kawai ita kuma Mujidat ta yi tafiyarta tunda dama dan Kar Iya su sani ne zan aure ta, ni wallahi bana son ta, zata iya tarwatsa min iyali,na zame hannuna daga nasa na zauna bakin gado tare da rike kaina na ce, Yaya ba dan Kar asirin ka ya tonu Kadai ba ne na ce ka aureta, don gudun kada kuci gaba da haihuwa a titi babu aure, don nasan bazaku rabuba. Shima ya zauna, sai dai in itace baza ta rabu dani ba Sadiya, amman wallahi ni tuni na barta,na girgiza kai, Yaya yin Aurenku yafi a kan barin shi, don Mujidat ta tabbatarmin da hakan kuma na San zaku iya... hawaye suka soma zubomin cikin rawar murya na ce. kuma duk laifin kane. Ya kwanto ni jikinshi, wallahi Sadiya nayi nadama matuka, kuma naji kunyarki Sosai ki yi hakuri kidaina kuka, Kecefa kike Karfafa min gwiwa,kike bani shawara. Ya dago fuska ta. Hankalina yatashi da yawa ganin kamannin yaron nan,nasan sai dai mutane su ji mu Kawai, ammababu wanda zai yarda cewa ba yaro na bane. Ya share min hawaye. Ki yafe min. Na ce, Yaya ni dai alfarma Kawai zan roka a gurin ka guda biyu. Da sauri ya ce, na miki alkawarin yi miki su fadi inji. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Na ce, na farko duk rintsi kada ka juya min baya ko ka wulakanta ni. Ya rike kafaduna muna kallon juna, insha Allahu Sadiya ba zan miki ba ko bisa kuskure insha Allahu. Nace sai na biyu, izini zaka yi min in nemi koyarwa a makaranta, ko L.E.A ta nan unguwar Mu'azu. Ya yi shiru yana nazari, can ya ce, kin gane Sadiya ba wai ina son hanaki bane, nafison ki nutsu a gida wallahi bana son matata tana yawo. Na ce, akwai dalilina, ka ga Kwanan nan zamu zama mu biyu a Kasan ka, duk wata bukata da zan nema a wurinka dole ne ka yi mana mu biyu, inko inada nawa zan yi bukata ta ba tare da na takuraba. Ya ce, wannan bai kai dalilin da zan bar ki ba sai dai in bar ki sbd tun farko na amsa cewa nayi miki alfarmar da kika nema,da dai tun farko na san wannance alfarmar da bazan yardaba, sai dai kimarki ta wuce in amince, sannan in dawo in ce a'a, kije kiyi koyarwa ki, amma ki tsare mutuncinki da nawa.Na sauke ajiyar zuciya 'nagode mijina, Allah ya saka da Alheri. Ya lumshe ido sannan ya bude. Yanzu wane suna za'a sa masa? Na ce, a'a wannan shawarar tsakaninkane da Mujidat, da safe ka sameta ku tattauna. Bai ce kalaba sai ya kwanta rigingine. Da safe falo ya zauna yace in kirata,ta fito tana yatsina cikin Riga da wnd ta zauna, ya ce, wane suna kika zaba? Ni kam mikewanayi. Ya ce,zo mana My choice. Na ce, ina zuwa. Dakina nashiga na bar su dan zancen na su ne.Ta mike daga Inda take ta koma kujerar da Ke daf da shi ta ce,Sweety kaine zaka bashi suna in dai nice nafi son sunanka don yaron yafi kama da kai. Darling kabiyani dakabani mai kama da kai. Ya waiwayo ya daga mata hannu, tsaya!baki dacikakken hankali ko? Ni ne nake bada haihuwa?Ki sawa yaron ki duk sunan da kike so amma ban da nawa kin gane ko? Ta ce, to ina son a samun Abdul-kareem. Ya ce, ya yi Allah yaraya shi.tace ameen. Sai maganar auranmu. Ya mike tace, na zata tun ranar dana haihu zamuyi maganar shine yanzu na kawo maganar za ka tashi? To bari kaji daurin auren nan in ya wuce gobe za ka ji mamakin abinda zai faru.Ya shigo daki, ina jiyo duk yadda sukayi nace, Yaya ka amince nima ina son a daura a wuce gurin kawai,ya ce, ba zanyi yanda takeso ba, tana ganin itafa wata cikakkiyar marakunyace. Bata San cewa ina daga mata kafa bane sabida Ke,nace, dan Allah kai dai gara a yi ko a wuce gurin. Sam ban zaci za a yi wani suna ba, don haka ban tanadi wani batun sunaba, kuma da zai tafi yace Usman zai kawo rago shi ma bai yi min batun suna ba, amma muna da kayan abinci na ce masa ya siyo mata sababbin kayan sawa ita maijegon,yace bazai siyoba, ko dan kyalle. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Washegari tin misalin 8 na safe naji bugun gida, dama na rufo kofar gidan ina sauri zan kai yara makaranta don munyi latti, kafin in bude sai ga Mujidat ta fito da gudu tana cewa, oyoyo Momy! Kaucewa nayi ta bude, ashe 'yan uwanta ne daga Lagos su 4, Mamanta,Babanta, Kawarta da Kanwarta suka kalleni nima na kallesu, don hauka har uban suka shige cikin gidan, nasa yarana a mota na fice cike da takaicin da ya Aliyu ya ja mana. Har na dawo raina a bace. Mujidat nasamu a kicin tana ta fasa kwai ita da kanwarta suna hada abincin karyawa, ban kula su ba, na shige dakina cike da bakin ciki. Ko da naji bugun gida ban fito ba a zatona wadansu dangin nasune, amma sai na ji wayata tana ruri na daga ashe Usman ne yace Madam ki bude gida ga Ragonnan,nabude ya shigo da Ragon muka gaisa yace kuyi hakuri banzo barkaba, wallahi Sadiya takaici ne ya yi min yawa bana son ko ganin matar nan, bare Dan, sanann ga kunyarki. Nayi murmushi tare da cewa, Haba dai, gurina bakomai ya Usman. Aunty Abida fa? Ya ce, suna lafiya,naji tana cewa zatazo anjima. Na ce, yauwa Dan Allah Yaya ina jiranta yanzu, bari in kira maijegon ka ba ta, dama danginta sun zo. Ya ce, daga ina, oho bansan garinsu ba. Nace dashi. Na leka dakin sunyi dirshan a kasa suna tacin abinci suna zuba yare har da uban, a raina na ce tabdijan! Hauka. Na ce Mujidat kizo inji Yaya Usman. Ta ce, in yazo ganin yarone ya shigo mana, ni bazan fitoba. Na ce, Rago ya kawo muku, shima sauri yakeyi. Ta mike tana yatsina ta fito. Ni kam ban koma gurin su ba sai da na ji yana kirana. Madam na tafi.,na fito nace to Yaya mungode, amma lallai ina jiran Aunty, yayi dariya zan fada mata kiyi ta hkr Kinji? Na ce ba komai. Sati 1 Kawai da suka yi a gidan naga takaici, gulma gurinsu ga shegiyar kazanta. Babanta wai ya so ya ga Aliyu saboda a yi daurin aure su zasu tafi ,kuma ganinsa baza su iya dawowa ba, shi kuma yaya yace dansu Bazai bar aikinshiba sai dai na lallabasu da cewa su tafi in Ya zo sai a je can garin. Haka kuwa sai tafiya suka yi, ya so ma har Mujidat ta bisu can, amma da yake ta san shi in har ta sa kafarta tabisu to sam ba zai nemeta ba, don haka tace aifa sam ina nan na baka lkc ka gama zaman ka dawo muyi aure. Yafi wata sannan ya dawo, lokacin Abdul-Hakeem yayi wayo sai gogewa yake yi, don ma ba ta san bashi nono sai madara, wai bata san nononta ya lalace, na ce Allah Sarki wata rana ma ke kanki sai kin lalace bare wani nononki. Aliyu kam tuburewa yayi cewa ba zai auri mujidat ba, nima na tubure cewa ban yardaba, matsalar da ta janyo rigima har sai da Usman yazo gidan.Usman ya cewa Aliyu, alkawari Kayi tun farko, kuma musulmi ne kai ka san muhimmancin alkawari, sannan matarka tana da gaskiya ba za ku rabu ba. Mujidat da Ke daki tana jiyo wa kuwa ta fito,ta ce, ai mutuwa ce Kawai zata raba su, kuma ta dibarwa kanta lokaci in har ya cika bai ce komai a kan auran su ba za ta maka shi a kotu, sanan zata nemi yan jaridu manema labarai ta ce shine a matsayin wanda yayi mata wayo yayi mata ciki bisa alkawarin zaiaureta, amma yanzu yaki cikawa.Take Aliyu ya tashi ya watsa mata mari, sannan yace bazai auretaba, taje tayi duk abinda take ganin zai fitar da ita,da kyar Usman ya tausheshi, ni kam daki na shige ina kukan takaici mijina wanda nake girmamashi da daraja shi, amma ga wata banza datti tana wulakantashi,a fili na ce shi ya jawa kanshi. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Sun yanke za'a kai sadakin ta can lagos, amma tare zasu har da ita da Usman da kuma su Yaya Suleiman. Aliyu ya ce amma sai dai ta fadawa dangin ta kada suyi maganar jariri, duk ina daki ina jiyo su,lokacin ne na soma sabon kuka saboda kishin mijina ta dai tabbata lallai mijina auran zai yi. Ya same ni a daki bayan tafiyar Usman cikinn halin kuka, ya tsorata mutuka, ya dagoni yana tanbayata dalili, ce masa na yi kaina ne kurum ke mini wani irin ciwo.ya kawo min magani ya bani a baki, sannan ya kwantar da ni. Cikin dare na farka naganshi zaune, na dafa shi,lafiya Yaya? Ya ce, Sadiya, ina ganin har in mutu ba zan daina nadamar laifin da na aikataba, ina cikin dana sanin zinar da na aikata da banyi ba da ban fada cikin wannan halin ba, yanzu tunanina da wane yare zan fahimtar da Iya cewar zan auri wannan yarinyar? Tsoron tunkararta nake da zancen Aunty wallahi,ban san me yasa a duk lokacin da mijina ya shiga damuwa hankalina kan tashi tausayinsa ya cikani,gaskiya da mutane suke cewa In kana son mutum kana tausayinsa. Sai na kwantar da kaina a kirjinsa, sannan nace. Don wannan Yaya Kar Ka damu, in Allah ya kaimu da safe zan samu Iya, ko kuma muje tare da kai. Ya ce, Sadiya bana son yadda nake ta saki karya don ki fitr da ni. Na ce, Allah zai dubani ya yafe min karyar insha Allah, tunda dan gyara nayi ba don batawaba,Ya rungumeni yana fadin, Sadiya Ke ce rayuwata, Ke ce abar alfaharina. Na ce, nima kaine rayuwata. Muka kwanta cike da damuwa a zukatanmu. Goma tagota muka fito zuwa gidan Iya. Yayaya yi mutukar kyau cikin shadda waganbari mai kalar sararin samaniya(sky blue), Hula mu hadu a banki,itama kalar kayan, wanda kyan shi ya tona tsadar shi, yana ta kamshi. Ni kuwa Atamfa na sha Purple mai ratsin fari, Takalmi da Hijabina kuma farare, muka jero tamkar sabon aure muka nufi gidan Iya. Tana zaune kan sallaya ta idar da salar walaha da fara'ar ta dubemu tana cewa. Masha Allah ina zaku haka tabarakallah amma kunyi kyau. Muka sa 'yar dariyar yake dan nayi Imani yadda nake tsananin fargaba, hakan nanma Yaya yake ciki. Nace gurinki muka zo. Yaya ya ce daga nan za mu je kasuwane ne sai muji ko kina son wani abun?. Ta ce, bana bukatar komai Gadanga. Duk wani abu da zan nema ka ajiye min, ga firji da ka sai min ina ta saida ruwan sanyi ina samun na batarwa, ba abunda nake bukata Allah ya shi muku albarka yasa yayanku su goyaku.Muka ce ameen,tace, yan uwnka sun zo sun fada min cewa ka kai musu kayan abinci su duka ko?yayi yar' dariya, 'Iya wannan aikin Sadiya ne, ta ce duk wata in dinga sai musu kayan abinci shi ne muka fara da wannan watan. Iya ta kalle ni da dariya, 'Hali Dubu rubutun dutse, halinki dubu duk na alkhairi, na san sai ke 'yata. 'Ta kalli Aliyu. Dadin auran mace tagari kenan zata dinga bai wa mijinta shawara ta gari. Aliyu ya dube ni, sannan ya kalli Iya, 'Wannan gaskiyane Iya. Nace, 'Yanzun ma gurin ki muka zo kan wani batu.....tace, to, ya aka yi? Na kalli Yaya, shi ma ya kalle ni na ce, 'Ka fada mata. Ya ce, 'A'a ban san ta inda zan fara ba ki fada mata kawai in ta amince shi kenan. Iya ta ce, 'Ku fada min mana, kun daga min hankali. Na sunkuyar da kai, 'Iya dama mun yi shawara da Yaya ne a kan cewa zai ....za ya... 'Sai na yi shiru. Ta ce, 'Inajin ki. Na ce, 'Zai auri bakuwar nan ta gidanmu sabida tana da hankali kuma.....' Da tsawa ta katse ni, 'Ke! Da kata kin san me ki ke fada kuwa? Waye zai auri wa? Na kalle ta 'In.. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Yaya ne (Na nuna shi) zai auri Mujidat, tana da hankali Iya sosai. To ya ce yana son kara aure shi ne na ce ya aure ta. Iya ta rabka salati,sannan ta ce, 'Amma ban taba sanin ke mahaukaciya ba ce sai yau, ni ban taba jin inda aka ce ga wata mace ta ce mijinta ya yi mata kishiya? Ta sake zabga salati tare da riqe haba tana kallona. 'Ko ni nan da nake tsohuwa bakeba a ce babanku zai dawo duniya zan amince ya yi min kishiya? Dan haka ban yarda ba. Muka kalli juna da Yaya, ta ce, 'Meye matsalar ka da har kake son kara aure? Ko har yanzu bata son haihuwar ne? Ya ce, 'A'a wallahi bata da laipin komai kuma ba inda ta kasa, dama sabida raya sunnah ne kamar yanda yake cikin musulunci, yarinyar nan kuma Iya ta musulunta ne in ta auri wanda ba na kwarai ba za ta dauka haka halin musulmi yake, amma mu za mu yi mata mu'amula ta kwarai yanda ba za ta yi da ta sanin musulunci ba. Iya ta ce, Eh, ai dama ke Sadiya ba a yada ke gurin magana,ni fa dan ke nake fadan nan amma ke na lura kamar zuga ki nake, wai ke ba kya kishin mijinki ne?nayi 'yar dariyar yake, sannan na ce 'Ina kishinsa mana amma hakan ba zai hana shi ya kara aure ba. Ta yi shiru tana kallon mu can ta ce, 'Ni fa ban yarda da yarinyarba, kallonta nake kamar wata 'yar bariki ko wadda ta buga duniya. Muka kalli juna,Ya ce, 'Ai kin san zaman Lagos, sannan ba ta dade da Musulunta ba.Nace, 'Eh, ba ruwan ta Iya. Ta ce, 'Oho! In ma da ruwanta ke ki ka sani tunda kin ji kin gani ai shi kenan, ni me zan ce, Allah yasa alheri. Yauwa, kwanaki yayanku kece min 'yan uwanta sun zo na ce shi ne don rashin mutunci ai sazo su min godiya. Muka sake kallon juna ni da Yaya, na ce, 'Af wannan laifina ne Iya ni ce ya kamata in rako su kiyi hakuri. Ta rike baki tare da cewa, 'Uhum! Abind ya same ki kar Allah yasa ya samu sauran dangi. 'Na ce Iya na gode bari mu tafi. Haka muka bar Iya baki bude tana mamakina,ni kuma na ce masa mu tafin dan kar ta canza ra'ayi,duk da ta amince, amma ba wai ina murna ba, bani da yanda zanyi da ya wuce in kauda da kai a yi auran, na san mata da yawa za su ga baike na amma ina san su sani DA KISHIYAR WAJE GARA TA GIDA.Daga nan gidansu Anty Abida ya ce mu tafi,,ni dai muna tafe ne ba kamar yandamuka taho dazu ba, ba wata hira bare annuri. Mun samu Usman a gida don haka muna shiga suka fita. Aliyu ya kalli Usman 'Aboki, Iya fa ta yarda da batun Mujidat. Cikin mamaki Usman ya kalle shi tare d fadin, 'Kai haba? Aliyu ya ce, 'Allah da gaske. Usman ya ce, 'Banzata ba, ya aka yi ta amince da sauri haka? Ya ce, Kai bari kawai,yarinyar nan Sadiya aboki ba ni d abind zan biya ta, ita ce ta shawo min kan Iya har ta amince da batun,sai na lura da akwai wasu shakku daga zuciyarta, Allah yasa ba ta gane cikina Mujidat ta haifa ba.Usman ya ce, 'Ka kara rike matarka da kyau,ina fada maka a wannan zamanin ba za ka samu tamkar ta ba, ina fada maka ko Abida matata ba za ta yi wannan jan aikin ba, tana fada min sai dai ta ce tana karfafawa Sadiyane dan tasan za ta iya kuma hakanne mafita. Aliyu ya ce, Allah ya ba ni ikon riqe ta da gaskiya. Usman ya ce, Ameen, yanzun mu tafi gidan su Yaya Sulaiman mu ji yanda za a yi. Aliyu ya ce to, Allah ya rufa asiri. Abida ta dube ni ina kuka, kallo na kawai take yi bata hana ni ba kuma bata bani hakuri ba. Sai da nayi mai isa ta. Sanan na share hawaye na, sanan ta dafa kafada ta. Sadiya kada kiga cewa ban baki hakuri na barki ne ki rage radadin dake zuciyarki, gaskiya ne in ka zubar da hawaye yana rage bakin ciki, amma in tambaye ki mana? Na kalle ta da jajayen idanuna, ta ce kukan nan na menene kike yi? Murya ta a dishe tana rawa na ce, anty... Abida ina da matukar kishin Yaya Aliyu,Dan ban san irin son da nake yi mashi ba, kukaba yakunshi abubuwa dadama, amma kishin mijina shine a gaba, wai mijina zamu raba da wata, inna tuna haka hanjina na kaduwa, da na sani ban amince ya aure taba.... Sabon kuka ya kubuce mun.Tace kijure, Allah yasan nufinki, karki bari yaga karaya daga gareki, domin ba mijinkiba har mijina ya ce kin burge shi kullum cikin yabonki yake tare daba mijinki shawarar cewa yayi maki kyakkyawar ruko, dan haka ki cigaba da dannewa. Na ce, to anty zan kula, yanzu na sha kanshi ya amince in nemi koyarwa, sai dai ban san ta ina zan fara ba. Ta ce kada ki damu shugabar makarantar firamare ta L.E.A unguwar Mu'azu kawar yaya ta ce zanyi mata magana sanan karamar hukumar Kaduna ta kudu ma babban wan su Usman yana gurin ne kuma nasan zai tai maka. Na ce, to, aikuwa nagode Anty Abida Allah yabar kauna. Tace amin. Haba ai ba komai wallahi. Nan muka wuni nakasa cin komai, Anty Abida har Dan wake tayi min wai taga inaso, amma da kyar naci uku ina taunawa tamkar ina tauna magani, ko ruwa na sha sai inga tamkar magani . Anty kanta ta shiga damuwa tana min fadan kan in kashe kai na a banxa. Na ce mata. Anty kiyi hakuri cikin kwanakin nan ko gida na bana iya cin abinci in na dauki littafin marubutan nan in dan duba sai komai ya tsaya min inkasa fahimtar me nake karantawa mai makon in karanta litafi sai dai shi littafin ya dinga neman karantani da ko ina da yar matsala inna karanta sai ya dan rinka debe min kewa. Ta ce ai duk ki ajiye batun littafi kirumgumi mai kankat wato, ALKUR'ANIR KAREEM. Na sauke ajiyar zuciya,, tabbas Anty Alkur'ani yana sanyaya zuciya mu kan musalmi bamu da kaico sai godiya ga ubangijin da yayo mu a musulmi. Ta ce haka ne Allah kasa mu mutu a cikin musulumci muna a musulmai. Na ce amin. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Kafin su dawo ta sani na wanke fuskata nayi yar kwalliya, duk da fara'ar da nadingayi sai da yaya ya gane nayi kuka, duk lokacinda na kalle shi sai in ga idanunsa na kan fuskata har dai ya kare ya ce Sadiya kukan me kikeyi? Muka kalli juna da Anty abida ta ce, sam bata yi kuka ba me kagani? Yayi dan yake shi dole murmushi, ko ba jami'in tsaro bane ni, kun san daini ba yaro bane. Na share zan cen da cewa, yaya mu tashi dan yara na jira na in daukosu. Ya ce madan saurareni. Abida ta kalle shi ya ce, nifa bana son abin da zata shiga matsala, in auren nan zai kawo mata damuwa wallahi sai a fasa duk abin da zai faru ya dade bai faruba kowa ya ji cewa nayi wa wata ciki ta haihu, daga nan fa? Na runtse ido, don Allah yaya mu bar maganan nan, nace maka ba damuwa nake ciki ba, ka yarda dani. Usman ya ce aboki ina ga dai na dawowa da hannun agogo baya din nan a bar shi. Abida ta ce ai sadiya jaruma ce bata cikin wata damuwa, kuma malamai sun sha fada muna cawa in Allah ya rufa maka asiri yayin da ka aikata wani laifi to kai kada kayi kokarin tonawa kan ka don haka barin batuna haka shine mafi a a'ala. Haka dai muka baro gidan nasu bayan sun yi mana rakiya. Saty daya bayan nan suka shirya tafiya lagos, sai dai ban da ya Sulaiman saboda suna son yan da haduwar su da dangin mujidat zai kasan ce, haka nan basa son yanda ya Sulaiman ya san cewa dan da ta haifa na shi ne. Sun tafi da Usman da shi Aliyun da kuma Mujidat da Danta. Sai dai lissafin da aka

Chapter 16 of 25