Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yaran nan fa karya suke yi. Aliyu ya ce ba karya bane Iya, sai dai sunfada maki a daidai lokacin da muka shirya na san in Usman yazo zai gamsar da ke. Wasa wasa har Usman ya shigo Iya ba ta daina fada ba shi ma shiru ya zauna yayi har sai da iya ta numfasa, sanan ya shiga bata hakuri tare da lallashinta. Ya tabbatar mata da cewa an daidaita, ta ce ina son jin wacce matsala ce ta taso har yarinya ta kode haka? Sanan in san wake da matsala? Muka kalli juna ni da yaya, Usman yace zai fi kyau Iya abin da ya wuce ya wuce muyi adu'ar Allah ya kare gaba. Ta ce sam sai fa ta ji menene ya haifar da rashin jituwar saboda gudun sake faruwar abin nan gaba dan ta san wane irin mataki zata dauka. Inko ba'afada minba to sai dai ya rubuta takardar sakin Sadiya ya bani. Kai Usman ai kasan ko mai, badan son raina akai auran nanba sabo da gudun haka, don haka yanzun ma bata baciba ya bar min 'yata. Aliyu ya ce Usman fada ma Iya komai duk hukuncin datayanke a kaina na cancanceshi. Nayi saurin kallon Usman, ko da wasa bazan bari Iya tasan ainihin abin da ya faru ba duk da na san Aliyu dan ta ne amma bazanso tajiba. Muryar Usman ce ta katseni, wato ainihin abin da ya faru....Nayu zaraf na katse shi gaskiya Iya ainihin abin da ya faru laifinane.Na kalli su Kausar kufita waje. Suka fita nasun kuyar da kai ina tunanin wane laifi zan dorawa kai na? Dama na ce ne bana so in sake hai huwa, yara uku sun isheni, shi ne yaya ya dauki gaba dani. Dakin yayi tsit, na fada haka ne dan nasan babu abun da iya take so kamar taga yayan ta suna haihuwa, na saci kallon ta ni ta ke kallo cikin bacin rai. Ta soma sabon kuka yanzu Sadiya ke ce baki son hai huwa? In baki haihuba me zakiyi? Wasu ma son haihuwar suke da kudi amma ba su samu ba, sai ke ishashshiya. Na soma hawaye don tausayin kaina, nazama kyandir in kona kaina don in haska shi, na ce Iya ki yafe min, domin shi ma yaya tuni ya yafe min. Na kalli Usman a gabanka aka yi komai ko? Usman ya lumshe ido, zuciyar shi cike da mamaki bai taba ganin irin Sadiya ba. Duk irin cutar da mijinta yayi mata amma ta yarda ta shafawa kanta kashi, don kurum ta wanke shi. Na danyi dim dan tsoron kada Usman yatona dan naga yayi shiru, na ce yaya Usman kuba Iya hakuri. Iya ce ta daka min tsawa da cewa, kada ki damu mutane, kuma ina son ki sani wanan ya zama na karshe, in na sake jin wani laifi makamancin wanan zaki ga matakin da zan dauka. Ta kalli yaya Aliyu cikin taushin murya kayi hakuri Aliyu, inshaAllahu bazata sake kwatanta haka ba. Yaya Aliyu dai ya kasa koda daga kai, jikinsa kuma ya mutu.Zan mike ta ce ke zauna ban gama da ke ba,nakoma na zauna. Ya aliyu ya zuba min ido, sanan ya kalli Iya. Iya kada ki damu, ko mai ya wuce ta shi mu tafi. Iya ta ce kuje zatazo yanzun, suna fita Iya tace, na san cewa abin da kika fada ba shi bane ainihin matsalar ku ba, kilama kin fada ne dan ki wanke shi. Amna in haka ne da gaske ina mai yi maki nasiha ki jitsoron Allah, ki bi abin da mijinkike so, duk mutum na kwarai ba zai ki yin murna da kyautar da Allah yayi mashi ba. Koma menene zan ci gaba da yi maku adu'a, tashi kije. Na mike zaraf ta re da cewa, to Iya nagode, insha Allahu bazaki sake jin kan mu ba. Ta ce kuma kar inji kin daki yaran nan, gashi a ban za kin sa suna jin haushin mahaifin su, har suna fadin basu son yadawo. Na ce bazan masu komaiba. nakirasu muka fita. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Usman ya kalli Aliyu bayan sunfita ya ce aboki in har ka sake cin zarafin matarka hakika Allah bazai kyalekaba. Dubi yanda ta dorawa kanta laifi don ta wanke ka. Aliyu ya ce, nikaina baka ga na kasa maganaba? Lallai Allah ya taimakeni Sadiya ta taimakeni, wlh kaji na rantse maka yau da Iya ta ji ko mai na kade, ba zankara kima a Idontaba. Sannan sai ta raba ni da matata. Usman ya ce, to sai kayi mata adalci tunda abin yazo da sauki. Da muka fito duk suka nufo gun mu Usman ya ce Sadiya Allah ya shi maki albarka,da'a ce mata da yawa suna da hali irin naki, na tabbata da aure da yawa ba zai mutuba. Nakalli Aliyu, shima ni yake kallo. Ya ce my choice na gode, ina sake rokonki afuwa ki yafe min. Na ce ya wuce. Na tasa yarana muka tafi gida nazaunar dasu,Kausar nace yanzu kun kyauta kenan da kuka sa Iya kuka? Kausar ta ce Momy Al'amin ne. Na ce to kar ku sake, Al'amin ya ce, momy ba zan sake ba. Ko daran ranar Aliyu banda hakuri babu abinda yake bani, duk ba wannan ce matsalata ba, ya ya za'a kare da batun (H.I.V) da kuma batun yarinyar nan? Don haka na waiwayo na dube shi daga inda nike kwance, shima rigingine yake idanunsa suna kallon sama. Tsakaninmu mutum guda zai iya kwanciya tsakaninmu, na ce ' Yaya! Bai amsa ba, na daga murya 'Yaya' shru, da alamu tunaninsaya tsawaita. Don haka na mike na kunna fitilar dakin,haske ya mamaye ko ina,na tsura mashi ido cikin faduwar gaba. Nagirgiza da ganin hawaye suna gudu layi bibbiyu daga idananun Yaya daya yamiko zuwa kumatu. Yayin da dayan ya bi gefen ido. A fili nafurta'Inna lillahi wa inna ilaihir raji'un! Yaya! Na kira shi tare d zama kusa dashi na kwantar d kaina a kirjinshi, kunnuwana suna jiyo yanda yake ta kokawa d kukanshi a kirjin. Ina zaton yana kokowar danne kukan ne, yayinda shi kuma kukan ke ta yunkurin fitowa. Da sauri na dora tafin hannuna a kirjinshi ina ta shafa kirjin, wai nufina in taya shi lallashin kukan. Bakina ya soma fadin 'Haba Yayana, me kuma ya faru? Tuni na yafe abinda kayimin, namaka alkawarin rayuwar da tafi wadda muka yi baya dadi. Sai naji hannunsa a gadon bayana, ya damki rigata d dan karfi alamun har yanxu yna ckin cikin kunci, muryarshi sarke cikin rawa irinta mai kukan baqin ciki. Ya ce, Sadiya ba anan matsalar take ba, Sadiya baqin cikina ciwon in ya kasance ina da ciwo...'' kasa karasawa yyi don kukan da ke son subuce masa. Nace Yaya ko kana da ciwon nan zan zauna d kai,ko banidashi zan yarda ka sa min. Nima kukan ne ya kufce min,cikin kukan na ce 'Yaya zan zaunada kai haka ina sonka.'' Sosai ya rungumeni tsam ''Sadiya ba zan cuce ki ba, bayan Allahya tsare ki,nikuma nine nacuci kaina, domin duk wanda ya bar dokar Ubangijinshi ya dauki son zuciyarshi, ya saki koyarwar Abul Kasim, Manzonmu mai tsira da aminci, ya bi ta Yahudu d Nasara to bako shakka karshenshi nadama da kuma danasani, lokacin da ba su da amfani. Sadiya lokacin da shaidaniyar yarinyar ta ziyarce ni da ban bi son shaidaniyar zuciyata ba duk da haka bata faruba. Ba ina kukan ciwon da kila zai zama ina da shi bane, ba ina kukan ci gaba da rayuwata ba ne ina kukan yanda zan bar ki da wahalar jinyata da dawainiyar yarana. Sannan kukan abinda da zan tarar a cikin kabarina ban san me zan gaya wa Ubangijinaba, Yayi shru cikin shassheka, nima kukana ya qaru. Nace, Yaya inshaAllahu bakadashi, ka ci gaba da neman gafarar Ubangijinka, Allah mai amsar tuban bayinshi ne.Ya yunkura ya tada mu zaune ya dago fuskata muna kallon juna ido cikin ido,ya ce 'Sadiya ban makara ba ko? Na girgiza kai, Baka makara ba Yaya. Ka daina tunanin cewa zaka mutu ka bar ni,insha Allahu kai ne wakilin gawata,kai zaka fara binne ni Yaya. Ya rungume ni tsam a kirjinsa tamkar ya buda kirjin ya saka ni. 'Ina sonki Sadiya,ina son yarana,ina son iya. Amma haka nan in ta kasance zan barku...... Wayarshi ta katse maganarsa, tamkar kada ya dauka don ji yake komai ma ya tsara shi rayuwarshi ta kare. Ni ce na dauko wayar na mika masa, Adewalene direbansa na can, tamkar kada ya daga na ce'Yaya ka amsa mana.' A kasalance ya yi sallama,Ade ya amsa sannan ya ce, 'Oga dama madam ce a Asibiti ba lafiya,shine take tasa aka dauki lambata a ka kira ni. Me? Naji Aliyu ya furta da karfi, 'Mujidat ba ta da lafiya?? Nima gabana ya yi wata mummunar faduwa,tamkar ni ce na daga wayar. Idanuna waje ni ke tambayr me ya same ta? Aliyu ma da ya rasa me zai fada sai ya maimaita tambayar da nayi. 'Adewale meyasame ta? A can bangaren Adewale ya amsa da cewa, shi fa bai sani ba,amma ga ta bari ya bata. Aliyu cikin daga murya ya ce,kada ka bata,bana son jin muryarta,macuciya. Na yi saurin fadin 'Yaya a bata wayar mu ji daga bakinta, da gaske tana da ciwon? Shiru Yaya yayi yana kallona,hankali tashe bayn ya katse wayar. Na ce Yaya don Alla ka kira a bata mu ji, ba don son ranshi ya kira ba,sai don na nace da cewa ya yi hakan. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 A handsfree ya saka ta, Ade ya daga ya ce bata,murya can kasa ta ce 'Hello' ya katseta da cewa,'Kiran ubanme kikace amin? Na fada miki bani bake, kuma ina Allah ya isa da sanin da na yi miki,macuciya.Dama kin san cewa kina da (H.I.V) shi ne ki ka like min sabida ki cutar da ni da Iyalina? Wani kara ta saki mai karfi tana fadin 'A'a, a'a ni ba ni d (H.I.V) sai dai in kai ne kasa min. Muka kalli juna ni da shi, ya ce 'Yanzun wane ciwo ki keyi dazakice baki da (H.I.V)? Tace, 'Ina dauke da cikinka ne yana wahalar da ni,amma bani da (H.I.V)....' Ya katseta da karfi Cikin tsawa cikin masifa take fadin 'Kada ka sake zagin ubana,wannan cikin naka ne ban taba yarda na bi wani ba tare da abin karyar cuta ko ciki ba sai kai daya danike So. In ma (H.I.V) ne kaika samin kamar yanda ka sa min wannan cikin,kuma ina sonka sani ba zan taba cire shi ba,zan haifi dan soyayya,zan zo har garinku gurin danginka don su san kana da da' ko 'ya da ni. Haka nan masoyiyarka da ka yi min wulaqanci sabida ita,ita ma ya dace mu san juna. Duk da tsawar da yake daka mata bata yi shuruba,sai data kai aya. Ni kam baqin ciki ya hana ni magana,sai hawaye. Na mike zan fita,ya riko min hannu tare da finciko ni na fado jikinshi,ya kashe wayar yana fadin. 'Haba Sadiya, ina ce murna zamu yi tunda ba ciwon gare ta ba? Na mishi wani kallo tamkar in hau shi da duka,cikin zafin rai na ce 'Ba gara ciwon ba da cikin da ka yi mata? Yanzun me ka shirya fadawa danginka in ta zo musu da da'? Ya ce, ki barta bata ma isa ba ne,taje can ta nemi Uban cikinta. Ya tausasa murya. 'Na rantse miki bazan karbi cikinba, kibarta zan nemi transfer in bar garin ba shienanba. Yayi ta lallashina ina kuka, ya yi ta tsara min zantuka har nayi shiru,amma sam naki magana, ga ciwon kai tamkar zai rabe. Ya jawo ni jikinshi 'Ba kincekin yafe min ba? Na dafe kaina tare da fadin 'Wash Allah na.. A rude ya tambayeta ''kan ki na ciwo ne? Na daga kai alamun 'Eh''ya kawo min panadol ya ba ni na sha. Haka ya yi ta ririta ni da lallashi tare da maganganun kwantar da hankali har bacci yadaukeni. Shi kuma ya mike ya shiga sintirin kai kawo dakin, daga bisa niya dau ki wayar shi ya nufi can harabar gidan, dan kada ya tashi wani daga cikin iyalin sa. Yanzu ya fi shakkar yaran sa, domin ya fahimta lallai in yayi wasa zai sha mamaki dasu. Layin mujidat ya kira, ringing na uku ta dauka Aliyu yace, na kirakine in gargadeki, kiyihanzarin fita harkata, kuma ki nemi uban cikinki, ni ba nine uban sa ba. Dama karuwa tana da miji ne da har zata sami uban da? Ta soma kuka, tana cewa kaine ubansa, kabidani ta lalama in ba haka ba zaka ga yanda ake iskanci. Kana kirana karuwa kai ya sunan ka? Gara ma kazo cikin satin nan in ba haka ba za ka ganni a Kaduna. Aliyu ya ce dole zan dawo tinda gurin aiki nane, amma ki sani babuke, zai fi maki sauki ki zubar da wanan cikin tunda baki tuna ubansaba... Mujidat ta katse shi ina zaton baka sanni ba ne shine yasa ka ce haka, amma zan nuna maka kalata. Kuma bazan zubar da cikin ba, wanan cikin shine ya zo min dai dai lokacin da nake bukatar shi zai tai maka min sosai. Wanan cikin shine zai hana rabuwar mu ni da kai, kasani mun hadu har abada . Ta katse wayar. Ranar da zai koma tamkar inyi me don ta kai ci, nasan dole sai sun hadu da yarinyar nan ga ciki. Shi kanshi tunda akayi batun cikin ban sake ko dariya ba, ya lura da hakan. Da zai tafi sai min dadin baki yake gaskiya ni fa Abban kausar gara min ace daga ni har kai muna da ciwon kan jamau da batun cikin. Nan ya rike min hannu, don Allah ki saki ranki ki aje maganar yarinyar nan a gefe, ke kiji a rankima an shafe babin ta a bayan kasa, kinji don Allah. Na ce hum! Shi ke nan Allah ya saukeka lafiya. Ko da ya sauka yana ta kokarin yawan kirana da sauransu. Nakula sosai yana son shikam lallai sai mun koma tamkar da, nima dai ina ta kokartawa don ganin anyi hakan duk da ina tsoron mai zai biyo baya kan batun yarinyar da cikinta. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Aliyu da yake zaune a bayan motar sa ya dubi Ade wale da ke tuki ya ce masa kasan gidan da Mujidat take? Ade wale ya ce a a sai dai gidan yarta yasa ni inda ya taba kaita sai ko asibitin da ta kwanta. Aliyu ya daga waya ya danna mata kira, har ta katse bata daga ba. Ya shareta da farko amma sai kuma ya tuna yana son kwarai su tattauna abu mai mahman ci. Don haka sai ya sake daga wayar da nufin kiranta, amma sai ga kiranta ya shigo, cikin sauri ya daga. Ta ce kamar kana jiran kira na? Aliyu ya ce ko daya ina dai yunkurin kiranki ne. Tayi yar dariya. Ashe dai ka damudani? Yace ke bankiraki don naji salon zancekiba, inaxan same ki? Ta sake yin yar dariya da ya tsana a yanzun, ka bari ni nasan indazan sameka,tunda ka shigo garinnan nasami labarin zuwanka, sanan ka manta nice na kiraka ba kai ne ka kirani ba da har zaka ce bakakirani dan kaji salobane. Ya katse ta, ki fada min inda xan same ki yanzu nace,tasake yin yar shewa tare da fadin ashe dai har yanzu kana tare dani, ni nasan tunda ka shigo dole ka neme ni ko dan cikinka. Cikin fushi ya ce, kar ki tsamma ci cewa haduwar mu zata haifa maki da mai ido, ko kusa ganina bazai farantamaki rai.... Ta katse shi da cewa, in ji wa? Ai ko zaka kashe ni ganinka ya fiye mun komai farin ciki ko kasan ina sonka fiye da mahaifana? tayaya zan kasa farin cikinganinka? cikinhaushi yace Amma kin yi asara tunda baza ki fadin in da kike ba bari in koma gida Cikin sauri tace ina Hotel din Hamada Daki na sahashida,ka iso lfy masoyina Tsaki yaja sannan ya katse layin sannan ya kalli direba muje Hotel din Hamada ko cikin harabar hotel bai shiga ba Aliyu yace ya tsaya ya sake kiran layin ta ta daga tare da fadin bude ka shigo mai sona yace ke shashasha fito ina can bakin gate sannan ya katse bai tsaya jin me xata ce ba sanye da dogowar bakar jallabiya da dan kwalinta sai takalmi baki mara tudu sam yanxun baya ko son ganinta don haka ya daure fuska tamkar baitaba dariya ba sam,yanxu baya ko son ganinta don haka ya daure fuska tamkar in ya bude baki xai fito da wuta don hada rai, tana isowa saitinsa ta nufa don tasan gurin xamansa yasauke gilashin tana kallonshi gabata ya fadi amma sai ta dake saboda iya bariki tace maigidana ina son in ganka cikin iri kamewar gaskiya kada kace aikinka kafito mushiga ciki ya yi mata kallon banxa tamkar yaga kashi sannan yace shiga mota muje tace ina? tace. sai kinji? Tace bari in dauko jakata yace (cikin tsawa ) in kin koma ciki ni kuma zan fi cikin sauri ta zagaya ta bude mota tana fadin gida zamu je kenan? ko tanka ta bai yi ba yace Adewale sai da ya harba motar kan titi sannan yace Oga. gida zamuje? Aliyu yace babban asibitin garin nan zamuje ta zaro idoda sauri tace yin me? ku tsaya in sauka bazanbikuba ,tasoma lalube zata bude kofa Aliyu yace bazan hanaki ki fita ba amma ki sani in ki fado kan titin nan ba lallai ne ki rayu ba wanda hakan ba zai dameniba yan uwanki ne za su yi rashi,ta dan shiru tana tunanin me zatayi don kuwa itakam bazata taba yarda a cire mata cikinnanba Don tasan shi ne kadai abinda ya rage mata wanda zata rike Aliyu da shi dole ya saurare ta ta kalleshi nifa bana son ka kai ni a cire min ciki ya dubeta. ina ruwana da cikinki bashi ne matsalata ba ta sauke ajiyar zuciya tare da jingina kanta a jikin kujerar mota ta tabbata gaske ne ba abinda zai kaisu kenanba ta sake kallon shi me zamu je yi ya dauki wayarshi yana naiman wani layi ya karata a kunne tare da fadin in mun je kyaji,Suna shiga dakin ganin likitan wanda ya riga ya shaida masa yana tafe, ya baiwa likitan hannu suka gaisa. 'Yan sanda sukan saba da likitoci sbd yanayin ayyukansu, don haka Aliyu yasan likitoci da dama a Asibitoci daban daban. Ya nuna Mujidat gata nan, Mujidat ta soma zare ido, sai dai ganin Likitan ya dauko kayan gwajin (H.I.V), sai ta kwantar da hankalinta dan tasan bata da shi din amma Likitan ya ba da lokaci wata uku nan gaba su dawon a sake gwadawa, ya umarta shima a gwada shi. Sakamakon dai duk daya ne, babu, Aliyu zuciyarshi yanzun ta nutsu d cewa bashi da (H.I.V) ya yi wa liktan godiya sannan suka yi sallama. Suna fitowa ya shiga motarshi. Direba zai tada kenan tazo ta bude zata shiga. Aliyu ya ce, (cikin tsawa) 'karki shigo min mota, sannan banida buqatar sake ganinki a rayuwata.' Ta ce, 'Labari kake yi'. Ta dafa cikinta, 'in kai danka ina? Kai ba ka san bala'ina ba ko? Za ka sha mamakin abinda da zai biyo baya in har ka ki tsayawa mu sasanta, Mujidat kawai ka sani amma ba ka san halinta ba. ya daka ma Adewale tsawa, 'Muje mana, 'Take ya figi mota suka yi gaba in da har Mujidat ta ku san faduwa, kofar motar ta rufe gam! Suka bar ta a nan. Ta bi motar da kallo cikin kunan rai, a fili ta ce 'Wannan bai sanni ba, bai san yana cin albarkacin so bane? Amma zai san ya kirama kanshi ruwa.' ta nufi titi don hawa acaba. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Tun lokacin d muka samu sabani d Yaya Aliyu,kusan ko yaushe dakin yarana ni ke kwana don samun sauqin wasu abubuwan, ko na ce tunane tunane. Yau ma niyyata kenan inna gama can zani cikinsu in kwanta, zan fita dakin kenan wayata ta soma ruri. Na koma kan gado na kwanta sannan na daga tare da yina sallama. Ya Aliyu ya amsa,sannan ya ce 'My choice Alhamdulillah.'Na ce, 'Shin ne abin godiya. Ya ce, 'Ina mana murna gaske yarinyar nan ba ta da (H.I.V). Na lumshe ido cikin jin dadi,amma sai na tuno d cikinta, na ce 'To cikin fa? Ya ce, 'Ina ruwana d cikinta, ban bi ta kanshi ba, don ba matsalata ba ce,' Nace, 'Matsalarka ce, tunda kwanka ne. Babu yadda za'a yi mace ita daya ta dauki ciki. 'Raina ya soma zafi, ya ce 'Ni kadai nayi hulda d ita?? cikin bacin rai na ce 'Amma kai ka ajeta a gida.' Kuka ya subuce min, sai na kashewayar nayi jifa da ita na ci gaba da kuka. Inaji yana ta sake kira amma na qi dagawa, inna tuno wai Aliyu shi ne ya yi ma wata ciki, abin nan yana soya min rai. Duk ranar d aka kawo mana dan me zai fada ma duniya? Mezai fada ma zuri'arshi? Musamman yaranshi masu wayon tsiya? Banji bude kofa ba, sai dai muryar kausar naji tana cewa, 'Momi wanene? Da sauri na share hawayena ta ce, 'Momi Abbanmu ba ya ce kun daina fada ba? 'Na ce, 'Jeki dauko min magani, kaina ke ciwo na kasa tashi ne. Da gudu ta fita, saiga ta da shi har da ruwa. Ina sha ne naji sakonni suna ta shigowa cikin wayata,na bata kofin na ce 'Kije ku kwanta, kiyi muku addu'a zan yi waya da Abbanku. Ta ce, 'Momi kin fasa yi mana tarihin d ki ka ce za ki yi mana na rayuwar Manzon Allah? Na ce,'kin ga kaina na ciwo,sai gobe. My choice ki bari mu sake daidaita kanmu, ki bari mu saita rayuwarmu, ki amince da ban hakurina. Tsaki naja sannan na duba dayan sakon. Kin yi alkawarin cewa kin yafe min, kamata yayi ki mance kmai,ina sonki my choice, kece rayuwata. Na sake jan tsaki a fili na ce, 'Kamar gaske. Wani sakon ya sake shigowa. Don darajar Allah da girmansa d darajar lokacind muka kasance a baya, d martabar soyayyarmu,ki amice da ban haqurina. Amicewarki kurum shine daga wayata , xan kira ki yanxun . Dagawarki itace zata tabbatar min cewa kin hkr. Na ajiye wayar tare da yin rigingine na kumaruntse idona, matsalata ina da rauni da sanyin zuciya, bugu da kari ina son mijina.Bana jure in wulakantahi, tausayinshi na daga cikin abinda ke sa in kauda kai ga abubuwan da yake min...ringing din wayarsane ya dawo dani tunanina. Na dauki wayar tare da yin sallama cikin makoshi , yace"ngd da daga wayata, yanxun na yarda kin yafe min.Inason mu koma kamar da, yanxun ki fada min abinda kikeson muyi. Nace kamar me? Yace wlh bana son bacin ranki ne, shine nake son ki tsara mana yanda zamu shimfida sabuwar rayuwa, wadda baza ta katse ba."Nace kamar gaske, kila sai kasa na soma farin ciki daga baya ka canza min. Allah sarki Sadiya sarkin son soyayya, sai gani ina 'yar dariya, nace duk lkcn da ka so. Shima yayi 'yar dariya.Inzo gobe? Nace koh yanxu ma ka zo. Yace insha Allahu ranar jumma'a xan taho, roko nike ma Allah yasa suyi min transfer zuwa arewa.Nace amin yace ina yarana? Nace suna dakinsu sunyi bacci. Yace, to bari in amsa waya xan sake kiranki.Ba'a fi minti dayaba ya sake kirana yace zan fita barayi ne a cikin wani kauye, shi ne aka kira ni yanxun. Nace Allah ya tsare. Nayi birgima a kan gado, zuciyata fes. Wata zuciyar tace lallai ke dai sakara ce, duk irin abinda mutumin nan ya kunsa miki shinecikin mintin da bai kai 10 ba har kin manta?Nadan yi tsai ina son inyi tunani, tabbas xuciyata shagalalliya ce ma'abociyar son a sota, da zaran abin son ta ya fuskance ta sai ta bude da yawa ta shiga cikin farinciki.Idan abin sonta ya juya mata baya sai ta shiga kunci ta tsuke , ta dinga zafi. Nayi murmushi tare da rungume filo, a fili na furta.Allah kakauda shedan tsakanina da mijina. kullum yanxn ina cikin farinciki sbd xan kira yaya a lkcn dana so, kuma shima yana kirana, sannn ga hirar kwantar da hankali tare da ban baki da yake min kullum.Tun ranar Alhamis naje gidan kitso na kuma biya gurin mai zana fulawr dayis tayi mana har da Kausar da Mama. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Tun safiya Jumua'a na hana kaina sakat da ayyuka. Funkasau na kwaba sai kuma farar shinkafa, nayi kunun zaki na sayo fura.Duk abinda nasan yanaso haka na tanade shi, a wayarmu ta karshe baifi saura minti hamsin ya isoba don haka na feshe yara nima na saka kayan da bai sanni dasu ba, a sunan Aisha na dinka su, atamfa ce blue mai ratsin yellow. Ina jin kwankwasa gida nace su Kausar Abbanku, maimakon su biyo ni kamar yanda da can mukeyi, sai naga duk sun tsaya.Kausar ma hade rai tayi, na kamo hannunta,kuzo muje mu taro shi. Biyo ni sukayi , na bude gida jan gwarzo na yau cikin kakinsa yake, ya aje jaka muka rungume juna cikin murna da doki.Muka kalli yaranmu lamarin ya zame musu tamkar sabon abu.Kausar ma rufe fuska tayia lamun kunya.Al'ameen ne ma naga yana tadariya. Muka kalli juna ni dashi , ya sakeni yaje ya rungumi Kausar, sannan Al'ameen da ya aje shi ne ya dauki Maama ni kuma na kwashi kayansa muka nufi ciki.Tamkar da ya basu leda dauke da kayan ciye ciye tasu tsarabar, nan muka barsu faloya shiga wanka, kamar da nice na taimaka masa yayi wanka.Tsaf ya shirya muka fito gurin cin abinci, yanda yaran suka ganmu har sun soma sakin jiki, abinci kam ya rasa da wanne xai soma.Ya kamo hannuna yana yabon lallena, kausar dake can gefe tace Abba nima kaga nawa, harda Mama akayi mana . Yace , iye! 'Yan gata kunyi kyau yarana, nayi kasa da murya ina cewa Kausar fa hankalinta yana kanmu. Yace, duk zatonta yau ma rigimar zamuyi? Nace wannan ya zama tarihi. Muka sa dariya, daya kammala ya mike.Dauko hijabinki kuzo mu fita. Yara suka hau tsalle muna gaba ni da yaya, su kam suna baya.Gidan iya muka soma zuwa, muka bata tsarabarta. Sai gidan Usman nan ne ma muka dan dade.Sun kama hirar siyasa ni kuma muka kulle da Anty Abida cikin daki, shawarwari tayi ta bani kan cewa kada in sake inyi fushi ko in dauki gaba da mijina don yana bin mata.Yin haka zaisa ya kara zakewa.tace kin ba shi dama kenan, amma in kika jawo shi kika ninka abinda kike masa ada, kika hada da addu'a sai kiga komai ya daidata. Nace bakisan wani abuba Anty, yanzun yarinyar tana da ciki, ko Usman bai fadawaba, abinda ke batamin rai kenan,

Chapter 13 of 25