Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shi ne babbar jami'ar ta.Ku dai yan zamani baku da magana sai dai in kun tashi aure kun fi son yan boko sabo da tarbiyan yayan ku.To amma kada ka manta ni banyi boko ba, amma duk in da kuka shiga yabon ku akeyi ana sha awarku.Aliyu yayi dariya, to iya in kin lura ai baban mu yayi boko, kefa kika ce mun lokacin su yaya sulaiman suna yara sun zo da home work shi yake musu.Nima lokacin da na taso sune suke yi mun ba, tace to wanan ce tarbiyar?Ban ce ilimi baya cikin tarbiyya ba, amma bashi ne gundarinta ba.Gun darin tarbiya shi ne ka dora dan ka kan hanyar Allah da monzo (S. A. W) su rinjayi komai a kan mazaunin shi.Sanan ka cusa musu Tauhidi su iya rike Amana,Cika Alkawari,Tausayin na kasa da taimakonshi, Girmama na sama, in dan ka ya san wanan sai ka hada masa da ilimin zamani da na adini shi ne tarbiyya.Kai in dan ka ya san wadancan ya rike ko bai je boko ba zai yi rayuwa ingantacciya.Aliyu ya ce, haka ne zancen ki Iya, Allah ya sa muma muyi tarbiyar yayan mu kamar yanda kuka yi mana.Ta ce ameen.Ina da ga ciki ina jin su na ce, in dai Iya ce duk musun ka da gardama tana yi maka baya ni sai ka fahimta.Abin da ya bani al'ajabi da mama ki, da dare na je kai masa abinci dama fakon sa na yi tayi dan ba zan yar da wata magana ta hada mu da shi ba, tunda ya ce sai da turanci, niko dan tsinta tsinta na iya.Dan haka ina ganin shigarsa ban daki na dauki abincin na nufi dakin sa na ajiye zan fita sai na hangi wata mujalla can kan katifar sa, ni kuma da shegen son kalon hotunan yan film.Na zata irin tasu ce yan fin din India, sai na koma na dauko na bude jiki na ya dauki tsuma ganin mata tsirara.Da sauri na rufe wato dai mujallar ta tsiraici ce, na sake bude wani shafin da sauri na rufe, ina fitowa yana isowa kofar dakin.Ya ce cikin harshen turanci me kike so na cecikin hausa, dama abinci ne na kawo maka.Ya matso ya damki kunne natamkar zai cire shi.Ba na ce kada ki kara yi mun hausa ba?Nayi shiru dan ina tsoron yi masa turanci ya ji ba dai dai ba ya ci uba na.Ya sake matse kunnan, cikin turancin da zaniya na ce yayi hakuri.Ya saki kin ci sa'a daga yanzu ba hausa tsakanina da ke.Duk cikin turanci yake maganar.Ni dai nayi daki ina Al'ajabinshi, mutum kamar na Allah ashe dan iska ne, ya tasa hotunan batsa yana kallo.Shi kuma da ya shiga dakin sai yaga kamar an jawo mujarlar daga inda ya ajiyeta, a ranshi yace wato dai yarinyar nan ta bude mujallar nan kenan,In ko haka ne ban ji dadi ba, amma sai wata zuciyar ta ce, kada ka zargeta, domin bata da rawar kai, tsoranka ma takeji ba zata taba maka komai ba, sai kurun ya samu natsuwa tare da gaskata hakan.Kwana biyu yaya Aliyu yayi ya tafi, niko cikinkwana biyun nan binshi nake da kallon mamaki.Bayan tafiyar shine na samu ci gaba da karatu na a makarantarmu ta maimuna gwarzo.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Kwanci tashi su yaya Aliyu an kammala wanan karatun, buki sosai akayi ko na ce walima dan su yaya Sulaiman su har can suka je nan gidan mu kuwa mun aikatu.Anyi wainar shinkafa, da su zobo da kunun zaki, daga can suka turoshi kaduna (headquarter) a matsayin A. S. P Aliyu Tukur.Ranar da ya zo gida na jima a uwar daki ina tunanin fitowa saboda tsoron maganar da zan masa da turanci, gashi a fallon iya suna fira.Na zauna ina bitan abin da zan fada masa da turan ci, can iya ta kwalo mini kira na amsa, ta ce me kike yi?Na fito, ya kalleni dama tana ciki, kin wani kunshe kamar wani munafiki?Na ce, sannu da zuwa. Cikin turanci na yi maganar, shi sai lokacin na tuna mai da batun wani turanci.Ya kalli iya sanan ya kalle ni ya amsa, na ce ina taya ka murna, ya ce ya gode.Ya tambayi nawa karatun na ce lfy lau.Da sauri nayi waje ina tsoron kada ya daukowani zancen da va zan iya amsawa ba, a rai na na ce, baka sanan wannan ba na fi sati ina haddar su.Bayan na fita ya cewa iya, to kin ga dai yarkita soma zama baturiya, iya ta ce, eh, ai hakan yana da kyau.Tunda ya dawo kullun zancen shi da iya ba ya wuce kayi aure gadanga, ka fito da mata sai dai in bai zo gidan ba, kokuma bai zo mata fira ba.Har ta kare ta ce yaje gidan hajiya talatu ya nemi diyarta Jamila, yace iya kiyi hakuri har inga wacce ta yi mun da idona, bana son cushe cushe.Ta ce, duk fadin unguwar Mu'azu har yau baka ga wacce kake so ba?Sai ya ce, ina nan dai ina binkitawa, har dai ta hakura ta zura mashi ido.Daga baya naji suna hira da yaya sulaiman wai ta sama mashi magani tana ganin kamar bashi da lafiya, niko da naji wanan xancen lokacin cewa nayi a raina, ras yake kila ma neman matan shi yake yi a waje tunda mai ya hada mara lafiya da hotunan tsiraici?Kuma bayan nan ina zaton yana kalon fina finan tsiraici, don lokuta da yawa in yana kallon in nayi sallama dakin zai kai abinci ko wani abu sai yayi sauri ya kashe, sanan ya ce in shigo.In kaset din arziki ne menene na kashewa?Amma na sa a raina wata rana sai na kama shi. Haka kuwa watara na xan kai masa abinci darana lokacin aikin dare yayi da safe ya dawo,Iya kurun ya gaisar muna aikin waina ya shige daki ya kwanta.Sai kusan sha biyu sanan ya farka, lokacin Iya ta tafi gurin sabo mai shikafar waina, ta ce in ya farka in kai masa ruwan zafin shida waina in kuma bredi zaya ci to in kai masa.Ya fito ya shiga wanka, da sauri na dauki dan flask din sa na ruwan zafi na nufi dakin, ko mai a kashe yake amma na san zan kunna in gani tunda wanka ya shiga saboda shi mutum ne mai dadewa a wanka.In dai ya shiga tamkar zai canza fata, don haka ina lokacin sallah ya katato xai shiga ban daki iya kance bari muyi alwala dan in ka shiga sai lokacin salla ya fita baka fito ba.Na jona komai ya kawo na ce oji bulumme can kasa dan muna funci aikuwa CD yana gama login sai ga mata da maza tsirara suna aikata masha'a.Da sauri na kashe na fita naje na ci gaba da aikina abin da na gani ya girgiza ni kuma naji haushin kaina da karan bani na.Na fito na dauki waina da bredi naje nayi sallama ya ce in shigo na shiga na ajiye xan fita ya ce tsaya, me kika shigo yi nan dakin?Gaba na ya fadi na ce ni flask na kawo, ya ce daga nan sai kika yiyi me?Cikin in ina na ce, banyi komai ba ya Ali.Ya tsareni da idanu, bashi da tabbacin nayi wani abu amma yana shigowa yasan an shigo.Ya kalleni, jiki.Na fita sanan na harari dakin na tafi.A raina na ce dan iska, amma wani lokaci sai ya kure wa'azi sai kace na Allah. Kwanci tashi ba wuya, muna cinye kwanakinmu har mun kammala (SS3) mun zana jarabawa kuma lokacin ya zo dai dai da saukar karatun mu na alkur'ani.Munyi komai cikin nasara, kuma nayi walimata a gidan mu inda iya ta matsawa ya Aliyu sai ya buga mun memo wanda zan rabawa kawaye na.Sauran yayyansa ma sun taimako, baba na kuwa da naje zaria na fada masa dubu biyarya bani wai inyi hakuri da yake ina zuwa danhutu can wani sa'in iya tace inyi sabon dinki da kudi na.Dangi kam sun xo babu laifi, har yan uwa na na zariya, babanmu ya zo da su komai na yayi babu laifi.Da yamma ni da kawata Aisha muna kwashe kujerun da muka zauna akai mukayi walima a waje da kawaye na.Mun hada su guri daya sai naga guda biyu wanda ya Aliyu da wani abokin sa suka zauna su na hira.Ta ce, kije ki amso wadancan cikin zolaya tayi maganar, don tasan ina jin tsoron shi.Na ce, ke kije ki amso.Tayi yar dariya bari inje.Tayi tamkar zata nufi gurin sai ta fasa.Muyarshi ta katse maganata da zanyi lokaci daya kuma gaba na ya fadi, Ke! Na wai waya, zo nan.Naje na rusuna na gaida su cikin in ina ya ce, ke daga jin maganar ki baki da gaskiya ko?Na ce, a a.Ya ce, to me nene nayin in ina din?Nayi shiru, ya kalli abokinsa ga ta.Abokin ya ce, ina yi muki murna da yin saukar alkur'ani mai girma, Allah yasa anyi na tsoron Allah.Na ce, amin.Ya Aliyu ya ce, jeki dama murnar zaiyi maki.Ina tafiya ya kalli Aliyu ya ce, kanwar nan taka tayi fa.Ya Ali ya ce, ok, iskancin naka har agida ma zaka yi?Auwal ya ce bada wani abu na ce ba, cewa nayi tana da kyau.Kai da ma ka shiga kayi yar gida tunda duk matan dake sonka baka kallon su.Ali ya ce don me zan tsaya kallon yayan mutane, alhalin na san cewa ba auran su zanyi ba?Auwal ya dan yi masa dukan wasa a kafada tare da cewa, ko jiya munyi gulmarka da Sajen Bello, wai ina ma shine mata keyiwa wanan shishshigin, da sai ya more kuriciyarshi son ranshi, amma kai kullun cikin Azumin dole, in kaga mata sai kace kaga Abokanan gaba.Aliyu ya ce, ban ga anfanin zina ba, koda ba haramun bace mutum ya gujeta, ya kyamace ta, dan kare kansa daga cututukan zamani.Ina fada maka ina da kyama ba zan iya hada jiki da wayan can ba, kuma dole in naga mata in hada rai tun da ba halali na bane, kuma ba muharramai na bane.Kullun dai ina adu'a Allah ya bani mace ta gari mai kamun kai, kuma da kuke bin matan Allah ya shiryeku, kai gashi kayi auran ma amma ba ka daina ba.Kayi hattara duk abin da ka shuka shi zaka girba, kana kallo wani can zai bata rayuwar yayan ka yadda ka fada ta yayan wasu.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Auwal ya ce , ka samu cikin adu'a abin ne dawahalar bari, mata ne nishadin rayuwa, hira da su ma a kwai dadi ne.Tsaki Aliyu ya ce in kaso kaji dadin ba?Ni kuwa bana fatan in ji dadin fira da mace wadda ba tawa ba, ina nufin halalina.Auwal ya mike, bari ni in tafi kai dama malami ya kamata ka zama ba dan sanda ba.Sam Aliyu be mike dan raka shi ba, daga nan suka yi sallama.Shi kam tunani ya shiga, shima yana sabo wajen kallon fina finan batsa da karantar mujallan batsa, duk da cewa bai taba aikata zina ba ya san wanan laifi ne babba.Kuma in mutum bai daina ba wata rana zai kai ga aikata zinar, kuma tunda Allah ya rufamini asiri tsawon lokaci yana yi ba wanda yataba ganinshi, ya kamata ya daina.Ya tuna lokacin da ya fara, wata rana yaje dakin su Auwal da rana lokacin suna jami'ar Ahmad Bello ta Zaria, ya ga wani novel a dakin ya dauka ya karanta, ashe na batsa ne.Daga lokacin sai yaji yana so ya gani, ya ko je wani shago a kasuwa ya siyo kaset din tare da mujallar tun daga nan lokaci zuwa lokaci sai ya siya ya kalla, sanan ya kona su ya sake siyan wani.Shi da kanshi ya sha fada wa kanshi cewa, yanda yayi Imani zai tsaya gaban Allah haka yayi imani za a tambaye shi yanda yayi ya sami kudi da kuma hanyar da yabi gurin kashe su.Me zai ce game da wanan kudin da yake sawa yana siyan batsa?San nan baya karanshi da komai sai karata da masu hankali?Lallai wanan abune da ya kamata yayi makansa tun kafin ya mutu.Ya mike tare da kudircewa daga yau ya tuba,ba zai kara ba. Dai dai gwargwado ba xa a ce bani da kyau ba tunda Allah bai halicci mumuna ba matsawar mutum yana da kyan hali, balantana a ce mutum musulmine.Aina ya ga kyau sai dai kuma in ba tsafta, ni fara ce sol amma bani da dogon hanci.Wanan baisa fuskata muni ba, haka idanuwa na matsakaita ne, ni mutum ce mai tsananin kwalliya ko alwala nayi sai na sake sabuwar kwalliya.Haka nan iya bata gajiya da siyan mun kayan kwalliya, sanan bata ganin bekena duk lokacin da zan bata gurin kwalliya.A cewarta ya mace doki ce sai da kwalliya, abinda kawai bata yarda da shi ba shi ne, ayimini dinkin da zai nuna surata, nan ne zata ce ba zata bada kwamasho ba gurin yada zina.Ta ce, shigar da yawancin mata keyi ita ce ke haifar da zinace zinace sannan zata zuba ko nawa ne ta yankan mini yadin hijabi amma mayafi dai sai dai inyi asusu in siya. Shima din ban isa in siya karami ba sai babba, kuma mai kauri ban taba jin haushinta ba dan nasan tana kare nine daga afkawa cikin shaidan.Dai dai misali ina da farin jinin samari masu sona, dan ma iya bata bari in fara fita zance da wuri ba sai da na kai SS2 duk masu zuwa gurina da aure suke sona.Sai dai ni cikinsu banga wanda yayi mini ba irin injishi kane kane cikin raina din nan ba, fada haka iya take cewa maza ki tsaya ruwan ido daga karshe kowa ya gudu kizo kina nema.Ai yanxu lokacin ya mace mai hankali ake dubawa wanda yake da hali mai kyau sanan ba jahili ba kuma ya kasance yanada yar sana'ar da zai rikeki, to ki kamashi.Allah shine mai azurtawa, in da rabo sai kuyi arzikin tare, ke in ma baku samu anan ba to ya baku na gobe kiyama.Yawan yi mun wanan nasihar yasa nake ganin zan iya tsaida Idris kuma zan iya auransa amman sai mun zauna da kawata aminiyata Aisha.Mun zauna da ita ita ma tace, gaskiya duk cikin masu sona babu kamar Idris a hankali.Mun yanke shawarar in tsaida shi ita kuma dama akwai makocinsu Bello dake sonta.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Wata safiya Iya tana kwance ba lafiya dole na fasa zuwa makaranta tunda mun riga mun hada kullun waina, sai kuma ciwon cikin dare.Ya Ali ya shigo da shirin fita, don bai san bata da lafiya ba sai da ya shigo dakin, ya girgiza da ganinta kwance cikin bargo dakyar take magana.Arude ya ce, ya babu lafiya ne?Tace, eh, yace meyasa ba a tashe ni ba a gida fa na kwana?Ita wacen sakaryar ba sai ta fada min ba.Iya ta ce ni na hanata ta ce bari ta taso ka, ya cire hula, bari muje Asibiti, bari in samo mota, ta ce, a a naji sauki.Fita yayi sai gashi da likita wani dan nan unguwar ya duba ta sai gashi hadda ruwa a dora mata.Ranar dai bai fita bahar rana, bai taba birgeni ba irin ranar, duk wani abu sai yayi, hatta bata magani a baki da abinci sai gurin la'asar sannan ya fita.Su yaya Sulaiman,Zakari da Sani duk sun zo da matan su, sanan makota na ta zuwa.Da yaje gurin aiki ya bada uzirin shi sai ya dawo kusan shabiyun dare, jikinta yayi sauki.Ina jiyo hirarsu,rokonshi take yayi aure ta ce Aliyu bani da wani burin da ya wuce inga auranka, kai na fuskanci kafi son sai na mutu sanan zakayi aure.Jikinshi yayi sanyi, dan ya kasa tuna ranar da ta kira shi da Aliyu, cikin tautasar murya da lallashi ya ce, zan yi iya, in sha Allahu kina raye.Ta ce, kayya, gadanga kullun haka kake cewa, ni dai ai tuni na cire rai ka tashi katafi na yafe maka Allah yayi muku albarka kai dasauran yan uwanka.Yarinyar nan sadiya dan Allah ko ban tashi ba kada ku bari ta koma zaria ta zauna gurin wannan yaron hardai ta sami miji kuyi mata aure.Ya ce, iya ke ce da kanki zaki aurar da ita insha Allahu, ta ce shi kenan tashi kaje ka kwanta.Hankali tashe ya fita bayan ya tai maka mata ya kawota cikin daki, na tashi idona naxubar da hawaye, na taimaka mata muka kwanta.Ina kuka kasa-kasa ta ce,Sadiya lafiya? Tace iya bana so inji kina cewa zaki mutu ki barni, ta ce in fada ko kar in fada sadiya ba zan kara lokaci ba sai dai in ajalina bai zo ba.Da kyar bacci ya daukeni, lokacin iya tayi nisa da bacci.Shima Aliyu tun da ya koma dakin shi fa ya kasa ko zama, lallai dole ne ya nemi mata, sai dai matsalar shi ta ina zai fara?Bai taba yin budurwa ba, bai taba soyayya ba, shi kuma yana ganin kamar raini zai ja masa in yaje kofar gidan su yarinya.Amma bari gari ya waye yaje wajen usman amininshi.Kafin ya wuce masallaci sai da ya fara lekowa dakin mu ni da iya duk muna sallah, sanan ya wuce,dan Allah ya kawo mata sauki a cikin daren daga masallaci gidan Usman ya wuce, ta wya ya kira shi cewa gashi a kofar gida,Usman ya ce, lafiya?Aliyu ya ce, lafiya ba lau ba, fito kaji.Da sauri usman ya bude gida ya fito, sama sama suka gaisa.Usman ya ce, aboki lafiya? Aliyu ya ce ina fa lfy, jiya tsohuwa ba lafiya, ta fara bar mun wasiya, sannan tayita jaddada min burinta kawai nan duniyar shine inyi aure.Usman yace aboki ba ita kadai ba, ni kaina buri na kenan, to tunda kaga tsohuwa ta tsananta gara kayi ko kwa rabu lafiya.Aliyu ya ce, ai baka sani ba, tunani na yanzu ina zanje nemo mata?Na rantse maka banda budurwa... Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 DARAJAR YAYANA1-02 Posted by ANaM Dorayi on 08:55 PM, 09-Mar-16 Under: DARAJAR 'YA'YANA ___________________NA ___________HALIMA K/MASHI Usman yayi yar dariya sanan ya ce, ni da zakaji shawarata wanan sadiya ta gidanku?Aliyu yace, ah haba?Usman yace, naga yanda ake yabon hankalin yarinyar, ko a gida tana da matsalane? Aliyu ya ce, sam ko a gida bata da matsala gaskiya, amma ban taba jin koda alamar sonta ba, to wanan yarinyar ma ina ganin ta tsaida wanda take so, in ma ba ta tsayar ba sai inga ta yi mun yarinya.Shekarunta sha bakwai fa yanzu in ban cika ma ba, usman ya ce, dai dai.Nafi son wacce ta shiga makarantar gaba da scondary a kalla ta mallaki hankalinta, ta san yadda zata kula dani sai nine zan koma in kula da ita.Usman ya ce, ba yaran yanzu ba, tunda kaga bata yiba in kaga wata da tayi maka ko a unguwarku ko a kafatanin unguwar mu'azu ka fada min yanxu anjima sai muje, kaga yanxu sai kaje wa iya da kwarin gwiwa.Aliyu yayi shiru yana tunani can ya ce, aboki kasan Allah?Nifa ba wai ina kallon mata bane, na layinmu ma ban sansuba balle na unguwa.Usman ya ce, to aboki ka tsaya a Sadiyar mai hankalice,Sadiya tayi.Aliyu yace inda ta kaicin yake sai kuma in kirata ince ina sonta?Usman ya ce in baka iyawa bi ta sama mana ka samu iya ka fada mata kana son Sadiya, nasan zatayi murna.Aliyu ya ce, aboki daina cewa ina sonta, zadai ayi aure amma ba wai ina sonta ba, Aliyu yace kuma ba zanyi karya ba tunda banji cewa ina sonta ba,har Aliyu yaxo gida tunani yake anya kuwa zai amince cewa yana son auren sadiya? Lokacin da ya shigo dai dai na bare magani na mikawa iya, ta afa tare da kora ruwa, ya tsaya ya rike kugu yana kallon mu, tunaninshi a wanan lokacin lallai babu wanda ya dace ya auri irina, bisa hujjarshi tacewa ba zai sami matsala ba wace take tsakanin iya da matan yayanshi ba.Iya tana kuka cewa cikinsu matar yaya Sulaimance kawai ta san darajarta, kuma tabbas hakane domin sai suyi wata uku basu zo sun gaida ta ba.Ita ba wai tana kwadayin abin hannunsu ba ne, a a ko ba komai taga yan jikokinta yayi, amma Sadiya bata da uwar da ta wuce iya.Dan haka yana nan ko baya nan zata zamo a karkashin kulawarshi, burinshi yaga ya daukewa iya duk wani matsalarta, su kuma yayinshi suji da iyalinsu. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Tunaninsa ya katse lokacin da iya ta ce, gadanga ka shigo ne?Yayi firgigit, na shigo iya.Na gaida shi na fita, shima a ranar bai iya yi mata zancen ba, karshe ma tunani yayi ya samu yaya sulaiman suyi shawara.Haka kuma bayan sallar isha'i ya nufi gidan yayan nasa bayan sun gaisa sai ya sanar dashi abinda ke tafe dashi.Yaya sulaiman yaji dadin zancen da Aliyu yazo dashi, sanan yace sai ka samu yarinyar ku daidaita, Aliyu ya ce, ina ga ba sai na sameta ba, indai iya ta amince shi kenan.Yaya Sulaiman ya ce, iya ba zata ki ba, yarinyar ce abinji, in ta ce bata sonka fa?Aliyu ya ce, ai nima ba wai ina sonta bane, dacewar auren kurum nake dubawa, shi yasa.Ya Sulaiman ya ce, shirme kenan, to kai in kaje wajen iyar ce mata zakayi ba sonta kake ba?Aliyu yayi murmushi ce mata kurum zanyi ina so na auri Sadiya, Sulaiman ya ce, Allah yayi mana zabi na alkairi.Ka bari zanje gurin iyar, duk yanda mukayi zakaji.Aliyu ya ce to.Yayi godiya yayi masa sallama ya tafi..Sulaiman ya sami iya cike da karfin gwiwa, ganinshi babu wanda zaikai iya murna kai yasan har goron albishir zata bashi.Amma ga mamakinshi yana gama labarta mata dalilin xuwansa sai yaga tayi kicin kicinda fuska ta ce kaine kaga sun dace ka bashishawara koko shine ya sameka da zancen?Yace, a a dazu ya zo mun da zancen sai kuma naga dacewar haka.Ta ce, to ka koma ka fada mashi ban amince ba, kace mashi ya nemo matarshi can itama ta nemo nata mijin.Jikin Sulaiman yayi sanyi ya sake tausasa murya ya ce, iya ban san dalilinki ba, kokuma akwai abinda kika hango wanda ba na Alkairi ba?Ta ce, na farko dai kasan halin gadanga, zuciya ce dashi ga saurin fushi, ga miskilanci tsiya, ga shegen jin kai.Sanan na sha ji ko in ce ya sha fada min cewa shi yar jami'a yake son aura.Niko tawa ko secondary din bata gama ba.Sulaiman ya ce, iya in kin duba tunda shi din ya ce ta mashi ai ina ganin ba za a sami wata matsala ba.Fir iya ta ki zancen, duk ta inda sulaiman ya bullo sai iya tabi ta wata hanyar, haka nan yaya sulaiman ya hakura ya fita rai babu dadi.Aliyu ya sunkuyar da kai yana sauraron sakonshi a gurin yaya sulaiman, sam bai zaci jin haka ba, amma sai ya ce, ba komai Allah yasa haka shine mafi alkairi, na shi ganin ba zai damu ba, tunda dama ba wai yana sonta bane.Sai dai kuma yanda ya tsammaci abun yafi haka, samun kanshi yayi da shiga damuwa, ko ba ya son yarinyar hakika ya tsananta dason aurenta.Ya samu iya da kan shi wata safiya yaxo gaida ta bayan yayi shirin fita cikin dakin sa.Ya ce, iya me yasa ba zaki bani auren sadiyaba? Ta lissafo mashi dalilinta kamar yanda ta lissafawa yaya Sulaiman takuma fada masayaje ya nemo mata can.Ranshi ya baci amma bai nuna ba, sai dai cikin sanyin murya ya ce, to shikenan iya na hakura, amma ba zan taba xuwa ko ina neman aure ba saboda ina da munmunan halayen da ban can canta a bani mataba,tace, ni ban ce ba,ya ce to iya tunda ba a bani a gida ba in naje nema a wani gida suka bani na cutar dasu tunda ba su san hali na ba,yana kai aya ya mike tare da cewa, sai na dawo.Ita kuma lafuzan nashi suka hanata magana.Ita zahiri ba wai bata son auren ya Aliyu da sadiya bane, na farko ta san halinsa, sanan tana tsoron ta tursasa min.Kullun Aliyu sai yayiwa iya naci amma taki ko ta ga zai dauko zancen sai ta hade fuska.Wata safiya ina kwance kangado ina fama da matsananciyar ciwon mara, dama mun rabu da yin waina tunda iya tayi rashin lafiya.Ya Aliyu ya ce, a daina yin wainar duk wata nake wanan ciwon marar.Yaya Aliyu ne ya shigo gaida iya, bayan sun gaisa ta ce, har ka shirya fita kenan?Ya ce mata eh, akwai wani case a hannunsane yana son ya kammala dashi kafin fitowar(AC) ta ce, to Allah ya taimaka, a can zaka karya?Ya ce, eh.Sanan yayi shiru ta ce, da magana ne?Ta sani in har yayi haka to da magana a bakin sa, ko da yake ta san zancen na sa daya ne, bai wuce na sadiya ba.Kuma tana son Sadiyar ta ji ma kunnenta in ta amince ruwanta don haka ta ce yaya autana?Yace iya dai maganar Sadiya, Allah iya ba maganar yabon kai ba, ina da kamalar da za'a bani mata, ya ko ta gidan waye 'yar taki ai ba kyau tafini ba,ya fada cikin sigar wasa, ta ce,duk da haka ba zan baka ba, kai ita fa tarigata fidda mijinta.Yace dan Allah iya ki fada mata kinji?Ta ce, au, nice ma zan fada mata?Lallai ba ma son auran nata kake ba.Ya ce, ni iya in na fada mata sai naga tamkar zata rainani ne.Iya ta ce, kun ji girman kan ba?Don Allah kayi hakuri nifa ka tayar dani,ba zan yarda ba.Aliyu da ya gaji ya fita.Tun daga lokacin da naji ya Aliyu ya ambaci sunana na mike zumbur hankalina atashe,ni Sadiya yaya Aliyu yake nufi ko wata?Kai in ko nice na more, dan gaskiya yaya ba irin mijin da zance bana so bane, tab!Wanan shine tsintar dami akala.A a iya kada kyi min bakin ciki, ina jin fitarshina fito da sauri ina kallon iya, ko zata ce wani abu, amma sai ta shareni, na ta nufintadaga yanda na dauki al'amarin tunda ta tabbatar naji.Ko daga irin fitowar da nayi, ganin iya ba zatayi magana ba sai na ce iya ta dubeni, wai ya Aliyu wa yake so? Ta tabe baki dan Allah rabu da shi, wai ke, na dafa kirji da karfi na furta da gaske?Ta ce, zan maki karya ne?Na ce to iya shine zaki ce mashi ina da wanda nake so?tace, au.Sharri nayi maki kenan?Ina ce ke naji kina cewa kin tsaida Idris? Na ce, ai ban fada mashi ba.Ta ce, meye nufinki yanzu?Kina so ki ce min kina son Gadanga?Nayi shiru tare da hade fuska, mamaki ya cikata, ta ce, Sadiya dama can kina son Gadangan ne?Na ce, nifa ban ce ina sonshi ba, amma ke meye dalilin da kika ca baki yarda ba?Iya ta shiga tafa hannu tana salati.Kin tirke nine lallai sai kinji?To ba wani dalili bane sai na kare mutuncinki, gadanga yana da zuciya, gadanga yana da fushi, sanan ga miskilanci,ina tsoron ki shiga matsala, gaki karamar yarinya, shi kuma shekaru sun dan soma ja.Da sauri na ce iya in dai dan wanan ne na yarda kinji?Ta

Chapter 2 of 25