Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kamar na mara lafiya, ko baya jin dadi ne?Ta ce, ba wani ke dai kina sonzuwa gurin mijinki ne, kuma ba zan hanaki ba.Na hade fuska, Allah iya nifa ba wai zanje bane fa.Ta ce, kije ki duba ko lfy,naki tashi, dan dama ina tsoron inje yayi mun wulakancin shi, ya ce nafita shiyasa naki zuwa.Ganin da iya tayi tabbas ba zan shiga ba kuma tabbas bai fito ba sai ta shiga dakin. Yan da ta ganshi warwas a katifa batare da ya cire ko takalmi ba, sai abin ya bata tsoro.Cikin saurin muyar ta ce, Gadanga!Ya dago kai da kyar ya dubeta, wani matsanancin ciwon kai ke damun sa.Ya ce na'am Iya sannu.Ya tashi zaune, ciwonkai ne ya hanani shigowa ciki.Ta ce, matarka nema ni take ce mun ka shigo cikin wani yanayi, bari a kawo maka magani ka sha.Yace zanje Asibiti in anjima bayan magariba.Duk kwanakin nan da haka nake ta yawo da ciwon kan nan. Ta ce, to kasha maganin yan xu sai kayi sallar da dan karfin jikinka, kaje asibitin da dan kwari.Ya ce, to.Ta kwala min kira Sadiya.Na amsa ta ce, dauko min magani panadol kizo da ruwa.Naje har gabanshi na ajiye da ruwan ina yi mashi sannu yaya, ya jikin?Ko kallo na baiyi ba bare ya amsa, mamakin yanda naga iya tan gutsi gutsi da maganin, ta dubeni dauko mun cokali.Na dauko ta jika ta bashi a baki tare da fadin, shiyasa nake fargaban ciwonka gadanga.Duk da dai ba yawan ciwon kake ba, amma kin maganinka shi ke wahalar da kai a ciwo dai dai yake da na yaron goye.Shi yasa duk lokacin da katashi ciwo bama jita dadi.Ya sha ya koma ya kwanta, dai dai lokacin aka kwada kiran magariba.Ta dube ni, bari inje inyi sallah, nima na biyo bayanta.Ta dakatar dani da cewa, jira tukunna muga yanda jikin zaiyi.A raina na raya cewa dan ta ga ina fashin sallah, shi kuma bashi da lfy.Shi kam yana kwance, na isa gurinsa gabana yana ta faduwa, duk da ina zaton zai daka min tsawa ban fasa yin abin da nayi niyya ba.Gabansa na tsugunna ina kwance masa takalmi, na cire su na aje gyafe, sanan na kwashi kafafunsa na zubasu a kan katifar.Har lokacin idanunsa biyu amma suna lumshe, haka nan hannunsa yana dafe da kai.Kusan minti shabyar ina zaune can gefe, ya tashi zaune yana kici kicin cire rigarsa, na taso na balle masa boturan, sanan na sabule rigar sai farar singiletin, ita ma ya kama ya cire.Na kalli kirjinshi gashi ne kwance na kauda kai don sai da naji wani iri.Ya sabule wandonshi, sai gajere na ciki, shima na kwashe su na zaba su a cikin kwandon da yake zubawa.Naga yana kokarin tashi nace mai zaka dauko in dauko maka?Ka zauna kawai.Ya ce, bani jallabiyata.Na bashi fara kal mai dogon hannu, ya mike zai fita, na ce ina zaka je?Ya ce masallaci.Yana fita na shiga gyaran dakin, ban taba yi masa gyaran daki ba sai yau.Ko yaushe da kansa yake yin gyaran dakinsa, nayi zaton zanga mujallun da na taba gani da, sai kuma ban gani ba, har na gama.Iya ta idar da sallah, ta sake lekowa ko ya tashi, na ce ya je yin sallah, shiru shiru ashe daga can ya tafi asibiti.Har kusan tara gashi bai fita da waya ba.Iya da kanta ta fita har masallaci layin mu, wanda suke sallah tana nemanshi.Duk wanda ta tambaya sai su ce mata tare dai suka idar da sallar isha'i.Da ta dawo sai na ce mata ko dai yatafi Asibintin da ya ambata ne?Ta ce zata iya yuwuwa ya tafin, tun da ya ambata.Nan dai muka zauna zaman jiran tsammani,mun kasa ko cin abinci.Sai sha dayan dare da yan mintuna dan acaba ya sauke shi, ni da iya har rige rigen fita muka yi, shi ne muka yi masa sannu ya amsa, iya ta ce, muna ta neman ka.Ya ce, natafi Asibiti ne shi yasa ciwon kai ya matsa min da yawa.Amma na sami allura da magunguna, kuma na kwanta canne kamar yanda likitan ya ce in dan huta, Alhamdulillahi kai yayi sauki.Ta ce to me zakaci yanzun?Ya ce, nasha tea a can kafin ayi min allura, muka shiga dakin shi ya zauna bakin gado.Iya ta fita nima na mike zan fita, sai ta ce ki dan tsaya ke saboda dare ko?Na koma na zauna ya kwanta tare da lumshe ido. Wayarshi tayi ringign, ya daga ya kalla sannan yaja tsaki, bari na kashe wayar nan ina so in dan huta.Har zai kashe sai ga ma bari yayi anfani da wanan damar ya nunawa sadiya anafa ribibin shi har da take masa yan ga.Don haka sai ya daga ni dai naji yana fadin yaya mati na me ya faru ne? Ban zaci jin muryarta ba, ashe ya saka hanfree.Sai kurum naji ta ce, lafiya lau sir, ban gankaba ne an ce ka tashi tun six, ya ce akwai wata matsala ne matina?Ta ce babu, naso in ganka kawai, kayi hakuri kasan ganinka kawai yana cire min damuwa dayawa, dayawa, amma sir sai kanayi kamar baka san haka ba.Yace matina yanzu bani da lafiya ne, ban dade da dawowa daga Asibiti ba in nafito da safe zamuyi maganar.Ta ce to Sir, nagode Allah ya kawo sauki.Raina yayi mugun baci, a gabana yake magana da wata arniya har take ce masa ganin shi yana sata sukunni da kwanciyar hankali?Yana ajiye wayar ya kalleni, na hada rai matuka na mike ya ce, ina zaki?Nace zanje in ci abinci ne, da kyar nake magana.Ya ce, au dama baki ci abinci ba?Kamar in kai masa duka don ta kaici.Mutumin da yayi nasa guri bai fada muna ba muka yi tsuru tsuru cikin damuwa.Shine zai ce dama ban ci abinci, ya mai maita tambayar nace um, ya ce kina ciwon baki ne?Nayi shiru yace in kin ci ki dawo, tunda Allah yasa yau naji da kunnena ba iya ce take hanaki zuwa wurina ba, karya kike yi mata.Ban tanka shi ba na wuce, a raina na ce ba zan dawo baCan kusan daya saura ina ta tubka da warwara na kasa bacci, ni nasan kaina ina da mugun kishi, sai ga sako ya shigo cikin wayata cewa ba zaki dawo bane?Na tura masa amsa da cewa eh, ka kira Matina.Yana ganin haka yayi ta dariya, sakonshi ya kai ke nan, don haka shima kurum sai ya kashe wayarsa ya kwnta.Da Asubahi iya taje dubashi ta sake shiga dan duba shi, sai ta samu jiki yayi sauki, har ma ya tafi masallaci.Don ya Aliyu ba rago bane namiji ne, ga juriya da izza, matsalarsa daya in yana ciwo kin magani,yayi tawa iya shagwaba sai kace karamin yaro, shi a dole auta.Nikam har gari yayi haske ban tashi daga makwanci na ba, tunda ina fashin Sallah ba wai ina bacci bane kurum takaici ne ya hanani tashi.Jiya ko baccin kirki banyi ba, saboda takaicin ya Aliyu.Iya ta shigo, ke ba zaki tashi kije ki gano mijinki ba?Ko da nafito kin xuwa nayi na debi ruwa na shiga wanka.Ina fitowa nayi zaman shafa mai duk ina jan lokaci ne don yayi abinda zaiyi ya kama gabanshi.Bana ma ko son ganinshi, lokacin da na shirya na nufi kicin a tsammanina ya fita.Ina tsakiyar kunna risho sai naga mutum a kofar kicin tsaye.Na rasa dalili in zan ga ya Aliyu sai gabana ya fadi.Na kalli fuskarshi, gaskiya har ya dan rame na ce ina yini?Ya ce ban yini ba, ni yanxu zafiya ce, sanan ba zan amsa ba tunda baki san hanyar daki na da bazakije ki gaida ni ba.A raina na ce ina matina?Ita batazo ta duba ka ba?Ya katse tunanin da cewa,ruwan zafi nake so zanyi wanka.Na kalleshi, ban taba ganin yayi wanka da ruwan zafi ba, nace to bari in dora yanzun, bai ce, kala ba ya koma daki.Da yayi zafi na sirka na kai masa ban daki, sai naje na ce masa ga ruwa can.Lokacin yana waya, da hannu yayi min alamar cewa in je yaji.Na tsargu da wa yake waya, don haka da nasaki labule sai na tsaya.Ji nayi yana cewa, kada ki damu, yanzu zanfito.Jikina yayi sauki, ai da tunaninki na kwana araina.Na girgiza kai tare da yin kwafa.Tabbas da matina yake yin waya, nayi kicin ina yin magana ni kadai, na ce to ita wanan shegiyar matinar me ke tsakaninsu?Nemanta yake yi ko me?Wata zuciyar ta katseni da cewa, ba kina gudunsa ba? Ai ga Matina zata maye gurbinki. Jikina ya sake mutuwa, na shiga tambayar kaina mafita.Wunin ranar sukuku nayi shi, na kasa tuna yanda zan bullowa abin.Duk jin su iya nake ko da can da suke cewa ba ruwanshi da mata, ni nasan da ruwanshi tunda ni naga mujallun batsa a dakin shi.Wanda baruwanshi da da mata me ya ruwanshi da irin kallon tsiraici?Dole ke nan inyi yakin rabashi da matan banza.Wata zuciyar tace haka ba zata yuwu ba, sai in zakiyi aikinki a matsayin matarsa, lallai saikin mika kanki a fili na ce ya na iya?Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Muna zaune a falo da iya washe gari da safe, yazo yiwa iya sallama zai fita, nima na bude baki da nufin ce masa sai ka dawo.Amma da yake matina ce a raina sai kurum naji na ce masa ka gaishe mun da matina.Har ya juya sai naga ya tsaya cak, sanan ya waiwayo fiskarsa dauke da murmushi ya furta cewa zataji in sha Allahu.Ya juya ya tafi, ni kam kamewa nayi tamkar gunki, a zuciyata tambayar kaina nake dama mutun na iya kuskuren magana ya furta abinda ke son zuciyarshi ya bar na saman leben shi?Kash!Ban so nayi zarar bunun nan ba, abin takaici harda murmushi na ambaci sunan masoyiyarshi. Kwana uku suka shude ina cikin damuwa,na san Iya ta lura banza kawai tayi mun,narasa abinda ke yi min dadi, ni ba fita nake ko ina ba, ba TV Garemu ba bare nayi kallo, ta lalace ni kuma ba ma abociyar radiyo ba.Wani kayan haushi ko littafi na dauka da sunan karantawa sai in kasa fahimtar komai.Na san kaina ina da shegen kishi na ban mamaki, ko saurayina naga suna yawan gaisawa da wata budurwa hankalina kan tashi, bare a ce miji na.Tabbas da Ya Aliyu ya skar min fuska da tuni na same shi munyi ta, amma ya Aliyu ya wuce haka.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Cikin sauri sauri ya Aliyu ya shiga shashin su, ya kalli sajan Ado ina barawon?Suka kaishi ya shiga.Ya tsura mutumin ido, aransshi ya ya ce kai wanan mutumin baiyi kama da barawo ba.Ya kalli Sajan, kawo abin zama, sai da ya zauna sanan ya kalli mutumin.Kaine barawon fili ko?Hawaye suka soma kwarara daga idanun tsohon, don bakin cikin sunan da aka kirashi.Ya ce cikin rawar murya, ranka ya dade ni ba barawo bane, ban taba sata ba.Aliyu ya juya kulkin dake hannunshi ya dan jefashi, sanan ya cafke.To baba ya akayi har ka mallaki filin da kake gini?Ya ce, ran ka ya dade filin nan na gajeshi ne a gurin mahaifiyata, don mahaifinta manomine.To ina zaune a gidan haya ga iyali, ina da mace daya ga yaya takwas.Yan samarin yara na a makota na roka sunakwana, ganin kullum nauyi na karuwa, sai nayake shawarar gina fili na ko da daki biyu ne rak.Na soma gini ni da yaya na, dan sana'ar mu ke nan ta leburanci da yaran.Mun soma ginin kawai sai ganin yan sanda nayi sun xo kamani, ban san abinda nayi ba.Aliyu ya ce, to baba naga takardar bayanin laifinka, naga cewa ana zarginka da laifin yingini a filin da ba naka ba, filin tsohon jami'in dan sanda ne.Tsoho ya ce, dana wlh wanan filin nawa ne, kowa ya sani a unguwar mu ina da takarduna ina da sheduna.Kuma ni da aka kawoni nan ba a tambayeni ankawoni nan aka jehoni ne kawai.Babu wanda yaji ta bakina.Aliyu ya ce ka tabbata kana da takardu da shedu?Tsoho ya ce ina dasu ranka ya dade.Aliyu yace zamu mikaka kotu kuma in sha Allah zan tsaya maka sai kayi nasara.Cikin izza ya nufi wajensu Sajan Ado, yace sajan, yace Sir, bayan ya kame.Aliyu yace waye ya kawo wanan mutumin?Sajan ya ce, barawon fili?Aliyu ya ce, eh shi.Sajan ya ce CP ne yasa a kamo shi.CP da kanshi?Ya tambaya cikin mamaki.Yace shi, amma AC ne ya tura.Kan Aliyu ya daure, ina takardar bayanan da kuka bani dazu?Sajan ya sake daukota, Aliyu ya kalla ya sake karantawa, wanan rubutun kofur bala ne ai, sajan ya ce, eh, Aliyu ya ce kira min shi.Ya juyya ya koma office din shi.Ya tsare kofur da idanun shi waddanda basadaukar raini, kainne ka rubuta wanan takardar ko?Ya kame, eh, nine Sir, ya juyya mishi baya, amma ai baka tambaye shi ba ka rubuta da yawun shi.Ko menene dalilinka?Kofur cikin daburcewa ya ce,Sir ai nima AC ne ya ce na rubuta haka, sabo da raini mutumin yake so ya kawo wa tsohon mataimakin IG.Aliyu ya daga hannu da nufin dakatar dashi, tsaya min kowa ya cuta sai a ari bakinsa a ci mai albasa?Ya ninke takardar ya zura cikin aljuhunsa, yace dauko wata kazo muje ka sake rubuta ainihin bayanin da yake daga bakinsa, mu masu kare Al'umma ne da rayukansu ba masu danne masu hakkin ba ne da kuma kashe su.Kofur dake biye dashi ya ce, sir, wanan tsohon mataimakin IG yana yawan kawo mana matsalolinshi a nan, kullum maganarshi bata wuce an cuceshi.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Aliyu ya ce dan ya taba zama jami'in dan sanda bazaiyi anfani da wanan damar ba, sanan yayi anfani da mu.Alkawari na daukarwa kaina ba zan bar zalunci ba, matsawar naganshi zanyi yaki dashi.Aliyu ya tsananta bincike kuma cikin kwanaki kadan yagano cutar tsoho wanan jami'in ke son yi, don hakka ya tattara dukkan bayanai ya turasu zuwa kotu.Gobe da safe ya tabbata in anje can tsohon zai sami hakkinsa, saboda bayanai da hujjojin da Aliyu ya hada.Yana tsaye a bakin titi zai hau a caba zuwa gida Inspector Kamal ya sameshi a gurin, ya ce ranka ya dade zuwa yanzu yakamata a ce ka mallaki abin hawa ko da mashin, amma in san samu ne a ce kana da mota.Aliyu yayi murmushi, kada kadamu, ko mai lokaci ne, ya ce in dauko maka na aiki mana ba sai ka sha mai ba?Aliyu ya ce, a a na aiki anyi shi ne dan aiki kawai.Ispector ya ce, kana birgeni Sir, komai kana barinsa a muhallinsa.Lokacin da aka raba mana mashina baka zoba.Aliyu ya ce, ko ina nan ba zan amsa ba, don bana son bashi.Ya karasa zancen tare da tare dan acaba.Wayyarshi ta dauki tsiwa, ya cirota cikin hanzari ya daga saboda ganin sunan AC, hakuri ya baiwa dan acaban, sanan ya komaciki kamar yanda AC ya bukata a cikin officeya same shi, kai kawo yake ransa a bace ya dubi Aliyu.Me yasa ba bada damar a kai barawon filin nan kotu?Aliyu ya ce, angama bincike ne sir, sanan doka ta hana a tsare mutum tsawan lokaci ba tare da an kaishi kotu ba.AC ya ce, na san dai na rigaka sa kaki ko?Bai jira amsa ba ya ci gaba da cewa, don haka kasan na rigaka sanin doka.Ya koma kujerarshi ya zauna.Wanene ya hada binciken? Kai kasan ma da wa yake rigimar?Kasan filin wayake son kwacewa?Aliyu ya ce, nine da kaina nayi binciken sanan nasan rigimarsu shi da tsohon IG ne, kuma CP ne ya sa a kawoshi.AC ya ce, gud, to zan sake mai maita maka, in an kawo mai laifi da umurnin CP dan Allah ba ruwanka da shi, in zaya shekara.Ran Aliyu ya baci, ya ce, Sir, amma ba akan haka mukayi rantsuwa ba.AC ya daga masa hannu ban ce maka inason tunatarwa ba, sai dai ina son kasani ka kusan kai CP bango, dan kana son shiga cikin lamarinsa.Sanan kayi hanzarin cire kanka daga cikin lamarin tsohon, ka barsa yayi nashi binciken.Shiru Aliyu yayi, amma ji yake tamkar ya kama da wuta don zuciya.AC ya ce, ka iya tafiya.Aliyu ya fice da kunan rai.Matina ta hangoshi cikin sauri ta bishi, yana tsayawa a bakin titi tana tsayawa, ta ce barka da warhaka yallabai.Ya furzar da wani huci mai zafi, sanan ya ce barka dai.Tace ina tuni yallabai ya runtse ido don yanason saita zafin da zuciyarshi ke yi.Baya so ta fahimci yana cikin damuwa, sanan ya budesu sun kada sunyi ja, sanan ya ce matina zanfiso mu zauna a matsayin abokai, na fada maki bani da sha'awar auran mata biyu.Ina yi maki adu'ar samun mijin da ya fini.Ta ce, samun kamarka ne yallabai sai an tona, kunyi karanci a cikin al'umma.Ba duka namiji mace kamata zata bashi kanta ya kauda kai, har yanxu ina tuna ranar, ranar da na fada maka ni da kai muyi soyayya koda bamuyi aure ba.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Na fada maka cewa wata gara basa da zan maka shi ne, zaka iya yin duk yadda kake sodani na mallaka maka kaina, amma sai kayi mun nasiha ka kuma nuna min cewa addininka ya yi hani da hakan.Na sami kaina da sonka tare da son addininka, sanan cikin aikinka kowa yasan kana kwatanta gaskiya da amana.Ina tsoron in auri wani cikin masu addininku ya sake ni, dan ku hausawa ance kuna da sakin aure amma kai nasan ba zakayi haka ba.Aliyu ya kasa kallonta dan ta daureshi da jijiyoyin jikinsa.Ya ce, Matina ki amshi addinina da zuciya daya, sanan kisa a ranki zaki sami mijin da ya fini, nima zan tayaki da adu'a.Ta gyara tsayuwa kada ka damu, ni zan ci gaba da zaman samun irinka, alfarma daya nake roko in zaiyuwu, in na kiraka ka daga wayata.Sanan in kazo nan muke rinka gaisawa.Ya ce dan mun hadu mun gaisa ba damuwa,abin da zaiyi dan wuya ki rinka kirana ina da mata, nasan bazata so hakan ba.Ta rausayar da kai gefe, cikin raunaniyar murya ta ce, na gode,ka fadiwa matarka cewa ta rikeka da kyau, dan tana cikin matan da sukayi sa'ar zuwa duniya.Murmushi yayi duk lokacin da kuka hadu saiki fada mata da kanki, na barki lfy.Yana kan mashin yana tunani ko me yasa yake samun irin wanan matsalar?Mata suyi ta sonshi suna binshi, amma shi bai damu da su ba.Matina yana kulata ne saboda musulantar da take sha'awar yi, ya san in yazama sanadiyya zai sami ladan hakan.Daga nan tunanin sa ya koma kan matsalarshi ta office, in dai da irinsu AC da PC anya kasar nan zata gyaru?Lallai kasarsa Nageria tana cikin wani hali, kullum burin nasama ya danne na kasa, sam ba a son gaskiya.In ka tsayawa halas dinka sai mutane su rinka yi maka kallon dan kauye.Ya girgiza kai sakamakon tuno tsohon nan da yayi, shi da gaskiyarshi da filin sa da komai ba a tausaya masa ba, kasancewarshi mai rauni ana neman a zalunce shi.Mai dama yana anfani da damarsa gurin cutar mai rauni, yasan in ba wani ikon Allah ba tsohon nan ya rasa filinsa kenan, in yasamu ya fita da ransa kenan.Duk lokacin da irin wanan ta faru sai yaji tamkar ya bar aikin dansanda, amma da ya tuna kudirinshi na kawo canji da gyara, sai ya hakura, da wanan sake saken ya isa gida. Niko tun lokacin da na furta masa cewa ka gaishe da matina cikin kuskure, ban sake yarda mun hadu dashi ba.Kusan kwana uku wasan buya muke yi har iya ta fahimci cewa na guje masa, amma bata nemi jin ba'asi ba, yi tayi ma kamar bata san me ni ke yi ba.Sam ban zaci dawowarshi a wanan lokacin ba, domin cikin kwanakin nan sai dare yake dawowa.Ni kadaice a gidan,Iya tun bayan la'asar sun tafi Asibitin dutse duba wata makociyarmu da bata da lafiya.Sun tafine da ma da sauran makotanmu.Na wanke hijabaina da na Iya ina shanyawa,daga ni sai best, zanina kuma iyarshi kugu.Ina shanya ina mitar cewa iya sunje sunyi zamansu, nasansu da son tafiyar kafa, yanzu haka ma da kafa suka tako.Banji sallamarshi ba sai dai naji ya ce ina suka tafi?Na waywaya na kalle shi, da gudu na shige daki dan kirji na duk a waje yake.Dan murmushi yayi sanan ya shige dakinsa.Ina zaune bakin gado ina kallon jikina sai ganin shi nayi tsaye a gaba na har uwar daki.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Naja hijabina, ya ce ina tambayar iya kina gudu? Ya hade fuska tamkar bai taba dariya ba.Tsoro ya darsu a raina, cikin in ina na ce,Asibiti suka tafi.Ya ce, dan kada ki bani amsa shine kika kwasa da gudu?Nayi shiru, ya ce kin min banza.Nace yi hakuri dama zan dauko dan kwali nein daura.Ya ce, ok, ni zaki boye min gashin kanki?To ajiye hijabin in ga gashin tunda halas dina ne.Gabana ya soma faduwa, na zame Hijabina ya ce ashe ma ba wani gashi kike dashi ba, cire hijabin daga jikinki in gani.Na kalleshi da sauri ya kauda fuska yana yatsina baki, sai kace zai ga abin kyama.Na cire hijabin na ajiye cikin sauri kuma na sa hannuna na rufe kirjina.Ya ce cire hannunki.Na cire tare da runtse idanuna.Sai kurum naji yasa hannu ya turani baya, na fadi rigingine na bude idanuna da sauri ina tsoro, yasa hannu ya janyo best din sai ta yage, kirjina ya bayyana.Tsayawa yayi yana kare mun kallo, ya tabe baki, dama best din taki rubabiya ce? Sallamar iya ta tsakar gida ce ta sani tashi zumbur, na dauki hijabi saka.Cikin tsoro mai tsanani na ce ga iya nan.Shi kam ko a jikinshi.Ya tabe baki tare da daga gira sai me?A zato na bai fahimci nufina ba, don haka sai nayi nufin fahimtar da shi katafi da sauri kada ta ganka a nan tayi zaton ko wani abu ne.Sai naga kurum ya zauna bakin gado, na zaro ido dai dai lokacin da ta shigo falo tana cewa Sadiya ina kika shige ne?Kin ganmu sai ynzu?Da sauri na fito cikin in ina na ce gani nan, kun...kun dawo?Eh, lafiya na ganki a hargitse?Ta ce ba ko mai.Na yi waje.Ita kuma ta nufi uwar daki, gabana yana faduwa.Tana shiga ta ganshi zaune bakin gado yanawaya, ta ce au, ka dawo?Ya ce, eh, na dawo tun dazu, waye babu lafiya kika tafi asibiti?Tace matar mai besfa ce a asibiti mukaje duba ta.Ya ce, Allah ya bata lafiya.Ya mike bari in karasa masallaci.Sai tin kunne na naji maganar shi, a hankali yace sarkin tsoro. Sam ya kasa bacci abin da ya kalla daga yarinyar kurum yake tunanowa, juyi yayi har gari ya waye sai ya dauki waya da nufin kiranta dan yana togon cewa ita din halas dinsa ce.Sai kuma ya tuna cewa yarinyar ba zatazoba, sanan ga iya, kai!Shi fa ba zai iya jira sai sun tare ba.Da safe naje kai masa abin kari, lokacin ya gama shirin fita kawai zaiyi, ya amshi kofin daga hannuna ya kurba.Sanan ya kalleni kin kawo a latti, kin san da wuri nake fita. Na ce, a shanarmu ce ta jike shi yasa, sai da masu shago suka bude iya ta fita ta siyo.Ya ce my choice.Na kalleshi zan sunkuyar da kai, ya ce a a kada ki sunkuyar da kai, kalli cikin idona, bana son wanan sunkuyar taki tana cutar dani.Na kalli idon shi, ya ce yau ina bukatarki, na gaji ina da mata kullum nine cikin azumi.Nayi kwalkwal zan soma kuka, ya tsareni da idonshi, ya kuma hanani sukuyar da kai.Cikin raunaniyar murya na ce, kasan dai iya ba zata bari ba.Ya ce daina karya da iya, na gano ma ba ita take hana ki ba tun da ranar nan in an ji ta ce ki zauna da ni, lokacin bani da lafiya.Ya mika min kofin tare da cewa, zan fada mata, jeki abinki.Na tafi ina mamakin shi, musanman da naji ya ce zai fadawa iya zanso inji ko me zai ce mata na kasa karyawa don zullumi, ina ta juya biredin dake gaba na, kamshin turarenshi ne yasa gabana faduwa. Ya ce, iya na tafi.Ta ce to auta na, Allah ya tsare.Ya ce, amin.Yana wucewa na sauke a jiyar zuciya.Cikin jin dadi na gutsire biredi, na dago kofin shayi na kurba sai naji takun sawunsa ya dawo, take naji shayin ya sane.Ya ce au, na manta iya.Ta ce, na'am iya za a zo a dauketa taje ta gaida matar oga, ko bani ba wani zaizo daukarta. Na kalli iya, shi dama vai jira amsaba ya tafi, ganin kallon da take min sai na tsargu, na taihashashen baki muka hada.Don haka na ce, iya ke ce masa ba zanje ba,Allah ni bana son xuwa.Ta harareni, bakya son zuwa ne kika bari ya tafi baki ce ba zaki ba, sai nice zance karki je? Bayan kun kitsa abinku?Ta taba baki haba yayan nan, na fa rigaku zuwa duniyar har da kuke son maidani wata sakara. Na ce iyya Allah ba haka bane, ba mu kitsa komai ba, ni bansan ko mai akai ba, ban san da wata magana ba sai da yayi yanxun. Ta ce kwaji da shi, nifa bance kada kije ba, ke da mijinki zan hana ki?Ta fada cikin gatse sanan tayi tsakar gida tabarni zaune cikin damuwa.Da naga har la'asar babu wanda yazo nemana, kuma shi bai dawo ba, sai naji dadi kuma na dan saki jikina. Cikin haka wayata ta fara ruri, na daga a raina ina adu'ar Allah yasa ya ce an fasa.Sai naji ya ce ki shirya Usman zaizo ku taho.Sai da na daga murya yanda iya zata jiyo, sanan na ce, yaya, Allah iya ta ce bazanje ba. Iya daga inda take ta ce, a a ba ruwa na ni Sa'adatu, ban hanaki ba ni ko baku hada baki ba ni yar bada shawara ce.Yace to najiyo abinda iya ta fada, don haka na baki minti talatin ki shirya.Sai ya kashe wayarshi.Na ce na bani yanxu yaya zanyi?Don Allah ku bani shawara, inbi mijina ko in nunawa iya harshashenta ba haka bane? Taku Halima K/Mashi kemuku godiya. Awanna gabarma Kanwarku Sadiya tana neman shawarar ku, Saimun hadu a cikin littafi na biyu.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Darajar Yayana2-01 Posted by ANaM Dorayi on 09:52 AM, 20-Mar-16 Under: DARAJAR 'YA'YANA ___________________NA ___________HALIMA K/MASHI Assalamu'alaikum, barkanmu da warhaka fatan kuna lafiya,nasan kunjini shiru a cikin wannan littafin,lallai kam kusan incemuku babu wani kwakwkwaran dalili face rashin kulawa daga gareku,saidai dayake ni nayi niyya dole incigaba,da wannan nake bawa masu yawan bibiyata hakuri,In Allah ya yarda da sannu zamu kai har karshen littafin, Na tashi na shiga wanka ina yan kun kunai,ko kallona Iya bata yi ba, sosai nayi gayu atanfa fara da sirkin purple ne. Haka takalmana da mayafina duk purple ne, na fesa turaruka sosai.Iya ta kalleni ta ce, da ma na san kun hada bakine shi ne za a gwada min bariki, in dai namijine kuje Allah ya taimaka. Ni dai nayi sororo raina babu dadi, sannan bani da mifita.Har cikin gida Usman ya shigo suka gaisa da Iya, sanan yace zamuje ne ta gaida Ogansu Aliyu.Iya ta ce, menene na shirya karya Usman ku da matarku.Nina haifeku fa har da kukega zaku yi mun wayo, a

Chapter 6 of 25