Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ce, wai me ya burgekine a dan sanda duk jikinki ya hau bari? Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Na ce, to iya gaskiya ya Aliyu ba irin mutumin da za a ce ba a so bane .Ta ce, ni dai na ce a a ban yarda ba.Na mike cikin fushi na fita tsakar gida, da kallo iya ta bini, matuka ta ji mamaki musanman ta sanni bani da rawar kai.Ni kuma kicin na shiga na zauna banyi aune ba sai kurum naga hawaye suna zuba a ido na, ni kaina har naji mamakin kaina.To da bai ce yana sona ba fa?Ranar haka na yini har dare, kusan mutum uku suka aiko kirana naki fita, iya duk tana lura dani tana kallona ranar bai dawo gida ba sai sha biyun dare, sanan tunda a subahi ya fita.Yau sam na kasa sukuni, iya sai kallona takeyi tana salla, can bayan ta idar ta ce sadiya!Nayi shiru, ta ce, nasan kina jina ta shi kawaiki tashi, na tashi zaune ta ce, sadiya ina ganin baki gane nufina ba game da zancenkike da gadanga shi yasa har kike fushi dani.Gadanga bahogon mutum ne, ni na haifeshi na sanshi tun yana dan karamin shi, gadanga bashi da dadin lamari, amma in kinji Allah ya baki sa'a.Sai dai ina so ki sani in da wanda zaiyi farin cikin aurenki da gadanga to ya biyo baya na,sai dai duk da haka ba zan kasa fada maki gaskiya ba.Shawarar da zan baki kuma ki rage rawar kai in ya fahimci kina doki kimarki ta zube.A zaton iya zan hakura amma sai taji na ce, in sha Allahu ba zan sami matsala ba.Ta tsura mini ido haka kika ce? Nayi shiru ta ce shi kenan, to da sharadi ba zuwa kawo kara.Da sauri na ce, to,da kallo tayi ta bina ni dai na tashi na koma makwancina ina murna.Na zaci da safe zata neme shi ne ta fada mashi ayi sai kurum ta share, ko da dai ya fita da wuri, wasa wasa sam taki zancen inaji lokaci da yawa da ya dauko zancen zata ce don Allah ya rabu da ita.Sai dai abinda ke bani mamaki, kullum yanda yaya Aliyu bai can za min yanda yakemin ba , amma nakanyi uziri cewa kila sai iya ta amince sanan za mu soma yin tadi.Cikin haka ne har aka dauki tsawon lokaci muka shiga shirin zana jarabawa (SSCE) duk na kori samari na babu wani mai zuwa tunda na fada musu na tsaida miji.Shikam ya Aliyu bai san na sani ba, kullum ya zo gurin iya sai yayi mata nacin shi fa yana nan yana jira ita kuma takan ce mishi kar ya dame ta, ba ya ce ya fi son yar jami'a ba?Ya je ya nema.Ni kuma in ya tafi wani sa'in in ce iya don Allah ba kince kin hakura ba, tunda na yarda?Sai ta ce min sakarya, dubi fa ko kallo baki isheshi ba, amma duk kin tsamgwami kanki don fitina, ni dan kare mutuncinki nake kin abin nan. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Usman abokinsa yaji shiru batun maganar Aliyu da sadiya, sai ya zo gurinshi musanman don zancen , dama ya kirashi a waya yaji cewa yana nan.Bayan sun gaisa usman ya ce, aboki wai haryanxu ban sake jin batunka da yarinyar nan sadiya ba, in mun hadu baka yimin zancen ba, ni kuma ban tambaye ka ba.Aliyu ya gyara zama yayi sanan ya lumshe ido don haushi ya ce, kabari kawai abokina, haushin maganar nake ji, shiyasa ban taba yi maka zance ba.Ya miko hannu ya dafa gyiwar usman abokina ban taba samun abinda ya bani matsala ba kamar maganar yarinyar, ni abin haushi duk lokacin da nayi kudirin hakura dazancen sai na kasa.Kullum adu'a ta Allah ya yaye min ita daga raina, amma abin ya faskara.Ko son yarinyar ne ya kamani? Usman yayi murmushi lallai sonta kake yi, Allah yasa ita ma ta soka hakan.Aliyu yace ina ruwana da ita?Iyace kurum damuwata, in da ta amince shi kenan, amma baiwar Allah nan wai zan cuci yarinyar ita ba zata bani yarinya karama ba.Ranar harda cewa na tsufa.Usman yace zanje in sameta aboki, kada kadamu.Aliyu ya ce, ko kaje matarnan ba zata yarda ba, na dai fada mata ni na hakura da yin auren. .Usman yayi ta dariya tare da zolayar Aliyu da cewa, aboki ka dai shiga da yawa, to da ka ajiye duk wani girman kai ka dinga kiran yarinya hira in taga haka zata fi yarda cewa da gaske kake yi.Aliyu ya ce ka yarda ni ba zan taba iya kiran yarinyar ba, ko ba Sadiya ba, kuma sanin kanka ne ban taba ba, so bansan ta ina zan fara ba.Ba ta ita fa nake ba, in iya ta yarda tayi hakuri ta aureni dan da cewa auren sai kuma ya ja tsaki kada ma ta hakura.Tama ji dadin zancen ta samu miji irina, Usman ya ce, yabon kai?Aliyu yayi dariya aboki ka fadi gaskiya, ni da ita wa yafi kyau?Bai jira amsa ba ya ci gaba na farko dai kaga ita fari ne kurum ya ceceta..... Usman ya katsishi au, wai dama haryanzu akwai mummuna?Ni dai yanzu na daina ganin mummunaai tunda naga alamun kai ya waye, ba a zama da kazanta, Aliyu ya ce, haka ne, amma wani wan wani ne a kyau.Usman ya ce, duk da ka fi ta kyau dai ita zuciyarka ta zaba, zanyi maka kokari, zanje in samu iya.Aliyu yace tunda ka dage jeka din, duk yanda kukayi zamuji. Kamar yanda Usman ya alkawarta yazo ya samu iya wajen la'asar ina yi mana tuwo, itakuma tana zaune a kofar dakinta.Na gaida shi sannan na dauko masa tabarma ya zauna, na kawo masa ruwa sanan naje na ci gaba da aiki na.Daga inda nike ina jiyosu suka gaisa sanan ya fara yi mata zancen da ya kawoshi.Iya dama akan batun abokina ne da yar uwarsa sadiya, iya dukkan su naki ne, a ganina wanan abin farinciki ne.Iya ta tsuke fuska,Usman ina ganin kimarka, zaifi kyau ka bar zancen nan bana jin cewa zan amince.Usman yayi shiru yana tunanin yanda zai bullo mata.Can ya ce, to shi kenan, amma na so ki amince domin yana cikin wani hali na son yarinyar nan, nasan halinshi kin san halinshi,baya daga cikin mutane ma su magana biyu.Yayi mun rantsuwar ba zai taba aure ba in ba Sadiya ba, duk duniya ita yake so.Zaman shi haka nasan yana damunki.Ta ce in duk duniya Sadiya yake so ita Sadiyar ya tambayeta ta ce tana sonshi? Nifa ba zanyiwa yata auren dole ba, don in faranta masa.Daga inda nake a kicin na da ga hannu ko nace ya tsa tamkar mai bada amsa a cikin ajinmakaranta, sanan na kwalawa iya kira!!Ta kalleni tare da yi mun da kuwa, shi dai baisan dalilin dakuwar ba, tunda ya bani baya, ita kila ya zaci laifin nayi mata. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Usman ya fahimci nufin iya, shi yasa ya ce mata Aliyu ya dinga kiran yarinyar suna fira.Ya dubi iya, to in sha Allahu za mu tuntubi yarinyar, idan bata amince ba shike nan.Yana fita ya dauko waya ya kira Aliyu, bugu uku ya dauka. Usman ya ce, Aboki da farko fara bani goron albishir.Cikin sauri Aliyu ya ce kada dai ka ce mun tasaurareka? Usman ya ce, in sha Allahu munyi nasara Aliyu ya ce shi kenan sai na xo aboki, gidanka zan sauka kaitsaye daga office yanxu ina kan wani aiki.Suna cin abinci a falonsu Usman yana koro mashi bayani duk yanda sukayi a karshe yace yanzu kaga tana nufin ta yarda sai dai amma tana so ka kira yarinyar ka nemi amincewar ta.Aliyu ya tsirawa Usman ido, sanan ya ce, ai wanan shine mai wahalar, gaskiya a boki ba zan iya kiranta ba.Usman ya ce, tsoronta kake jine?Raini ne bana so, yanxu dai kai kaje ka sameta kuyi magana.Usman ya ce, nima ke nan zan yi maka yakin neman sonta?Aliyu ya ce, duk yanda ka ce amma ni in na kira tafa ba ra'ayinta zanjira ba, umurni xan bata.Usman ya ce, shi kenan ka bari xanje.Bayan sallar isha'i muna zaune ni da iya muna cin abinci tare kamar yanda muka saba, yaya usman yayi sallama shi da matarshi Anty Abida da yaran shi guda biyu,tsam na mike daga cin tuwon ina yi musu sannu da zuwa, suka zauna na kawo musu abinci da ruwa, sukace yanxu suka tashi daga kan cin abinci.Na koma tsakar gida bayan na dauki yarinya wato Ummulkhairi, yarinyar tana da wayo yar mai kyau taji kitso, na ce Ummulkhairi kina makaranta? ta ce eh mana, kuma Abban mu yake kaini har ma da Abulkhairi, nace, iye, to koya mun karatu.Ta ce, na islamiya ko na boko?Na ce, a a islamiya dai.Ta gyara zamanta a cinyata ta ce, in miki sunayen Allah kyawawa?Na ce, eh,ta fara kenan babanta ya fito, ya kallemu karatu kuke yi? Na ce, eh, tana koya mun ne.Yayi dan murmushi ya ce ummu jeki wajen umman ki, ki ce mata ta jira ni ina zuwa.Ta na shiga daki ya ce, kanwata zo mana.Na mike na bishi zuwa kofar gida, nasake gaisheshi nayi , bayan mun tsaya ya ce,Sadiya nasan ba zakiji mamakin kiran da nayi maki ba ko?Na ce ba wani mamaki, kila zaka aikeni ne. Yyace bahakabane na kiraki ne dan in sanardake wani abun alkairi, ko da yake ban san yanda zaki amshi abun ba.Na gane zan cen ya Aliyu, ya duba duk cikin matan da ke garin nan yaga babu wadda tayi masa sai ke, tamkar bai san zancen ba na furta da karfi so!!!Usman ya ce ba wani abun mamaki bane, dami ne kika tsinta a kala.A raina na ce lallai ma yaya usman din nan, to bari in latsa shi.Na ce, ya Usman ka ce masa yayi hakuri kawai dan na riga na tsaida mijin aure wanda nike so.Ya Usman ya ce, kin kai shi gida ne?Na ce, gobe ne iyayan sa zasu shigo gidan mu.Usman ya ce, in har zan baki shawara ki yarda zan so ki dakatar da su domin kowa zaki aura na tabbata bai kai Aliyu ba, samunsa sai an tona, ko na ce irinsa.In kika sameshi a matsayin miji tabbas zakiyi alfahari samun muji kamarshi, mata da yawa suna sonsa, kila sun fahimci nagartarsa, amma ba matsi in baki sonshi zan koma in fada masa cewa baki sonshi da aure.Na kalleshi bance bana sonshi ba, saboda duk abinda iya ta haifa dole ne in soshi, kai ko wani ne can ba danta ba in dai ya mutunta ta to zan soshi bare dan cikinta, na riga na zabi wani ne.Usman yayi shiru, ya zaci da yayi mun magana zan amsa da murna, can ya ce, to yanxu mai zanje in ce masa? Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Na ce, ka fada masa zanyi tunani zuwa gobe. Ya ce, shi kenan, zan kiraki amma kiyi shawara da kawarki wadda ta sanshi, na san zata fada maki qualitie din Aliyu. Na ce, ba damuwa. Ya ce, shi kenan gobe zanzo naji. In kin shiga kicewa Abida su fito mu tafi daman na sallami iya. Na ce, to. Bayan tafiyar su iya tashiga yi mun fada wai ai gashi nan saboda bai daukeni da muhimmanci ba abokinsa ya turo min, ta san jikina yana bari na ce na yarda. Na vata fuska tamkar zan saki kuka na ce, ni fa iya banyi fa rawar jiki ba, ce masa kawai nayi zanyi shawara zuwa gobe. Ta ce, ato in kin kimanta kanki yaga darajarki in kuma kinki ni dai na fada maki babu zuwa a kawo mun kara. A waya Aliyu yaji duk yanda mukayi, mamaki ya dinga yi wai wanan yarinyar ce zata ce sai tayi shawara, dawa zata yi? Kuma ita ce wa? Usman ya ce ita ce mace. Aliyu ya ce, shi yasa kaga ba zan iya kai kaina ba ga wata ya in ce ina son ta ba, bare tayi mun yauki, nidan oya-oya ne. Usman ya ce ka barni da itakawai na san jan ajine zamuyi nasara cikin jin haushi Aliyu ya ce, in taki ka kyaleta kawai, yarinya sai kace wata ta gold sai ga ruwa nake yi a kanta. Ya ja tsaki nan ya kashe wayar ba tare da ya sake jin mai Usman zai ce ba. Kwana Aliyu yayi da zullumin halin da zai tsinci kanshi, in yarinya taki amincewa da shi. Da safe ina shara ya fito daga dakinsa ban san me ke sani faduwar gaba a duk lokacin da na ganshi ba.Na gaida shi ya amsa cikin isa, kuma a ta kaice kamar yanda ya saba. Sanan bai ko kalleni ba sai dai nice na bishi da kallo. Namiji ne sosai ko tafiyarshi ta shaida haka, daga ganinshi baka ga rago ba, dama abin da ya dace dashi kenan jami'in dan sanda. Iya daga daki ashe tana kallona ta ce, in kin gama kallonshi sai ki ci gaba da sharar ko? Cikin kunya da shauki na ci gaba da sharata. Da rana naje gidansu Aisha kawata nake bata labari duk yanda muke ciki, tace, tabbas! Sadiya idan zan fada maki gaskiya ki amince kawai, kada ma ki tsaya wani jan aji,sau nawa nake fada maki Aliyunku unique ne?Allah in kika yi sake kin tsaya yauki kya zo kina na dama, kin san shi da zuciya ya ce yafasa.Kash!Ina ma nice ya ce yana so?Jin haka yasa na kagu dare yayi.Har na debe tsammanin xuwansa dan tara ta kusa, duk na tsure kar dai ya Aliyu ya hakura da gaske.Can sai na tsinkayi muryar wani yaro yana sallama ni ina cikin daki a kwance kan kujera.Iya ce ta amsa salamar don tana tsakar gidan, ya ce an ce sadiya ta zo inji wani a waje.Ka fin ya rufe baki na mike, zaraf na suri mayafi na fita.Iya ta ce, kai jama'a!Kai jama'a!!Ni wanan yarinya ko dai zaki kai kanki ne?Na ce ban fa san ko wane ne ba, ma ai iya.Cikin gatse iya ta ce, ina zaki sani, shiyasa kike ta sintiri tun daxu kin kosa ko wanene maya zo?Na ce, sai na dawo.Ta ce, kada ma ki dawo ki kwana can.Usman yana tseye a gurin da muka tsaya jiya, na sameshi da sallama, muka gaisa ya ce to kanwata nazo jin me kika yanke?Na danyi shiru kamar mai nazari, ya ce, kada ki damu in har baki sonshi ya ce babu komai.Na ce, ai ba zan iya cewa bana sonshi ba ko dan iya, don haka ka ce masa na amince.Usman ya ce, Alhamdulillah, sai kin ji mu.Ranar nayi farinciki har nafila nayi don godiya ga Allah, iya ta ce yau kuma ibadar ce ta motsa har da nafilar dare?Ni dai ban tanka mata ba, ta ci gaba, Allah ya sa a dore, ina ta samun gadanga ce akayina san daga yau shi kenan. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Washe gari yaje ya samu yaya zakari da yaya Sulaiman yayi musu bayani, su kuma suka sami dan uwan mahaifinsu dake nan layin kasuwa, a nan unguwar mu'azu.Nan dai suka sa ranar zuwa zariya gurin mahaifina don jin zance, Aliyu da zasu tafi ya bada dubu hamsin ya ce har sadaki duk yanda ta kaya shi kenan.Mahaifina yayi murna har yana cewa wannan abu ai da ba sai anxo ba, ita iya Sadiya tata ce, Aliyu ma nata ne, da ba shi kenan ba sai dai muzo a yan gayyata.Kawu ya ce, a a kun wuce haka, kuma dole abaku hakkinku.Baba yayi ta godiya kafin daga bisani ya ce bari ya kira dan uwansa.Sun yanke sadaki dubu talatin sanan aka basu na gaisuwa goma, sai dai suna dawowa suka fadawa iya duk yanda akayi.Iya ta ce sam yarta tafi talatin, su kawo goman nan hamsin ne sadakin yarta, sanan gadanga ya ciko goma kudin gaisuwa.Da kyar suka shawo kanta ta amshi goman, sadaki arba'in kenan.Aliyu dai yana zaune yana jin su yana kallonsu amma bai ce ko mai ba.Suka ce an tsaida rana watan tara sha biyar da shi, lokacin kuma ana watan shida.Aliyu ya ce yaya Sulaiman lokacin nan bai yi tsawo ba kuwa?Anawa ra'ayin nafi son wata biyu, iya ta ce, har ka gama shiri ne zaka ce wata uku yayi maka kadan?Aliyu ya ce, wane shiri ne mai zafi?Ba lefe bane ko meye ne kuke cewa ya rage ba?Ta ce, kana da gurin zama kenan ko nan zaka gyara mu zauna?Ya ce, a haba dai, zan nemi gurin zama duk a cikin wanan lokacin.Ta kalli Sulaiman ni fa in nayi auran nan zataci gaba da karatunta ku shaida wanan, in ya ce a a za a jimu.Aliyu ya ce, na sani iya, nima ina son ta ci gaba da karatun.Ta ce, to batun aure a barshi wata ukun, sai kaga lokacin ya zama ba ka kammala da wani abun ba har kake raina lokacin.Ya ce Allah ya kaimu.Ina zaune cikin ajinmu bayan mun gama zana paper din mu ta karshe, ina kallon yanda yaran ajinmu suke ta jin dadi da murna tun da muka baro hall din.Ta gumi na zabga ina mamakin irin halin ya Aliyu, yau kusan sati hudu da sa muna rana amma ko sau daya bai taba kirana ba, haka nan kuma ko cikin gida ya shigo ban isheshi kallo ba.Nima fa yanxu na soma sarewa, anya kuwa mutumin nan yana sona? Kullum iya sai tayi min gori, yau kam zanje in nemi ya Usman.Bayan nan na cewa Anty Abida in yadawo tace ya zo, ina son magana da shi, ta ce to zata fada masa na ce ina su Ummulkhairi?Ta ce suna makaranta.Da daddare kuwa sai gashi ana sallama dani, na mike har ina tum tube.Iya ta ce, sai karaftu kike sai kace a dakin Ajantina, na san dai ba wanda kike son gani bane, dan nasan shi ya fi karfin ya kiraki. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Nace, iya to ai ina so ne na ga ko wanene.Ta ce, oho ke dai kika sani.Ina fita yaya Usman ne kamar yanda nayi tsamani bayan mun gaisa ya ce, Abida ta ce kin zo nema na.Na ce, eh.Na sunkuyar da kaina ina wasa da yatsuna, na ce dama nazo ne a kan maganar mu ne da ya Aliyu, in abin ba zai yuwu ba gara mu hakura tun yanzu.Ya gyara tsayuwa wani abu ne ya faru?Na ce to ya Usman a haka ne za mu fahimci juna in san abinda baya so yasan abinda bana so?Na ci ga ba, bai taba kirana da sunan muyi zance dashi ba, ko gida ya shigo ban ko isheshi kallo ba, shi bashi da wani lokaci ne sai na aikin shi?Usman yace ba wai zan goyi bayan shi bane amma ninasan kina ranshi,ki fahimce shi, shi mutum ne mai kishin kasarsa da aikin sa, shi yasa baya samun lokacin kansa.Amma da zarar kin zama a gidansa na san dole ya baki dukan lokacinki.Nayi shiru kamar maganar ta shigeni, ammada na tuna ko kallo na bayayi na ce, yaya Usman ka san Allah ba dan aikin shi bane, ko kallo fa ban isheshi ba.Usman ya ce, to bari zanyi mashi magana.Na ce, don Allah kada ka ce nayi maka magana, kada yayi tsammanin na damu da shi ne.Usman ya ce, zanyi masa maga na da ma ai, ba zan ce kece kika sani ba.Kusan sha dayan dare Usman ya daga wayar Aliyu tare da yin sallama, bayan sun gaisa Usman ya ce aboki dazun ina ta kira baka daga ba.Aliyu ya ce, bari kawai aboki, lokacin ina tsakiyar wani case ne abin nan yana matukar daga hankalina tare da bani mamaki.Ka san wani mutum dan kimanin shekara arba'in aka kama yayi wa yar shekara hudu fyade.Usman ya zabga salati tare da cewa, wai aboki wanan wace irin masifa ce?Ko dai wani tsafi ne?Aliyu ya ce, wa ya sani?Wannan fyaden na kananan yara yayi yawa.Kullum sai mun sami wanan case din wlh yanda abin nan ke mun zafi a raina zan iya kashe irin wadannan mutanen, don mugaye ne.Idan mata ne su je mana ga karuwai nan,Usman ya ce, to Allah ya shirye su, ya tsare mana daukacin musulmi.Aliyu ya ce, amin aboki to kaji halin da nake ciki, lokacin da ka kirani lafiya lau dai ko?Lafiya lau dama zance ne ya kamata mu shirya muje muyi hira da yarinyar nan ko?Aliyu ya ce, wace yarinya ke nan?Usman ya ce, sai karinka yi kamar baka san da zancen ba bayan nasan tana ranka.Aliyu ya ce, tsakani da Allah sai ka tuna min.Usman ya ce, ok, tunda yanxu iya ta yarda dole ka manta.Aliyu ya ce subuhanalla? Dama wai Sadiya kake magana?To wacce hira kuma zamuyi tun da na rigaya an gama magana, sai jiran lokaci.Usman ya ce, ai duk da haka za aje ayi hira ta san abinda baka so don a samu zaman lafiya.Aliyu yayi yar dariya.To ni ba haka tsarina ya ke ba, ina zaton in har zanje gurin budurwa zan jene don ina tallata kaina in in samu shiga,tonina riga na samu shiga babu dalilin da zan matsawa kaina.Usman ya ja tsaki kai dai bahago ne wlh, to sai ka sai mata waya ko ta waya kunyi magana.Aliyu ya ce, to yan zu dai kaine sarkin yakinta ko?Suka sa dariya.Usman ya ce, da gaske nikeyi, akwai wata waya da ake saidawa mai kyau nan kusa daoffice din mu (MTN OFFICE) ya ke aiki.Aliyu ya ce, ka suyo mata in kazo sai na baka kudin, sanan kai zaka bata don har karshen satin nan ban san lokacin dawowata, kafin ita ta tashi na fita.Usman ya ce shi kenan.Washegari da daddare ya usman yazo ya kawo mun waya wai iji yaya Aliyu, inyi hakuriza mu rinka waya aikine yayi masa yawa.Bani da zabi dole na hakura tunda ga waya har da layin (MTN) ko da na nuwa wa iya baki ta tabe sanan ta ce Allah ya sa alheri.Tun da na karbi wayar ko flashing ba a taba yi mun ba, ga dai lambarshi a ciki ya usman ya samun duk da cewa har da kudi a layin nawa nima cewa nayi ba zan kira shi ba.Sai dai in ta kiran kawaye da yan uwa wadanda nake da number su. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Wata rana da dadare naji Iya tana yi masa fada cewa yana zaton haka za ayi auren ba lefe, biki saura wata daya da kwanaki, amma ba a ga yana motsi ba.Ya ce, abin ne ya shige masa, amma gobe zai je ya sami matar ya sulaiman.Ita da matar Usman Anty Abida sukai ta zaryar zuwa kasuwa, saura sati biyu lefe ya kammala da dinki da komai.Iya ta ce ya Aliyu ya bada kudin mota a kaisu zariya, ni kuma nan kawaye na sun matsa da batun anko, lokaci yana tafiya gashi ba zan iya yi mashi magana ba.Aisha ta ce, kiyi wa iya magana.Na ce, iya kwana biyu bata sana'a , bata da kudin anko?Tab! Ba zai yuwu ba.Wayata na dauka inyi kamar zan kira shi in fasa, Aisha ta amsa na ce kada ki kira shi dan bai taba kira na ba, ba wani kiranshi da nima zanyi Allah aisha ni auren nan tuni ya fitan min daga rai.Ace kai kafi karfin kazo sai dai abokinka?Aisha ta ce, Allah sai na rubuta masa tex.Ina kallonta ta rubuta masa.SALAM.INA FATAN KANA LAFIYA?KAYI HAKURI KILA YANXU KANA CIKIN AIKI NA TSAIDA KA, DA MA NAYI MAKA WANAN MESSAGE DIN NE DON NA TAMBAYEKA A KAN MAGANAR ANKO, DONKAWAYENA SUN DAMU SABODA LOKACI YANA KAREWA.NA GODE, KA HUTA LAFIYA.Tana gama rubutawa ta tura masa, maji amsa-maji amsa shiru, nace kin gani ko?Ke ayi biki haka bani kara masa batun anko.Aisha ta ce, niko yanda yake nashi salon birge ni yake, na ce, au!Wulakancin da yake min din ne yake burgeki?Tayi dariya, ai ba wulakanci bane rayuwar sa ce haka. Lokacin yana office din commissiner ya je a kan nemansa da yayi tsam ya kame kamar yanda yake al'adar yan sanda, sanan ya soma magana cikin natsuwa ranka ya dade an ce kana nema na.Commissioner ya dube shi cikin natsuwa sanan ya ce da ma na kira ka ne a kan maganar barawon shanu din nan da aka ce kaki yarda a bada belinshi.Aliyu ya sunkuyar da kai don girmamawa, yace ranka ya dade haka ne, naki bada belinshine saboda bincike ya nuna shi din ba karamin mai laifi bane.Daji suke shiga da motoci suna kora shanayen fulani suna kwashewa su kai kudu su saida, wanan kamawar ita ce ta goma sha uku amma ba a taba mikashi kotu ba, azzalumine na gaske,Commisioner yayi dan murmushi sannan yazo ya dafa kafadar Aliyu ya bubbuga alamun jinjina, san nan ya ce, Dan Sanda mai kishi, lallai kasan aikin ka da ka tsaya binciko wannan files din, ka tattarosu ka miko min nan, ni nasan yanda zan kawo karshen lamarinsa.Zan shigo gurinku anjima kaje.Aliyu ya sara masa, sanan ya fito.Gaskiya in son samu ne case din nan ya tsaya a hannunsa dan kam zaiyi gogaiya da zalunci.Shigarshi office din sa kenan sako ya shigo wayarsa, sai da ya zauna sanan ya duba.Murmushi yayi bayan ya karanta, a fili kumaya ce, ko me nene anko?(hahaha,kunjifa dan rainin hankali inji,shin kuna ganin zai yuwu ace baisan Ankoba,ai dai kayan yansanama Ankone,kuma kala biyu, wasu su sa baki kawai,wasu kuma baki da light blue ko? Cewar ANaM Dorayi) Ya kira layin Usman bayan sun gaisa ya tambaye shi ko menene Anko? Usman yayi murmushi wato kai dai in kaje ka shige caji ofis dinku shi ke nan baka tuna meye a cikin garin.Aliyu ya ce, aboki mu kuwa dake wanan ofishin mu muke da labarin abunda ke cikin garin, amma ba wanda ya shafi biki ba.Usman ya ce zaka bata kudi ne kurum ta shiga kasuwa da kawayenta su zabo, haka su ke yi.Aliyu ya ce, gashi ni kuma bana son yawo bare kuma xuwa kasuwa, in dai zani ne in zan je gidan zan tsaya nan wani super market in sayan masu, guda nawa ake siya?Usman ya ce, da ka basu kudin.Aliyu ya ce, ba zata kasuwa ba, wanan shine ra'ayi na, zan siyo musu zani.Usman ya ce shi kenan, sai ka suyo musu mai kyau.Aliyu ya ce ina ruwa na da zabe, ni dai kawai in dau zani.Don haushi Usman ko sallama babu ya kashe wayar.Aliyu ko da wuri ya bar office din ya bi ta kasuwa ya sai zaunnuwa kala uku ko wanneguda bibbiyu ya nufi gida.Iya tana zaune tana yankan kubewa ni kuma ina daga kicin ina kwashe tuwo ina mulmulawa a leda ina sakawa a kula ya Aliyu ya shigo da sallama. Kusan kwana hudu ban sashi a ido na ba , da ya zauna yana gaisheta.Ta amsa ya ce, ga zaunnuwa anko

Chapter 3 of 25