Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a kan lokaci.Na san kin fi kowa sanin ni dan oya oya ne, komai cikin hanzari bani son kasala, bana son musu ko gaddama.Abu na kusa da karshe bana son duk wani abu da zai shiga lokacin aiki na, ina fata kin fahimta?Na ce eh.Ya ce yan zu sai inji naki.Na ce, ni dai bai wuce uku ba, duka da zagi ne bana so.Sai nayi shiru.Ya ce, ina jinki, saura daya.Na ce imm.... Bashi kawai ma.Ya ce a a, ki fada in nayi maki cikin rashin sani fa?Bana son mu munafunci juna,fadamin duk abinda ke ranki da xuciya daya.nace amm...dama kishiya ce bana so dai,kuma bamuyi sabo daxan fada maka ba.shi kanshi shiru yayi,nasan yana mamaki ne don bai zaci jin haka ba,a zuciyarshi shi kamshiru yayi saidai bai ji wani mamaki ba saboda yasha samun case din mata akan kishiya.ganin kishiya ce abu na karshe da mata suka tsana.nima shiru nayi gabana yana ta faduwa,tsai din dana ji araina na raya cewa magana xai dankaramin mara dadi,can yace ba xan yi miki alkawari ba in na duba cewa komai na rayuwata rubutaccene tun fil'axal kamar yanda yake ga kowa.kifahimta,baxan taba yi miki karya ba,don kawai kiji dadi.sai dai shawara daya xan baki,kiyi kokarin tsare duk hakkokina,ta yiwu in kinyi hakan bazaki rage gurbin wata ba Kuma kila baxan ji sha'awar karawa ba.(Lallai yaya kazama abokona,muna da ra'ayi daya dakai, dan haka me sona nima namiki nasiha makamanciyar ta Yaya Aliyyu,kiyi kokarin kyautatawa,tayanda zaki rufe idanuna daga ganin dukkanin wata mace da matsayi irin na soyayya bayan ke. ANaM Dorayi) Nayishiru tabbas nasan gsky yafada,amma kishi ne daninasan wanan tundaga ranar da kunnena yaji ya Aliyu ya furta yana son aurena.can kasan xuciyata tunani ne kada wata rana yace xai so wata har ma ya aureta.duk sauran samarina da duk wanda yaxo da niyyar aurena nakan fada mishi koda na aure ka banason kishiya fa.Toh shi xakin nawa ina naha fuskar fada masa,shine sai yanxun...ya katse tunanina da cewa,nasan baki fahimce ni ba akan batun kishiya,don haka a aje zancan gefe muyi mai amfani.nima naji abinda bakiso zan kuma kiyaye insha Allahu.kiyi baccinki sai dasafe kar ki manta gobe akwai ranar yan sanda.bikin da suka shirya mana,ina fatan zakiyi shiri?muryata sarke nace Allah yakaimu goben. shine ya katse wayar sannan nakashe tawa na kwanta,kalamansa ne ke yawo cikin kaina na damu da bai min alkawari cewa baxai min kishaya ba har bacci yayi gaba dani.(kabwata duk lokacin da saurayi yace bazaimiki kishiyaba to kisani hakan mafificiyar karyace a hasashena,pls kabwata karkisa saurayin yayimiki wannan alkawari kawai dan gudun bacin ranki,ANaM) Ya aliyu ya iya magana cikin natsuwa,kai inason gayen sosai. Dasafe kin fitowa nayi ina yin sallah asuba dama komawa nayi nacigaba da bacci. da Iya ta tashe ni sai na langabe nace mata kaina ciwo yake yi nan ko banason tashine in ta aiki ga mutane. sai kusan sha biyu sannan na tashi nayi wanka na karya.Aisha taxo muka sha hira anan ma muka xabi kawayanmu da zamu je bikin anjima dasu.yau kam shigar Green da Golding nayi nawani leshi mai kyan gaske,abinka da farar mace kayan sun dauke ni duk da cewa wai farin ne yacece injiwasu Duk yau ban sa shi a idona ba sai yanzun da za mu tafi., yau kam gadanga kusar yaki kakinsa yasha na yansanda, ya iya aje hularsa a kai tamkar sai da ya yi course din sata,wani dan sanda ne ya jamu zuwa wajen, guri yayi guri,Usman shi ya taho da sauran kawayena, Police band sai tashi take ga wasu yan sanda suna ta bin kida fareti. gurin zamanmu na musamman muka nufa înda masu kidan suka dafo bazanmu da kida. ya Ali da abokansa da fareti suka yi tafiyar har zuwa gurin zaman har wani yana cewa yakamata matar dan dan sanda ta îya fareti itama . sun yi wasa kala kala har wani wasan su wai lokacin suna makaranta suna cin garin kwaki,anci ansha anyi rabon abubuwa.sai bayan magriba muka dawo gida.karfe sha biyun dare dai dai wayata ta soma ruri da sauri natashi nadaga yace xo mana natashi xaune na kalli shashin da Iya take, tadan rumtsa kafin lokacin sallarta ya karato,Na tashi sadaf-sadaf tamakar munafuka nafita, a kofar daki nayi sallama, ya amsa na shiga.Kwance rigingine na same shi yana danna wayarshi, jikinsa sanye da farar singileti tareda gajeran wandonta.Nayi saurin dauke kaina don kunnyar ganinshi a haka.Na rusuna kaina a kasa ga ni yaya ba tare da ya dube ni ba ya ce, tun cake din da kika bani a baki dazu gurin party nan ne a ciki na,yun wa nake ji.Na dube shi me zaka ci? Shima sai lokacin ya dube ni, me kika ga ya dace in ci?Na ce, ko za ka fara shan ruwan zafi tun da ka jima baka ci abinci ba, saboda cikin ka yawarware?Ya ce to yaya za ayi, na samu ruwan zafin?Na ce sai na dafa maka, na mike tare da ajiye wayata a gefe na nufi kicin, ina kunna risho naji takun tafiya, sai ga iya tsaye a kaina ta ce, na farka ban ganki ba lfy kika kunna risho?Na ce, yaya ne ya kirani a waya wai yana jin yunwa shi ne zan dafa mashi ruwan zafi , ta ce, hum!Ki dai kiyayi kanki, kuma ri rage wanan barin jikin, sanan kiyi maza ki dawo daki na ce, to.Ina komawa dakin dauke da dan flaks dinsa na ruwan zafin na same shi yana danne danne cikin waya ta, na juyo na jawo kofi zan zuba masa ya dube ni baki da numbata a she?Na ce ina da ita mana.Ya ce in gani.Ya ciro number ya miko min wayar, na amsa na danno sunansa inda na sa ya Ali, ya ce ok, bani ruwan zafin, na zuba a kofi na hada masa sanan na mika masa.Sai da ya amsa ya kurba sanan ya ce, amma na zaci cewa na wuce wanan matsayin na yaya.Na kalle shi eh haka ne.Ya dauko wayarshi ya danna ya nunu min numbata a wayarshi.Yayi saving dinta da suna my choice, a fili nafurta my choice, ya ce nima sai a canja min suna ko?Muka kalli juna cikin ido sannan na soma danna wayata, ya ce zauna sosai mana, sai kace ba dakin mijinki ba? Na zauna sannan na soma rubutawa na sa honey, sai na goge na sa darling, shima na goge sai kuma na rubuta sweet Aly.Zan goge yayi zaraf ya amshe wayar ta re da cewa in gani me kike rubutawa kina gogewa?A fili ya ce sweet Aly.Yayi dadi ki barshi haka.Ni kuma tuni na sunne kaina cikin cinya ta don kunya. Ya ce ai babu wani sauran kunya tsakanin mu, kinyi alkawarin za ki rinka kirana sweet dinki har gaban kowa?Na dubeshi cikin kunya sanan na sunkuyar da kai ina wasa da gefen hijabina na ce ba dai ga ban muta ne ba, yace to ni gaban kowa zan ce maki my choice, sunan ya da ce?Na saka yatsa a bakina ina dan wasa da shi,na ce me yasa ka zabi ka sanya min zabin ka?Ya dan kara matsowa, dan duk duniya ke kurum zuciyata ta zaba har mamakin ki tai lokacin da muka taya wai saida kikaimana yanga kafin ki amsa.Na yunkura bari inje in kwanta, ya ajeye kofi bakya jin dadin firar tamu ko?Ya ci gaba, kiyi hakuri dani ban taba fira da mace ba shi yasa, na dube shi tare da dan zare ido ya ce baki yarda ba ko? Nace naga kana dan sanda ka ce baka taba fira da mace ba?Amma ba wai ban yarda bane yayi dariya gaskiya bana yi, tsakanina da mace sai dai in matsalar da ta shafi aikina ne ta hada ko har yanzu baki yarda ba?Na ce na yarda na mike tsaye ya ce, firata ba dadi ko?Na ce, da dadi mana.Ya ce to shi yasa kike so ki gudu? Iya ta ce kar na dade,yace ta manta ni mijinki ne ya ce ok sai da safe?Na ce tam, har na kai bakin kofa yace, gaki dai baki son kishiya sai ina ganin ba zaki iya kula dani ba.Ina tsoron kada hakan ya ja maki kiashiya. Cak!Na tsaya cikin wata murya wacce ban san ina da ita ba na ce, sweet Aly, Allah zan iya kula da kai fa ka ji?Kasa amsa ni yayi don jin irin muryar da nayi anfani da ita.Na ruga da gudu cikin kunya shi kam shiru yayi yana mama kin mata.Lallai mata abokan nishadi ne, dubi yar hirar nan da yayi da yarinyar nan ya shagaltar dashi ya koma kamar sakarai, yayi murmushi sanan ya kwanta.Nima kwanciya nayi ina tuno abin da ya faru tsakaninmu duk da kallon da Iya ta bini da shi, da na shigo sai dai yi nayi kamar ban lura ta ji haushin dadewar da nayi a wurin yayan ba.Washegari ban tashi da wuri ba sai wajen tara lokacin baki suna ta shirin tafiya gida jen su.Sha biyu kowa ya kama gaban shi, sai mu munata aikin gyaran gida ni da iya.Kusan karfe uku na yamma ya kirani wai a kwai fura ko?Don anzowa iya da fura da nono lokacin biki, na ce masa nono yayi tsami, sai dai in ya siyo yogot ya shigo da shi ya ce to. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Tunda na idar da la'asar na zauna zaman zabar kayan da zan saka iya dai tana kallo na na sauke akwatuna na zabo atamfa cikin kayan aure na.Da na idar da sallar isha'i kuwa na shiga zabga kwalliya ina ta feshe jikina da turaruka.Iya ta shigo ta zauna bakin gado ta tsareni da idanunta ko da bata fada ba nasan abinda kallon nata yake nufi.,don haka nakoma nima bakin gado na zauna tare da ajiye dan kwalin da na dauko zan daura.Ta ce sadiya ni ba wai ina hanaki ki lura da mijinki bane ko ki shige masa a ana fi so ki bari sai kin tare, shi fa namiji babu ruwan sa da zancen kunya, in baki ji nauyi na a matsayin mahaifiyar Aliyu ba ai kyaji kunya na a matsayina na uwarki.Saboda iya shege ko watsewa yan biki basu tafi ba kin tafi dakin miji kin raba dare saboda rashin kunya?Na sunkuyar da kaina rai bace a zuciya ta na ce, har ga Allah shi yasa na so in tare a daki na, ta ce daina bata rai, daraja nike nemamaki da kima in kin tsare kanki har sai kin tare kifi kima a idonsa, ga dai misali a gidan ku.Kiji tsoron abinda ya faru da yar uwarki ta zariya Harira ya faru dake, kan ta tare tayi ciki a gidan mijin nata ya shiga yi mata wulakanci.Kin manta banda ubanku tsayaye ne ai cewa zaiyi cikin ba nasa bane, shi yasa in andaura aure ba a tare ba mace ta mika kanta ba karamin so mijin keyi mata ba za ya daraja ta.Wani dama sha'awa ce ta kawosa gurin mace da ya biya zaiji baya sonta, amma in tana gidansa fa?Ai yasan da kunya ya ce yayi aure sati daya ya kori matar.Jikina yayi sanyi, tabbas babu ja a batun iya,kuma haka ne batun Harira, tayi goyon ciki a gida ta haihu a gida ba ta tare ba.Kuma ya saketa da kyar ya amshi cikin amma har yanzu dan yana hannun uwarta agidan mu ita kuma tayi aure a Hunkuyi.Na saka kaya a sanyaye na zauna ina kara nazarin abubuwa.Har dakin iya ya shigo suka gaisa ya ce, ina yarinyar nan?Ta ce, tana ciki.Kamar daga sama sai naji ya ce, my choice.Na fito da sauri tare da amsawa, duk da nasan iya bata san me yake nufi ba.Amma tana da saurin dago abu, zata san cewa suna ne na musanman ya sa min, na amsa sannu tare da gaishe shi.Ya miko min yoghot din in kin gama ki kawo min.Na ce to,ya dubi iya bari nayi wanka. .Na shiga da sallama, yana zaune kan sallaya da alama salla ya idar, na ce baka sami jam'i bane? Yace, shafa'i da wutiri nayi.Zan tsugunna ya ce zauna a bakin katifa mana.Kina yi ya ce, sai kace ba dakin mijinki ba.Ya gyara zama kan sallayar, sanan ya dauko wata laide dake gefe ya bude ya ciro kunshin takarda ya warware yana fadin.Kin ganni da son kilishi shi yasa na saimuku Balango.Ya dauki daya ya saka a bakin shi, zo in baki a baki. Nace na koshi ni na ci abinci tun dazu.Yace wanda kika ci da ban nawa nama ne, matso kiji.Na dan sunkuyo ban sauka daga kan katifarba, shima ya matso ya miko nannu ya sa min abaki, na amsa tare da rufe fuskata cikin tafukan hannaye na.Ya ce fada min gaskiyarki, ni dake yanzu ba wani batun jin kunya. Kin kosa ko? Na daga kai alamun eh, yayi yar dariya kinyi kyau da wanan kwalliyar ta wace?Nasake makale kaina cikin cinyoyi na, na ce eh. Ya matso sai kurum naji ya kama ka fada ta, ya saka dan yatsansa yana bin zanen fulawar, jikina ya dauki bari don ji nake tamkar susa yake min.Shima nasan yaji abin da naji don naji muryarshi ta dan sarke.Ya ce wata gwana ce ta zana maki wanan fulawar?Na ce wata yarinya ce.Ya ce, yayi kyau.Ina son farar mace na dan ware ido ina duban shi.Me yasa?Ya saki kafada ta Ra'ayi nane kawai ba dan komai ba, ke fa?Na sun kuyar da ka, kalar ka nafi so a cikin maza.Yayi yar dariya, wace iri ce kala ta?Na ce, wankan tar wada baka cikin farare kuma fara cikin bakake.Ya tashi daga mazaunin shi ya dawo kusa dani kan katifar.Kina nufin duk mun dace da zabin mu?Ban iya amsawa ba saboda yanda ya kusance ni, jiki na da na shi har suna haduwa.Ya saka hannun shi a kafada ta ya manno nijikin sa, fada mini gaskiya can dama kina sona?Duk da halin da nake ciki na faduwar ga ba sabo da irin yanda ya makale ni, bai hana ni tunanin wanan mutimin ya cika tam baya.Ko yana zaton nima mai laifin ce?Ya dago fuska ta, kalli cikin ido na ki fada mun. Zan gane in kinyi karya kwa yar idonki xata nuna mun.Naji mamakina lokacin da nake furta can dama ina son ka kai fa kana sona?Cikin wata ma yaudariyar murya nayi maganar.Kurum sai na fuskanci le bunan shi a kan nawa yana yi mun sumba, lamarin ya zo min sabo, ko na ce bako.Ya dinga yi mun wasu abubuwa masu firgitani har na zama bani da karfi.Tsoro na daya kada ya gota daga haka, saboda ina tsoron Iya.....zandakata Anan,muhadu a lokaci nagaba Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Darajar Yayana1-04 Posted by ANaM Dorayi on 10:48 PM, 16-Mar-16 Under: DARAJAR 'YA'YANA _______________NA _____HALIMA K MASHI Nayi karfin halin zame jiki na daga na shi, yakwanta rigingine na mike sai da safe.Ya miko hannu ya riko nawa hannun, cikin wata rikitaciyar murya ya ce, ki zo nan mu kwana.Da sau ri na ce, tab Iya ba zata yarda ba.Ya ce, ina ruwanta, ni ba mijinki bane?Na ce to ai ban tare ba.Ya saki hannu na.Da sauri na fice.Na tabbata in na shiga daki haka iya zata fahimci wani abu, don duk kwalliyar fiskata ya goge min.Don haka sai na bige da sabar buta na nufi bandaki, na zo nayi alawala.Ina shiga uwar daki ta bini da kallo tana kwance kan gadonta.Na cire kayan jiki na dauko rigar sallata nayi shafa'i da wutiri.Ta tabe baki bata dai ce min komai ba ko takula duk na tsargune?Oho.Da kyar na samu bacci ya soma dauka ta sabo da tunanin abubuwan da suka faru tsakani na da shi.Shigowar sakonshi dan sautin ya farkar dani, na bude na duba cewa yayi, kin hanani bacci my choice kixo ki taima ka min please.A raina na ce mai zanyi maka sweey Aly, ka dan bani lokaci mu tare, kiranshi ne ya katse tunanina,sa sauri na farka dan ina tsoron kada ringing din ya farkar da iya, duk da cewa na san tana jina don bata da nauyin bacci.Can kasan makoshi na nayi sallama ya amsa muryarsa a raunane, har mamakinsa nake ina girman kan? Ina isa da jin kan?A she dai mace dai ita ce namiji.In ba mace rayuwar namiji ragaggiya ce.Ya katse mamaki na da cewa, kizo kinji?Ba zan iya bacci ba ki taimake ni.Nace iya fa tana jinmu ka bari sai tayi bacci.Ya ce dagaske zakixo in jira ki? Na ce eh.Sai ya yanke niko gaba daya ma sai na kashewayar, na amsa masa cewa zan xo ne kurum amma ba dan zan je din ba, sai don ya barni.Kuma ko ba dan iya ba ina tsoro, tunda ban san yanda abubuwan suke ba.Na makele fulo ina tunanin ko a wane hali yake ciki yanzun, na jima kafin bacci ya tafi dani.Nayi mafarki kala kala masu dadi wai muna ta shawagi a cikin wata duniya ni da ya Ali.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Da safe kuwa fuskarshi a murtike, don ko amsa gaisuwata baiyi ba, lokacin da yazo gaida Iya ina gai da shi,hakan bai yi min dadi ba, na kunna waya ta na tura masa sakon ban hakuri tare da ce masa jiya naso inzo Iya ce bata bari na fito ba.Ko ya gani ko bai gani ba oho, bai dai bani amsa ba, na dafa ruwan tea na kai mai na same shi ya gama shirin fita yana daura ta kalmi.Na shiga da sallama ciki ciki ya amsa, ina shiga ya dubeni fuska daure ya ce, lfy?Cikin wata murya irin ta a salin jarumin maza.Jiki na ya dauki bari na ce, dama....dama tea ne.Ya ce fitan min da shi ina azumi, fargaba na ya karu, iya ce jiya ta fash....Ke!Ya katse ni, fita a nan dan Allah.Na fita da sauri, zugun na zauna ina tunanin yanda ya Ali yake canza launi tamkar hawainiya... Kimanin kwanaki uku kenan yayi mun dif, inna gaida shi baya amsawa, haka nan in abinci na kai mai ko yaushe sai ya ce yana azumi.In iya tayi mashi magana ke nan, in nice ma na kai mishi ni abu sai ya koro ni, ina girki a kicin iya ta fita lokacin sai ga Aisha kawata.Naji dadin zuwanta ta tayani,muna fira na bata lbr duk halin da nike ciki na kara da cewa, ya Aliyu gaba yake dani, iya ta sa ido sosai dan ganin ban bada kai ga miji na ba, ba tare da mun tare ba.Don Allah Aisha ki bani shawara, ta ce, ni dainawa ganin in har zan fada maki gaskiya kibi mijinki, daga lokacin da aka daura muku aure da shi dukkannin hakkokin shi sun hau kanki.Nayi ajiyar zuciya tace, nasan kin san komai ma kina yi ne kamar baki sani ba nace Aisha nasani,Iya fa idonta yana kanmu.Ko daki na shiga sai kiga tana kai kawo, in na fito kuma tayi ta yi mun kallon tuhuma, to ki bashi shawarar ku fita wani wurin mana.Nace tap nice ma zan bashi shawarar?To an ce maki iya za ta barni in fita ne?Aisha ta ce, yanda kika gani, amma in nice zan bi miji nane.Rayuwar nan ta yanxu mata suna bin maza har inda suke, balantana mijinki dan kwas irin wanda basu da yawa a cikin jama'a?Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Na ce nima ina tuna haka, shiyasa wlh ban so ba da ban tare ba, kamar yarda ko wace Amarya take tarewa a dakinta. Ki tayani da adu'a don sun sani a tsakiya ita tana kallo na a mai rawar kai na shige masa,shi yana kallo na mara biyayya.Aisha ta ce, abu ne fa mai sauki ke ce kika dauke shi da zafi, in kin bi mijinki kinga dole ta barku.Na dubi Aisha ta ce, fa ba zai dubi mutuncina ba, Aisha ta ce, in bai sameki a mutuncenba ba?Kin bi maza ne?Na kai mata duka, kinji ki da wani zance, in na bi tare muka bi kenan.Ta ce ke ce da wani shirme, in kin ga namiji yaga rashin mutuncinki ya sameki kin bi wasu....(Biri fa kuma yayi kama da mutum,watakila irin haka tafaru da yar uwarki da Zaria,shiyasa mijin yayi inkarin kasancewarvcinkin a matsayin nasa,hartakai ga saki ANaM Dorayi) Kalu bale ga masu saida mutuncinsu a banxa. Aliyu tukur ya tsaya a gaban shugaban shashin su na binciken manyan laifuka, mataimakin Commissioner.Ya ce ASP Aliyu zanfi so idan kana tsayawa a kan aikinka, ina nufin ka rinka dakatawa a madakatarka.Sanan ka rage kishin ka, domin kasar mu a yau in kace haka zakayi lallai ba zaka kai ko ina ba.Ina yi maka magana ne a kan barawon shanu din nan, mutumin mai girma commissioner ne, na tabbata da yana gari baza ka kamashi ba bare tsarewa.Inma kayi nasara ka kama shi, ba zaiyi minti talatin a tsare ba kai ba a taba kama shi ba, yaranshi kurum ake kamawa.Da sunyi waya da commissioner zaisa a sake su, nayi mamakin ma da commissioner bai tsawatar maka ba, ya ce kawai ka bar case din a hannunsa.Ran Aliyu ya baci, shi da ya shiga aikin dan sanda kishin kasarshi da kawo gyara, sai kuma su rinka ganin barna suna kauda kai?Ya ce, yallabai ina rantsuwar da mukayi da alkur'ni cewa zamuyi aiki tukuru bisa amana da gaskiya, idan dannanda bai zama mai kishi da gaskiya me za a kirashi?Idan dan sanda zai rinka amsar cin hanci yana hulda da manyan azzalumai yana daurewa barayi gindi suna zalunci, za a kirashi mai tsaron lafiya al'umma.AC ya dagawa aliyu hannu, dakata ASP, wannan tambayoyin zasu fi dacewa kayiwa CP su, ni shawara na baka.Da akwai mutane irinka da yawa wadanda suka nuna kishi, wasu anyi musu canjin gurin aiki zuwa wasu garuruwan da ba zasu sami irin wanan barnar ba bare suyi gyara.Wasu anyi musu sharri an koresu, kai wasu sun mutu yayin da wasu da yawa suka ajiye hularsu.Ban hanaka yin kishi da gaskiya tare da kin karbar cin hanci ba, sai dai ina mai baka shawara ka dinga tsayawa ga kananan masu laifi, jeka abinka. Aliyu yana zaune a office din shi, kansa ya dauki zafi yana tuno sa'insa da sukayi da Barawon shanun, inda barawon yace, kai yaro wanan ba wani bakon abu bane satar shanun da muke yi.Haka nan mu nan Headquarter gidan mu ne kaine mutum na farko da na taba bawa cin hanci ya maido mini.Nafi tunanin kana daga cikin mutanen da basu da rabo, amma kai bako ne ko?Aliyu ya ce, ba jin tarihi ko maganar cin hanci na xo ba, nazo nan ne dan in kama ka,a matsayinka na mai laifi, ni kuma na hukuma.Duk wadan nan baya nan zasu biyo baya in munje office, yaranka muka kama kuma suka ja sunanka.Barawon ya zaro ido tare da daga murya ya ce, kai bako ne shiyasa baka sanni ba amma muje.Aliyu ya ce nasan ko ban sanka ba, bako ne ni bako ne wannan ba damuwata ba ce.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Sun san Aliyu bai san wanene wanan barawon ba, shi kanshi barawon cewa yayi zakayi da nasanin kamani.Aliyu bai ce kala ba, ya nufi Office din sa zuciyarshi cike da son nunawa wanan baron cewa hukuma bai bar kowaba.Amma me? daidai lokacin da yake bada ummarnin ashigar da kara ne shugaban shashin su AC ya ce, kajira tukunna sai an sami ummurni daga commissioner.Dafawar da akayi mashi itace ta dawo dashi daga dogon tunaninsa.Ya dago kai.Insperctor kamal kaita ne ya ce Sir, ka daina damuwa da irin wadan nan matsalolin, sanan ka ci gaba da yanda kake, Allah zai kawo maka dauki dan yana tare da irinku.Sai dai dama baku cika farin jini ba a cikin yan sanda, saboda kowa yana ganin cewa zaku toshe masa kafar samu.Shawarata ka bar batun Barawon nan ko ba komai kayi namiji tunda ka kamo shi, ka kuma tsare shi.Sanan Allah ya doraka a kan CP bai dauki zafi a kanka ba.Aliyu ya mike tsaye, na shigo aikin dansanda cike da kishi da buri, gami da kwazo.Manufata insamu waddanda zasu fahimci niyyata don mu kawo gyara cikin hukumar yan sanda.Na tabbata ko cikin headquarter din nan akwai masu kishi da yawa wadanda suke jin irin abinda nake ji yanxu a zuciyata. Inspector ya ce, hada dani, sai dai ina mai bakin cikin sanar da kai cewa ba zamu kai labari ba, tunda daga sama a ake tadiye mana kafa.Aliyu yace inko haka ne zaya ci gaba da faruwa, watarana zan iya ajiye hulana.Inspector ya ce, ranka ya dade kada kasaka haka a ranka tun yanxun, kaji a cikin xuciyarka cewa burinka ya cika, Allah yana tare da mai gaskiya.Ranka ya dade ka duba tashin farko bin diddiginka yasa sashinmu na bincike suke shakkarka, ina son mutum irinka.Aliyu ya lumshe ido tare da cewa zantukanka sunyi mun allura inspector, zan kara kaimi.Da wanan ya cigaba da aikin sa.Daf da zai tashine aka shigo da wani da ake zargi, ya kalle gobjejen mutumin sanan ya dubi yan sandan.Me yayi shi kuma wanan? Sajan Ado ya ce, ranka ya dade, kato kamar wanan aka kama yayiwa yar shekara takwas fyde,ran Aliyu ya tunxura, ya runtse ido cikin takaici, ya ware ido ya kalli mutumin cikin tsana ya ce, wai wane irin zaluncine wanan kuke yiwa jikokinku?Cikin rawar murya mutumin ya ce ranka ya dade na rantse maka ba ni bane, sharri sukayi min, na rantse maka.Aliyu ya harareshi, ba kowa bane yake amsa laifinsa da sauri.Ya kalli yan sandan suwaye suka kama shi?Sajan ya ce ranka ya dade ga mutanen da suka kawoshi can, sune suka kamashi da yarinyar a shagon shi tana ihu.Yace ina yarinyar yanxu?Sukace an tafi kaita Asibiti.Ya kalli mutumin yaja tsaki ya ce, ya ce ku rufe shi, yanxu ba wani sausauci ga irin mutanen nan masu cutar da kananan yara ta ta hanyar fyade Ya koma office din sa cikin ta kaicin fyadan nan, kullum sai sun samu irin wanan case din da yar da jarirai yafi yawa, amma yanzun yanaga zasu xo daidai.Ya kira sajan ya ce, ya kawo masa takardar tuhumar (statement) da ya duba tsaki yaja, ya dubi sajan.Kullum dai abin iri daya ne.Ya tabe baki, sanan ya dubi a gogonsa, yau shida zan bar nan, duk wanda ya nemeni saidasafe.Sajan ya sake kamewa tare da fadin yes sir!Sai kuma wanan mutumin yaya za ayi da shi?Aliyu ya ce, ba maganar beli ko wani ya zo zuwa gobe za a hada bincike a turashi kotu.Sajan ya sara masa sanan ya fito.Da dunbin wanan damuwar ya iso gida, daga ganinshi kasan akwai abin da yake damun shi, kan katifarshi ya zube rigingine bata re da ya cire koda ta kalmi ba.Lokacin da ya shigo ina zaune a kan kujera a kofar daki ina karatun wani littafi (SIRRIN BOYE) na Anty Bilkisu.Ga al'adarshi in ya shigo dakin Iya yake fara shiga kafin ya dawo dakinsa, ya cire kaya in sun gaisa.Ya shiga wanka.Amma yanxu tunda ya shigo shiru, iya ta fitodaga bayi (ban daki) na dubeta na ce, yaya fa?Ya dawo yanayin shi

Chapter 5 of 25