Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gaida Gyambo karshen girma kenanko? Usman ya sunkuyar da kai yana dan murmushi cikin jin kunya, ni dai na ce sai na dawo.Da mota yazo na shiga, gidansa muka fara zuwa ya ce inga Abida matarsa minti biyu. Ina yin sallama ta amsa, sanan ta ce kai Amarya kin tsula kyau sosai, taja hannuna zuwa bedroom din ta. Zo muyi yar shawara,Bakin gado muka zauna.Ta kalleni a da banyi zaton zaki zama mai taurin kai ba.Na zaro ido ina kallonta, ta ce, ranar juma'a da daddare mijiki nan ya ci abinci tare da mijina, ina daga ciki ina juyo su mijinki yana fadawa mijina halin da yake ciki na takura.Gashi kinki ki bashi hadinkai, har yana cewa wani dare da kika ki sauraranshi har ya dagawaya ya kira wata yar sanda dake nacin sonshi ta kuma sadaukar da kanta gareshi.Har ta daga sai kuma tsoron Allah ya shige shi, Allah ya taimaka ya tashi ya shiga yin nafila, daba dan haka ta faru ba, me kike tsammani?Na ce, wai Allah, daga nan sai zina.Tace kina da kwamasho ko baki da shi?Na ce, ina dashi.Madallah.Ta dafani yanxu abinda nakeso dake, kinga ke yar zamani ce, ki rike mijinki, in ba haka ba sai wasu su rike maki shi.Na ce, anty iya ce, Allah ba dan Iya ba zanyi duk abin da yake so.Ta ce, to baga shi yau zaku fita ba, in kin dawo Iya ganewa zatayi?In ba ke kika fada mata ba.Nayi shiru ta ce, to kisani kina cikin tsinuwar ubangiji, in yanxu kika mutu mijinki yana cikin wanan halin sai kin hadu da fushin Allah, ma tsawar ba shi ya yafe maki ba.Gabana ya shiga faduwa, na ce, Allah anty nitsoro nake ji ban san yaya abubuwan suke ba, nima bansan yana fushi dani.Tayi murmushi ba wani wahala.Ta girgiza kafadarta, ki amince da mijinki a duk lokacin da ya bukaci haka na rokeki.Na raunana muryata, in na sa muku aure ba?Na ce eh.Ta ce ki ceci kanki daga halaka fa, kin san komai ke ba jahila bace....Muryar Usman ta katsemu da cewa wai me kike kitsa mata ne?Zo mutafi kinji.Ta ce, jeki kada yajimu basusan naji firarsu ba, dan Allah ki kama mijinki hannu bibbiyu ko bakya son shi?Na sunkuyar da kai ina sonshi mana, bari dai in gani ko zan iya ina tsoro.Na fita muka tafi.,ban san ina muke tafiya ba, don kaina yana sunkuye ne ina wasa da yatsuna.Har zuwa lokacin da motar ta tsaya.Ina daga kaina COMMAND GUEST na gani.Ya ce jirani kadan ina zuwa.Gaba na ya shiga faduwa, koda ban san ko inane nan ba na tabbata Hotel ne tunda naga an rubuta guest.Bayan wasu lokuta ya dawo yana waya, danhaka da hannu ya yafito ni, na fito a baya nabishi yana ci gaba da tafiya tare da tin waya.Kuma na fahimci kamar da ya Aliyu suke magana, dan naji yana fada mai ga mu nan yanxu zamu shiga cikin hotel din.Kuma ni zan wuce ne dan Allah kayi hanzari muka ratsa falon muka nufi jerin dakuna yasa makulli yana bude wani daki.Dai dai lokacin sako ya shigo cikin daki wayata, na ciro na duba.Cewa yayi kishiga kijirani kadan my choice.Na kalli Usman yayi murmushi ba da jimawaba zai zo, yanzu zaki ganshi.Na shiga cikin dakin ina dari dari, tare da yankalle kale, ya tako ya shigo dakin.Kada ki damu ya dauki remote ya kunna TV, kiyi kallo ga tashar India nan abin sonku mata.Ya nuna mata wata takarda.In kina da muradin wani abu ga wanan takardan ga numbe waya ki kira ki zabi dayadaga nau'in abincin da kike so ko na sha, za a kawo miki.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Har ya kai bakin kofa sai kuma ya dawo, ya ciro wallet dinsa ya bude ya ciro katin MTN ya miko min.Gashi ki loda a wayarki.Ya sake juyawa ya tafi, tare da cewa ki kulle kofar in yazo zai kwankwasa sai ki bude, na barki lafiya.A sanyaye na ce, na gode.Tunda ya fita ta gumi na hada, tunani da zullumin abu biyu ne na farko in ya zo mai zai faru?Sanan yaya zan kare da fada iya in na komagida?Ban ma san takaimaimain lokacin da zamu bar nan ba.Fim din da ake yine ya dan shagaltar dani, don haka ban lura da lokaci ba, sai da na kalli a gogo na rude, shida dai dai na yamma.A raina na ce tafiya zanyi.....kwankwasa kofar ya dakatar dani, na bude cike da faduwar gaba, a zatona shine ashe ma aikacin gurin ne yake tambayata ko zanci wani abu?Na ce a a yace kada ki damu Oga ya na nan zuwa, ban tanka shi ba na maida kofar na rufe.A raina nace wato har sunsanshi tunda gashi suna cewa yana zuwa.Na ce wa yasani ma ko yana zuwa da mata.....na katse zancen da cewa a'u'zubillah, ba kyau munmunan zato.mikewa nayi ina ta kai komo a tsakar dakin, tunanina wa zan kira wanda zaikaiwa iya waya in mata bayanin cewa yaya nake jira mu dawo.Can na tuno da Bello, na kira wayarsa dan akwi number shi a wayata, kuma yana kiran Aisha itama tana kiranshi da layi na.Muka gaisa, na ce dan Allah Bello in kana kusa ina son magana da Aisha ne, tayaya zaka taimaka min?Ya ce bani minti hudu zuwa biyar a kai mata. Na ce nagode. Sai da na bari kusan minti shida sanan na kira cikin sa'a kuwa ta daga.Na ce,Aisha taimako nake nema a wajenki, don Allah.Ta ce na me?Na ce, kin sani ne?Mun fita har yanzu bamu dawo ba, shine nakeso kije kicewa iya don Allah kada taji shiru mun nan dawowa.Ta ce, keda wa kuka fita?Na turo baki tamkar ina gabanta, nace da wanan ya Aliyun mana.Da sauri ta ce, au, ke da mijinki kika fita? Bata jira amsa ba ta ci gaba da cewa, to ba zan fada mata ba, na zata ma ke da wata ce, to in shekara ma zakuyi ina ruwanta?Ta ja tsaki.Dan Allah malama in zakiba mijinki kulawa ki bashi kulawa kawai, sai an jima ta kashe batare da nasake jinta bakina ba, nayi sororo ina kallon wayar.Shi kuwa ya Aliyu daidai wanan lokacin ya isa gidansu iya.Tana girki yayi mata sannu da gida, ta ce yauwa ina yar tawa?Ya ce, yace yanxu zanje in sameta in nayi wanka daga gidan oga xuwa gidan sauran Abokai na.Murmushi iya tayi ta ci gaba da cewa, wai ni za'a yiwa wayo, nifa na haifesu, ni fa duk abinku kar nake kallonku. Shiri yayi ango sosai, sai zuba kamshi yake yi, ya nufi masauki na comman bayan yayi tsarabar kaji da lemuka da kalolin madara masu tsafta. Ya gaisa da masu tarbar bakin inda wani daya yake tabbatar masa da cewa a jiyarsa na nan a ciki, sun lura da ita yanda ya kamata.Kwankwasa kofar ta re da muryarsa naji, inda yake cewa Dear my choice.Jikina ya dauki bari, naje na bude kofar tare da yi masa sannu da zuwa.Na amshi ledojin hannunsa, kallo yake tayi tunda ya shigo har ya maida kofar ya rufe, na ajiye ledar na zauna kan kujerar dake kusa da gadon.Kai tsaye yazo ya zauna kan hannun kujerar.Dear my choice kinjini shiru ko?Yayi maganar cikin wata laulausar murya Na kalli a gogo gabana ya ci gaba da faduwa, nace gashi har magariba ta karato, yanzu iya tana can aiki yayi mata yawa, tana kuma jira na.Ya kama hannuna me zakiyi mata da zata jiraki?Na ce abincin dare mana.Ya hada tafin hannuna da nashi ya sarke.Sanan ya dan matsa, in kin tare a gidanki wane zai dinga yi mata aiki? Cikin raunaniyar murya na ce, zan ke aika mata duk abin da naci.Idanu na suka kawo ruwa don tunanin rabuwa da iya.Ya dago fiska menene na kuka?Na ce, ina tunanin rabuwa da iya ta ne.Ya kwantoni jikinsa.Yi hakuri kanwata, ai ba wani nisane tsakanin mu da iya ba, kullum nasan zatazo ta duba ki, in bata zoba kuma mu zamuje.Na kalli cikin idanunshi, da gaske zamuje? Ka min alkawari fa.Ya ce, in sha Allahu.Ya ciro fari kar din hankici mai kamshi daga aljihunsa ya soma share min hawaye.Tashi kiyi alwala muyi sallah sai muci abinci.Gurin da na idar da sallar ya sameni, ya bajekomai gani da shegen kwadayi, amma fargaba ya hana ni ci.Duk hankalina tashe yake, ya lura da haka, sai ya soma lallashi na.Haba Sadiya my coice, me nene naga duk kin damu?Nifa mijinkine na sunna.Nace, to ai iya ta ce kada wani abu ya faru tsakanin mu, har sai mun tare.Ya ce to zata sani ne, ko ke zaki fada mata?Na soma kuka, ina kallon fuskarshi.Wlh yaya zata gane.Zumbur ya mike daga kusa dani ranshi a bacce, ya soma yin magana cikin daga murya.Kina fakewa da Iya ne kurum dan kawai ki cucheni, ba fa haramun zan aikata ba.Kinsan ina kyalekine ina lallabaki, in nace zan gwada maki isa ba zaki iya kwatar kankiba ko?Jikina ya soma bari, yaya don Allah kayi hakuri.....Yi mun shiru.Ya katsane, sai wahala kike bani kina wani inyi hakuri, ba zan hakura ba, haka nan ba zan matsa maki ba, amma ki sani baki ba komawa gida ko da zamu shekara a nan harsai kin yardar min a bin da ya halasta min.Na fara kuka wiwi shi kuma ya fice ya zare makulli ya kulle ni ta baya.Na fada kan gado ina kuka, wata zuciya ta ce mun gara fa kiyarda dan sai kin dibi kunyar da bakiso a hannunki, don dan shi namiji babu ruwansa.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Dasauri na dauki wayata na soma kiran layin sa.Tayi ringing kusan sau biyar sanan ya daga, cikin kuka na ce, yaya dan Allah kazo na yarda....Da zafin rai ya ce, bana so, ke har kin isa mzacen da zaki ja raina?Bari kiji wani abu, baki son ki dade kada iya ta zargeki ko?To ina mai shaida maki cewa nan zaki kwana, in yaso in kin koma gida sai inga maizai faru.Ya kashe wayar, ransa ya baci dani sosai.Daya wayarsa ta soma ruri da sauri ya cirota don in yaji ringingi din ta daga office ne, duk da ba ganinsa yake ba sai da ya nutsu da ya daga ya ji muryar.Cikin sauri sauri yake magana.ASP kana ina ne?Aliyu ya ce, ina nan kan titin waff Road.Ya ce, yauwa kana kusa ma, yi hanzari ka iso nan (headquarter) ka kwashi yara ku nufiunguwar rimi layin dan marina gida mai lamba tara, yan fashi sun shiga gidan sunyi fashi.Sanan sunyi gaba da babban yaron mai gidan.Ga ni nan zuwa ranka ya dade.Aliyu ya amsa cikin izza, a duk lokacin da aiki ya taso Aliyu yakan mance da duk lamarin dake gaban sa matsawar ba salla ba ce.Sun isa gidan da yan fashin suka shiga, Aliyu tare da inspector Adamu da sajan Musa, sai kofur Bala.Cikin natsuwa Aliyu ke kallon ko ina, kafin ya soma magana.Hajiya sannunku da juyayi.Ta ce, yauwa.Cikin kuka da rawar murya ta amsa, ya ce ina mai gidanki?Ta ce, baya nan, kuma dama sunce shi sukazo nema.Ya kalli kofur wanda tuni ya soma rubuta komai, ya sake maida kanshi ga Hajiyar.Ta ina suka shigo?Ta ja majina, sanan ta ce ta kofa.Ta ci gaba, sun ga Yusuf ya shigo a cikin motar baban su to sunyi tsammanin shine tunda gilashin mai duhu ne.Don haka sai suka biyo shi.Aliyu ya ce, shi Yusuf din daga ina yake?Ta ce, daga masalaci ya ke, babansu yayi masa waya, cewa yaje ya dauko motarsa.Don ni ya soma kira wai in kira masa Yusuf ya dauki motar, sai na ce ya kira layin sa ya fita masallaci.Kuma ba lallai bane daga can ya dawo gida ba, Aliyu ya gyada kai alamun gamsuwa sanan ya ce, motar ta samu matsala ne?Ta ce, a a.Sau biyu ana biyo shi ana kai masa hari a motar da dare shi ne dalilin da yasa sam bayason karfe tara tayi masa a motar na dare.Yau ma mitin ne zasuyi da ya taso musu da gaggawa kuma bai san lokacin da zasu tashi ba.Aliyu yayi taku zuwa tagar ya daga labulen windon yana kallon harabar gidan haskenta kamar duhun magariba baiyi ba.Ya waiwayo ya dubeta wace mota ce daga cikin wayan nan motocin guda uku?Ta karaso ta daga dayan labulen windon wanacan (hondar ce) baka CRV.Ya saki labulen yanzu mai gidan ya sani?Ta ce, a a yana kashe duk wayoyin shi ne in zasuyi mitin.Ina ne gurin aikin nashi?Aliyu ya bukata cikin rawar murya ta ce, shine manaja a first bank. Aliyu yayi shiru kamar mai wani nazari, can ya ce zaki iya fada mun kamannin yan fashin?Ta ce, eh, zan iya.Babban su baki ne dogo kuma kamar yanada yare, don hausarshi bata goge ba.Sai dai kila muslmi ne, sauran kuma biyu fararene ina zaton fulanine, biyun dake waje ne ban tantance su ba.Aliyu ya jefeta da wata tambayar, yaya kika yi tsammanin musulmine? Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ta ce, haka kawai naga kamar musulmine.Aliyu yayi guntun murmushi.Bari mu barki haka, yanxu bari muje mu dora bincike.Ta sake fashewa da kuka.Ran ka ya dade ka taimake ni yanzu yaya za'ayi mijina ya samu labari dan kada ya fito sukama shi?Aliyu ya ce, kada ki damu, zamu bashi kulawa da tsaro, sanan ki saurara sosai nasan zasu kiraki ina zaton garkuwa zasuyi dashi.Kiyi mana saving din number, in kuma ba number ki kiramu ki sanar da mu.Ta ce, to yallabai na gode.Ya ce ba komai kiyi adu'a.Suna fita ya kira AC ya koro masa komai, AC ya ce, to yanxu ku fara ji da maigidan nata, sanan kunsan yanda zakuyi ko?Aliyu ya ce, yes Sir!Sai dai ina kake ganin za a bashi mafaka tunda ba dama mu barshi ya koma gidansa?AC ya ce kuxo nan dashi daga nan sai a kaishi inda ya dace.Aliyu ya kara cewa yes sir.Ya dubi yaran kumaje first bank.Sha biyu da minti ashirin, Alhaji auwal ya fitoa rikice daga cikin banki, gama mitin dinsu ke da wuya police commissioner ya kira shi bayan ya kunna wayarshi.Ya fada mashi cewa ga yarana nan zasu taho dashi dan kare lafiyarsa.Alhaji auwal ya ce saboda me ranka ya dade?Commissioner ya ce, masu bibiyara ne suka shiga gidanka, amma ka kwantar da hankalinka za a kama su.Suna tafe cikin mota Alhji sai adu'a yake yi yana tunanin me ya tarewa wadan nan bayin Allah?Kofur ya ce, Alh kaji cewa sun tafi da yaronka?Aliyu yayi mashi tsawa da cewa kofur?Da sauri kofur yace yes sorry sir.Alhaji Auwal ya ce ranka ya dade wane dan nawa dauka Yusuf? Aliyu ya ce kada ka damu, in mun isa can zakaji komai a bakin yallabai, kuma duk abubuwan zasuxo da sauki. Alh. Auwal ya ci gaba da adu'a. Ofishin commissioner yayi tsit tamkar babu mutane sai karan (ac) da na fanka.CP ya kalli Aliyu dake kame, ya ce nasan kana da kwazo Alhamdulillahi,yanzu sashin binciken mu na takama da kai.Domin aikinka kanayinsa da karsashi gami da izza.Ya kalli Alh. Auwal kada ka damu Alh, babu abin da zai samu yaronka.Zamu baka kula shi kuma zamuyi dauki badadi da su.Alh, ya ce, kana ganin ba zasu kashe shi ba? CP ya ce, ai kudi zasu nema munsan irinsu, sai dai yanda tayi kwatancen shi ina zaton bako ne kila kuma ya jima yana yi bamu taba arba dasu ba ne.Amma wanan karon in sha Allah za mu hadu.Ya kali Aliyu ASP aje ayi shiri yanda ya kamata.Ina bukatar barayin nan tako wane hali sai dai banda kisa zan saurari wayarka a ko wane lokaci kwa iya tafiya Sai da Aliyu ya tunkari gida sanan ya tuno da wata Sadiya, amma duk da haka bai wani damu ba dan yasan zata sami kulawa yan da ya kamata.Ya sake ciro waya ya kira, jim kadan aka daga, ya ce Ibrahim dan Allah ajiyata na nan?Aiki ya rike ni da safe zan turo aboki na ya tafi da ita.Ibrahim ya ce ba ko mai yalla bai.Sun saba da Ibrahim ne sakamakon wata matsala da ta taba tasowa a Hotel din su Aliyu suka bincika case din.Ibrahim shine me kula da dakunan kwana na cikin Hotel din.Motar yansanda tayi faking a kofar gidansu Aliyu ya shiga gidan da hanzari.Sai da ya gama shirinsa sosai sanan ya nufi dakin iya.Tana kokarin fitowa suka ci karo, yace iya na kama hanya zantafi wajenta aiki ya taso.Usman zai tafi ya daukota ko da gobe ne.Kar ki damu canma gida ne gidan Oga ne.Haushi ya hanata magana, Aliyu ya dafa kafarta, ki min adu'a iya da yan fashi zamuyi arta bu, kin san aikin mu bakin rai muke yin shi.Ta ce Allah ya baku sa'a.Gudu gudu ya fito.Da kallo ta bishi har ga Allah bana son aikin dan sanda amma bata so ta bata rai a kan haka, dan kada ta tauye shi.Ta tabbata adu'ar ta ita ce daukakarshi, fushinta zai iya tauye shi a fili ta furta, Allah ka yi wa yaran nan Albarka dukansu, ka dorasu a kan hanya ma daidaiciya amin.Nikam a a lokacin ina can tsoro, fargaba da bakin ciki sun isheni.Kai har da nadama.Naji haushin kaina da naki bin umurnin mijina, gashi yanzu ya tafi yana fushi dani.Nasan mala'iku ma ba zasu raga min ba, kuma iyar da nake cewa zata yi mun fada in taga na dade, to sai dai ta kashe ni.Dan ina ganin tabbas nan zan kwana.Da na bi umurninsa kila da yanxu mun tafi gida cikin jin dadi.Kila ma yayi ta shi min albarka, mala'ku suna amsawa.Naja tsaki tare da cewa, kash! Nima ban yi ba wlh.Haka nayi kwanan zaune, danma na rage daren da yin nafilfili, sai da nayi sallar asubahi sanan na kwanta.Bacci ya tafi dani, ban farka ba sai kusan sha daya.Kwankwasa kofa ne ya tasheni, nazo na ce wanene?Ya ce, Ibrahim ne.Na ce, ai ya rufe dakin ya tafi da makullin.Ya ce, ba ko mai ga wani makullin, me kike bukata? Nace ba ko mai, akwai abinci a nan dakin dayazo dashi jiya.Ibrahim ya ce, to shi kenan.Ina jin takun tafiyar sa, na zauna a gurin dantsabar takaici, bani da ma ranar tafiya gida ke nan.Shi kam dai dai wanan lokacin yana gidan Alhaji Auwal cikin falonsu inda yake sauraron bayani daga bakin Hajiya.Yanda sukayi da yan fashin da suka kirata.Ta ce, kamar yanda kayi zaton zasu kira sunkira ni yau ya da safe.Aliyu ya ce, karfe nawa?Ta ce takwas da rabi dai dai suka ce kudi suke so naira miliyan uku da rabi.Sun ce in har ba a sami kudin ba zuwa jibi zasu kashe shi, kuma sun ce basa son jami'an tsaro su shigo ciki, kuma basa so a nemi ragi.Me kika ce musu?Ta ce, ni kuma duk abin da suka ce da to nake ta amsa musu. Ya gyara zama ya ce, ina suka ce a kai musu kudin?Wai filin golf.Ina number da suka kiraki?Ta dauko wayar ta fito da namber ga ta nan. Ya amsa ya dauki number sanan ya fita harabar gidan yana sanar da CP halin da ake ciki.CP ya ce, ka tafi da layin kamfanin su, wane layi ne? Aliyu ya ce (MTN) ne.CP ya ce, maza ka tafi dashi ka tambatar kayi abin da ya dace da wuri, dan kila cire layin zasuyi ko kuma anjima su kira da wani layin da ban.Aliyu ya ce, an gama sir.Sai da yaje office din Usman sanan ya tuna da Sadiya.Bayan sun gama magana akan abin da ya kai shi, dama usman MTN yake aiki, sanan ya ce, wanan yarinyar mai shegen tsoron tsiya, kuka tayi ta min na barta na tafi abina.Idan ka tashi dan Allah katafi ka taho da ita don ni ko ganinta bana son yi.Usman yayi murmushi, sanan ya ce, kayi mata uzuri, kasan yarinya ce sai a hankali.Usman ba da bata lokaci ba ya sanar da manajan su, nan take aka soma gudanar da bincike a kan lambar.Sun gano layin a yanzu baya kan waya, amma sun hada komai yadda da an dora shikan waya zasu gano inda mai layin yake.Nan take kuma ya kira CP yayi masa bayani.CP ya ce, good! Kara zage damtse in kuma kana bukatar yara duk sanar dani.Yes sir!Inji Aliyu.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Na idar da sallah azahar ke nan sai naji alamun ana bude kofa, fatana Allah yasa yaya Aliyu ne, in sha Allahu yanzu nan zan bashi mamaki Sai dai kashi!Ya na budewa sai naga yaya Usman, ya ce tattaro kayanki muje gida.Na dauki jakata da mayafi, sanan na gaishe shi, ya amsa tare da cewa ki kwaso lemukanmana.Na ce, na kishi da su. Ya ce, ai kya kai wa iya tsara ba ko kina nufin gidan Oga ba a baki ko mai ba duk da cewa kin kwana? Yayi tambayar cikin zolaya, na dawo na dauka, har ya taya ni sai lokacin naga Ibrahim din da suke nagana, gajere ne baki.Sai da muka tsaya Marhaba Store ya kara min tsaraba wai harda turmin zani matar Oga ta ce a ba Iya.Da zan fita nace masa nagode, ya gai da anty Abida, ya ce zata ji.Sanan ya ce, ki saki jikinki don kada ta gane ba can kika je ba.Ina yin sallama iya tana zaune, cikin faduwar gaba na isa gurinta ina yi mata sannu, ta amsa fiska daure.Jikina yayi sanyi, nayi karfin halin cewa.Iya kin ganni sai yanzun?Tun da yaya ya kaini ya Aliyu bai zo ba har sai da na kwana, wai suna aikin wani case ne a hannun sa.Iya ta ce, kai ma dallah da jin haka sai nayi shiru, don na san zance na bai shiga Iya ba, na mika mata leda.Gashi inji matar ogan yaya din wai in baki tana gaida ke.Sai naga iya tayi murmushi ta girgiza kai, sanan ta ce an gode.Tun lokacin ban sami bakin magana ba sai daki da na shige na kwanta.Har yanzu haushin kaina nake ji, da na sani nabi umirnin miji na, gashi wanda naki don ita bata yarda ba, kuma nayi imani ko da mezan ran tse ba zata yarda da ni ba.Aliyu yayi nasarar kama dan fashin nan tare da taimakon masu layikan wato network na waya.Don yan fashin sunyi anfani da layika dabandaban, ya kama oga tare da wani yaronsa guda daya, jim kadan bayan an basu kudi sun saki yaron.Sun dauki hanyar kawo da a lamun zasu bar Kaduna ne, ya harbi tayarsu sanan ya harbi ogan a kafa.Sauran sun gudu shi kuma dayan tsayawar da yayi zai dauki kudin daga but din motar shi ya kawo Aliyu yayi nasarar kama shi.Wanan gaggarumar nasarar ta sa an karawa Aliyu girma daga ASP zuwa DSP, inda aka tara yan jaridu suka watsawa duniya. Duk kwanakin nan da aka dauka sam Aliyu baya shiga harka ta, in na gaida shi zai amsa amma ko kallo ban isheshi ba.Haka nan har daki na same shi don inyi masa murna kan karin girman da ya samu, amma sai ya ce dan Allah in fitar masa daga daki.Har Iya ta na ce mun Allah ya kara, tun da na ba da kaina ba loka cin da ya da ce ba ai yazama dole in jure wulakanci, bani da hujjar yin musu dole in yi shiru.Gadan gadan ya tada aikin gidan sa, da alamu ya sami kudi, ranar wata a Abar bai fita da wuri ba.Sai da suka shirya sanan sun fita hanya sanan ta soma yi masa fada me yasa yake yiwa marainiyar haka?Ya ce, bata jin magana ne, gara ma ki mata fada tun yanxun don ba zan dauki gaddama ba.Sunje iya nata santin gidan, ta ce gobe kawo kayanta ko?Aliyu ya ce, amma na dakin anjima zan kwasosu har da TV da su Radiyo, kema na sai miki TV.Ta rinka godiya.Washegari makota da yan uwa tare da matan yayan mu sukazo suka yi mun jere, da dddare kuma aka yi mun rakiya.Iya tayi mun fada sosai, kuma ta kara nanata mun cewa tunda ni na dage da son ya Aliyu lallai in lallaba halayanshi.Don bata so in kawo mata wani kara'i sananta sa mana Albarka tare da yi mana adu'a tagari.Kowa ya tafi sai ni daya, nayi sallar isha'i da shafa'i da wutiri, sanan nayi wanka, kwalliya sosai nayi duk da cewa ina cike da fargaba zai kalleni ko ba zai kalle ni ba.In ma ya kalleni ni me zai faru?Goma da wani abu naji ana kwankwasa kofar gidanmu.Da sauri naje na bude, shi daya ne kuma sanye da kakinsa na dan sanda, ke nan shi Abokanai ba zasu rakosa ba kamar kowane ango.Na amshi kayan hannunsa, jakace da leda tare da yi masa sannu da zuwa, ban zaci zai amsa ba, amma ga mamakina najini a jikinshi ya rumgumeni tsam.Sanan ya amsa da yauwa sannu.Ina makale a kafadar shi ya kulle gidan mu.Ina mamakin halin yayan mu sosai, tamkar bashine yake gaba dni ba.Abaki yayi ta bani kazar da ya shigo da ita tare da madarar holandia.Duk fargaba ya cika ni, amma haka naita sha har sai da yaga kamar zanyi amai, ya ce, kin koshi?Na ce eh.Munyi Sallah inda ya dafa kaina yayi mun addu'a.Bai bata lokaci ba gurin ibadar aure, wasanninsa sunyi mun nauyi.Don haka na soma rokonsa yayi hakuri, mai makon haka sai yaji kamar wata sarewa nake busa mashi.Nasha wahala a wanan daren nawa na farko, domin duk wani haushinsa sai da ya huce shi, sanan ya dawo yana tausaya min.Don shi da kanshi bai sai saita kanshi ba.Shi ya taima ka min na gyara kaina.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ba mu jima da kwanciya ba aka kira sallah, ya tafi masallaci nima nayi tawa sallar.Naso kwanciya amma sanin cewa zai fita da wuri yasa ni shiga kincin don hada abin kari.Lokacin da ya dawo zatonsa zai sameni a kwance, sai ya ganni kicin.Ji kawai nayi an rumgumeni ta baya.Na gaida shi ya amsa ya ce, naje nayi bacci don yasan ina jin bacci, na ce ba komai inya fita zan kwanta.Tare muka karya, sanan ya ce, inzo in cuda masa bayan sa tun ina jin kunya har na gyare don kuma yariga ya tsomani cikin ruwan.Tundaga ranar komai tare muke yi, wata masifafiyar soyaya yake nuna min har na dinga mamaki, sai dai ina gyaruwa wajen kwanciya.Don ya Aliyu mabukaci ne fiye da zatona, rana, safe, dare office ma sai ya dawo, haka nayi ta jurewa, saboda yana ririta ni kamar ya hadiye ni.Satin mu biyu nayi fari fiye da da, fatata ta goge, amma na rame.Dan Almajirin da ya so min shine ke min aike, kullun sai na saka mai abinda muka ci ya kai ma iya.Ranar da nacika sati biyu ranar iya tazo, dukinda nayi iya tana da ido, bayan na bata ruwa da abin tabawa sai na zauna kusa da ita ina cewa iya nayi kewarki sosai ke fa?Ta ce, Sadiya kewa ai ba a magana.Amman kuna zaune lafiya?Na ce lafiya lau, Iya.Yaya na ji dani, baki gani ba.Tace Sadiya ni sai naga kin rame, kina cin abinci kuwa?Na ce, ina ci mana.Aka kwankwasa gidan, na ce gashi nan ma.Da sauri naje na bude, ya manneni a jikin sa na

Chapter 7 of 25