Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shi yanzun idan sun iso kafin su isa gidsn malamin ya sauke yashige daki. Aliyu yakalli malamin. Allah yagafarta malam naga jama'ar wannan garin suna alhinin rabuwa dakai shin bazamu dan kara kwanakiba? Malam yakalli Aliyu ina da dalilin barin garinnan asubahin gobe.Aliyu yace Allah yasa haka shine mafi Alkairi. Malam yace ameen. Sai dai kai ina mamakin yanda kake son bina ban cika sakewa da mutaneba amma kai raina ya kwanta dakai amma daganinka ka taba zaman cikin birni? Aliy yace e duk cikin gari nayi rayuwata ban zauna gidaba, Malam yayi murmushi toh Aliyu sai dai kayi hakuri ina zaton bazanje dakaiba. Aliyu yace saboda me malam? Malam ya gyara tsayuwar wato malam Ali an sanar dani cewa duk inda zan shiga kada in shiga da mutumin cikin gari domin shine zai zamemin hadari cikin rayuwata. Aliyu yace Allah gafarta malam an fada maka kamannin shine munyi kama? Yace ko kusa an dai ce min zai shiga jikina sosai kuma zai cutar dani a rana irin ta gobe shiyasa duk lokacin dazan bar gari nakan barshi tun asubahi. Aliyu wanda ya kosa yaga isowar jami'an tsaro yace toh Alagafarta yaya zaka yarda da irin wannan kila ba gaskiya bane. Malam yadafa kafadar Aliyu inayimaka fata nagari Allah yasa zamu hadu wata rana amma wanda yafada min zancen nan yasha fadamin zantuka suna tabbata ina ji ajikina zamu sake haduwa da..... Jiniyar motar 'Yansanda ce tasa malam bai karasa zancenba sai Aliyu yaga malam ya daga kafada yasa gudu cikin azama da kwarewa Aliyu yaciro bindiga daga bayan wandasa ya harbi malam a kafa take malam yafadi amma burinshi yakai daki dan haka ya yunkura Aliyu yayi azama yacafkeshi. Mutanan gurin sun cika da mamaki harma suka taso da nufin jin ba'asi sai dai kafin suji dalili tuni yan sanda sunyi zobe a gurin sun kuma cafke wasu daga cikin makarraban malamin sannan an samu muggan makamai cikin kayan malamin da kudin kasar Amuruka(Dollar) da irin namu na gida. Mutanan unguwar suna ta al'ajabin lamarin yayinda wasu ke mamakin Aliyun wanda suka zata shima yana cikin mukarraban malam. Ta gidan lima suka bi mai masaukinsa,Aliyu yayi musu sallama yadauki yan kayan shi tare dayi masa alheri haka ma yen majalirarsu yatafi yabar su da labarinshi tare da jinjinawa aykin shi. Cikin wata hudu da aka damka aykin hannun Aliyu ya samu nasara ya fara bibiyar malamin tundaga maiduguri har kawo Kaduna sannan Zaria inda yayi nasara sakamakon haka ya samu lambar yabo tare da karin girma zuwa mataimakin kwamishina na can Abuja haka nan nasarar taja masa farin jini inda akayi ta haskashi gidajen talabijin. Ina kallon Iya tunda Aliyu yazo da batun aykin nan kullum cikin yimasa addu'a take tare dayawaita sadaka. Araina nace da da mahaifi sai Allah. Dubi duk haushinsa datakeji be hanata yimasa addu'ab. Inzanje aiki yanzu gida nake barin Sadiq sabida yana shan kamu. Iya tasani gaba tana min fada wata ranar Litinin na shirya zantapi aiki. Sadiya! Dan Allah shekarunki nawa? Nace me yafaru Iya? Tace fadamin. Nace 26 Tace dubi duk yanda kika koma ba wani ado ba kwalliyar da kikeyi ada, ki dage ko dan ki ba Gadanga haushi,amma kullum sai kina yawo kamar me takaba,Nace ni banima da kayan kwalliyar,tace inzaki dawo ki tsaya kasuwa ki saya in ma baki da kudi in baki,nace ina dashi a cikin account dina,tace to. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ina zaune bayan na sallami daliban ajina sun fita break nazabga tagumu ina tunanin zancen Iya gaskiya ta fadamin bazan tsaya in tsufar da kainaba tilas in nafita in shiga banki sannan in shiga kasuwa. Shigowar alert ne ya tsaida tunanina na dauka na duba kudi ne naira dubu saba'in sannan yaya ne ya turo min. Haushi da bakin ciki kamar inyi kuka don haushi. Dakyar nabari aka tashi na nufi banki na ciri kudin daya turomin naira dubu 70 na maida masa cikin account dinsa sannan naciri dubu 20 dan yin siyayyata acikin account dina. Nashiga cikin kasuwa nasiyo mai na perpect nasiya duk kayan shafawa, sannan nasai turaruka na har da kayan humra dan dakaina nake hada humrata nasai mayafai da takalma har atamfa na kara. Iya na gani tace ko kefa. Nanfa nashiga gayuna kafin wata daya na komo da farina da gayuna, sai dai ban maida kibata sosaiba, ba wanda zai ganni yazata ina da yara har 4. Wani abin dariya sai ga mutane sun soma yin sallama dani. Ranar wata juma'a ne sunan wata malamar da muke koyarwa tare nayi kyau cikin leshi mai ruwan madara ni kaina nasan nayi kyau taku dai dai nake yi na tsallaka titi zan hau abin hawa sai mota ta tsaya a gabana na waiwaya zanyi masifa sainaga yaya Usman ne cikin dariya na isa gurin shi. Yaya ashe kaine? Yace to na tsaya kafin inyi magana sai naga za'syi min masifa nayi dariya ka san mutane wai dasunga mutum ya tsaya sai suce zasu dauki mutum. Yace hakane sai ina? Nace nan Askulaye zani suna watace da muke koyarwa tare ta haihu. Yace muje. Nace a'a dakaje kada in batamaka lokaci yace hanya tace ni gaba naci don kurmin mashi zanje. Nace ok. Nashiga muka hau titi nace ina su Auntyna da su Ummul? Yace duk suna lfy shine bakya son fita da Sadiq koh? Nace shima ya saba da Iya baya son bina. Yace ya huta da shan rana. Nace wallahi. Naji cewa abokina yasamu karin girma kwanaki? Nabata rai ina ruwana. Yayi dariya da ruwanki mana koba dangantaka akwai su Kausar nace harsu duk na barmasa na yafesu. Yace bacin raine. Nace wai ya batun binciken? Yace ina kan binciken kiris yarage in kammala. Murna ta cikani cikin zakuwa nace kun gano kowane ne? Yace eh toh na dai yi nasarar gano cewa mutum dayane a abu uku Sulaiman din daya kawowa aboki gulma shine malamin makarantarku kuma shine Sadiya Abubakar mun gano hakan ne ta hanyar lambar MTN Din dayayi amfani da ita gurin cike form na account din da ya bude. Nace a'a duk lamba daya yayi amfani? Yace a'a daban daban ne sa'ar da muka ci duka na MTN ne kuma duk yayi musu rijista taimakon dayayi mana kenan. Nace Alhamdulillah. Muka danyi shiru nawasu yan dakiku sai Usman yayi gyaran murya yace, Sadiya! Nadube shi irin kallon dayayimin yasa gabana faduwa nayi ta maza nadauke kaina. In tambayeki mana? Nace eh...ina...jinka. Nafada cikin in ina yace in abokina yaji gaskiyar batun nasan zaku sasanta koh? Nakalleshi da sauri nan take raina yabaci na sunkuyar da kaina yaya Usman dan Allah na roke ka kadaina yimin zancen yaya nayi rantsuwa bazanyi kaffara ba,Muka danyi shiru na wani lokaci,sannna yasake yin 'yar gyaran murya "Sadiya nasan kisoma tsayawa da masu sonki ko?" Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Nadubeshi "banajin zan bata lilacina gurin kula su,domin al'amarinsu sai su." Yayi dan murmushi "karkiyi kudin goro" Nan nanunamasa layin muka shiga,gabana yana ta faduwa sabida irin kallon da yaya Usaman yake yimin. Nace ga gidannan.ya tsaya ya dubeni. "Zan dawo in daukeki" Nace a'a kayi hakuri daga nan zanwuce wata unguwar,nagode. Yace "ina zaki!" Nadubeshi "Gidan kawata" Yace "Ok! Shikenan, kila zan dawo nanda anjima inna zaton zamu tattauna wata magama mai muhummanci Nace to sai kazo. Jiki babu karfi nashiga gidan sunan,duk da irin shewa da wasa da dariya da abokan aikina keyi ni nakasa ko murmushi. Malama Bilkisu ta dubeni tace wai Malaman sadiya kodai baki da lafiyane?nai dan yake kaina ciwo yake Sukayimin sannu mai jegon har dacewa ke kam tunda kika haihu shi kenan kika zama sarkin ciwo. Nace aykam gashi nan na kasa maida jikina. Adaddape nayi minti 40 agidan nafito na nufi gidan Ayshata sai taganni kamar an jeho ni ta tashi tare dapadan lfy? Nace Uhm wata sabuwace tasamu. Tace kuma, to zauna kisha ruwa kin taki sa'a yau alalar gwangwani nayi. Naja tsaki ni wallahi yau ko nama kikayi zalla bana zaton zan iya ci. Tace meyafaru? Nan na bata lbrn duk yanda mukayi da yaya Usman itama dai ta damu amma tace balallai yace yana sonaba wai kila zuciya tace kawai ta zargi hakan nace toh shikenan. Sai bayan magariba na yimata sallama ta rako ni na hau mashin ina hanya naji wayata na ruri, ina dagawa iya ta rufe ni da fada ina natsaya ga Sadiq yana ta ihu? Nace gidan Aysha nawuce gani nan tafe. Ina shiga yaya naci karo dashi zai fito dashi a kafada yana ta kuka, duk da darene na raya cewa fuskar shi a daure take ranshi kuma a bace yake, nashige nazauna a falo ina ninke mayafina sai gashi. Kin tafi yawon banzanki kin bar yaro yana ta kuka ko? Ina kikaje? Naki ko dubanshi nagama ninke mayafina na mike zan shiga uwar daki yace baki amshe shiba yana kuka? Iya ta sallame sallah tace ki daukeshi mana ya jima yana kuka, nace to. Saida nakai mayafina na ajiye sannan nafito fuska daure na isa gurinshi namika hannu cikin harara yabani shi sannan yayi kwafa. Kisani in zaki tafi yawon banzanki ki daina ajiye min yaro a gisa yana kuka banda shashanci me zai sa mace tafita har magriba. Na zaci acikin zuciya nake magana ashe tafito fili ina ruwana da kukan shi zan kiyin harkar gabana ne saboda shi? Sai muryar Yaya naji yace Iyee haka kikace? Nayi shiru. Tozan dauki yarona in hada shi da yan uwansa in yaso ke kije kiyi ta gantalinki. Nazauna nasoma bashi nono ina jijjiga nace Tabdi Ay wallahu bazan bada dana ba koh gaban Alkali Za'a,Iya dai tana jin mu bata tankaba yace basai Alkaliba ahannunki zan amshe shi kicika baki kigani. Nakalli iya don na soma fargabar zantukanshi tsaf zai iya,Nace iya kifada masa yafitga harkata yadaina cemin ina gantali. Iya tace ki kyaleshi yazo yadauki dan nasa gantali kuwa ai kin isa yine. Yatausasa murya Iya kidena dauremata gindi tanamin rashin kunya. Yakalleni. Zan targadaki in kika yi wasa. Namike nashige daki shi kuma yawuce.......Zandakata a nan, acigaba da hakuri dani. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Darajar Yayana4-03 Posted by ANaM Dorayi on 10:47 PM, 13-Apr-16 Under: DARAJAR 'YA'YANA _________________NA ___________HALIMA K/MASHI Mama natawasan ruwa a karamin fanfon cikin bandakin,Khausar ta kalleshi cikin fargaba amma bata tashi daga inda takeba,jiratake yafara yimata fada kamar yanda in Mujidat taci Zalinta sanna tayimata karya gurin Abbanta cewa Tayi kaza-tayi kaza, yayi mata fada amma sai taga yamaida kofar ya rufe kuma yamaida mukullin,dan tajiyo kara,sabon kuka tasoma Mama ta juyo tan kallonta. Cikin zafin rai Aliyu Yayi dakin Mujidat,turo kofar dayayi da karfi shiyasa ta tura wayar a karkashin pillow sanna ta mike zubur, ya kalli pillon sannan ya kalleta,rashin gaskiya ya bayyana fuskarta. Sanna tace, "My Dear sannu da zuwa." Ya dauke kansa daga kallonta sannnan yace, "ina yarana?" Gabanta yabadi sakamakon tinowa datayi ta kullesu a bandaki,cikin inina tace sun..suna falo kokuma dakinsu bari inkirasu,yadan kauce ta wuce shikuma yabi bayanta. Cikin takun isa tashiga cikin dakin sannna tafito tace, "ina yarannan suka shiga?" Nahanasu Khausar yawonnan amma sunki,bari induba gidan maman Markus, Aliyu yace,"kinsan inda suke dan haka nunamin" Tace, "ni bansab inda suka shigabafa a falo na barsu" Yace, "yaya basu tafi da yaronkiba sai sukadai" Tace, "Amma dai kasan Abdul bashi yarda dakowa" Yace, "bansaniba, kin rufemin yara a toilet?" Ta zaro ido "suna Toilet?" Ta nufi bandakin da sassarfa,Aliyu yabi bayanta,ta bude mukullin hannunta na rawa,zunmbur Khausar ta mike hannunta na rawa tana cewa yi hakuri Aunty nadena kar ki dokeni. Tace zonan Khausar me kukeyi a nan? Tadaga Al'amin tana cigaba da cewa, "haba Khausar".... Aliyu yana tsaye cikin takaici da bakin ciki, domin ko karamin yaro zai fahimci cewA kawo yarantayi ta rufe amma tana nema ta raina masa hankli. Sai da tayiwa yaran wanka tana cewa haba yarana karku kara ba'a wasa a toilet. Saida tagama musu wankan suna fitowa zata fito ya hankada ciki ta koma da baya tafadi,ya maida kofar ya kulle sannan ya zare mukullin yabi yaran zuwa dakinsu, yazauna bakin gado yana kallonsu.kausar ta dakko musu kaya,hawaye ke zuba daga idanunshi, yaranshi duk sun lalace ba wata cikakkiyar tsafta,yaran da mutane ungwa suke labarinsu a makaranta suke amsar kyautuna sabida tsafta dubesu duk sunyi baki, gashin su khausar ya lalace, kayansu duka bakula. A fiili yace, "Sadiya kin tarwatsamu," yasake kallon yaran yaga suna kallonshi yamike yaje ya hadasu ya rungume yana cewa, "Kuyi hakuri yarana, ba laifina bane laifin mamankune" sunfi minti daya haka sannan ya sakesu yace, "inkaiku gurin wasan yar ko? Skace, "e" Yace, "to,kokuma kuna jin yunwane." Nanma sukace, "e" Yace, "to bari inyi wank" Yace, "ina sababbin kayan dana siyo muku." Khausar tace, "suna dakin anty" Yatafi dakin ya hau bincike har ya binciko kayan yazo yasamusu,sannan shima yaje yayi wanka yafito cikin wani yadi mara nauyi me ruwab siminti, sannan takalmin da hular wadanda suka dace, har zai wuce sai yaleka dakinta, har yanzun danta na bacci, yadaga fillon sai ga waya BB ya dakko ya zura a aljihu yafice ya kwashi yaran,yanajinta tana buga kofa tanacewa, "My Dear dan Allah ka budeni." Yace, "kiji abinda sukaji" Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 yafice yazuba yaranshi a mota suka wuce. Ranar dai yaran sunji dadi duk da Khausar ta kasa walwala amma fuskarta a sake alamar taji dadi, yaymusu siyayya sosai Basu dawo gidanba sai da yayi sallar isha. Yasamu Abdul yatashi yayi kashi da fitsari a gado da kasa, yaje ya budeta tayi kuka ta gaji dan tana jiyo kukan danta badamar ta je gunsa, tasakarmasa harara sannan taja tsaki ta wuce, dariya yayi don turamata haushi.yana ta re da yaransa har sukai bacci sanna yaciri wayar yasoma binciki amma hakan ya faskara saboda security datsa, yamike yatafi dakinta yatara da ita tana waya da karamar wayar da kullum yake tsammanin ita kadai ke gareta ya tatsuramata ido dan son fahimtar da wa take wayar amma sai tayi sallma tare sa cewa, "momyi sai anjima." Ya dago ya nuna mata wayarta dake hannunsa yace, "wannan wayar waye?" Tace, "tawace" cikin gadara yace, "ina kika samu kudin siyan wannan wayar dubu sittin?" Gabanta ya fadi amma sai ta dake tace, "ni ba haka na siyaba second hand na siya." Yace, "gurin wa kika siya?" Tace, "gurin kawata." "Wacece kawar taki?" Tace, "Azima" Nawa kika siya? Tace, "dubu ashirin" Yace, "a ina kika samu kudin?" Cikin kosawa tare da daga murya tace, "Auncle yabani, Wai sata nayi da kasani a gaba da wadannan tanbayoyin?" Ya mika mata, "ciremin scurity" Ta amsa ta cire tana kokarin shiga wasu guraren ta goge wasu abubuwan ya fisge wayar yafita, ta biyoshi tana cewa ni kabani wayata ba kai kaseminba, Afalo yazauna sanna ya kalleta kallon zargi, "karki karso min nan, inbadan kinsan baki da gaskiyaba menen dan mijinki yadauki wayarki?" Tace, "nadamune dan zaka duba wayata meye a ciki? Kayi ta dubawa nidai nace kabani a buna tinda bakaine kaseminba" Baisake tankamataba, yayi iya bincikensa baiga wani abu ba amma cikin inbox dinta na message yaga wani sako da yadauki hankalinsa cewa akayi, "Malama ki aikomin da cikon kudin aikina inba hakaba zanyi miki rashin mutunc daga Jamilu." Yaduba ranar da aka turo sakon ya lissafa kwana tara kenan,ya tura sakon zuwa wayarshi sannan ya aje wayar a hannun kujera tazo ta dauka ta wuce. sam bata tinanin wannan sakon damuwarta karyashiga group dinsu yaga abinda sukeyi,dan in hirar da sukeyi da mazane tasan bazai ganiba tinda tana gogewa shikuma bai tsaya wani shiga group ba. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Sunfi kwana uku suna gaba,tafita lamarinshi da yayanshi,shinma yafita shirginta,sai hidimarsa yake da yaransa.Nazari tayi taga suke cutuwa,don haka ta sauke girmankai tare da samunshi a dakinshi tsakar dare inda tabashi hakuri,tare da yimasa alkawarin bazata karaba. Cikin kwanakin da suka biyo baya tana kokarin dannar zuciyarta dan ta kyutatawa yaran,sabida ubansu ya yarda ta canja,saidai yaran sunki sakin jiki da ita, data lura yasaki jikin sai takoma halinta,yanzu bata rufesu a bandaki saidai duka kamar jakuna, dan kuskure kadan na yaro sai takama tayita duka. Cikin haka wata ranara litinin su Khausar sun dawo daga makaranta dauke da yunwa,sunfi minti talatin sannan ta tashi daga chatting din tabasu abinci,wanda ko Al'amin sai yacinye. Kausar tace, "Anti Wannan fa bazai ishemuba," Ta watso mata wata harara ta nufi dakinta tana cewa, "Dama ni nace ku koshine?" Khausar ta Mika musu tace, "kuci," sun cinye Amma basu koshiba, Don haka khausar tace kibari in ta dan dade zanje in debo muku nima in debo nawa,Don ka dayushe dama idan basu koshiba takan dan lababa ta debomusu. Kamar kullum ta taka kujera tana cikin zubawa sai taji kamar motsin Auntynsu ashe Mamace,tana kokarin sakkowa kujerara ta gurde, Kausar ta fado, shi kuma plate din yayi sama sai yafada kan wasu plates din 'yan uwanshi na tangaran,nanfa kakejin tartsatsi yana tashi,da gudu Mujidat ta fito. Khausar ta mike jiki na bari tsoma cewa , "Anty yi hakuri tana kka." Mujidat tace, "ok! Allah yakamaki dama kece me satar abinci kullum inna tanbaya kice bakebace ko?" Cikin rawar muraya khausar tace, "zasu karane,ni ko cima banyiba." Tace, "Ina ruwana,dole inzaneku yau, kizo ki gyaramin kitchen bari innemo wayar wuta." Ai tana juyawa khausar tafita da gudu inda tadau takalmansu suka gudu,Mujidat tafito bata gansuba,tace "oh! Kunguduko?zaku dawone." Duk da cewa barikin 'yan sanda da tsaro amma sai Allah yakauda idon kowa basu gansuba har suka fice. Al'amen yace, "yaya Khausar ina zamuje? Ko mutafi Office grin Baba?" Khausar tace, "inmunje zai dawo damune ko Yayi mata fada,in Yayi tafiyrs Sai ta dakemu," Al'amin yace, "emana , kawai mu tafi gurin Momy." Khausar tace, "zamu iyane? Kadunafa?" Mama tace, "nima zanje Momy kinji Yaya Khausar" Khausar tace, "to mama zaki iya Zuwa a kasa?" Mama tace e Almen yace, "in tagaji sai ki goyata" Khausar tace, "muje to kila mugane.' Sunyi ta zagaye cikin garin Abuja har duhun Magriba yasoma shigowa,inda suka Isa kusa da wani Store na saida kayan shaye shaye na zamani, suna son su sha ruwa, ga yunwa,in mama tayi kuka sai Khausar tace, "yi shiru mun kusa" Khausar ta Isa gurin wani mutumi dake tsaye yana shan kankanar gwangwani, tace, "Baba dan Allah kasammana ruwa." Yakalleta ya kalli su Mama yace, "kai inazaku?" Khausar tace, "Kaduna" Yace, "Inna zuwa" Yaje yafito da ruwan gora yabasu suka sha sannan yakirasu gefe yanayimusu tanbayoyi har mutane suka taru,nanfa akayi ta shawarwari wasu suna Cewa akaisu makaranarsu inyaso su can sai su kira iyayensu,tunda ansan makarantar,jin haka yasa Khausar tashiga kuka tana cewa, "Kutaimakamana wallahi antynmu zata kashemu,kukaimu kadna gurin Momynmu." Suma su Al'amin kuka sukeyi dan haka sai sukace, "tinda shi wanna daya saimusu ruwa direban motane sai yatafi dasu Kadunan indai sunsan unguwarsu." Dayake daga gurin babu nisa zuwa tasha dan haka sai suka tafi.. Mujidat bata tina da cewa yarannan basa gidanba saida Aliyu yakirata a waya yace ta shirya yarannan zaizo yakaisu Islamiyyar dayayi musu register,firgigit ta mike tana cewa ai saita dokesu babu fashi.saidai me?tayi Neman duniya cikin gidan da makota basanan,nanfa hankalinta ya tashi,makota suka firfito,kafin wani lokaci ankarade rukuninsu da neman yaran,amma babu wanda yagansu, saidai masu cewa tabbas sungansu da takalman makaranta a hannusu,wasu kuma suce da kayan makaranta. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Mujidat taci kuka ta koshi,gashi ta kasa kiran babansu dan tsoro.makotansu kuwa da suka San abin da takeyi wa yaran cewa suke Allah yakara, saidai munafukn dake bin bayanta ne ke tayata damuwa. Yana shirin zuwa don kaisu sabuwar islamiyyar da yasasu saiga wayar makocins wai bafa aga 'ya'yansaba, cikin tashin hankali yanufo gidan.Sai yasamu gida dankam da mutne,ya kalli Mujidat "Ina Yayana?" Tace, "bangasuba sunyi barnane a kitchen suka gudu." Baice kalaba ya nufi gidan,sannan yafito yakira "yansanda suzo gidan shi,sanna yace kowa yatafi yagode. Kafin wani lokaci "Yansanda sun karaso nan yasa sukama Mujidat sai ta fadi inda takaimasa yara. Cikin dare 'yansanda sai faman neman yara suke, duk inda yakamat asanar an sanar, hanklin Aliyu yatashi Karshe.karshe yakira Usman yafada masa,amma yace yabar zancen a tsakaninsu dan bayason su Iya suji,Usman yace Allah ya bayyanasu. Abu kamar wasa har cikindare babu labarin yaran. Daidai wanna lokacin suna can akan hanya,inda direban yasasu a bayan Mota yakashe kujer daya kusa da wata mata inda yace "Don Allah ta lurar masa dasu," duk da tsare motocin da 'yansanda sukeyi suna haskawa sam babu wanda yagano yaran,shiko direban bemasan yaran ake nemaba balle yayi wani bayani. Sunyi isowar dare,don haka yagama da fasinger yanufi gidansa da yaran,wadanda harsunyi bacci, matarsa tanada fahimta,baisha wahalaba wajen fahimtar da itaba, nan yaran suka kwana. Washgri akayi Tayi musu tanbayar Sunan unguwar ta momynsu Amma suka kasa tunawa,gidan me unguwarsu ba nisa,don haka sai yaje dasu gurinsa,suma dai sunyi iya tanbayoyinsu ba'aganeba,Sai matar me ungwar tabasu shawara suje gidan TV da yaran,aikuwa basuyi kasa agwiwaba suka nufi gidan DITV inda ake gabatar da wani shiri na gari ya waye. Daidai wanna lokcin inna zaune agaban TV inna kallon shirin domin dama baya wuceni,innayi innashan Tea. Iyama na son shirin sosai,don haka tana ta kokari tafito daga kitchen ta iso.Kamar daga sama sai akace ga wasu bayinAllah suna bada Cigiyar iyayen wadannan Yara, mai sanarwar yafada, ganin an hasko fuskar Khausar cikin daga Murya nace Iya Iya zo kigani,da tuntube tafita tana fadin lafiya? Itama nan tazauna dabar.daidai lokacin ana tanbayrsu sunayensu suka fada,dan Jaridar ya haska Khausar "Yarina yakikace Sunan ki?" Tace, "Khausar Aliyu Tukur Hadeja" "Daga ina?" "Abuja" "Ina Zaku?" "Kaduna gurin momynmu" "To can Abujan gurin wa kuke?" "Gurin antynmu" "Ina bbanku?" "Yana gurin aiki." "Me akayi muku zaku dawo gurin momynku?" "Dukanmu Auntynmu keyi,kuma bata bamu abinci muna kosh,jiyama naje zankaro aboye batasaniba,zan krawa su Momy dama ni banciba duka nabarmusu,shine nafadi,dataji karar fashewar abu tafito,shine taje dakko wayar wuta sai muka fito Muka kwashi takalmanmu Muka gudu." Yace, "to kinsa unguwar da momynku take?" "Da nasani yanzu namanta." "To yasunan mamanku?" "Sadiya" "Babankufa?" "Aliyu Tukur Hadeja" "Meye sana'arsa?" Tace, "dansadane" Nantake dan jaridar yace badai Aliyu Tukur din danasaniba,in shine kuwa ai sanannene,yataba rike kakakin rindinar yansanda alokacin yana ASP. Mai unguwa yace shekarun baya ko. Ai tini na jike shrkaf da gumi da hawaye har da majina, yaranane wadannna ? Sai ga Habu yashigo da sauri yace Aunty Ku kunna TV,Sai yasamemu cikin kuka,yace iya kutaso muje gidan me unguwa,na dauki lanbar wayar dayabayar, gidan sa kuma hayine layin yandinki,dakyar namike wayata tana ta ringi amma nakasa dagata,nasan kawyenane dasukaga yaran,tin kafin mutafi mkota dai shigowa suke suna mana jaje gami da barka da arziki. Munshiga gidan,sashin matar me unguwar, Mama tana wasa,khausar da Al'amin suna ta zantuka kasakasa,mukayi sallama yaran suka dubemu, da karfi kausar tace Momy! Se rige rigen tahowa gurina,na hadasu su ukun na rungumesu jikina,inna kuka suma suna kka, duk mtanen gurin suma kuka suke.nadauki Mama inna kallonta,nadubi Iya cikin kunci Nace, "dubi yarana yanda suka llce," Iya tace, "su da Allah sun cuci Kansu,menene riba don ka cuci karamin yaro?" Nandai akayi abin dayakamata muka dauki yara muka nufi gida. Gidan cike da makota Sai barka da arziki akeyimana,Allah yasa sunfada hannu nagari.har lanbar direban na karba dan yimasa godiya ta musamman sabida taimakon dayayimana. Tini Habu yafesawa Yaya cewa abga su Khausar anan Kaduna.Habu yabashi labarin komai,shi kansa yasan tinda yarannna sukazo gurin iya dole ya hakura dasu,amma yaji dadin ganinsu.yanufi office dinsu yasa asaki Mujidat,ta fito tayi wujiga wijiga, yace to bafa gidanshiba sai ta nemi gurin zuwa,tace ina Abdul? Yace ai ba yaronkibane yaronane na amshi dana. Tace, "kana zaton dan ka boyemin Yaro zanki inje infadawa iyayenka? ai dole su Sani." Yace, "kekisani,saidai kisani zakikoma Kadunane bayan kinkoma gidan Ubanki Lagos." Aikuwa yasa aka kaita har garin da 'yan kayanta,ko gani Abdul din ya hana tayi,yakaishi gidan wani abokinsa a Asokoro.Mujidat ta jinjinawa wulakancin da Aliyu Yayi mata,Amma tace indai itace yaci Bashi,sannna tinda be saketaba da sauki. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ya nufo kaduna cikin fargaba. Nikam na tsefe kan yarana na wanne,akaje akayi musu kitso nayi musu lalle. Munsha labarin irin wuyar da suka sha a baki Khausar ni da iya, aikuwa munsha kuka sabida tausayinsu. Karfe uku ina zaune da 'Ya'yana cikin farinciki inna yanke musu farce,Mama nakeyiwa magama yiwa sauran.Khausar na dauke da Sadiq tanayimasa wasa tace "Momy Sadiq dinki wallahi dariya Yake yimin damun hada ido ya sannine?" Nace, "kullum sainabashi labarinku, yasanku dukkanku...."Sallamar yayace ya katsemu,sainaga Khausar ta mike da gudu ta nufi daki Al'amin ma yabita,Mamace kawai naga ta nufi Yaya tanamai Oyoyo oyoyo,na hade raina tamkar zan saki kuka,sanna na kauda kai nadauki wayata inna latsawa. Yanufi cikin daki gurin iya, su Khausar duk sun makale a bayanta tana Cewa, "lafiya kuke boyewa?" Sai kuwa Yaya Yayi sallama,tsaki Iya taja takasa amsa sallamar, yazauna tare da sunkuyar dakai yace, "ina yini" Ta kauda kai tace, "lafiya," Yace, "nazone inbada hakuri kan laifin danasan za'a gani nawa,duk dacewa bansan fitarsuna tinda ni bama na gida,laifin Mujidat ne kuma nayi mata hukunci." Iya tace, "can da matsalarku, sai dai abinda zanfadamaka yarannan sunzo kenan,kuma abin da kukayi musu Ku da Allahnku," Aliyu yace, "Dama ni bawai zan Koma dasubane." Iya tace, "ai nazaci takardara sammaci kazo kawomana." Ya mike yasake fadin aymin afuwa. Ya dubi Khausar, "bazaku gaisheniba?" Tace, "ina wuni Abba," Almin kuwa cewa Yayi, "mudai bazamu bikaba," Yace dama badaku zan tafiba. Ya iso gurin su Khausar ya dauki Sadiq yafita. Bai zaci zai samu sauki a guri Iyaba,yasandai damuwar dama kar yakuma daukan yaran, kuma dama ya yanke hukuncin barinsu fishintama na yaune. Yakira Usaman a waya suka gaisa samasama yace ,"Aboki kana gidane in iso ? Yunwa nake ji,gidan su Iya kuma babu fuska." Usaman yayi 'yar Dariya sannnan yace, "ka isa gidan zan sameka a can." Aliyu yace, "kayi nisane?" "Inna Office din 'yansanda na nan unguwar." Aliyu yace, "lafiya me kake a gurin?" Usam yace, "wani dan case ne." Aliyu yace, "shine bazaka sanar daniba, bari inzo." Ciki yakoma yamaida Sadiq, a cinyata ya ajiyeshi ya fita,yana Isa office yansanda suka soma kamewa suna sara masa, Oga yana ciki. Agaban DPO yasmu yaron tare da Usama, DPO ya mike ya kame sannan suka gaisa. Aliyu ya kalli Usman, "Yaya, me yafaru aboki," Usaman yace, "irin yarannanne masu bude account da Sunan mutane su kullamusu sharri." Aliyu yace, "to shi wa yayi?" Usma yace, "shine yayiwa Sadiya," Aliyu yace cikin sauri, "wace Sadiya," Usman yace,"wadda nake neman aurenta." Kan Aliyu ya kulle yace, "dama zakayi aure?" Yace, "Eh,bamuyi zancen dakaiba ko?" Ya kalli yaron, "kasan Wannan?"Yanuna masa Aliyu, yaron yace, "a'a," Daga nan Usman ya kalli DPO; "yanzu ni zan tafi " Aliyu ya zauna, "bangane zaka tafiba, wai yaya case din yafaru?"Nan aka umarci Jamilu yayi bayani kamar yanda Yayi dazu. Jamilu yace, "nidai wani yarone kanin Aunty Ramatu ya kirani inzo zanyiwa wata Auntynsu wani aiki,dama yana zuwa Cafe dinmu yana Browsing, danazo sai tace inbudemata wasu account guda biyu,zata yiwa kishiyarta sharri, kawai Sai na yarda sabida ta yarda zata bani Dubu5,nikuma dama inna neman dubu 5 din sabida zanse JAMB Form dan shiga Jami'a.shine nayi mata har yau kuma bata cikamin dubu biyunba,sunma tashi daga garin." Aliyu ya dinga kallon Jamilu tamkar yanason Yayi tajin labarin kokuma labarin ya burgeshi. Usman yace Jamilu sakamakon wanna hada Chat din danayi nafada maka kasan aure yarabu? karaba uwa da 'Ya'yanta? yanuna Aliyu Kaga mijinsu nan,wadda kayiwa sharrin da wadda tasaka kayi aikin." Mamaki Yakama DOP yace, "Dama abin yafaru ne a gidan Oga?" Aliyu dai hannu a cikin aljihunsa yarasa me zaice, Jamilu kuwa zubewa Yayi gban Aliyu yana rokonshi cewa a yafemasa, shi dama wannanne karo na farko da yasoma kuma bazai karba.Aliyu yamike yakalli Jamilu, "Ayimaka hukunci daidai da lefinka sabida masu hali irin naka." Har waje DPO ya rako Aliyu, sam Yakasa magana sai zufa yakeyi, zuciyarshi

Chapter 22 of 25