Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kai ku Asibiti." ta yatsine baki "kin sanar da mjnki?" nace, a'a kin San Iya tana nan ba dama in masa zancen ki.' ta dauko wayarta tana cewa, "ina ruwana da Mamansa taji. Layinsama a kashe yake.' tayi tsaki ta jefar da Wayar, Ni dai na fice na kama aiki na raina bace, ban cika ganin laifinta ba Dan shine musabbabin komai. Da zamu Asibiti na sauke Iya a gida na wuce dasu. An duba su ance duk suna lfy, muka tsaya kasuwa na siya abubuwan da basu da shi,sannan muka nufo gida. Tsakiyar gado na zauna sannan na soma Kiran layin mijina, bugu biyu ya daga, nayi Sallama ya amsa tare da cewa. "Yaya na jiki cool da yawa?" Na ce, 'Yaya budurwarka ta haihu." budurwata kuma? Ya fada cikin sauri. Na ce, eh Mujidat danta yana nan namiji......zandakata a anan zuwa wani lokacin kuma,fatan zaku kara hakuri dani Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Darajar Yayana2-03 Posted by ANaM Dorayi on 04:31 PM, 23-Mar-16 Under: DARAJAR 'YA'YANA _________________NA ___________HALIMA K/MASHI Ta soma kwalla a kwai su, amma sun zo sun kasa kamo barawon.Ya ce, to daga sun zo ne zasu kamo barawo kamar suna da Allahn musuru?Ina ganin ki hakura kawai in ba a kwai wanda kike zargi ba.Ta ce, cikin jaka ta yake a dakin na, ni na tafigidan kawata, mama ta tana shigowa sai kanena sun ce kuma basu ga wanda ya shigo cikin dakin ba.Aliyu ya tabe baki.Shirme kenan, sai ki hakura kawai.Ta mike tana share hawaye, shi ke nan nagode.Sanan ta tafi.,har ya gama shirin sa tsaf zai tafi sai ga wayar commissioner yana neman sa yana isa aka dan ka wani aiki a hannunsa.Dole ya fasa tafiya ba don ranshi ya so ba.Washe gari ranar goma dai dai dawowar shi ke nan daga wurin motsa jikin da yaso xuwajiya hakan bata samu ba sai yau. Waya ta buga daga bakin gate ne, mai gadi ya ce, yallabai bukur jiya ce ta dawo.Cikin damuwa take oga.Dan sanda ya kara da haka ne don don tunanin cewa in ta fito yau ma zai sami kwaleliyar dubu daya tamkar jiya.Aliyu ya ce ka ce mata zan fita ne ta dawo da yamma, bata jin dadin haka ba amma me nema yana tare da samu, don haka sai ta hakura ta tafi.A ranar ta saka hotonta da ainihin sunanta aaccount din da ta bude kuma Aliyu ya amshia botar ta.Da yammancin ranar bata zo ba domin ta dana sabon shairi, sha biyu zuwa karfe dayan dare ta san lokacin da take ganin shi a online ne, don haka sai ta hau.Cikin sa'a yana nan ta soma da tura masa hotonta a inbox, yana ganin hoton ya gane ta.Ya ce, oh, daman ke ce kika yi mun basaja don in karbeki?Ta ce, naga in ba haka nayi ba ba za ka kulani ba.Kuma ina da matsala kai ne nake ganin zaka magance mun.Aliyu ya ce matsalar me?Ta ce, kafin in fada maka matsalar tawa, ka fara kallon hotunan nan.Aliyu ya ce, to.Duk a tunanin sa matsalar ta ta shafi aikin sa ne.Matsalar farko sassan kirjinta ne, haka ta turo gabobi duk tsiraicinta ba inda ta babu inda ta rage.Ya ce me nene ma'anar hakan?Ta ce, ka duba hotunan da kyau?Ya ce, eh.Dama ina so ne ka gani da kyau don in nayi maka saimatsalar tazo da sauki, domin tun ranar da na ganka na haukace da sonka.Ka taimake ni.Aliyu ya rasa me zaice don ta kaici da bakin ciki, sai kawai yayi blocking din ta amma mehotunan da ta turo sun hau cikin hotunanshi.Ya dinga bin su da dai dai yana sharewa, amma da yazo kan na farkon na kirinta sai ya tsaya yana ci gaba da kallon hoton har ma ya kasa goge shi.Cikin daren tunaninsa ya soma gurbacewa, da safe karfe shida wayar bakin gate ta shigo, bai dauka ba don lokacin bacci yana kanshi.Don baiyi wani bacci ba can kuma a bakin gate din shi kanshi mai gadin yana son wanan bakuwar ta samu shiga sabo da ya san in ta fito zai samu wani abu.Ya ce, madan me yasa jiya da yace ki dawo baki dawo ba?Ta lallaba jakarta ta ciro yan dubu guda biyu, gashi kasa kati.Da sauri ya amsa ya tura a aljihu kamar yana tsoron kada wani ya amshe masa, ko kuma ita ta ce ta fasa.Ya shiga zuba mata godiya, ta ce, tunda jiyaya ce na dawo ban dawo ba me zai hana in shiga kawa yanzu?Dan sandan ya zaro ido oga yana da ka'da sai dai in yayi fada zaki fiar da ni?Tayi masa fari da idanunta, kada ka damu inyayi fadan zan wanke ka.Tun da shiga falon ta ke ta kalle kalle, falon nashi ya birgeta duk da cewa ba wani kayanalatu ya zuba ba.Ta zauna kan kujera ta bude jakarta ta dauko hoda da turare ta sake gyarawa.Sanan ta cire rigar sanyin dake jikinta saura singilrti, ta ajiye mayafinta ta gyara gashin dokin dake kanta.Sanan ta dauki wayarta ta soma kiran wayar ne ya tasheshi, wata isaka yaji tana kadawa tamkar za ayi ruwa.Windo ya nufa ya daga labule kamar yanda ya zata, hadari ne, yaji dadin haka ko don yakara mikewa.Wayar ta sake kacamewa da ruri, yana dubawa yaga number yarinyar, tsaki ya ja tare da yin jifa da wayar kan katifar sa.Ya bude kofar nifinsa yaje kicin ya samu abin tabawa, cak ya tsaya sabo da ganin yarinyar gaban shi ya soma faduwa, lokacin da zuciyar shi ke tuno mashi hoton.Yayi karfin halin daure fuska, sanan ya ce, da izinin wa kika shigo min gida?Ta mike ta nufosahi, da izininka masoyi na, ka manta ka ce in dawo jiya? Ban sami dama ba shine na dawo yau.Ya ce, to fita a gidan nan fita, ya nuna mata hanyar waje.Ta zauna a hannun kujerar dake kusa da ita,da ma ka bari mun fahinci juna.Ya juya ya shiga dakinsa a fusace, durowa yaje ya dauko bindiga nufinsa yayi mata barazana.Ya fito da ita ya saita ta, kwashi kayanki ki fita.Hakika gabanta ya fadi don bindiga ko makerinta yana shakarta.Amma duk da haka sai ta jajirce, ta runtse ido hawaye suka soma zuba,zanfi so ka kasheni feye da ka barni a raye amma baka amshi soyayyata ba.Zanyi alfahari in ka kashe ni da kanka, kuma kacewa jami'an tsaro ni na yafe maka ko sun tsinci gawata a gidanka.Aliyu ya ce, muje ki fita ni bana son jin komai daga bakinki.Sun isa bakin falo Ruwa ya tsuge mai karfi wanda hakan ya sa ya kyale ta.Ya shiga daki ya adana bindigar, sanan ya hau katifar sa ya kwanta. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Gurbataciyar zuciyar sa ta shiga kitsa masa wasu abubuwa, dauko wayar sa yayi yana kallon hoton da yarinyar ta turo masa.Cikin jikinsa sanyi yake ratsawa na ruwan dake sauka.Mujidat turo kofar dakin ta shigo, kasa magana yayi lokacin da ya waiwayo yaga ta raba jikinta da tufafi.Yayi ta maza ya daka mata tsawa, mai makon ta fita sai ta nufo gurinsa da gudu ta fada masa.Shedaniyar shu'uma ce yarinyar, don haka bata samu matsala sosai ba gurin amincewa da gayyatar da tayi masa, zuwa ga fadawa tafkin zunubin shedan ya sake kawata abin ga zuciyar Aliyu. Har yake ganin haram ta shigeshi fiye da halalinsa.Mujidat ta amince Aliyu ne irin mijin da take so ta samu.Duk runtsi ba zata barshi ba, sai da kanwa takar tsami kwannafi ya kwanta.Aliyu ya shiga jin cewa bai kyau ta ba.Na dama ta shigeshi, ya mike cikin bakin rai ya nufi ban daki zuciyar shi yar bakin ciki tana tunanin shi cewa, wanan wankan da zaiyi anya zai fidda mai da dattin zunubin daya kwasa?Ya fito ya same ta kwance, haushinta ya kamashi sosai.Ya dauki makulli ya bude durowarshi ya ciro kudi batare da ya irga ba yan dubu dubu sabbi ya mika mata.Gashi an gama ruwa ki tashi ki tafi na rokekikar ki sake dawowa gidan nan.Ta kalleshi cikin damuwa an ce maka neman kudi nake yi?Ta mike ta soma saka tufafinta, so da kauna kurun nake nema a gurinka baka da kudin da zaka iya bani.Ta fice ta dauki jakarta yana tsaye a tsakiyar falo yana kallonta ta fita tare da cewa sai ka sake jina. Ranar Aliyu yajima bai fita ba, na shi ganin mutane zasu gane abin da ya aikata, kuma sam baya son ya tuna.Sai istigifari yake yi, in dai haka mazinata suke ji lallai zina bala'ice, ya gargadi masu gadinsa lallai kada su sake barinta ta shiganmasa gida. Mahaifiyar mujidat yar asalin wani kauye ne a Ilorin can jahar kwara, an ce dai asalinsu fulani ne, amma yarbanci suke yi kuma yarbawa suke kiran kansu.Musulmine su amma musulincin nasu sai a hankali. Mahaifiyar Mujidat mai suna Bukolatayi aure da Mahaifin Mujidad hakimu bayansun haifi yayan Mujidat dan suna fari kenan, mai suna Latif.Wanan al'adar yarbawa ce mace taje aure amma sai ta haihu za a daura, tasu hikimar wai a gani in mai haihuwa ce.Bayan Latifa sun sami Sikirat sanan Mujidat, mahaifin su mujidat direban taxi ne, mahaifiyar su kuma tana da shago a bakin kasuwa.Tun tasowar Mujidat bata ji sam yar karya ce da son bobo, tunda ta lura tana da kyau ai sai ta mai da kyawun nata tamkar abin kasuwanci. Tun tana shekara tara ta soma amsar kudi tana fansar da mutuncin ta, haka ita mahaifiyart fitina gareta ko yau she tana biye da mata wanan ya sa ko karatun kirki bata yi ba, tana secondary idanunta sun gama budewa, manyan mutane suke daukanta.Da farko iyayanta sunda mu don mahaifiyarta ta sha yi mata duka sanan tayimata tsarki da ruwan barkono, amma da ga baya da ta soma harka da manyan mutane tana kawo musu kudi sai suka shiga shi mata albarka.Haka nan basu damu tayi wata bata zo ba in dai zata yi musu aike.A zuciyar su tafi yan uwanta Latifa da Sikira wadda take aure a garin Ilorin.Kuma dalilin ziyarar da ta kawowa anty sikira ta hadu da Aliyu.Kuma har ta koma gida so da kaunar Aliyu yasa ta ta dawo Ilorin don samun muradin ta.Jin kai da jan aji irin na Aliyu shi ne ya sake burge ta, amma sai gashi tashin farko ta same shi cikin sauki.Tabbas in ta nace ba da dadewa ba zai zo hannunta.Karfe tara na dare ta kira numbar wayan mai gadin gidan Aliyu wanda ta amsa dan bukatar kanta.Bayan ya daga ta tambaye shi ka ganeni?Ya ce, a a ban gane ki ba.Ta ce, sanana Mujidat daga nan cikin gari ni ce wace na amshi numbar ka jiya bayan na fito gurin Oga ya ce, ok madam ce ko?Sorry madam na gane ki, ta ce oganka ya shigo?Ya ce, eh, tun bakwai yana gida kuma naga alamar ba zai fito ba, sai dai yayi mun kashedin cewa ko kinzo kada in barki.Mujidat tayi shiru tana mamaki, me zai sa ya tsaneta haka?Duk da ta mika masa kanta kyauta, amma sai tayi wani murmushi.Indai kissa tana magani to zatayi mun, ta ceda me gadi in na baka dubu biyar yaya zan samu in shiga?Yayi shiru yana nazari.Lallai yana bukatar kudi don yasha kan matsalarshi da maman Bilikis, amma dubu biyar yayi masa kadan.Yace madan zan iya dabara in kin ban dubu goma, zan fadawa Oga cewa mamana ba lafiya nasan zai barni in tafi.Don haka ta ba faruwa amma nasan kafin inbar wurin sai an kawo wasu lokacin ke zaki samu shiga dan su basu sanki ba.Kuma kafin in tafi zan lalata wayar cikin gidan, ta ce hakan yayi zan sameka da kudin in ka kamla komai ka kirani.Yana kashe wayar yaga Aliyu tsaye a bayan shi Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Dfarko ya rude sai kuma ya tuna cewa duk sun yi maganar ne cikin yarensu na yaroba.Aliyu ya ce, ina ta kiran waya baka daga ba?Ya ce, oga jikin mama ne ya tashi shine dan uwa na ya kirani.Aliyu ya ce, jikin ta ya sake tashi?Wani ciwo ne ke damun ta?Ya ce hawan jini ne, Aliyu ya sa hannu ya lalubo dubu biyu ya mika mashi tare da cewa, Allah ya kara sauki. Ya kara da cewa kaje ba sai ka jira wasu ba, bari nayi waya su zo.Da murna mai gadi ya fita ya kira mujidat yace, tayi sauri kafin wasu masu gadin su zo.Cikin sa;a ta tura kofa ta shiga, haka nan cikin sa'a ta riske shi a cikin falo zaune da yar shirt fara irin mai kama jikin nan.Sai gajeren wando, kalkon labarun kasa yake yi NTA, turo kofar ne yasa shi waiwayawa, zunbur ya mike yana nuna mata waje.Fita la'ananiya, ta saki jakarta ta nufeshi, haba masoyina, ina sonka sosai tsaya kaji.Ta kai hannu zata taba shi ya ja baya.Ki fita kawai, ta zauna kan kujera, ba zan sake barin gidan nan ba ko zaka kashe ni.Ya biyota ta zagaya ta fada bedroom dinsa.Ya rasa me zai yi mata, sai kurum ya kira yaransu daga headquarter, jin haka dama tariga ta tanaji dabararta.Taciro wayarta ta danna wani hoto ita da shine suna tsaka da aikata masha'a ta dauko.Kalli hoton nan ka gani, ina da irinsu da yawa har na kati na wanke.Aliyu ya fizgi wayar ya kalla, duk da ya girgiza amma bai nuna mata ba ya ce, yace amshi wayarki ba kati ba in kin gadama in kin tashi ki sa shi a kan profile din ki na fcbk,ko a jikina.Ke ce mace mutuncinki sai yafi nawa zubewa.Tayi shiru ta rasa me zata ce, ya ce fita.Ta daga hannuwa biyu, naji naji zan fita, ta matso gunsa amma ya kamata a ce kanayiwa mesonka kallon mutunci da kima.Ta soma kuka, ka tuna ba nice na dorawa kaina sonka ba, ya kamata ko baka sona saika fada min magana mai sanyi.Ya runtsa idanu, burinsa ta fita domin zuciyarshi ta soma tausayinta.Sanan ga shi dan can gefe yana rada masa wani abu.Ya bude ida nunshi, shi ke nan naji ban kyauta ba amma dai yanzu ki fita kawai, domin ni da ke ba hurumai bane.Ki tuna da abin da ya faru ni dake she karanjiya laifi ne babba, kin sani.Ta matso ta kama hannuwansa ka min afuwa sonka ne ya sani haka.Yanzu ina jin yunwa ko zaka tai maka min da wani abu in ci sai in tafi?Ya ce, duba kicin sai dai in bread za ki ci.A kicin tayi ta zagayawa tana tunanin me zatayi ne don ta samu ta kwana a gidan.Ta dauki wuka ta dauko bread wai za ta yanka, amma sai ta kulle ido ta sharbi yatsanta da gangan, sanan ta saki kara.Cikin hanzari ya nufi kicin da ganin yanda jinike zuba ya sa shi shiga da sauri ya rike ya tsan nata.Kasancewar yana da yar akwatinshi ta taimakon sai ya gyara mata ya rufe shi sanan ya ce, muje a maki Allura sai ki wuce inda kike.Ta soma rawan sanyi wai ba zata iya tashi ba, barinta da yayi ta dan warware shi ne ya kawo kwananta a gidan.Domin tuni shedan ya ribace shi, duk da yana zargin ta yanka kanta ne dama don kada ta tafi, tun daga ranar ta zama gidan tamkar matarsa, wanan ne yasa ko da ya koma gida sadiya taga canji. Wata hudu kenan da soma shiga matsalar mu da ya Aliyu, amma tamkar na shekara biyu, duk na rame na lalace har bana so inyi baki don kada suce lafiya?Cikin wata hudu ya zo so hudu duk karshen wata ke nan kwana dai dai yake yi ya tafi sam baya kulani in yazo magana fiska a daure yake min.Ya manta da wani hakki nawa da yake kanshi, domin nima mutun ce ba ice ba, ina shan wahala da kewarsa.Darare da yawa ina zubar da hawaye don kunci da kewa, gashi yayi mun sabo da yanayin sa na rashin hakuri.Usman da Anty Abida sune kawai suka san halin da nake ciki, ko iya da amininiyata Aisha sunyi juyin duniya amma ban shaidar musu da ko mai ba.Usman ya ce, duk lokacin da nake bukatar wani abu bai min ba in tambaye shi, ni gaskiya ina da jin nauyi.Yau in na ce gashi gobe in ce gashi ba zai yuwu ba, abin da kawai na tsana shi ne inga arana babu makaranta, amma don abin anfani kamar su abinci ina maneji.Tunanin kama sana'a ya shigeni, na ce lallai ina bukatar in kama sana'a don in samu in kare DARAJAR YAYA NA, wadanda a yanzu sunfahimci tsakanina da baban su a kwai matsala.Ba kausar ba hatta Al'amin ya san cewa mahaifinsu ya canza, don watarana da ya shigo daki ya same ni ina kuka, sam banji shigowarsa ba sai naji an dafa ni.Nayi ta maza na share hawaye na na kalle shi da murmushi, ranshi a dagule ya ce, momy waye ya saki kuka?Na ce Idona ke ciwo.Ya ce, mama Abban mu ne ko?Na ce, a a Abbanku bayanan? Yace, shi ne mana, ya ce ki barshi in na girma zan maki duk abin da kike so, in kaiki maka, in sai maki komai.Na rungume shi tare da cewa, to yarona naji dadi na gode kaji.Ya ce momy ki daina kuka kin ji? Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Bayan fitar Al'amin ne na shiga sabon tunani, lallai matsala tsakanin miji da mata tana kawo rabuwar kan yaya, tana tauye yara.Domin zuwa da nayi open day din su a makaranta nan malamarsu take yi mun korafin cewa yarinyata Kausar sam yanzu bata da hazaka kamar da.Bata da kuzari sam, ta ce kowa ya san Kausar Aliyu Tutur a makarantar nan ya san ta da kokari ga surutu, ga wayo.Haka nan duk wanda ya yi mata bata kyalewa, amma daga wancen term zuwa wanan tazama tamkar doluwa ba karatu.Bata iya rama fada, karamin yaro sai ya doke ta ta tsaya kuka, sanan tsaftar su ta ragu, a da yaran suke zuwa na daya a tsafta wanan karon sun koma na biyu.Don haka kiyi kokari ki canja kila matsalar daga wajenki ne.Afili na ce, lallai daga gurin mu ne, matsalarmu zata maida yaranmu baya, dole in kawo canji duk yanda zanyi gidan mu ya koma gidan farin ciki kamar da da taimakon Allah,Wayata na dauko na soma ruga sako kamarhaka.KALMOMI SUN YI KARANCI TSAKAKKEN YANAYI, FADIN YI HAKURI KADAI BA ZAI GAMSAR BA.AMMA DUK DA HAKA INA ME BAKA HAKURI, BA DAN NAYI LAIFI BA, SAI DAI INA DARAJA DANGATARMU FIYE DA SHEKARUNA.DA WANAN SAKO NAKE SAKE BAKA HAKURI TARE DA AIKO MAKA DA ZUCIYATA KA AMINCE DASHI DON SAKE DAWO MIN DA FARINCIKI NA.INA FATAN ZA MU KOMA FIYE DA DA, ZUMA TA ALY NAYI KEWARKA, INA TSNANIN SONKA. Na tura mashi ina tsammanin ganin sako kokira amma shiru, duk wani tunani ko dabara nayi amma babu nasara.Wata laraba da yamma su kausar an koro su kudin islamiya, gashi dama abincinmu ya kare, nafita hannuna da Nera Dari na siyo garin rogo da suga.Nufina su sha da dare, duk da ina tunanin yaya zan sha kansu su sha gari da dare, sai lokacin da nake dawo wa yana ba yana a mota direbanshi yana janye da shi. na shigo gidan zan Rufe sai naga mutum kamar daga sama ya nufo gida, gaba na yayi muguwar faduwa.Sam yanzu bana son ganin shi, don tsananin tsoron sa nike ji, ko sallama baiyi ba ya fara da ce mun, daga ina kike?Cikin in ina na ce sha....shago baje can gurin hadi.Yin me?Na ce, gari na suwo da suga.Gari?Ya tam baya tare da zaro ida nu.Na sa dan yatsa na akan le buna na tare da fadin yi hakuri yara suna ciki.Sai me? Ya katse ni, na ce sai me in yara suna ciki, wato sabon salon zubar da mutunci wanan kika samo ko?Kamar ni a ce matata tana zuwa shago siyan gari?Na nufi ciki raina a dagule, in ya bamu abinda zamuci ishashshe ai ba zan fita siyan gari ba, na raya hakan cikin raina.Kai tsaye daki na shige na ajiye garin na fada ban daki don gudun kada yara suji, da gudu suka rungumeshi suna mashi oyoyo, al'amin da shi da mama, Kausar tsayawa tayi tana kallon su.Ya dube ta ke Kausar ba zakiyi min oyoyo ba? Ta ce sannu da zuwa Abba.Ta juya ta nufi dakin su.Da kallo ya bita cikin mamaki, me hakan yake nufi?Ta soma yiwa yaran sa fanfo ne?Ya mike ya nufi dakin ni kuma jin shiru sai na fito ina shigowa falo najiyo muryar sa.Kausar ina tambayarki kin yi mun shiru na ce me nene kike fushi?Sai na jiyo muryarta tana cewa, Abba ni bana so ka dawo, sabo da in kana nan kullum cikin fada da momy, ni bana son tana kuka.Itama ta soma kuka, na zaro ido cikin mamaki yarinyar,na saurara inji me zai ce, fatana Allah yasa zancen Kausar yazama sanadin fahimtar shi.Muryarshi ne ta katse ni, ok wato uwarku tana kitsa muku magana a kaina ko? Mamanku ta shirya muku in nazo ina cutarku ko?Ya sake tambayarta cikin daga murya, ban san lokacin da na fada dakin ba ina fadin haba yaya.Yanzu me ya kawo wanan tunanin?Tayaya za kayi mun wanan zaton?Na kalli kausar fita.Ta fita na maida kofar na rufe yana tsaye rai bace yana kallo na.Nayi kasa da murya tare da tausasa ta, yaya wanan sauyin da kakawo mana cikin gidan nan wlh ba sai na kintsawa Kausar ko mai ba.Tana ji tana gani, duk kokarin da nayi dan cewa basu fahimta ba amma hakan bai samu ba.Saboda ka kasa gyarawa, har takai ko a makaranta yaran sun koma baya.Hawaye suka soma zubo min masu zafi, na taka na isa inda yake tsaye nafada jikinshi na kan kame shi.Yaya ka taimaka kayi hakuri ka zubar da makamanka ka dawo mana da farincikin mu.Ya ban bareni tare da hankade ni har sai da na fadi, ya soma magana cikin ihu.Tayaya kike so in yarda dake cewa bake bace kike bata ni a wrin yarana ba?Yar wanan yarinyar da bata gama sanin kanta ba shine har zata san matsalar wani? To ni dake dasu munsa hannu tunda kin zabi haka.Shiyasa sam bana son zuwa garin nan, saboda takaicinki, kin zama saikace sanda don Rama. Kullun mahaifiyata tana tuhumata cewa bana kula da ku, yanzu dan zubar da mutunci wai kinje shago siyan gari.Na fashe da kuka yaya yaushe rabon ka ajiye mana abinci?Tun zuwan da ka tawo da wanan matsalar.Ya daga hannu rufe min baki, yanzu ina yi maki magana ne a kan shiga tsakanina da yarana.In zandau komai ba zan dau wanan ba, ya kamata ki sani.Ya juya ya fita bayan ya bude kofa.Kuka sosai nayi na tsawon minti daya, sanan zumbur na mike na fita.Mama tana kwance a tsakar falo tana ta tsotsan yatsanta, ita bata san me ke faruwaba.Ahmad yana zaune kan kujera ya takure, Kausar na shiga raba ido in gani, can na hangota gefen kujera ta makure tare da toshe kunnuwanta, tana nufin bata son jin abinda ake yi, ga kuka tana yi.Tayi sharkaf da majina, dakinsa ya shige shikam naje na rumgumo Kausar nazo na hadasu da Al'amin ina lallashinsu.Duk da cewa nima hawaye ke kwaranya a idanuwa na, Al'amin yazo yayi mun rada a kunne, ki hada shi da Iya kinji Momy ta rama maki(don duk zatonsu ni iya ta haifa ba baban su ba) Najasu muka koma dakinsu, na ce, Kausar Al'amin kuyi hakuri ni da Babanku za mu koma kamar da, ba da jimawa ba kunji ko? Kausar ta dago kai, yaushe momy?Na runtsi ido hawaye na kwaranya na ce, bada jimawa ba Kausar kinji?Duk suka makaleni, Al'amin yasake cewa kin hada shi da Iya ne, da sauri na ce a a ko ku kada ku fada mata, ba na ce muku bata da lafiya ba?Kuna so in taji da muwa ciwonta ya tashi?Duk sukayi shiru, nace kuna so ta mutu? Da sauri suka ce, a'a,na ce to in kun fada mata zata mutu.Kausar ta ce, bazamu fada ba.Na share hawayena sanan na kallesu.Muna ciki har aka kira magariba, na taso su mukayi salla.Tinda na fito banga Mama ba, nasan tana gurinshi, suna ciki ko sunfita oho.Na jika musu gari suka zauna, Allah ya taimakeni suka kama sha. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Kausar tana cewa,Momy in nazama babba zan dinga siyo mana kayan abinci.Al'amin ya ce, momy ba na rigata ba.Yaya kausar nine zandinga siyan ma Momy ko mai, na ce to tun yanzu nagode, Allah ya raya ku, ku girma cikin aminci da Albarka, suka ce amin.Raina yayi sanyi yar firar nan da muka yi da ya rana sai gashi sunyi sallama shi da mama tsam ya tsaya, ganin suna cin gari.Na lumshe ido na hadiye takaici na, sannan na ce sannu da zuwa.Bai amsa ba yayi ciki, kamar in zauna sai kuma na bishi.Ya aje mama ya zauna bakin gado tare da dafe kai, na ce, ina maka sannu.Ya dubeni idanu jajur.Yaya na ke cin gari da dare?Na ce, to yaya bamu da komai ne.Na dubi mama, zomuje ki ci gari.Ya daka min tsawa, ki daina kira min sunan garin nan, ba zataciba.Ko Inyamuri ya sha gari da daddare? Wanan shine na karshe in ba haka ba rai zai baci, ban ce kala ba na juya, cirko cirko nagasu Kausar a falo.Kausar ta toshe kunne, Al'amin na tsaye cikin damuwa,nakamasu muka koma na ce su ci garin amma sai suka ce sun koshi.Kausar ta kwanto kan cinyata, Al'amin ya kwanta kan kujera na kwantar da kaina nima a hannun kujera.Wai ta wace hanya zanbi gidana ya dawo kamar da?Wa zai ban shawara dan ni ina ganin tawa basirar ta kare kan haka.Allah ka bani mafita.Muna nan har aka kira isha'i, na tashi naje nayi sallah suma sukayi sai ga mama ta shigo da nama da Holandia, na ce, suci.Al'amin dai ya ci amma Kausar kin ci tayi waita ta koshi, na rungumo ta, Kausar kina fishida Abbanki ne? Tayi shiru, na ce ki fada min.Ta ce, eh momy shima yanzu ya daina sonmu nace, a a yana sonmu fushi yake yi in ya huce zai dawo kamar da.Sai kurum naji ta ce, wane ne yayi masa laifimomy?Na ce, ni ce, ta ce, bakiyi mashi ko mai ba, ba ma kullun kina bashi hakuri ba tunda yaki yayi hakuri ya daina sonmu.Bani da bakin magana sai shiru ina mamakin Kausar, yar wanan yarinyar har tana fahimtar abubuwa kai abin da mamaki sosai.Haka na lallaba su har sukayi bacci na kulle mana kofa sanan nima na kwanta na fada kogin tunani. Wa she gari da wuri na tashi nayi salla da wanka, sanan nayi musu shirin makaranta, duk a dakinsu.Nace suje su gaida baban su.Kausar ta noke tare da daure fuska za ta soma kuka, na ce, haba Kausar, kuje ku gaida Babanku mana.Kina so ne ya j haushi irin jiya?Jiya ma kin ki sakar mashi fuska ne shi yasayayi fada.Ta ce, to momy yanzu tsoronshi nake ji.Na ce, daina jin tsoro kinji Kausar, yana sonku.Daga nan ki bashi hakuri.Ta ce, to.Amma sam fuskarta ba wani annuri, ina biyeda su har kofar, Al'amin ya kwankwasa daga ciki yaya ya ce, wanene?Mama da jin muryarshi sai ta ce, Abba.Ya ce mama.Na bude kofar suka

Chapter 10 of 25