Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
za a ce muna gida daya karkashin miji daya, amma mu raba girki,sai kuma na ce bari dai in bar shi tunda shi ke nemowa.sai kuma ta tsiri fita zuwa gurin wasu 'yarbawa yarensu,sai ta kai dare. Randa ta fita na uku na yi mata magana,tana shiga dakinta na bita. Maman Abdul. Ta waigo ta dube ni,sannan ta ci gaba da kwantar da dan ta a kan gado. Na ce, Amma kin san mijinki ya cekar ki fita ko? Ta ce, Na fita din zan ta zama a gida ne? Ya amsar min waya,sannan ya cezai hana ni fita, ba zan iya zaman takura ba,nace,zaman aure shi ne zaman takura? Ta ce, Maman Kausar don Allah ki barni kawai, kije ki harkar ki. Jin haka sai na tafi na kyale ta. Yaya bai zo ba har sati biyu,duk da yana kiranmuta waya ko yaushe yana tambayata ko akwai wata matsala a zamanmu da Mujidat,nace masa babu wata matsala, ina zaton bai fadamata cewa yana zuwa yau ba, tadaiga na haukace da aiki,munyo kitso da lallae ni da yarana. Ina da nacin yin lalle dan na san mijina yana matukar so, ya ce min shi zan tayi masa a gida,don haka su Kausar suna dawowa daga Islamiyya suka cire kayan makaranta na shirya su cikin sababbin kaya.Allah ya taimake ta tana shigowa ko minti goma batayiba na ji tsayuwar motarsa,nafito daga dakinsa inda na kai turaren wuta nace su Kausar ga Abbanku,da gudu muka fita ni da su, nan ta fito kallonmu, duk da cewa ko a da ta saba gani lokacin renon cikinta.Dukkanmu muka rungume shi,tsaki ta ja sannan ta juya cikin dakinta. Duk hidimar da mukeyi bata fito ba, har lokacin da muka shirya fita zuwa gidan Iya, na ce baka duba su Abdul bafa.Yace, Uhm! Yaushe nashigo gidan? Ni zan je in duba su koko suzasuzo duba ni? A nan na yi Magriba na yi Isha'i,ba ta fito ba,in ma za ta ce ba ta sanna dawo ba da Kausar ta kai mata tsarabar su ai ta san na dawo,nace, duk da haka ka leka,Tsaki yaja,sannan ya fita abinshi. Na leka dakin, tana zaune bakin gado ta zabga tagumi ranta a bace, nace, Sai mun dawo za mu je gidan Iya,ga mamakina sai naga taja wani uban tsaki tare da banko min harara, sai na ji dariya ta subucemini, don haka na yi 'yar dariya tare da sakin labulan nata, ina jiyowa ta yi wata kalma da yaransu wadda nake zaton zagi ne. Iya ta yi murna da ganinmu,sannan ta ce ina 'yar uwarki? Nace, Tana gida, ta ce a gaishe ki. Tace,Ina amsawa. Ita bata fitane bakuzo da itaba?Yaya ya ce, Ba za ta zo ba. Iya ta ce, Sadiya ke ce zaki dinga janta in zaki fita, don ta saba d mutane tunda kin ga ba ta san kowa ba. Nace to Iya. Mun je gidan Yaya Sulaiman, Yaya Zakari, da kuma Yaya Sani, duk mun ziyarcesu, inda Yaya ya yi musu alkhairi. Ina jin dadin yanda Yaya ke kula da danginshi suna shi masa albarka, sai dai bayamin kara yayi wa mahaifina.amma na sha alwashin koya masa.Daga nan muka dawo gida,kai har yanzun na tabbatar Yaya yana sona.sabida irin soyayyar da ya gwada min ta dare dayan da yayi a dakina. Washe gari mun yini gida cikin jin dadi da annashuwa, amma Mujidat taki fitowa, sai lokacin bacci sannan ya nufi dakinta. Kuka ya sameta tanayi wiwi,ya isa kusa da ita ya ce, Lafiya? Ta watso masa kallon banza da manyan idanunta da suka kada suka yi jajir, ta ce, Haka dama aurenku yake? Ka nuna min cewa matarka kawai kake so, babiba. Ya ce, Menayi miki? Ta ce, Tunda ka dawo ka ajiye ni kamar kashi, matarka da yaranka kadai ka sani. Ya ce, Kece ki ka ja jikinki damu, na dawo kinki zuwa ki gaisheni.Ta ce, Ka fada min cewa zaka dawo? Sai na fada miki dole sannan zaki gaishe ni? To ni ba haka tsarina yakeba. Ta ce, Eh, amma ka iya fadawa matarka ai, tunda naga sun shirya,nima in ka fada min ai zan shirya. Ya ce, To shi kenan next time zan fada miki tunda dakin ki zan sauka, dan gobe zan tafi. Ta tashi ta dawo daf da shi tasa hannu a kumatunsa, Aliyu ina son ka da yawa, nima ka daure ka soni. Ya yi murmushi, sannan ya ce, Ina son ki mana, Ya kalli kitson ta. Har yanzu ba ki cire wannan gashin dokin ba? Bana son shi. Ta ce, To zan cire gobe. Ta dauko Abdul tasa masa a cinya.Tunda ka dawo ba ka dauki yaronka ba,ya kalli yaron cikin kauna, sannan ya soma yi masa wasa da kumatun,sai dai koyaushe ya rike yaron gaban shi yana faduwa, kuma yana tuna masa cewa fa akwai wani asiri da ya boye. Ya kan ji tausayin Mujidat a irin son da take masa, kuma yana son ya kyautata mata ko don yanda ta hakura da rayuwar bariki ta yarda zatayi zaman aure,har inzata zauna da su lafiya to zai mata adalci, don haka ita ma ya nuna mata soyayya daidai gwargwado, wadda ita da kanta ta yarda cewa ya soma sonta.Haka nan da zai tafi ya sake tara muya yi mana nasiha,sannan ya tafi. Dama makarantar da aka dauke ni koyarwa sunce sai andawo hutu, tunda tuni sun min duk wani abini da ya dace kafin a dauki duk wani malami, don haka ana komawa hutu na soma koyarwa a matsayin sabuwar malama, aji biyu na nake dauka, wato 'yan safe. Don haka tun Asubahi inna tashi nake kammala yarana ina sauke su in wuce tawa makarantar, sai dai matsala daya aikin gidana dole sai na nemi 'yar aiki kenan. Kodanayi wa Aliyu wannan batun sai ya ce dalili kenan da baya san aiki ga matarsa, ba danbazai iya biyan 'yar aiki ba, a'a sai dan ba za a tsaya a duba masa gida da kuma yara ba. Na ce ni dai zan biya mai aikin cikin albashina, ya ce ai ba wai ba zai iya biya ba ne ya fi son ya ganni a gida.Iya na fadawa a samo min 'yar aiki,tace in kuna da wadatar gurin kwanane sai ku dauko Nasiba 'yar gidan Yaya Zakari. Na ce ai matsalar gurin kwanan ne, na fi son wadda ke kusa da gida,in ta yi aikin ta ta je gida. Iya ta ce haka ne. Ansamo min wata yarinya 'yar matashiya, kullum zatazo ta yi min wanke wanke da shara,haka muka ci gaba da tafiyar da rayuwa da dadi ba dadi, ina kuma yabawa Yaya yanda yake kwatanta adalci tsakaninmu, amma kullum Mujidat gani take yi Yaya ya fi sona da ita. Albashina na farko naje na sayo kayan abinci da zannuwa turmi biyu. Ranar Yaya ya dawo ya tsaya yana kallon kayan abincin.Wanna fa? Na ce, Babana zan kaiwa,tunda na yi aure ban taba yi masa wani abu ba. Ina kallon Yaya ya yi shiru yana nazari,sannan ya ce, Nawa ne kayan nan? Na fada masa ya ce to kafin in tafi zan baki.Nace ayi haka Yaya daka barshi. Ya ce, Nima ai 'dan shi neko? Na yi shiru, ya ce, To zan ba ki ba zan so ba a ce kin riga ni kaiwa mahaifinki wannan alheirin. Na ce, To shikenan Allah ya saka da alkhairi. Ya ce ameen. Na ce, Ni dama ko da na kai da sunanka zan kai.ya ce, Yanzun ma duk ba haka ba,wai ke za ki je Zariyan? Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 na ce, Eh, wai da. Ya ce, 'A'a gobe zan je in kai musu. Na ce don Allah ka je da ni. Ya ce a'a,ina ce ke ce na ji Iya tana fada miki bikin kannanki guda biyu? Na ce cikin shagwaba, Allah Sarki Yaya bikin fa sai daf da Azumi akwai saura. Ya ce, Eh, ki hakura sai lokacin. Na ce, Shi kenan. To yanzun in kabani kudin nan me ya kamata in siya? Yace, Oho! Miki, ki bude account mana. Na ce eh, tozan bude. Cikin wannan lokacin na soma rasa gane kaina, ba sai an fada min ba na san cewa ciki gare ni, ban taba irin wannan cikin ba mai masifar laulayi. Binta yarinyar da ke min aiki ita ce ke ta dawainiyar aikinta, har ma jinyata. Mujidat kuwa ba ta zama,bata taba yimin sannu ba, sai dai in jiyo tana ta yi wa yara wasa.Su Khausar su ne suka sanar da Iya cewa ba ni da lafiya sai ga ta. Ranar ita ce ta gyara min gida,sannan ta kira Mujidat tana ta yi mata fadan cewa. Me yasa 'yar uwar kina ciwo amma ba za ki taya ta aiki ba? Sai ta ce wai ita ba ta sani ba, ko da Iyan ta shigo tana fada na ce mata kar ta damu Mujidat ba mai son aiki ba ce, don ko dakinta ba kullum take gyarawa ba,Iya ta ce Allah ya kayuta, ni sai in gakamar ba kwa zaman lafiya? Nace, Lau muke ni da ban cika zaman gidan ba, don dai ciwon nanne. Iya ta ce, To kin sanar a makarantar? Na ce, Har malamai sun zo duba ni. Ta ce, Allah ya kara sauki, ga shi kinki zuwa Asibiti. Na ce to ko na je ba wani abu da za su yi min sai magani, to ko maganin ba zan iya shaba, ko fa ruwa na sha sai ya dawo. Nan Iya ta yini kafin ta tafi.. Cikin dare kuma tamkar ba zan kwana ba, Kausar da Binta mai aikina sune a kaina. Kausar nata kuka,ta je ta fadawa Antynsu amma ta ki zuwa, tama ki bude kofa, duk da irin kwankwasawar da Kausar take yi, na ce su dau waya ta kira Babansu,sabida gani nake tamkar ba zan tashi ba. Ya daga kiran farko, Kausar ta ce, Abba, Momy fa ba ta da lafiya. Cikin muryar kuka ta yi maganar. Ya ce, tabani na amsa sannan nace sufita,suna fita cikin muryar wadda ke cikin matsananciyar jinya na ce, Aliyu ka yafemin bana zaton ciwon nan na tashi ne. Cikin daga murya na ji ya kirani da karfi, SADIYAA me ke damunki? Cikin rauni na ce ka yafe min? Bai amsa ba ya kashe wayar. Can jimawa sai ga Mujidat ta shigo, na san cewa shi ne ya kirata,ni dai daga karshe bansan me ke faruwa ba ma, ashe wai suma nayi.Ihun Mujidat shi ne ya sa su Kausar tashi daga bacci.ta kira shi tana ihu wai bana motsi,kila na mutu ne,ya kidime sosai da jin hakan kuma nan take ya kira Usman, yasanar dashi duk abin da yake faruwa, cikin daren Usman ya zo yana buga gida Mujidat sai tace da Binta mai aiki taje ta bude, cikin tsoro yarinyar ta ce waye? Ya ce nine Usman bude, ta bude. Har dakina Usman ya shigo, Mujidat tana ta ihu ya ce takama su sani a mota, ta ce ba mutuwa ta yi ba? Usman ya ce sai na ji daga likita. Asbahin fari na farka na ganni a gadon Asibiti,an samin ruwa. Usman da Mujidat na gani tana zaune shi kuma yana jingine da bango,ya zo kaina yana min sannu, na kalli ruwan na gane ina Asibiti ne. Ya dubi Mujidat ta farfado. Mujidat wadda bacci yake fizgarta,ta ce uhm,uhum, tare da tabe baki,ta soma jijjiga danta, sannan ta ce, sannu Maman Kausar. Idona yana lumshe kai kurum na daga,ina ji lokacin da Usman ya kira yaya fada masa cewa na farfado. Yace shi ma yanzun haka ya wuce Nasaraw daf yake da Unguwar Ma'zu , Usman ya ce muna asibitin Biba ne. Aliyu ya ce ka fada min. Yaya ya rude da ganin yanda na dawo,ya kama hannuna ya zauna bakin gadon, Sadiya me ya same ki? Na bude idanuna ina kallon shi ya rusuno ya sumbaci kumatuna. Sannu kin ji? Ya kalli Usman. Sannu Aboki, na gode Allah ya saka da mafificin alkhairi. Usman yace , Haba dai sai ka ce wani abu? Allah dai ya ba ta lafiya. Aliyu ya ce ameen, na gode. Da ya samu labarin cewa ciki gare ni sai na ga Yaya ya soma murna,tamkar cikin fari. Usman neya taho da Mujidat wacce ke ta yin gyangyadi a zaune. Tunda duku duku sai ga Iya wai da Asuba Binta da Kausar suka je suka fada mata, ita ce ma ta tashe mu daga bacci, domin bacci ya sace mu Yaya na kan kujera ya dora kansa a gadon, hannuna yana kan nasa kawunan mu a hade, motsinsa shi ne ya tashe ni, suka gaisa ya fita sallah. Sai lokacin na tuna da 'yan yarana su kadai kenan su ka kwana. Kafin yamma naji karfi sosai sakamakon ruwan da aka yi ta dura min mai dauke da sinadarin abinci,likitan ya sallamemu tare da ba mu magunguna. Tunda muka dawo gida yaya ke jinyata,Sallah kurum yake fita har abin da zanci shi ne ke girka min,, ya min wanka,abin ya kunna Mujidat har ta kai su ga fada ya mareta, tun daga lokacin ta yi wa kanta alkawarin kawo karshen zaman shi da matarshi ko ta halin kaka. Yayan da zai yi kwana biyu sai da yayi biyar ya ga nadan murmure,sannan ya tafi.. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Duk abin da nake so sai da ya tanadar min isasshe sannan ya tafi. Kullum gidan ba ya rabuwa da 'yan dubiya. Aisha ta yi ta yi min iskanci wai na narke sai ka ce cikin fari, Yaya shi kuma ya daure min gindi tun da tazo ta ga yana ba ni abinci a baki shi kenan fa,nace na ji dai ai ko wane ciki na fari ne tunda wuyar dana ke ciki da wannan na fari ban sha ta ba. Na rarrafa kicin ina dafa taliyar Hausa, sai ga Mujidat daga yawonta an zugo ta ta shigo da fushi, Mama tana wasa da abin kama shanyar ta da ya fado daga igiyar yaronta, ban ma lura da shi a gurin ta ba sai na ga ta kwace tare da rankwashin ta a kai tana zagin ta da Turanci. Maama ta yanka ihu raina kuma bace na ce mata. Ke! Na nuna ta da yatsa. Ki shiga hankalin ki, wannan 'yar yarinyar zaki doka? Wallahi ba zan dauka ba. Ta harareni tare da ce min ta doketa, kuma kada in ga wai nayiwa mijina asiri yana mata wulaqanci in dauka za ta tafi ta bar shi, to in sani ita fa ba inda za ta, domin shi kadai ta gani miji,sannan in shirya barin gidan bada jimawa ba. Na yi dariya. 'Ke ko Agumin ku yayi kadan bare ke, ba da tsafi ku ke takama ba? Mu zuba ni na riqe Allah.Ta shiga daki fuu! Na yi mutuwar tsaye ina mamakin lamarin,wannan ai ke ce kwarkwasa fidda mai gida a gidansa,iInshaAllahu ta Allah ba ta ki ba. Haka muka ci gaba da zama cikin husuma kullum sai ta tsokaneni,in na yi kamar in hada ta da mijinmu sai in kyaleta. Ashe ita kullum aka yi saita kirashi a waya. Sai da ya yi wani zuwa yake min zancen wai me ya hada mu da Mujidat ne?nace me akayi, tace anyi wani abune? Ya ce, Eh tace kin canza yanzun kintsaneta, kiyi ta zaginta kina mata gorin bana sonta,in ko har hakane bazanji dadiba, domin batun ina sonta ko bana sonta tunda yanzun ita ma matatace bai kamataba. Yafa bata rai wai dole sai ya kare mutuncin matarsa,inzaiyi adalci ai nasan ya fi nuna so da kauna gare ni. Nayi 'yar dariyar takaici, sannan na ce, Tunda ka mance halina har ka yarda da batunta shikenan. Amma in har adalcin zakayi kamataya yi ka tara mu,dama 'yan sanda da bangare daya suke aiki in sun ji ta bakin me kara ya isar musu hukunci? Ya yi shiru sannan ya ce, To muje falo a kirata, Na ce a'a a barshi ni nayarda na dauki nauyin zunubin.ya ce ni dai na ce ku fito falo. A gabanta na maida komai kuma ba ta musa ba,baisan tana fita ba sai lokacin danace ina taje aka zugota. Nan fa ya zaro ido ina take zuwa? Na ce ga ta nan ita ta sani, hankalinshi ya tashi ya ce mata gurin wani take zuwa? Ta zaro ido wai a'a gurin yaren su ne, dama shi irin wannan auren haka kullum a yi ta zargin juna, nan na tashi na bar su suna ta masifarsu. Kafin ya tafi sai da ya kafa mata dokoki har da na fita, amma yana tafiya ta sa kafa ta shure dokar,sabida jarabarta ma ni na lallaba na soma zuwa aikina, yara ko na kwaso su sai in kai su gidan Iya in bana gida bana barin su a gida. sai dai wani abu da na lura da shi shi ne wata dinkewa tsakanin Yaya da matar shi Mujidat, duk da cewa bai canza min ba, amma ina mamakin sabuwar shakuwar in yana dakinta har wani zumudi yake yi,sannnan ya kan dauki danta ya fita da shi wani dare ma har saloon ya kai ta, ko da dai ya min tayin zuwa na ce a'a, sannan ya kan dauke ta da yara su fita shopping duk da dai ya kan min tayin zuwa,ce masa nake a'a sai sun dawo. Haka nan zasu zomin da tsaraba,abin yana ta damuna hatta abincin ta da yake cewa ba zai ci ba yanzun nadeshi yake yi. Wani zuwa da ya yi sai na yi niyar gwada shi ranar da ya dawo dakin Mujidat zai sauka sai na yi tuwon shinkafa da miyar Ogun, bakwai da wani abu ya iso gidan. Taliya ta dafa dama girkinta bai wucetaliya da shinkafa da miya ba, ga shi ta zabga uban attaruhu, ta saka wando da riga an je an wanko kai, dan ma ba wani gashi neda ita ba da na doki ake gayun, kuma ya hana sawa,da in ya dawo ni yake fara nema a ko yana dakinta, yanzun kum in dakinta yake can yake yada zangoi,sai daga baya sannan ya zo. Ina sallar Isha'i ya leko, sai kuma ya shigo ciki ya zauna,sannan na gaida shi ya amsa tare da tambayar jikina na ce da sauki sosai, na kalle shi. In kawo maka tuwon shinkafa miyar ugun ce? Kafin ya yi magana sai wayar shi ta soma kara, da ya daga sai ya ce, Ya? Ina jin haka na san Mujidat ce, ko me ta ce sai na ji ya ce'O.k, gani nan, Ya kalle ni. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Mujidat ce take jirana muci abinci, na so cin tuwon amma yaya zan yi tunda girkin ta ne zai fi kyau mu ba ta hakkin ta ko? Raina ya sosu matuka, amma sai na danne na ce, Haka ne, na ga ai kuna ta dasawa. Ya kalleni, Kamar yaya? Na ce,gani na yi kana ji da ita. Ya ce, Lallai Sadiya,harma zakice haka yanda na fifita ki a kanta kuma ta hakura? Nayi guntun murmushi, Ni ba ni san ka fifita ni a kanta, na fi son ka yi adalci, ni na san dama duk zance ne da ka ke cewa ba ka sonta. Ya hade rai, 'Wannan wace irin magana ce? Kin san ai matata ce, batun ina son ta ko ba na son ta ki aje shi. Ya mike tare da fadin. Banason irin zantukan nan kowacce ta zauna a matsayinta. Ya fice abin shi. Na jima ban iyatashi ba, eh na san ba laifi ba ne dan ya nuna kulawa ga matarsa,amma abin da ke ban tsoro yanda na ga yana son hada matsayin da a da ya ce ni kadai ke da shi ya raba mana. Anya nan gaba Yaya ba zai bijiremin ba? Wata zuciyar ta ce haka wane shi, zai manta asirin da Allah ya rufa masa kuma ke ma ki ka rufa masa. Da safe muka shirya da yara zan aje su a makaranta nima in wuce gurin nawa aikin,sai lokacin suka bude kofa muka gaida shi, sannan muka wuce. Ko a makaranta a ranar tunani nake ta yi in zan lura da kyau yanzun ma bai cika nema na ba sosai, ga zatona don ba ni da lafiya ne, amma yanzun na gane ba haka bane. Da muka tashi na kira shi na ce zan biya gidan Anty Abida,sai cewa ya yi shi fa ya tsani wannan yawon,daga can bai ce in je koina ba, na ce to. Cikin kuka nake fadwa Anty Abida matsalata, dariya ta yi tare da cewa, 'KISHI ke damun ki Sadiya ga shi kin fada kin ce mijinki bai canza miki ba,dan ya nuna kulawa ga matar shi ya ci abincinta sun fita tare laifi ne? Na yi shiru. Ta ce, ko yana miki sababbin dabi'u? Na ce, Eh, to jiya dai da na yi masa korafin cewa yanzun yana sonta kinga yanda ya bata rai,yana ta fada. Ta ce, Kar kikara yi masa zancenta, ba ruwanki da harkarsa. Na ce to shi kenan,amma fa bai cika son Taliyaba ko na dafa sai na yi masa abin da zai ci,amma ita sai ta yi masa yayi taci. Anty Abida ta ce, Na ce miki babu ruwanki. Nace, Yanzun duk ba shi da laifi? Ta ce, Babu. Na ce, shi kenan. Tace ki kauda kai ga tunanin zai canza kiyi ta kanki da lafiyarki. Na ce to Anty shi kenan. Na nufi gida ina zaton sam Anty ba ta hasashi abin da nake hasashe ba. Tsakiyar falo muka same su ya dora Abdul saman kafadar shi yana yi masa wasa, yara suka yimasa sannu da gida,su ka nufi dakin su,nima dai sannun nayi masa zan wuce yace, Abdul yana ta kallonki MY CHOICE. Na dawo na daga masa hannu tare da yin dan yake,nawuce dakina.Ina kwance kan gadona ya shigo baifi minti biyar da shigowa ba, Sadiya! Ya kira sunana,bayan ya zauna bakin gado, na amsa da na'am ba tare da na taso ba. Ya ce, Ni na ga kamar kin canza min? Na ce, Kamar yaya? Sai in ga kamar idanunki suna tuhumata a duk lokacin dana kalleki? Na ce, A'a kai ne dai ka ke zargin kanka. Yace,shikenan, ya jikin naki? Alhmdllh. Ya ce, To haka akeso.Yakai hannunsa ya shafi cikina,ya babyna? Ban tanka ba dan ni fa yanzun abu kadan ke bani haushi, ya juya zai fita kenan sai karar shigowar sakonni cikin wayata, ina ji na san daga facebook ne,na kai hannu zan dauka shi ma ya kai, saiya riga ni dauka, gabana ya fadi dan na san cewa ya ce na goge,ban goge ba. Ya dawo ya zauna, 'Sadiya. 'Na waiwayo na dube shi. Bana ce ki rufe wannan account din ba? Na ce, 'Zan rufe ai. Ya ce, ba kida niyya. Ya soma fada. Ni fa bana son taurin kai,wata nawa da cewa ki rufe,mekikeyi a internet?na ce 'Karuwa! Nima cikin zafin rai na fada,ya ce in ban da shashanci dubi yadda maza suke requesting dinki. Na ce, sai ka duba ka gani na yi accepting? Ya ce, Ina ruwana, na dai ce ki rufe kuma kin ki don haka yaune karshe, in ba ki rufe ba sai kin daina rike babbar waya. Zuciyata ta tunzuro na ce, O.K, sabida nice zakace ma haka, amma matarka da yake ita kana shakkarta ba yini take yi chatting ba? Ya ce, Ita ma tunina hana,ita da har wayar na amshe na ba ta karama me ta ce? Na dago na kalle shi, Har yanzun chatting take yi. Ga mamakina sai na ji ya ce, Karya ki ke, 'yar Nokia ce a hannunta,ina ruwanki ma in me take yi? Ke dai ki hanu mana da abin da na hana ki? Ke yanzun kin kama taurin kai,nema kike ki canza hali ko? Kinfi son a yi ta fitina? Fuu! Yafice abinsa. Sai na samu kaina da jin zafin kalamansa,kuma na dauke su a matsayin wulaqanci da tozarci,wata zuciyar tace me yasa tuni da ya ce ki rufe account din kika qi? Ina kokarin amsa laifi na ne sai wata zuciyar daga gefen hagu tace shi ne zai fadamiki kalaman batanci har da kiran ki shashasha? Bayan ita waccan tana yin chatting ma bai hana ta ba har da cewa karya ki ke mata, to kema kar ki rufe duk abin da zaiyi yayi. A fili na ce, Ni da nake karanta abubuwan karuwa a ciki ma ba zan rufe ba. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Har ya tafi sama sama muke, amma duk da haka yana kiran wayata sai dai ba na iya yi masa hira dan haushisa. Tabbas in ma ya hana Mujidat hawa internet to tana yi a boye dan tana yi a gabana, sannan ba ta daina zuwa gurin yarensu ba. Ni kam yanzun ba abin da zai fi min illa in yi watsi da su in yi ta kaina. Kwanci tashi cikina ya shiga wata na biyar,na dan gyagije daga laulayi,kuma na soma siyayyar kayan babyna. Tabbas Mujidat tana jin haushin cikina,don ina lura da irin yanda take yawan zabga min harara, sannan in ba ni ce na yi mata magana ba itabata yi mini. Haushin da take ji nawa a yanzun ko da da yayan bai damu da ita ba ba ta ji kamar yanzun. Wata Litinin na dawo daga aikina tare da yarana, na kai minti biyar ina buga gida ba a bude min ba, har nasoma zaton ko ba kowane a ciki, sannan aka zo aka bude, sai dai wani rainin wayo ashe suna zaune a harabar gidan ita da wadanda take zuwa gurinsu su ma yau sunzo gurinta. Cikin fushi na kalleta. Maman Abdul kina nufin zamanku a nan bajuji duk bugun gidan da nayiba? Ta yatsina fuska, Na ji mana ba gashi na bude mikiba? Na yi kwafa tare da juyawa na nufi ciki,sai na ji sun yi wata magana cikin yarensu,sai kuma suka kwashe da dariya, na dawo baya cikin zafin rai na ce Maman Abdul ki ce da mutanen nan su fita,tace yazakice su fita,wurin ki suka zo? Na shiga kicin na dauko muciya nanufe su. Ku fita daga gidan nan maza maza.Cikin sauri suka fita suna yare, itama tabisu, na maida gida na rufe, na koma ciki, ina ta huci. Hatta su Kausar sai kallona sukeyi tamkar na zamar musu sabuwa. Kusan awa daya na ji tana buga gidan, banza na yi da ita har Al'ameen sai da ya zo ya ce Momy ana buga gida, shi ma na kore shi, kusan minti goma waya ta ta soma ruri na gane Aliyu ne, dan ringing din shi daban ne, na daga raina a cushe,ban raini shi yasa dukwanda ya yi min raini nake jin zafi. Ya ce, Sadiya yaya za ki rufe mata kofa, ki bar ta a waje? Na ce, Wa? Ya ce, Au! Ba ki ma san kowace ce ba? Bari ki ji Mujidat fa matata

Chapter 18 of 25