Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
zai auri Mujidat, tana da hankali Iya sosai. To ya ce yana son kara aure shi ne na ce ya aure ta. Iya ta rabka salati,sannan ta ce, 'Amma ban taba sanin ke mahaukaciya ba ce sai yau, ni ban taba jin inda aka ce ga wata mace ta ce mijinta ya yi mata kishiya? Ta sake zabga salati tare da riqe haba tana kallona. 'Ko ni nan da nake tsohuwa bakeba a ce babanku zai dawo duniya zan amince ya yi min kishiya? Dan haka ban yarda ba. Muka kalli juna da Yaya, ta ce, 'Meye matsalar ka da har kake son kara aure? Ko har yanzu bata son haihuwar ne? Ya ce, 'A'a wallahi bata da laipin komai kuma ba inda ta kasa, dama sabida raya sunnah ne kamar yanda yake cikin musulunci, yarinyar nan kuma Iya ta musulunta ne in ta auri wanda ba na kwarai ba za ta dauka haka halin musulmi yake, amma mu za mu yi mata mu'amula ta kwarai yanda ba za ta yi da ta sanin musulunci ba. Iya ta ce, Eh, ai dama ke Sadiya ba a yada ke gurin magana,ni fa dan ke nake fadan nan amma ke na lura kamar zuga ki nake, wai ke ba kya kishin mijinki ne?nayi 'yar dariyar yake, sannan na ce 'Ina kishinsa mana amma hakan ba zai hana shi ya kara aure ba. Ta yi shiru tana kallon mu can ta ce, 'Ni fa ban yarda da yarinyarba, kallonta nake kamar wata 'yar bariki ko wadda ta buga duniya. Muka kalli juna,Ya ce, 'Ai kin san zaman Lagos, sannan ba ta dade da Musulunta ba.Nace, 'Eh, ba ruwan ta Iya. Ta ce, 'Oho! In ma da ruwanta ke ki ka sani tunda kin ji kin gani ai shi kenan, ni me zan ce, Allah yasa alheri. Yauwa, kwanaki yayanku kece min 'yan uwanta sun zo na ce shi ne don rashin mutunci ai sazo su min godiya. Muka sake kallon juna ni da Yaya, na ce, 'Af wannan laifina ne Iya ni ce ya kamata in rako su kiyi hakuri. Ta rike baki tare da cewa, 'Uhum! Abind ya same ki kar Allah yasa ya samu sauran dangi. 'Na ce Iya na gode bari mu tafi. Haka muka bar Iya baki bude tana mamakina,ni kuma na ce masa mu tafin dan kar ta canza ra'ayi,duk da ta amince, amma ba wai ina murna ba, bani da yanda zanyi da ya wuce in kauda da kai a yi auran, na san mata da yawa za su ga baike na amma ina san su sani DA KISHIYAR WAJE GARA TA GIDA.Daga nan gidansu Anty Abida ya ce mu tafi,,ni dai muna tafe ne ba kamar yandamuka taho dazu ba, ba wata hira bare annuri. Mun samu Usman a gida don haka muna shiga suka fita. Aliyu ya kalli Usman 'Aboki, Iya fa ta yarda da batun Mujidat. Cikin mamaki Usman ya kalle shi tare d fadin, 'Kai haba? Aliyu ya ce, 'Allah da gaske. Usman ya ce, 'Banzata ba, ya aka yi ta amince da sauri haka? Ya ce, Kai bari kawai,yarinyar nan Sadiya aboki ba ni d abind zan biya ta, ita ce ta shawo min kan Iya har ta amince da batun,sai na lura da akwai wasu shakku daga zuciyarta, Allah yasa ba ta gane cikina Mujidat ta haifa ba.Usman ya ce, 'Ka kara rike matarka da kyau,ina fada maka a wannan zamanin ba za ka samu tamkar ta ba, ina fada maka ko Abida matata ba za ta yi wannan jan aikin ba, tana fada min sai dai ta ce tana karfafawa Sadiyane dan tasan za ta iya kuma hakanne mafita. Aliyu ya ce, Allah ya ba ni ikon riqe ta da gaskiya. Usman ya ce, Ameen, yanzun mu tafi gidan su Yaya Sulaiman mu ji yanda za a yi. Aliyu ya ce to, Allah ya rufa asiri. Abida ta dube ni ina kuka, kallo na kawai take yi bata hana ni ba kuma bata bani hakuri ba. Sai da nayi mai isa ta. Sanan na share hawaye na, sanan ta dafa kafada ta. Sadiya kada kiga cewa ban baki hakuri na barki ne ki rage radadin dake zuciyarki, gaskiya ne in ka zubar da hawaye yana rage bakin ciki, amma in tambaye ki mana? Na kalle ta da jajayen idanuna, ta ce kukan nan na menene kike yi? Murya ta a dishe tana rawa na ce, anty... Abida ina da matukar kishin Yaya Aliyu,Dan ban san irin son da nake yi mashi ba, kukaba yakunshi abubuwa dadama, amma kishin mijina shine a gaba, wai mijina zamu raba da wata, inna tuna haka hanjina na kaduwa, da na sani ban amince ya aure taba.... Sabon kuka ya kubuce mun.Tace kijure, Allah yasan nufinki, karki bari yaga karaya daga gareki, domin ba mijinkiba har mijina ya ce kin burge shi kullum cikin yabonki yake tare daba mijinki shawarar cewa yayi maki kyakkyawar ruko, dan haka ki cigaba da dannewa. Na ce, to anty zan kula, yanzu na sha kanshi ya amince in nemi koyarwa, sai dai ban san ta ina zan fara ba. Ta ce kada ki damu shugabar makarantar firamare ta L.E.A unguwar Mu'azu kawar yaya ta ce zanyi mata magana sanan karamar hukumar Kaduna ta kudu ma babban wan su Usman yana gurin ne kuma nasan zai tai maka. Na ce, to, aikuwa nagode Anty Abida Allah yabar kauna. Tace amin. Haba ai ba komai wallahi. Nan muka wuni nakasa cin komai, Anty Abida har Dan wake tayi min wai taga inaso, amma da kyar naci uku ina taunawa tamkar ina tauna magani, ko ruwa na sha sai inga tamkar magani . Anty kanta ta shiga damuwa tana min fadan kan in kashe kai na a banxa. Na ce mata. Anty kiyi hakuri cikin kwanakin nan ko gida na bana iya cin abinci in na dauki littafin marubutan nan in dan duba sai komai ya tsaya min inkasa fahimtar me nake karantawa mai makon in karanta litafi sai dai shi littafin ya dinga neman karantani da ko ina da yar matsala inna karanta sai ya dan rinka debe min kewa. Ta ce ai duk ki ajiye batun littafi kirumgumi mai kankat wato, ALKUR'ANIR KAREEM. Na sauke ajiyar zuciya,, tabbas Anty Alkur'ani yana sanyaya zuciya mu kan musalmi bamu da kaico sai godiya ga ubangijin da yayo mu a musulmi. Ta ce haka ne Allah kasa mu mutu a cikin musulumci muna a musulmai. Na ce amin. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Kafin su dawo ta sani na wanke fuskata nayi yar kwalliya, duk da fara'ar da nadingayi sai da yaya ya gane nayi kuka, duk lokacinda na kalle shi sai in ga idanunsa na kan fuskata har dai ya kare ya ce Sadiya kukan me kikeyi? Muka kalli juna da Anty abida ta ce, sam bata yi kuka ba me kagani? Yayi dan yake shi dole murmushi, ko ba jami'in tsaro bane ni, kun san daini ba yaro bane. Na share zan cen da cewa, yaya mu tashi dan yara na jira na in daukosu. Ya ce madan saurareni. Abida ta kalle shi ya ce, nifa bana son abin da zata shiga matsala, in auren nan zai kawo mata damuwa wallahi sai a fasa duk abin da zai faru ya dade bai faruba kowa ya ji cewa nayi wa wata ciki ta haihu, daga nan fa? Na runtse ido, don Allah yaya mu bar maganan nan, nace maka ba damuwa nake ciki ba, ka yarda dani. Usman ya ce aboki ina ga dai na dawowa da hannun agogo baya din nan a bar shi. Abida ta ce ai sadiya jaruma ce bata cikin wata damuwa, kuma malamai sun sha fada muna cawa in Allah ya rufa maka asiri yayin da ka aikata wani laifi to kai kada kayi kokarin tonawa kan ka don haka barin batuna haka shine mafi a a'ala. Haka dai muka baro gidan nasu bayan sun yi mana rakiya. Saty daya bayan nan suka shirya tafiya lagos, sai dai ban da ya Sulaiman saboda suna son yan da haduwar su da dangin mujidat zai kasan ce, haka nan basa son yanda ya Sulaiman ya san cewa dan da ta haifa na shi ne. Sun tafi da Usman da shi Aliyun da kuma Mujidat da Danta. Sai dai lissafin da aka yi masa ya same wuce hankali, domin ko auren Sadiya bai kashe wannan kudin ba, sannan kudin sa da ke accout yayi shirin siyan wani gida ne da aka yi masa tallansa can kasan su a sabuwar unguwa da ke nan unguwar Mu'azun. Ya kalli Usman ya ce aboki ni fa ba zan iya biyan wayan nan kudinba. Usman ya ce, to ka kirata ta fada musu baza ka iya yin al'ada ba. Ya kalli waliyin ya ce a kirata. Sai suka ce ai su al'adar su ba a magana da amarya sai su waliyanta. Usman ya ce to su basa yin wanan al'adar sadaki kawai zasu biya. Sauran suka ce sam ai tunda ta haihu a tasu al'adar yin biki dolene, kuma abubuwan al'ada dole ne, domin ita mai albarka ce mai haihuwa ce, sannan ba dama ya ce ya fasa tunda ta haihu. Shi da Usman suka kalli juna a ran shi ya ce lallai ya debowa kanshi ruwan dafa kanshi. Usman ya ce kawai ka basu inya so sai ka sai fili bana son a samu matsala. Nan dai ba da son ran shi ba ya amince bayan sun fita suka tafi banki in da ya ciro kudi suka dinga yi masa lissafi yana ba su, nan fa suka ce jibi za su yi hutu, suka amince a haka. Ni kam ko da suka dawo bai fada min ba gurin Anty Abida na samu labarid Usman ke fada mata, na ce shi dai ya sani can da yawarsa. Idanu na zuba ina kallonsa yau da na ga yanzun yana dan zakewa tare da rawar kai, sam ban zata ba, ya sa a yi gyaran gida. An yi fenti na kwashe kayan yarana daga dakin da ta zauna tunda nan za'a sa ta, ya ce da ya so canza min gado,amma in yi hakuri ko daga baya ne. Yaba ni dubu talatin,na yara ashirin na karba na aje tare da cewa mun gode. Na dauki waya ta ina dannawa ya ce, Wai Sadiya akwai wani laifi da nayi makine?na kalleshi' Me ka gani? Ya ce, Na ga tun jiya da na zo ba wata fuska a gurinki?Na maida kaina ga kallon wayata,sannan na ce, Akwai abin da ban makaba daga cikin wanda na saba yimaka?Yace, A'a,kin min komai MY CHOICE, sai dai ni na gane kamar ba ki da walwala. Na ce, Ba ka yi min komai ba. Ya ce, To anjima zan tafi, Na ce, Allah ya kai mu. Har ya kai bakin kofa na ce, Au! Na manta in fada maka an dauke ni amma ba aprimary ta nan unguqar Ma'azu ba, ta can Tudun wada. Ya tsaya yana kallona, nima shi nake kallo don son jin ta bakin shi,a zuciyata ina cewa yanzun dai a ce ya hana ni, tabdijan! Da sai ya ji magana. Tamkar ya sani sai ya ce na san kina zaton zan hana kineko? Ai ba ni da yanda zan yi tunda na rigana yi miki alkawari,amma ki sani raina baya so. Ban ce kala ba na ci gaba da danna wayata shi kuma ya fita. Ban tabbatar da cewa ina da kishi ba sai da lokacin auran ya gabato,wallahi ko abinci kasa ci nayi duk datausar da Aisha ke min da kuma Anty Abida dan ganin na kwantar da hankalina, amma na kasa, bana bacci sosai duk da cewa bana nunawa Yaya damuwata sai dai shi duk lokacin da muka yi waya sai ya yi min korafin in daina damuwa in kwantar da hankali,To kurum nake ce masa, amma zahirin gaskiya zantukansa ma soya min rai suke yi. Ana gobe daurin aure zasu tafi can Lagos din ina kallo shi yana ta shige da fice yana shiri,an zuba sababbin dinkuna an sai Huluna da Takalma sai ina mamakin mutumin da na dinga shan kan shi da kyar shi ne yake zumudi. A fili na ce Allah yasa abin ya tsaya nan. Ya fito cikin shiri ina kwance kan gadon yara ya ce 'My Choice mun shirya,na dago na kalle shi, yayi matuqar kyau cikin Shadda Wagambari Blue shar kaladaya da hularsa mu hadu a banki, kamshinsa ya cika gidan, kishi ya kama ni mai tsanani,na kau da kai gefe. Ya ce, 'My choice yaya ne? Ban tanka masa ba sai zuciyata ta ce gwada shi ki gani da yake cewa in na ce ya fasa zai fasa,in ya so duk ma abin da zai faru to ya faru. Ya tallabo fuskata. 'My Choice, yaya ne? Na ce, 'Ni fa gsky na sake tunani a kan wannan auran, gaskiay ina tsoron abin da zai biyo baya. Zai fi kyau a barshi. Zumbur ya mike tsaye daga russunawar da ya yi, na kalle shi ga mamakina fuskarshi daure, ya ce, 'Me ki ke nufin maidani? Karamin mutum? Kin sa mun yi magana yanzun kuma kizo ki ce ke kina jin tsoro, ya kamata ki fadi haka ne tun kafin yau, sai dai ki yi hakuri,mamakida tsoro suka sa na kasa daina kallonsa sannnan ga hawaye yana ta zuba tamkar an bude famfo, na girgiza kai tare da sauke ajiyar zuciya,sai kuma ya zauna kusa da ni tare da dafa kafadata. My choice bana nufin cutar da ke kece kika karfafani kika nuna min yin auran nan shine mafita, to me zai sa yanzun ki bijiro min da wani sabon batu bayan aski ya zo gaban goshi? Kuka ya kwace min na shiga rera shi, tsam ya makaleni jikinsa yana lallashina. Sadiya in kin ce baki so wallahi abar shi. Ya ciro wayar shi yasoma dannawa. Bari na fadawa Usman ya kira Yaya Sulaiman ya fada masa cewa nafasa.ina jiyo shigar wayar ta soma ringing a can,da sauri na dago na amshi wayar da sauri na katse. Ya ce, yaya kuma za ki katseki bani in dakatar dasu su daina shiri. Na cecikin shagwabar kuka, Ni fa ban ce ka fasa ba.yasa hannunsa ya dago fuskata,To me kika ce?Na kalli cikin idon shi 'In ka aure ta zaka daina sona? Sai kurum naji bakin shi cikin nawa, minti1muka dauka, sai wayarshi ta shiga ruri,ya sakeni tare da daukar Wayar. Usman ina zuwa. Ya katse ya kalleni. My Choice in na yi rantsuwa bazan yi kaffaraba Ke ce 1 tak nake so, kum na soma son ki ne tun lkcn da kika soma zama mace. Da farko ban fahimci ina sonki bane sai da Usman ya kwadaita mini da nazo iya ta ki sai na samu kaina da kasa hakura, wannan ya tabbatar min cewa ina mutukar sonki,Ke ce zabina, kada ki damu da Mujidat sam ba na son ki hada son ta da naki, Ke ba ita ba in miki ta mahaukaci duk duniya ba wata mace da nake so ko kuma zan sota sama da ke, ki rike wannan a cikin zuciyarki,so 1 tak Ke na ke yiwa shi.,lumshe ido na yi inma karya Yayaya fada min to na yarda don gaskiya maza da ace zasu gane furta son ka ga matar ka komai dadewar aurenku yana susutar da mace komai shekarunta ta ji ta tamkar sabuwa,amma matsalar maza musamman irin na yankinmu ba sa iya cewa matar su suna sonta, ko wasu kalamai na soyayya irin wanda suke yi mata yayin yakin neman aurenta da zarar sunga cewa sun aurenta shi Kenan ta tsufa Nima haka na ji tamkar farkon aurenmu duk damuwar dake cikin zuciyata sai ta gushe, sabida ina son a so ni,ina son a nuna min soyayya, ina son a fada min kalaman so. Nasa hannu a kumatun shi na shafa ina kallon cikin idon shi, Yaya na gamsu da kalamanka, Allah ya tsare hanya gobe zaku dawo? Ya ce, insha Allah ko jibi, tunda da nisa in mun taso da yamma ko da dare sai safe zamu iso. Na ce shi Kenan. Ya mike tsaye, me zan sayo miki a can? Na ce, gdnsu lesuka, in ka siya min zanyi murna. Ya ce insha Allah zan zabo miki masu kyau. Na ce to nagode. Har waje na raka shi. Sai dai duk da haka kasa bacci nayi daren ranar sai damuwa da sake saken zuci. Washe gari kuwa data kasance ranar daurin aure ba zan iya lissafa tashin hanklin da na shiga ba. Da safe kasa zama na yi a gidan na tafi gidan Iya wai don in manta da batun auren amma duk da haka na kasa sukuni, har Iya ta fahimta, sai kurum naji ta ce. Sadiya, hakika kishi wani abu ne mai rai, amma yana da sauki in kin saukakashi, ina son ki nutsu ki rike girmanki. Shawarar da zan baki ki kara zage damtse gurin kyautatawa mijinki kada ki dauki halayen wasu matan masu cewa in miji ya kara aure zasu daina yi masa komai suce ya je can matar da ya auro tayi masa, wannan kuskure ne, don in aka samu wadda ta san hannunta kafin ki samo mijinki sai wani ikon Allah,ki zama a gidanki Ke ce uwar kowa. Ina nufin duk abinda ya taso na kudi ko matsalar lalacewar wani abu a gida Kar ki tsaya jiransa kiyi da kudinki in yaso in yazo kya karba ko yaturo miki, sannan ba'a fata in har sabani ya shiga tsakaninki da ita tunda an ce zo mu zauna zo mu saba, to kada ki sake ki fara kai kara Kinji ko? Na ce, to. Yauwwa sabida in kinyi nazari cikin ya'yanki mai yawan kawo kara duk gaskiyarshi sai kinji haushinsa. Na ce, haka ne. To ki rike hakuri da addu'a ki dinga yawaita karatun Alkur'ani mai girma, ki zauna da ita zuciya1, sannan ga aikin ki ma, ai ni naji dadin barin ki da yayi wannan koyarwar, na ce, nima naji dadi iya, don ina da yara gara dai yanzu da muke mu 2 aikin ya dauke masa matsalolina in ina samu ba sai na jira shi ba, kudin da ya bani ma nawa da yara wai muyi siyayya su dai na Dan sai musu wani abu, so nake in hada jari in dinga saye da siyarwa. Iya tayi dariya tare da cewa, da kyau Sadiyayyena. Haka nayini Iya tana kwantar min da hankali tare da bani shawarwari sai kusan 10 na dare na debi ya'yana ta raka mu har gida, nima na sake rako ta hanya.ina sa hakarkarina a kan gado na dauko wayata nakunna dama yinin ranar kashe ta na yi. Nan fa sakonni suka soma shigowa na yaya sai na Aisha da Anty Abida, na su na soma dubawa. Tanbayata suke ina naje sun zo ba nanan? Na yi dan murmushi, a fili na ce da kun zo gidan Iya ni kam ba zan yi wani taro ba, sai na soma duba nashi,duk kusan yana nuna damuwane akan ya kira bai sameni ba. Sai na karshe da yake cewa sun taso 9 suna hanya, akwai yiwuwar su iso kafin 9 na safe, kuma suna tare da wasu daga danginta dan Allah ta tanadar musu abinci. Kiran Abida ya katse karatun sakon da na keyi, na daga muka gaisa, ta ce min, ina na shige yau? Na ce ina gidan Iya,tace to, ki yi sammakon tashi don mijinki zasuyi shigowar safe ne, nace Anty me zanyimusu?tace karin kumallo mana kiyi zuciya1 kada ki sa kishi ciki, bakin kine, kin kuma san darajar baki a musulunci. Na ce to Aunty zanyi. Tin 4 na tashi na fara firar dankali da nayi sallah kuma na hau suya, har kaji biyu nayi musu farfesu, kwai ma isasshena yi musu kwai da kwai na dafa ruwan tea mai yawa, sannan na gyara gidana nayi wa yara wanka na zabo musu sababbin kaya nima na sheka nawa adon. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Takwas daida na ji tsayawar motoci,gabana ya yanke ya yi wata muguwar faduwa,sai na hau karanta Hasbunallahu wa ni'imal wakil. Na mike na je na bude musu kofa gabana yana ta faduwa,zuciyata tana maimaita addu'a.suka shigo suna yi min sannu, wasun su suna kallona wani iri,amma duk da haka na saki raina ina yi musu sannu da harshen Turanci.Najee na bude musu dakin suka yi sororo a tsakar daki don ga al'adarsu miji ke shiryawa mace daki ya zuba komai, ita kuma iyayenta su yi mata kayan sawa, nan fa suka soma yare, duk da bana ji amma ganin yanda suke magana suna tabe baki na fahimci zancen nasu bana dadi ba ne, naje nasoma fito musu d kuloli. Sai gasu Yaya sun shigo, na kirkiro fara'a ina yi musu sannu da zuwa. Falo suka je suka zauna na gabatar musu suma da abin kari, na kula yaya ya ji dadin yanda na saki jikina na kuma yi musu abin kari.Nan nabarsu nayi daki,bayan Mujidat da danginta sun gama karyawa sai suka samu su Aliyu da Usman suna yi musu korafin ba su ga kmai a dakin ba.Usman ya ce, Mu a nan da kaya amarya take zuwa. Suka ce su kam ba haka ba ne, nan suka fito masa da akwatunan amarya har da na mijin da na Maman shi da kuma na danginsa. Aliyu ya ce shi kenan zai siya daga baya, amma yanzun a kwaso na dakinsa a sa mata,sukace bakomai. Ina dakin nashi ya shigo wanda zuwa yanzun ya zama nawa,ya zauna. Sadiya kin ji wata sabuwa. Na kalle shi, ya ce, Wai ni zan sai mata gado. Na ce, ina zaton haka al'adar su take don mun taba yin zancen da wata 'yar ajinmu da muka yi N.C.E take ba mu labarin al'adunsu, miji ke yin kayan daki kuma sadakin su yana da tsada, amma mace za ta ja jari da su ita ce za ta rike gida,wasu kuma jarin daban miji zaibada, wadanda ba Musulmi ba sun fiyi, Musulminsu kamsai sunyi aure suke tarewa gidan mazajensu,yace,nidai yanzun ya za'a yi? Na ce su zo su dauki wannan gadon. Na tsura masa ido cikin mamaki,sai ya ce, ko ya ki ka gani? Na mike na nufi dakina bayan na ce, Me zan ce kai da abinka. Na shiga dakina na soma kallon dakin ina lissafa yanda zan gyara shi ni da yarana da na bar musu gadona tunda dama katifu gare su. Sai ga shi ya shigo.Haba Sadiya,me zai sa ki yankemin wannan hukuncin? Nazo miki da shawara amma sai ki yi watsi da ni kitaho abin ki? Na ce, Yaya kainefa da abinka kuma ka ba matarka, mene ne laifina dan na taho? Yace, Ok, kije amma ki sani kada nan gaba ki ce na daina kawo miki Shawara,kin sani dai ke ce kurum nake tunkara da duk matsala ta. Shiru na yi dan nasan in hakan ta faru lallai ba zan zama uwar gidaba. Ya mike zai fita na ce, Yaya'' ya dawo,Mene ne? Na ce, Shi kenan ka yi hakuri. Ya zauna tare da kamo hannuna, Nagode da ki ka fahimce ni, yanzun ya ki ke ganin za'ayi? Na ce, Ka ba ta,ni kawai sai naringa kwana a nan da yarana. Ya tsura min ido, To nifa? Na ce, Ba komai ka yi ta kwana dakinta. Ya yi dan murmushi, Har yanzun baki huce ba.Na yi 'yar dariyar yake, Bana fushi da kai. Yace, Zan siyo katifu yau a sa can dakin in komai ya warware zan canza gadajen gidan.Na ce to maimakon ka ba ta tsohon gadon ba gara ka sai mata katifar ba? Amma yanda ka gani, Ya ce na riga na fada musu ne na ce to su dauka bari. In zo in kwashe kayan na wardrobe din. Ya ce, A'a, gado kawai da katifa za ta dauka. Na ce, Shi kenan, Allah ya rufa asiri. Ashe tashin hankali yana gaba,sai lokacin bacci, Mujidat ta kira shi a waya wai tana jin bacci, ya kalle ni muna zaune kan gado,sannan yaci gaba da magana. To ki kwanta mana. Ta ce, Ba dakin ka zan kwana ba? Ya ce, A'a yanzun bani da daki in danginki sun tafi na kwana adakinki. Mamaki da haushi suka cika ni, ga kishi kamar in hade raina, na ce, Kuje dakin naka mana? Yaja tsaki tare da cewa, Don Allah ki bar wannan maganar. Na kwanta tare da juya bayana na rungume yarana bankara sauraron shi ba, shi ma ya kwanta a daya gefen Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Washe gari tun Asbahi suka soma shiri,suna karyawa suka tafi, wata daya ce daga cikinsu kadai ta yi min sallama da godiya, suna kama ina zaton yarta ce dake illorin din, domin nayi dawainiya dasu sosai ta fannin abinci. Ya tsaya da su sun shiga gurin Iya sun gaisa duk da cewa ba sa jin yaren juna, sannan ya wuce dasu zuwa gareji. Ranar ne matan Yaya Sulaiman da su Anty Abida sukayi ta zuwa ganin Amarya. Anty Abida ta yi ta yi min fada wai ya zan sa abu a cikin raina ga shi nan duk na rame, na ce Anty dole in sa a raina, ba za ki fahimci zafinkishi ba, duk irin bayanin da zan yi miki, kuma bana fatan a yi miki ki ji.Anty Abida tace, Ameen,don Allah ina son ki saki ranki. Amarya dai tana daki bata fito ba, da za su tafi na raka su ganin amarya ta ci rigarta da wando na bakin Jeans, danta yana cikin gadon shi ta yi ruf daciki kan gadon da suka kafa tana chatting, a yatsine ta amsa sallamar,sannan aka gaisa,suka yi fatan alkhairi suka fita. Daran ranar ne ya hada mu a falo yana yi mana nasihar zama lafiya, sam ban san me yake cewa ba, ina can gurin tunani. Yau ga shi abin da nake karantawa cikin littattafai ya zo kaina, ji nake tamkar cikin mafarki, ashe dai nima za a min kishiya. Girgiza nin da yayine ya sa na dawo cikin hayyacina,cikin damuwa ya ce, Menebe? Na girgiza kai ba komai. Ya ce, ina tambayar ki game da kwana,na ce, Nawa nawa? Nayi hamma kirkirarra, sannan duk yadda kace. Ya ce, To a bar shi bibbiyu kamar yanda aka fi yi. Na ce shi kenan. Ita dai tana ta jijjiga danta,na sake kirkiro hamma, zanje in kwanta bacci. Ya kalli agogon bango; Da wuri? Na ce, Na gaji ne. Na kalli amarya wadda ta sha leshi kai ya ji gashin doki ya zubo har kafada, na ce, Sai da safe,ta dube ni da 'yar yatsina eh, dama ban jira amsar ta ba na yi tafiyata. TABDI! Daran ranar kasa bacci na yi har zuga ni zuciyata ta dinga yi wai inje in labe inji me suke yi, amma sai na

Chapter 15 of 25