Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Ga mamakina sainaga yazube gabana gwaiwa biyu biyu yanacewa, "Sadiya dan Allah na rokeki ki yafemin kidawo aurena wallahi ke kadai nakeso,kanki nasoma sanin wacece mace, dake kadai nake samun nutsuwa, Sadiya ki amince kiyimin takaba." "Takaba kuma?" "Inna nufin kikoma gidan har inmutu kiyimin takaba." Na tabe baki,"ga Mujidat can zatayimaka takaba ni bazan iya zama dakaiba," nasake juya baya, sainaji muryar Khausar, "Dan Allah Mama dan girman Allah mamanmu," nace nifa bazan koma wani sabon gidankaba bare aurenka inkamanta abindakayimin to ni banmantaba, yamike, "ke wace irin zuciya gareki bayan na kaskantar da kaina na rusuna a gareki akan kiyafe kidawo kince a'a to bari kiji dole nema ki Koma gidan," nace, "bazan komaba" Yace, "to ai nanma gidan ubanane,meye banbancinsa da nawa?" Na kalleshi cikin bacin rai, "dadin abin nima ubana yanda gidan, kuma zankoma yanzunnan." Nasoma hada kayana, da sauri yafito yana fadawa baba Hauwa wainace zantafi gidan banana, sai gata tashigo, "haba Sadiya, me yayi zafi haka," "Gorin gida yayimin, dan haka zan tafi gidan ubana," "inkinyi haka kuwa iya bazataji dadiba," nasoma kuka to Baba Hauwa duk yatakuramin, ina ruwansa dani? gara intafi abuna." Tace, "ba inda zakije, kuma yanzunnan zamu tare a sabon gidan idan na isa dake, inkuma taurin kan zaki nunamin ina yabinki to bisimilla." Shiru nayi dan babu abinda natsana a duniya irin babban yaga na raina shi, banson ayimin shaidar rashin kunya, inna kuka riris Muka shiga Mota zuwa gidan da yaya ya ginamana. Sam barka,gaskiya gidan ya tsaru. Abin mamaki can Muka samu makotanmu sunje kallon gidan, inna zaton Yayane yasa Habu yasanar musu zamu tashi. Anzuba komai sabo, tafkeken falo da dakuna hudu, nawa dana Iya dana yara,sai na baki. Can gefe ga wani gini, dana tanbayi Habu sai yacemin na megidanne in yazo hutu, "muje kigani." Nace bazaniba. yara kuwa sai murna suke suna tsalle ga kayan wasansu nan kala-kala. Bayan kowa ya watse na daga waya nakiraki Aunty Abida inna gayamata yanda mukayi, tace zatazo, A'isha ma haka. Inna kitchen dinmu mai dauke da kayan girkin zamani, inna yiwa yara abincin tafiya makaranta, dayake da safene, zani na daura akan rigar baccina,Sai hula akaina, sai naji maganar Yaya a bayana. "My choice, me kikeyine.? Nadafe kaina cikin takaici,na kalli jikina, yaci ace da hijabi a jikina, sabida kirjina yafito, dayake rigar tana da katon wuya, nace, " Lafiya?" Yace, "lafiyalau, nazo ingaishekine " Nace, "nagode, jeka." Ya iso daf dani, "kintashi lafiya?" "Don girman zati kafita, mufa musulmine, bai dace kazo inda nake cikin kowane yanayiba." Yace, "Ok! Hakane, sai anjima,amma ataimakamin da abin kari." Sabida yafita nace, " toh." Banyimasa abin karinba,ina sallamar yara nakoma na kwanta. Baba Hauwa tashigo gurin sha daya ta tasheni. "Kin karyane Halimatussa'adiyya?" Nace, "a'a" Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Alhajima yana ta shigowa, wai kin hadamai abin kari. Nace, "bazan hadaba Baba Hauwa, ni matarsace?" Tace, "amma Kanwarsace ko?" "Eh, amma banason wata alaka ta hadamu." "Aiko da alaka ta hada, 'Yaya hudufa, don haka kibar batunnan,abin karidai nayimasa, shine ma ya kunna kayan girkin." Nace, "ni bamanajin yunwa, sai anjima zanci na rana gaba daya." Tace, "to shikenan, Allah yakaimu." Can saiga Aunty Abida wajen karfe daya muna kitchen muna girki. Gaskiya tayi santin gidan, muna cikin hira sai mukaji sallamar A'isha, nan muka yini muna hira, dan ko dakko yara a makaranta Baba Hauwa ce ta dakkosu. Aisha tace, "Kyan gidannan kunmaida aurenku." Na daka mata duka a baya, "aniyarki tabiki." Abida tace nidai ba ankimuba, mene aibun mijina? Kin gwammace mai mata biyu da yara." Nace, "Haka nake sonshi." A'isha tace, "kikoma gidan mijinki Hajiyar Allah Ku rungumi yaranku." Nace, "Zanje in haifi wasu a can." Tace, "shikenan." Sun yini har dare sannan suka tafi,nakira Alhaji a waya nace mai muntashi har yakemin korafin Cewa bandaukeshi da muhimmancibane sai bayan muntashi sannan nafadamai? Nace masa, "tashinne yazomana cikin bazata, Yayane ya uzzura." Yadanyi dif, sannan yace, "nifa duk lokacin da kikace Yaya dinnan sai gabana ya fadi gani nakeyi kamar har yanzu kinasonsa ." Nace, "dan Allah adaina maida hannun agogo baya, ni bazan Koma gidansaba." Yace, "to zaibari inshigomasa gida?" Nace, "tinda yakawoni dole inshigo dakai." Yace, "a'a, bazan shiga gidansaba, in nazo kya fito. Ina kikacema gidan Yake?" "Nan unguwar mu'azune,Amma sabon gurine." Yace, "to zamuyi waya, anjima zanzo." Nace, "Allah yakawoka." Washegari yashirya zaitafi Abuja inna kwance kan gadona na saki A.C inna Karanta wani littafi maisuna Yayana safara na Asma'u Lamido sainaji sallama,kafin na amsa har yashigo, naja hijabi na rufe jikina, fuskata a hade na dubeshi. Dan murmushi naga yanayi, sannan yace, "menene Bako ake rufe-rufe?" Cikin zolaya yayi maganar. Nace, "aidai haramunne ka kalleni cikin wannan yanayin." Yace, "to nidai zantafi." Nacigaba da karatuna,kudi ya ajiye a gefena, bankalleshiba ballantana kudin, har yakai bakin kofa sai yajuyo yace. Karkijawa wani kato duka dan nacewa 'yansanda dake gadi su daki duk wanda yashigo gidan. Tsaki naja tare da cewa, "Dadin abin nasa gidan yafi Wannan." Bai tankaba yafita yabani ina ta fada. Kamar ance ya wai waya, Aliyu yaga Mujidat cikin mota tare da wani Mutum,kasancewar bata ganshiba, sai kurum yabi bayansu,dayake mota ukuce tsakaninsu, amma yaga Hotel din da suka shiga, shima yabisu, ga alama ba lokacin zasu kama dakinba,sun kama tuni, don baigansu nan gurin karbar bakina.(Reception) Yashiga kai tsaye yanuna katin shaidarsa ta zama Dansanda, sannan yayi tanbaya game da dakin da suka kama, yayimusu kwatance da motar da yagansu, har dakin aka kaishi, ya kwankwasa shiru, sai ya murda kofar, baizaci zata budeba,amma sai ta bude.Irin kamun dayayimusu ya kazanta,domin haihuwar uwarsu suke, sannan maimakon saduwa irin ta mace da namiji, sai yakamasu yana saduwa da ita ta dubura,wato luwadi. Wa'iyazubillah! Allah yayimana tsari da mugunji da mugun gani, Ameen. Salati Aliyu yasaka,Mujidat tayi wuki-wuki,Alhajin yasoma yiwa Aliyu fadan meyasa yashigo? Mujidat tace mijinane, juyawa yayi batare dayace kalaba. Ni naga yasake dawowa washegari da Abdul da kaya niki-niki,ko kallonshi banyiba,Baba Hauwa itace ta tare shi,itacema ta bawa Abdul abinci,nabar falon nakoma dakina, sai gashi cikin raunanniyar murya yace,"Sadiya inna maikara nemana afuwarki, jiya naga abin dayaban tsoro bayan komawata daganan, wai ashe har yanzu Mujidat tana bin maza, dumu- dumu na kamata da aurena akanta wani kato yana luwadi da ita." Na kalleshi cikin zaro ido,ban tankaba yacigaba. "Don Allah ga Abdul nan na rikeki kisakashi cikin 'ya'yanki, kodadai yazone ba tahanyar data daceba jinine, nasani bashi da gadona amma baidace inbarshi ya wulakantaba,donshi ba ruwanshi." Ya aje kudi a gefena. "Kisashi makarntar Isalamiyya da Boko wadda 'yan uwanshi keyi, nasan zaki iya." Duk bantakamasaba, har sai dayace "zakuyi kwanaki baku ganniba akwai aikine a hannu na kila ya daukeni lokaci, kiyimin addu'a." Na tabe baki, "Allah ya tare ." Yace, "nagode." Haka kuwa cikin kwnaki uku Abdul yasoma bin 'yan uwanshi makaranta. Aliyu wani course yaje na wata biyu India,Yasamu Wannan damarne daga gwamnati me ci a yanzu,yasan sunyi hakane Don ayi zabe baya nan,tinda yanuna baya goyon bayansu suyi yanda suke so, shikuwa ya karbi wannan dama da zuciya daya, dankuwa ba kowane dansandane ke samun wannan damar ba. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Su Iya sun dawo, muna ta murna,kullum gidanmu sai yacika da Iyalai da abokan arziki, anata rabon tsaraba, abakinta nakejin inda Yaya Yake. Baba Hauwa daki daya muke kullum sai tayimin zancen Yaya tayi ta kwarzantashi tana bani shawara har abin ya isheni nagudu dakin yara, suma suka isheni da tanbayar ina Abbansu, nace bansaniba kuma kada wanda yasake tanbayata. Iyace kurum ke goyon bayan aurena da Alhaji, ni dama tsarabar zannuwan gado yayomin sai Jallabiyya. Kwanci tashi saiga Yayay kamar daga sama,duk dacewa natsaneshi bankasa ganin kyawun dayakaraba, har da dan haske, a raina nace anje course ko anje Hutu?......zandakata anan, Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Darajar Yayana4-05 Posted by ANaM Dorayi on 02:28 PM, 20-Apr-16 Under: DARAJAR 'YA'YANA __________________NA ___________HALIMA K/MASHI Assalamu'alaikum, kuyimin afuwar shiru da kukajini, hakan yafarune sakamakon tsaiko dana samu sabida wasu dalilai,saidai yanzu nayi yunkurin kawomuku Babi na karshe fatan kuna tare dani, inna kuma fatan kuna sane da inda muka kwana... Tsarabar daya kawo dan gulma harda ni,banki karbaba, Pakistan yakawomin kala shida masu kyau sosai, zanyi gayuna a gidan Alhajina, ga turaruka masu tsada. Yara kam ba'a magana harda yaran Usman. Ba'ayi wataba sai karin girma zuwa matakin kwamishina 'yansanda na jihar Kaduna, anyi biki tare da duk wani abu dayakamata,. Tuni yatare a gidan kwamishinan yansanda dake kaduna. Sai naga antilomana wasu yansanda wai masu tsaron lafiyarmu. Tinda Yasamu wannan matsayin saikuma ganinshi yayi wuya,baya zuwa gida ya kwana kamar da, sai da daddare jefi-jefi yazo yagaida iya yatafi. Hidima kuwa baifasaba, saima karawa da yayi. 'Ya'yansa yana aikowa a daukesu ranar da babu makaranta su yini can, ko zama yakeyi dasu, komenene bantaba tanbayarsuba. Daidai wannan lokacin na yaye Sadiq, kuma muka tsaida lokacin aurenmu. A lissafi yau saura kwana ashirin da takwas,inna ta shiryeshiryen gyara jikina da duk wani abu nasha wanda zan rike mijina,dan kuwa Aunty Abida zugani kawai takeyi indage innada kishiyoyi,cikin dan lokacin ni dakaina nasan nayi zam-zam. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Direban dake zuwa daukan yara yakaisu gun Babansu nagani tsaye nadawo daga makaranta yace, "Madam ance in kaiki Gida." Nace, "Inji wa?" Yace, "inji mai gida," Tsaki naja nace, "bazanjeba." Kasancewar layin shiru sai tsoro yakamani, yace, "Kishiga kawai da arziki Madam, sabida kalli can." Yanunamin Karshen titin, motar 'yansandace. Yacigaba dacewa. "Zasu daukeki da tsiya." Nace, "ai da kukuke kaini gidan?" Yace, "Umarni akabamu daga yau, shiga muje kawai." Nace, "Innakifa?" "Hakuri zakiyi ranki ya dade,sabida kare lafiyarkine." Nace, "Allah ke Kare lafiya ta." Yace, "To kitemakeni kar inrasa aikina." Cikin muryar tausayi yayi maganar. Nace, "zanshigane don aikin naka,amma badan isar wanda yaturokaba. Yace, " Nagode ranki ya dade." Tinda muka hau titi 'yansandannan suka dafemana baya, haushi duk ya isheni. Munyi tafiya me tsayi kafin na fahimci cewa ba a hanyar gidanmu muke tafiyaba, Nace, "ina zaka kaini?" "Gida mana." Daidai lokacin naga munsha wani round about, kafin nasake magana muka shiga wani layi muka hari wani babban gate, Nace, "Mallam ina zaka kainine?" Yansanda dake kofar gidan suka bude muka shiga. Gidan yanada dogayen bishiyoyi, dankuwa girman gidan bazan iya musaltashiba,inna cikin motar naki fitowa, wayata tasoma ringing, Bansan lambarba, na daga, muryar Yaya naji yanacewa. "Karki zubar da kimata kishigo magana zamuyi kitafi abinki." Ban musaba nabi bayan direban kamar yanda ya bukata. Cikin wani kayataccen falo nasameshi Zaune kan kujera daya daga kujerun falon na Alfarma, Laptop ce a kan wani tebur a gabanshi yana latse latse.jikinshi sanye da wata shadda ruwan kasa wadda haske da kyanta suka tona asirin tsadarta,kamshinsa na yau da kullum yacika gurin. Batare da yadubeniba yanunamin kujera da hannunsa Yace min cikin harshen turanci, "Zauna." Ba musu na zauna, saidai raina a bace Yake, Jira nake yayi magana insoma zubar da bala'i. Yanata danne dannenshi, na dubi agogon dake falon nace, " Gaskiya innada abinyi, innason intafi." Ya dago ya dubeni kibani minti uku kacal in kammala muhimmin aikina." Naja tsaki tare da kauda kai. Wayata tayi ringing, nadauka A'isha ce,nace, "ya akayi?" Tace, "ga Humra ankawo me kyau," nace, "cikon nawa zanbada?" Tace, "dubu ukune, namabada, dama gudun mowar dazanbakine." Nace, "a'a A'isha zanbaki kudinki, nasanfa yanayin garin." Tace, "Kin raina kenan?" Nayi 'yar dariya, "wallahi ni banrainaba Nagode Allah yabar zumunci, zanfadawa Alhaji kokarinki." Mukasa dariya. Tace, "kina inane?" "Oho! Ni banmasan inda nakeba, kibari innakoma gidazamuyi zancen." Na kalli agogo, minti ukun tacika, yature na'ura me kwakwalwar dake gabansa yamike a hankali yazago gefen danake, kafafunsa babu takalmi. Yazauna a kujerar dake daf dani ya karkato. "Sadiya!" Yakira sunana cikin lallausar muryarsa, nasake tsuke fuska, yacigaba. "Sadiya meyasa kika zabi ki auri wanina? Bayan nasan cewa ni kikeso" Da sauri nace , "a daba, lokacin da bansan inda kemin ciwoba,amma yanzu gaskiya bana wani sonka." Yayi dariyar yake, "nasan kinfadane amma in gaskene ki kalli cikin Idona kice bakyasona." Cike da rashin kunya na kalli idonshi, "Aliyu bana sonka, bana kaunar......" Yadagamin hannu tare da rintse ido , " naji nayarda bakyasona,amma kiduba wasu abubuwa. Nafarko, 'ya'yan dake tsakaninmu, kinfiso kije ki kula da nawasu kibar naki? Bansan wace mata zan auroba, ke nifa tinda Mujudat ta wahakar da yarana na janye batun aure indai bakebace." Nace, "wannna ra'aynka kenan, ni nawa ra'ayin na auri wanda yasan kimata da darajata, wanda zaimin adalci akan komai." Yace, "Sadiya dan Allah kitaimakamini, wallahi inna sonki, haka zaki tafi gurin wani kibarni? Kinsandai yanayina kullum cikin Azumi nake, sabida tsoron fadawa barna." Nace, Aliyu kayi hakuri, kanemi wata, gaskiya bana sonka,tini kagama fita daga raina." Namike. Sai kawai naga yazube gwiwoyinshi a kasa, "Sadiya kitaimakeni bandamu cewa kowa yaganni a gaban ki a hakaba, indai zaki amince. Sadiya inkincire soyayyar Allah da manzonsa, sai mahaifiyata kece kike bayanta, don Allah kitaimakeni kisake bani dama, zanrikeki da kyau, namiki alkawarin zanzama tamkar bawanki." Nace, " kai bame cika alkawaribane, akwai alkawurra dakayimin tun a baya wadanda baka cikaba, nifa gaskiya banajin zan kara rayuwa irin ta aure da kai, muyi zumunci kawai na 'yan uwantaka." Sainaga kwalla tasoma sakkowa daga idanunshi, ya mike tare da juyamin baya, " Matsayina,mukamina da Shekaruna duk na karyardasu na durkusa miki, amma kin kunyatar dasu." Nace, "Kaine kaja." Ya isa kan tebur yaciro tissue ya goge hawayenshi, yadaga waya yakira direban, ya dubeshi, "kaita gida." Na mike na fuce, sam banji tausayinsaba ko kadan a cikin raina. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Shi kuwa sintiri ya dinga yi cikin falon cikin tsananin damuwa, duk yanda yazaci zaisha kan Sadiya abin yaci tira, saidai bayajin zai iya hakura da ita. Zumbur ya mike yayi hanyar fita yakira direbansa, yasa takalmi da Hula ya debi kudi ya zuba s cikin aljihu yafita. Zari'a yanufa, yaci sa'ar samun Baba a gida. Suka gaisa, Baba yayi ta murna da zuwan Aliyu, 'yan uwansa sukazo suna kara yimasa godiya game da aikin hajjin da sukayo, Aliyu yace bakomai. Yakalli Baba yace "Baba dama nazone in nemi wata alfarma a gurinka." Yace, "Kamar mefa?" Yace, "Innson in maida Sadiya mu rike yaranmu, nabi ta iya, yarinyar kuwa har durkusawa nayi a gabanta amma taki." Ya karonto masa irin azabar da yaran sukasha a hannun Mujidat, da matsalolin da suka shiga sakamakon rashin kasancewarsu tsakanin uwa da Uba, har yanda Mujidat ta shiga harkar banza da irin kamun da yayi mata, yakara da cewa, " nayi mata saki biyu, don na tanbayi malamai sunce yin uku babu kyau." Baba yace, "dama kanason maidata kayi shiru aka karbi batun wani? Amma kabari InshaAllahu dakai za'ayi domin dama ni mutuminnan bai kwantamin a raiba, saboda bai taba zuwa yagaisheniba, tinda yaturo wakilabsa, bawai inna neman wani abun hannunsa bane, amma mai son auren yarka yakamata yakawo kansa gurinka ku gaisa, kodon haduwa a hanya. Karkadamu kakoma zanzo gidan gobe." Aliyu yacikasu da kudi yatafi zuciya fal murna. Nikam inna ta shirina, iyace kurum me tayani, amma Khausar ko zancen bataso. Washegari Lahadice, inna kwance daki yara suna hadda, najiyo muryar Baba cikin Falo, sama sama yake magana, nafito da sauri nashigo falon, daidai lokacin dayake cewa. "Don ni indai ni na haifi Sadiya to takoma gidan mijinta shine albarkata, ta rike yaranta, ai banzaci yana ta bintaba da yaushe zan amshi batun wani, wanda ma ban isa yazo yagaidaniba, matsayin mahaifinta." Cikin sauri na zube gabanshi, "Baba wallahi dama gobe zamuje yagaidaka." Iya tace, "nima zanfiso suna tare da 'yan yaransu, amma Aliyu yasaki damarsa tin farko, don haka ni duk abinda Sadiya takeso nima innasonshi," Na mike nakara kusanto Baba, "don Allah Baba ka taimaka." Yace, "inni na haifeki to kikoma kirike yaranki." Ya mike. "Ranar da akasa ta auranki babu fashi, amma da Aliyu za'a daura." Na kalli Iya, "kinfayi rantsuwa akan bazan komaba." Iya tace, "Mahaifinki ya nuna ikonshi natsaya inyi ta jayayya? In takasance yanda yakeso zanyi azumin kaffara guda uku." Fuuu! Nayi daki,wato iya madai danta takeso baniba. Nakira Aunty Abida a waya inna kuka na fadamata, nace yanzu anyimin adalci kenan? Tace, "Eh!, wannan shine adalcin, ki zauna ki rike yaranki shine daidai, kiyi hakuri da rayuwa duk inda kikaje shine jagoran zama ballanatana tsakanin kishiyoyi ." itama na kashe waya kafin takarasa abindatake cewa. Bankira Ayshaba dan nasan ita yar partyn Aliyu ce. Na kira Alhaji inna fadamasa cewa Aliyu yaje ya zuga Babana bansan me yafada masaba. Sai kawai mukaga yazo wai inkoma gidana.yayi shiru yanaji har nagama,bayan kusan minti biyu sannan yace, "Shikenan Allah yasa haka shine mafi alkahairi." Nasaka sabon kuka , "Haka zakace kaima? Dama ba sona kakeba?" Yace, "Inna sonki mana, ammafa ni ba yaro bane da zan tsaya inna jayayya, sannana tini jikina ke bani gidanki zaki koma, Allah yasa haka shine mafi alkhairi." Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ranar yini nayi kuka har yara suka dawo, Khausar da Al'amin suka tsareni da tanbaya , haushinshi yasani jin haushinsu suma, nace, "Ku fita ko inyu muku dukan tsiya," suka fita sukaje suna tanbayar Iya. Iya tace, "wai dan kakanku na Zariya yazo yace takoma gidan Babanku." Sai iya taga yara sun soma murna, Khausar me wayon tsiya sai ta saci wayar iya ta nufi dakinsu ta kira layin Babansu, Cikin murna tace, "Abba innayimaka murna, ashe Momy zata dawo gidan ka?" Yace, "Eh, Babyna. Ina Maman naku yanzu?" Tace, "gatacan daki tana kuka,dan Allah kada ka karayimata abinda zaisa kuyi rigima." Yace, " To Khausar zan kiyaye, kije ki lallasheta," Tace, "To." Tana aje wayar yayi murmushi, yarinya yar shekara tara da rabi wayonta kamar na manya. Yashigo, "Momy inji Abba wai yana gaisheki,yace kiyi hakuri kidena kuka."Tsawa na dakamata ta tashi, ga mamakina sai naga tana dariya. Cikin dare naga sakonsa, wai: Saura sati uku ko? Nakosa inrike lallausan hannunki, My choice ya kike ganin darenmu na farko zai kasance? Inna jiran amsa. Tsaki naja na goge sakon. Shida na safe naki tashi infita,sabida inna fishi da kowa na gidan, wayata tasoma ruru na duba, koda banyi saving number shiba nasan yayane, don haka naki dagawa. Kiranshi goma inna lissafawa, sannana sako yashigo. My choice kiyimin addu'a zantafi wani daji dakaina zan jagoranci yarana don cafke wasu barayin dana gano suna tare da tsohon kwamishinan da aka canza daga Kaduna. Nafadamikine ba dan wani abuba sai dan kila bazan dawo ba, nafitane a bakin raina. Shiru nayi, dan kalaman sun tsirka zuciyata kadan, amma duk da haka sai na tabe baki na ture wayar. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Tamkar almara karfe goman dare na jiyo muryar Usman a dakin iya, can sai naji tana salati na fito ina tambayarta lafiya? Tace, "Aliyu ne wai yan fashi sukai masa harbi uku, amma dai anyi nasarar kama wasu, sannan aka harbe wasu." Take zan tukan da ya turo min dazu da safe suka fado min, na zauna kan kujera nace, "Iya yanzu yana ina?" Usman yace, "an tafi dashi Abuja babban asibiti." Kai gaskiya hankalina yayi mutukar tashi, cikin daren nayi ta kuka amma bazance ga dalilin kukanaba. Washe gari su Usman da sauran yayyanmu su yaya Sulaiman suka kwana acan sannan suka dawo, sunce an cire masa harsashin amma ba'a bari ma anganshiba saboda tsaro. bance zanjeba amma zuciyata tana can. Satin shi daya iya ta matsa zataje ta dubo shi, ya samu sauki sosai sannan hankalin iya ya kwanta. Data dawo nace, "ya jikin?" Tace "da sauki,ana dai bashi kulawa ne." Nace, "masha Allah." Ban ko kirashi ta waya ince ya jiki ba harya dawo gida, satinshi biyu da kwana biyu wanda ya rage saura kwana biyar aurenmu, nan gidan aka kawo shi can shashinshi. Su Baba Hauwa sunzo duba shi shine yake bata labarin ban taba ce masa ya jiki ba, tazo tana yi min fada. Su Abinda da Aisha kuwa gaba suka dauka dani. Iya dai bata taba ce min inje ba niko zuciyata ta kekashene ina saran zaice ya fasa tunda na nuna masa kiyayya karara. Washe garine ya tako zuwa ban garen mu ina zaune a falo ina kallon T.V ya shigo, yadan rame kuma yayi haske, yace, "ina kwana?" Na kalle shi cikin jin kunya nace, "lafiya, ya jiki?" Yace, "au ashe kinji, koda yake nasan kinso ace na mutu ko?" Nace, "duk wanda lokacinsa ya yi babu kari, harni din." Bai sake magana ba ya shige wajen iya, ina jiyo muryar ta tana cewa na zaci za'a daga bikinne,shi kuma ya ce a'a jiya su Yaya Sulaiman sunje Zaria sunyi magana da Baba, sunkai sadaki ya ce yau zaizo gurinki Tace, "to Allah yasa albarka," wani abin haushi wai ashe ya ba Usman sun hado min setin akwatuna cike da kaya masu tsada harda yara duka, nidai ina ta kallon ikon Allah za'a yimin auren dole. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ranar daurin aure kuwa kwanciya nayi abina, gida cike da dangi, su A'isha suna tamin tsiya wai inaso ina kaiwa kasuwa, jin haka naki wanka, sai dare nayi wanka dan naji iska. Ina sallar isha'i sai gasu Baba Hauwa tace, wai na fito a kaini gidan mijina, sai da nai kuka mai isata sannan na fita, wai inje gurin iya taimin fada, "nace ba zuwan da zanyi, ni yanzu meye ban sani ba sai kace wata yarinya? bayan itama Iyan ta daina sona." Ashe Iya tana jina sai kurum tace, "ni dai da kike fishi dani Allah ya bada sa'a, fadan ku da Aliyu ba'a shiga kwanan nan za'a jiku shuru." Haushi ya sake kama ni na saka sabon kuka, dan wulakancin sai aka samin dariya. Gidan shi aka kaini, dakina yayi kyau mutuka, sai dai ba kayan gadon dana zaba bane wadannan sunfi su kyau da tsada. Sha biyu ya shigo dakin, cikin fushi nace, "indai kana wa girman Allah ka fita in kuma nizan fita to in fita." Sai yace, "Asuba ta gari." Tin daga ranar bai sake shigowa daki naba, kullum shine yake min magana amma bana kulashi. Ya siyo wannan ya siyo wan can inya fita zai kirani yafi sau biyar naki dagawa. Satina biyu ya debo yara, niko yaranma Sadiq kurum nake kulawa kuma yaki zama shi sai gurin Iya, nace a sauka lafiya, itama Iyan ta sami dan tayin hira tunda ita daya ce, danma da masu aik. Ranar wata Alhamis ina xaune bayan isha kusan tara saura Khausar ta shigo, "momy kizo inji Abbammu yana dakinsa," nadanyi shuru nasan ya hada da Khausar ne dan yasha kirana kullum dare ta waya inki zuwa, ta zauna bakin gado, "Momy yace kije fa," ta katse min tunani, nace, "ke karki dame ni, kije zanje," data fita taga shuru ban fito ba sai ta shigo da takardunta tahau tsakiyar gado na wai zatayi home work, nace in gani in tai maka miki tace, "a'a kije Abba na kiranki ko kinje?" Dole tasa na mike, acikin dakunan bansan wannene dakinsa ba sai da Abdul ya fito nace inane dakin Abba? ya nuna min nace meya fito dakai yace ina neman yaya Khausar ne bata yimin Home Work ba, nace ka shiga dakina. Na murda kofar dakin ta bude na shiga yana sanye da jallabiya mai gajeran hannu kamshi da sanyin A.C suka buge ni na ji sanyi yana ratsani sabida yanayin sanyinne ake ciki nace "lafiya?" Yace, "Shigo mana ciki," Na shiga tare da maida kofa na rufe, ya tako ya kama hannuna ya zaunar dani a bakin gado shima ya zauna ya lalubo hannuna ya matse cikin nasa ya sauke wata irin ajiyar zuciya, na kalli fuskarshi idon shi a lumshe, Yaya mutum ne da yayi dai dai da kowanne zamani yana da kyau abin son kowacce mace amma ni sam bana jin sonsa a zuciyata, ya bude ya kalli cikin ida nuna, "nasan kin tsaneni koh?" Nima na cigaba da kallon cikin idanunshi, wata siririyar kwalla ce naga ta taru a cikin idanunsa yace, "duk da haka ina neman alfarma ki bani hakkina,wallahi ina cikin wani hali sai dai bazan matsa mikiba, babu matsala in kinga cewar da takura kije abinki karki damu kiyi baccinki," nayi shiru ban motsaba, ya cire hijabin jikina, rigar baccina ta bayyana, Sky blue ce mai santsi, ya soma shafa min gashin kaina hawaye suka soma zubo min, bansan ko na menene ba,sai na tsinci labbansa saman nawa, jikinsa kuwa bari yake sai kace tsohon daya dauki budurwa, ni kaina ban san ina muradi ba saida abubuwa sukai nisa. ranar dai mun kwana muna aikin lada cikin wata duniya da masu auren sunna ne kurum suka santa. Wannan karon yaya bai dauki al'amarina da wasaba, ji yake dani kamar yar yaye Ko laifi nayi baya yi min fada, inna ce ina son abu baya ja ko aiki da nake nace zan daina yace a'a in kina son dai nawa na daina jayayya dake, nace to zan daina dan dan nasan bakaso, yace nagode. Haka nan tun ina dari dari da shi na saki jikina da shi nima ina nuna masa kulawa, zamammu yafi na farkon aurenmu, 'ya'yanmu sun warware, damuwarsu ta yaye, sun ganmu a tare cikin aminci sun zama cikin farin ciki da walwala karkashin kulawarmu. Wurin shi na sami labarin Mujidat ba lafiya tana asibiti wai bata rike kashi da fitsari, yace, "kinga illar zina da Luwadi ko?" Nace, "Allah ya bata lafiya," yace, "yanda nake samin labari gwara mutuwarta da rayuwarta, Allah yasa mufi karfin zuciyarmu." Nace, "ameen ya rabbi........" Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Tammat bi hamdullahi taku Halima Abdullahi k/ mashi kecewa kusaurari littafinta na gaba, SAUYIN RAYUWA........ Alhamdulillah yaudai cikin ikon Allah gamu mumkawo karshen wannan labarin da muka dau tsahon lokaci muna yi, fatan zamu anfani da dukkanin anfanin da yake ciki sannna mu kiyayi kusakuran cikinsa. Inna neman afuwarku idan na sabawa daidaikunku kokuma jamhuri. Nagode sai kunji daga gareni. Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100An dauko wannan littafi daga shafin www.dlhausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na www.dlhausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from www.dlhausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name

Chapter 24 of 25