Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
daka fito da abunka kana ganin ya maka tsufa sabo kake so, lokacin wani kuma zai ga cewa na kannan shine sabo agurinsa Allah yayi miki zabin Alkairi, nace amin. Daren ranar su Yaya Sulaiman suka zo da shi su hudu wai iya tayi hakuri tayafe masa sannan suka matsa masa cewa ya maido da matarsa kuma ya yarda amma da sharadin zata daina koyarwa. Ina kwance kan gado a uwar daka ina jin su tamkar in taso in fito in ce bazan koma ba amma sai na tsaya inji me iya zatace? Ay kuwa sai naji Iya tace da farko dai kamar yanda na shaida masa dazun ni bai min laifi ba bare ya bani hakuri in da ace ni wata ce lokacin da rigimar tafaru yaneme ni mana sai kurum yatafi ya aikata son ransa yanzun yazo yana ban hakuri,ni a wa? Batun kome kuwa ga matarsa nan adaki tazo in zata koma bazan sata ba kuma bazan hanata ba, Tadaga murya Sadiya na'amsa tace zo nafito da dana akafada na zauna gefe.tace nasan kinji komai dan haka in zaki koma sai ki fada musu, shidai sun bashi baki ya yarda,Budar bakin da nayi sai kuka nace yaya kuyi Hakuri da abinda zance in Yaya Aliyu ne ya rage namiji a doron duniya wallahi tallahi bazan aure shiba bana kosan ganin shi ya fita a raina sam.Iya tace tashi ki koma ciki sannan tace kunji koh? To kuma na roke ku da kar ku sake zuwamin da wannan zance ko gaba an rufe wannan babi in dansa ya isa yaye yazo ya dauka,bansan lokacin da nace Iya harda wannan ma za'a rabani tace Allah ya baki wani mijin na gari ki haifi wasu yayan Sadiya,sai lokacin Aliyu ya dago ya dubi Iya sabida yaji zafin kalmarta sannan ya sake sunkuyar da kai Aliyu yaba yaya Sulaiman kudin yadan matsa yace iya ayita hakuri shin ina Sadiyarne? Na fito ya miko mini nace a, a yaya muna da komai na koma ciki yace ke Sadiya zoki karba hakkinkine da danki Iya tace tunda tace bata so saiku barta ko ku tashi kuje zamu kwanta...zamudakata anan,fatan zamuyi sallar juma'a lafiya ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Darajar Yayana4-02 Posted by ANaM Dorayi on 12:11 AM, 12-Apr-16 Under: DARAJAR 'YA'YANA _________________NA ___________HALIMA K/MASHI Haka suka fita jiki babu karfikowa ya nufi gidan shi suka nufi nasu da safe na gama yiwa yarona wanka kenan sai gashi ya shigo sanye da kananan kaya sai yaune ma na kalleshi yadan rame yayi duhu natabe baki sannan na bata rai Iya ta fita siyo mana biredi na gama na kwantar dashi kan kujera zan fita da ruwan sai naga yakai hannu zai dauke shi da sauri na dauki yarona na sashi a bayana na kwance zanin jikina wanda dama na dora ne a saman dogon wando na goyeshi sannan na dauki ruwan, yako ji haushi cikin zafin rai yace me kike nufi? Nace duk abinda kake nufi ,na kalleshi sama da kasa yace nufinki bazan dauki yarona ba? Nace au shima danka ne? Na zata inda nake zuwa na yoshi yace karfa kiga Iya na daure miki gindi ki zata har kin kai matsayin da zakiyi min rashin kunya dan kinga na kyaleki ban dauki mataki a kankiba, nace don Allah kaini kotun musulunci yace bani yarona in ganshi? bazan bayarba,Sallamar Iya tasa yazauna kan kujera nima nazauna, na kwantoshi nasoma shafa masa mai Iya tashigo dakin ganinshi sai ta daure fuska tace lafiya me kuma yakawoka? Yace Iya gurinki in gaisheki tsaki taja sannan tafita zuwa kicin Yakalleni Nan gidan ubanane ba mai hana ni zuwa. Nima na harareshi ina ruwana Allah yasa nima ina da gidan uban. Kafin yayi magana sai ga Iya ta shigo da ruwan zafi takalle ni zo ki karya cikin jego, kawo shi in sa masa kayan. Nace to, bayan na karasa sa masa pampers din na mika mata shi. Ina zama yayi caraf ya mika hannu ya dauke shi a hannun Iya na kalleshi cikin tsana nazauna shima yaharareni sannan yazauna yana kallon yaron, banzaci ya san sunan shiba sai naji ya ce Iya Sadiq ma dani yake kama sosai yanda ban tankaba itama bata tankaba. Yarungumeshi tsam a kirjinshi, sai kurum nafita tsakar gida ina karyawa. Ashe Iya ma ta shige uwar daka dan haka yadauki kayan yana sa masa yagama yamike yafito da shi ganin zai yi waje nabishi da gudu a ganina zai tafi da shine, ina fadin Iya zaitafi dashi nasha gabanshi,bani yarona dasauri Iya tace kyaleshi yatafi dashi din seme? Nasoma kuka shikuma sai hararata yake yi yaja tsaki yawuce nace Yaya inka tafi dashi saina tona asirinka tsam yatsaya sannan yawaiwayo yakalli Iya itama shi take kallo sannan takalleni na isa gabanshi namika hannu Bani yarona.Sai yamiko minshi sannan yafita da sauri naje kan kujera nazauna ina cika,Iya ta iso gabana wane irin asirene zaki tona masa?yaken dariya na kakaro birgace kawai nayi masa babu komai Iya. Tayi yar dariya haba Sadiya shi mahaukacikane bayan ba wani sirri jikinsa yayi sanyi haka? In dai da wani abu kifadamin,Nace ba komai iya tace oho miki in ma dashi, shiyasa wani lokacin banasan shiga shirginku.Ni dai sim sim nayi daki. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Hudu da ashirin ina kwashe tuwo naji sallamar shi ciki ciki na amsa, banyi tsammanin ma zaijiba na dago nadubeshi cikin tsana, sai naga hankalinshi yana kan yarona wanda nashimfida a tabarma akan katifar shi nakwantar dashi akofar daki Iya tana zaune kusa dashi. Dagudu na aje tuwon dake hannuna nafito har ina tsallaka iya nasuri dana nasa a baya naja zanina a igiyar shanya nagoye shi sannan nakoma kicin ina jin tsakinshi a raina nace kadai karata can.Daga inda nake ina jiyo shi yana gaida Iya, dakyar ta amsa. Yace zantafi zaria dama wani ayki nazoyi Kaduna akwai wani malami ne da ake zaton kasurgumin dan fashine to kan shi nake aiki,rahotanni sun same mu cewa ya koma Zaria acikin satin nan kafin inzo dan wata na biyu kenan ina nemanshi tun daga Maiduguri nake biye dashi har zuwa nan ina son Iya kitaya ni da addu'a Allah yataimake ni. Iya tace Allah yabada sa'a. Yace amin. Tace malami kuma dan fashi in banda son duniya? Ay irinsu suna da yawa Iya kuma yana siffatuwa ne da malai manyan malamai yana da ilimin, sai dai shi dan fashine ga tsafi ,sama da shekaru goma ankasa kamashi,kingako kamashi nasarace. Iya tace Allah yataimaka yace amin yaciro kudi gashi Iya. Tace a'a ai na fada maka bamu da bukatar komai,yasake tausasa murya Iya wannan fa tsakanin mune ni dake in baki amsaba sai inga tamkar kin cire ni a tsatsonki, Ya'ajiye gefenta. Iya kiyafemin natafi.,Bata ce komaiba kuma bata dauki kudinba yazo bakin kicin yajeho min wasu mukullai ga mukullin gidanki nan kije ki dauki motarki aciki. Nadubeshi fuska daure cikin harara nace bani da gida bare mota in kana nufin motarka to bana so,tsaki yaja sannan ya wuce batare daya dauki mukullanba. Nafito gurin Iya rai a bace nace Iya naga har kulashifa kikayi kuna hira har yana wani baki kudi kina karba? Iya tace kin san shi naci zai tayimin shiyasa narabu da shi ya aje kudin dan yatafi yabamu guri sannan ina zulumin yanayin aykin nan nashi wannan malamin kuwa dan fashi tunkararsa hadarine ina tsoron karya halakashi. Gadanga shiba mutumbane mai son neman tsarin kai, da kaikayi koma kan mashekiya,da kai magana zaice yana addu'a an san dai ita ce dama kan gaba. Don haka itama Iya ban tanka mataba wato ma tausayin shi takeji. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Aliyu yayi masauki unguwar Mazan Gudu gidsn limamin unguwar da sunan cewa shi bakone matafiyi ne. Hannu 2 aka karbeshi kwanansa 2 yace a nema masa daki na haya yana son yadan kama sana'a yafada musu cewa rani yake Zuwa garin Kaduna daga Hadeja yake,Liman har yayi masa tambaya game da wasu unguwanni a can Hajejan Allah yasa garuruwan da Aliyu yasani ne ya kuma fada masa cewa ya sani. Liman yace sun zauna sun danyi karatu a garin shekarun baya lokacin suna yawon neman ilimi. Liman yace Aliyu yazauna ga daki nan a zaure a gidansa na dansane dake karatun boko a jihar sokoto a jami'ar shehu dan fodio. Cikin sati daya yasaba da makota. Akwai wani dan dandali da mazan unguwar ke zama ko in ce majalisa. Tuni Aliyu ya saba da yan majalisar in da ake zama ayi ta labarin wane da wane ko duk wanda yagifta. Anan yasamu labarin wannan malami daya sauka gidan sarkin malaman kusfa ance yanda ilimi sosai kuma yana bada fatawa. Aliyu yace dan Allah wanda yasan gurin yayimasa rakiya don yana son daukan karatu. Kullum 'yan majalisar nan suna mamakin Aliyu duk irin shigar dayakeyi ta kaya marasa kyau amma fatar jikinsa bata nuna cewa daga kyauyen hadeja yakeba kamar yanda yafadamusu. Akwaima wanda yakecewa shifa yana wa fuskar Ali kallon sani. Cikin sati 2 sukayi sabo da Malamin wanda yasaki jiki da Aliyun amma sai dai Malamin ya fadawa Aliyu shifa malamine mai yawon yada da'awa don haka daga nan zai wuce Katsina ne tafi tafi har Nijar. Aliyu yace in ba damuwa zaibi shi,Aliyu ya lura da yanda malamin ke daga waya akai- akai sannan ya lura da irin kudin da malamin ke rabawa jama'a sadaka. Duk binciken dayayi ya gano cewa malanin ne wanda yake nema sai dai dama yana da labarin matsawar malamin yana cikin daki bazai kamuba. Ana gobe zasu bar garin kamar yanda suka shirya har da shi Aliyu shikuma ya daura aniyar kama shine aranar jajiberen tafiyar. Karfe 2 sun taso daga sallar Azahar Aliyu hankalinshi tashe burin shi yanzun idan sun iso kafin su isa gidsn malamin ya sauke yashige daki. Aliyu yakalli malamin. Allah yagafarta malam naga jama'ar wannan garin suna alhinin rabuwa dakai shin bazamu dan kara kwanakiba? Malam yakalli Aliyu ina da dalilin barin garinnan asubahin gobe.Aliyu yace Allah yasa haka shine mafi Alkairi. Malam yace ameen. Sai dai kai ina mamakin yanda kake son bina ban cika sakewa da mutaneba amma kai raina ya kwanta dakai amma daganinka ka taba zaman cikin birni? Aliy yace e duk cikin gari nayi rayuwata ban zauna gidaba, Malam yayi murmushi toh Aliyu sai dai kayi hakuri ina zaton bazanje dakaiba. Aliyu yace saboda me malam? Malam ya gyara tsayuwar wato malam Ali an sanar dani cewa duk inda zan shiga kada in shiga da mutumin cikin gari domin shine zai zamemin hadari cikin rayuwata. Aliyu yace Allah gafarta malam an fada maka kamannin shine munyi kama? Yace ko kusa an dai ce min zai shiga jikina sosai kuma zai cutar dani a rana irin ta gobe shiyasa duk lokacin dazan bar gari nakan barshi tun asubahi. Aliyu wanda ya kosa yaga isowar jami'an tsaro yace toh Alagafarta yaya zaka yarda da irin wannan kila ba gaskiya bane. Malam yadafa kafadar Aliyu inayimaka fata nagari Allah yasa zamu hadu wata rana amma wanda yafada min zancen nan yasha fadamin zantuka suna tabbata ina ji ajikina zamu sake haduwa da..... Jiniyar motar 'Yansanda ce tasa malam bai karasa zancenba sai Aliyu yaga malam ya daga kafada yasa gudu cikin azama da kwarewa Aliyu yaciro bindiga daga bayan wandasa ya harbi malam a kafa take malam yafadi amma burinshi yakai daki dan haka ya yunkura Aliyu yayi azama yacafkeshi. Mutanan gurin sun cika da mamaki harma suka taso da nufin jin ba'asi sai dai kafin suji dalili tuni yan sanda sunyi zobe a gurin sun kuma cafke wasu daga cikin makarraban malamin sannan an samu muggan makamai cikin kayan malamin da kudin kasar Amuruka(Dollar) da irin namu na gida. Mutanan unguwar suna ta al'ajabin lamarin yayinda wasu ke mamakin Aliyun wanda suka zata shima yana cikin mukarraban malam. Ta gidan lima suka bi mai masaukinsa,Aliyu yayi musu sallama yadauki yan kayan shi tare dayi masa alheri haka ma yen majalirarsu yatafi yabar su da labarinshi tare da jinjinawa aykin shi. Cikin wata hudu da aka damka aykin hannun Aliyu ya samu nasara ya fara bibiyar malamin tundaga maiduguri har kawo Kaduna sannan Zaria inda yayi nasara sakamakon haka ya samu lambar yabo tare da karin girma zuwa mataimakin kwamishina na can Abuja haka nan nasarar taja masa farin jini inda akayi ta haskashi gidajen talabijin. Ina kallon Iya tunda Aliyu yazo da batun aykin nan kullum cikin yimasa addu'a take tare dayawaita sadaka. Araina nace da da mahaifi sai Allah. Dubi duk haushinsa datakeji be hanata yimasa addu'ab. Inzanje aiki yanzu gida nake barin Sadiq sabida yana shan kamu. Iya tasani gaba tana min fada wata ranar Litinin na shirya zantapi aiki. Sadiya! Dan Allah shekarunki nawa? Nace me yafaru Iya? Tace fadamin. Nace 26 Tace dubi duk yanda kika koma ba wani ado ba kwalliyar da kikeyi ada, ki dage ko dan ki ba Gadanga haushi,amma kullum sai kina yawo kamar me takaba,Nace ni banima da kayan kwalliyar,tace inzaki dawo ki tsaya kasuwa ki saya in ma baki da kudi in baki,nace ina dashi a cikin account dina,tace to. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ina zaune bayan na sallami daliban ajina sun fita break nazabga tagumu ina tunanin zancen Iya gaskiya ta fadamin bazan tsaya in tsufar da kainaba tilas in nafita in shiga banki sannan in shiga kasuwa. Shigowar alert ne ya tsaida tunanina na dauka na duba kudi ne naira dubu saba'in sannan yaya ne ya turo min. Haushi da bakin ciki kamar inyi kuka don haushi. Dakyar nabari aka tashi na nufi banki na ciri kudin daya turomin naira dubu 70 na maida masa cikin account dinsa sannan naciri dubu 20 dan yin siyayyata acikin account dina. Nashiga cikin kasuwa nasiyo mai na perpect nasiya duk kayan shafawa, sannan nasai turaruka na har da kayan humra dan dakaina nake hada humrata nasai mayafai da takalma har atamfa na kara. Iya na gani tace ko kefa. Nanfa nashiga gayuna kafin wata daya na komo da farina da gayuna, sai dai ban maida kibata sosaiba, ba wanda zai ganni yazata ina da yara har 4. Wani abin dariya sai ga mutane sun soma yin sallama dani. Ranar wata juma'a ne sunan wata malamar da muke koyarwa tare nayi kyau cikin leshi mai ruwan madara ni kaina nasan nayi kyau taku dai dai nake yi na tsallaka titi zan hau abin hawa sai mota ta tsaya a gabana na waiwaya zanyi masifa sainaga yaya Usman ne cikin dariya na isa gurin shi. Yaya ashe kaine? Yace to na tsaya kafin inyi magana sai naga za'syi min masifa nayi dariya ka san mutane wai dasunga mutum ya tsaya sai suce zasu dauki mutum. Yace hakane sai ina? Nace nan Askulaye zani suna watace da muke koyarwa tare ta haihu. Yace muje. Nace a'a dakaje kada in batamaka lokaci yace hanya tace ni gaba naci don kurmin mashi zanje. Nace ok. Nashiga muka hau titi nace ina su Auntyna da su Ummul? Yace duk suna lfy shine bakya son fita da Sadiq koh? Nace shima ya saba da Iya baya son bina. Yace ya huta da shan rana. Nace wallahi. Naji cewa abokina yasamu karin girma kwanaki? Nabata rai ina ruwana. Yayi dariya da ruwanki mana koba dangantaka akwai su Kausar nace harsu duk na barmasa na yafesu. Yace bacin raine. Nace wai ya batun binciken? Yace ina kan binciken kiris yarage in kammala. Murna ta cikani cikin zakuwa nace kun gano kowane ne? Yace eh toh na dai yi nasarar gano cewa mutum dayane a abu uku Sulaiman din daya kawowa aboki gulma shine malamin makarantarku kuma shine Sadiya Abubakar mun gano hakan ne ta hanyar lambar MTN Din dayayi amfani da ita gurin cike form na account din da ya bude. Nace a'a duk lamba daya yayi amfani? Yace a'a daban daban ne sa'ar da muka ci duka na MTN ne kuma duk yayi musu rijista taimakon dayayi mana kenan. Nace Alhamdulillah. Muka danyi shiru nawasu yan dakiku sai Usman yayi gyaran murya yace, Sadiya! Nadube shi irin kallon dayayimin yasa gabana faduwa nayi ta maza nadauke kaina. In tambayeki mana? Nace eh...ina...jinka. Nafada cikin in ina yace in abokina yaji gaskiyar batun nasan zaku sasanta koh? Nakalleshi da sauri nan take raina yabaci na sunkuyar da kaina yaya Usman dan Allah na roke ka kadaina yimin zancen yaya nayi rantsuwa bazanyi kaffara ba,Muka danyi shiru na wani lokaci,sannna yasake yin 'yar gyaran murya "Sadiya nasan kisoma tsayawa da masu sonki ko?" Nadubeshi "banajin zan bata lilacina gurin kula su,domin al'amarinsu sai su." Yayi dan murmushi "karkiyi kudin goro" Nan nanunamasa layin muka shiga,gabana yana ta faduwa sabida irin kallon da yaya Usaman yake yimin. Nace ga gidannan.ya tsaya ya dubeni. "Zan dawo in daukeki" Nace a'a kayi hakuri daga nan zanwuce wata unguwar,nagode. Yace "ina zaki!" Nadubeshi "Gidan kawata" Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Yace "Ok! Shikenan, kila zan dawo nanda anjima inna zaton zamu tattauna wata magama mai muhummanci Nace to sai kazo. Jiki babu karfi nashiga gidan sunan,duk da irin shewa da wasa da dariya da abokan aikina keyi ni nakasa ko murmushi. Malama Bilkisu ta dubeni tace wai Malaman sadiya kodai baki da lafiyane?nai dan yake kaina ciwo yake Sukayimin sannu mai jegon har dacewa ke kam tunda kika haihu shi kenan kika zama sarkin ciwo. Nace aykam gashi nan na kasa maida jikina. Adaddape nayi minti 40 agidan nafito na nufi gidan Ayshata sai taganni kamar an jeho ni ta tashi tare dapadan lfy? Nace Uhm wata sabuwace tasamu. Tace kuma, to zauna kisha ruwa kin taki sa'a yau alalar gwangwani nayi. Naja tsaki ni wallahi yau ko nama kikayi zalla bana zaton zan iya ci. Tace meyafaru? Nan na bata lbrn duk yanda mukayi da yaya Usman itama dai ta damu amma tace balallai yace yana sonaba wai kila zuciya tace kawai ta zargi hakan nace toh shikenan. Sai bayan magariba na yimata sallama ta rako ni na hau mashin ina hanya naji wayata na ruri, ina dagawa iya ta rufe ni da fada ina natsaya ga Sadiq yana ta ihu? Nace gidan Aysha nawuce gani nan tafe. Ina shiga yaya naci karo dashi zai fito dashi a kafada yana ta kuka, duk da darene na raya cewa fuskar shi a daure take ranshi kuma a bace yake, nashige nazauna a falo ina ninke mayafina sai gashi. Kin tafi yawon banzanki kin bar yaro yana ta kuka ko? Ina kikaje? Naki ko dubanshi nagama ninke mayafina na mike zan shiga uwar daki yace baki amshe shiba yana kuka? Iya ta sallame sallah tace ki daukeshi mana ya jima yana kuka, nace to. Saida nakai mayafina na ajiye sannan nafito fuska daure na isa gurinshi namika hannu cikin harara yabani shi sannan yayi kwafa. Kisani in zaki tafi yawon banzanki ki daina ajiye min yaro a gisa yana kuka banda shashanci me zai sa mace tafita har magriba. Na zaci acikin zuciya nake magana ashe tafito fili ina ruwana da kukan shi zan kiyin harkar gabana ne saboda shi? Sai muryar Yaya naji yace Iyee haka kikace? Nayi shiru. Tozan dauki yarona in hada shi da yan uwansa in yaso ke kije kiyi ta gantalinki. Nazauna nasoma bashi nono ina jijjiga nace Tabdi Ay wallahu bazan bada dana ba koh gaban Alkali Za'a,Iya dai tana jin mu bata tankaba yace basai Alkaliba ahannunki zan amshe shi kicika baki kigani. Nakalli iya don na soma fargabar zantukanshi tsaf zai iya,Nace iya kifada masa yafitga harkata yadaina cemin ina gantali. Iya tace ki kyaleshi yazo yadauki dan nasa gantali kuwa ai kin isa yine. Yatausasa murya Iya kidena dauremata gindi tanamin rashin kunya. Yakalleni. Zan targadaki in kika yi wasa. Namike nashige daki shi kuma yawuce. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Haka suka fita jiki babu karfikowa ya nufi gidan shi suka nufi nasu da safe na gama yiwa yarona wanka kenan sai gashi ya shigo sanye da kananan kaya sai yaune ma na kalleshi yadan rame yayi duhu natabe baki sannan na bata rai Iya ta fita siyo mana biredi na gama na kwantar dashi kan kujera zan fita da ruwan sai naga yakai hannu zai dauke shi da sauri na dauki yarona na sashi a bayana na kwance zanin jikina wanda dama na dora ne a saman dogon wando na goyeshi sannan na dauki ruwan, yako ji haushi cikin zafin rai yace me kike nufi? Nace duk abinda kake nufi ,na kalleshi sama da kasa yace nufinki bazan dauki yarona ba? Nace au shima danka ne? Na zata inda nake zuwa na yoshi yace karfa kiga Iya na daure miki gindi ki zata har kin kai matsayin da zakiyi min rashin kunya dan kinga na kyaleki ban dauki mataki a kankiba, nace don Allah kaini kotun musulunci yace bani yarona in ganshi? bazan bayarba,Sallamar Iya tasa yazauna kan kujera nima nazauna, na kwantoshi nasoma shafa masa mai Iya tashigo dakin ganinshi sai ta daure fuska tace lafiya me kuma yakawoka? Yace Iya gurinki in gaisheki tsaki taja sannan tafita zuwa kicin Yakalleni Nan gidan ubanane ba mai hana ni zuwa. Nima na harareshi ina ruwana Allah yasa nima ina da gidan uban. Kafin yayi magana sai ga Iya ta shigo da ruwan zafi takalle ni zo ki karya cikin jego, kawo shi in sa masa kayan. Nace to, bayan na karasa sa masa pampers din na mika mata shi. Ina zama yayi caraf ya mika hannu ya dauke shi a hannun Iya na kalleshi cikin tsana nazauna shima yaharareni sannan yazauna yana kallon yaron, banzaci ya san sunan shiba sai naji ya ce Iya Sadiq ma dani yake kama sosai yanda ban tankaba itama bata tankaba. Yarungumeshi tsam a kirjinshi, sai kurum nafita tsakar gida ina karyawa. Ashe Iya ma ta shige uwar daka dan haka yadauki kayan yana sa masa yagama yamike yafito da shi ganin zai yi waje nabishi da gudu a ganina zai tafi da shine, ina fadin Iya zaitafi dashi nasha gabanshi,bani yarona dasauri Iya tace kyaleshi yatafi dashi din seme? Nasoma kuka shikuma sai hararata yake yi yaja tsaki yawuce nace Yaya inka tafi dashi saina tona asirinka tsam yatsaya sannan yawaiwayo yakalli Iya itama shi take kallo sannan takalleni na isa gabanshi namika hannu Bani yarona.Sai yamiko minshi sannan yafita da sauri naje kan kujera nazauna ina cika,Iya ta iso gabana wane irin asirene zaki tona masa?yaken dariya na kakaro birgace kawai nayi masa babu komai Iya. Tayi yar dariya haba Sadiya shi mahaukacikane bayan ba wani sirri jikinsa yayi sanyi haka? In dai da wani abu kifadamin,Nace ba komai iya tace oho miki in ma dashi, shiyasa wani lokacin banasan shiga shirginku.Ni dai sim sim nayi daki. Hudu da ashirin ina kwashe tuwo naji sallamar shi ciki ciki na amsa, banyi tsammanin ma zaijiba na dago nadubeshi cikin tsana, sai naga hankalinshi yana kan yarona wanda nashimfida a tabarma akan katifar shi nakwantar dashi akofar daki Iya tana zaune kusa dashi. Dagudu na aje tuwon dake hannuna nafito har ina tsallaka iya nasuri dana nasa a baya naja zanina a igiyar shanya nagoye shi sannan nakoma kicin ina jin tsakinshi a raina nace kadai karata can.Daga inda nake ina jiyo shi yana gaida Iya, dakyar ta amsa. Yace zantafi zaria dama wani ayki nazoyi Kaduna akwai wani malami ne da ake zaton kasurgumin dan fashine to kan shi nake aiki,rahotanni sun same mu cewa ya koma Zaria acikin satin nan kafin inzo dan wata na biyu kenan ina nemanshi tun daga Maiduguri nake biye dashi har zuwa nan ina son Iya kitaya ni da addu'a Allah yataimake ni. Iya tace Allah yabada sa'a. Yace amin. Tace malami kuma dan fashi in banda son duniya? Ay irinsu suna da yawa Iya kuma yana siffatuwa ne da malai manyan malamai yana da ilimin, sai dai shi dan fashine ga tsafi ,sama da shekaru goma ankasa kamashi,kingako kamashi nasarace. Iya tace Allah yataimaka yace amin yaciro kudi gashi Iya. Tace a'a ai na fada maka bamu da bukatar komai,yasake tausasa murya Iya wannan fa tsakanin mune ni dake in baki amsaba sai inga tamkar kin cire ni a tsatsonki, Ya'ajiye gefenta. Iya kiyafemin natafi.,Bata ce komaiba kuma bata dauki kudinba yazo bakin kicin yajeho min wasu mukullai ga mukullin gidanki nan kije ki dauki motarki aciki. Nadubeshi fuska daure cikin harara nace bani da gida bare mota in kana nufin motarka to bana so,tsaki yaja sannan ya wuce batare daya dauki mukullanba. Nafito gurin Iya rai a bace nace Iya naga har kulashifa kikayi kuna hira har yana wani baki kudi kina karba? Iya tace kin san shi naci zai tayimin shiyasa narabu da shi ya aje kudin dan yatafi yabamu guri sannan ina zulumin yanayin aykin nan nashi wannan malamin kuwa dan fashi tunkararsa hadarine ina tsoron karya halakashi. Gadanga shiba mutumbane mai son neman tsarin kai, da kaikayi koma kan mashekiya,da kai magana zaice yana addu'a an san dai ita ce dama kan gaba. Don haka itama Iya ban tanka mataba wato ma tausayin shi takeji. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Aliyu yayi masauki unguwar Mazan Gudu gidsn limamin unguwar da sunan cewa shi bakone matafiyi ne. Hannu 2 aka karbeshi kwanansa 2 yace a nema masa daki na haya yana son yadan kama sana'a yafada musu cewa rani yake Zuwa garin Kaduna daga Hadeja yake,Liman har yayi masa tambaya game da wasu unguwanni a can Hajejan Allah yasa garuruwan da Aliyu yasani ne ya kuma fada masa cewa ya sani. Liman yace sun zauna sun danyi karatu a garin shekarun baya lokacin suna yawon neman ilimi. Liman yace Aliyu yazauna ga daki nan a zaure a gidansa na dansane dake karatun boko a jihar sokoto a jami'ar shehu dan fodio. Cikin sati daya yasaba da makota. Akwai wani dan dandali da mazan unguwar ke zama ko in ce majalisa. Tuni Aliyu ya saba da yan majalisar in da ake zama ayi ta labarin wane da wane ko duk wanda yagifta. Anan yasamu labarin wannan malami daya sauka gidan sarkin malaman kusfa ance yanda ilimi sosai kuma yana bada fatawa. Aliyu yace dan Allah wanda yasan gurin yayimasa rakiya don yana son daukan karatu. Kullum 'yan majalisar nan suna mamakin Aliyu duk irin shigar dayakeyi ta kaya marasa kyau amma fatar jikinsa bata nuna cewa daga kyauyen hadeja yakeba kamar yanda yafadamusu. Akwaima wanda yakecewa shifa yana wa fuskar Ali kallon sani. Cikin sati 2 sukayi sabo da Malamin wanda yasaki jiki da Aliyun amma sai dai Malamin ya fadawa Aliyu shifa malamine mai yawon yada da'awa don haka daga nan zai wuce Katsina ne tafi tafi har Nijar. Aliyu yace in ba damuwa zaibi shi,Aliyu ya lura da yanda malamin ke daga waya akai- akai sannan ya lura da irin kudin da malamin ke rabawa jama'a sadaka. Duk binciken dayayi ya gano cewa malanin ne wanda yake nema sai dai dama yana da labarin matsawar malamin yana cikin daki bazai kamuba. Ana gobe zasu bar garin kamar yanda suka shirya har da shi Aliyu shikuma ya daura aniyar kama shine aranar jajiberen tafiyar. Karfe 2 sun taso daga sallar Azahar Aliyu hankalinshi tashe burin

Chapter 21 of 25