Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ne suka ce ko menene ma?Ta dauki ledar tana cirowa ta re da fadin kaine ka siyo ankon gadanda da kanka?Ya ce, to duk ba zani bane, shi nan sai su zaba.Ina kallo daga ciki kuma ina jin su, tun kafin in fito zaunuwan suka tafi dani.Ya ce, naki ne da nata.Iya ta ce, to mun gode, da ma ina so inyi maka zancen gidan ne, a ina kasamu?Ya ce, to ni dai nafi so a can kasan layinku, gefen makabarta din nan, to ba a samu ba sai na dawo neman na siyarwa, kudina dakekasa yanxu za su iya semin gida, amma albashin wanan watan da na wancan watan hada mana za ayi.To ganin kurewar lokacin sai kurum na barshi yanxun anjima zamuje mu ga wani gida da yaya Sani da Usman wai ciki da falo sai kichin da ban daki dubu dari da hamsin.Iya tayi shiru tana nazari, can ta ce ina nufin kasan gidan su babba ne?Ya ce ciki uku ne da kicin da ban daki sanan ga filin da mutum zai iya fakin din mota har biyu.Iya ta ce kuma nawa?Da sauri ya ce wai miliyan daya da dari takwas.Ta ce, ina ganin zaifi ka siya gidan in yaso sai a daga bikin.Ya dubi iya, ai saboda bana son dagawar shiyasa na hakura da siyan gidan.Iya ta ce siyan xai fi maka sauki ka huta da biyan haya, auran kurum za a daga ba.Ya ce ba dagawa za'ayi ba, abinda ya sa in an daga za ayi asara da yawa.Abokaina sun kashe kudi gurin kati mai tsada tare da wasu abubuwan abokan aikina suma sun kashe kudi gurin shirya bukin.Iya ta ce to, kana ji ko, yanda za ayi kawai a daura auren da buki, sai ta zauna gida kafin a gama gyara tunda dai nan a gida ne ba a dawa ba, bana so ka rasa gidan nan ne muhalli a bariki ba karamin rufin asari bane Aliyu ya ce, shi ke nan sai ayi haka din bari zan kira yaya Sani sai muje dake ki ga gidan sai a biya.Lumshe ido nayi cikin jin dadin an fasa daga bikin, kai naso in tare a gida na ranar amma baji, buri na dai a daura auren, amma da iya ta so kwafsawa wai a daga.Ya mike ya juya da nufin fita ida nunsa sukasauka a kichin a inda nake, da sauri na ce ina yini?Sai da ya dauke kai sanan ya ce, lafiya.Har ya fita ina kallonshi.Iya ta katse ni da cewa, wata rana sai kin gaji da kallon shi.Na sunkuyar da kai kunya ta rufe ni, ban santana kallona ba sa karya, in dai gadanga ne gaki ga shi nan. Pink din muka zaba ni da Aisha, sai dai muna zuwa kasuwa aka ce dubu uku ce gashi kudin aisha bai kai ba.Sai muka dawo gida da kyar mamanta ta cika mata muka koma muka siyo.Muka roki mai shagon ya ajiye mana da mu siya da yawa.Yamma tai mana a kasuwa gashi ana wahalar mota.Muna tsaye a kan titin kano Road, na ce bana son magariba tayi mana tun daya muka fito gashi iya ba ta san mun koma unguwar mu'azu mun dawo kasuwa ba.Aisha ta ce, sai dai muje mushiga dambancen ko za mu samu, na ce zamuje.Ta kan legas street wani lokacin ba a wahalar mota.Muna tafe wai wani mai mota ya tsaya, 'yan mata kuzo mana.Na ja tsaki tare da kara sauri, Aisha ta ce, lafiya?Ya ce rage muku hanya zanyi.Na ce Aisha, kema kika tsaya tambayarshi.Haka mutumin nan ya ci gaba da bin mu yana magiya, duhun magariba ya shigo na ce Aisha ko dai mu tsayar da mutumin nan ya kai mu gida?Don ina tsoron fadan iya. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Tace, nima hakan zan ce,dai dai lokacin ya sake cewa ku kuwa tunda na ce Allah ya kamata ku saurare ni, dan kun san mugu dai ba zai yi muku sallama ba.Aisha ta ce unguwar Mu'axu muke.Ya ce, ai hanya ta ce ni kuma Nasarawa zanje.Cikin far gaba muka shiga motar ya ce mun a'a ke dawo gaba dai ki nuna mun hanya , na koma ga ba.Ya tam bayi sunayen mu, ina shirin xollo masa karya sai naji Aisha daga bayana ta ce, ita Sadiya ni kuma Aisha .Ya ce, masha Allah , sunaye masu ma'ana.Ya dube ni, Sadiya dan ke fa nake ta wanan bibikon sai aka ci sa'a kina da sunan matata, ni sunana Auwal.Hakika jin sunanki ya kara samun sonki Halimatu duk wace ta amsa wanan sunan takan zama mai hakuri da hange, bata rani bata daukar raini, macen rufin asiri zan so na sake samun ki.Na ce matar taka ta hada duk wanan halin shine zaka yi mata kishiya?Ya ce jin dadin halinta yasa zan kara.Aisha ta ce bakai mata adalci ba, au, ke fa sunan uwata ne ke da zaki tayani yakin neman shiga?Aisha ta ce, nan da sati biyu ita ma tana dakin angonta.Da sauri ya ce, da gaske?Ta rantse mashi tare da fada mashi ashobe muka zo siya.Daga nan nayi shiru bai sake magana ba harya shigar damu layin kasuwa, na ce sauke mu a nan ma mun gode.Sai mu karasa.Ya tsaya muka fito, ya ce marya ba godiya?Na dawo dai dai saitin shi na ce, mun gode, na ce kayi hakuri muna sauri ne dare yayi.Ya ce shi kenan, Allah ya baki zaman lafiya.Juyawar da zanyi in tafi tare da cewa amin, sai maganar ta tsaya, sa kamakon ya Aliyu da nagani tsaye yana kallon mu. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Darajar Yayana 1-03 Posted by ANaM Dorayi on 10:51 PM, 14-Mar-16 Under: DARAJAR 'YA'YANA __________________NA ___________HALIMA K/MASHI Duk da kasan cewar duhun magariba ba zai sa in kasa gane bacin ran sa ba.Gaba na ya fadi, irin wanda ban taba yi ba.A fili na furta na shiga uku!Aisha ta ce, me nene?Bakinta yayi shiru sakamakon ganindatayiwa abin da nagani.Kusan minti biyu yana kallo na, ko da banga fuskarshi sosai ba na san a daure take .Sai yaja tsaki sanan yayi babban titi abin shi.Muka kwashi sauri ni da Aisha inayi ina waiwaya shi, a zuciyata ina cewa yau na kade, Aisha ta ce muyi wa ni kin ga da sauki tunda mama ta san mun xo mun koma ne.Munyi sallama iya tana tsaye tsakar gida tana cewa, kai ni wadan nan yara ko ina suka shige ne?Kai Sadiya bata da hankali, ki fita tunda hantsi har magariba, to ko kasuwar kwari ta kano suka je?Ko jiran mu gama sallamar bata yi ba bare ta amsa ta hau fada, Aisha ta shiga jero mata dalilan mu, ta ce ku refa mun baki, ko kasuwar kano kuka je ya ci a ce kun dawo tadubi Aisha ta ce uwaki ta ganki hankalinta ya kwanta, masu shegen rawar kai.Ta bini ke kuma, sai ki jira xuwan gadanga don tun yamma yake shige da fice bai ganki ba, har dai ya kare ya ce ita wanan yarinyar ina tayi ne?Ina son ta hada mun abin shan ruwa ina azumi, na dafa kirji na ce, to me kika ce masa?Ta harare ni karya zan masa?Ce masa nayi kinje kasuwa sayan anko, yayita fada me yasa na barki don baya son xuwanki kasuwar ne yasa shi siyo ankon dakansa.Na ce, na kade.Na dauki buta dan yin auwala, a xuciyata inatuno yanda ya ganmu muna fitowa a motar, da nayi salla nayi addu'a Allah ya yayyafawa abin ruwan sanyi.Da a zamar sa ya shigo da sallama ga ba naya fadi da sauri, don haka ma ban iya amsa sallamar ba, dakinsa ya shiga bayan wasu mintina ya fito tsaf tsaf cikin shirin fita.Ban taba ganin dansanda da kaki yake masa kyau matuka ba irin ya Aliyu, kan cinya ta na dora fiskata ganin ya nufo dakin Iya.Ga zato na da ya karaso zai zabga min mari,ina jiyoshi yana cewa iya ya tafi sai da safe, ta ce, can zaka kwana?Ya ce eh, ta ce, Allah ya tsare mun kai, ya kuma bada sa'a ka yawaita adu'a.Ya ce to ina yi iya, zan kara kulawa.Ya sake wuce ni ya nufi fita, da kallo na bishia raina na ce, zaki na maza sarkin jin kai.Nan ya tafi ya barni da kamshin sa sai dai da dukkan alamu yana fushi dani.Da dare ina cikin daki kwance kan gado, juyi kawai nake zuciyata tana mun nazari a kan kallon da ya Aliyu zai mun, ganin da yayi mun a motar wani kamar in kira shi in bashi hakuri, sai na fasa.Na rubuta sako kamar haka:YA ALI DON ALLAH KAYI HAKURI IN NA BATA MAKA RAI. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ban jira amsa ba don nasan ba samu zanyi ba, amma ga mamaki na sai naji sautin shigar sako.Da sauri na bude na soma karantawa.KUL! BANA DAYA DAGA CIKIN MUTANEN DA SUKE DAUKAR LOKACIN AIKINSU, SUNA HADA SU CIKIN LAMURANSU NA DABAM.SAI KI RIKE WANAN DAN GABA.Na lumshe ido ina son yin nazari a kan kalaman nasa, na san dai kul! Dan gargadi ne ya yi mun kenan ba ya bukatar a shigar masa lokacin aikin sa.Nayi juyi ina mai yiwa kaina jajen auran ya Aliyu, yanxu auren ya fi ban tsoro fiye da birgeni.Washegari sukuku na tashi,Iya ta ce jiya kuna can kuna gararin yawon ku mahaifinki ya zo yayi ta jiranki har ya tafi.,na ce kash!Ko da yake na san dole ya dawo kafin bikin.Ta ce ba dole ne ba , kudi ne ya kawo sadakin ki da akayi, sai gudumawar su dubu hamsin.Na ce hamsin iya?Yaushe hamsin zatayi mun kayan daki?Ta ce, ina laifi, mahaifinki fa yanxu ba aiki yake yi ba, tunda yayi ritaya sai dai dan noma.Shi ko noma a kasarnan yanxu dai ba a dauki maiyinsa da mutunci ba, shine koma baya a gurin gwamna ti.Su ba ga taki ba ba ga tallafi ba, dan gurarenda suke nomawan ma kwanaki yakecemun gwamnati ta ce zata amshi wurin.Na ce iya gurin da ma ba nasu bane?Ta ce, Sadiya kenan, dama talaka yana da guri ne a a wanan karnin?Sai wanda Allah ya taimaka ya kuma tsaga da rabonsa.Gurinka da takardu da komai za a amshe maka,dubu hamsin ai yayi kokari.Na ce haka ne Allah ya rufa asiri, duk abindaza ayi dai dai karfinmu za muyi.Iya ta ce, in sha Allahu sai kin zaba yata.Jugun nayi ina kallon Iya, baiwar Allah nan tana sona fiye da yayan da ta haifa, abin da take min ko ita ce ta haifeni sai haka.Kusan duk dare sai bacci na ya katse, in yi kiri kiri ni kadai cikin xullumi irin zaman da zanyi gidan ya Aliyu.Na gama duk hashashen da zanyi ban hango jin dadi ko kulawa a cikin auren ba, sai yanxu na gane nufin iya ta guje mun wahala ne, gashi lokaci ya kure mun bani da damar in ce bana so.Kusan karfe uku na rana ina zaune ina yankan farce na tare da gyarawa, sautin shigowar sako naji, sharewa nayi amma naki dubawa don nasn MTN ne.Sai kuma wata zuciyar ta ce mun in duba, gaba na ya fadi ganin sunan ya Ali, na duba cewa yayi.KI SAMENI A DAKI NA YANXUN.Duk da cewa ina fargaba sai da na dan sakemurza hoda tare da man lebe, sanan na fesaturare.Iya ta kalle ni tana zaune gefe tana gyaran goron ta da yayi tsutsa Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ta ce, to mai aljanun kwaliya don a sarar turare ana zaune kin hau feshe feshe.Na ce, iya yaya Aliyu ne yake kira na, ta ce ya shigo ne?Na ce ina zato, amma ta waya ya turo min.Na suri hijabi na na nufi dakin gabana na matukar faduwa.Nayi sallama ya amsa, na shiga kallo daya nayi mashi yana sanye da gajeren wando da(t-shirt) fara sol na sunkuyar da kai sanan na tsugunna tare da cewa gani yaya.Sam bai ko kalleni ba, hasalima danna wayarsa yake abinsa, nayi kusan minti uku sanan ya ce (ba tare da ya kalli inda nake ba).Ya sunan saurayinki da na ganku jiya ya sauke ku a mota?Ban san lokacin da na zauna ba don tsabar tsoro.Sanan na ce, ba saurayi na bane.Lokacin ne ya dubeni cikin wata irin harara da murya ta isa ya ce, ba karamin zunibi ba ne wajen dan sanda mai laifi yaki amsa laifinsa.Kar ki raina hankalina kokaryata ni, sunansa kurum na tambaya.Murya ta ta soma rawa alamun kuka zai kubuce min, ya dora yatsansa dan manuni akan leben shi ta re da cewa, shhhhhi!Kul!Kika min kuka, ko rawar muryar nan bani son ji.Ya ci ga ba duk da dadewarku da shi baki san sunan shi ba?Nayi kokari na kalaci miyau na hadiye shi tare da kukan da ke son kwace min.Na ce, yau ne na soma ganin shi, yana ta binmu yana rokon mu wai mu tsaya muka ki, toda muka ga duhun dare muka yarda ya kawo mu, don ana wahalar mota kuma kudin mu ba zai ishe mu mu hau achaba ba.Ya maida kanshi ya kwanta rigingine, ya kuma ci gaba da danna wayarshi.Kusan minti biyu sanan ya ce, wa yake so cikin ku da yake ta binku?Da dama yana ta binku ne kawai ya rage muku hanya duk da dimbin jama'ar da ke jiran mota a gurin?Tsoro ne da faduwar gaba suka karu gareni, cikin in-ina na ce, am.. Em.. Haka ya ce wai ni yake so.Da sau ri ya tashi zaune, cikin daga murya ya ce, menene?Da sadakin nawa a gurinki?Da sauri na ce, ai Aisha ta ce mashi aure za ai min.Ya zuro kafafunsa kasa, oh, da ke baki fada mashi ba?Na ce, ta rigani yin mga na ne shine dalilin da ya tsareni da idanunsa.To me yace da ta fada masa?Haka ya ce Allah ya sa alkairi.Ya sake komawa ya kwanta.Jeki zan bincika, in na samu zantukanki ba gaskiya sai kin sani.Zaraf!Na mikexan fita sai ya sake cewa, me ya fada miki lokacin da zaki tafi ya kiraki?Na ce, ya ce ne ba godiya?Shine na ce mun gode.Tamkar ba shi na bawa amsa ba, don bai komotsa ba bare ya dubeni.Ina ta tsaye har lokacin da ya kula dan kansa, sanan ya ce, kina da wata maganar ne?Na ce, a a.Ya ce, to kin tsaya min a kai.Na tabe baki a raina na ce, masiffafen ikon ka zan dauke shi kuwa?Tsuntsun dayaja ruwa......ANaM)Na fice, duk da ba lokacin zafi bane jikina sharkaf da zufa, kan kujera na zauna ina maida numfashi.Iya ta ce, me ya ce miki ne?Ko abinci zai ci?Na ce a'a mun dai yi hira ne.Ta ce, shine kika yi wujiga wujiga sai ka ce kunyi dambe?Sakon da ya kara shigowa wayata shi ne ya hana ni baiwa iya amsa, ko da yake dama bani da amsar.Sunan shi na kara gani na bude sakon, cewayayi.NA MANTA BAN GARGADEKI BA, DOMIN KE TAWA CE TUN KAFIN NA BADA SADAKI, BARE NA BIYA KUDINKI.Naaje wayar a gefena, na zari buta zuwa ban daki ba don zanyi wani abu ba sai dan inkaucewa tam bayoyin iya.Sauran sati daya biki iya ta zauna da duk yayanta, sun shirya yanda za su gabatar da komai cikin tsari.Ina tsakar gida ina jiyo su, iya ta kwala min kira sadiya!Na amsa, zo kije gidan Hajiya Umma Rimaye matar Likita Hassan ki ce mata tayi wa maiyin alkaki magana?In sunyi maganar nawa ne kudin?Na ce to.Na shiga dakin, kaina sunkuye dan harda ya Aliyu a gurin, ta ce maza-maza ki dawo, dukkwanakin nan na kula baki son aike.Ina shiga uwar daki na tura mashi sakon cewa iya ta aikeni, ya bude ya gani amma sai ya ajiye wayarsa, sanan bai ce mun kala ba.Neko sai nayi zamana gefen gado, jin shiru ban fito na ta fi ba iya ta ce, kin tsaya kwalliyarki ta jaraba ko?Na ce, a a.Ya san shi nake jira, sai ya ce ba aikenki akayi ba kina jiran menene?Na fito na tafi.,ya Usman ne ya kawo mun katinan bukin a ranar da dare.Lallai su na kula biki zasuyi na sosai.Farko zasuyi walima bayan daurin aure, sai kuma dinner, sanan akwai police day, shi kuma washe garin daurin aure zasuyi shi, damisalin karfe uku.Ni da Aisha da Fatiman ya Sulaiman muka shiga rabon kati.Ana saura kwana hudu biki, Anty Abida matar Usman ta kirani ta waya naje, bayan mun gaisa ta ce, kina dan gyaran jikinki ko?Na ce da me?Ta ce dan shirye shiryen mu na mata.Na ce, a a ni bani da kudi anty.Anty ta ce, baki tambayi ango ba?Na ce anty, ni ba zan iya tambayarshi ba.Nan take ta kira wayarshi ta sa handsfree, ya daga tare da amsa sallamarta, ya ce madam ya akayi ne?Ta ce ango, ango ka sha kamshi.Ya ce bansha ba tukunna.Suka yi yar dariya, ta ce dama maganar gyaran jikin amarya ne, ka san anayi.Ya ce ban sani ba gaskiya wane irin gyara kenan?Ta ce dogon bayani ne yanzu dai kudi muke bukata.Ya ce nawa ne?Ta ce talatin ne kacal ba yawa.Ya ce madan kuna so sai kun tsotse ni tas! Ya fadi? Ta ce tashi muje gidan Hajiya Umma Rimaye.Na ce, a a, ita ce mai gyaran jikin?Ta ce, eh.Nace na ga iya gurinta ta aikeni in kai kudin alkaki.Ta ce, eh, ai kawarta ke yin kayan buki, ita dai ke gyaran jiki.Na ce gaskiya tana da kirki.An hada kayan dilka masu kyau an lailaye ni da su, duk da kasantuwata fara ba karamin kyau nayi ba, kwana uku zanyi ina zuwa.Kuma ran na uku za ayi mun lalle.Iya da kanta tayi ta yabon kyan da nayi, haka naita zuwa ranar da na cika kwana uku ta kira mai zanen lalle inda aka zuba min fulawa.Abinka da fara, kowa sai tanka ni yake ta ce,tunda gidan su yana da girma kawaye na suzo nan a yi masu na su lallan na ce, to na gode.Abida ce ta amso kudin ta bada, Usman shine ya bamu kudin walimar mu.Wani abun da ban gane ba duk dare sai iya ta dama mun wata fura wace ita ta hada kayan hadin da kanta, sanan ta va inno yar sokoto ta daka mata.Furar tana da danko, furar sai kace magani gashi duk yawanta in ta dama sai ta tsare nina shanye.Sanan da safe ta xuba gero a turmi ta surfe shi, wai zata tara na dama kunun safe saboda yan buki, amma tana gamawa zata wanke shi ruwan farko ta tsareni sai na shanye ina kuka ina komai.Tun ana jibi daurin aure wasu suka soma sintirin taya aiki, makota dangi duk sun cika gidan, yan gefen su iya da na baba na. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 An yi mini kamu inda aka feshe mu da turareni da kawaye na kamar yanda muke yi a nan Kaduna.(Ina yan kadunan,yakukeyi kubamu Labari,ANaM) Gidan matar yaya sani mukakwana. Zariya za a daura aure amma an ce ni ba saina je can ba, tunda ba tarewa zan yi ba.Na nufo gida dan kwasan kayan da zanyi anfani da su in nayi wanka.Su ya Aliyu na ta shirin tafiya gurin daurin aure, an kawo motoci.Ya Aliyu ba ya gurin sai abokanan sa sun taru a kofar gidan mu, kunya ta kamani, na ja gefen hijabina na rufe fuskata.Ina jin wani cikin su amaryarmu ki bude idonki kada ki fadi mana.Sai naji muryar Usman yana cewa, sarkin kunya kenan.Zan shiga soro (zaure) naji mun zabga karo da wani, da sauri na bude fuskata, gaba na ya fadi.Ya Alyu ne har wayarsa da ya na magana tafadi.Da saurina tsugunna dan dauke, tare muka hada hannu zamu dauki wayar. Hannunshi ya taba nawa.Ba ni kadai ba, na kula harshi yaji abin da naji, tamkar wutar lantarki ta jamu.Shi ne ya janye hannunsa, na dauki wayar na mika masa tare da furta kayi hakuri.Kala bai ce ba, sai amsar wayar da yayi ya tafi, na bishi da kallo yayi matukar kyau cikintsaleliyar shadda mai ruwan suminti, tana tamaiko.Kamshinsa ya cika zauren, a fila na ce na more muji, na juya na nufi ciki.Sai tsiya ake min Amarya-amarya. Munyi walimama inda nai ta canjin kaya, kusan karfe hudu Aisha ta miko min wayata, sa ko ya shigo na bude kamar yanda na zata ya Aliyu ne, in da ya ce, "Alhamdulilla" na kalli Aisha dubi abin da ya ce, ta karanta da murmushi ta dube ni, kin zama tashi dole yayi hamdala ga Allah.Nace, Allah ya sa haka yake nufi, wanan danjin kan?Sakon shi ya sake shigowa musalin karfe bakwai na safe, na idar da sallah ke nan, ya ce kije gidan Usman da ga can za a dauke mu ni da ke dan zuwa dinner, kawayenki kuma su xama cikin shiri su tsaya a kofar gidan mu, please, banda marasa hankali, bayan sallar isha'i za a tafi.Na ce, Aisha kinji mutuminki ko?Ta da fani, me ya ce?Na mika mata wayar ta karanta ta dube ni.Ki dauki kayanki da zaki sa ki tafi can ki shirya, ni kuma zan kula da sauran kawayenmu a nan dan mu shirya cikin tsari.Kinsan su ya Aliyu masu aji ne ba irin tarkacen nan suke so ba.A gidan Abida nayi salar isha'i sanan na shirya da taimakon abida da yake ita ma in dai kwalliya ne, matirial ne na saka riga da siket ruwan madara da ratsin kore.Sai nesa kore takalmi da jaka duk koraye, sarka kuma ja sai muka yi anfani da ja a kwalliyar fiska ta gashi ya sha gyara, da ta shiga fesa mun turare sai da na soma atishawa, kaloli ta samun masu kamshi.Da na kalli kaina a madubi sai na ce Alhamdulillah ni ce haka?Ita ma sai yaba ni take yi, ta shirya, sun zo daukarmu Usman ya ja motar suna gaba shida Abida ni kuma a ka bude mun baya ashe ya Aliyu na cikin motar.Sanye yake cikin lallausan yadi ruwan madara, kalar kayana ke nan hular kube ce kai yayi kyau matuka, sam bai kalleni ba.Waya ma yake yi motar tana tashi wutar motar motar ta dauke dai dai lokacin kuma ya gama wayar.A hankali motar ke tafiya motar shiru sai sanyin (AC) da wani dan sauti dake tashi a raidiyon motar mai sanyaya rai, ban san ko wacce zabiya bace mai wakar ba, tunda ba sauraran wakar turanci nake ba.Sai dai wakar tamasoya ce, kalamar zabiyarsun haddasa min shiga wani irin yanayi, na lumshe ido tare da jingina baya na a kujerar motar.Kamar daga sama naji saukar tafin hannunsa a saman nawa, da sauri na ware idona, a zatona bayanan zabiyar ne suka sani dan karamin mafarki.hhhhh,kujita da shiririta.. Amma sai naji yatsunsa suna ratsa tsakiyar nawa, lokaci guda kuma ya matsatse su tsam.Na dube shi da sauri sam ba zaka ce shi bane.Don har yanxu yana fuskantar inda dama yake fuskanta, na kalli hannuwa na ma duk da cewa a kwai karancin haske bai hana ni ganin sarkakun hanuwan namu ba.Na sake mai da baya na jikin kujerar tare dasauke yar karamar ajiyar zuciya.Lumashe ido nayi ina tuno karon da mukayi dashi da zun, goshi na da hanci na suka dakikirjinsa.Na tuna hanuna da nasa suka hadu wajen daukar wayar.Hannuwa na farare sun sha lalle, na lura da yanda ya tsurawa hannuna ido na yan sakwanni a lokacin. A raina ina ta mamaki da tam bayar kaina, shi wanan ya canza daga jin kan ne?Koko isa ce tasa shi yin haka?Wata zuciya ta ce koma me nene mijinki ne a yanzu.Tsayuwar motar ne yasa ni bude ida nuna.A zatona in zai fita dole ya sakar min hannu,amma har muka fito hannuwan mu sarke, a haka yayi ta daga waya na kalli gurin da muka zo, an rubuta Cristal Garden da wani rubutu mai yi kala kala na wuta.Usman ya shiga ciki ya fito sanan muka shiga tare.Dam gurin ya cika da mutane an wadata ko ina da kayan ciye ciye da na shaye shaye, naga muta ne manyan mutane da banyi tsammani ba. Anci ansha kuma anyi wasa da kudi, sai dai duk yanda abokan ya Aliyu suka so muyirawa yaki ko mikewa tsaye.Dan haka duk wanda ya matsu da ya yi mana liki sai dai ya ishe mu a kan kujerar mu, abokan shi da kawaye na sun sha rawa.Sai kusan sha daya a ka tashi, mu kam sai sha biyu sanan muka tafi don sai da aka kwashe kowa.A kofar gidan mu motar ta tsaya, na yunkura zan fita, sai naji ya dafa hannuna, wato ya dora hannunshi a kan nawa.Na kalleshi shima ya kalle ni, dai dai lokacin Usman ya fita, da ma mun sauke Abida a gida.Aliyu ya ciro wayarshi ya haska fiska ta, ya cire hannunshi da ke kan nawa, ya dora a kan kuma tuna ya shafa har zuwa dokin wuya na.Sannan ya juya bayan hannunshi ya shafi haba ta, dole na lumshe idanuna abin sai kace a mafarki.Ya tsansa dan manuni ya saka ya gewaye lebuna na, na bude ido ina kallonshi, murya kasa kasa ya ce, ki bar wayarki a kunne zan kira ki.A jiyar zuciya na sauke, sanan na amsa a kasalance to.Tsakar gidan mu cike da mutane duk sunyi shinfida sun kwanta, kasancewar lokacin damina ne amma anyi kwana biyu ba ayi ruwa ba.Don haka gari duk ya dauki zafi.Na nufi uwar daka, nanma duk jama'a ne kwance, gado na dai ba kowa.Na cire kayan jikina nai daurin kirji sanan na fada kan gado.Iya can na varo ta a falo tana yin sallar nafila, a rai na na ce iya koda biki ba a daga kafa.Filo na dauka na rumgume ina tuno abubuwan da suka faru yau, tamkar almara ji nake yau na zama mace sosai.Karar ringing din waya ta shi ne ya dawo dani cikin hankali na, na dauka cikin faduwargaba na ce salamu a laikum.Muryarshi can kasa kasa ya amsa sanan yace ke da waye ne a nan?Na runtse ido dan yanda muyarshi take ratsa dodon kunnena, na ce ni da mutane amman sunyi bacci sunyi shinfida ne a kasani a gado nike, ya ce ok, kin san me yasa na kira ki?Na ce a a ya ce, saboda mu fahimci juna... Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347. A raina na ce abin da ya kamata a ce shine a farko ya koma karshe.Tamkar ya shiga raina.Ya ce kila kiga abun babu tsari ko?Kafin na bashi amsa ya ci gaba.Ni irin nawa tsarin kenan, kina jina?Na ce eh.Yace to yanxu sai ki fada mun dokokinki kafin kiji nawa.Da sauri na ce ya Aliyu ai bani da wata doka sama da ta Allah da manzonsa, wada suka tsara ita ce abin bina doka ta ni kadai in bika.Gud to me kike so me bakya so?Zan so in soma jin naka yaya, tunda kaine babba.Ya ce, to da farko dai bana son kazanta, duk inda zan shiga a gidan bana so in shaki wani wari.Kuma bana so in ganki babu tsafta ko in shaki wani wari daga jikinki, sannan ina son komai

Chapter 4 of 25