Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels DARAJAR 'YA'YANA1-01 Posted by ANaM Dorayi on 11:41 PM, 08-Mar-16 Under: DARAJAR 'YA'YANA ___________________NA ___________HALIMA K/MASHI Cikin sauri sadiya take yin komai dan bata son mai gidanta ya dawo ya sameta ba yanda idonsa yake bukata ba.Tuwon (semo) tayi mashi miyar kubewa danya, sai farfesun kafar sa, sanan ta tanadifura da nono, tasa a cikin fridge don tana bukatar yayi sanyi.Ta share ko ina na gidan fes ta wada tashi da kamshi turare, taje ta fesa wanka sanan ta bata lokaci a gun kwalliya.Kankwasa kofar da taji ne ta tuna da 'yan yaranta, da sauri taje ta bude musu, kai tsaye ban daki tace su nufa.Wanka ta sake yi musu sanan ta shirya su cikin sababin kayansu masu kyau ta feshesu da turaruka.Ta dawo dakinta inda ta rasa wane kayane ma zata saka, a karshe ta yanke shawarar saka wani jan material riga da siket.Ta dubi kitsonta kanana da ta yarfa a madubi, sanan ta kashe daurin dan kwali. Tasan yau zata burge mijinta, musanaman da ta kalli lallen hannunta na fulawa da aka zana mata.Ta kalli agogo karfe shida da kwata, wayarta wadda ta dauke saboda rashin chaji, ta jonata chaji.Ashe garin sauri bata sa dai dai ba, don haka bata samu chajin ba har aka dauke wuta. banda haka da taji yanzu mijinta yana dai dai ina?Kwnkwasa kofar ne ya dawo da ita daga haushin rashin cajin da wayarta bata da shi, ita da yaranta suka diba da gudu don taryo mijinta.Tana bude kofar shine tsaye, sanye cikin kayan yansanda, daga ka ganshi kasan babban jami'ine, ta fada jikinshi tare da rumgume shi, amma me?Sai taga ya sabule tare da cewa sannu da gida.Cikin mamaki ta amshi ledar hannunsa tare da jakarshi, ya tsugunna yana sha kan yayan sa cikin jin dadi da kewa, sadiya ta tsaya cike da mamakin saboda al'amari da take gani a gurin me gidan nata.Abin da tasani a duk lokacin da ya dawo yakan iso ne a marmatse cike da kewarta, da ya shigo burinsa kawai ya rungumeta tsam a jikinsa kafin yaran, amma yau sai taga ita ce ta rumgume shi har yana sabulewa, lallai wanan sabon al'amarine a gurinta.To ko dai gajiya ce take damunsa?Kokuma fushi yayi ya gaji da kiranta bai samu ba?Ta dubi kanta, kokuma kwaliyarta ce batayi ba?Ta sake wai wayawa ta kale su inda yake rungumarsu daya bayan daya.Da kausar ya soma, sanan Al'amen, sai mama ta tuno yanda yake mata a duk juma'ar da yazo, ya kamata ya fi dokinta a wanan karon da ya hada saty biyu bai zoba.Abin duk ya dameta, tana tsoron kada wata masifa ko annoba ta ratso cikin kyakkawan zaman nasu, tana tuna da yadda take makale a gefen damansa sannan ya dauki mama da hannun hagunsa har cikin falonsu.Yanxu dai ba zatace ganin yara bane, domintasan yaransu sun taso sun samesu cikin wata rayuwa da suka shinfida ta shakuwa da kaunar juna.Sun saba ganinsu rungume da juna, sun saba ita da yaran suyi ta kokuwa a jikinshi, basa yin wani abu da zai kawo matsala ga tarbiyar yaransu, amma sukan rungumi junako yin falo da junan ana hira.Sun rigata shiga falo, ta shigo nan ma ta sake kallonshi, mamaki ganin ya zauna shi da ke zarcewa dakinsa, can suke zuwa ya basu tsarabarsu. Sanan ya basu ta iya ya ce su kai mata, sanan kada kudawo in na huta zanzo in gaidata, sai mu dawo tare.Su ce to Abba, su tafi suna tsallensu.Shi kuwa suna fita wata ran ko wanka baya yi zai rungumota ya ce Dear my choice a matse nake.Ya wancin lokacin sai ya samu natsuwa kafin ya ci abincin ba yan yayi wanka.Dan Aliyu mutum ne mai matsanan ciyar bukata.Cikin damuwa ta isa kusa dashi.Yaya Ali yau kagaji sosai ko?Ya dubeta me kika gani?Ta ce, baka saba zama cikin falo ba.Ya miko hannu bani ledar nan in sallami yaran nan.Ya fada ba tare da ya bata waccen amsar ba.Ta miko masa kanta daure ta nufi dakinsa da jakarsa, ya ba yaran tsarabarsu, kayan ciye ciye ne da na wasa, sanan ya mike ya nufi dakin sa.Kausar tace, abba yau ina tsarabar iya?Sadiya daga cikin dakinta ta kaso kunne taji amsar da zai ba da.Ba tare da ya waiwayo ya dubi kausar ba, yace kinga magariba ta kusa, bari in anyi sallah sai muje ko?Ya shiga daidai lokacin ta shiga ban daki dan hada masa ruwan wanka.Ta fito yana zaune bakin gado yana kwance igiyar takalminsa ta iso gurin.Da sauri ta tsugunna tare da cewa abba kausar yau kuma harda aikina zaka shigar min?Ta ci gaba da kwance takalmi tana cewa, yau duk na ganka wani iri daban, ko duk gajiyar ce?Ya ce gajiya saikace ba jami'in tsaro ba?Ta soma balle masa maballen riga, to baka jin dadin jikinka ne ko? Yaja tsaki, dan Allah ki bar ni da tambayoyinnan naki please, gabanta ya fadi, ta dubeshi da gaske yake yi fuskarshi daure.Jikinta yayi sanyi, ta gama balle botiran, ya mike ya nufi ban daki ta mike zata taimaka mashi kamar yadda ta saba, ya shiga sai ya banko kofar zata tura sai taji karar makulli yana kulle kofar.Cike da tsoro taje dakin tana kallon kanta a madubi, ko dai batayi kyau ba ne yau?Ta duba ba wata makusa, ta kara jan baki da turare sanan ta fito ta same shi yana shafa mai,ta isa gurinshi, ta ciro masa kaftani da wando na shadda mai ruwan sararin samaniya, ta ciro hular da zata dace da kayan ta ajeye masa, amma sai taga ya janyo jallabiya mai dogon hannu fara sol ya saka.Daga nan sai ta koma ta jingina da bango dan jiran ganin sarautar Allah.Ya fita, ta bishi ganin zai fita waje ta ce, tabban kausar abincin fa?A sanyaye tayi maganar.Ba tare da ya waiwayo ba ya ce, sallah zan yi tukunna.Kausar ta ce,Abba ina kayi sallar ka dawo kaje damu gidan iya, kada kaje daga can.Ya dubi yaran da murmushi zan zo muje kunji?Suka ce to Abban mu, bari muyi muma sallar.Ko da tayi sallar sake zama tayi gaban madubi tayi sabuwar kwalliya sanan tayi canjin kaya daga jan yadin zuwa leshin ruwan dorawa mara nauyi .Ba kamar ko yaushe da yake kashe waya baina zasu ci abinci wayarshi kunne kuma jifa jifa yana amsa kira.Guri daya taji dadi ya zage ya kwashi abinci kamar yanda yake yi ko yaushe, haka nan haka nan 'ya'yan shi yana ta surutu da su.Amma ita ya dauke wuta da lamarinta har ta kasa cin abincin ma, so take ta tuno kurun laifin da tayi masa dan kawai ta bashi hakuri.Bata saba da wanan yanayin da suke ciki ba, zuciyarta ta ce ko ya ta kiran wayarki ne ba a ji?Da sauri ta dube shi.Abban kausar nasan kayi ta nema na layi naa kashe ko?Ya dubeta ban nemi layinki ba, ba wuta ne ta ce eh ba wuta.Kutashi muje gidan iya,suka mike cikin murna,Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Kausar ta ce,Abba, momi bata dauko hijabinta ba.Ya ce, bata son zuwa ne, tayi aiki ta gaji.Wanan ya nuna mata ba a son zuwa da ita tunda ba a tambayeta ba bare a ce ita ce tace ba za ta je ba.Sun barta cikin tunani da jimami, ta gyare gidan musanman gurin da suka ci abinci, tayi ta jiransu tana zaune a falo tana kalon TV amma inda zaka tambayeta abinda ake yi a TV din ba zata fada maka ba.Ita burinta kawai ta san laifinta, amma ina ta tuna da cewa anjima da yazo dole zai sauke ko mai dan tasan cewa ba zasu taba kasancewa gado daya da shi ba ya iya kauda kai daga gare ta.Itama zata ja aji lokacin har sai taji dalilinsa, ganin sun kai har sha daya sai kurum ta cire tayi shirin bacci, kayan baccin bakake masu matukar daukar hankali, ta dora hijabi saboda da yara zai shigo.Kausar ce kurun batayi bacci ba, Al-Amin yana sabe a kafadar dama, mama a ta hagu, kausar din tana biye dashi suka shigo.Kai tsaye dakinsu ya nufa da su, tabi bayan su yana kwantar da su, ya fita ita kuma ta gyara su, sanan tayi musu adu'a taja musu kofa.Dai dai lokacin kausar tana cewa momi sai da safe, sadiya tace, Allah ya kaimu kausar.Dakinta ta nufa ta sake fesa turare, sanan tanufi fridge don ta dauki furarshi wadda ta riga ta dama.Shiru ta tsaya dan ya riga ya dauka, ta nufi dakin shi.Yana zaune bakin gadonshi sanye da kayan bacci, laptop ce a gabanshi kan dan tebirin da ake ajeye mai fura.Kofin yana hannunshi yana kurbar furar, idonsa sanye cikin farin gilashi ta ce, tace ashe har ka dauko furar ka?Ba tare da ya dubeta ba ya ce eh.Ta zauna kusa da shi wai abban kausar nayi laifi ne da ake ta share ni? Ban gane na neke ta share ki ba?Ta ce na gane yau duk ka canza ko na ce abubuwa sun canza kamar ba mijina ba maita rairayata?Ya dago ya dubeta baki min komai ba.Ta dora hannunta a kan cinyarsa, abba kausar to naganka ne ni yau irin kamar banyi kyauba din nan.Ya kalleta Dan Allah ki barni ina yin abu mai muhimmanci ne.Ta ce, amma dai da aka saurare ni bai fi abin da ka ke yi muhimmanci ba?Ga mamakinta sai kawai taji ya daka ma tsawa,kin san me kike fada kuwa dan Allah tashi ki bani guri a nan,ta zaro ido, mikewa tayi ta nufi kan gado ta kwanta a ranta tana cewa ka gama kazo ka same ni ina nan kwance.Abin ta'ajibi ranar dai haka ya raba dare yana harkokinshi a internet sabon abu ga Sadiya mutumin da in yazo satin karshen mako hatta wayoyin shi kashewa yake suna manne da juna har sai ya tafi yana cike da kewarsu.Ko da ya kashe laptop ya kwanta juya mata baya yayi,don Allah babban kausar me yake faruwa ne?Dan Allah in wani abu ya faru ne ka sanar dani zan baka hakuri, ban saba da wanan rayuwar ba.Cikin zafin rai wanda banta ba ga ni ba ya ce, nace bakiyi mini komai ba, kina son dole sai nayi maki karya ne?Dan Allah ki bar ni in huta ki barni na ce.Ta rike kai to banyi maka laifiba me yasa ka canza min?Nasanka kai mutun ne mai bukata a marmatse ka ke zuwa in kayi saty daya, wanan satyn har saty biyu kayi amma sai naga kazo bana gabanka.Ya zoro ido to yau ban da bukata ko dole ne?Ya ja tsaki, tashi dan Allah taf dakinki bana son jaraba kada ki dameni.Kuka ne ya subuce mata, ta fita a dakin tunda aka kawota gidan yau ce rana ta farko da zata kwana a dakinta ita daya.Dan ko haihuwa tayi basa raba makwanci, ta fito falo ga mamakinta sai taga kausar tsaye a falo tayi saurin dai daita fuskarta tare da share hawayenta ta nufi kausar.Me kika fito yi?Kausar me kike so?Ta ce, mome naji abba ne yana fada ne, me kika yi masa?Ta kama hannun yariyanyar suka nufi dakin yara.Kan katifarsu ta kwantar da ita ta kuma ta kwanta a bayanta tare da rungumeta, kausar ta sake tambayarta momi kinyi laifi ne Abba ya ce ki fita? kasa magana tayi don al'ajabi ne ke dankare cikin ranta, ta danne hawayenta ta ce kausar laifi nayi masa.Kausar ta ce, momi ki bashi hakuri mana,'to' Sadiya ta ce zan bashi sai da safe in ya huce kinji?Kausar tace, eh.Sadiya ta ce ki daina tashi cikin dare kin ji, tadinga shafa kan yarinyar tana lallashinta hartayi bacci ita kuma ta koma duniyar tunani tuno farkonsu.Iya mahaifiyar Aliyu ya ce ga mahaifiyata, uwarsu daya ubansu daya,su 'yan asalin jahar jigawa ne, a karamar hukumar Hadeja.Mahaifiyarsu ta rasu ta barsu su hudu mazabiyu mata biyu, kawu Adamu da kawu Dauda duk iya ce babbar su.Lokacin da mahaifiyata ta na budurwa, dan haka iya ta dauketa lokacin suna zaune a Dutse da mai gidanta da yaranta hudu.Yaya sulaiman yayazakari, yaya sani, sai cikin yaya Aliyu.Mijinta ma'aikacine a ma'aikatar gona ta jahar Jigawa, daga baya yayi ritaya inda ya dawo kaduna da zama sana din dan uwansa dake noma.A unguwar mu'azu ya sai gida madaidaici a ciki aka haifi Aliyu kuma a nan aka aurar da mahaifiyata inda ta auri mahaifina wanda yakasance ma'aikacin gidan Raidio kaduna.Amma dan zariya ne kuma zariyar aka kaita,yana da mata biyu da yara kusan goma, ko a lokacin.Maimuna mahaifiyarta ta kasance mai hakuri da juriya, duk da cewa bai kasance mutum mai cika hakkokin iyalansa ba.Amma bata taba kawo kararshi gurin iya ba,don tasan iya tana da fada sam bata da wasa.Shekarar da yaya sulaiman yayi aure shekarar ce mujin iya Allah yayi mai rasuwa,sunji mutuwar ta farat daya yana cikin sallah yayi sujjada a masallaci har aka idar bai dago ba.An dago shi sai gawa, ashe mutuwar kenan.Yaya sulaiman koyarwa yake yi a makarantar yan mata dake Tudun wadan wada wato Sai yaya zakari kasuwanci a babbar kasuwar kaduna, duk da cewa ba wani babban dan kasuwa bane,Sani kuma da ya gama secondary sai kurum ya shiga wurin gyaran motoci dan a lokacin babu halin ci gaba saboda yanda karatu ya zama a kasarmu sai yayan masu shi.Talaka yana so yake hakura.Ya Aliyu karamin su kuma suna tallafa mashi don ganin ya samu karatunshi, kwanci tashi suma duk suka yiyyi auransu.Lokacin da mahaifiyata tana dauke da da tsohon cikina don ta jima bata haihu ba, har lokacin iya bata gane yar uwarta tana cikin matsala ba, sai bayan ta haife ni.Lokacin da taga komai babu, abin ci a gidan gashi ya sake yin aure ya ciko mace ta hudu,iya ta same shi ta ce, yanzu tsakanika da Allah Abubakar hakan da kake yi dai dai ne?A ce ka ajiye mata babu kulawa ba abinci badai baka da shi ba sai don zalunci?Ya ce ai za a siyo.Tace, gara ma ka siyo don ba zan dauki zama da yunwa ba, in an ganka a waje kwas kwas har da mshin din hawa gareka amma a gidanka da yunwa.A daddafe akayi suna inda aka rangada min Halimatu Sadiya, iya ta tasa mahaifiyata ta tafi da ita, tace ba za a bartaba haihuwar fari ba kulawa ba,Ita kenan gareni dan wadan can yan uwan namu sai munyi tafiya mai tsawo kan mu gansu.Sai da mahaifiyata tayi kusan wata shida lokacin ni da ita munyi bulbul tamkar kada iya ta bari mutafi, amma yanda mahaifina ke ta suntirin zuwa yana kuma turo mutane don baiwa iya hakuri sai ta hakura tace mu koma.Amma ta ja masa kunne sosai, to dan saukin yanzun ba kamar da ba, hakan yasa ki shiyoyin jin haushinta suna ganin ya fifitata shi ko tsoron karr a dauke ta ne don iya ta tabbatar masa in tazo taga ba daidai ba to zata tafi damu.Shakarata biyu ta sake samun wani cikin tun yana karami take fama da laulayi iya tana zuwa tare da yayanta akai akai suna duba mahaifiyata tare da kawo mata abubuwa.Iya taso ta tafi dani amma lokacin an ce inna da kalafucin uwa, kulafaci gareni sosai ta hakuraKu ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Gurin haihuwarta kuma taji jiki da kyar ta haifi yar bubu rai.Sanan itama jini ya balle mata ya dinga zuba kafin aje Asibiti rai yayi halinsa, ance iya taji mutuwar nan kaman me.Bayan anyi bakwai aka raba dan abinda ta bari sanan iya tace ba zata barni ba dani zata tafi da kyar mahaifina ya yarda don shima yaji mutuwar yayi kuka tamkar ranshizai fita , to mafarin zamana a gun iya kenan.Na taso cikin gata da tarbiya duk da irin son da iya take yi min, bai sa ta kasa bani tarbiya ba.Lokacin da aka kawoni gidan yaya Aliyu yana shekararshi ta karshe a makarantar kwana ta barewa kwaleji dake zariya.Sam yaya Aliyu halinsa ba iri daya bane da yayyansa, don su suna da sakin fuska da fara'a, amma shi kullun rai a hade ta bakin iya in tana masa tsiya takan ce na rasa inda ka gado wanan halin naka na shegen miskilanci, kullun cikin bacin rai sai kace jakadan yan wuta. Tunda nake gidan bai taba yi mun wasa ko hira ba, magana in ta hada mu to bata wuce yazo bai ga iya ba, yace Sadiya ina iya?Tare da haka ba shi dai raini ko rashin kunya, sai dai kafi ya ga saurin fushi gami da zafin zuciya. Yanada matsananciyar tsafta da ibada Iya na yaba masa a nan, tunda na taso Allah baitaba nuna mun bacci iya na dare ba, sai dai na rana, bayan azahar. Duk lokacin da na farka zan ganta tana yin nafilfilu. Yaya Aliyu akwai iya saka kaya, bani manta kawayena in sun biyo mini makaranta suka ganshi sai kiji suna cewa, sadiya yayan nan naki dan kwambo ne, ya cika yanga gashi baya fara'a.Nakan ce kurufa mini asiri kada yaji.Burin yaya Aliyu aduniya bai wuce ya zama police ba, kalmar da Iya ta tsana duk lokacinda ya ce mata shifa in ya gama karatunshi zai shiga makarantar horar da yansanda.Sai ta ce masa ya daina wanan tunanin don ita bata son dan sanda, wai a nata ganin sharri kullun ake koya musu, kullin suna kan titi suna karbar cin hanci.Wani lokacin tace, dan sanda da aka ce ko ya mutu gawarsa tana fita da ban, dan baki take to ban amince ba.Shi kuma sai yace, iya kiyi min adu'a buri na kenan zancen zancen ace kaza kaza duk sharri ne babu ma'aikatan da babu na gari, kuma babu inda ba battace.Kimin adu'a in zama mai kawo gyara a cikinsu kuma in na zama dan sanda in sha Allahu sai kinyi alfahari dani.Takan tabe baki ta ce, uhm ni rabu dani da wanan zancen, ni dai insuna yi sauraransu kurun nake yi, don sam in yaya Aliyu yana fira da iya bana sa baki, domin tsawa zai daka min ko ya harareni, haka nake rayawa a raina ba wai dan haka ta taba faruwa ba.Iya tana yin wainar saidawa a cikin gida, muna yin ciniki sosai, wani lokacin har da sha'anin buki suna ko walima duk muna yi da sana'ar ta take yi mana dawainiyar karatu ni da yaya Aliyu, sai dan abin da sauran yara suka kawo mata.Dan suma yanzu ko wanensu yana nan da dawainiyar iyalansa, karatun ya Aliyu shine mai cin kudi, dan Alokacin yana karatun digree sa ne a jami'ar Ahamadu bello dake zariya.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Yana karantar (Engineering) ban san yanda zan kwatanta muku ra'ayinsa ba, amma shi mutum ne mai babbancin hali da ra'ayi.Bayan ya kammala karatun sa ne ya dagewa iya yayyinsa shifa sai yaje police Acadamy, wato makarantar horar da manyan yansanda dake wudil jahar kano, dakyar ya sha kansu.Ko da yake har sai da kawunsu kannan iya dake Hadeja,Kawu Adamu ne yaje har gida ya lallashi iya.Bayan ta yarda tace, to ita fa bata da kudi,yaranta kuma suna fama da iyalansu, dan haka yaje ya nemi kudi.Aliyu ya ce, iya ai na fada miki asaida gona ta, ta gadonmu da aka raba mana.Nan ma da kyar ta yarda kawu Adamu shineya saida gonar Aliyu yaje ya amsa, haka yayita zirga zirga tsakanin kano da kaduna har sai da yayi nasarar shiga police Acadamy.Ranar farko da yaxo ni kadaice ina cikin wanke kayan waina bayan mun tashi, iya bata nan taje kai kudin kayan miyan wainar gobe, sai kurum naji sallamar sai naga mutum tsaye kyam da kayan dan sanda riga blue mai haske wando baki, ga wanan takalmin na su da hula.Nikuwa dama gani da tsoron Dansanda, sai naji cikina yana kugi, fuskarshi daure yace, bakinki yana ciwo ne, bakya iya amsa sallama ko? Cikin in-ina nace, wa...alai...kassalam.Ya zuba min harara, yau ne kika fara ganina ne da har zaki tsareni da idanu ko na can za maki ne?Na sunkuyar da kai, a'a ya nufi dakin nace bata nan ta je wurin Isa mai kayan miya, ya ciji ya tsa to dauko min makullin dakina najena duba inda na san iya tana ajewa na dauko masa da zan bashi sai da na dan rusuna.Ya amsa ya nufi dakinshi nazo na karasa wanke wanken na gyara gurin ya fito cikin gajera wando da yar T-shirt irin ta yansanda,Ina cikin kicin zan dora tafashen kashin waina, yace baki san mutun yazo kiyi mai tayin abinci ba, kenan ina ganin rowa zakiyi?Nace nayi zaton ko kana azumi ne, na ga kullun kana yin azumi,yace, oh, dama kina samun ido ne har kika san cewa kullum ina Azumi?To yau ban yi.Nace, duk abincin ya kare sai sauran tuwo kuma baka cin dumame, sai dai in ko na dafa maka wani abu.Yace barshi nasha cornfilakes,ya juya ya nufi dakin sa.Na sauke ajiyar zuciya ban san meyasa ba yaya Aliyu in yana guri bana so in tsaya a gurin sai in ga duk ya cika gurin,gashi tsananin tsoransa nake bai dai taba duka na ba watarana ne dai da yake iya gadanga take ce masa sai tace in kira mata shi, ni kuma naje nace iya ta ce kazo gadanga.Wata tsawa da yayi min kadan ya rage in saki fitsari, ya dora yatsinsa a dan manuni a goshi na.In kika sake ce min gadanga sai na zaneki tas kinji ko?Jikina yana bari nace, kayi hakuri.Don tsoro lokacin har fitsari nayi a wando.Lokacin da iya ta dawo tai murna da ganin autanta, nan suka zauna suna yin fira, cikin hirar ne naji tana yi masa zancen aure, inda ta ce gadanga dan Allah ka nemi matar aure kasan shekarunka nawa yanzu?Yayi dan murmushi ni kwan nasan shekaruna, muke nan kullum cikin rubuta date of birth ba dole in rike shekaruna ba?Talatin da uku ne kacal. Iya tayi dariya talatin da uku shine kacal?Ai dai cikin sa'anninka ina tsammanin kai kadai ka rage ba kai aure ba.Ya ce iya ba ni kadai na rage ba, kin manta da usman?Ta ce, usman bikin shi kafin Azumi ba kuyi waya bane?Aliyu ya zaro ido, iya da gaske?Tace, ko jiya na kira shi na fada masa yau zan shigo shi ne zai ki sanar dani?Iya ta ce kila sai kazo din za ka ji zancen.Ya ce, iya kiyi adu'a kawai amma ayanzu ba mata a ga bana, kokari na in hada wanan course din nawa.Ta ce, Allah ya taimaka.Ya ce sauran mu wata shida.Ta ce, to Allah yasa a gama cikin nasara, ni dai fata na ka zama mai gaskiya da amana, kayi aiki a kasarka da kishi.Ya ce in sha Allahu, na gode.Duk ina jin su har suka gama ya dube ni ita waccen sunyi jarabawar J S. C.E din?Iya ta ce, tin yau she har sun amso yan zu kici kicin shiga SS din ta muke yi, ya ce zo ki bani saka makon na ki in gani, dan nasan bawata kwanya ce da ke ba.Iya ta ce, in ji wa?Sadiya boko da islamiya tana da kokari.Na dauko gaba na yana faduwa na bashi ya duba sanan ya kalleni babu laifi, amma kina jin turanci?Na sunkuyar da kai, amma ban iya bada amsa ba.Ya ce shirmen yaran hausawanmu kenan, kuna jin tsoro ne kada kuyi ba dai dai ba ayi muku dariya, to ai gara ayi muku dariyar sanan a gyara muku.To ni dai daga yau kada ki kara mun hausa.Har in koma duk kuma zuwan da zanyi in baturanci zakiyi mun ba bana son jin maganar ki.Iya ta ce, kuji mun fin karfin hali gurin gadan ga, wanan ai mugun horo ne.Yare ba na uwarka ba, ba na ubanka ba kace dole sai tayi maka magana da si.Ya ce, in ba haka ba yau she zata iya ga yanda zamanin namu ya zama sai da karatu, ko da ta gama scondary zaki mata aure? Iya ta ce, tana samun miji zan sallamata, don haka kar ka takura mata.Ni dai nayi ciki na barsu nan suna ta jayayya, yana cewa ilimi ko dan tarbiyar yara ai ko ni ba zan auri matar da bata ta shiga jami'a ba.Iya ta ce Allah ya taimaka ni tawa tana samun miji zan turata can gidan mijinta

Chapter 1 of 25