ya 'kare da ikon Allah._
🍃*DANGIN UBANA*🍃
Story & Written
By
Milhaart
Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne.
*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________
*Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.*
Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
Page
33&34
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._
_Continuation........_ jiki a sanyaye mummy ta nufa part d'insu Haisam na Mata magana Amma Bata kulashi ba, a parlor ta zauna tana matsar kwalla, Haisam cikin tashin hankali ya zauna a gaban ta had'e da riko hannayen ta, cike da kulawa yace "Umma me ya Faru ne ban tab'a ganin daddy acikin irin Wannan yanayin ba a iya zaman da mukayi dashi ba, Haka ma mummy har kuka naga tana yi kema gashi kukan kike yi what Happened Umma?"
Cikin shesshekar kuka Tace "Nothing Haisam, babu abinda ya Faru"
"Dan Allah Umma ki fad'a ya za'ayi kice babu abinda ya faru Kuma kike kuka Dan Allah ki fad'a"
Mikewa tayi a d'an tsawace Tace "Nace maka Babu ko"
Ta shige d'akin ta.
Ya dad'e a wurin yana zaune daga baya ya tashi ya bar gidan ma gaba ki d'aya.
"Kin 'bata min Rai Maryam, Akan me Zaki sa ta agaba dole sai ta amince kar ki manta fa kece Kika sa na d'auko su na ajiye su akarkashina ba takura babu takura Jan su da mukayi a jikine yasa har suka sake jiki damu muka Zama one and family, tunda tace Bata so let her be ana Dole ne? Bafa yarinya bace ba tasan me take so da abinda bata so, Shima Abdallah zan Kira sa na fad'a Masa ya bar maganar sabida na lura ya na neman sata a Rai daga jiya zuwa yau"
"Uhmn Alhaji Kenan yanzu duk abinda mukayi masu da abinda zata saka Mana Kenan, Alhaji dama don mu ba wallahi nasan inda Bata mutu ba da ta kusa mu...... "
A tsawace yace "Ke Zaki kashe ta? Nace ke Zaki kashe ta?"
Ta girgiza Kai had'e da sunkuyar da Kai, iska ya hura kana ya sassauta Muryar sa yace "Maryam zaki goge ladan da Kika Samu idan Kika cigaba da fad'an haka mun taimaka Mata don Allah Ne ba don ta biya mu ba, kar ki manta fa kece Kika kawo shawarar taimaka musu har Kika sa na dawo na su cikin gidan nan, Dan Allah idan na Isa dake ki bar maganar nan ban yarda ki sake Mata maganar ba bare ki nuna Mata a fuska"
" Insha Allah zanyi yanda kace kayi hakuri"
Ma'isha da Meerah Havilla Ice cream suka nufa, Bayan Meerah ta tabbatar da ta kwantar wa da Isha hankali, ice cream suka Sha har sai da akayi la'asar tayi suka koma gida, sai da Isha ta ajiye ta a gida kana ta wuce gida.
Haisam kuwa school ya Shiga, Duk da bayi da Lectures jiran ta yayi ta gama Lectures suka Sha hiran su ya samu hankalin sa ya kwanta , sai Kuma yayi sa'a yau bata fito da motar ba hakan ya bashi kaita gida.
Bayan sallar Isha Umma kasa zuwa gun Mummy tayi suyi hirar da suka Saba, Ma'isha na d'akinta taji Duk bata jin dad'in zaman hakan Yasa ta fito parlor ganin ba kowa ta nufi d'akin Mummy da sallama ta shiga Tace "Mummy ya na ganki a kwance yau baza a yi hiran parlor bane?"
"Uhmnn bani Jin dad'i ne"
"Subhannallah me ya same ki?"
"ciwon Kaine ba wani Abu ba"
"Amma kinsha magani ko?"
"Eh Nasha"
"To Allah ya sauwaka"
"ameen"
Mikewa tayi Tace "Bari naje part d'insu Umma"
"Okay" tab'e baki Isha tayi ta nufi part d'insu Umma.
Ganin Umma Bata parlor ta wuce d'akin ta cike da mamaki Tace "Umma kema a kwance ko kema bakya Jin dad'in ne?"
Kirkirerren Murmushi tayi tace "Eh wallahi bana Jin dad'in jikina"
"Oh ikon Allah sai kace Kun had'a baki ga mummy ma a chan ta kwanta wai kanta na ciwo"
Umma a ranta Tace "Oh Allah kar dai ita ma tasa maganar a ranta kamar Ni" a bayyane ta ce "Lallai kamar mun had'a baki"
"Allah ya baku Lafiya"
"Ameen"
"Ya Haisam fa yana Nan?"
"Ki duba shi a d'akinsa d'azu dai baya Nan ban San ko ya Shigo ba"
Ta amsa da "Ok sai da safe Allah ya sauwaka"
"ameen daughter nagode."
'dakin Haisam ta nufa ta shige d'akin taga wayam Bayanan, kwan kwasa kofar d'aki tayi ko Yana ciki taji shiru hakan ya tabbatar mata da Bayanan d'aga kafad'a tayi irin I don't care, ta fice.
A hanyar ta, ta fita suka had'u da Isha yace "Princess kin dawo Kenan?"
"Eh na dawo tun d'azu"
"Su Umma fa"
"Suna kwance wai Basu da lafiya"
"Duk su biyun?"
" Eh Umma wai zazzab'i take ji Mummy Kuma Wai ciwon Kai"
"Hmm kin San d'azu bakyanan me ya Faru?"
"A'a sai ka fad'a"
Nan ya jero Mata abinda ya gani da idon nunsa , cike da mamaki tace "eh Lallai no wonder biri yayi Kama da mutum, to Amma me ya faru haka?"
"Allahu a'a lam, Umma taki fad'a min amma ki gwada tambayar mummy muji ko menene"
"kaji ka ya Haisam mummy ce zata fad'a min sai kace baka San halin ta ba, dama kaine maybe zata fad'a maka"
"Okay muje hope tana d'akinta ba d'akin Daddy ba?"
"Eh tana d'akin ta"
"Alright muje" Yana tafe tana biye da shi da sallama suka Shiga d'akin mummy sunyi sa'a bata rufe ba don tashin ta Kennan zata rufe, tana ganin si tayi Murmushi Tace "ku Kuma fa daga ina?"
"Daga d'akin Umma" Ma'isha ta bata amsa ba.
Mummy ta amsa da "okay"
Haisam yace "Mun Zo gunki ne mummy"
"Lafiya dai ko?" Ta kalli Haisam ta kalli Isha
Haisam murya na rawa yace "la.....Lafiya lau,kawai magana zamuyi mummy"
" To ku zauna mana" ta koma ta zauna a Kan gado ta d'auki Pillow ta d'aura a cinyar ta sannan ta d'aura hannayen ta akai tana kallon su.
Zama sukayi akan kushin d'in dake d'akin kasa kasa Haisam yace "kiyi magana Mana"
Ita ma Tace "Kayi magana Mana"
"Princess kiyi magana Mana Dan Allah"
"A a wallahi Yaya ai kai kace min zaka mata magana mun Zo Kuma ka kasa"
Mummy na Kallo ikon Allah, sai kuskus take ji bakin su na motsi Amma bata jin abinda suke fad'i,a d'an fad'a fad'a Tace "Idan baza ku fad'a min ba ga hanya Nan ki fice min bacci zanyi" tana nuna musu kofar fita.
Haisam ne ya gyara Zama Yana wasa Yana d'an bubbuga kafar sa da hannun sa yace "mummy dama.....dama.....dama d'azu da na Shigo ne naji Abba na fad'a,naga Kuma kin Fad'i kalma wa Umma Sannan kina kuka Kika shige ita ma kukan naga tana yi,mummy dukkanin ku bamu tab'a ganin ku a cikin Wannan yanayin ba a iya zaman da mukayi daku bamu tab'a Jin Kan ku ba,shine muka zo ki fad'a mana Inda Hali,don naga duk Kuna cikin damuwa"
Ajiyar zuciya Mummy tayi Tace "Son ina da niyar yi maka maganar ko da kuwa baka Zo ba, sabida nasan Kai kad'ai Umman ku ke Jin maganar ka Idan mukayi sa'a ta amince da bukatar mu,ba wani abu bane ba dama Abban kune............ "
Nan ta bayyana Masa komai Kama daga Kan mutuwar Matar sa da 'ya'yan sa da kuma dalilin sa na kin yin aure.
Murmushi Haisam yayi Wanda yake Kara bayyana kyawun fuskar sa yace "Mummy yanzu dama Akan wannan ne kike kuka Duk kuka tashi hankalin ku? Ni a ganina wannan abun ba abin tashin hankali bane ba, zanyiwa Umma magana Kuma Insha Allah zata amince, ko ba komai ai abun farin cikine wannan duba ga irin tsawon shekarun da Abba ya d'eba bayi da niyar aure ace Rana d'aya ya ce zaiyi, Kuma na tabbata Insha Allahu Abba zai rike ta da zuciya d'aya sabida na lura Shima Yana da son Mutane Shima kamar daddy, insha Allah zata amince fatan mu shine Allah ya tabbatar da alhairi"
"Kaai Amma naji dad'in maganganun ka son, Allah yasa ta amince d'in"
"Ameen Mummy"
Ma'isha da tun d'azu take kallon su Tace "Ni Idan akayi auren Nan ai barka na sabida Abba na auren mummy gidan su zan koma da Zama in huta da....... " Turo kofar da akayi ne da d'an karfine yasa ta kasa karasa maganar ta Duk su ukun suka Mike a razane mummy baki na rawa Tace "Al.... Alh..... Alhali Lafiya? Tana leka Bayan sa ganin ba kowa ta cigaba da magan "Alhaji Lafiya na gan ka a Haka?"
Rai a mugun 'bace yake nuna ta da d'an yatsa Yana fad'in "Haven't I warned you not to talk about it again? Haven't I?"
"Alhaji Amma...... "
"Shut up!!! Amma me? Nace amme? Akan me Zaki zauna kisa yaran Nan a gaba kina fad'a musu abinda bai shafe su ba iyee? Answer me?"
Mummy kasa magana tai ta sunkuyar da kanta a kasa tana kuka Mai cin Rai Duk yanda taso ta Hana kukan ta ta kasa sabida yanda daddy ya ke mata tsawa da fad'a a gaban yara, da su ya sune abun Sam bazai Dame ta ba.
Ma'isha Murya na rawa Tace "Daddy please Daddy kayi hakuri wallahi ba laifin mummy bane mune muka sata a gaba Dole tasa ta fad'a Mana, Kuma....... "
"Ma'isha!!! Ya Kira sunan ta a wani irin Murya Wanda hakan yasa ta rike bakin ta da hannun ba tare da tasan tayi hakan ba, ba tare da ya kalleta ba yace "Idan na Kuma Jin bakin ki a wurin Nan sai na 'ballaki"
Ya cigaba da fad'in "Taya za'a yi ni da gida in kafa doka Amma ki take shi? Yaushe Kika Zama Haka Maryam?"
Haisam cikin girmawa yace " Daddy please kayi hakuri Dan Allah Ni a gani na wannan abun ba abin tada hankali bane ba, yes kamar yadda princess Tace mune muka Masa wa Mummy Akan ta fad'a maana abinda ya faru sabida d'azu a gabana naga kana Mata fad'a, abinda ban tab'a gani ba Kennan tunda na dawo gidan, ta fad'a min ne sabida tasan Idan nayi wa Umma magana zata amince, sannan Abba nasan Idan hakan ta kasance zaka fi kowa farin ciki, Amma Dan Allah kayi hakuri"
Shiru Daddy Yana sauraron sa jikin sa Duk yayi sanyi, tabbas maganar Haisam hakane zaifi kowa farin ciki sannan idan Haisam yayi wa Umma magana babu Makawa zata amince, shiru d'akin yayi na d'an wasu lokuta Banda kukan mummy da na Ma'isha babu abinda ke tashi a d'akin jiki a sanyaye Daddy ya nufi inda Mummy me tsaye tana matsar kwalla, bai tsaya 'bata lokaci ba ku Jin kunyar su Haisam ba ya rungume ta Sam a jikin sa Yana d'an bubbuga Bayan ta a hankali, yace "Am sorry Maryam, am sorry please wallahi raina ne ya 'baci jin kalaman Zainab a Jan d'an uwana Sai na kasa jurewa yanda na ga ta ki Abdallah karara naji zafi sosai da kalaman ta, Amma bani da ikon da ita bazan iya tirsasata ba, na d'au lokaci Mai tsawo na ganin irin wannan ranar da Abdallah zai kawo min maganar aure, nayi matukar murna sosai Allah Allah nake na dawo gida don Jin labari Mai dad'i sai Kuma najie akasin hakan, ke Kuma da na hanaki magana akai sai Kuma Kika ki jin magana Amma maganar da Son yayi sai na gane kuskure na" d'an d'ago Kan Mummy yayi yasa hannu Yana goge mata hawaye yana fad'in "am sorry am sorry"
Haisam d'an Buge kafar Isha yayi da kafar sa ta juyo ta kalle sa murya kasa kasa yace "Kinga ko mijin ta ya rarrashe ta,Yana share Mata hawaye ta daina kukan, gwamma kiyi shiru don ba Mai rarrashin ki anan"
'dan Buge shi tayi da kafan ta yana gumse dariyar da ke kokarin kwace Masa.
Mummy zare jikin ta tayi a hankali daga jikin daddy tasa Bayan hannun ta, ta share hawayen ta kana ta gyara murya Tace "Son kaci gidan ku" Kama baki yayi yace "Laaaa Ashe ta ji" da gudu ya fita isha ta Mara Masa baya, Tace "Ja'irai kawai" suka bar daddy dashi da Matar Nan, suka Shiga soyewa abinsu.
Haisam da Ma'isha kuwa a parlor suka zauna Banda dariya babu abinda suke yi, su Haisam harda rike ciki itama Isha dariya take sosai ba kakkautawa tana cikin dariyar ne kwasam ta Mike a zabure ta wuce d'akin ta da gudu, Haisam kuwa baki ya sake Yana kallon ta har ta haura d'akin ta sai da yaga ya daina kallonta kana ya kawar da kansa Yana mamakin Shagwab'a irinta Ma'isha , a bayyane yace "Mutum bata da aiki sai kuka"
Ma'isha kuwa tana Shiga d'akin ta ta had'a kai da gwiwa ta fara rera kuka son ranta, tunawa tayi da Haisam na son wata ita ba, yanzu duk dakon soyayyar sa da ta dad'e tana yi ya tashi a banza Kenan?
Karar shigowar Kira taji ya shigo wayar ta mikewa tayi ta duba fuskar wayar ta ganin sunan Meerah yasa ta daina kukan ta yi picking ba tare da Tace komai ba, Meerah Tace "Hy Isha kin koma gida kalau, da fatan kinsha maganin da muka saya d'azu?"
"Nikam Na manta da wani magani" a ranta ta ayyana hakan Amma a bayyane Kuma Tace "Uhmmn Nasha"
"Subhannallah Isha kuka kikayi yana ji muryar ki haka Lafiyan ki kuwa?"
"Uhmn Lafiya na Lau daga bacci na tashi"
"oh sorry na tashe dama so nake na ji ko kinsha maganin nakin gudun kar jinin naki ya sake Hawa"
"Kar ki damu Nasha"
"Tohm Shikenan zan Zo gobe Insha Allah na gwada BP naki ko ya sauka, da fatan baki da Lectures gobe?"
"Akwai But da safe ne zuwa la'asar zan dawo"
"alright sai mun had'u goben please take care"
" Insha Allah thank you" a tare suka katse wayar d'ago kanta da tayi ta sauke kanta a Kan haisma da tun da ta Fara wayar Yana tsaye Yana kallon ta, Murmushi tayi Tace "Yaya ka Shigo Mana"
Girgiza Kai yayi yace "Ba Zama ya kawo ni Nan ba, Princess meyasa ki kuka? Kuma ke da wa kike waya naji kina maganar kinsha? Me ke damin ki baki da lafiyane?"
Yar karamar dariya tayi Tace "Yaya irin wannan tambaya haka wanne zan amsa a ciki?"
"Dukka" ganin ba wasa a fuskar sa Tace "Uhmn dama kaina ne yake ciwo"
"Uhmn sai akayi Yaya? Da wa kike waya?"
"Ameerah ce dama da naje gidan su ne, saai.... Umm kaina ya Fara ciwo shine ta bani magani Nasha Akan in na dawo na Sha, shine ta Kira taji ko Nasha"
"Toh naji shi Kuma kukan na mene ne?"
"umm... Ummm..... Kai na.... Kaina ne yake ciwo"
"Ciwon Kan ne ya saki kuka?"
Kai a kasa ta amsa da "Eh shine" ganin ya kure Idanun sa yana kallon ta Yana kokarin gaskata maganar da.
"Ya ciwon Kan, kin Sha maganin?"
"Eh Nasha"
" Alright, sai ki samu ki kwanta kar na Dame ki, good night" ya jaa kofar ya rufe Mata bai tsaya Jin abinda zata ce ba.
Ajiyar zuciya tayi Tace "That was closed I thought yaji" girgiza Kai tayi ,ta Shiga ban d'aki ta yi wanka tana fitowa ta Sanya sleeping dress d'inta ta kwanta sannan ta kunna datarta, ta Shiga WhatsApp, ganin Haisam a online yasa ta Masa "Hy Yaya ba kayi bacci ba?" Sai da ya d'auki kusan 5 minutes kana ya mata reply da "Eh banyi ba me ya hanaki bacci?"
Emoji na kuka ta jero masa had'e da tura masa "Sai yanzu Zaka kulani?"
"am sorry Video call muke da auntyn ki"
Tana bud'e wa ta kashe datar ba tare da ta Masa reply ba, ta gyara kwanciyar ta tana ta tuna abubuwa dayawa daga bisani bacci yayi awon gaba da ita.
```Washe Gari```
Haisam ne ya Shigo ya tarar da mummy da Daddy a parlor suna karyawa gaishe su yayi suka amsa kana ya tamabaya Ma'isha fa.
Mummy ce ta amsa Masa da "Bata fito ba kana da Lectures ne?"
"Eh Umma Lectures na karfe takwas nake dashi" ya maida kallon sa ga daddy yace "Daddy naga jaka tafiya zakayine?"
"Eh son zani abuja zanyi 3 days a Chan"
"Gaskiya daddy sun sa makan Kai a gaba Sam baka Zama Ni na manta ranar ma da kayi one week a gida"
Dariya yayi irin tasu ta manya yace "To ya zanyi Dole ce tasa"
Haisam ya ce "Hakane Allah ya dafa maka daddy"
"ameen son Mike ka Duba ta kar ku makara, mikewa yayi da sauri ya haura sama, a hankali ya tura kofar had'e da lekawa ya hango ta Akan gado ta na sharar baccin ta hankali kwance, a bayyane yace "lallai yarinyar Nan"
Ban d'akinta ya Shiga ya bud'e tap ya d'an Tara da hannun sa ya fito ya watsa Mata a fuska a razane ta farka tana ambaton sunan Allah ganin Haisam yasa Tace "Haba Yaya me Haka" ta koma ta kwanta.
"Princess ya haka baki da Lectures ne ki tashi please Karki makarar da mu"
Ido a rufe ta amsa Masa "Sai 10 kaje kawai sai anjima zan Shigo"
'daga kafad'a yayi ba tare da yace Mata komai ba, Yana fita yaga mummy na shigowa ciki yace "Har ya tafi?"
"Eh "
"Allah ya tsare, sai na dawo" ta amsa da "a dawo Lafiya"
Ya shige motar sa ya fice daga gidan ya wuce school.
Ma'isha sai karfe 9 ta tashi ta shiga ban d'aki ta shirya, a gurguje ta karya tayi wa Mummy sai ta dawo ta fice itama da motar ta Shiga school yau, Bayan sunyi Lectures karfe 1 suka Samu break ta nufi Masallaci domin ta gabatar da sallar azahar Kan su koma , Bayan sun idar suka koma class karfe biyu sai karfe 3:30 suka gama Lectures d'in wurin motar ta, ta nufa, tun daga nesa ta hango Haisam da Aysha suna Hira suna dariya alamu ya nuna Duk su biyun suna cikin farin ciki, ki tayi jira na d'aban ta da sauri ta nufi motarta ta bud'e ta Shiga, kwantar da kanta tayi steering motar ta dad'e a haka tana ambaton La'ila ha ila anta subhanaka inni kuntu Minal zalimin take har Saida taji d'an dama dama ta jaa motar ta fice daga cikin makarantar ranta ba dad'i.
Bayan ta Isa gida, ganin mummy da Umma a garden tasa ta d'an ji dad'i alamun babu wacce ta rike kowa a Rai, Bayan ta gaida su ta shige d'akin ta ruwa ta watsa kana ta gabatar da sallar la'asar ta kwanta tana tunani kala da iri har karfe biyar da rabi kana Meerah ta Shigo cikin gidan Bayan ta gaida su Mummy ta shige d'akin Isha.
Tana Shiga d'akin ta Ciro BO apparatus d'in ta ta hau gwada ta cikin Murya kamar fad'a Tace "Haba Isha Haba Isha 220 Isha, jinin ki ya hau har 220 ina mamakin ma yadda akayi har kike tafiya, Anya kinsha maganin da na ce Kisha"
Turo baki tayi ta ce "Nasha Mana"
"Wallahi baki Sha ba da kinsha da ba Haka ba, kin San Allah Idan baki cire shi a ranki ba Wallahi tallahi zan fad'a Masa"
" Karki min haka Dan Allah"
"Isha Ni Banga dalilin 'boye Masa ba, gara ya sani ya San halin da kike ciki a dalilin sa, jinin ki Kara Hawa yake wallahi zuciyar ki zata iya bugawa"
"Insha Allah baza ta buga ba, ki tayani addu'a d'azu ma na gansu sai kin gansu gwanin sha'awa"
"oooh no wonder yanzu nasan inda matsalar take ganin su da kikayi ne yasa hankalin ki ya Kuma tashi ko? Isha soyayyar da kike Masa na gaskiyane baza ki iya cire shi a ranki cikin sauki ba"
Haisam ne ya turo kofar Yana kallon su, wani yawu Mai zafine ya wuce ta makoshin Isha murya na rawa tace "Ya... Yaya ka dawo?"
_________________________
Please comment and Share
Milhaat ce
Yar Terawa
🍃*DANGIN UBANA*🍃
Story & Written
By
Milhaart
Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne.
*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________
*Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.*
Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
Page
35&36
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._
_Continuation.........._ Kofar d'akin ya tura ya nemi gu ya zauna kana yace "Eh na dawo maganar me kuke tattaunawa?"
"Uhmnn ba komai fa"
Kallon ta yayi kana yace "Oooh really ba komai? Naji Ana maganar Isha na son wani wane ne wannan lucky guy d'in?"
Daram daram kirjin ta ya buga, Meerah Tace "Ya Haisam dama........" Ma'isha katse ta tayi da fad'in "Yaya ya school d'in d'azu na ganka da Aunty na Kuna ta soyewar ku a love garden"
"oh ashe dama dagaske ked'in ce , Dama habibty Tace min ta ganki Amma na karyata ta, har ina fad'in inda kece zaki min magana, Ashe yaudaran kaina nayi" idon sa ya Kai kan gado ya hango BP apparatus kallon abun yake da mamaki.
Murmushi tayi Tace "Ba Haka bane dama........ " Katse ta yayi da fad'in "Princess ya naga BP apparatus baki da lafiyane?" Ganin baza ta amsa ba yamaida kallon sa ga Meerah da take aikin kallon sa yace "Likita me ya sami princess d'in?"
"Yaya jinin ta ne ya d'an hau Amma insha Allah zai sauka na bata magani ta Sha"
"jinin ta ya hau how comes?"
" Ga ta Nan ask her"
Murmushi tayi ta Fara inda inda yace "Tell me princess me ke damin ki? Na lura a Yan kwanakin Nan Akwai abinda ke damin ki Amma kina 'boyewa mene ne?"
"Ummm Yaya kasan Exam ya sako kai to yawan tunanin exam ne da rashin samun hutu yasa"
"Oh Hakane please ki rika samun hutu sosai, kar ki wahala karatun Kuma exam yazo ki kasa Exam , Kinga anyi ba'a yi ba Kenan"
"Hakane Insha Allah zan kiyayye"
Mikewa ya musu sallama ya fice. Sai da Meerah tayi sallar Isha , Ma'isha ta maida ta har gida da kanta.
Haisam
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 24