in tunanin abinda kuke Shirin aikatawa nee, Kar ki manta Haisam d'an uwan kine mahaifiyar sa Kuma kamar uwa take a gare ki, kamata ai idan Kika ga wani zai cutar dasu ki Kare su Amma ke da kanki?"
Dafe kanta tayi Tace "Ya Rasullullah, Mamy wai wa yace miki cutar dasu zamuyi after all haryanzu ban shirya abinda nake sonyi ba, amma wallahi sai ya d'an d'ana kud'ar sa na wulakanta min mahaifi da yayi" tana Kai Nan ta d'auki ledar ta da ta Shigo dashi ta fice daga d'akin.
Mamy Tace "Allah kana gani nayie iya bakin kokari na wajen ganar dasu Kuma sunki saurarata Allah ga bawan ka Nan Haisam bawan Allah da mahaifiyar sa ka kare su daga sharrin su, sannan ka Kare Musulmi a duk inda yake, ya Allah ka Shiga tsakanin mugu da na gari" Ni ko na amsa da ameen.
Da guda na koma gidan su Haisam don ganin Wace wainar ake Toyawa.
Bayan Umma da Ma'isha sun gama girki suka zauna zaman ci, Umma da kanta taje ta Masa magana Akan yazo suci abinci yace Mata ya koshi, ta dawo abinta Ma'isha kuwa duk yanda take son Tuwo ta kasa ci , gashi Nan tuwon shinkafa sukayi da Miyar alaiyahu yaji gyad'a sai zuba kamshi yake. Har karfe 9 Haisam yaki fitowa hakan yasa tayi wa Umma sai da safe ta koma part d'insu.
Mummy da Daddy ta tarar a parlor ta musu sannu ta Shige d'akin ta Bata zauna sukayi Hira ba kamar yadda suka saba, gyara Zama daddy yayi yace "Hajiya baki lura ba kamar yarinyar Nan akwai abinda ke damin ta"
"Na lura da hakan ya wuce ita da Yayan nata?"
"hmm Haisam da Ma'isha Kenan wannan karon Kuma me ya Faru"
Nan mummy ta Sanar dashi abinda tayi, tsaki yayi yace "Ni kaina ta 'bata min Rai banji dad'i ba bare shi da akayi wa, ko da yake zasu shirya kansu"
Mummy Tace "Sanin hakan ne yasa ban Shiga cikin maganar tasu ba, sun fi kusa" Nan suka cigaba da kallon su suna Hira, daga bisani suka kashe TV suka koma d'akin su.
"Allah kawata kice kin kuntata mata yau?"
"Trust me mana, nice fa Kuma kin San me abun burgewar?"
"A a sai kin fad'a"
"A lokacin da na kashe wayar naga kiranta ya fara shigowa na kashe , bayan Nan kusan thirty minutes sai na hango ta tsaya tana kallon mu sai ta juya ta tafi"
Wata irin shu'umin dariya Mardiya Tace "That's my girl idan kina haka Zaki Shiga tsakanin su a saukake ba tare da sun gane ba"
"Hmm ke dai bari zan so da Kinga fuskar ta d'azu Amma Anya Qawata yarinyar Nan ba son shi take ba kuwa?"
"Haba ke kuwa ya za'ayi ta so shi bayan d'an uwan tane?"
"Ina ta tunanin hakan Amma zan Kara tambayar sa nayi don ina tunanin na uwa d'aya uba d'aya suke ba, babu yanda za'ayi suna uwa d'aya uba d'aya su shaku har haka"
"Da wannan ma to ki kirashi Mana tunda kuka rabu kunyi waya kuwa?"
"A a 'bata min Rai yayi Kinga wani saurin da yake ya barni a gun kamar wata wawayi yasa aka tsaya kallona"
"Fushi fa ba naki bane ki kirashi kawai, don na tabbata tana fushi dashi Kinga kin samu damar waya dashi ko ba komai zaiji dad'i"
"Wannan hakane, bari na kirashi"
Sai da safe sukayi wa junan su, Aysha wanka ta Shiga abinta Akan in ta fito tazo kwanciya sai ta kirashi.
Haisam har karfe goma ya kasa bacci sai juyi yake , Yana ta jiran Kiran Ma'isha Amma Bata kirasa ba a bayyane yace "wato ma baza ta iya Kirana ba ta bani hakuri bayan tasan tamin laifi"
Yar karamar tsaki yayi ya d'auki wayar sa ya Shiga kiran Aysha, fitowar ta Kenan daga wanka jikinta sanye yake da bath robe, Murmushi tayi Tace "Alhamdulillah"
Picking tayi cikin sanyin Murya ta Masa sallama ajiyar zuciya yayi ya amsa kana ya Shiga Bata hakuri Akan tafiyar da yayi ba tare da yayi Mata sallama ba, ta nuna Masa ba damuwa.
Nan tayi ta jaan shi da Hira har ya manta da Yana cikin 'bacin rai, suna cikin wayar ne yaji shigowar wani Kiran dubawa yayi Yana ganin sunan *Princess* yayi Yar karamar tsaki.
Aysha Tace "Lafiya kuwa ya da tsaki?"
Yace "Wani ne yake ta damina da call"
"To ka d'aga Mana"
"Kar ki da mu it's not important, Uhmn kina bani labari"
Yar karamar dariya tayi Tace "Yauwa bayan na gama......" Nan ta cigaba da bashi labarin shimen ta shi Kuma ya biye mata, har wayar ya Kai awa d'aya yanke ya Kuma kiranta suka cigaba da hirar su, Ma'isha Kuma ta Kira yafi sau ashrin idan taji yana waya sai ta katse, har karfe Sha biyu na dare suke waya jin ta Fara hamma ya mata sai da safe ya katse wayar missed call 57 na Ma'isha ya gani da message guda d'aya
_"Yaya Dan Allah kayi hakuri, na yi ta jiran ka baka Zo ba Kuma wayar ka akashe bayan naje neman ka Kuma naga Kuna Tutorial da Aysha shiysa na dawo gida don kar na katse ku am sorry please"_
Bayan ya gama karantawa tsaki yayi ya ma kashe wayar Baki d'aya ya yi baccin sa, Ma'isha ta sake Kira taji switch off kukane Mai karfi ya kwace mata tana fad'in "Shikenan Shikenan dama na San Yaya ba so na yake ba ni kad'ai ce nake hauka na, insha Allah daga yanzu na cirewa kaina soyayyar ka"
Kasa bacci tayi yanda taga rana haka taga dare, idan tayi kukan ta gajie sai tayi shiru tana tuna abinda ya mata Kuma sai ta fashe da kuka a Haka har gari ya Waye, tana Jin an Kira sallar asuba ta Mike tayi wanka sannan tayi alwala, bayan ta idar da sallah ta nufi kitchen breakfast ta d'aura bayan ta Gama ta dawo d'akin ta ta Fara Shirin school.
Bayan ta gama ta d'auki Jakarta ta fice daga d'akin, dinning ta nufa ta tarar da su Mummy da Daddy na karyawa cikin girmamawa ta gaishe su suka amsa.
Ta sa wa kanta abincin ta hau ci bayan ta gama ci ta musu sai ta dawo, tayi ficewar ta Mummy da Daddy kallon junan su sukayi yace "Haryanzu fa Basu shirya ba"
Mummy Tace "zasu shirya don na tabbata yana waje yana jiranta"
Haka kuwa akayi tana fita ta hangosa a mota Yana jiran ta, Kuma waya yake hankalinsa kwance da kamar baza ta Shiga ba sai Kuma ta fasa ta bud'e gaban motar ta Shiga Kallo d'aya ya Mata ya cigaba da wayar sa.
Ya d'auki tsawon minti uku Yana waya kamun Nan yace "karfe nawa Zaki Shigo?" Daga d'ayan 'bangaren ta ce "Karfe 4,kaifa?"
"Ni bani ma da Lectures yau"
Cikin wani irin murya Tace "Yau bazan ganka ba Kenan?"
" Me zai hana idan kina son gani na zaki ganni, Kuma kinsan Dole na Kai princess makaranta"
"Albarkacin ta zanci Kenan"
"Umm umm ko don ke zan Shigo ai idan kin bukaci hakan"
Murmushi tayi Tace "Nagode Amma yallab'ai uwa d'aya uba d'aya kuke da ita ko naga Kuna Kama?"
"A a Yar Baffana ne"
"oh Masha Allah ka gaida min ita sai na Shigo d'in"
" Okay bye"
Ma'isha tana Jin su kamar zuciyar ta zata fashe Amma tayi kokoran saita kanta, ganin ya tada motar Tace "Ina kwana?"
Ya amsa da "lafiya" kawai yace mata a takaice, yasa wa motar key suka wuce makaranta.
_______________________
Please comment and share
Milhat ce
Yar tarewa
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._
🍃*DANGIN UBANA*🍃
Story & Written
By
Milhaart
Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne.
*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________
*Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.*
Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
Page
27&28
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._
_Continuation.............._ Ma'isha ganin har sun Isa bai kulata ba cikin Murya kamar zatayi kuka Tace "Yaya yanzu Dan Allah baza ka kulani ba? Duk hakurin da nake baka baza kayi hakuri ba tsakani da Allah, bayan Kuma Kai ne kamin laifi"
Kallon kin Raina min hankali ya Mata sannan yace "Ni ne ma nayi Miki laifi?"
"Eh Kaine"
A dai dai suka Shiga School d'in sai da yayi parking kana yace "Uhmn ina jinki laifin me na miki?"
"Kasan time d'in da zan gama Lectures sannan ka kashe wayar ka bayan Nan Kuma kaje ka zauna da yarinyar Nan kana hiran ka hankali kwance ka ma manta dani" ta karasa maganar tana matsar kwalla.
Murza goshinsa yayi ya ce "Amma meyasa baki min magana ba?"
Bud'e kofar motan tayi Tace "Haka kawai" ta rufe kofar motan da d'an karfi yayi Kara har Saida yayi saurin rufe idon sa, hatta mutanen da ke tafiya da Wanda ke zaune suka kalli inda suka jie karar wasu suna magana kus kus.
Haisam kuwa fita yayi daga makarantar Sai da ya daidai ci lokacin da Aysha zata Shigo ya dawo,Bayan sun had'u suka Shiga hirar su har ta manta da wani abu Wai shi Lectures, ganin karfe 6 ya kusa yace ta tashi ta wuce gida maghrib ya kunno Kai, ba musu tayi yanda yace.
Har wurin motar ta ya raka ta sai da ta Shiga ta tada motar ya bar gun ya d'aga mata hannu ya nufi gun motar sa, daga nesa Ma'isha ta hango su girgiza kai tayi a tare suka nufi wurin motar, zagayo wa yayi ya bud'e mata ta Shiga ta zauna sannan ya rufe, kana yanzagaya Shima ya Shiga ya tada motar suka wuce gida.
*AFTER 1 WEEK*
Wata shakuwace mai karfi ta Shiga tsakanin Aysha da Haisam, yayin da tsakanin shi Ma'isha ina kwana ina wuni ne kawai.
Wata ranar lahadi, ta shirya ta Sanar da Mummy zata gidan su Ameerah Mummy ta mata fatan a dawo lafiya sannan ta jaddada mata kar ta dad'e, Haisam ta hango a garden d'in gidan kanta ta kawar kamar bata gansa ba, gun Driver ta nufa ta umurce shi da ya d'auko mota ya Kai unguwa, cikin sauri ya d'auko yayie parking ita kuwa ta Shiga gidan baya.
Haisam kallon ikon Allah yake a bayyane yace "Wato yarinyar Nan ta ganni Amma tayi kamar bata ganni ba, Kuma ma ina zata je da Rana tsaka haka?" Ganin ba samun amsa zaiyi ba ya zaro waya ya kirata.
Tana ganin call d'in tsaki tayi ta kashe wayar ma gaba ki d'aya, Haisam bin wayar sa yayi da kallon ganin ta danna Masa Line busy,ciza leb'en sa yayi,ya Shiga cikin d'akin sa ya d'auko key d'in motar sa ba fice daga gidan,basu d'au lokaci Mai tsawo ba suka Isa, sai da ta fita ta waigo ta kalli driver Tace "Baba kabiru kar ka manta karfe biyar Zako d'aukana"
A d'an rutsune yace "Inshallah rankashidad'e, karfe hud'u da rabi anan zata same ni"
Murmushi tayi Tace "To sai anjima"
Ta shige ciki.
Ma'isha ne zaune a Kan gadon Ameerah suna kallon juna, tana kwararo Mata bayani, sai da ta gama bata labarin duk abinda le faruwa tsakanin ta da Haisam kana ta fashe da kuka mai cin Rai.
Ameerah taji tausayin kawar tata sosai, ta Shiga rarrashin ta har sai da tayi kuka mai isan ta don kanta tayi shiru.
Ajiyar zuciya Ameerah tayi Mai d'an sauti tace "Isha gaskiya Yayan ki bai kyauta ba tun ba yau ba nake fad'a miki kin nunae damuwa sosai akan shi na miji ba a mishi haka, in fact ma d'an Adam haka yake idan ka nuna masa ka damu dashi sosai sai ya d'auka duk duniya baza ka tab'a samun irin sa ba ko Kuma baza ka iya Rayuwa babu shi ba, Ni shawarar da zan baki shine ki cire Shi a ranki alamu sun nuna Yana son So Called Aysha d'in Nan, Don iya abinda Kika fad'a min Haisam a matsayin kanwa ya d'auke ba masoyayi ba"
Murmushin takaici Ma'isha tayi Tace "Nayi kokarin fahimtar hakan Ameerah Amma na kasa ke Kanki kin sani tun muna makaranta nake crushing d'insa, in fact tun muna primary, Har Saida muka Isa SS 3 da ya bani amsar tambayar da ake kana na Samu damar Shiga rayuwar sa, yanzu Kuma kice na rabu dashi?"
"To Isha fad'a min me zakiyi idan baki hakura ba? Cutar dake zaiyi Isha, na damu da lafiyar ki"
"Gaskiya Ki kawo wata shawarar banda wannan rabuwa da Haisam tamkar rabuwa da numfashi nane"
"Hmm isha Kenan" mikewa Ameerah tayi ta nufi Yar karamar fridge d'in dake d'akin ra d'auko ruwa Mai sanyi da Hollandia, had'e da glass cup ta dawo ta zauna Tace "wanne zan sa Miiki?"
"Hollandia" kawai a takaice zuba mata tayi ta cika cup d'in kamar zai zuba ta Mika Mata, Ma'isha tasa hannu ta karb'a, bismillah tayi ta kafa a bakin ta bata sauke ba har sai da ta shanye Tass.
Ameerah Tace "Should I add more?" Cike da kulawa
Girgiza Kai Ma'isha tayi had'e da fad'in "No Thanks"
Tissue ta zaro a jakar ta, tagoge bakin ta.
Ameerah Tace "As I was saying isha, rabuwa da Haisam is the best solution, cos Haisam baya son ki ya kamata ki gane hakan"
Kallon ta Ma'isha tayi sai Kuma ta sunkuyar da kanta kasa.
Dafe kafad'ar tayi Tace "Isha!!"
'dago kai tayi a hankali ta na kallon ta, Tace "I know how you feel son Wanda baya sonka babbar matsala ce but you can't force him to love you"
Cikin Murya kuka Tace "Kin fad'i gaskiya, Dole na rarrashi zuciya ta" sai Kuma tayi Murmushi bayan hannun ta tasa ta share hawayen dage gangaro wa a fuskar ta d'aya nabin d'aya kana ta d'aura da fad'in "Insha Allah zan cire Ya Haisam a raina please ki taya ni da addu'a"
"Insha Allah dear"
Ma'isha Tace "Kwana biyu ba mu had'u ba ba wani gulma ne?"
"Hahaha Allah ya shirye ki Isha kina cikin damuwar ma baza ki Canza Hali ba?"
"Ahhh ya zanyi to? Kefa Kika ce min na cire shi a raina to it starts from now"
Dariyar ta Kuma yi Tace "Akwai su dayawa har sai kin gaji da fatan wuni zakiyi?"
"Eh sai 5 zan koma"
"Kai Amma naji dad'i wallahi"
Murmushi kawai Ma'isha tayi bata ce komai ba.
Ameerah Tace "Yauwa mutumin ki kullum sai ya tambayeni ke"
Cike da rashin fahimta Tace "Wa Kenan?"
"Ma'aruf Mana"
"Mtswww wai dama yana Nan? Ni wallahi na ma manta da wani ma'aruf"
"Hmm to na tuna miki, please give him a chance"
" I can't dallah,Ni yunwa nake ji ma me Akwai?"
Girgiza kai Ameerah tayi ta fahimce ta so take ta kawar da maganar sabida tun shigowar ta Tace zata kawo mata abinci tace a koshe take, riko hannun Ma'isha Ameerah tayi had'e da fad'in "Zo muje kitchen mu duba me suka girka don dama Nima tun breakfast ban ci komai ba"
Nan suka nufi hanyar kitchen, a hanyar su ta Shiga kitchen suka ci karo da mahaifiyar Ameerah har cikin girmawa wa ta gaida ta ,ta amsa ba yabo ba fallasa, suka shige cikin kitchen.
Haisam kuwa Yana fita gidan su Farukh ya nufa, a d'akin Farukh na hango sa yana zaune hannu a goshin sa yana murzawa Wanda hakan ya zame Masa jiki da zaran ransa a 'bace yasa hannu yayi ta murza goshinsa a Haka har ya huce.
Farukh yace "Look nifa banga laifin yarinyar Nan ba, Bayan Kaine ka mata ba dai dai ba Kuma ta baka hakuri sannan ka nuna Mata Kai d'an iskane"
Gyara zaman sa yayi kana yace "Jiman ya za'ayi na fad'a maka matsala ta Kuma na tsaya kana goyon Bayan ta?"
"Ba goyon Bayan ta nake ba,Ina dai fad'a maka gaskiya ne, yarinyar Nan fa son ka take Amma ka kasa gane hakan"
A zabure ya Mike yace "so bangane tana Sona ba"
Shima farukh mikewa yayi ya ce "Eh Mana baka lura da hakan ba,kishine yake cin Ma'isha"
Yar karamar dariya yayi yace "No No it can't be ba so na take ba nifa Yayan tane" ya koma ya zauna.
"Eh kai Cousin Brother d'inta ne like you told me and Akwai aure a tsakanin ku,Kuma kaima kana sonta baka gane hakan bane haryanzu"
"Yes she is my cousin but,bazan tab'a son Ma'isha ba, a matsayin Kanwata na d'auke ta wallahi Bayan hakan babu komai a raina,And wani abunda baka sani ba,ina ji na Fara son Aysha"
Zama farukh yayi yace "nasan za'a Zo Nan, Amma Ni Kam am not in support gaskiya Wai Aysha mtsww"
"Me Ayshar tayi bata had'u bane? Ko tana da wani mugun Hali Wanda Ni ban sani ba?"
" NO NO ko kad'an kyakkyawa ce Kuma na lura kanta na d'an rawa ba kamar Ma'isha ba,Gata kyakkyawa,ga sanin ya kamata sannan Bata da rawan Kai"
"Nifa Kuma a hakan nake son kayana,idan Kuma kana son Ma'isha ne zan maka jagorawa har wurin daddy"
"Ai da kuwa na Rika sa maka Albarka har karshen rayuwata in dai na mallaki Ma'isha a dalilin ka,Amma bazan iya son maso wani ba so count me out"
"Shirme kayi rawa kayi kid'a duk Kai kad'ai" mikewa yayi yace "Tashi muje Masallaci daga chan zan wuce gun habibaty"
Dariya Farukh yayi yace "Wata sabuwa inji yan cha-cha wai har an Canza ma Aysha suna?"
"sa wasa" yayi maganar yana shafa kirjin sa,Yana jin kansa a sama.
Tab'e baki Farukh yayi yace "Nawa Ido Allah sa kar kazo daga baya kana da na sani,Ni dai bata min"
" Ni Kuma tamin" Yana kai Nan yayi hanyar fita har ya bud'e kofar ya waigo yace "gwamma ka fara sonta sabida she is my wife to be idan ka gama Kallo na ka same Ni a waje." Yayi ficewar sa da d'an gudu Farukh yabi bayan sa.
Bayan sun idar da sallar la'asar ya Kira Aysha ya Sanar da ita yana hanyar gidan su, da kwatancen ta ya kai kansa gidan su, abinka da unguwar manya bai Sha wahala ba ya Isa kofar gidan su a GRA.
Har cikin gidan ya Shiga yayi parking motar sa,kujera tasa a ka fito musu dashi suka zauna ta sa aka jera Masa kayan shashaye da fruits ruwa kawai yasha Nan ya fara kwararo mata da abinda ke zuciyar sa, Aysha ba 'bata lokaci ta karb'i bukatar sa,Hira suka Sha sosai sai har Saida ya ji an fara Kiran sallar maghrib ya Mike ya yi Mata sallama,har wurin motar sa ta raka shi Yana fita ta koma cikin gida zuciyar ta fal farin ciki.
Ma'isha hira suka Sha sosai karfe 5 saiga mallam kabiru ji sukayi kamar kar su rabu, har jikin mota ta raka ta, da tabbacin Sunday Mai zuwa Ameerah zata Zo gidan su, Nan ya tada motar suka wuce gida.
Isowarsu yayi dai dai da Shigowar Haisam gidan, Zama yayi a motar Yana kallon ta, ta ganshi Sarai su Amma tayi kamar bata gansa ba ta shige cikin gida, kitchen ta Shiga ta tarar da Mummy da masu aiki suna girki tana supervising ta baya ta rungumeta had'e da fad'in "Mummy na, na dawo"
Mummy dariya tayi Tace "Daughter so kike ki karyani ko?"
Sake ta tayi had'e da fad'in "A'a mummy na Isa, idan na karyaki ina zan sa kaina?"
"Ina fa zaki zauna da Umman ki da Yaya ki da Daddyn ki"
Rufe Mata baki tayi da hannun ta Tace "Yi shiru mummy bana son kina fad'in hakan"
"Nima zolayar ki nake Ma'isha"
"Yauwa, Mummy naga kuna ta aiki daddy zai dawo ne?"
"Eh Kuma zaiyi baki shiyasa"
"Gaskiya daddy Kwanan nan baya Zama baya yin sati a gida fa"
"Aikin Kenan sai dai mu bishi da addu'a"
"Allah ya taimaka Masa, ya dafa Masa"
"Ameen daughter je ki Samu kiyi sallah ki Zo ki tayani"
Ta amsa da to ta nufi d'akin ta Tora kofar tayi a hankali, wurin ajiye takalmi ta nufa ta cire takalmin ta sannan ta rataya jakar ta juyowan da zatayi ta hango mutum a kwance a Kan gadon ta, dafe kirji tayi tana ambatan "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un"
_______________________
Please comment and share
Na kusa na Fara removing marasa comment, and please idan na cire ki kar kiji haushina
Milhaat ce
Yar Terawa
🍃*DANGIN UBANA*🍃
Story & Written
By
Milhaart
Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne.
*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________
*Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.*
Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
Page
29&30
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._
_Continuation.........._ Hannun ta ta sauke daga kirjin ta, ta sauke ajiyar zuciya Tace "Kai Yaya ka tsoratani yaushe ka Shigo?"
Tashi yayi ya zauna daga kwanciyar da yake yana kallon cikin idonta tabbas ta tsoro ta, yace Mata "Yanzu na Shigo, Ashe dama kin ganni?"
Kawar da kanta tayi kamar bata ji abinda yace ta hard'e hannun ta, ba ganin bata da niyar bashi amsa ya taso ya nufe ta, dab da ita ya tsaya ganin har yanzu bata kula shi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 24