Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
idan Kika min hakan na yafe Miki duniya da lahira." "Inshallah zan maka ko ma mene ne Daddy don samun albarkar ka" "Malam kar ka saka yarinyar Nan acikin matsalar ka ka fama Kai kad'ai" "a'a mummy mahaifina ne fa, matsalar da ai tawa ce, so kar ki damu" Murmushi daddy yayi yace "Good My Girl wuce muje kafun tayi poisoning mind d'inki" Ficewa sukayi a d'akin a tare suka bar ta ita kad'ai, Mamy ta rasa abinda yake mata dad'i, ajiyar zuciya tayi Tace "Ya Allah ka shirya min su ka ganar dasu gakiya." *BAYAN KWANA BIYU* Daddy na zaune a parlor shi da Haisam suna kallo suna Hira sama sama kasantuwar Yau lahadine yasa bai fita office ba, Mai gadi ya shigo bakinsa d'auke yake da sallama, suka amsa. Cikin girmamawa yace "Yallab'ai kayi baki" "Baki Kuma su wane ne Haka?" "Wai DPO ne da malam Hassan" "okay Ce musu su Shigo" " To yallab'ai" ya fice. Daddy yace "Son wai ina mutanen gidan Nan suke ne?" "Suna part din Umma" "Okay je ka Kira min su duka" Mikewa yayi tare da fad'in "to daddy." Tun daga bakin kofar parlor yake jiwo muryar su suna Hira suna dariya , da sallama ya shigo shima Yana daruyay duk da bai San dariyar me suke ba, yace "Nima nazo ne ayi hiran Dani" Umma tace "A'a you're not welcome here, yau ranar ta Mata ne" Yar karamar dariya yayi yace "Nikam dama nasan ba'a yina a gidan Nan Ma'isha kawai ake so" Ma'isha Tace "Ji Yaya fa dan Allah ni Kuma me ye nawa acikin maganar ku?" " Oh ma baki sani ba?" "Eh ban sani ba" "To ki taso Mana kawai ki shake min wuya na fad'a maki" Taso wa tayi ta nufe shi tana dariya yace "Ki karaso Nan kiga abinda zan Miki" Mummy Tace "Yaran Nan Basu da kunyan wallahi,Amma alhaji duk baya gani" Haisam yace "Laaa Kinga na Manta wallahi daddy ne ma ya aikoni wai nazo na Kira ku" Umma Tace " Kuma ka tsaya shirme ba" Mummy Tace "Lafiya dai ko? Nifa bana son irin Kiran Nan" Murmushin yayi Wanda ya kara bayyana kyawun fuskarsa yace "Lafiya Lau, Baffan hassane suka Zo" Dukkanin su Saida suka ji gaban su ya fad'i kallon juna Mummy da Umma sukayi a tare suka Mike suka fice a tare suka shiga dasu Malam Hassan. Mummy gefen daddy ta zauna yayin da Umma, Haisam da Ma'isha suka zauna a Kan three sitter dake d'akin DPO da Malam Hassan suka zauna a one one sitter dake kusa da su Daddy. Daddy yace "DPO shine kazo da kan ka? Ai da ka kirani zuwa office d'in" " A a y'allabai kasan an rufe case d'in Kuma naga maganar yanzu na gidane ba sai a office zamuyi shi ba" "Wannan ma hakane" Mikewa DPO yayi ya Mika wa daddy wasu files, karb'a daddy yayi ya shiga dubawa, bayan ya Gama dubawa yace "Ka tabbata ka had'a komai da komai?" Murya na rawa yace "Eh Alhaji" Daddy yace "Son Zo ka karb'a, har ya sa hannu zai karb'a yace "Daddy da dai ka bar su a wurin ka tukanna, Ni ban San me zanyi dasu ba a yanzu gaskiya" Yar karamar dariya daddy yayi yace "Son Kenan dukiyar kace fa, ba nawa ba" "Eh na sani daddy shiysa nace ka rike su tukunna" "A a son ba za a yi Hakaba" Umma Tace "Alhaji haryanzu Haisam yaro ne ka rike d'in kamar yadda ya bukata" " Toh Shikenan" Sai ya ajiye su a Kan side table dage gefen kujerar da suke zaune. Ya maida kallon da ga DPO yace "Nagode sosai dpo Allah ya saka da alhairi" "a a Alhaji bakomai aikina kawai nake yi" ya maida kallon sa ga Malam Hassan yace "Mu tafi ko?" Yace "Umm umm Dan Allah Alhaji alfarma nake nema a wurin ka" "Babu wata alfarma da zan maka ka tashi ka fice min daga gida" Mummy ce ta dafe shi a fad'a alamun plz ka saurare shi Sai Kuma yace "Fad'i ina jinka" "Alhaji Dan Allah so nake a taimaka min da muhalli ko da gidan da muke cikine naci Albarkacin yayana Dan Allah, bani da inda zan zauna da iyalai na" Kallon kallo a ka Fara yi a d'akin Haisam Kuma Murmushi kawai yayi. Daddy yace "Hakan ba Mai yiwuwa bane ko da yake bani da iko da dukiyar nan, dukiyar Nan ta Haisam ce shi zaka roka ya maka wannan alfaramar bani ba" Malam hassan har kasa ya durkusa a gaban Haisam yace "Haisam Dan Allah ka taimaka min , nasan ban chanchanchi yafiyar ka ba amma dan Allah find a place in your heart and forgive me" Haisam kallon Umma yayi da tun dazu take ta aikin kallon sa, Murmushi tayi shima ya maida Mata. ___________________ Please kuyi min sharhi, shi kad'ai zai bani karfin gwiwar typing. Sannan Kumin sharing Milhaat ce Yar Terawa 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 15 and 16 Kallon Baffan sa yayi yace "Dan Allah ka tashi baffa meyasa zaka durkuwa a gabana bayan kana matsayin ubane a gare ni, Ni na yafe maka duniya da lahira, maganar gida Kuma na bar maka shi halak malak hatta company d'in da kake aiki a Cikin na mallaka maka" Malam hassan kirkirerren kuka ya Fara yi yana fad'in "Nagode, Nagode Haisam Allah ya maka Albarka" ya maida kallon sa ga Umma yace "Zainabu kiyi hakuri ki yafe min Dan Allah" "Bakomai na yafe maka, Allah ya yafe Mana baki d'aya." Duk suka amsa da amiin, Malam Hassan Banda godiya babu Abinda yake har suka fice daga gidan, Nan su Daddy suka shiga hirar su suna farin cikin nasarar da suka samu. Tana ganin shigowar sa ta mike tana fad'in "Daddy ya dai? Da fatan anyi nasara" Murmushin irin zasu gane kuren su yayi yace "Yar daddy ai daddyn nakin ba daga nan, plan d'inmu zai Fara ne daga yau, na gama nawa saura naki" Murmushi tayi Tace "Insha Allah Daddy kasa ranka anyi an gama kawai" "Allah ya miki Albarka Yar Daddy" Ta amsa da "Ameen." Umma da Haisam hankalin su kwance ko bakomai sun karb'i hakkin su, Basu da sauran damuwa a rayuwar su, duk wanni abu da suke bukata na jin dad'in Rayuwa suna dashi. Wannan Kenan Haisam da Ma'isha shakuwace Mai karfi ta shiga tsakanin su tare suke zuwa makaranta su dawo tare, kullum Haisam ke Kai su school, ko da kuwa bai da lectures yakan kaita ta idan sun tashi ya koma ya d'auko ta wasu lokutan Kuma ya jira ta har sai ta gama su koma gida. Umma da Mummy komai tare suke hatta unguwa zasuje tare suke zuwa shopping, har kauyen su Mummy tare suke zuwa. Haisam ke zaune a Cafeteria yana cin abinci,Yana jiran Ma'isha ta Gama lectures,cin abincin sa yake hankalinsa kwance yayin da d'ayan hannun sa yake Kan wayar sa, wata budurwa da baza ta haura shekaru 20 ba ta nufi inda yake, da sallama ta karasa inda yake a hankali ya d'ago kansa had'e da amsa sallamar ta, kallon ta ya tsaya yi, Murmushi tayi Wanda hakan ya kara bayyana kyakkyawar fuskar ta Tace "Sannu dai" Dai dai ta nutsuwar sa yayi ya amsa da "yauwa sannu da" "Dan Allah idan baza ka damu ba zan iya Zama anan?" Tana nuna kujerar da ke fuskan ta nasa. Yace "Eh... Eh zauna Mana" Tace "Nagode, ta jaa kujerar kana ta zauna tana Murmushi, waige waige ta Fara yi kana ta hango wata ta d'aga Mata hannu had'e da fad'in "Waiter!!!" Cikin sauri ta karaso inda take Tace "Welcome ma what will I offer you?" Kallon Haisam budurwan Nan tayi da ya maida hankalin sa Kan wayarsa, Murmushi tayi Tace "Ki bani irin abincin da yake" Haisam d'an d'agowa yayi ya kalleta ya girgiza Kai had'e da Murmushi ya cigaba da cin abinci sa, ba a d'au lokaci ba ta dawo plate d'in chicken and chips, tasa hannu ta karb'a. Ganin Haisam bai kulata ba tayi gyaran murya Tace "Ni suna na Aysha kaifa?" Ba tare da ya d'ago ya kalleta ba yace "Haisam" Tace "Wow Nice name, kai a school d'in Nan kake ne?" "Eh" "Wani department?" "Medicine" "Nima a medicine nake Amma ban tab'a ganin ka ba, Amma aji nawa kake?" "200 level" "Oh shiyasa ni a 100 level nake" Yace "Maybe" Duk maganar Nan da suke bai d'ago ya kalleta ba. "Lalle gayen Nan akwai rainin hankali duk yanda nake so muyi Hira ya kasa sakin jikinsa , dama ance kyawawan mazan Nan haka suke da girman kai" duk maganar Nan a zuciyar ta take. Bata lura ba har ya Kira Waiter ya biya su kud'in su ya Mike zai tafi, karar kujeran da ta jaa Ne ya dawo da ita daga tunanin da ta lula da murya mai d'an karfi Tace "Ina Kuma zaka?" Kallon ta yayi cike da rashin fahimta yayi d'an Murmushi yace "Gida" ya juya zai tafi tayi saurin mikewa Tace "Dan Allah ko zaka iya bani number ka?" "Number ta Kuma?" "Eh number ka" " Da fatan dai ba laifi nayi bako?" Murmushi tayi Wanda hakan yasa Beauty point d'inta ya nuna tace "A a kawai so nake muyi wata magana da kai idan bazan takura maka ba" Yace "Okay" ya Mika hannun sa alamun ta Mika Masa wayar ta, cikin sauri ta Mika masa wayar Yana sawa ya Mika Mata ya fice daga gun, bata samu damar yi Masa Godiya ba, Yar karamar tsaki tayi Tace "Anya gayen Nan zai Soni kuwa?" Komawa tayi ta zauna ta Fara cin abincin ta, Haisam kuwa zuwa yayi ya tarar da Ma'isha na tsaye a jikin mota tana jiran sa, ta had'a raai, tun daga nesa ya fara dariya don yasan ta dad'e tana jiransa tun Kan Aysha tazo dama ta kirashi yace mata sai yaga cin abinci tazo ta same shi Kuma Taki. Yana karasawa yace "Yar karamar Kanwata har an fito?" Cikin Muryar Shagwab'a Tace "Ba a sani ba" "Haba Mangana me yayi zafi wai fushi kike dani?" "Nikam ka bud'e min na shiga so nake naje gida" Kai kawai ya girgiza da kansa ya bud'e mata motar ta shiga sai turo baki take ita a lallai an 'bata mata raai, Yana shiga ya tada mota suka nufi hanyar gida, sai surutu yake Yana bata Labari bata kulashi sai da Tace Umm ko hmmm har suka Isa gida, suna Isa ta fice ta shige gida ba ta Tsaya jiransa ba kamar yadda suka Saba ba, mummy na ganin ta Tace "Ke Kuma yau ko sallamar ma baza ki iya ba" Cikin sanyin murya tace " Sorry mummy na shafa'ane" wuri ta samu ta zauna tace "Mummy ina wuni" "Lafiya daughter ya school d'in dai?" "Lafiya Lau Mummy, ina Umma?" "Tana part d'inta, yanzu ma tashi a inda kike zaune zatayi wanka zamu je saloon wanke Kai" "Yauwa Mummy Nima zan biku" "Ahhh yau Kuma ba yayan naki bane zai kai ki?" "Eh zan biku" Haisam da sallama ya Shigo mummy ta amsa har kasa ya tsuguna ya gaida ta kana ya nemi wuri ya zauna yace "Ni zan kai ki, aiki nane wannan" Turo baki tayi Tace "Bana so zanbi su mummy" Yace "In ko hakane baza ki ba don bazan bari ki fita a gidan Nan ba" Mikewa tayi Tace "To an fasa wanke Kan" ta shige d'akin ta, Haisam yace " Kin ganta ko" Mummy tayi saurin fad'in "Ah ah ba ruwan nikam kun fi kusa in sa muku baki ku kunyata ni ba dani ba" ta Mike ta shige d'akin ta itama Haisam Yar karamar dariya yayi ya bi bayan Ma'isha ya tarar da ita tana kwance a Kan gado tana kallon saman d'akin. Turo kofar yayi a hankali tasan ba mai shigowa sai shi hakan yasa ta juya Masa baya, Murmushi yayiw ya zauna akan couch d'in dake d'akin ajiyar zuciya yace "Please princess kiyi hakuri duk da ban San laifin me nayi ba, don na tabbata fushin Nan da ni akeyi, Amma duk da hakan kiyi hakuri" Hmmm kawai Tace ba tare da ta juyo ba, tashi yayi ya zauna a Kan couch d'in dake fuskantar ta, Kama baki yayi yace "Laaa ila kuka Princess? Me yayi zafi har Haka Dan Allah ki fad'a min laifi me nayi haka?" A zuciyar ta Tace "Taya za'ayi na fad'a maka cewar ganin ka da nayi da watane ya sani kuka? Taya za'a yi na fad'a maka cewar bana son ganin wata mace ta rab'e ka? Taya za'a yi na fada maka ganin ka da wata da nayi cafeteria ne ya sani kuka?" Cikin wani irin salo ya ambaci sunanta "Ma'isha!!! A hankali ta d'ago kanta ta sauke su akan kyakkyawar fuskar sa kasa jure kallon da yake mata tayi ta Kuma rufe idanun ta. Yace "Ma'isha tell me please ko Nima so kike nayi kukan?" Girgiza Kai tayi had'e da fad'in "A'a" Yace "To tashi ki zauna" Ba musu ta tashi ta zauna yace "Princess ina jinki Dan Allah me ya same ki?" Shiru tayi sai kokarin 'boye hawayen da ke idon ta take Amma ta kasa, daga bisani ta fashe da kuka Mai sauti. Haisam har cikin ransa baya jin dad'in kukan ta, musamman ma ace shine silar kukan nata ajiyar zuciya yayi yace "Dan Allah Dan Annabi na roke ki fad'a min dalilin kukan naki , bana jin dad'in ganin ki a hakan karya min zuciya yake Dan Allah kiyi shiru" Bata ce mishi komai ba ta cigaba da rera kukan ta. Mikewa yayi yace "Shikenan tunda ban kai matsayin da Zaki fad'a min matsalar ki ba na kyale ki, sannan yanzu nasan matsayina a wurin ki" har yasa hannu zai bud'e kofar d'akin yaji saukar Muryar Tace "Yaya kayi hakuri" Murmushi yayi yasan hakan ne kad'ai zai sa ta kula shi, kin juyo wa yayi jin ta nufo shi ya had'a raai kamar bai tab'a dariya ba Tace "Yaya na" Joyowa yayi Yana kallon ta , kanta a kasa tana wasa da yatsunta yace "Uhmn ina jinki?" "Kayi hakuri Dan Allah" "Hakurin me Kuma? Ni baki min laifi ba, kawai dai yanzu nasan matsayina a wurin ki Ni ba komai bane a wurin ki" "Wallahi Yaya ba Haka bane ba , wallahi bayan mummy da daddy bani da Wanda ya fika a wurin Kuma Kai ma ka sani" "In da hakan ne kamar yanda kikace ai da zaki fad'a min matsalar ki, da Allah fa nake ta had'a ki tun a hanya Amma kin ki kulani Kuma a hakan Zaki wani cewa ina da matsayi a wurin ki? In dai da Gaske ki ke ki fad'a min abinda ya same ki" Turo baki tayi Tace "Ba Kai bane" "Bani bane me?" "Ai Kaine ka shanyani nayi ta jiran ka, ga Rana" Murmushi yayi ya jaa hancin ta yace "yanzu dama don wannan ne kike uban kukan nan?" Ka ta d'aga Masa alamun eh, yace "Ai Saida nace miki kizo Kika ki zuwa, abinci fa nake ci princess, Amma kiyi hakuri na Miki laifi" yasa hannun sa biyu ya rike kunnuwan sa, Murmushi kawai tayi yace "Kin hakura? Idan baki hakura ba bazan sake kune na ba" "na hakura" Ajiyar zuciya yayi yace "Kai na gaji" "Laa d'an rike kunnen ka da kayi da bai Kai minti d'aya ba har ka gaji?" " Eh Mana da wahala fa" Dariya tayi harda tafi Shima dariyar ya shiga yi yace "Zo mu je dining nasan princess d'in yayanta tana jin yunwa" Tace "kamar ka sani Yaya" Shima yace "Kamar ka sani Yaya" Yana kwaikwayon Muryar ta. Dariya sukayi a tare suka fita, shigan su parlor yayi dai dai da shigowar mummy parlor baki a bud'e take kallon su suna Hira suna dariya Mummy Tace "Ahaaaf ni da sani za'a Rina ai, mutum ya shiga tsakanin ku kunya zaiji" sosa keya yayi yace "Mummy in gaya miki da kyar da makerkyasa na rarrashe ta" "Uhmnn to maza je ki d'auko mayafin ki mu je saloon d'in" Cikin Muryar Shagwab'a Tace "A a mummy sai kun dawo Yaya zai kaini" Mummy Tace "Kinci gidan ku ja'ira kawai Ni Zaki jawa raai" tsaki tayi ta fice a hanyar ta tafita suka had'u da umma hakan yasa suka juya kawai hannu Ma'isha da Haisam suka d'aga musu suna a dawo lafiya. Mummy Tace "Yaran Nan sun maida mutane kamar kakannin su" Umma Tace "Bakamar Haisam bama sai a hankali" Mummy Tace "Kin samin son a gaba wallahi ke Sam bakya ganin laifin yarinyar Nan ko kad'an" "Hmm Hajiya Kenan ai ni gaskiya nake fad'a ke dai da son d'a ya rufe Miki Ido bakya gani" a haka suna Hira har suka Isa parking lot already dama driver yasan da fitan su yana hango su ya fito da motar a baya suka zauna, ya Danna wa motar key suka wuce saloon. Haisam da Ma'isha suna zaune a dinning tana cin abinci shi Kuma sai tad'i yake ta mata tana ci tana dariya har kamar zata kware,kwasam wayaey sa ta fara ringing hannu yasa a aljihun rigar sa ya zaro wayan ganin sabon number yasa bai d'auka ba, sai da aka sake Kira a karo na biyu yayi picking sallama yaji jin Muryar mace ya sa shi tunanin Wace ce wannan da zakin Muryar da bai tab'a jin irin ta ba, a ransa yake ayyana hakan, ta sake sallama a karo na biyu ya amsa bayan sun gaisa daga d'ayan 'bangaren Tace "Ka gane mai magana kuwa?" Yace "A'a " a takaice. Murmushi tayi Wanda Yana iya jinsa Tace "Nice na karb'i number ka d'azu a Cafeteria d'azu, ka tuna" Yace "Eh na tuna, ya kike? " Tace "Lafiya, idan baza ka damu ba Dan In na so muyi wata magana dakai idan baka komai?" " For now am busy gaskiya sai zuwa anjima when am less busy I'll call you" Tace "promise?" " Yeah Insha Allah" "Okay sai na jika" Kiit ya katse wayar, tunda ya fara wayan hankalin Ma'isha yake kansa Tace "Yaya who is that?" Yace "A friend" Tace "Okay" Yace "Yau ina Baki Labari........ " Nan suka cigaba da hirar su Saida ta cita koshi suka koma parlor suna kallon favorite series d'insu a zeeworld Mai sun I Do. ___________________________ Ina barar addu'ar ku fansa ina cikin wani yanayin da yake hanani komai hatta typing ma shiyasa kuka jini shiru. Please Comment Share Milhat ce Yar Terawa 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 17and 18 Haisam da Ma'isha kallo suke hankali kwance har Saida aka Fara kiraye kirayen sallar maghriba, mikewa yayi ya kashe TV turo baki tayi Tace "Yaya meyasa zaka kashe min Kallo na?" "Lokacin sallah yayi baki ji ana Kiran sallah ne?" "To ai Ni bana sal...... " Sai kuma tayi shiru ta kasa karasa maganar dariya yaso yi sai Kuma ya matse yace "karasa abinda zakice bakya me?" Mikewa tayi da sauri ta nufi d'akin ta tana dariya kasa kasa,dariya yayi ya kad'a Kai yasa Kai zai fita knn sai ga shigowar su Mummy, d'an Jaa da baya yayi ya basu wuri suka wuce Yana fad'in "Har kun dawo?" Umma Tace "harne? Bayan munfi 2hours" Yace "Naga kunyi sauri ne ai" Mummy Tace "Son ana Kiran sallah kana Nan kuna ta aikin surutu ko?" Murmushi yayi Yana Jin dad'in yanda mummy ke nuna kulawa a garesa tamkar ita ta haife shi yace "Yanzu Masallacin nayi" Tace "To a dawo lafiya" Ya amsa da "Ameen" Sai yayi ficewar sa. Ma'isha na shiga d'aki ta kwana abinta ta d'auki wayarta tana chatting da kawayen ta, Bata fito parlor ba har sai da ta ji shigowar Daddy, da gudu ta fito tana Masa sannu dazuwa. Daddy yace "Daughter baki san kin girma bako, ya kamata ki rage Shagwab'ar nan Haka" Haisam yace "Daddy ai saima abinda ya karu, Mijin ta zai Sha wahala sosai don na tabbata ko da bayan ta haihuwane Reno biyu zaiyi" A zuciyar Tace "Zaka Sha Reno dai, don kaine mijin nawa Insha Allah" a bayyane Kuma Tace "Uhmnn daddy kace Masa ya daina tsokana ta" har da bubbuga kafar ta kamar yarinya Yar shekara biyar daddy yace "Son ka daina tsokanar ta" Haisam dariya kawai yayi baice komai ba, mummy ce ta Shigo parlor taci kwalliya sai zuba kamshi take Tace "Daga dawowar sa kun sashi a gaba da shirmen ku babu Wanda yayi tunanin karb'ae jakar sa" Ma'isha saurin karb'an jakar hannun da tayi tace "Laa sorry daddy wallahi farin cikin ganin sa ne yasa na manta" Haisam yace "Hakane mummy 2 weeks fa dad baya Nan Dole muyi kewar sa" "Naji yanzu dai ku bari idan yaci abinci ya samu ya huta sai kuyi hirar taku" A tare sukace toh. Karb'an jakar hannun Ma'isha tayi, Ma'isha Tace "Mummy ki bari Mana na kai Masa d'akin sa" "Anki d'in mijinkine ko mijina?" Ma'isha hannu tasa ta rufe bakin ta Tace "mummy abin harda gorine Kuma?" Hararar ta mummy tayi ta bi bayan Daddy da tun d'azu ta wuce d'akin sa. Zama Ma'isha tayi a Kan couch d'in dake gefen na Haisam bakin sa ya kawo dai dai kunnen ta yace "kinji abinda mummy Tace ko dama maza ki Nemo miji in yi miki aure idan bakya son Gori" Dariya tayi Tace "Na baka huka da nama yaya ka Nemo min mijin aure na maka alkawarin ko wane ne ka kawo zan aure shi" "kamar dagaske, confidence d'inki dariya yake bani wallahi kina nufin ko Mai gadi na kawo miki zaki aura? " "Da gudu ma, ai Mai gadi mutum ne kamar kowa ko?" "Shikenan tunda kince haka Zaki Sha mamaki." Dariya kawai tayi suka cigaba da kallo. Umma ce ta Shigo parlor Tace "Kun samu sana'a ku Kam, a haka za'a samu likitocin?" Haisam yace "Ai gobe ba school ne Umma Sunday ne fa ranar hutun d'an boko" " Gafara Chan ka zauna kana kallon zeeworld kamar wata mace" "Wallahi umma ba laifina bane, laifin Yar kice itace ta koya min Kallo" "nasan abinda zakace Kenan ai" wuri ta Samu ta zauna suna kallon tare. Daddy ne da mummy suka fito baka Jin abinda suke cewa Sai dariyar su kawai, Haisam kasa kasa yace "Kin gani ko princess kiyi aure ki Rika samun farin ciki abunki" "sai na fadawa Daddy abinda kace yanzu" "a a yi hakuri nayi shiru" Dinning suka nufa, Umma, Ma'isha da Haisam Suma suka wuce dinning d'in Tuwon shinkafa da miyar kuka mummy tayi yaji daddawa da citta sai nama da kifi da suke ta shawagi a ciki, suna ci suna Hira har suka gama suna gamawa Haisam ya Mike yace "Yau bacci nake ji sosai zan kwanta" Ma'isha a take ta 'bata Rai Tace "Yaya but kace min zamuyi Kallo tare fa" "Am sorry Kanwata wallahi a gajiye nake akwai gobe wuni zamuyi muna Hira kinji?" Bata so hakan ba Dole ce tasa ta hakura yayiwa su mummy sai da safe ya wuce part d'insu Yana tafiya Ma'isha itama tashi ta shige d'akin ta. Haisam na shiga d'aki ya ban d'aki ya fad'a yayi wanka ya sanya vest da d'an gajeren wandon sa ya d'ale Kan gado ya bud'e datar sa ya Fara chatting, emoji da stickers na kuka ya Fara cin karo dasu Ma'isha ta jero Masa dama yasan za'a Rina Nan ya shiga rarrashin ta suna cikin chat d'in ne bakuwar number ta kirasa. Yana picking Tace "Haba yallab'ai kasa ina ta jiran ka, nan ne ma ya tuna cewar yace zai kirata dafe kansa yayi yace "Am so sorry Aysha na d'anyi busy ne gafar ce ni" Murmushi tayi ko ba komai bai manta sunan ta ba, tace "Bakomai yallab'ai Ni da na damu da nayi magana da kai ai na kiraka" Murmushi yayi yace "Afwan ina jinki" "ummm dama ba wani abu bane

Chapter 4 of 24