Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
inda motar take yace haisam ya zauna a gaban motar,shi Kuma ya zauna a gun zaman driver,Ma'isha Kuma tazauna a baya. Bayan mummy ta gama gyara ta, da taimakon Mummy da Ma'isha suka sa Umma a mota, Kai tsaye asibiti suka nufa, likitoci sunyi matukar jajincewa wurin kula da ita hakan yasa acikin Yan kwanaki ta samu sauki kamar ba ita ba. Wata rana Mummy ta kaiwa Umman Haisam ziyara, zaune suke suna Hira zuwa yanzu sun saba sosai, Nan take tambayar ta dalilin da yasa haryanzu bata biya wa haisam Kud'in WAEC ba, Bata 'boye mata ba ta Sanar da ita cewar Mijinta guba aka sa Masa a abinci da yanda kanin sa kwace Masa dukiya, ta tausaya musu sosai, a haka har suka gama hirar tasu ta dawo gida. Cikin dare ta kasa bacci, tashin Daddy tace "Am sorry na katse maka bacci" Zama yayi cikin muryar bacci yace "Kar ki damu,me ya Faru?" Nan ta shugay fad'a Masa Labarin da Umma ta bata, bayan ta gama basa Labarin ne tace "Darling ina so mu taimaka wa haisam da mahaifiyar sa" "Ina sauraron ki" "Me zai Hana tunda Boys Quarters d'in Nan babu kowa aciki a Basu part d'aya su zauna, Naga jikin nata bai gama warwarewa ba, sannan Ina so a biya wa Haisam WAEC" Murmushi yayi ya riko hannun ta yace "Madallah da samun mace kamar ki a rayuwa, tabbas ke d'in rayuwa tace, Maryam Allah ya Miki Albarka, a irin Rayuwar da muke ciki yanzu kowa kansa ya sani Amma ke kullum cikin taimakawa na kasa dake kike" Murmushi tayi Tace "To mijina mene ne amfanin Kud'in namu? Idan baza mu taimakawa na kasa damu ba,Kuma na lura Ma'isha tana so a taimaka musu ne kuma ina matukar son farin cikin ta,nasan idan taji Haisam zai dawo gidan nan kuma taji za a biya Masa WAEC zatayi matukar farin ciki" " Hakane Yar Albarka,Halin ki ta d'auko tana da tausayi sosai,ga son mutane" "Kaji ka da wani zance kai ta d'auko dai" "Zancen kike so,yanzu dai naji dukkanin maganar ki, Kuma zanyi yanda kike ce, Kuma Insha Allah zan rike Haisam tamkar d'ana, da niyata gidan nasu nake so a gyara musu" "A a tun da ga nan Kuma gidan ya mana girma mu kad'ai, su dawo Nan kawai" "To ba matsala, idan Allah ya Kai mu gobe zanje makarantar tasu na biya Masa, sannan ina so kije gidan ki d'auko mahaifiyar Haisam d'in, ban yarda ta 'dauko komai ba, Zan tura miki Dubu d'ari biyu, ki saya mata kaya, idan na nadawo zamu fita da Haisam d'in Shima na Masa sayayya" Farin ciki da Murna yasa ta rungumi mijinta had'e da yi masa godiya, a haka sukayi bacci. Washe Gari Daddy Kan yaje gun aiki ya biya ta makarantar su Haisam ya biya masa Kud'in WAEC harda NECO. Mummy na fad'a wa Ma'isha maganar da suka tattauna Akan Haisam da Umma tayi farin ciki sosai harda tsalle, tayi ta musu godiya da musu addu'a Wanda ya dace d'a yayiwa iyayen sa. Tana Isa school a kusa sit d'in Haisam ta zauna, tunda ta lura shi d'in ba mai son magana bane Hakan yasa sai ya kulata take kulashi. Principal ne ya shigo yana Kiran sunan wa'anda basu biya Kud'in WAEC d'in su ba, ga mamakin Haisam har aka gama ba a kira sunan sa ba, hannu ya d'aga yace "Excuse me sir!!! Yace "Yes" Mikewa yayi yace "I haven't paid and you didn't call my name" Cike da mamaki yace "You didn't pay? What's your name?" "Haisam Ahmad Umar" Ya shiga dubawa Bai ga sunan Haisam ba Yana duba list d'in wa'anda suka biya yaga sunan Haisam yace "Mr Man you already payed" Cike da mamaki yace "I payed? But sir please can you check the date of the payment for me?" "Sure" Yana dubawa ya Maida kallon sa ga Haisam yace "It was payed today"Yana Kai Nan ya sa wa'anda basu biya ba a gaba har Saida ya kai su bakin gate ya jaddada wa Mai gadi Akan Kar ya bari su shigo ya koma ciki. Haisam mamakine ya rufe, a zuciyar sa yake fad'in "Wa ya biya min Kud'in nan?" Da sauri ya d'ago kansa ya kalli Ma'isha ita ma kallon sa take, murya kasa kasa "kin San wani abu Akan haka ko?" Kai ta girgiza Tace "Ni ban sani ba" ta karasa maganar tana rufe bakin ta alamun dariya take son yi. Cikin sanyin murya yace "Ma'isha Please" Tace "Daddy ne ya biya" "Dan Allah dagaske?" "Uhmn gashi ka gani" "Amma....... " Shigowar malamin sune ya Hana shi karasa maganar da yayi niya, suna fita break ya Shiga neman ta bai ganta ba, Murmushi yayi yace "Alhamdulillah Allah na gode maka, yau Dole. Naje gidan su Ma'isha da Umma muyi musu godiya" Ma'isha da tun d'azu take tsaye a bayan sa tayi gyaran murya Tace "Anya zuwa gidan mu zakuyi ko Kuma Zaku koma gidan mu?" "Hmm zuwa Zamuyi dai" "Za dai ku koma gidan mu" "Ban fahimce ki ba?" "zaka fahimta idan driver yazo sannan ko ka gudu zamuje har gida mu d'auko ka" tana kainan ta ruga a guje, Yana Kiran ta Amma ina tayi nisa. _____________________________ Please comment and Share 🙏🏻🙏🏻 Milhat ce Yar Terawa 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 7 and 8 Haisam duk a kage yake a tashi sabida shi Sam bai fahimci Ma'sha ba, bayan an tashe su ne ya shiga neman ta, ai kuwa yana hangota da gudun sa ya nufi inda take Tana ganin sa tayi Murmushi, ya "Ma'isha wai me ke faruwane?" Cikin muryar dariya Tace "Ga Nan driver yazo" shiga tayi ya tsaya Yana kallon ta, ganin baida niyar shiga Tace " Haisam come in Mana" Ba musu ya shiga. Bayan ya gaida driver ya Maida kallon sa gare ta, yace "Ma'isha please tell me Mana" Dafe kanta tayi Tace "Ya Salam, Haisam Dan Allah ka kyaleni Idan muka je gidan zaka ga koma mene ne." Gyara Zama yayi yace "Tell me something Ma'isha" "Uhhmnn ina jinka" "idan Kika fada min mutuwa zakiyi ne kome?" "A a ko 'daya baza ka mutu ba" " So tell me" " No I won't." Cikin muryar dariya driver yace "Haisam ga naci, Ma'isha Kuma taurin kai to duk kuyi hakuri in muka koma gidan zakaji Kan zancen" "Hakan na nufin kaima kasan abinda ke Faruwa kenan ko?" "A a ba abinda na sani nikam" Girgiza kai yayi babu Wanda ya furta komai har suka Isa, Kai tsaye parlor suka nufa, Haisam duk ya kasa sakin jikin sa, ganin Umman sa a zaune a gun yasa mamaki ya rufe shi. Cike da mamaki yace "Umma kina kema Nan aka kawo ki?" Murmushi tayi, Mummy tace "Eh Nan aka kawota" Tsosa keya yayi ya durkusa ya gaida su,Daddy dake zaune yayi Murmushi ya amsa ba yabo ba fallasa. Yace "Tashi ka zauna akan kujera" Kai ka sa yace "A a Alhaji Nan ma yayi" Murmushi yayi yace "Haisam wannan umarni ne, ba shawara ba ne ba." Tashi yayi ya zauna gyaran murya yayi yace "Haisam naji tarihin ka, mahaifiyar ka Bata boye Mana komai ba hakika na tausaya muku, sannan na nemi ganin kune sabida ina so ku dawo Nan da Zama,sannan zan dauki nauyin karatun ka daga yanzu har Allah yasa ka gama" 'daga kansa yayi da sauri ya kalli Daddy sannan ya Maida kallon sa ga Umma, 'daga Masa Kai tayi alamun eh, a zuciyar sa yace "Wato Umma ta ta San da zancen" Gyaran murya Daddy yayi ya daura da fad'in "Nayi maka alkwarin zan dauke ka a matsayin d'an da na Haifa da ciki na, sannan kofa Bud'e take duk Sanda kake neman wani Abu kar kaji tsoro ko shakkar tinkarata ko Maryam" " Nagode Alhaji Allah ya saka, ya biya ka da gidan aljanna" " Umm Haisam, daga yanzu bana so na sake ji ka kirani da alhaji, ka Kirani da Daddy kamar yadda Ma'isha take kirana kaga Kenan Ma'isha ta samu wa" " To Alhaji, auu daddy nagode" Duk sukayi dariya, Maida kallon sa yayi ga Ma'isha yace "Daughter kuje kuci abinci, don zamu fita da Haisam din" Mikewa tayi Tace "Ya Haisam Tashi muje ko?" Mikewa yayi ba tare da yace komai ba ya bi bayanta, Umma tace "Alhaji, hajiya nagode sosai Allah ya saka da alkhairi, ban San wani irin godiya zan Muku ba" Mummy Tace "haba ke kuwa tun dazu fa kike ta godiyar nan, ya Isa haka, mu Dan Allah mukayi ba don komai ba, sannan mun lura akwai shakuwa a tsakanin yaran Nan Baki ga yanda ta tada Mana hankali ba nikaina mamaki ne ya kamani" "Ikon Allah, Amma ni Haisam bai tab'a min maganar ta ba ko da da wasa ne" "Ai bazaiyi ba don na lura Haisam na da zurfin ciki" Murmushi tayi tace "haka yake kamar ubansa" Alhaji dake Danna wayar sa, jin ta ambaci uban sa, yace "Yauwa please a ina baffan Nan nasa yake?" "Ya Nan cikin garin Nan" " Kina nufin cikin garin Gombe?" "Eh" " Abun zaizo Mana da sauki insha Allah" Mummy da Umma a tare sukace " Allahu yasa" Ya amsa da amin ya daura da fad'in "Maryam ku samu kuje shopping din Nan kar dare yayi, sannan please kar su d'auko komai a chan, za a Saya musu duk abubuwan da suke bukata, sannan idan kudin Bai Isa ba ki Kirani" Ta amsa da "to Alhaji" Mikewa yayi yace "idan yaran Nan sun gama ina ciki" "To alhaji a fito lafiya" 'bangaren su Haisam da Ma'isha kuwa abinci kala kala ne aka jera su,akan dinning duk ta bud'e Masa, Haisam Kan sa ne ya kulle ya rasa ma wani abinci zai ci,daga bisani yace ta sami fried rice din, bayan ta zuba Masa a plate ita ma tayi serving kanta sannan ta tsiyaya musu juice Wanda mummy ta had'a na Banana,kwakwa da Madara, Yana ci yana Santi har Saida ya cika cikin sa tam, yayi hamdallah, Ma'isha Tace "Ya Haisam na Kara makane?" Kallon ta yayi da lulu eyes dinsa yace "So kike ki hallakani?" "Laaa yaushe abinci ya tab'a hallaka mutu?" " Baki da Labari ko?" "Eh gaskiya ban tab'a ji ba" " To yau kinji" " Na daiji Amma ban yarda ba,taya za a yi abinci ya hallaka mutum?" "Yanzu ai a koshe nake idan na Kara sa wani abincin a cikina ko da kuwa spoon 'dayane mutuwa zanyi" Kama baki tayi tace "Mutuwa Ya Haisam nikam ban shirya kuka ba" "Ma'isha ke dai kin samu sabon salo" "wani irin salo Kuma?" "Naga kin dage Sai Yaya kike ce min,ni yayan ki?" "Eh Mana ko baka ji abinda daddy yace bane?" " Naji Mana Wai ke katuwa dake ki wani Rika cemin Yaya" Ajiye spoon din dake hannun ta tayi Tace "Nice katuwar?" "Eh Mana" Nan wasu siraran hawaye suka Fara saukowa daga idanun ta,Kama baki yayi yace "ikon Allah Dan Allah ki rufa min asiri,me yasa ki kuka?" Cikin muryar kuka tace " Ba Kai bane kace min katuwa" "Shiyasa kike min asarar hawayen ki?" Bata ce Masa komai Sai sautin shesshekar kukan da take kawaii yake iya ji, cikin murya Mai sanyi yayi yace "Yi hakuri Yar Kanwata ke baki San wa bane?" "Kanwar ka bayan kace ni katuwa ce?" "Ni na Isa na ce miki katuwa tuntuben harshe ne,bazan sake ba kiyi hakuri" " To naji zan hakura Amma Sai dai in zaka dauke ni a matsayin kanwar ka sannan idan na Kira ka da yayana zaka amsa?" "Na amince Sai Kuma me?" " Shikenan?" "Ah to ai hikenan baki da case kanwata" Rufe fuskar ta tayi wai ita a lallai taji kunya, Murmushi yayi yace "to kije ji fad'awa daddy na gama ko ina zamuje?" "bari naje na tambayo maka shi" "a a ni ban saki ba." Tashi tayi Tace " bari naje na fad'a Masa" Kai kawaii ya d'aga mata,d'akin Daddy ta nufa ta Sanar mishi da cewar Haisam ya gama. Bayan daddy ya shiga ciki Mummy Mikewa tayi ta d'auko makullin motar ta, Tace wa ummu "Tashi muje ko" Ba musu ta Mike a dai dai Nan Ma'isha ta shigo parlor cikin muryar shagwa'ba tace "Mummy tafiya zakuyi ku barni bayan nace Miki zan biku" "afwan daughter na sha'afane" "To Dan Allah mummy ku jira ni bari na canza Kaya" "To ki same mu a mota" Suka fice. A dinning daddy ya tarar da Haisam ya umurce sa da ya ajiye jakar sa, su fita hakan akayi, a tare Suka fito da Ma'isha, motar mummy ta Shiga yayin da Daddy da Haisam suka shiga motar Daddy, Mai gadi ne ya wangale musu gate, su mummy ne suka Fara fita sannan su daddy suka fita. A hanyar su ta tafiya daddy ke tayi masa Hira shi Kuma Sai dai yayi Murmushi idan ya Masa tambaya ne ya amsa da eh ko a'a a haka har suka Isa inda zasuje, kananan Kaya da shaddodi masu tsada daddy ya Saya Masa Sai kallan da Haisam ya zab'a a bashi, takalmomi da huluna Kuma ba a cewa komai. Haisam tsabagen farin ciki bakin sa ya kasa rufuwa don shi a iya sanin sa bai tab'a rike Kaya masu tsada haka ba bare ace nashi ne, bayan sun gama da shagon Kaya suka kaiwa telan Daddy sannan ya umurce sa da Yana son kayan Nan da kwanaki uku, ya amsa da to, ya cika Masa aljihu da kudi suka Kara gaba. Shagon sayar da waya suka nufa, daddy yace "Haisam ka zabi duk wayar da kake so anan" Haisam kallon daddy yayi yace "Daddy ka dai za'ba min ni ba sanin waya nayi ba" Daddy Har cikin ransa yaji dadin kiransa da Haisam yayi Daddy, Murmushi yayi yace "To why not mu d'auka maka iPhone 14?" Zaro Ido yayi yace "iPhone 14? Daddy naji ance wayar nada tsada sosai Kuma ma ban iya amfani da ita ba" " Kar ka damu Ma'isha zata nuna maka yanda ake amfani da ita, itama iPhone d'ince a hannun ta" " To Daddy nag....." Hannu ya 'daga Masa yace " A'a Haisam bana son godiyar Nan, daga yanzu bana so kalmar godiya ta Kuma Shiga tsakanina da kai" "Amma ai daddy masu iya magana sunce yaba kyauta tukuici ce" "Wannan Hakane Amma ni ban bukata" Shiru kawaii yayi don baya son jayayya da daddy. Kallon Mai shagon daddy yayi yace "Sa Mana iPhone 14 a leda sannan ka bani acct number ka na maka transfer" "Ai Alhaji babu wayar ba a ma samun ta anan sai dai idan kana so za a yi Muku order" "Okay to zuwa yaushe zai iso?" " Nan da sati haka" " Sati ai yayi nisa, anyways bamu iPhone 13 in yaso daga baya Sai a saya Masa wanchan d'in." Sa musu yayi leda sannan ya Saya Masa sim, had'e da earpod, Haisam farin ciki bazai misaltu ba, bayan sun gama suka wuce gida, daddy ganin mummy basu dawo ba ya "Na sani ai za a rina,Mata mata" Kallon Haisam yayi yace "Zo muje na nuna maka side Dinki" Bin bayan Daddy yayi wani d'an madaidaicin flat ne ya had'u iya had'uwa, Wanda tsaya kwatanta muku yanda take zai d'auke mu lokaci Mai tsawo. Tunda suka Shiga cikin gidan Haisam Sai kallon gun yake baki a bud'e a haka har Daddy ya gama nuna masa, daga karshe ya kaisa wani d'aki Wanda makeken Italian bed Ne a ciki,da wall drop Shima kalan gadon sannan da sofa masu kyau guda uku,'daya three sitter sauran biyun Kuma 1 1 sitter ne. Yace "Haisam wannan ne d'akin ka" Haisam durkusawa yayi Yana kuka Mai sauti yanayiwa Daddy godiya,da kyar daddy yasa shi ya Mike ya umurce sa da yayi wanka ya huta Kan su Mummy su dawo yayi ficewar sa. Haisam ya dad'e Yana zaune Yana mamakin abubuwan da daddy yayi musu,Ashe dama akwai mutanen kirki a Duniya, da wannan tunanin ya Shiga wanka,bayan ya fito ne yayi sallar la'asar dake suna shagon sayan wayar akayi sallar la'asar,bayan ya idar da sallar ne ya hau Kan gado ya kwanta,tunanin sabowar rayuwar da ya shiga yake a haka har bacci Mai nauyi ya d'auke Shi. Daddy ma wankan yayi bayan Nan yayi sallah ya kwanta Shima ya hau baccin sa Mai dadi. 'bangaren su mummy kuwa San Hussain suka Shiga zannuwa masu tsada da dogayen riguna,mayuka,gyalalluka takalmomi da jakkakuna baza su irgu ba, ta loda wa Umma,Umma kuka ta Shiga yi. Matsowa mummy tayi daf da ita tace "Haba Hajiya Fatima kisani fa muna cikin mutane,Zaki sa ayi ta kallon mu" Ma'isha ta miko Mata handkacif had'e da fad'in " kiyi hakuri Umma ki daina kuka" Murmushi tayi Tace "Na daina Ma'isha" Bayan sun gama sayyayan duk abui da zasu Saya suka nufi saloon,Umma rabonta da zuwa saloon tun Abban Haisam na Raye,wani irin iska Mai dadi take ji Yana Shiga kanta duk da kusan kullum saita wanke,Amma wankewan Kai a saloon Daban yake da wanda zakayi a gida. Bayan sun gama da saloon suka nufi gida suna Shiga Ana Kiran sallar magrib,a dai dai Nan daddy ya fito da alwalar sa,ya hango motar su tana parking girgiza kai kawaii yayi ya tsaya kallon su. Ma'isha na fita daga motar taje ta Kira Haisam su Shiga masallaci,da saurin ta,ta nufi part d'in da Haisam yake hannun ta dauke fa ledodi,a parlor ta ajiye su ta nufi d'akin sa,dake da ita aka gyara d'akin shiyasa tasan d'akin sa. Tana sa hannu taji kofar a bud'e take,lekawar da zatayi ta hangosa a Kan katafaren gadon sa yana sharban baccin sa hankali kwance. _________________________ Please share and comments Milhaat ce Yar Terawa 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 9 and 10 Shiga d'akin tayi ta tsaya kallon sa, Haisam a baccin sa yake ji kamar akwai mutum a Kan sa, a hankali yake bud'e idanun sa har ya sauke su Akan ta, Murmushi yayi cikin muryar bacci yace "Ya dai malama? Kin wani sani a gaba kina ta kallo na am in safe?" Murmushi tayi Tace "Of course you are safe, Daddy ne yace na Kira ka ku tafi Masallaci" "Daddy ne yace na Kira ka ku tafi Masallaci" ya fad'in hakan ne Yana kwaikwayon muryar ta ya daura da fad'in "Kuma kika tsaya kallo na ko?" Cikin muryar shagwa'ba Tace "Yaya shine kake kwaikwayata ni dai ba haka muryata take ba." Mikewa yayi ya nufi hanyar ban d'aki ya waigo ya kalle ta kyaji dashi" ya shige ban d'aki a gaggauce yayi alwala ya fito ganin Ma'isha na tsaye a inda ya barta ya sashi Kama Baki, kallon ta yayi cike da mamaki yace "Wai ke dama baki tafi ba? Ko so kike sai kin sani a gaba tukkunna?" Kai ta d'aga Masa alamun eh, girgiza kai yayi yace to muje Yana gaba tana biye dashi. Daddy na hango su yace "kaji yaran Nan har na ma manta na aiketa" Suna karasowa inda yake yace "Daughter ke kuwa daga aika ai ki zauna Sai kace an aiki baiwa gidan su?" Yar karamar dariya tayi Tace "Daddy ai Yaya ne, yake ta bacci dakyar na tashe shi" Haisam yace "Ji Dan Allah ko kunyar karya ma ba kyaji bayan...... " Daddy ne ya yanke Masa zancen yace "Ya Isa ya Isa, yanzu sai ka wuce muje Masallaci idan muka dawo sai ku cigaba da musun naku, kema ki wuce kije kiyi sallah" Ta amsa da "To daddy sai Kun dawo a Mana addu'a" Ya amsa da to ba tare da ya waigo ba,cikin gida ta wuce su Kuma suka wuce Massallaci" A parlor ta tarar da Mummy da Umma, mummy na ganin ta tace "daga zuwa aika Ma'isha sai ki zauna abunki?" "mummy ya Haisam ne da surutun sa" "Da surutun ku dai, ina sauran kayan Nan kike ajiye su?" " Yana part d'in su Umma, na d'auko ne?" "A a bar su kawaii d'auki wannan d'in ki Kai su Chan" Ta amsa da to had'e da d'aukan sauran kayan ta wuce dasu part d'in su Haisam, Umma ta rufa Mata baya. A chan Ma'isha tayi sallar maghrib da Isha, Haisam da daddy tunda suka fita basu dawo ba har Sai da aka yi Isha suka dawo gida. Mummy na ganin su Tace "Alhamdulillah to ba komai nasan yanzu bani kad'ai bace a gidan" Murmushi daddy yayi ya ce "Toh me Kuma ya Faru rankishidad'e?" "Duk fita kuka yi kuka barni Mana ni kad'ai kamar mayya" "Ahh ina su Ma'ishan suke?" "Tunda nace ta Kai Mata Kaya shiru kake ji ba ta dawo ba" Yar karamar dariya yayi yace "Ai Ma'isha ta iya zuwa aika, Haisam je ka kirawo min ita" Ya Mike Kenan ya hango shigowar su yace "Daddy ai ga sunan ma sun shigo" ya koma ya zauna. Girgiza Kai yayi yace "Wato shine kuka bar min Mata ita kadai ko?" Murmushi Ma'isha tayi Tace "Daddy wallahi Hira muke tayi muna kallon zee world bamu San lokaci ya tafi har Haka ba" "To kun kyauta, Hajiya yunwa fa nake ji" Mummy mikewa tayi Tace "Muje Dining dama dazu na kirb'a sakwara na sa a food flask" " Yauwa Yar Albarka na" ya Maida kallon sa ga Haisam yace "Son muje ko?" Mikewa yayi ba tare da yace komai ba ya bi bayan sa, Ma'isha hannun Umma ta rike tace "Umma muje" Mummy Tace "Shikenan nikuma an yaye ni ko?" Dariya kawai sukayi suka nufi dinning suna cin abinci suna hira har suka gama, bayan sun gama ci Haisam yayi musu Sai da safe ya koma part d'in su, Umma da Mummy da Ma'isha a parlor suka zauna suna Hira a yayin da daddy ya shiga bed room dinsa, sun dad'e suna Hira har karfe 10 ta wuce Umma sai hamma take cikin muryar bacci Tace "Ni ina gani zan wuce bacci nake ji sosai ga gajiyar da muka kwaasa d'azu" Yar karamar dariya mummy tayi tace "Ni kaina baccin Nan nake ji muje na d'an taka Miki" "To Shikenan" mikewa Umma tayi had'e da Mika tana ambaton "La'ila ha illallalah Muhammaddar rasulullah" Ma'isha cikin muryar shagwa'ba tace "Umma zan biki mu kwana tare please" Murmushi tayi Tace "To Muje daughter" riko hannun ta tayi sukayi wa mummy Sai da safe suka fice, mummy Murmushi tayi ta girgiza Kai ta shige d'akin ta. WASHE GARI Bayan sun idar da sallar asuba Ma'isha ta dawo part d'in su, Kai tsaye d'akin ta tashiga ta yi wanka sannan ta fito don Taya mummy aiki a kitchen, Tana Shiga kitchen ta tarar da mummy juya ruwa a flask. "Mummy ina Good Morning" "Ahhhh 'yar Umma har Kun tashi?" Murmushi tayi Tace "Eh mummy" "To ya kuka tashi,ya Umman taku?" "Lafiya Lau Alhamdulillah" "Amma meyasa baki tsaya kin tayata aiki ba Kika dawo?" "Itace Tace na dawo, shiyasa Kuma Kinga , zamuje school, bara nayi wanke wanken" "A'a ki bari yarinyar nan zata Zo ta yi kije ki samu ki shirya naga har kinyi wanka je ki kawaii ki shirya" "mummy tun yanzu? Karfe 6 fa" "Ki dai sake dubawa 6:30 ne" Agogon bangon dake manne a kitchen d'in tace "Gaskiya lokaci yana gudu Bari naje na sa uniform" "Okay" Ta fice a kitchen d'in Bata d'auki lokaci mai tsawo ba ta dawo, a lokacin bakwai har ya wuce, a dining room ta tarar da mummy da Daddy bayan sun gaisa ta karya, a gaggauce ta fice tana musu sai ta dawo, inda ake parking mota ta nufa, ta tarar da driver da Haisam suna Hira cikin girmamawa ta gaida driver kana ta maida kallon ga Haisam tace "Good Morning Yaya" Murmushi yayi yace "Morning" Duk suka shige motar suka, ba su tsaya a ko ina ba sai makaranta. Haka rayuwa ta kasance wa ma'isha da

Chapter 2 of 24