Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ne a d'akin Umma cikin sanyin Murya da kamar rarrashi yace "Umma please, Dan Allah ki duba lamarin nan" "Haisam Kenan, haryanzu baka fahimce ni ba Sam, bazan iya auran wani ba Bayan mahaifin ka zan cigaba da Zama haka har nima mutuwa ta riske Ni" "Umma ki dubi girman Allah ki sake tunani a Kai, kar ki manta fa Daddy shi ya taimaka mans muka fita daga cikin kuncin Rayuwa har muka dawo Mutane, kin San abubuwan da bazan iya lissafa su ba, yau yana neman abu a wurin Wanda zamu iya bashi Kuma mu hana shi, Idan mukayi hakan ba muyi Masa butulci ba kuwa?" A razane ta d'ago kanta ta kalli Haisam d'in kana ta sake kawar da kanta, ba Tace Masa komai ba magana yayi tayi Yana bata hakuri Amma bata tanka Masa ba har ya gaji yayi shiru mikewa yayi da niyar fita, har yasa Kai ya tsinkayo Murya Umma tana fad'in "Shikenan Na amince" Da d'an saurin sa ya dawo cikin d'akin ya d'an rungumeta ta kana ya sake ta yace "Yauwa Umma ta ai nasan Zaki amince" mikewa yayi Yana fad'in "zani na fad'awa Mummy" "Wa ya aike ka? Ka bari da kaina zan Sanar da ita dama yanzu zan Shiga part d'insu" Murmushi yayi yace "Shikenan Umma" Mikewa tayi ta d'auki mayafin ta, ta nufi part d'insu mummy ta tarar a parlor sun dad'e suna Hira sama sama kamun ta fad'a Mata cewar ta amince mummy murna yasa ta Kira daddy a waya ta Sanar mishi, yayi farin ciki sosai shima Nan take ya Sanar da Abba, Abba baiyi kasa a gwiwa ba yasa aka tura masa number ta Sannan mummy ta bata na Abba, Ba 'bata lokaci ya neman Soyayyar ta. Haisam kuwa d'akin Isha ya Shiga ya Sanar da ita labari Mai dad'i tayi murna sosai, Nan sukayi ta hirar su. *BAYAN WATA 5* Shirye shiryen biki su ke tayi duk da ba wani events zasuyi ba daga walima sai walima shima anan gidan su Ma'isha kawai za'ayi. Yayin da Haisam da Aysha wata soyayya ce Mai karfi ya Shiga tsakanin su kusan kullum suna tare, Ma'isha kuwa damuwa Sai abunda ya karu, Meerah kuwa kusan ko wani sati zata Zo ta duba lafiyar ta sannnan ta bata shawarwarin da ya Dace Amma Duk da hakan Isha ta kasa daina son Haisam. Alhamdulillah an d'aura Auren Umma da Abba sannan Amarya ta tare a gidan ta anan cikin garin gombe, Daddy ne yayi iya bakin kokarin sa ganin ya dawo da dukkanin aikin Abba a gombe. Ma'aruf kullum cikin Kiran Meerah yake Akan maganar Ma'isha, Amma Ma'isha Taki bada had'in Kai shi Kuma ya kasa hakura. Wannan Kenan "Isha please think about it Mana, Wallahi ma'aruf na sonki ke ko tausayin sa bakya ji? Ki duba kiga ni fa tun d'azu Yana waje Yana jiran ki Amma kin ki, ki saurare shi" "Nifa na Riga na fad'a muku bana son sa Kuma bazan tab'a son wani ba bayan Haisam meyasa Kika kasa fahimta na ne?" "To ai Banga amafanin hakan ba, tunda kin kasa fad'a Masa har yayi nisa da soyayyar wata hakan zai tabbatar miki da cewar kin rasa shi Kennan har abada" Hawaye na a idanun Ma'isha d'aya na bin d'aya, taji zafin maganar Meerah Amma Kuma tasan gaskiya ta fad'a mata sabida masu iya magana sukace shi Gaskiya d'aci gareta. "Na Sani Meerah, nasan kin damu dani kin damu da farin cikina gami da lafiya ta Amma Dan Allah kar kiyi kokarin sani Dole sai na Kula shi" Mikewa meerah tayi Tace "fine then Ni zan tafi dama shine ya ce na rako shi, ki sani baza ki sake gani na ba a gidan ku, sannan zan fad'awa Haisam halin da kike ciki" ta Kama hanya zata wuce Ma'isha ta Sha gaban rike hannayen ta tayi tana kuka "Please don't do this to me Meerah ke ce kad'ai kike saurarata ke ce kad'ai Kika San damuwa ta Akan me zakimin irin wannan hukuncin Kuma Kar ki manta kin min alkawarin baza ki tab'a fad'a wa kowa matsala ta ba" Fin cike hannun ta tayi da karfi Tace "Dallah malama gafara min na wuce idan ke baki da shi to ni Ina dashi, idan baza ki bawa ma'aruf dama ba ya maye miki gurbin Haisam ba to Dole ne ki samu Haisam" Har kasa ta durkusa ta rike kafafun ta tana Mata magiya Akan Kar ta fad'a Masa. Meerah Sam Bata Jin dad'in ganin kukan ta Amma Dole ce tasa tayi Mata hakan, Dole ta samarwa kawarta farin ciki gudun Kar ta kamu da ciwon zuciya. Cikin murya Kamar fad'a Tace "Wallahi tallahi sai na fad'a Masa in dai baza ki kula ma'aruf ba ai zab'i na Baki" mikewa Isha ta tayi ta share hawayen ta Tace "Shikenan na amince wallahi zan kula ma'aruf, Dan Allah kar ki fad'awa ya Haisam Dan Allah" Murmushin samun nasara Meerah tayi kana ta sa hannu tana share Mata sauran hawayen dake fuskar ta. Cike da kulawa Tace "Am sorry Isha, ki daina kuka Sam bana jin dad'in ganin ki a Haka ne shiyasa nabi ta wannan hanyan, yanzu ki d'auko mayafin ki muje Yana chan yana jiran mu Amma ki wanke fuskar ki tukkunna" Ba musu tayi yanda Tace mata suka fita suka tarar dashi a cikin motar sa, jiki na rawa ya fito suka gaisa, Mai gadi tasa ya kawo musu kujera ya ajiye musu a inuwa, suka zauna daga bisani Meerah ta koma d'akin Isha tana jiran su, sai da suka gama hiran ma'aruf ya kirata ya maida ta gida, tun daga wannan ranar Isha ta fara kula ma'aruf lokaci zuwa lokaci Kuma Yana zuwa gidan su tun bata sake Masa har ta Fara Duk da ba son shi take ba, ma'aruf mutum ne mai abin dariya yakan sa taji ta manta Duk wata damuwar da take dashi in dai suna tare. *AFTER 1 YEAR* Sosai Ma'isha ke mayar da hankalin ta Akan karatun ta, Sannan Duk weekend a gidan Umma take yi, Haisam kuwa tunda Umma tayi aure aka rufe part d'insu ya dawo part d'insu mummy Yana d'akin sa kusa da na Ma'isha , idan suna gida sukan zauna a parlor suyi Hira Duk sanda ya kawo maganar Aysha kuwa sai tayi yanda tayi ta kawar da maganar. Ma'isha ne zaune da Ma'aruf a garden suna hirar su, labari yake Bata dariya take Sha sosai yayin da shi Kuma sai aikin kallonta yake. Haisam kuwa dawowar sa Kenan daga gun Aysha tunda ya Shigo gidan yake kallon su, ji yayi ransa ya 'baci Amma bai San dalilin hakan ba, ya d'auki kusan mintuna biyar Yana kallon su su kuwa Basu ma ji shigowar sa ba, kasantuwar motan da tint yasa Basu ganshi ba, ajiyar zuciya yayi Sannan ya fice daga cikin motar har ya wuce Ma'isha Tace "Yaya ka dawo?" Kirkirerren Murmushi yayi Sannan ya dawo mikawa ma'aruf hannu yayi suka gaisa turo baki Isha tayi Tace "Dama Yaya wuce wa zakayi Kamar baka ganmu ba?" "Am sorry princess , kin San hankali shine gani ban lura bane" kallon Ma'aruf yayi Wanda shima kallon sa yake yi, da sauri ma'aruf d'auke Kan sa gani yayi ya Masa kwarjini, maganar su sukayi tayi kana ya shige cikin gida. Ma'aruf kuwa natsuwar sa ya rasa yace "Wannan fa Yayan kine?" "Eh Yayana Ne" "Amma ya kuke dashi?" "My cousin, meyasa kake tambaya?" "No..... Bakomai naga Kuna Kama ne shiyasa" Murmushi kawai tayi gani kawai tayi ya mike yace zai tafi, ba don taso ba ta rakashi jikin motar sa, sai da taga fitan sa ta koma cikin gida. Kamar wasa Ma'isha tana final year kasantuwar pharmacy 5 years akeyi shi Kuma Haisam saura Masa shekara d'aya ya gama, Meerah kuwa ta dad'e da gamawa har tana aikin ta a medical center dake cikin garin gombe. Bayan Ma'isha tayi graduating Abba ya sa ma mata aiki itama a medical center hakan yasa kullum suna tare da Meerah, Haisam kuwa kullum cikin bibiyar Aysha yake da ta gabatar dashi gun iyayen ta Amma taki kullum amsar d'aya take bashi zan had'a ku idan lokaci yayi. Yau ma hakan Tace Masa "haba Habiby saurin me kake Ne Kam" "Aysha!!! Jikin ta ne yayi sanyi da jin yanda ya Kira sunanta ta amsa da "Na'am" tashi yayi ya zauna daga kwanciyar da yake wayan dake hannun sa ya maida d'ayan kunnen nasa yace "Anya kina Sona kuwa?" "Wannan wace irin tambaya ce Haka, kafi ko wa Sanin irin soyayyar da nake maka Kuma kake min irin Wannan tambayar?" "I doubt much gaskiya in dai dagaske kina sona ki barni na tura su Daddy gidan ku gudun Kar wani ya shige min" "Allah kar ka damu habiby next year fa zaka gama karatun ka kaga Ni Kuma sai Nan da 2 years na maka izini kana gamawa kazo ko da kuwa baka Sanar dani ba in yaso sai na gama a gidana ko" Dad'in maganar natan yaji Amma ya basar yace "Shikenan sai anjima zan Zo gidan" Da sauri Tace "A a kar kazo" Cike da mamaki yace "Meyasa?" "Umm.... Umm... Dama.... Dama Mom ce ta aike Ni zanje gidan kanwarta sai dai idan zamu had'u a Chan" "Okay wani unguwa ne?" "Federal low cost" "Oh unguwar mu nema idan kin Zo let me know" Bai jira yaji abinda zata ce ba ya kashe wayar, d'akin isha ya nufa ya tura kofar yaga wayam Bata nan. Layin ta ya Kira tana picking yace "Yau weekend ina Kika shi ne, tun safe ban ganki ba?" "Wallahi Yaya ina gidan Umma ne" "Shine baza ki fad'a min ba mu je tare?" "Am sorry na Shiga d'azu na ga kana baccine shiyasa" "okay Nima gani Nan zuwa" Ta amsa da "okay" sai ta kashe. Haisam dama da already yayi wanka Kaya kawai yasa ta fice, ya nufi gidan mummy, sai Bayan da iya sane ya tuna ya bar wayan sa a d'akin, ganin yanda Umman sa tayi kyau tayi fresh hakan yasa shi jin dad'i sosai. Umma na zaune a kasa, gata da babban ciki Wanda haihuwa yau ko gobe, Isha ganin tana wahala sosai ta fad'awa mummy zata zauna anan har sai Umma ta haihu Kuma ita kad'ai take aikin ta ga ciki, ita Ma'isha kullum mamaki take meyasa su Daddy basa son Yar aiki a gida. Aysha kuwa ta Kira layin Haisam yafi sau a irga har ta koma gida bai kirata ba , a ranar Kam raba dare yayi Yana rarrashin ta dakyar ya Samu ta hakura. Ma'aruf kuwa Duk sanda yake son ganin Isha Yana zuwa asibiti su gaisa sama sama yayi tafiyar sa ganin ta koma gidan su Umma yasa ya Fara zuwa gidan nasu, shi Sam bai San dalilin da yasa baya son ganin Haisam ba, Kuma hankalin sa ya kasa kwanciya shi duk tunanin sa Soyayya suke, sai da Meerah ta tabbatar Masa da cewar shakuwa ce kawai irin ba Yan uwa da Yan uwa. Wata Rana, cikin dare Isha taji Umma na Kiran sunan ta , da gudu ta fita ganin Umma a cikin jini yasa tayi matukar tsorata gashi Abba baya gari Sannan Kuma karb'an haihuwa ba 'bagaren ta bane, da gudu ta d'auko wayan ta ta Kira Haisam, kasantuwar unguwa d'aya suke bai Kai mintuna goma ba ya Isa da taimakon Sa da Isha suka sa ta a mota, suna Isa asibitin aka tabbatar musu da nakuda ce. _____________________________ Please comment Vote And share Milhaat ce Yar Terawa 🍃*DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 37&38 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ _Continuation........_ Haisam da Ma'isha na zaune a reception, Haisam Kam kwata kwata ya kasa nutsuwa ya zauna ya tashi ya fara kaiwa Yana kawo wa, ya dawo ya zauna. Ma'isha tausayin sa ya kamata sai ta tuno lokacin da Umma bata da lafiya, cike da kulawa Tace "Yaya please ka zauna Mana addu'ar mu take bukata a yanzu" "Princess wallahi na tsoratane sosai, mata suna wahala sosai wallahi duk Wanda yace zai tozarta mace ko ya wulakanta ta bai san ciwon kansa bane bare Kuma ace uwa" "Uhmn hakane Kam Amma fa ga Wanda ya sani, sabida wani abun idan kaji sai kaji Kamar Duniyar Nan an Tara zallan mahaukatane, kwanaki naji labarin wani ya Mari mahaifiyar sa akan kawai Tace Masa ya aske gashin Kan sa" "kin gani ko to wannan ina zaiga dai dai fisabilillahi" "Allah dai ya rabamu da iyayen mu Lafiya" Ya amsa da "Ameen summa ameen" Tace "Amma Yaya ka fad'a wa mummy zaka zo kuwa?" "A a wallahi a birkice na fito, Amma bara na Kira daddy" "shi da baya Nan?" "Eh gara shi d'in ya fad'a mata" "Toh" Kiran daddy yayi ya Sanar Masa shi Kuma ya Kira mummy ya fad'a Mata, mummy Kiran Haisam d'in tayi, tayi ta fad'a akan bai Sanar Mata ba suna Yara sun kaita asibiti idan ana bukatar wani abu fa, cikin Daren ta bugawa driver kofa kasantuwar yana zaune ne a boys quarters shi da Matar sa, d'auko motar sukayi gidan Umma suka fara nufa ta d'auko Duk wani abunda za a bukata kana suka wuce asibitin. Bayan ta Isa asibitin na had'a su duka tayi ta masifa Banda hakuri Babu abinda suka ce mata, haka Umma ta kwana ba ta haihu ba sai uban wahalar da take Sha, har gari ya waye sai abin ya tashi ya sake kwanciya. Ganin har karfe 8 tayie bata Haihuwa ba Umma Tace su koma guda Ma'isha ta had'o musu breakfast ta kawo, a gidan Umma Haisam ya ajiye ta ya Koma gida yayi wanka ya dawo gidan Umman sai da ya karya Ma'isha ma tayi wanka suka koma asibitin. Abba na Abuja ji yake kamar ya dawo Amma ba hali kasantuwar washe gari yana da meeting da zasuyi, Daddy Kuma yana bauchi yaje yin wasu harkokin sa a Chan, anan asibiti sukayi sallar azahar, Haisam banda matsar kwalla ba abinda yake yi Mummy da Isha Kuma sai aikin rarrashin sa suke suna kwantar Masa da hankali Likita ce ta fiti fuskanta d'auke yake da Murmushi gunsu ta nufa Tace "Alhamdulillah Allah ya sauke ta lafiya, ta Samu Twins duka Mata" A tare su Umma suka Shiga hamdallah, Likita kuwa Tace "Amma ta zubar da jini sosai Gaskiya tana bukatar jini" Haisam a rud'e yace "To a d'i a nawa mana" Hannu ta d'aga Masa had'e da fad'in "Come with me." Yabi bayanta. Sai da aka gyara su tsaf da jariran ta Mummy da isha suka Shiga suka gansu Yara kyawa Masha Allah, wayar Ma'isha ce Fara ringing picking tayi ta dafa Kai "Tace am sorry wallahi yanzu haka ina specialist ne mom d'ina ce take labour, Amma gani Nan zauwa yanzu" Mikewa tayi Tace "Mummy zan tafi ni na manta ma yau afternoon nake karfe biyu ya kamata na karb'e ta gashi har quarter to 3 yanzu" "Yi maza kije Allah ya tsare" Ta amsa da "Ameen Mummy" sai da ta d'auki hoton jariran kana ta fice, napep ta Tara ta koma gidan Umma ta d'auko lab coat d'inta kana ta d'auki motar ta ta wuce asibiti, tana Isa wacce zata karb'e ta, ta tafi, wayar ta ta zaro ta turawa Daddy da Abba hotunan, Abba na gani ya kirata Yace "Dama ta haihu ne babu Wanda ya fad'a min" "Eh Abba d'azun Nan ta haihu" "Amma shine baku fad'a min ba tun d'azu hankali na a tashe yake" "Yi hakuri abba wallahi Mun shafa'a ne, Kuma ance tana bukatar Karin jini" "Subhannallahi an samu an Sa Mata?" " Ban sani ba wallahi nima yanzu ina bakin aikine" "okay bari na Kira su naji" Ya katse wayar Murmushi tayi Tace "Lalllai Abba bai ma damu da yaran ba matar sa kawai ya sani" Nan ta cigaba da aikin ta. Haisam kuwa jinin sa bai Dace da na Umma ba sai da suka saya sannan aka sa mata, bacci Tasha sosai har sai yamma lis ta farka, Murmushi kawai tayi ta yi, tana kallon 'ya'yan ta. Mummy kanta ne ya kulle ta rasa yadda zatayi , Ma'isha na gun aiki gashi suna bukatar abinci yau ga ranar Yar aiki, Kiran abba tayi ta rarrashi shi cikin ikon Allah ya amince dama akwai wacce take son Fara aikin a gidan mummy Amma ya Hana, Mummy ba tayi kasa a gwiwa ba ta kirata, ta fad'a mata Duk abinda zatayi tana zuwa Mai gadi ya bud'e mata gate ta shiga sabida mummy ta Riga ta fad'a Masa hakan yasa bai tsaya tambayar ta ba. Duk abubuwan da Mummy ta fad'awa Sadiya duk tayi su kasantuwar ita d'in Mai nutsuwa ce, Bayan ta gama ne ta Kira Hajiya ta Sanar mata akan ta gama, Mai gadi mummy ta Kira tasa ya kawo ta asibitin ta kawo musu abinci da duk da duk wani abun da zasu bukata. Kwanakin su uku a asibitin aka sallame su, a ranar Kuma Abba ya dawo, bakin Nan a wage an kasa rufe shi, Mummy Kam gaba ki d'aya ta dawo gidan Umma tana kula da ita, bayan Nan mummy tasa Dole sai da aka samawa Umma ita ma Yar aiki, sai Bayan suna Mummy ta koma gida kasantuwar Daddy zai dawo, Twins kuwa Ana Kiran su da Aaima da Aymana. Sosai suke samun kulawa a gun familyn gaba ki d'aya kun San Twins da Shiga Rai musamman ma ace identical Twins ne. Kwan a tashi ba wuya a wurin Allah, Haisam ya samu ya gama makarantar sa sabida good Results d'insa ma Asibitoci da dama suna son su d'auke shi aiki, Amma Isha ta kafa ta tsare Dole ya karb'a a inda itama take aiki, acikin shakara d'aya komai ya canza, Haisam kuwa dama a kage yake ya gama don ya samu damar mallakar Aysha, Ma'aruf kuwa Ma'isha ta kaishi sun gaisa da su Daddy an San da zaman shi, komai tafiya normal yake sai godiyar Allah. Haisam ne zaune shi daddy suna Kallo a parlor sai yayi Kamar zaiyi magana sai Kuma ya kasa, mummy Ce ta fito hannun ta rike take da Plate fruits ne a ciki ta ajiye a gaban Daddy, Kallon Haisam tayi Wanda ya Shiga duniyar tunani, Kiran sunan sa da tayi "Son!!! Ne ya dawo da shi daga tunanin da ya Lula ya amsa da "Na'am Mummy" "Lafiyan ka kuwa?" "Lafiya Lau Mummy" Murmushi daddy yayi yace "Tun d'azu na lura dashi Akwai abinda yake damun sa amma yayi shiru, ka fad'a Mana Son me ke faruwane? Ko dai matsalar daga gun aikine?" "A a daddy dama.... " Sai Kuna yayi shiru yana Sosa keya daddy yace "Feel free man, ka Fad'i Duk abinda kake so ni Kuma na maka alkawari zan maka shi in bai fi karfina ba" "Umm dama... Dama Akwai wacce Muke soyyaya da itane , to ina so a nema min auren tane" Murmushi mummy tayi Haka shima daddyn yace "Wace ce Kuma Yar gidan wace ce?" "Sunanta Aysha,Amma Gaskiya daddy tun da muke ban samu damar ganin mahaifin ta ba, Amma na San gidan su" "Toh Shikenan ba matsala, sai ka Sanar da ita su sa mana Rana" "Daddy Kuna iya zuwa gobe ma don munyi magana da ita" "To Shikenan dama Abban Kuma yana gari kaga sai muje goben kawai" "To Shikenan Allah ya kaimu." Mummy tunda Haisam ya ambaci sunan wata ba sunan Ma'isha ba sai taji ba dad'i Haisam mikewa yayi ta Shige d'akin sa, mummy cikin damuwa Tace "Alhaji wallahi na d'auka yaran Nan soyayya suke" Cikin rashin fahimta yace "Wasu yaran Kenan?" "Ma'isha da Haisam Mana Gaskiya na dad'e ina burin naga an had'a su aure" "hmm bake kadai ba har Ni kaina na yaba da halin yaron Nan, Amma tunda ya ce ga wacce yake so ai baza mu Masa Dole ba ita Ma'ishan sai ta fad'awa wannan yaron da yake zuwa gun ta ya turo Iyayen sa sai a had'a ayi rana d'aya." Ma'isha ce ta Shigo cikin parlor bakin ta d'auke da sallama da kayan aiki ajikin ta da alama daga asibiti take Zama tayi a Kan kujerar da yake fuskantar su Daddy a kasalan ce ta gaida su suka amsa daddy yace "Yauwa daughter kin dawo a dai dai, ki fad'awa wannan yaron da yake zuwa wurin ki ya turo magabatan sa in har da gaske yake sai a had'a Rana d'aya da na Yayan ki shima gobe zamuje mu nema Masa aure" Zumbur ta Mike Tace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un Aure Kuma? Yayan aure zeyi?" Mummy cikin fad'a Tace "Ke Lafiyan ki kuwa me haka?" Jiki a sanyaye ta d'auki Jakarta ta haura sama da gudu tana kuka, Daddy yace "Meyasa Kika yi Haka?" "Alhaji me Kuma nayi?" "Baki San ma me kikayi ba?" "Umm to Alhaji maganar aure fa akayi, sai kace zancen mutuwa akayi, Kuma Alhaji ban ma San nayi hakan ba,Amma Alhaji nifa ina ganin yarinyar Nan tana son Haisam" "Kamarya Kenan fa?" "Baka lura da hakan ba yanzu fa maganar auren sa da kayi ne ya razanar da ita yanzu Nan tabbata kuka takeyi" Ajiyar zuciya daddy yayi yace "Maybe shakuwa ce kawai ba soyayya bace , Amma shekaru nawa sukayi suna tare a gidan Nan ai in da Soyayyar ce da mun sani ko? " "Hakane Kam, to Allah ya tabbatar da Alhairi" "ameen." Kamar yadda mummy Tace Isha kuka take tun da ta shiga d'akinta take aikin kuka Haisam kuwa Yana kwance hankalin sa kwance Yana waya sa masoyoyar sa, ya sanar da ita su daddy zasu zo gobe, tayi murna sosai harda Yar tsallen ta, Tace "Yanzu bari naje na fad'awa Mom ta sanarwa da Daddy" "Toh ki bari mu gama wayar Mana tukanna" "Aaa wallahi za dai muyi waya anjima zanje na fad'a mata" "Uhmn habibty zumud'i Kenan?" Cikin muryar Shagwab'a Tace "Toh habib ranar da nake jira Kenan fa kaga zumud'i dole, so kar kaga laifina" "A a Banga laifin ki ba ko kad'an ni kaina na kosa goben tayi, don a gaskiya ban so auren mu ya wuce Nan sa da 3 Months" Zaro Ido tayi kamar yana kallon ta tace "Har 3 Months Gaskiya yamin Nisa Habib" "A hakan yayi nisa? To ya ya kike so ayi?" "Nan da 2 months dai,kaga dama muna Shirin Exams ne zamu samu hutu Mai d'an tsayi kawai sai ayi" "To Shikenan hakan za'ayi zan Sanar wa su Daddy idan sun amince Shikenan" "Zama su amince,yanzu dai bye naji kamar daddy ya Shigo" "Bye" ta katsewayar, da kanta ta Sanar da dad halin da ake cike Murmushi yayi yace "Yaran zamani ba kunya wato ma zan yi baki Shikenan Allah ya Kai mu goben sai sun Zo" "To Daddy." Ma'isha kuwa sai da tayi kuka Mai isarta kana ta fito parlor mummy Tace "Dama yanzu zan Shiga na duba ki Lafiyan ki kuwa?" "Lafiya Lau Umma" "Ya naga idanun ki sun Kumbura?" "Bacci nayi Mummy,an gama abinci?" Ta fad'i hakanne don ta kawar da maganar ba don tana Jin yunwa ba. Mummy ta amsa da "Eh an gama,Yau anan Zaki Kwana ba gidan su Abba ba?" "Eh Mummy sai jibi zan koma chan d'in" "To Shikenan Allah ya kaimu,zo muje dining d'in." A tare suka zauna Ma'isha Tace "Mummy ina daddy?" "Ya fita yaje gidan Abban ku zasuyi maganar zuwa gidan su budurwar Yayan

Chapter 10 of 24