Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba ya hannu ya riko hannayen ta, wani abu taji yarrrr tun daga tsakiyar kanta I'xuwa tsakiyar kafan ta, da sauri ta zare hannun ta. Murmushi yayi yace "Princess wai haryanzu fushi kike dani?" 'dan ja da baya tayi ganin haka Shima ya matsa kusa da ita ta Kuma yin taku biyu ta baya shi Kuma yayi Taku biyu ya iso ta haka sukayi tayi har ta Kai jikin bango, hannu yasa ya riko hab'arta ya juyo kanta ta kalle shi. Idonta cikin nasa, idanun ta sun taro ruwa kiris suke jira su zubo ganin hakan yaji duk ba dad'i kasa da murya yayi yace "I Know I hurt you, Dan Allah ya Isa Haka bana jin dad'in hakan duk kin Canza min kamar ba princess d'ina ba" Hawayen da dama jira suke suka fara bin juna suna sauka da sauri yasa hannu yasa ya fara share mata yana girgiza kansa, ya kuma cewa "Am sorry My princess" Ma'isha runtse idanun ta tayi tana Jin dad'in sunan My princess wani 'bagaren Kuma ji take kamar zuciyar ta zata fashe sabida gani take kalmominsa na yaudara ce kawai. Haisam ganin hawayen Ma'isha ba karamin tada masa hankali yake ba ji yake kamar yasa harshen sa ya lashe hawayen ta yana Kuma ji kamar ya rungumeta a jikin sa ko zata ji saukin abinda take , amma bazai iya hakan ba sabida tun ba halaliyar sa bace. Riko hannun ta yayi ya zaunar da ita a bakin gado, ya durkusa a gaban ta hannun ta d'aya ya rike yasa hannun ta a tsakiyan hanyen sa, murza hannun nata yake a hankali yana kallon ta, banda hawayen dake zubiwa daga idanun ta Babu abinda take yi, har sai da ya ga ta daina kukan ya sake hannun nata sannan ya mike ya zauna a gefen ta. Still yana kallon ta yace "Please ki daina kukan haka bana son ganin ki haka, sannan dama na kawo miki labari ne Mai dad'i Amma na fasa" ya karasa maganar kamar yaro d'an shekara 3. Kirkirerren Murmushi tayi Tace "Na daina kukan fad'a min me ya faru?" "Zan fad'a miki but da sharad'i" "Ina jinka" "Sai kin min alkawarin kin daina fushi dani tukunna zan Sanar dake" " Toh ai Yaya Kaine kake fushi dani bani ba, tunda ko magana ma ka daina min ko da na maka ma amsa mara dad'i nake Samu ko Kuma kaki kulani, Kuma in ba Ni na maka magana ba bakayi min" "I Know, kin 'bata min raai ne wallahi, Amma yanzu komai ya wuce am sorry kinji?" "Hmm Shikenan" Mikewa yayi Tace "Haa'ah ina zuwa Kuma?" "Sallah zanyi kema na San bakiyi ba, so ki tashi kiyi" " Labarin da kace zaka fad'a min Kuma fa?" "zan fad'a miki anjima ki tashi kiyi sallah, bye" ya d'aga mata hannu kana ya fice. Murmushi tayi tana kallon hannun ta da ya rike ta dad'e tana kallon hannun ta tana shafawa da d'ayan hannun nata, sai gani nayi ta Mike firgit ta shige ban d'aki ko me ta tuna oho. Haisam Bayan yaje Masallaci ya dawo ya koma d'akin sa yayi wanka, wando three quarter baki ya saka sannan ya saka Riga armless Shima baki kana ya fito yazo part d'insu Daddy zaman sa ke da wuya daddy ya Shigo da Baki sun Kai su Shida cikin girmawa ya gaidasu suka amsa, Kai tsaye dinning suka wuce, mummy da Umma suka fito daga kitchen da sauran abincin Nan aka Shiga gaishe gaishe, Bayan sun ajiye suka koma d'akin mummy suka fara hirarsu a chan. Bayan su Daddy sun gama cin abinci suka d'an zanta har karfe takwas da rabi kana suka gama meeting d'in, fita sukayi duka a tare har wurin motocin su ya raka su duk suka wuce Amma banda mutum d'aya a tare suka sake shigowa a parlor suka zauna Haisam ya musu sannu suka amsa Nan fa daddy suka fara Hira ba kakkautawa da mutumin nan. Ma'isha kuwa Saida tayi sallar Isha kana ta fito daga d'akin doguwar Riga ce Mara nauyi sannan ta saka baby hijab ta fito parlor ganin su daddy da gudun ta karasa inda suke ta fad'a jikin Daddy tana fad'in "Daddy sannu sa dawo wa" Ya amsa da "Yauwa Daughter." Dariya sukayi mutumin nan da suke tare da daddy yace "Oh daddyn ki kawai Kika gani baki ganni bako?" "Laaah Abba wallahi ban gan ka ba, ina wuni?" Ta d'an duka ya Masa da "Lafiya su Isha manyan mata kaga yarinyar Nan yanda ta girma" Daddy ya amsa da "Wallahi kuwa kasan girman mace" "girman mace ai kamar Taki ake saka musu, ya school d'in dai dafatan ana kokari?" "Eh daddy Alhamdulillah" "Allah ya taimaka" "Ameen nagode Abba" Wanda ta Kira da Abba ne ya Kara maida kallon sa ga Haisam a karo na sau ba adadi ya maida kallon sa ga daddy yace "Yaya ina ta zuci zucin tambayar ka wane ne wannan?" Murmushi daddy yayi yace "Ai shine yaron da nake baka labarin sa kwanaki" "Ohhhh" girgiza kai yayi alamun ya tuna kana ya d'aura da fad'in "Haisam ko?" Yana kallon Haisam d'in, cikin girmawa Haisam yace "Eh yallab'ai" Murmushin gefen Baki yayi yace "Yallab'ai Kuma Haisam Kuma ka Kira Yaya na da Daddy? Ko Ni ban Kai a kirani da Daddy bane?" Ya karasa maganar a sigar wasa, sosa keya Haisam yayi yace "A'a ba Haka bane" Gyara Zama Abba yayi yace Sunana Abdallah Aminu Tahir, d'aga Malam Tahir Mus'ab wannan da kake gani.... Yana nuna daddy haisam ya kalli daddy kana ya maida kallon sa gare shi,ya d'aura da fad'in "Yaya nane uwa d'aya uba d'aya muke dashi shi ya sha nono ya bar min kaga Kennan Ni Abban Ma'isha ne zanzo ka Kirani da Abba kamar yadda Isha take Kirana" Murmushi Haisam yayi yace "Insha Allah Abba" Daddy Har cikin ransa ya ji daddy, hakan zai tabbatarwa da Haisam ya zama d'an gida. Daddy yace "Daughter jeki ki Kira su Mummyn ku" Mikewa tayi had'e da fad'in to, tana Shiga d'akin da sallama ta Sanar dasu cewar daddy na Kiran su a tare suka fito, gaisawa suka Kuma yi Nan sukayi ta Hira tare yayin da Alhaji Abdallah sai Satan kallon Umma yake ta lura da hakan, hakan yasa duk take jinta wani iri, sai da karfe 11 tayi ya mike da zummar zai tafi daddy da mummy sukayi duk yanda sukayi suka sa ya Kwana. *TSOKACI* ```Shin wane ne Alhaji Mus'ab Aminu??``` Alhaji Mus'ab Aminu d'ane ga Alhaji Tahir Mus'ab da Hajiya Maryam Muhd, Tahir Mus'ab cikekken bafulatanin Gombe ne gaba da baya, shaharen Mai kud'i ne Wanda yayi suna a fad'in Nigeria suna da 'ya 'ya biyu dukka maza Mus'ab Wanda yaci sunan mahaifin sa sai kanin sa Abdallah sun taso cikin gata dukkanin su kuma sunyi karatu ne a kasan waje Sannan dukkanin su Business suka karanta, Bayan Mus'ab ya gama karatu a India ya dawo gida Nigeria, Bayan ya dawo ne ya da Yan kwanaki karayar arziki ya Kama mahaifinsa kasantuwar asarar da yayi zuciyar sa ta buga. Tun daga sannan mahaifiyar su ta kwanta rashin Lafiya yau da lafiya gobe ba lafiya a haka har ta shekara daga bisani ita ma ta rasu, da Taimakon Allah da na Mus'ab ya farfad'o da business d'in mahaifin nasu har ya samu Abdallah ma ya Zama mutum Shima ya fara business d'in. Tare suke koman su har suka samu sukayi aure, a Rana d'aya suka yi aure, Shi Mus'ab Yar Gombe ya samu ya aura Mai suna Maryam, shi Kuma Abdallah a yawon business d'insa ya had'u da fauziya, fauziya bahaushiyar kano ce, Bayan shekara biyu Fauziya ta haifi d'a na miji sai yayi wa Yayan sa Mus'ab takwara, Bayan shekaru uku ta haifi Yan biyu dukka mata wata hassana da Hussaina,daga Nan suka koma Kano da Zama sabida ya cigaba da lura da business d'insu na Kano d'in. Maryam hankalin ta kullum a tashe yake bata da wani buri da ya wuce ta samu ciki, kullum cikin kuka take Mus'ab shine Mai rarrashin ta. Cikin Muryar kuka Tace "Mus'ab Zaka rabu har dani ko? Ko Zaka karo min kishiya" Rungumeta yayi tsam a jikin sa yace "Bani da wacce ta fiki maryam, bazan tab'a miki kishiya ba insha Allah, kullum ina fad'a miki ki daina tada hankalin ki shi fa Haihuwar Nan na Allah ne" "Amma ai ganan Fauziya a Rana d'aya akayi auren mu yanzu yaran ta uku yanzu haka tana d'auke da cikin wata hud'u Ni ko 'batan wata ban tab'a yi ba, sama da shekaru 7" ta karasa maganar cikin kuka. Bubbuga Bayan ta yake yace "Amma ai ba dabarar ta bane Kuma kema ba laifin ki bane, tunda munsha zuwa asibito ci da dama har kasar waje munje duk zancen d'ayane dani dake duk bamu da matsala Kinga Kenan lokacin Haihuwar ne bata Zo ba, ki daina tada hankalin ki mu cigaba da addu'a" *AFTER 10 YEARS* Maryam ta tashi da zazzabi Mai zafi banda amai babu abinda take, cikiin tashin hankali ya kaita asibiti, Likita ya Sanar dashi labari Mai dad'in da ya dad'e yana son ji, farin ciki fal ransa ya Kira Abdallah ya Sanar dashi, dashi da Fauziya sunyi muran matuka, Bayan wata 9 Maryam ta sami yarta, yarinya kyakkyawa kama take sak da ubanta Amma da d'auki hasken fatar Maryam, kasantuwar Mus'ab ba wani haske yake dashi sosai ba. Abdallah najin labarin Haihuwar ya sa suka shirya dashi da matar da yaran sa hud'u , Mus'ab, hassana da Hussaina sai Autan su Faisal, Wanda a lokacin Mus'ab nada shekaru 10, Hassana sa Hussaina 8 years sai Faisal a lokacin bai cika shekaru 4. A Ranar suna Mus'ab ya Sanar musu da yarinya taci sunan mahaifiyar su wato Maryam Amma ana Kiran ta da Ma'isha, tun da sassafe suka shirya suka Kama hanyar Gombe a hanyar su ta zuwa gomben sukayi hatsari,Fauziya da 'ya'yan ta duk 4 suka rasu,yayin da Abdallah ya bugu sosai Yana kwance a asibiti Rai a hannun Allah. ________________________ Please comment and share Milhaat ce Yar Terawa 🍃*DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 31&32 _Continuation........_ Tun daga Nan Abba yake kwance a asibiti, Rai A hannun Allah buguwar da yayi ne ya sa bai farka ba yayi dogon Suma, Satin sa d'aya a kwance. Su Fauziya Kuma da 'ya'yan ta tun a ranar aka kai su makwancin su, bayan ya farfad'o mutuwar tasu ta girgiza shi Kennan, tun daga Nan ya ji baya bukatar aure sabida gudun kar ya sake rasa su, hakan yasa ya bar kasan gaba ki d'aya ya Koma dubai, Yana kula da harkokin su na chan,sai lokaci zuwa lokaci yake zuwa duba su, Nan ma kwanaki biyu zuwa uku kawai yake musu ya koma,wani lokacin Kuma ya kwana hotel. Wannan Kenan. *CIGABAN LABARI* Abba ba don yaso ba ya Kwan,washe gari kuwa Ma'isha Bata sa Lectures a ranar akayi sa'a Haisam ma bayi da shi, a tare sukayi breakfast karfe 10 na safe flight d'in su Abba zai tashi. Bayan sun gama karyawa Abba yace dasu su fito waje akwai abinda zai nuna musu,Bayan sun fitane ya zaro key a aljihun sa ya mikawa Ma'isha, sa hannun tayi ta karb'a had'e da fad'in "Abba ajiye maka zanyi?" Yar karamar dariya yayi yace "A a My Isha,Taki Ce na Saya mikine sabida kokarin sa kike a school" Benz Ce baka sidik sai sheki yake wani uban ihu tayi had'e da salle,da gudu ta rungumi Abba had'e da yi Masa godiya "Abba Thank You Thank you" Shima rungumeta yayi Yana "fad'in mention Not Daughter, ki dai Kara kokari akan Wanda kike yi kinji?" Ta amsa da toh da gudu ta nufi gun Mummy tana nuna Mata,Duk sukayi Masa Godiya, Sannan suka koma cikin,Abba lokacin tafiyan sa ya kusa Amma bai ga Haisam da Umma ba,cike da kulawa yace "Yaya ya Banga sauran mutanen gidan ba?" "Eh suna part d'insu Amma yanzu nasan zasu Shigo" Aiko Yana rufe baki sai ga shigowar Haisam cike da girmawa ya gaidasu Duk suka amsa. Ma'isha da saurin ta Tace "Yaya ka gani Nima an Saya min mota babu ruwana da jiran ka bare ka jaa min ajii" Murmushi yayi yace "Masha Allah , congratulations gaskiya na tayi ki murna" Mikewa tayi Tace "Kazo muje kaga motar" wucewa tayi shi Kuma ya bi Bayan ta mummy girgiza Kai tayi Tace "Alhaji bari na Shiga daga ciki" ya amsa da "Toh." Ya rage daga Abba sai daddy a parlor ,gyaran murya Abba yayi yace "A gaskiya Yaya bazan yi shiru na cuci kaina ba Umman Haisam ta kwanta min a Raina,da fatan zaka bani auren ta?" Yar karamar dariya daddy yace "Ikon Allah daga ganin ta sau d'aya kace min ka kyasa?" "Eh Mana love at first sight kake ji,look Yaya ka daina min dariya Kai da ya kamata kayi farin ciki ma" "Sosai Kam,naji dad'i sama da 20 years kaki aure ai abin a duba ne,Kuma Insha Allah baka da matsala sabida Zainab bata da matsala ko kad'an tana da kirki" Shafa kirjinsa Abba yayi had'e da fad'in "Alhamdulillah abinda nake son ji Kennan tunda ka yabe ta magana ta kare,yanzu dai ya za'ayi?" "kar ka damu zansa Maryam ta Mata magana Insha Allah,Allah dai yasa ta amince" "Amiin ya Allah Ni da kaina zanyi Mata magana ma, Maryam Uwar Maryam" Fitowar Mummy Kennan ta ce "To me Kuma ya Faru naji ana Maryam Uwar Maryam nasan cuta ta za'ayi" Dariya sukayi daddy yace "A'a ba cutar ki za'ayi ba alfarma Zaki Mana ko ince taimako" Zama Mummy tayi Tace "Ahaaaf na sani ai da wala kin goro a miya, nasan ba a banza ba wannan kirarin" Daddy ya Sanar mata da abinda Abba yake bukata, Murmushi tayi Tace "Kai Alhamdulillah finally addu'ar mu zata karb'u, a gaskiya idan ka auri Zainabu zan ji dad'i sosai sabida mutuniyar arziki ce, gata da tsoron Allah, mace Ce ta gari, fatana shine Allah ya Sanya alhairi yasa Kuma ta amince kasan dai baza'a mata Dole ba" Abba yace "Nima ban bukaci hakan ba, in dai Bata so ki kyaleta Amma fa zanzo ki sa mata ra'ayi na gaskiya" "Kar ka damu Insha Allah ma zata amince kaga Shikenan ta Zama ta gida Duk da dama Yan gida ne" Nan sukayi ta hirar su har karfe 9:30 daddy da kansa ya kaisa Airport yaso ganin Umma Kan ya tafi Amma bata fito ba, Ma'isha Kuma da Haisam d'akin Haisam suka nufa suna ta Shan hirar su. Suna cikin hiran ne Tace "Yauwa Yaya Kace Akwai maganar da kake son fad'a min, mene ne?" "Yauwa kin tuna min, ba kince kina so na sama Miki aunty ba?" "Eh hakane" "To burin ki ya kusa ciki" "Ban gane burina ya kusa cika ba? Soyayya ka fara ne?" Murmushi yayi yace "Dad'i na dake kanki naja sosai princess, hakane soyayya nake Kuma ina sonta sosai" Ma'isha jin maganar Nan dai dai yake da kamar wuka aka dab'a Mata a kirjinta ji take d'akin na juya Mata, shiru tayi kana tace "Wace Ce haka Yaya?" Murmushin Jin dad'i yayi yace "Kin santa ai" "Haba dai ya sunan ta?" "Aysha!!! A razane ta Mike Tace "Aysha?" Shima mikewa yayi yace "Eh Aysha lafiya naga kin razana haka?" Ma'isha a ranta ji take kamar ta shake mishi wuya ya Kuma cewa "Princess kuka, meyasa ki kuka?" "Yanzu duk soyayyar da nake maka baka gani, da abun da zaka saka min Kennan? Baka san cewa ina sonka ba, me zakayi da wata Aysha? Dame ta fini? Kiran sunan ta da yayi da d'an karfine yasa ta dawo daga tunanin da take ya Kuma cewa "Princess tell me please what happened, why are you crying?" Cikin Muryar kuka Tace "Yaya ba Kai bane?" "Me nayi princess?" "Har zaka Fara soyayya ba tare da ka fad'a min ba" Dafe Kai yayi ya sauke wani ajiyan zuciya "Na d'auka maganar Farukh zai tabbata ne Ashe ba hakan bane ba?" " Me Farukh d'in yace?" Girgiza kai yayi had'e da Murmushi yace "Nevermind Amma princess Allah ya shirye ki komai kuka komai kuka gaskiya mijin ki zai Sha fama Kam, don wallahi aka Kai Masa ke raino zaiyi" Murmushi tayi "Nikam bari na tafi Kan Abba...... " Ganin agogon dake d'akin yasa Tace "Wayyo karfe 10 da rabi" ta nufi kofa da gudu Haisam yace "Lafiya me ya Faru?" "Abba zai tafi bamuyi sallama ba Kuma idan ya tafi sai yafi 3 years bai dawo ba" Ta fita da gudu, parlor ta nufa, tana Shiga ta tarar da Umma da Mummy a zaune mummy da d'an fad'a fad'a Tace "lafiyan ki Kike Mana gudu a gida haka?" "Mummy Abba da Daddy fa?" "mtsww sun fita" kawai Tace Mata had'e da kawar da kanta. Dafe goshin tayi Tace "Kai Amma naso mu yi sallama wallahi Amma ba komai zan kira shi a waya" tana Kai Nan ta shige d'akin ta, ba ta dad'e ba ta fito ta shirya cikin sutura mai kyau Tace "Mummy zanje gidan su Ameerah" "Aikin Kenan ai bare yanzu kinyi mota" Murmushi tayi Tace "Sai na dawo Umma sai na dawo" Umma Tace "Ai Ni munyi fad'a dake" Kama baki tayi Tace "Na Shiga uku Umma laifin me nayi kiyi hakuri" "Uhmn wai ace a miki babbar kyauta haka Amma baki fad'a min ba" Fad'awa jikin Umma tayi tana fad'in "Kiyo hakuri Umma wallahi d'azu ma da na Shiga da niyaan fad'a miki ne Amma Yaya yasa na manta kiyi hakuri kizo muje kiga motan" "To na sani dai Dole mantawa kikai, kar ki damu kije sai kin dawo ki kaini d'ani" Da murnar ta ta Mike Tace "To Umma sai na dawo d'in" Ficewa tayi tana ganin Haisam hannu kawai ta d'aga Masa ta shige motar ta key ta sa wa motar ta fice abin ta girgiza Kai yayi ya Koma ciki wayar sa ya d'auka yan kirata tana gani taki d'auka a bayyane Tace "Chaap ina driving d'in zan d'aga call d'in ka sai na Isa" Har ya katse Bata d'aga ba text ya tura Mata yace ```"Wato yanzu na Zama 0 a gun ki kinyi mota ba komai nagode"``` Bud'e text d'in tayi ta karanta Murmushi tayi parking tayi ta Masa ```"reply da ba Haka bane Yaya zanje gidan su Meerah ne, Kuma zan dad'e sai na dawo"``` ta ajiye wayar tana Isa gidan su Ameerah ta nuna Mata motar ta ta taya ta murna sosai, sai da suka gama kallon motan kana ta suka koma d'akin ta, wani irin Kallo Ameerah takeyi Mata Wanda yasa har ta Fara tsarguwa Ma'isha kallon kanta tayi Tace "Lafiya me ya Faru kike min Kallo haka?" Cike da kulawa Ameerah Tace "Isha wai ke Dan Allah baza ki cire damuwa a ranki ba? Haka Zaki cigaba da Zama?" Kirkirerren Murmushi tayi Tace "Me Kika gani ni Lafiya na Lau fa" "Haba Isha na sanki fa over 10year you're my best friend ko da baki fad'a min ba na miki sanin da zan iya gane farin ciki da bakin cikin ki, tell me maganar Haisam d'in ne haryanzu?" Ajiyar zuciya tayi sannan Tace "Shine kin San d'azu yake fad'a min wai Ashe soyayya suke da Aysha?" "I said it, ai na fad'a miki ki cire shi a ranki ko Kuma ki fad'a masa Amma kinki and now it's late" "Anya Ameerah kin San soyayya kuwa? Kar ki manta fa shi so halittace ba yin kaina bane wallahi abun ya fi karfi nane" ta karasa magani cikin kuka. Hannu Ameerah tasa a goshin Ma'isha Tace "Akwai zazzab'i a jikin ki" Mikewa tayi ta d'auko BP apparatus kasantuwar ita d'in a school of Nursing take tana final year yanzu, gwada BP d'inta tayi ta Kuma gwada har sau uku zaro Ido tayi Tace "Isha jinin ki ya hau sosai har 200 Inna wa Inna ilaihirraji'un, gaskiya dole in fad'a wa Ya Haisam gaskiyar magana bazan bari ki cutar da kanki" wayar ta d'auka zata Kira shi Ma'isha tayi saurin kwace wayan Tace "Me haka Ameerah me kike Shirin aikatawa haka?" "Ke zan tambaya Isha me kike Shirin aikatawa, zaki ja wa kanki matsala a banza Bayan wannan matsalar idan kina so a Yau d'in Nan za'a yi maganin sa" "kince na cire shi a Raina Insha Allah zan cire shi I just need some time please" Hawaye wani na bin wani haka ya rik'a fita daga cikin idon Ma'isha,ta kalli Ameerah ta rik'e hannunta tace "Please Dear ki taimaka min dan Allah karki fad'a,baki san irin son in da yaya yake ma Aysha ba ,haka itama wallahi suna son junansu bani son lalata masu farin ciki muna k'aunar junanmu ni da d'an uwana" Haushi yasa Ameerah ta fara magana cikin fad'a "oh kenan kin fiso ki mutu?kina so mu rasa ki kenan?shin keda Aysha wa ya fara son yaya Haisam? tun kafin ya dawo gidan ku a school baki da wata magana sai tashi shin idan ba'a fito fili an fad'a masa gaskiya ba ya kike so muyi?kina so ki dawwama cikin damuwa Kenan?" Kukanta a yanzu ya fito fili ta saka hannayenta ta rufe fuskarta tace "alkawari kika d'auka Meerah karki manta girman alkawari da mahimmancin sa ki rufa min asiri"dan Allah karki fad'awa kowa" Itama Meerah kuka ta fara, ta jingina kanta a kafad'ar Ma'isha ta cigaba da fad'in "karki damu da duk halin da nake ciki ni dai fatana karki fad'awa kowa kamar yadda kikayi alk'awari" "Shikenan Insha Allah bazan karya alkawarin da na d'auka ba Amma kema kimin alkawarin Zaki cire shi a ranki" "Insha Allah." "Hajiya wai kina nufin Kanin Alhaji ne wannan ko da yake na d'an ga kama Kam" "Eh kanin sane uwa d'aya uba d'aya....... " Nan fa Fara bata labarin sa da halin da ya Shiga girgiza kai Umma tayi Tace "Allah sarki na tausaya mishi, wato Duk halin da ka Shiga a Rayuwa idan Ka ga na wani sai ka Raina naka" Mummy tace "Wannan hakane" riko hannun Umma mummy tayi Tace "Please Zainab ki taimake mu ki maye Masa gurbin abinda ya rasa" Cikin rashin fahimta take kallon ta, "ban gane na maye Masa gurbin abinda ya rasa ba?" Nan mummy ta kwararo mata bayanin yanda sukayi da Abba a razane ta Mike tace "Gaskiya bazaiyu ba, bani ba aure kice Masa bana son sa ban amince ba, Kai baza ma na tab'a son sa" Mummy mikewa tayi ta fara Mata magiya, hakan yayi dai dai da Shigowar Daddy a tsawace yace "Maryam!!! Ba Mummy ba har ita Umman ta tsorata , sai da ta maso inda suke, sai Kuma yayi kasa da murya yace "Ba haka mukayi dake ba Akan me Zaki matsa mata Tace Bata so then let her be" sai ya wuce d'akinsa, Haisam kuwa Jin Muryar daddy ya Shigo da gudu, karaf maganar da daddy yayi ya sauka kunnen sa. Mummy cikin kuka Tace "Haba Zainab yanzu da abinda Zaki saka Mana Kenan" ta juya tabi bayan daddy. __________________________ Alhamdulillah naga yanzu ana comments ba laifi Amma fa ina Kan baka na, na removing Insha Allah Kuma zanyi. Nanarh Ummu Ziyad Ayusher Da sauran masu comments bazan iya irgu sunayen ku duka ba, nagode sosai inajin dad'in comments d'inku musamman Nanarh Allah ya bar Kauna. Please comment And share Milhaat ce Yar Terawa _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki

Chapter 8 of 24