Haisam a tare suke zuwa school Kuma su dawo a tare, sun shaku sosai haka ma mummy da Umma kusan komai tare suke, sannan daddy yana iya bakin kokarin sa wurin ganin ya cika alkwarin da ya d'auka wa Haisam, duk abunda yake so yanayi masa, a hakan har suka rubuta WAEC and NECO d'in su Kuma Alhamdulillah paper su duk yayi kyau.
Daddy yayie matukar farin ciki hakan yasa bai 'bata lokaci ba wurin yi musu registration na JAMB ba,Kuma Alhamdulillah sun ci yanda a ke bukata duk su biyun a gombe state University sukayi(GSU) applying,suna zaman jiran admission.
Da gudu ta shigo ta murna had'e da tsalle tana Kiran sunan Daddy da Mummy, Mummy dake kitchen ita da Umma cikin Sauri suka fito a tare sukace "Lafiya? Me ya faru?"
Tambayar su yayi dai dai da lokacin da Daddy ya fito cikin Sauri daga d'akin sa, yace "Ma'isha me ya faru?"
Sai tsalle take Haisam kusa hard'e hannu yayi Yana kallon ta, Umma Tace "Kai kunci gidan ku ana muku magana baza ku amsa ba?"
Da gudu ta rungumi Umma tace "Admission ya fito kuma duk mun samu"
Girgiza kai daddy yayi yace "Dad'i na dake ba a raba ki da shirme wallahi, shiyasa Kike Mana ihu a cikin gida?"
" Daddy ai Dole ni da Yayana mun samu admission a department d'in da muke so"
Umma Tace "Masha Allah, kice yanzu muna da Doctor da Kuma pharmacists a gida"
Ta amsa da "Insha Allah"
Mummy maida kallon ta tayo ga Haisam cike da kulawa Tace "Son ya naga Kai baka tsallen? Ko bakaji dad'in admission d'in bane?"
"a'a mummy kawaiiii...... "
Daddy ne ya katse shi yace "Toke Banda abunki hajiya Ma'isha tayi Shima yayi ya za a banbanta yaro da babba"
Duk dariya sukayi, ya d'aura da fad'in "Allah ya taimaka, Haisam yaushe zaku karb'o admission d'in"
" Ai daddy mun karb'o"
"Sharp sharp Kenan, anyways congratulations to you both"
A tare Ma'isha da Haisam suka amsa da "Thank you daddy."
"Emmm yanzu abunda za'ayi ku biyuni sai muyi maganar kud'in registration d'in don Ina so a Fara Lectures daku" ya wuce d'akin sa su biyun suka bi bayan sa mummy da Umma Kuma suka koma kitchen.
Daddy ya Basu dukkanin kud'in da suke bukata,washe gari a tare sukaje sukayi registration tun safe suka fita basu dawo har sai dab da magrib a gajiye suka dawo,hakan yasa dawuri sukayi bacci.
Bayan sun gama registration,suka Fara Lectures d'insu yanda ya kamata.
Daddy na gani zaune a office, kwankwasa kofar da akayi ne yasa ya d'ago kansa yace "Come in" sannan ya cigaba da rubuce rubucen da yake, Jin an shigo ya d'ago kansa don ganin Wanda ya shigo Murmushi yayi yace "Bismillah zauna"
Ba musu mutumin ya zauna, hannu ya Mika Masa suka gaisa, mutumin ne ya ce "naji Labari kaje gida har Sau Uku baka sameni ba, gashi kuma ban Sanka ba"
"eh hakane kamar yanda nace maka a waya wata magana nake so muyi da Kai Mai muhimmanci, shiyasa ma kaga na takura kazo office Dina"
Murmushi yayi ya gyara Zama yace "Business ne Kennan, kasan na dad'e ina so na fara business da company ku Amma Allah baiyi ba"
Daddy yace "Malam Hassan zamu Zo Nan d'in ma Amma kamun Nan....."
Wayarsa ya zaro a aljihun gaban rigar sa gallery ya shiga ya Mika Masa wayan yace "ko Kasan wannan?"
Karb'an wayan yayi ya dad'e Yana kallon sa, a zuciyar sa yace "Wannan kamar Haisam, Kai ba shi bane ya akayi ya Zama Haka maybe kamane"
A bayyane Kuma yace "Yallab'ai ban sanshi ba Gaskiya" ya Mika Masa wayan, Kan wani hoto ya koma ya Kuma Mika Masa wayan yace "Wannnar fa da fatan ka gane ta?" Yana karb'an wayan yana ganin Hoton a raza ya Mike hannun sa rawa yace "Zainab, wannan kamar Zainab dama tana raye ne, Zainab ce fa matar Yayana ko? Ko dai Kama ne ya naga ta canza?"
_______________________
Please share and comments
Milhat ce
Yar Terawa
🍃 *DANGIN UBANA*🍃
Story & Written
By
Milhaart
Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne.
*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________
*Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.*
Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
Page
11 and 12
Daddy Shima mikewa yayi yace "hakan na nufin ka santa Kenan?"
Malam Hassan Sai kallon sa yake ya kasa cewa komai, girgiza Kai daddy yace "calm down, calm down ka zauna"
Jiki a sanyaye ya zauna Idon sa akan hoton Sai zare Ido yake Yana kallon Hoton, daddy yace "Na dad'e ina neman ka tsoratan da kayi hakan ya tabbatar min da maganar da Zainab ta fad'a min Akan ka gaskiya ce"
Murya na rawa yace "me me me ta taa fad'a maka? Kar ka yarda da ita makaryaciya ce"
"Give a good reason da zan gano cewar makaryaciya ce"
"Ashe dama tana raye ni na d'auka ta mutu"
Maganar da yake ta maimaitawa Kenan.
Daddy yace "Bata mutu ba,ko ince Basu mutu ba,Ashe dama Kaine Wanda yasa aka Kona musu gida ina da labarin gidan ya Kama da wuta nayi iya tunanin Duniyar Nan ya akayi wuta ya Kama,ashe Kaine?"
Mika Masa wayan yayi ya Mike,ba tare da ya bashi amsar Tambayar da ya Masa ba,har ya Kai bakin kofa Daddy yace "Ka dawo musu da dukiyan su ko Kuma mu had'u a kotu,kuma idan kace zaka bar gari wallahi tallahi duk inda ka shiga a fad'in Duniyar Nan zan Nemo ka"
Waigowa yayi, yayi tsaki yace "To hell with you mu had'u a kotun" Sai ya fice, motar sa ya shiga duk hankalin sa a tashe Sai zufa yake ta goge wa da hannun sa, farar shaddan da ke jikinsa duk ya jike, Kai tsaye gidan sa ya nufa, yana parking d'akinsa ya shiga matar sa na ganin sa ta gane ba lafiya don ko sallama baiyi ba ya shige.
Cikin sauri tabi bayan sa tarar dashi tayi a d'aki yana kaiwa Yana kawo wa, cikin nuna kulawa da damuwa Tace "Malam lafiya me ya Faru na ganka haka sai safa da marwa kake?"
Murya na rawa yace "Rabi akwai matsala, akwai matsala wallahi"
"Malam zauna ka fad'a min me ke faruwa?"
"Zama? Ai banga ta Zama ba, ina naga ta Zama bayan asirina yana kokarin tonuwa?"
"Asirin ka? Ban fahimta ba Malam me kake nufi da hakan?"
"Ashe dama Munafukar matar Nan tana raye? Ashe bata mutu ba ita da d'anta?"
Cikin rashin fahimta take kallon sa, yace "Dad'i na dake kanki baya ja wallahi ko kad'an Zainabu nake nufi Zainabu na Raye ita da d'anta"
Dafe kirjin ta tayi Tace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, suna raye Malam? Amma ya akayi ka sani, na d'auka kasa an Kona inda suke?"
"eh ni da ido na, na gani to Amma abinda ya d'aure min Kai hakan na nufin fa basu cikin d'akin don Babu yanda za a yi su tsira gas fa nasa aka sa hatta Wanda yasa wutan ya mutu da idona na gani fa"
"ka gani ko Malam tun wanchan lokacin na Hanaka Amma kaki ji, yanzu gashi wa gari ya waya"
"Rabi yanzu fa ba lokacin wannan bane..... " Nan ya sanar Mata yanda sukayi da Daddy, Rabi Tace "Malam ka maida musu dukiyar su, ai yanzu ka samu fiye da abinda ka samu agun su, idan ka bari ya kaika kotu duk abunda ka Tara za a Basu"
"inaaa bazaiyu ba kin San tsawon shekaru nawa na yi ina tara kud'aden Nan kuwa?"
" Ni kuwa na sani malam, ko dai barin garin zamuyi ne Kam?"
"ai cewa yayi ko na bar gari Sai ya Nemo Ni"
"Nikam wane ne haka? Da yake kokarin tozartamu?"
"chairman ne fa Mus'ab Aminu"
Zaro Ido tayi Tace "Eh lallai malam baka nemi zaman lafiya ba wallahi in dai baza ka maida musu ba, kasan mutumin Nan yanda yake da taimakon al'uma baya bari a cutar da kowa"
"Na San da hakan, dole zan nemi mafita amm....."
Kwankwasa kofar da akayi ne ya katse maganar da yake niyar yi.
Cikin tsawa yace "Waye anan nace Waye ne?"
Cikin sanyin murya Tace "Daddy wani mutumine ya kawo sako yace a baka"
Rabi Tace "Shigo"
Tana Mika Mata ta fita, Yana bud'ewa yaga tsammaci daga kotu kallon paper da yake ne yasa ta karb'a don ta gani girgiza Kai tayi Tace "lallai malam mutumin Nan dagaske yake, ranae Monday fa zaku shiga kotun"
Tashi yayi ya fice ba tare da yace Mata uffan ba, ya shiga motar sa kenan ya hango Yan sanda guda biyu, jiki na rawa ya fito Yana kallon su, bayan sun gaisa 'daya daga cikinsu yace "Kaine Malam Hassan Umar?"
Murya na rawa yace "Eh eh nine"
ID card d'insu suka zaro suka nuna masa, "Yan sanda ne an turo mu da warrant arrest d'inka"
"Ni Ni kuma, me me Kuma nayi?"
"Idan mukaje office zakaji koma mene ne"
Nan take suka zaro handcuffs suna kokarin Sanya Masa a hannun sa, cikin tashin hankali yake Kiran sunan ta "Rabi !! Rabi!!! Da gudu ta fito ita da 'ya'yan ta guda uku, Yaran na kuka rabi ma na kuka, har suka fice dashi suka sashi a mota.
Suna zuwa police station suka tarar da Daddy, mummy, Umma, Ma'isha da Haisam duk suna zaune, cike da mamaki yake kallon su, hannu Daddy ya d'aga musu hannu, gani nayi sun cire Masa handcuffs din.
Mikewa daddy yayi yace "Malam Hassan tun wuri ka taimaki kanka ka maida musu dukiyan su yanzu zan sa a sake ka idan Kuma kaki wallahi wallahi sai ka Raina kanka"
Kallon Umma yayi yace "Zainabu kina jin abinda yake fad'a ko? Ki fad'a Masa gaskiya cewar dukiyar Nan Yaya nane ya bani"
Umma fashewa tayi da kuka ta fice daga gun, mummy, Ma'isha da Haisam suka bi bayanta.
Daddy ciza le'be yayi yace "Na lura kana da taurin kai, Amma kar ka damu...." Maida kallon sa yayi ga police d'in dake gefen sa yace "A kulle shi Kuma ban yarda a yi bailing sa ba, sannan kar a bari kowa yazo ganin sa ko da kuwa matarsa ce" Yana Kai Nan ya fice.
Tarar dasu yayi a jikin mota Umma na kuka mummy na rarrashin sa, a yayin da Haisam ji yake kamar yaje ya shake baffan sa ya mutu ko zaiji sanyin abinda ke damin sa.
Daddy yace "Ki daina kuka insha Allah komai zai wuce"
"Alhaji dole nayi kaji abinda yake cewa fa, shi ya kashe min miji ya kwace dukiyar sa,sannan nima ya so kashe ni da d'ana Amma yana rayuwar sa hankali kwance"
Mummy Tace "Kar ki damu ranar Monday komai zaizo karshe insha Allah, ke dai kawai ki fad'i duk abinda kika sani shine kad'ai zai sa a mishi hukunci dai dai da abinda ya aikata"
Haisam yace "Amma mummy bamu da wani hujja, kinsan komai sai da evidence karshe ma a nemi a karyata mu"
Daddy yace "matsala d'aya zamu samu shine evidence d'in da shi ya kashe shi Amma duk sauran zaizo Mana da sauki insha Allah, ku shiga mota mu tafi" mikawa Haisam key d'in motar akan ya jaa su, karb'a yayi duk suka shige, Kai tsaye gida suka nufo.
Zaune suke a parlor,duk jikin su a sanyaye yake ganin kukan da Umma take yake ci yaki cinyewa Mummy Tace "Kukan na mene ne haka ya Isa Dan Allah"
Cikin shesshekar kuka Tace "Wallahi ina ganin sa hankali yayi mugun tashi, tsayuwar da yayi a gabana sai naga kamar Ahmad ne Kai hatta muryar sa ma irin ta Ahmad ce, Hassan ya cuce ni bazan tab'a yafe Masa ba" ta karasa maganar tana kuka, Haisam Tashi yayi ya fice, Kai Tsaye d'akinsa ya nufa da gudu Ma'isha ta bi bayan sa.
Daddy girgiza Kai yayi yace "Allah ya kyauta" ya nad'e garen sa ya shige d'akinsa.
Ma'isha har cikin d'akin ta bishi, ya zauna a baki gado ya had'a Kai da gwiwa kuka yake sosai Mai sauti, Zama tayi a gefen sa baiji shigowar ta ba sai muryarta da yaji Tace "Ya Haisam."
'daga kansa yayi a hankali ya sauke idanunsa akan ta, kirkirerren Murmushi yayi, wata farar kyalle ta Mika Masa Murmushi ya Kuma yi yasa hannu ya karb'a ya share hawayen sa, bayan ya gama ya Mika Mata yace "Thank you"
Murmushi kawai tayi tace "Ya Haisam kuka fa ba naka bane, addu'a ya kamata muyi Allah ya d'aura mu a Kan sa"
" Ma'isha ba kukan dukiyar nake ba ko wani abu ba a'a ganin Umma ta a cikin irin wannan halin shi yake tada min hankali ko kad'an bana son zubar hawayen ta, ba sanin mahaifina nayi ba shiyasa bana jin kewar sa duk da cewar na San na rasa gata na Amma Umma itace uwata itace ubana bazan juri ganin ta a haka ba"
"I know how you feel insha Allah komai zai dai daita"
"Allah yasa."
"Ameen"
Ma'isha sai surutu take Haisam kuwa sai aikin kallon ta yake tun baya kulata har ya Fara kulata suka Sha Hira sosai, a yayin da Mummy na chan tana rarrashin ummu, wannan Kenan.
RANAR LAHADI
Daddy na zaune a garden Yana karanta jarida, yayin da Haisam da Ma'isha na daga gefe suna Shan hirar su, mummy ce ta fito cikin Sauri ta miko Masa waya tace "Tun d'azu ake ta kiran ka da sabon number"
Karba yayi ya Kara a kunnen sa banji me akace ba ya Mike yace "okay gani Nan zuwa"
Mummy Tace "Ina Kuma zakaje?"
Bai Bata amsa ba yace "Haisam maza d'auko makullin mota akwai inda zamuje"
Da gudu Haisam ya shiga d'akin Daddy ya d'auko makullin motar ya shiga ya tada motar, Mummy Tace "Alhaji lafiya?"
"Lafiya Lau police station zamuje kar ki fad'a wa Zainab sai mun dawo" ya shige motar suka fice daga gidan, mummy da Ma'isha suka kalli Juna, Mummy tab'e Baki tayi Tace "Allah ya kyauta.
________________________
Watan March 2022 ya kasance wata mara Dad'i a gare ni a cikin sati biyu na rasa mutane na kusa dani.
Kakata ta rasu washe gari kanwar mahaifina ta rasu, basu cika sati ba cousin brother na da abokanan sa guda uku sukayi hatsari duk su ukun suka rasu, shiyasa duk na kasa typing naso ace kamun Ramadan na gama littafin Nan Amma kana naka Allah na nashi, dole zan dakatar da Rubutun sai bayan sallah insha Allah, Dan Allah kusa Yan uwana a addu'a, Allah ya jikan Musulmai idan tamu tazo yasa mu cika da imani ameen.
Please comment and share
Milhat ce
Yar Terawa
🍃 *DANGIN UBANA*🍃
Story & Written
By
Milhaart
Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne.
*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*
```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻```
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________
*Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.*
Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
Page
13 and 14
Da gudu Haisam ya shiga d'akin Daddy ya d'auko makullin motar ya shiga ya tada motar, Mummy Tace "Alhaji lafiya?"
"Lafiya Lau police station zamuje kar ki fad'a wa Zainab sai mun dawo" ya shige motar suka fice daga gidan, mummy da Ma'isha suka kalli Juna, Mummy tab'e Baki tayi Tace "Allah ya kyauta." Ta shige cikin gida.
Basu zarce ko Ina ba Sai police station,bayan sun shiga ciki Kai tsaye office din DPO suka shiga bakin su d'auke da sallama,ga mamakin su suka tarar da Baffan Haisam a zaune a cikin office d'in,DPO ya nuna was daddy kujerar dake gaban sa yace "bismillah yallab'ai"
Ba musu ya nemi wuri ya zauna,bayan sun gaisa DPO yace "Nasan kayi mamakin Kiran ka da nayie ko?"
Ya amsa da "Eh sosai ma"
Gyaran murya DPO yayi yace "Dama malam Hassan ne ya bakaci ganin ka shiyasa ma na Kira ka"
Daddy maida kallon sa yayi ga Malam Hassan yace "Ina sauraron ka"
Malam Hassan yace "Na yanke shawara ne zan maida musu da dukiyar su" a gadarance.
Girgiza Kai kawai daddy yayi yace "Ni Kuma ban amince da hakan ba, a lokacin da nake ta bibiyar ka da ka dawo da duk abinda ka San nasu ne Amma kamin kunnen uwar shegu, maganar kotu Kuma bazan janye ba Sai munje"
Malam Hassan yace "A lokacin da kace na bayar banji zan iya bane ba Amma a yanzu na shirya" Daddy ransa yayi mugun 'baci sabida ganin yanda malam Hassan yake magana a gadarance, mikewa yayi yace "Haisam tashi mu wuce gida" ya nufi kofar fita, DPO yace "Yallab'ai Dan Allah ka tsaya" waigowa yayi yace "Na tsaya nayi me da na San sabida Shirmen Nan ka kirani wallahi da banzo ba"
"Hakane yallab'ai dole ranka ya 'baci Nima cemin yayi zakuyi Sulhu shiyasa na Kira ka" ya maida kallon sa ga Malam Hassan yace "Malam Hassan ba haka mukayi dakai ba, Ce min kayi zaka nemi gafarar su kuyi Sulhu Amma ya za'ayi Kai da kake Neman Abu daga gare su kana musu magana a gadarance? Ka bashi hakuri ka fahimci juna don wallahi idan ka bari kuka shiga kotu da dukiyar d'an uwan ka da naka duk za a had'a a karb'a, Amma fa ba tilasta maka nake ba shawarace idan kaso ka d'auka"
Malam Hassan Jin za'a raba shi da komai da komai ya Fara wiiki wiki da ido Nan take zufa ya Fara keto Masa duk da AC dake cikin office d'in, Chan ciki yace "Alhaji kayi hakuri Dan Allah" ya maida kallon sa ga Haisam yace yace "Dan Allah kasa baki Haisam"
Haisam dake tsaye Yana kallon su yace "Daddy mu saurare shi a gama abin Nan once and for all ko ba komai hankalin Umma zai kwanta"
Ajiyar zuciya daddy yayi ya koma ya zauna yace " Shikenan DPO wani formalities za a bi don a tabbatar da zai bada komai da komai don wallahi I don't trust him ko kad'an"
"Kar ka damu yallab'ai zan kula da komai, Na maka alkawari Nan da 2 days zan kammala komai,amma zamu ciga ba da ajiye anan d'in ne ko Kuma mu sake shi?"
" A a no need ai Ku sake shi" ya maida kallon ga Malam Hassan dake zaune a kasa ya nuna sa da manuniya yace "Mind you if try acting smart with me I'll deal with you and make your life miserable" Yana Kai Nan ya fice Haisam ya bi bayan sa, tunda suka shiga mota babu Wanda ya sake cewa komai har suka Isa gida.
Horn Haisam yayi Mai gadi yayi saurin bud'e musu kofa, parking lot ya nufa yayi parking motar, Mummy , Umma da Ma'isha na zaune a garden d'in gidan suna jiran dawowar su, daddy d'akin sa ya wuce abinsa suna mishi sannu da zuwa ko kallon su beyi ba bare ya amsa.
Haisam kuwa inda suke ya nufa ya nemi wuri ya zaunan, Mummy Tace "Son lafiya me ya Faru ne haka na ga ran Alhaji a 'bace?" Gyara Zama Haisam yayi ya fara jero musu yanda sukayi a police station, tunda ya fara magana suke kallon sa har ya Gama Babu Wanda yace komai, Mummy girgiza kai tayi ta tashi ta shige cikin gida, d'akin Daddy ta shiga taje tana ta aikin rarrashi.
Ma'isha ganin Umma ta shiga cikin damuwa Ta d'an dafe kafad'arta tace "Umma wannan ba abin damuwa bane ba, tunda shi da kansa yayi ra'ayin zai dawo da dukiyoyin ai farin ciki ya kamata muyi, matsalar kawai gani nake bazai dawo dasu duka bane"
Umma Tace "uhmm yaro yarone baza ki tab'a ganin abinda nake hangowa ba"
Haisam yace "Umma Me hakan yake nufi, kina nufin akwai wata matsalane idan akayi hakan?"
"babba ma kuwa Haisam, Baffan ka mutum ne Mai had'ari ni dukiyar Nan wallahi bataw dame ni ba , dama don kai ne nake so a karb'a maka hakkin ka, ina ji ajikina akwai abinda yake Shirin aikatawa"
Ma'isha Tace "Insha Allah babu ma abin da zai faru Umma, aniyar shi ya bishi"
Ta amsa da "Amin Allah ya shiga tsakanin mugu da na gari" duk suka amsa da Amin.Nan dai Haisam da Ma'isha sukayi ta kokarin jaan ta da Hira tun bata kulasu har aka fara hirar da ita.
"Ka gani ko malam ai tun farko Haka nace maka kayi Amma kayi kunnen uwar shegu da ma baza a kai Nan ba"
"Kinga Rabi ni bana son Mai maita magana, Allah ya kaddara hakan Sai ya Faru in ma maganar kulleni da akayi ne ai ba yau na fara shiga cikin cell ba so Dan Allah ki kyaleni naji da abinda yake damina ko Kuma na sauke 'bacin ran a Kan ki"
Rabi na jin hakan ta shi ta fice daga d'akin ba tare da tace komai ba, binta yayi da kallo ya ja wani dogon tsaki.
'dakinta ta nufa tana Zama Kenan taji an turo kofa, kallon kofar tayi ganin irin kallon da take mata tayi kirkirerren Murmushi Tace "Ayra Shigo ciki mana"
Wacce aka Kira da Ayra naga ta Shigo ta zauna a bakin gadon dake d'akin Tace "Mamy wai Dan Allah me ke faruwane, naga duk kina cikin tashin hankali, nasan hakan bazai rasa nasaba da Abinda ya faru da daddy bane ba, Dan Allah me daddy yayi har aka Kama shi"
"Babu komai Ayra, ai daddyn naku ma ya dawo komai ya Riga ya wuce kar ki tashi hankalin ki"
"Amma Kuma Mamy ke naki hankalin ai a tashe yake just in 2 days ki duba Kika yanda Kika rame Kika lalace"
"Ayra kin San fa bana son ina magana Kuma kema kina yi sabida haka ko ki bar maganar Nan ko ki fice min daga d'aki bana son Shir........"
"Me yasa baza ki fad'a mata ba, ai Ayra ba karamar yarinya bace ba, ta girma ya kamata ta San halin da ake ciki tunda baza ki iya sanar da ita ba Ni zan fad'a Mata"
Wuri ya samu ya zauna, yace " Ayra" ta amsa da "Na'am Daddy"
"Kin tuna cousin brother d'inki Haisam?"
"Eh daddy d'an Uncle Ahmad"
"Good"
Nan ya shiga jero mata abubuwan da ya Faru shekarun baya kamo yanzu, Murmushin gefen baki tayi tace "Daddy wai dama suna Raye na d'aukan sun mutu fa"
"Suna Nan a Raye"
"To shi Alhaji Mus'ab d'in me had'in shi dasu da yake son taimakon su kalen dangi kawai"
Mamy Tace "Na Allah Kenan ba, tun ba yau ba nake nuna wa mahaifin ki abinda yake ba dai dai bane ba, Yana ciyar damu da haram, sanan yana tufatar da mu da haram"
"Haba Mamy so kike daddy ya kashe kansa da wanne zaiji? Ni daddy dama mu gudu mu bar kasan wallahi"
Mamy yarfa hannu ta shigayi tayi tana sallalalami ta ce " Ayra Ashe baki da hankali ban sani ba? Kina nufin goyon bayan mahaifin ki zakiya bayan Kin San abubuwan da yake yi haramun ne, dukiyan maraya fa yake ci, nasan kinyi karatu kinsan kudin da mahaifin ki yake ci wutane Amma wallahi kin bani Mama....... "
"Ke ke ke, me haka nace me haka? "
Mikewa yayi ya nufe ta yace "So Kika kisa mata tsanata a ranta ko me kike nufi, wannan wani irin mumunar hud'uba kike Mata haka"
"Amma malam kasan....."
" Amma me, nace Amma me wallahi tallahi Rabi zan sab'a miki akan wannanw maganar wallahi daf kike da rasa auren ki"
Mikewa itama tayi Tace " In rasa Mana ai auren Nan da shi da Babu duk d'aya"
Cike da mamaki yace "Oh haka ma Kika ce ko?"
"Eh Haka nace"
"toh Shikenan kije ki na sak....."
Ayra Tace "A'a daddy kayi hakuri Dan Allah, kar ka aikata, Dan Allah kar ka saki mamy" ta karasa maganar tana kuka.
Tsaki yayi yace "Kinci Albarkacin Ayra, Allah ya miki Albarka Ayra"
Ta amsa da amiin, yace "Naji dad'in maganganun ki hakan ne yake kara tabbatar min da cewar bazan wahala wurin d'aukar fansan da nake sonyi ba, Akwai aikin da nake so kimin,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 24