duk abinda yake fad'a gaskiyane, na kasa Mai son zuciya da son Kai, ban damu da kowa ba, ban damu da komai ba in dai zan samu abin da nake so...... " Ajiyar zuciya yayi Mai d'an tsawo kana yace "Na cutar dake da ke da 'ya'yan mu, ban kasance miji na gari ba sannan ni ba Uba na gari bane da ko wani yaro yake fatan samu, ki yafe min Abu, Dan Allah"
Cikin muryar kuka Tace "Na yafe maka mallam, dama ban rike ka a Raina ba irin wannan ranar na ke jira Wanda zaka gane koren ka kuma kayi Dana sani , Alhamdulillah Allah nagode maka" ta karasa maganar tana kallon sling na d'akin tana matsar kwalla.
Faisal da dawowar sa Kenan ya manta wayar sa , yaji dukkanin maganar da suke Yar karama tsaki yayi a zuciyar sa yace "Yanzun ma tuban muzuru ne don dama halin sane" kofar ya bud'e ba tare da yayi sallama ba ya sa kai ya shige,Mamy da Malam Hassan duk suka kalle shi,kawar da kansa yayi kamar baiga kowa a gun ba, ya nufi inda wayarsa take ya sa hannu ya d'auka sannan ya fice, girgiza Kai many tayi a zuciyar ta Tace "Allah ka shirya min yaran Nan" kwasam Ayrah ta Fad'o mata a rai mikewa tayi ta fice ta samu d'an corridor ta zauna tana kuka mai cin Rai, tana Jin zuciyar tana mata zafi,tana addu'ar Allah ya bayyana mata Yar ta,ko da kuwa gawar tane,sai da tayi mai isarta kana ta koma ciki.
Soyyaya ce Mai karfi ta Shiga tsakanin Abdallah da Mardiya musamman ma Mardiya da take ji baza ta iya Rayuwa babu shi ba, don ta shaku dashi.
Adnan na bawa Ayrah duk wata kulawar da miji ke bawa matar sa, tasan tana son Adnan Amma da zaran ta bar gidan dole ne ma ya sake ta taya ma Za'ayi ka 'boye Mutum har na tsawon watanni 8?
Mardiya da Abdallah na hango a wani d'an madaidaicin shopping complex , Hirar su suke suna d'aukan abinda suke so kana ganin su kasan masoyan Nan suna suna cikin farin ciki, Bayan sun gama suka nufi inda zasu biya kudi, Mika mata wayan sa yayi Sabida ya samu damar ciro wallet d'insa.
Tana rike da wayar a hannun ta yayin da take Danna wayarta da d'ayan hannun ganin ana ta Kiran sa Tace "Baby ana ta Kiran ka fa" a Shagwab'ance tayi maganar ba tare da ya kalle ta ba yace "wane ne?"
"Adnan"
"Bari in na gama zan kira sa"
"Okay"
A dai dai nan ya gama dasu suka nufi hanyar fita,Yana gaba tana biye dashi,booth ya bud'e ya sa kayan dake hannun sa.
Mardiya na tsaye tana kallon sa ji take kamar ta sace shi,Jin Shigowar message yasa ta kalli fuskar wayar nasan,zaro Ido tayi ta bude sakon, kasantuwar wayar ba Key, sai da ta gama karanta sakon tayi saurin fita a ciki,tayi kokari dai dai ta kanta.
Sau biyu yana Kiran sunan ta Bata ji ba,a d'an razane ta amsa da ya Kira sunanta a karo na uku,cike da kulawa yace "Lafiyan ki kuwa?"
Turo baki tayi Tace "Bana jin dad'ine"
"Ban gane ba yanzun Nan fa lafiyar ki kalau"
"Uhmn Nikam ka maidani gida"
"Kin fasa cin kifin ne?"
"Eh na fasa ka maidani gida" ta karasa maganar kamar zatayi kuka.
"Ikon Allah,to Shiga muje"
Had'e da bud'e mata marfin motar ta Shiga ta zauna,ganin ya zaga tayi saurin ciro karamar wayarta a jaka ta wurga a Bayan mota, ta yi saurin gyara Zama kana ganinta kaga Mara gaskiya.
Kallon ta kawai yayi ya girgiza Kai kana yace "Baby na Mai abun mamaki"
Murmushi kawai ta masa,suna Isa gida Bata Tsaya Hira dashi kamar yanda ta saba ba, ajiye masa wayarsa tayi,tayi saurin fita,bai Ankara ba har ta isa gate,da d'an karfi yace "Kin manta ledan naki"
"Au Na manta" ta dawo da d'an saurin ta karba had'e da fad'in "Thank you bye" ta shige gida da sauri,ya d'anyi Jim yana tunanin canzawan ta, kafad'ar Sa ya d'aga kana ya Shiga,Yana tada motar ya bar wajen,hannun ya sa d'auki wayar sa ya Shiga dialling number Adnan.
Da sauri ta Shiga cikin gida bata ma lura da Haisam da ke zaune a parlor ba ,shi Kuma tab'e baki yayi ya girgiza Kai ya cigaba da danna wayarsa,tana Shiga d'akin ta yatsar da ledojin da jakar dake hannun ta kana ta cire gyallen dake Jikin ta,Zama tayi a bakin gado kana ta Kara wayar ta a kunnen ta.
Ta dad'e a haka kana Naga ta miki zumbur ta d'auki jakar ta da mayafinta ta yafa ta fita da sauri, Haisam da Ma'isha ta hango Amma tayi kamar bata gansu ba tayi ficewar ta da sauri had'e da d'an gudu.
Ma'isha Tace "Ita kuma wannan fa?"
Hararar ta yayi kana yace " miko mini takalmin ki na rike miki Naga Alama sun miki nauyine sai kije ki tambayeta" dariya kawai tayi.
Mardiya kuwa motarta ta fad'a tun Kan ta Isa gate take Masa horn, da sauri ya bud'e don ya razana sosai, tana fita daga gidan ta Kara gudun motar.
Su Mardiya ko ina za'a je, me take Shirin aikatawa oho?
________________________
Kumin afuwa mun koma school shiyasa kuka jini shiru, Amma Alhamdulillah yau muka Gama exam.
Please comment and share.
Milhaat Ce
Yar Terawa.
79&80
Continuation..............'''
"Yane abokina"
"Dallah Malam ina ka ajiye wayar Kane ina ta Kiran ka Amma baka d'aga ba, Ina ka Shiga ne?"
" Afwan mun fita da baby ne ya ake cikine? "
" Baka ga sakon da na tura maka ba"
"A a ban gani ba Wallahi, dake wayar bata hannu na"
Waro Ido yayi yace "Ban Gane ba Abdallah a hannun wa wayar take?"
"Mardiya ce fa ta rike min wayar ne"
"Innalillahi Shikenan asiri na ya tonu idan har mardiya taga sakon Nan don Wallahi nasan baza ta rufa min asiri ba"
"Wai me ka turo min ne duk Naga ka Riki ce?"
" Ka duba ka gani please ta bud'e ko bata bud'e ba"
'dan cire wayan yayi daga kunnen sa ya duba, Murmushi yayi kana yace "ba a bud'e ba ka kwantar da hankalin ka bata gani ba"
Wani ajiyar zuciya ya sauke kana yace "Alhamdulillah dama Ayrah ce ba Lafiya nake so ka kawo Mana maganin zazzabi please"
" Okay bara na je na sayo, yanzu zan Shigo gidan"
" Okay" a tare suka katse wayar.
Direct police station ta nufa, tana parking da saurin ta ta fito tana gudu ta Shiga, Police din dake Kan canter har ya tsorata sabida irin gudun da ta Shigo da dashi leka Bayan ta yake ko wani ne ya biyo ta yayinda mardiya Kuma sai faman haki take kamar numfashin ta zai d'auke, sai faman kallon ta yake Yana kifkifta Ido yace "Madam Lafiya wa ya biyo ka?" Da Yar hausar sa da bata gama nuna ba .
Murya na rawa ta fara magana "Qawata wacce ake nema kwanaki ba a ganta ba naji labarin inda take"
"To yallab'ai wani kawarki Kenn....... " Bai karasa maganar ba sai ga shigowar DPO Sara Masa yayi had'e da bankare kirjinsa Kallo d'aya ya Masa yace "relax" maida kallon sa yayi ga Mardiya yace Wace ce kike magana akai sannan ya sunan ta"
"Ayrah..... Ayrah Alhassan" zaro Ido yayi had'e fa fad'in " kin tabbatar da abinda kike fad'a?"
"Eh na tabbata"
Maida kallon sa yayi ga Police din kana yace "Take her statement, Sannan ku shirya don dani za a fita"
Sara Masa yayi had'e da fad'in " okay sir"
Nan ta Basu dukkanin details din, dama ta bar karamar wayar tane a cikin motar Kuma wayan is on call taji maganar da suke, Luckily ya sa wayan a handsfree hakan yasa taji dukkanin maganar da suke.
Number ta bawa Police din don yin tracking ai kuwa ba a d'au lokaci Mai tsawo ba aka gano inda Abdallah yake Nan da Nan suka Fara binsa a sace, da motar Ayrah sukayi amfani sabida bai santa da wannan motar ba, Bayan Abdallah yayi horn a gate d'in ba d'au lokaci ba Adnan yazo ya wangale Masa gate d'in, Yana Shiga tun Kan ya rufe kofar motar Mardiya ta sa Kai cikin gidan nan da nan polisawa sun fi biyar suka sauko daga cikin motar dukkanin su day bindigogi , Suna pointing din Adnan.
Nan da Nan Adnan hankalin sa ya tashi, Abdallah da ya fito daga motar baki a bud'e yake kallon su, hannun sa rike yake da ledan magana, cikin wata iriyar murya kamar zaiyi kuka Adnan yace "Abdullah ya zaka min Haka?"
"Wallahi tallahi ban San sun biyo ni ba"
Mardiya ce ta fito tana wani irin Taku tana tauna cin gum , tazo daf da Adnan Tace "Hello Mr Adnan" kana ta kauda Kai had'e da Murmushi Tace "Hello baby"
"Mardiya kece?" Abdallah ke mata tambayar Nan cike da mamaki, tace "Eh nice kayi mamakin gani na ko?"
"Ai dama na fad'a maka yarinyar Nan idan ta gani baza ta rufa Mana asiri ba"
"ya Isa haka,ina yarinyar take?" DPO ya yi magana a tsawace .
Adnan tun da ya gansu ya San Shikenan ya rasa Ayrah, shi ba hukuncin da za a Masa bane ma damuwar sa baya son rabuwa da ita, d'aya daga cikin Police din ne ya ture shi had'e da fad'in "wuce muje" jiki ba kwari ya Fara tafiya Yana tafiya biyu daga cikin polisawan Suna biye da shi sauran Kuma suna tsaye a waje, har da Mardiya aka Shiga ciki, har cikin d'akin da Ayrah take ya kaisu, Mardiya na hango kawarta ta saurinta ta ture Adnan ta nufi inda Ayrah ke kwance tana baccin ta hankalin ta a kwance.
Kamar a mafarki ta ji Muryar Mardiya tana Kiran sunan ta, a hankali ta Fara waro Ido har idon ta ya bud'e duka ta tabbatar ba mafarki take ba, daga Chan nesa ta hango Adnan ya rakube a gefe Yana kallon ta daga shi sai vest sai boxer Yana kallon ta, idanun Sa sun canza daga launin fari suka koma jajir kamar zaiyi kuka.
Kiran sunan ta da Mardiya tayi ne a karo na ba adadi ta ya dawo da tunanin ta gare ta, rugumar juna sukayi dukkanin su suna kuka.
Basuyi wata wata ba suka sa masa handcuffs dashi da aminin sa Abdallah, Ayrah na ganin hakan ta yanke jiki ta fad'i.
Haisam na kwance a d'akinsa dawowar sa kenan daga masallaci ya cire jallabiyar sa daga shi sai wando Wanda bai Kai gwiwarsa ba, ya Zo zai kwanta yaji ihu Kuma kamar Muryar isha, tsawaya yayi daga kwanciyar da yake son yi ya Kuma kin ihun ta tana Kiran sunan sa "Ya Haisam zan mutu" da gudu ya fita d'akinta ya fad'a, ya hango ta Akan gado tana mirginawa har tazo Fad'uwa yayi saurin tare ta kanta babu ko d'an kwali.
Gashin kanta ya baje kamar wata mahaukaciya kuka take tana yarfa hannu had'e da rike Bayan ta a kid'ime yace "Princess mene ne, me ya same ki?"
"Zan mutu Yaya, zan mutu bayana, Inna lillahi wa Inna ilaihirraji'un"
"You're in labour princess"
Blanket masu nauyi ya d'auko a Waldrop ya shimfid'a,Sau Kar da ita yayi a kasa yayi ganin ruwan ya fashe, ya gyara mata kwanciyar ta, bata kulawa ya farayi kasantuwar sa na likita, d'akinsa ya koma ya d'auko duk wani abunda zai bukata, ba wannan bane karo na farko ba da yake ganin mace a haka Amma bai San Meyasa hankalin sa ya tashi sosai ba, ko don Yana sontane oho.
Duk wani abunda ya kamata ayi wa mace Mai haihuwa ya Mata, Yana d'an matsa Mata baya Yana Mata sannu had'e da fad'in "push princess" kusan awa d'aya suka d'auka a haka, gashi Umma bata gida dukkanin dasu Twins suna gidan Mummy, Abba da Daddy Kuma sunyi tafiya suna Germany sunje wani business trip, Mai aikin Kuma taje kasuwa don yi sayyaya.
Wani nishi ta saki Mai d'an Kara , jariri ya Fad'o sai Jin kukan jaririn sukayi, wani ajiyar zuciya ya sauke shi zufa ita zufa, mikewa yayi ya gyara kwanciyar jaririn kana da taimakonsa mahaifa ya fito, Raba jaririn yayi da mahaifan, zanin ya sa ya nad'e jaririn a Kai kana ya kwantar Mata a kirjin ta, da sauri ya Shiga toilet d'an karamin roba ya Samu ya tari ruwan zafi ya sirka ya dawo d'akin.
'daukan jaririn yayi ya Shiga Toilet din ya wanke jaririn tass yanda dai akewa sabbin jarirai, Kaya mai kyau ya d'auka ya sakawa jaririn, ya kwantar da jaririn kana ya koma Kan Isha dake kwance idon ta lumshe duk kunya ta ishe ta Murmushi yayi ya girgiza Kai kana ya d'aga ta chak sai ban d'aki, tsayar da ita yayi kana yace "kiyi wanka bari na Kira su Mummy"
Kai kawai ta d'aga Masa ya fice ya barta a ciki.
Yana Fad'awa Umma Isha ta haihuwa sukayi ta fad'a wai Meyasa Bai Kira suba, Murmushi yayi yace "Umma Kennan kin manta da Dr Haisam kike magana ko?" Sai tayi shiru, fizge wayar mummy tayi daga hannun Umma tace "Sannu da kokari son gamunan zuwa"
Ta kashe wayar, Kan Isha ta fita ya tattare gun tsaf, ya sa jik ya goge back yard ya nufa da blankets din da suka baci sai ga Yar aikin ta dawo, tana ajiye ledan a kitchen tazo ta karb'i wanki ta hau wankewa, ya koma d'aki yayi wanka ya sanya kaya marasa nauyi ya koma d'akin Isha ya tarar ta fito wanka har ta Sanya kayan tana tsaye tana kallon jaririn, Murmushi yayi yace "Ya dai maman baby?" Kallon jaririn yayi a kwance a inda ya bar sa, cike da mamaki yace ya Naga Baki d'auki Baby ba?"
"Uhmn Wai me na Haifa ne mace ce ko na Miji?"
A sume aka Kai Ayrah asibiti, yayin da Abdallah Kuma da aka wuce dasu police station,mardiya batayi kasa a gwiwa ba ta Kira Mahaifiyar Ayrah, Nabila ta kwala wa Kira Akan ta Shigo ta kula da Malam Hassan an ma yi sa'a a asibitin da Malam Hassan yake aka kwantar da ita, Malam Hassan yace suje su kawai zai kula da kansa.
Shigowar mami yayi dai dai da fitowar likitan dake Kan Ayrah, inda suke ya nufa yace "babu wani damuwa kawai dai fargabane and congratulations tana d'auke da ciki na tsawon wata uku" Yana Kai Nan ya tafi ya bar su agun Baki a bud'e.
____________________________
Please comment and share
Milhaat ce
Yar Terwa
🍃 *DANGIN UBANA*🍃
Story & Written
By
Milhart
Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne.
*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*
*Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.*
Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️
*BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM*
Page
81&82
*End page*
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._
Continuation...............
Mardiya ce tsaye tana kallon d'an jaririn Isha Kuma d'a agun Yayan ta , jiki na 'bari ta d'auki d'an tana kallonsa kamar yayanta ne yayi kaki ya zubar, Kuka tayi sosai sabida mutuwar yayanta da iyayen ta sun dawo Mata sabo fil, har kasa ta durkusasa ta roki yafiyar Isha dama Mutanen gidan gaba ki d'aya, duk wani munafurcin da tayi ta kullawa ta fad'a musu hatta 'bata auren Farukh da Ameerah da tayi Niyan yi, kowa sai da yayi mamakin abubuwan da ta aikata Amma ance d'an Adam ajizine, Isha ta yafe Mata, anan take shaida musu anga Aurahi suyi murna matuka musamman ma Haisam da haryanzu Yana sonta Amma a matsayin soyayyar ya da kanwarsa.
Har gida taje ta nemi yafiyar Meerah da Farukh, Kuma sun yafe Mata,duk da Farukh da kyar ya hakura sabida ya d'au alwashin sai ya d'auki fansar abinda ta yiwa meeran sa.
"Ayrah me hakan yake nufi? Congratulations? Ciki kike dashi?"
Duk a jere mami ta jero mata tambayoyin nan. Kallon ta kawai Ayrah take yi sai ta kawar da kanta tana fuskantar bangon d'akin.
"To Wallahi Dole ne a zubar da cikin Nan, wannan abun kunyan ba dani ba Baki Isa ki haifa min shege a cikin zuri'a ta ba"
"Mami!!" Ayrah ta kira sunan ta kamar ba ita tayi maganar ba, Zama tayi ta jigina jikin ta ta pillow kana Tace "Mami bazan zubar da cikin Nan ba sabida ba d'an shege bane"
Baki a bud'e take kallon ta Tace "Ashe baki da hankali Ayrah ban sani ba? Ko dai kin samu tabin hankali ne?"
"Ni Lafiya ta kalau au..... " Bata karisa maganar ba taga shigowar Mardiya wani irin Kallo ta mata sai Kuma ta kawar da kanta.
Mardiya karasowa tayi ta dafe ta a kafad'a had'e da fad'in "sannu Qawata" ture hannun ta Ayrah tayi cikin tsawa Tace "Kar ki tab'a Ni" a d'an zabure ta jaa da baya tana mamakin abinda ke damun ta, mardiya Tace "Ayrah lafiyan ki kuwa, me ke damin ki?"
"ina mijina?" Shine tambayar da ta wurga mata kallon Kallo Mami, Mardiya da Nabila suka Shiga yi kana suka maida kallon su gareta, Mardiya ta ce "Mami bari naje na Kira likita don na lura bata cikin hayyacin ta maybe ya tab'a mata kwakwalwar ta"
"Ke malama da hankalina Kuma a cikin hayyacina nake nace miki ina Kika Sa aka Kai min shi"
"Auuu Wai Adnan kike nufi? Yaushe Adnan ya Zama mijin ki Kuma, Ayrah na lura baki da hankali"
"Kar ki Kuma cemin bani da hankali Adnan mijina ne Kuma ina son sa" mikewa tayi Tace "ina yake?"
Kallon ta Mardiya tayi kana Tace "Me nake gani kamar cikine a Jikin ki Ayrah? Fyad'e ya Miki?"
Zafin zuciyar Ayrah ya Shiga yi mata saisaita kanta tayi kana Tace "Kina 'bata min lokaci ina yake?"
"Mutumin da ya sace ki? Ya Miki fyad'e? Sannan yayi kidnapping d'inki shi kike Kira da miji Ayrah?"
Mami ne tayi karfin halin rike hannun Ayrah ta zaunar da ita cike da tausayin Yar nata don zuwa yanzu a tsorace take ga kukan da Ayrah ta fara, cikin Muryar rarrashi Tace "Ayrah ki fad'a min abinda ya faruwa tun daga ranar da Kika barni a asibiti Akan zaki je gidan su Mardiya?"
Shiru tayi tana kallon ta zancen zuci take " Taya za'ayi na fad'a mata abubuwan da ya faru,Taya za'ayi na fad'a mata cewar ina son Wanda yamin fyad'e a karo na ba adadi? Taya zan fad'a mata irin abubuwan da Adnan yamin?"
Sai ta tsinka kanta da fad'in "Mami a hanya ya tare ni sannan yayi barazanar zai kashe ni idan ban bishi ba,Ni Kuma naji tsoron Kar ya cutar Dani sabida nasan na yaudare shi,Bayan na Shiga motar sa sai ya kaini gidan gonan sa tun daga wannan ranar take bani duk wata kulawa sai nake mamakin meyasa ya d'auko ni in dai bai cutar dani yake Shirin yi ba? Dana tambaye shi dalili yace Yana so ya hora nine Amma Kuma bai tab'a cutar dani ko na second d'aya bane....."
Ajiyar zuciya na ta sauke ta cigaba da fad'in "Tun a wannan lokacin yace zai dawo dani gida Amma da sharad'in zan aure sa,Ni Kuma a wannan lokacin wutar tsanar sace a zuciya ta naki amincewa da bukatar sa,aiki kawai yake fita idan ya dawo yana Nan a cikin gidan sai abinda nake so yake yi ,Mami kin San zuciya Kuma ya Hadu da dama Nima inason shi tunda akan sa ne na San mene ne soyayya, soyyaya ce Mai karfi ta Shiga tsakanina dashi daga bisani muka yanke shawarar a d'aura Mana aure,Bayan Yan watanni ya nemi mu dawo gida sai naki sabida ina tsoron zaku rabani dashi" ta fashe da wani irin kuka Mai cin raai. Kallon ta Mami tayi ji take kamar karya take mata,Amma duba da yanayin jikinta da bata rame ba ,jikinta yayi kyau tayi fresh hakan ne ya tabbatar mata da cewar gaskiya take fad'a mata.
Rungumar ta Mami tayi tana patting Bayan ta kamar wata Yar baby,babu Wanda ya Kuma cewa komai sai sautin kukan Ayrah da AC dake aiki a d'akin,Mami Tace "Ayrah lamarin kin Nan ya d'aure min Kai,wannan wani irin rashin hankali ne Ayrah kin sani cikin damuwa,bana iya bacci bana Kuma iya cin abinci duk a kanki Ayrah, ga Jikin baban Kuma abin Sai Kara gaba gaba yake yi" ta fashe da kuka, cikin tashin hankali Ayrah Tace "Mami Dan Allah ki daina kuka,kinsan kukan uwa Akan 'ya'yan ta ba abu bane Mai kyau"
Murmushi mami tayi Wanda yafi kuka ciwo Tace "Kin San da hakan Kika yanke wannan d'anyen hukuncin? Kin tab'a tunanin a wani Hali nake ciki ko da na second d'ayane?"
Ayrah kasa magana tayi idan mami tasan wahalar da tasha baza Tace haka ba idan Kuma ta kuskura ta fad'a mata tasan cewar ita da Adnan har abada.
*Bayan kwana biyu*
Adnan da Abdallah horo ake musu mai tsanani, duk sun lalace sunyi baki, musamman ma Adnan da shine babban Mai laifi, dakyar Ayrah ta shawo Kan Mami suka dunguma zuwa asibiti, tu daga waje take jiyo ihun say da gudu ta Shiga cikin Suma Mami suka rufa mata baya, Ayrah na kokarin shigewa inda take Jin kukan sa, wani police dake tsaye yaga shigowar ta ya daka mata tsawa ba ita kadai ba hatta su Mami Saida suka tsorata.
"Ina Zaki?"
Cikin kuka Tace "Dan Allah kace su daina dukan shi ni ba sace ni yayi ba"
Isha da jaririn ta na samu kulawa sosai a gun Umma da Mummy , harda Haisam da yake ji kamar d'ansane, ranar suna yaro yaci sunan mahaifin sa wato Mansur (Mansur Mansur) su Mardiya sai rawar kai ake, su Meerah uwaye ita ma da d'an katon cikin ta anci ansha daga bisani kowa ya watse anan Mummy ta bukaci Isha ta koma gida Sam Umma bata ji dadi ba dakyar ta amince ta koma gida.
Rikici akayi sosai tsakanin family d'insu Adnan dana Ayrah sabida Mahaifiyar shi sama taki amincewa da wannan auren, Adnan kuwa ya kafa ya tsare bazai tab'a rabuwa da matar Sa ba musamman a a yanzu da yasan tana son shi duba da irin karyar da tayi don ta kare shi ya tabbata da ayanzu yana gidan yari.
Dakyar mahaifin Adnan ya shawon Kan hajiya larai(Mahaifiyar Adnan) Akan idan ta haihu za'a kawo Masa matar sa, Adnan ya nuna shi Sam bai San da wannan zancen ba a haka yasa dole aka kawo Masa matar sa.
'bangaren Malam Hassan kuwa hankalin shine ya kwanta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 24