Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shine ranar da yafi shekaru har hud'u yana jiran wannan ranar, Bayan sallar jumma'a za a d'aura auren amma a kofar gidan su Aysha za a d'aura dalili kuwa shine mahaifin Aysha ne ya bukaci hakan. Bayan sallar jumma'a jama'a sun taru, ga Nan waliyin Ango Amma babu waliyin amarya, Abba ne ya bukaci da a d'an jira su, wurin shiru yayi kwasam suka jiyo horn d'in mota da gudu motar ta karasa rumfar da Mutane suke zaune, Kura motar ta tada mutanen daga masu Allah ya wadai sai masu zagi, sai wa'anda Kuma suke kokarin toshe hancin su. Kowa hankalin sa a Kan motar take kowa son ganin Wanda ke cikin motar suke son gani, ai kuwa Mahaifin Aysha suka gani da Kanin sa, inda su daddy suke suka zauna, Haisam kuwa fararen jamfa da garen sa Sannan kansa bakar hulace Kamar yadda takalmin sa yake Baki,sai baza kamshi yake,  Murmushi yake abokanan sa na tsokanar sa babu ma Kamar Farukh, Malamin da zai d'aura auren ne yayi hamdallah zaiyi magana mahaifin Aysha ya dakatar dashi malam yace "Lafiya dai ko?" Ya amsa da "Uhmn lafiyar Kenan Akwai Wanda ya kamata ku gani kamun a d'aura auren na" Abba yace "Wane ne? Kuma yana ina?" Hannu ya d'aga ya nuna Masa jikin motar, Haisam, Abba da Daddy naga sun mike Daddy ne yace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un" _____________________________ Naji dad'i Sosai da addu'oin kuyi hakuri ban samu damar muku reply ba nagode Sosai Allah ya saka da alhairi. Please comment and share 🍃*DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 41&42 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ _Continuation........_ Abba kallon su Daddy yayi ya dafe kafad'ar sa had'e da fad'in "Yaya Lafiya naga Duk kun rud'e" Haisam cikin rawar murya yace "Kanin Mahaifiyi na" a dai dai lokacin Malam ya iso Haisam karo zaro idon sa yayi da ganin Aysha a bayan sa, cikin kid'ima yace "Habibty dama kin San shine?" Yar karamar dariya tayi tace "Na San shi mana" "Amma.... Amma ta yaya? Kin San shi Kuma baki sanar dani ba? Why?" "Yaya Haisam kenan, Dole na sanshi sabida jinin sa ke yawo a jinin jiki na" Tana maganar tana kallon jikin ta, Haisam kama baki yayi Nan da Nan zufa ya keto masa yace "Kina nufin...." Tayi saurin katse shi da fad'in "Eh mahaifina ne, Nayi mamaki da ba ka gane kanwar ka ba" Zaro Ido yayi waje yace "Ayrah!!! Dariya tayi Tace "Yaaap you got it right, d'azu ka tambayeni meyasa ban fad'a maka na San shi ko?" Shiru yayi Yana kallon ta bashi kad'ai ba kowa da kowa na son Jin dalilin ta, gyaran murya tayi Tace "To ga amsar ka Nan, nayi hakan ne saboda na karya maka zuciya, na sa maka soyayya ta a ranka sabida na ga bayan ka" Idon sa fal da kwalla Yana Fara magana suka fara gangarowa yace "Amma me na miki what have I done to deserve this?" "Oh so you don't know? Kar ka rainawa kan ka hankali mana don't act innocent" Murmushin gefen baki Malam hassan yayi yace "Just tell him Yar daddy, fad'a masa ya kamata ki tunatar dashi" "Toh daddy" kallon ta ta maida ga Haisam Tace "Dr Haisam, wannan shine sakamakon tozarta mahaifina da kayi ka kwace Masa dukiyar sa sabo son zuciya irin naka" Daddy Rai a 'bace yace "Dukiyar sa? Ko Kuma dukiyar Haisam?" Kallon mallam Hassan yayi yazo ya tsaya gaf dashi yace "Bayan ka kashe shi yanzu Kuma so kake ka kashe d'an sa?" Cikin rashin fahimta Ayrah ko ince Aysha 😁 Tace "Wa aka kashe?" Girgiza kai Daddy yayi "Hakan ne ya tabbatar min da baki San komai ba, you are just dancing to your father's tone amma Ni zan fad'a miki gaskiya wannan mutumin da kike gani...." ya nuna malam Hassan ya d'aura da fad'in "Shi ya Kash........ " Da sauri malam Hassan yace "Kul ka fita daga idona na rufe Kar ka d'auka don kana da kud'i ka d'auka kafi karfina Wallahi ka fita daga harkan family na" Kallon Haisam malam Hassan yayi yace "Kuskuren ka shine da ka d'auko zuciyar yafiya irin na iyayen ka shine ya cutar da Kai da ace ka koreni daga gidan Nan da company da ka bani da Duk hakan bai Faru da Kai ba" Daddy kallon su yayi yace "Amma ya akayi kune kuka bamu aure ba shi ba?" 'daya daga cikin sune yace "Wallahi biyan mu yayi bamu san komai ba" Haisam Banda zubar da hawaye babu abinda yake. Abba yace "Amma baku kyauta ba sabida kud'i a had'a baki da ku a cutar da wani, yanzu fisabilillahi baku ji Kunya ba?" Jikin sune yayi sanyi d'ayan yace "Wallahi tallahi bamu San Shirin su Kenan ba, mu ce mana sukayi baya gari Kuma zai dad'e bai dawo ba, Sannan ya tabbatar Mana da cewar Kun matsane in ba ayi baikon ba zai iya fasawa" Haisam kallon Ayrah yayi kusa da ita ya tsaya suna iya shakan numfashin juna yace "Naji kin yi hakan ne sabida ki d'au fansa a kaina Amma Dan Allah Duk rintsi Kar ki rabu dani don wallahi idan na rasa ki zan iya rasa Raina ko Kuma nayi karamin hauka." Jikin ta sanyi yayi tasan tabbas ta cutar dashi amma lokaci d'aya ta tsinci kanta da rashin tausaya Masa maganar da mahifinta ya fad'a mata ta tuna "Haisam har marina yayi sannan yaci mutunci dakyar na roke shi ya bar Mana wannan gidan da 'dan karamin company Bayan duk wannan gumi nane hassada ce da kyashi irin na d'an Adam" Muryar Haisam ce ta dawo da ita daga tunanin da take Yana fad'in "Dan Allah Kar kice zaki rabuna dani Dan Allah, please ki bari a d'aura Mana aure and I'll make things right." Tace "Over my death body, Bayan abunda kayi wa mahaifina Wallahi ko mutuwa zakayi bazan tab'a auren ka ba, idan ka mutu ma bani da asara" Tari Haisam ya Fara yi ya rike kirjin sa Nan da nan ya fara tarin jini, Abba da Daddy ne sukayi saurin rirrike shi, tsaki tayi had'e da fad'in "I hate you, fool Wai soyayya, soyyaya my foot" Malam hassan ne yace "Allah ya miki Albarka daughter ina alfahari dake" hannun ta ya rike suka shige motar da suka zo dashi, suna barin gun kuwa Haisam ya yanke jiki ya Fad'i a sume, Abba ne ya d'auko mota da taimakon daddy,da Farukh da wasu daga gun aka sashi a mota, Basu Zarce ko ina ba sai asbiti. Nan da Nan Mutane suka Shiga jinjina lamarin Nan kowa na tofa Albarkacin bakinsa wasu suna ganin hakan da aka yi wa Haisam ba dai dai bane wa'anda suka yarda da maganar malam Hassan kuwa suna Allah ya kara. Emergency aka kaishi, daddy ne ya Kira Mummy ya fad'a mata Umma najin hakan ta fashe da kuka a lokacin suna tare Kuma wayar na handsfree ne, Isha fitowar ta Kenan taji wannan mumunar labarin Duk da bata San dalilin sumar tasa ba, driver suka Kira ya kaisu asibiti, Isha hankalin ta yayi mugun tashi Bayan sun Isa asibitin aka hana su Shiga. Duk suka tsaya zugum kowa da abinda yake ayyanawa a ransa, ganin Shirun yayi yawa Ma'isha cikin kuka Tace "Daddy me ya sami yayan, me ya faru haka har ya suma? Kuma naji kace yana aman jini how comes" Daddy kasa magana yayi haka ma abba, dukkanin su basu tunanin kowa sai Umma. Inda Farukh yake ta nufa cikin kuka Tace "Ya Farukh Dan Allah ka fad'a min me ya faru nasan kana gun kasan me ya sa meshi" Nan ya Sanar mata da komai Duk da shi bai San me dangantakar ta da Haisam ba, Umma fashewa tayi da Kuka Kan mummy ta karasa inda take tsaye ta Fad'i a sume, da gudu sukayi kanta, mummy Ce ta fara Kiran sunan "Nurse Nurse" nurses biyune suka karaso inda suke da gudu, gado suka d'auko suka tura ta suka kaita d'akin da yake kusa da Haisam,Nan Nan likitoci sukayi kanta. Abba Zama yayi a kasa ya fashe da kuka, kuka yake Sosai Kamar karamin yaro daddy ne ya durkusa a gaban sa yace "Haba Abdallah mene haka kake kuka Kamar wani karamin yaro, be a man mana." Cikin kuka yace "Dole nayi kuka Yaya Dole nayi kuka, why me? Why me wani laifi nayi wa Allah da yake horani Haka first was fauziya with my four kids and now Zainab and Haisam sannan fa Tana da karamin ciki, Yaya ina tsaron rasu Suma don wallahi idan na rasa su kuma zaku rasani" Daddy yace "Subhannallah haba Abdallah Kar kayi sab'o Mana, Allah Yana sonka Allah Yana jarraba bayin sa da yake so ne, ka d'auki hakan amatsayin kaddarar ka" "I can't Yaya bazan iya ba, fi kowa Sanin halin da nake ciki I was a sad and lonely man over 25 years sai yanzu da na fara samun kwanciyar hankali Kuma ace na rasa wannan am back to square one" Ma'isha kasa jurewa tayi ta bar gun ta na kuka mai tsuma zuciya, Farukh ne yabi bayan ta don ya samu ya kwantar mata da hankali kasantuwar yasan tana da ciwon zuciya. Abba sai surutai yake Kamar ya fara zarewa, mummy itama kukan take daddy ya rasa yadda zaiyi mikewa yayi yana safa da marwa ji yayi Mummy ta fashe da "Ihu Innalillahi wayyo mun Shiga uku da gudu tayi Kan Abba da ya Fad'i Daddy shima yayi kansa yana jijjiga shi yana Kiran sunan sa, nurses d'in da suke Kan Umma ne suka fito da gudu da taimakon Daddy suka kai shi d'akin da mummy ke ciki suka kwantar dashi a gadon dake gefen nata dama d'akin gadaje biyu ne aciki, Nan da nan wani likitan ya shigo shima ya fara duba shi. Mummy kuka take Sosai daddy ne ya rike ta suka fita suka zauna a kan kujera irin Wanda ake ajiye wa a ko wani ward, kwantar da ita yayi Yana d'an bubbuga Bayan ta yace "Ki daina kukan Nan please addu'a suke bukata a yanzu Dan Allah kiyi Shiru" "Alhaji taya za'ayi na daina kuka, son fa da Zainab Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un ga Nan Abdallah shima Wallahi tausayin sa nake ji, a cikin Yan awanni ta fita hayyacin sa" "To ya zamuyi? Haka Allah yaso Dan Allah I need you now kukan ki na tada min hankali Dan Allah Kar ki daina kina karya min zuciya" shiru tayi bata sake cewa komai ba ta cigaba da kukanta, shi Kuma bai daina bubbuga Bayan ta ba a haka har ta d'an samu relief. Likitocin Dake d'akin Su Abba da Umma ne suka fito a tare d'aya daga cikin su yace "Ku kwantar da hankalin ku, Suma sukayi duk su biyun, munyi musu allurar bacci zuwa anjima kadan zasu farka" Daddy ne ya amsa da "Mun gode" sukayi wucewar su, Bayan sun tafine likitocin da ke kan Haisam suka fito su uku, shugaban sune yace "Me ya sami Dr Haisam Haka?" Shiru sukayi d'ayan yace "Ya kamata musan me ke damin sa sabida musan ta yanda zamu 'bullo wa al'amarin" Daddy yace "Nasan Kun San yau ranar d'aurin auren sane ko?" A tare suka amsa da "Eh mun sani" 'dayan ya d'aura da fad'in "maganar zuwa gun dinner sa ma muke aka Sanar da mu an kawo patient Emergency, ga mamakin mu da muka zo muka tarar ashe shine Mara lafiyan" Ajiyar zuciya Daddy yayi yace "Auren ne aka fasa" A tare suka ce "subhannallah Abu baiyi dad'i ba" Sai kuma sukayi shiru suna kallon junan su. Farukh ne yabi bayan Ma'isha inda Meerah take ta nufa Meerah na ganin Isha a haka ta yi saurin tare ta had'e da zaunar da ita tana fad'in "Lafiya Isha? Me ya same ki Haka? Mutuwa akayi ne?" Muka take Banda sunan Haisam babu abinda take kira, cikin kukan ta Sanar da ita abinda Aysha tayi ka karasa maganar da fad'in "I know something was fishy about her,Ya Haisam ya cutar dani Kuma ya cutar da kansa Bayan irin Soyayyar da nake Masa Amma Baya gani Akan sa fa na kamu da ciwon zuciya,Ashe haukata kawai nake akan wata fa ya shiga halin da yake ciki"ta karasa maganar cikin kuka. Farukh Bayan ya karasa inda suke Jin maganar da Ma'isha keyi ya jaa da baya ya tsaya don Jin abinda take fad'a,sai da ya gama jin maganar da take ne ya samu gu ya zauna yace "Isha Yayan ki fa ba mutuwa yayi ba Suma yayi kuma Wallahi shima yana sonki kawai na kasa gane wane dalili ne yasa ya kasa fahimtar hakan, Dan Allah ki daina kukan Kuma Insha Allah hakan da ya faru zai Zama alhairi kinji" Meerah hannu tasa tana share mata hawaye Tace "kinji ko ai na Sha fad'a miki shima yana sonki, da ace kin bi shawarata kin Sanar Masa da Duk wannan bai faru ba" Farukh ne ya amsa da "Wannan hakane Amma kin san bamu muke sarawa kanmu Rayuwa ba we plan but Allah knows what is the best for us, kawai dai sai dai muyi fatan dacewa" Nan sukayi ta mata baki har ta samu ta daina kukan, sai ajiyar zuciya take sabida tayi kuka sosai Farukh pharmacy ya nufa ya Saya mata magani kana ya sayo ruwan sanyi bai dad'e ba ya dawo ya Mika Mata ta Sha, Duk su ukun suka nufi inda Su Daddy suke, suna Isa ganin daddy da mummy a tsaye sai Kuma likitoci biyu a gefen su, Farukh Mika musu hannu yayi suka gaisa yace "Dr Musa, Dr Sani ya jikin Haisam d'in hope everything is okay?" Dr musa yace "Gaskiya Akwai matsala Dr Farukh" Ma'isha Tace "Please Dr Musa wace matsala Kuma Bayan Wanda muke da ita a yanzu? Me ya sami Haisam d'in? Ko dai ya mutu ne kuke 'boye Mana?" Ta Karasa maganar tana matsar kwalla. Dr sani yace "No no bai mutu ba Pharm isha, yana Raye" "So tell me, what's wrong?" Ajiyar zuciya yayi yace "Ya Shiga comma." Ma'isha jaa da baya tayi ta jingina da jikin bango tana girgiza Kai had'e da fad'in "Shikenan Shikenan Shikenan Nima lokacin mutuwa ta tazo" Farukh yace "Haba Isha sai kace ba health practitioner ba? Kin fa San yanda comma take wani aranar ma zai farka wasu Kuma sukan d'auki sama da shekaru 20 suna comma Kuma ana sa ran zasu farka watan watarana, misali Kamar d'an sarki saudiya tun da yayi hatsari ya shiga comma yafi 20 years bai farka ba Kuma bai mutu" Mummy Tace "To me banbancin sa da mamaci ya mutu kawai" Dr sani yace "Bai mutu ba Mummy sau dayawa Akan binne Mutane ba tare da sun mutu ba wasun duguwar Suma ce amma rashin sani sai a binne su" Daddy ne yace "Allah ya Basu lafiya, don comma fa babban tashin hankalin" Ganin sukayi Isha ta tsuke sai ganin ta sukayi a kwance mummy kuka ta fara Farukh yace "Mummy kwantar da hankalin ki ni na bata maganin bacci,tayi kuka sosai gudun Kar ciwon ta ya tashi,na d'auka ma zata gane" Meerah Tace "Aikuwa nima shi nake Shirin bata, baza ta gane ba sabida ai ba a hayyacin ta take ba" Murmushi Daddy yayi yace "Madallah da samun Mutane irin ku a gaskiya daughter da Son sunyi dace" Mummy Tace "Hakane Kam na dad'e Banga Qawa ko aboki Haka ba, Allah ya muku Albarka ya barku tare" Duk suka amsa da ameen. Mummy da Meerah ne suka kai Isha wani d'aki don ta samu damar baccin da kyau,Nan tayi ta baccin ta. ____________________________ Ga masu bukatar Shiga WhatsApp group kumin magana 07083818353 Mata zallah pls , sannan idan kin San baza kiyi sharhi ba Kar kimin magana Dan Allah,don sharhi nake so ba Thanks ko Allah ya kara basira ba,idan ba kyayi zan cire ki. Please comment and share Milhaat ce Yar terawa [7/6, 1:26 PM] Miilhaat: 🍃*DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 43&44 _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ _Continuation........_ "daddy wai me Mutanen Nan suke fad'a ne? Wa aka kashe?" Ayrah keyi wa Daddyn ta da yake tuki tayi wa wannan tambayar, cikin inda inda yace "Don't mind them please,shirme ce da irin sharrin su da suka Saba" "To Shikenan, Amma daddy har naji tausayin sa Wallahi, Ya haisam na da kirkii Sosai" Taka birki yace "Tausayin..... Tausayi Kika ce" Ganin yanda ya ke zaro Mata Ido kana Yana maganar cikin fad'a ya tsorata tata Sosai. Murya na rawa Tace "Am sorry" Tsaki yayi yace "You better be, Banda wawiya irib rashin mutuncin da ya min baki ji tausayi na ba sai Tausayin sa? Kuma kul na sake jin kin ambaci sunan sa sai na sab'a miki shasha kawai" A dai dai Nan suka Isa gida zata fita yace "Dawo Nan" Dawo wa tayi ta zauna bata ce Masa komai ba, ganin bai yi magana ba Tace "Daddy gani" "Mtsss ai na zaci Zama zakiyi kina Kallo na tunda na Zama sa'an ki, kina jina?" Ta amsa da "Eh daddy" "Good, Kar ki kuskura naji kin fad'awa maman ki maganar Nan" "Toh" "Wuce ki fita min a mota." Tur baki tayi kana ta fita, likowa yayi yace "Ni kike turawa baki ina zan Shigo gidan na same ki Sai na ci mutuncin ki" Da guda ta shige gida, shi Kuma ya fita daga gidan. Bayan farfad'owar Abba da umma, Tunda mummy ta fad'a mata cewar Haisam ya Shiga comma ta bud'e sabon babin kuka Daddy kuwa yayi ta fad'a Yana fad'in "Ai dama sai da na Hana ki fad'a mata Amma kinki ji, yanzu ki ga halin da Kika sata a ciki" Abba yace "haba Yaya ya Isa haka Mana tun d'azu kake ta fad'a Kuma, ai dama Dole ta sani ko idan bata sani ba Dole gaba zata sani so ni Banga abun tashin hankali anan ba" Shiru kawai yayi bai ce Masa komai ba, Ma'isha na farfad'owa Meerah ta gani a gefen ta, da taimakon Meera Isha ta zauna abinci ta bata da ruwa da kyar ta karb'i spoon 3 ta Sha ruwa, ta tashi zata fita, Meerah ce ta rike ta had'e da fad'in "Ina Kuma zaki?" "Gun Ya Haisam" "Amma......" Dakatar da ita tayi da fad'in "Yanzun ma hanani ganin sa zakuyi? Bayan d'azu maganin bacci kuka bani?" Sake ta tayi kana Tace " ya akayi Kika sani?" "uhmn Kar ki manta fa Ni pharmacists ce nasan drugs" tana Kai nan ta fice d'akin da Haisam yake ta nufa taga wayam. Da sauri ta fito ta hango Bayan Meera Kiran sunan ta tayi ta tsaya, su Daddy najin Muryar ta Duk suka fito , da sauri ta Karasa inda take Tace "Ya ban ganshi ba?" "To ta ya za'a yi ki ganshi ce miki akayi ya shiga comma to where do you expect za a Kai shi pharmacists?" "Oh so that's mean yana ICU" Hannu ta d'aga mata alamu oho, ta juya tayi tafiyar ta tana ganin su Umma ta nufi inda suke, dukannin su Sannu suke Mata ta amsa. Abba ne yace "Ya kamata mu koma gida ko tunda duk Mun farka" Umma Tace "A bar Haisam d'in dawa?" Ma'isha Tace "Umma Kar ki damu ina Nan, Kuma baza a bari a Rika Shiga kansa ba , kin san ba'a son motsi ko kad'an a ciki" "Hakan na nufin bazan sake ganin sa ba ko?" Ta karasa maganar tana matsar kwalla, Ma'isha rungumar Umma tayi Tace "Please Umma ki rage kukan Nan haka Kinga nima na daina ko muyi ta Masa magana, Kuma Insha Allah zan nemi hanyar da Zaki Rika ganin sa lokaci zuwa lokaci, Kuma fatan mu shine Kar ya d'auki tsawon lokaci a ciki" Mummy Tace "Allah yasa hakan ne don nifa Sam ban yarda da likitocin Nan ba, a Haka sukayi wa wata makwanbciyar mu ba Ashe kashe ta sukayi ance fa yawanci likitocin Nan mayu ne" Ma'isha tayi saurin fad'in "Laaah mummy Kenan Nima mayya ce ko?" Duk sukayi dariya a Haka suna Hira har suka fita, Umma da Abba suka Fara ajiyewa a gida kana su daddy suka wuce gida. "Qawata ya akayi haka? Meyasa zakiyi wa Haisam haka? Dama ba son shi kike da Gaske ba?" Mardiya ke yiwa Ayrah wannan tambayar, mikewa Ayrah tayi Tace "Na fad'a miki kwanaki a kwai wani buri nawa Wanda nake so na cika, Wanda Wannan burin nawa burin mahaifinane, Wanda na cika Masa burin sa Amma na rasa dalilin da yasa bana farin ciki da hakan" Amma "Ayrah me ya Kai ki aikata irin Wannan d'anyan aiki tunda kinsan ba auren shi zakiyi ba, me yasa Kika had'a harda asiri?" "uhmn Qawata Kennan to ai da ba don ke ba ai bazan samu damar Shiga ransa ba, kinga Kenan amfanin bokan Kenan ko" Mardiya mikewa tayi cikin rashin fahimta Tace "I don't get you please ki Kara min Karin haske Akan abinda ban sani ba" "zauna kiji" Zama sukayi Nan ta Fara Sanar da ita duk abinda mahaifin ta ya Sanar da ita da hanyan da tabi har akayi maganar aure, Kama baki Mardiya tayi Tace "Innalillahi Ayrah Amma gaskiya banji dad'i ba Kuma Ni gaskiya ina kokonta Akan maganganun kin Nan Haisam Sam bazai aikata hakan ba" Rai a d'an 'bace Ayrah tace "Kina nufin kice Daddy na makaryaci ne?" Cikin inda inda tace "A....A'a Ni Sam ba Haka nake nufi ba Amma..... " Murya Mamy sukaji ma'ana mahaifiyar (Ayrah)

Chapter 12 of 24