Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ba, so nake Dan Allah ka Zama Tutor na" "Tutor dai? 'dan Ni d'in Nan bani da wannan ilimin ai Ni dolo ne fa" Yar karamar dariya tayi Tace "na amince ka koya min dolon cin naka, duk da nasan Kai ba dolon bane ba sai dai in rowa zaka min Kar na karu da kai sai na hakura" Murmushi yayi yace "Toh yaushe kike so mu Fara?" Tace "Ko gobe ma" "A a gobe Sunday ba inda nake zuwa ina gida, ki dai bari idan muka had'u Monday mayi maganar" Cikin murna Tace "Toh nagode sosai" "Bakomai sai da safe" Ya katse wayar Aysha bin wayan tayi da kallo tace "Mtssw ya katsewayar kamar shi ya Kirani" wurga wayan tayi akan gado ta kwanta ta fara sharar baccin ta dama ta Riga ta shirya cikin kayan baccin ta. Ma'isha kuwa ganin bai mata reply ba tayi tunanin ko bacci ne ya d'auke sa, ta shiga kiransa Amma busy, ji tayi kamar ta kurma ihu, cikin sanyin jiki ta tashi ta shiga wanka ta d'aura da alwala,bayan ta fito tayi shafa'i da wutiri bayan ta idar ta shiga rokon Allah da ya yaye Mata sayayyar da take Masa in shi d'in ba alhairi bane a gareta ba, in ko alhairi ne yasa ya Sota kamar yadda take son. Wayar Tace ta fara ringing tana dubawa taga yayana Yar karamar tsaki tayi Tace "wato ya gama waya da ita" Sai da ya kusa yankewa ta sa hannu ta d'aga ta Kara a kunnen ta, yace "Haba princess kin shanyani bacci Kika yine?" "a'a wanka na shigane" "Shine baki fad'a min ba?" "gani nayi kana wayar da tafini muhimmanci" " Ki daina fad'in haka princess waya nake da wata course mate d'ina" "Oh mace ce ma ko?" Yace "Eh" "Na sani ai" "Me Kika sani?" "Babu komai" " To hau online d'in mu cigaba da hirar mu" Tace "Nikam bacci zanyi kaina ke ciwo" Babu yanda baiyi ba ta hau Amma taki hakan yasa ya kyale ta,katse wayar yayi, yayi wurgi da ita Yana tsaki yace "Yau na kasa gane Kan yarinyar Nan ko me ya same ta oho" Da wannan tunanin bacci yayi awun gaba da shi. Ma'isha kuwa kasa bacci tayi, tana kuncewa sa sakawa idan har bata mallaki Haisam a matsayin miji ba zata iya samun matsala, Kila ma ta rasa rayuwar ta a dalilin hakan, Amma meyasa haryanzu bai nuna Yana sonta ba? A bayyane Tace "Ya Allah kasa Yayana Yana Jin abinda Nima nake ji akan sa, Allah yasa ba Ni kad'ai nake haukataba" a Haka har bacci ya d'auke ta. WASHE GARI Ma'isha tunda tayi sallar asuba ta koma bacci bata tashi ba har sai da aka Fara Kiran sallar azahar, tana farkawa wayarta ta fara dubawa taga missed calssy da dama, amma na haisam yafi yawa harda texts shi a tunanin sa fushi ta Kuma yi dashi. Murmushi kawai tayi ta tura Masa text *"am sorry Yaya na bacci nake , wayar na silent ne shiyasa banji ba"* Yana gani ya Mata reply da *"okay idan kin shirya ki Sanar dani Ina d'akina sai na kai ki saloon d'in"* Ta amsa reply da *"Alright"* tashi tashiga wanka,sai da tayi sallar azahar kana tashirya cikin wasu lallausar riga da siket na voyel less dark blue wanda aka mata ɗinkin tamkar ajikinta aka dinka yayinda adon jikin kayan pink ta yafa pink din mayafi da takalminta hill da kuma handbag ɗinta pink yar karama ,ta saka wayarta aciki ,Batayi wani kwalliya ba abisa dabi'arta na rashin damuwa da ɓata fuskar ta wajan ciki masa hayaniyar kwalliya ,Ta fesa turaren ta mai kamshi ta fito. Tana fitowa ta samu mummy da Umma a parlor suna Hira sannan suna Kallo sama sama Umma tace " masha Allah daughter kinyi kyau" Ma'isha kanta akasa tana murmushi tace "Nagode umma " Mummy Tace "Yau sai ina Haka?" "Saloon zani" "uhmnn" kawai Tace Tace "Sai mun dawo" Mummy kallon ta kawai tayi Umma Tace "A dawo lafiya,Allah ya tsare" Ta amsa da Ameen, part d'insu Haisam ta shiga Kai tsaye d'akin sa ta nufa,ta tarar ya gama Shima hakan yasa basu 'bata lokaci ba fita sukayi atare, sadaddiyar mota suka shiga da Alama sabuwace an wanke ta sai sheki take. Bayan sun shiga motar ya kalleta ta yace "Princess irin wannan kyawu Haka, kamar Zaki je gasar sarauniyar kyau" Turo baki tayi cikin Shagwab'a tace "Sai yanzu ka ganni?" Dafe Kai yayi yace "kefa na lura Sam bana Miki gwanin ta ko?" "Ni dai bance ba, ai tun Shiga na d'akin yakamata kace nayi kyau"for "kyau din naki ne yayi yawa baki ga sai kallon ki nake ba na kasa magana,Kuma nayi maganar baki ji bane, yanzun ma dakyar maganar ta fito" Dariya kawai tayi tana Jin dalilin kalaman sa masu sanyaya zuciya, shiyasa Bata gajiya da magana dashi bataki ace tana tare dashi ba a ko wani lokaci ba. Sunyi tafiya kusan na minti uku sai Tace "kaima fa kayi kyau sosai Yaya" "Au ramawa zakiyi? Sai yanzu Kika ganni Kennan?" "A a na Isa ramuwa Kuma, tun d'azu nake son fad'a maka cewar kayi kyau sosai Amma ya kasa fita yanzun ma dakyar sai da na dage na furta" Dariya ya Shiga yi, itama tana dariya tuki yake a hankali har suka Isa saloon ta fita shi Kuma ya zauna a mota Yana jiran ta. Fitar ta ke da wuya wayar sa ta Fara ringing Yana dubawa yaga Aysha, picking yayi bayan sun gaisa ta Fara Jan shi da Hira har ta a ka Gama wanken Kan nata suna waya da Aysha bud'e motar tayi ta zauna, yace "Aysha am sorry please zan kira ki anjima" Tace "Tohm bye" ya katse wayar. yace "Princess har kin Gama?" " yau Kuma Yaya? " "Yau Kuma me? " "To ai ka Saba cewa na dad'e ne,yau Kuma nayi sauri ko?" Dariya yayi yace "Wallahi Aysha ce ta ke ta bani dariya" "Wace ce Aysha Kuma?" "course mate d'inace" " Wato da ita yake waya Kennan jiyan ma koma wacece ke baki Isa ki rabani da Yayana ba,baki Isa ki rusa min ginin da na dad'e ina ginawa ba" take ayyanawa a ranta. Tafi yayi Tace "Na'am" "Lafiyan ki kuwa tunanin me kike haka?" "Bakomai bacci nake ji yaya" "Shopping d'in fa?" " Na fasa mu koma gida kawai" "Ikon Allah yau wa zai Mutu princess ce tace Bata son shopping" Kirkirerren Murmushi tayi yace " Your wish is my command" Ya tada motar suka bar gun. Suna Isa gida bata tsaya jiran sa ba ta bud'e motar ta fita, tarar da su Mummy ta musu sannu ta shige d'akin ta. Umma Tace "mutanen ki sun fara" Mummy Tace "Chan ta matse mu Basu da damuwa ne ko kad'an" __________________________ Please comment and share Milhat ce Yar Terawa 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 19 and 20 Haisam na shiga parlor cikin girmawa ya gaidasu mummy suka amsa, Umma kallon tuhuma take Masa Tace "Haisam me kayi wa 'yata?" Cikin rashin fahimta yace "Umma ce Miki tayi na mata wani abun" "Gidan ku Haisam ina tambayar ka kana maida min amsa da tambaya?" "Wallahi Umma Ni ba abin da na Mata, sai dai Kuma in sharri ta fara yi" " Wani irin sharri yarinya ta fita tana walwala da farin ciki ta dawo cikin 'bacin Rai ka dai..... " Mummy ce ta dakatar da ita tace "Ki daina shiga maganar yaran Nan wataran Zaki ji kunyane Tohm" "To ai abun ne da mamaki daga fitan su ta dawo Haka?" "Da dai kinyi shiru da kin taimaka wa Kan ki sabida kunya zakiji, Ni da ranar na shiga maganar su ba kunya tani sukayi ba, ina Nan ina goyon bayan Son Ashe ya lallab'a sun shirya, kawai nazo wucewa naji Muryar su suna Hira suna dariya tun daga Nan na fita harkan marasa kunya" Haisam yace "Ma'isha dai akwai abinda ke damin ta nayi nayi da ita ta Sanar dani taki daga bisani ma kuka tayi tamin dakyar na rarrashe ta" Mummy tab'e baki tayi Tace " Kwaji dashi" Umma Kuma Tace "Nikam ai baza taki Sanar dani ba" mikewa tayi ta shige d'akin Ma'isha ta tarar tana kuka ta kwanta ruf da ciki, Bata ma San da shigowar Umman ba. Dafe ta tayi had'e da Kiran sunan ta cikin murya Mai sanyi "Daughter!!! A firgice ta tashie ta zauna tasa hannu tana share hawayen dake fuskar ta, kirkirerren Murmushi tayi Tace "Umma kece ban ji shigowar ki ba" Ganin irin kallon da Umma take mata yasa ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da yatsunta Umma tace "Ma'isha me ke damun ki? Yayan ki ya Sanar dani kina cikin damuwa Kuma kin ki fad'a Masa sannan yace min kina kuka na d'auka shirmen sane Ashe da Gaske ne tunda na gane wa Ido na, me ke damun ki? Ki saki jikin ki Nima tamkar mahaifiyar kice" Murya na rawa tace * "Ba ... Babu komai fa Umma" "Baza dai ki fad'a min ba, ko kina ganin ban Kai ki fad'a min bane?" "A'a Umma har kin wuce ma, kawai ban San ta ina zan fara Sanar dake damuwata bane" "ki fad'a min ta ko ina zan fahimta Kuma Insha Allahu zamu samu mafita" "idan na fad'a mata dalilin kuka na tabbas nasan zata Sanar da Haisam sannan idan na 'boye Mata Kuma baza taji dadi ba Dole ma nasan yadda zanyi, na gwammaci nayi ta dakon soyayyar a zuciya ta har izuwa ranar da zai bud'i bakin sa yace Yana so na" Dafe kafad'ar Ma'isha Umma tayi hakan yasa ta dawo daga tunanin da take Umma Tace "Ki Sanar dani matsalar ki" "Umma...... Ina.... Ina son... " "Kina son me?" "Inaso na Sanar dake Amma this is not the right time idan lokaci yayi Zaki ji Insha Allah, Amma for now ina bukatar addu'ar ki please" "hmmm Shikenan Daughter Allah ya yaye Miki damuwar ki" "Ameen Umma" "To tashi muje parlor muyi Kallo" "Ya Haisam na parlor ne Umma?" Mikewa tayi Tace "Dama zan karb'i sako a wurin sa" "Ai na d'auka fushi kike da yayan naki" "Umma ai ni da Ya Haisam sai Allah" "Allah ya muku Albarka" Ta amsa da ameen. Suka fice, suna isa parlor ba taga Haisam ba Tace "Mummy Yaya na fa?" Wani irin Kallo ta mata Tace "Sandan kiwon sa ya 'bata" Turo baki tayi zatayi magana Umma Tace "Jeki d'akin sa maybe yana chan" Tace "To umma" da saurin ta ta fice. Mummy ta bita da Kallo kana ta maida kallonta ga Mummy Tace "Kinga abinda nake fad'a Miki ko?" Umma Murmushi tayi Tace "Na gani." Babu Wanda ya sake cewa komai suka cigaba sa kallon su. Tun daga Baki kofar d'akin sa take ji yana waya yana dariya d'an tsayawa tayi Tace "Waye Yaya samu haka?" Jin ya ambaci sunan Aysha yasa taji kamar an soketa da kibiya a kirji, shiru tayi har ta juya xata koma sai Kuma ta dawo ta bud'e kofar had'e da sallama, Yana ganin ta yace "Am Sorry zan Kira ki anjima" ya katse wayar, Ma'isha Murmushi tayi har cikin ranta taji dad'i ko ba komai tana da muhimmanci a gun sa, sai wata zuciya Tace Mata "idan Kuma 'boye Miki wani Abu yake fa?" Yace "Princess ya dai kin tsaya kina kallona ki zauna Mana" "Yaya meyasa ka katse wayar da kake yi?" "Sabida princess d'ina ta Shigo lokacinta ne ba na kowa ba" Taji dad'i sosai hakan yasa ta zauna Nan fa suka fara Shan hirar su sosai suna cikin farin ciki. Aysha kallon wayan ta ke Tace "Ya Rabbi gayen Nan zai bani wahala, a hakan zan samu soyayyar sa? Amma ba komai insha Allah sai nasan hanyar da nabi na sa ka Fara Sona ko ta wani hanya ne" *MONDAY* 7:45am Kiranta yayi a waya murya cikin fad'a fad'a yace "Wai me kike haryanzu ne? So kike na makara?" "Am sorry gani n...... " Kitt ya katse wayar cikin sairi ta fito ta bud'e motar ta shiga tana Zama bata ma rufe kofar ba ya ya tada motar tana rufewa ya jaaa motar suka nufi hanyar school kana kallon fuskar sa zaka gane ransa a 'bace yake cikin sanyi murya Tace "Yaya Dan Allah kayi hakuri wallahi na tashi da ciwon Kaine" "Dama kin tab'a rasa abin fad'a ne? Inaga ma Dole na bar driver ya Rika kaiki aini ba driver d'inki bane ba" "Yaya har abun ya kai ga Haka?" "Wuce Nan ma" "Ai Yaya naga lectures d'in naka karfe 8 ne Kuma haryanzu da sauran time" "Malama test nake dashi Kuma malamin Nan ba imani bane dashi, 8 na cika yake rufe kofa ba Mai Shiga ba Mai fita, sabida Kinga baki da lectures sai 9 yasa Kika 'bata min Lokaci" "Wallahi ba haka bane Yaya" "Hakane Mana, wallahi ki ka Kuma maimata irin haka tafiya zanyi na bar ki" "Insha Allah bazan sake ba kayi hakuri" "Da kuwa kin taimaka wa Kanki, don Kanki kika taimaka bani" "Kayi hakuri" "Naji" kawai yace Mata har suka Isa cikin makaranta babu Wanda ya ce uffan a cikin Saida yayi parking Tace "Yaya ka saki ranka Mana in ba haka ba test d'in bazai maka dad'i ba" "Kin San da hakan ai Kika bata min raai? Fita yayi a motar ganin zai iya kulleta a ciki itama tayi saurin fita jakarsa kawai ya d'auka a back sit yayi tafiyar sa ba tare da yace Mata komai ba. Ma'isha mamaki ne ma ya kamata bata tab'a ganin sa haka ba, "ko da yake ni na 'bata Masa raai zuwa anjima nasan zai huce tunda hakan ba halin sa bane ba." Haisam sauri yake sosai sabida saura minti biyu kachal time ya cika, Yana Shiga LT zaman sa kenan zai ga shigowar malami, ai kuwa yana Shiga yasa aka rufe Masa kofofin, Nan ya Shiga arranging d'insu zaman da sukayi babu Wanda zai iya magana da wani inko kayi za'a jika sanan baka Isa Kati satar amsa ba layin medicine ba wasa kwata kwata su sha Tara ne a ajin bayan mutum sama da talatin ne suka samu admission sauran tun a aji d'aya aka zubar dasu GSU Kenan ba wasa. Alhamdulillah test yayi wa Haisam dad'i mintuna 30 aka basu Amma shi a cikin sa'a ya gama cikin mintuna 20,bayan sun gama duk suka fita, wurin motar sa ya nufa jin an Kira sunan sa yayi saurin juyowa Murmushi yayi yace "Kaga manyan mutane" "Su ku Kenan ko?" Hannu suka Sha yanda samari suke Haisam yace "Ya test d'in dai?" Yace "Alhamdulillah" "Masha Allah, Allah ya bamu sa'a ya amsa da amiin. Haisam yace "Dama cafeteria zanje ban samu na karya a gida ba muje Mana" "Wallahi Nima ban karya ba muje d'in" Sai da ya ajiye jakarsa a mota kana suka wuce suna tafiya suna Hira sabida dakwai d'an tafiya daga College of medicine zuwa commercial area. Inda ya Saba cin abinci Suka nufa, as usual chips and chicken yace a kawo Masa, abokin tafiyar tasa Kuma ya ce Fried Rice suna cikin cin abincin su ya hango Aysha Wanda itama tana d'ago Kai Kennan suka had'a Ido dashi Murmushi ta sakar Masa Shima ya maida Mata. Karasowa sukayi da ita da kawarta sallama sukayi suka amsa musu, Tace "Zamu iya Zama?" Haisam yace "Bismillah Ku zauna" Bayan sun gaisa Tace "Yallab'ai wannan kawatace Sunanta mardiya a pharmacy take" Murmushi ya Wanda a ko da yaushe shine abun yinsa yace "Nice to meet you pharmacists" Ta amsa da "Nice to meet you too" Ya maida kallon sa ga Aysha yace "Yallab'iya wannan abokina ne sunan sa Farukh a medicine yake" Yar karamar dariya tayi Yallab'iya da yace ne ya bata dariya Tace "Sannu Dr Farukh" Zaro Ido yayi yace "Dr? Da saurana tukunna, cemin Farukh d'in ma kad'ai ya wadatar" "Hahaha to shikenau Sannu Farukh" Yace "Yauwa ai yafi dad'i ko? " Dariya sukayi dukkan su, suna cin abinci suna Hira, wayar Haisam ce ta Fara ringing ajiye spoon d'in hannun sa yayi, Yana picking cikin Muryar Shagwab'a Tace "Yaya" Ya amsa da Na'am "Princess" Cikin sauri Aysha ta d'ago kanta suka had'a Ido da mardiya, ji tayi kanta ya fara sarawa a ranta take maimaita sunan Princess? Shin Yana da matane ko kuma budurwa,inaa duk yadda akayi budurwar sace taya ma za'ayi ace wannan yarin santalelen Saurayi ace bayi da budurwa? Lallai aikina ya jiku zanyi fafutakan neman soyayyar sa sannan ne rabashi da so called princess d'in nasa. Haisam yace wayan sa yake hankalin sa kwance, tunda ya fara wayar bai daina Murmushi ba alamun Yana Jin dad'in wayan, yace "To princess kizo Mana ki sameni a cafeteria Sai kici abincin" Dariya yayi yace "Na Amince zan saya miki duk abinda kikaso Kuma sai kin cinye ehe." Bata d'au lokaci Mai tsawo ba ta karaso cafeteria dake dama ba wani nisa tayi ba tun daga nesa da ta hango Aysha taji gaban ta yafi a bayyane Tace "Itace na gansu tare ranar, ba shakka itace Aysha" Ajiyar zuciya tayi Tace "Koma mene ne zanji gaskiyar a yau" _____________________________ Please comment and share Milhat ce Yar Terawa 🍃 *DANGIN UBANA*🍃 Story & Written By Milhaart Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne. *🌍MANAZARTA* *WRITERS ASSOCIATION📚🖊* *M. W. A* ```Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻``` https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa ____________________________________ *Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.* Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️ *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM* Page 21 and 22 Tafiya take kanta a kasa, hannun ta rike yake da Yar karamar jaka Wanda bazai wuce handout biyu bane aciki, a hankali take tafiya hankalin ta kwance har ta Isa inda suke sallama tayi had'e da jaan kujerar dake gefen Haisam ta zauna. Murmushi Haisam yayi yace "Barka da zuwa the only princess in Haisam Palace" "Uhmn Yaya Kenan princess kawai ashe da saura na" "Wa ya gaya miki? Ke Kanki kin San ke ta dabance" Murmushi tayi sai Yanzu ta maida kallon ta ga su Aysha dake aikin kallon ta Murmushi tayi Tace "Sannun ku fa" Mardiya ce ta amsa da "yauwa" Ganin Aysha tayi nisa a tunani ta d'an tab'a ta, a d'an razane Tace "Yauwa sannu ya kike" "Lafiya Lau" Haisam yace "Princess meet Aysha and Aysha this is My princess bani da tamkar ta a Rayuwa" Kirkirerren Murmushi Aysha tayi Tace "Nice To meet you, to Amma ita d'in bata da suna ne? Haisam Yar karamar dariya yayi yace "Tana dashi Mana kawai dai sunan ne yayi min nauyi bana iya Kiran sa sai on special occasions" Aysha zaro Ido tayi sannan Kuma ta tab'e baki had'e da girgiza Kai Tace "oh lallai" Yace "Sai dai idan ita zata fad'a miki da bakin ta" Aysha Tace "Ya sunan ki?" "Ma'isha"kawai Tace a takaice. "Suna Mai dad'i" " Thank you" Ma'isha ta maida kallon ta ga Farukh da aikin cin abincin sa kawai yake, Ma'isha dariya tayi Tace "Haba Ya Farukh duk don Kar naci ne kake ta sauri ko?" Sai da yasa hannu ya kurb'i ruwa kana yace "Na Isa Ma'isha kawai dai naga baku da niyar gama surutun nakune kin San ance kowa da damuwar sa Ni abincin ne damuwa ta" Haisam yace "Zaka ji da shi ai" Cikin sanyin Murya Tace "Yaya My promise yunwa nake ji" "Me Zaki ci?" "Ka zab'a min komai ma nikam" "To kin San Ni abinci na d'ayane idan Zaki ci sai a kawo miki" "Ai Yaya tun bana son chips ka sa na Fara son shi" Murmushi yayi yace "Barka na kinnga ko ba komai Zaki Rika yi Mana a gida" Murmushi kawai tayi Nan da Nan yasa aka kawo Mata ta hau ci, har ya karb'i spoon d'in ya Fara Bata baki. Aysha kamar zata had'iyi ranta ta Rasa abinda yake Mata dad'i tsinta kanta tayi da mikewa ta bar wurin ba tare da Tace komai ba, mardiya ma ta bi bayan ta. Haisam kuwa bai ma San sun tafi ba , Yana Nan Yana feeding princess d'insa Saida taci ta koshi ya lura ba su Nan, kallon Farukh yayi dake Kallo a wayar sa yace "Haa'ah yaushe Kuma suka tafi?" "To ka Zama Romeo ina zaka ji tafiyar su? Duk da ma na ga Kamar sauri suke don Nima ba kulani sukayi ba suka tafi" Tab'e baki yayi ya d'aga kafad'ar sa irin halin ko in kula d'in Nan ya maida kallon sa ga Ma'isha yace "Karfe nawa zaki gama lectures d'in?" "Karfe 4" "Ni Kuma sai 6 ya zamuyi Kenan? Zaki jirani ko Zaki koma da napep don bazan barki Kiri driving ba" d'an turo baki tayi Tace "sabida me Yaya?" "Umarnin daddy ne, akan Kar na barki kiyi driving sai kin Kara girma" "Yanzun wai ni yarinya ce?" "Eh Mana sosai ma Amma..... " Farukh ne ya dakatar dashi da fad'in "Malam kana da niyar Shiga lectures d'in Nan kuwa ko kuma na tafi na Barka da kanwar ka ku gama surutu?" "A a tashi muje, princess ki jirani kinji?" Kai ta d'aga Masa alamun to basu fita ba sai da ya biya su kud'in su, a tare suka fita ta nufi Lt din da zata yi lectures Suma suka nufi nasu. 'Bangaren Su Aysha Aysha Rai a 'bace ta nufi garden d'in cikin makaranta inda d'alibai sukan zauna su Sha iska, wasu suna karatu wasu Kuma hirar su suke Maza da mata. Zama tayi ta dafe kanta da hannun bibbiyu, ji take kanta ba tsarawa Kamar zai rabj gida biyu, mardiya ce ta zauna a gefen ta tana kallon ta ba tare da tace Mata kala ba. Aysha ta d'ago kanta ta kalli mardiya kana ta maida kanta kasa cikin Muryar kuka Tace "Mardiya I need your help ki taimaka min wallahi Ina son gayen Nan har cikin Raina Dan Allah give me advice" Cike da mamaki take kallon ta tunda ta Fara maganar,Baki a bud'e ta ce" Wai ke dama dagaske son gayen Nan kike?" Hararar ta tayi Tace "Eh Mana" "ikon Allah Amma ya akayi Haka bayan ranar Asabar d'in Nan kika ce min kun had'u ko dama kin San shine?" "Ba wani sanin sa nayi ba, kawai dai ina yawan ganin sa a cafe ne tun ina ji yana burgeni har naji na fara son sa, ranar Asabar d'in ne Naji bazan iya jurewa ba na tinkare sa har na samu damar karb'an Number sa" Kad'a Kai mardiya tayi had'e da fad'in "Eh lallai gayen Nan na daban ne, nifa duk tunani na shi ya tinkare ki ashe kece, Amma wallahi ba girman ki bane ki zauna kina kuka akan na miji ba, ki dube ki fa kyakkyawa dake babu na mijin da bazai so ki ba sabida kina da duk qualities na kyau" "Hmm mardiya Kenan ai wallahi duk kyawuna yau da naga yarinyar Nan na Raina Kai na, kamar ita tayi kanta,moreover ki ga yanda yake rawar jikin akanta, alamu sun nuna Yana sonta sosai" "Gaskiya Allah yayi halitta a wurin Nan,kamar ka sace ta,Amma Ni a gani na ai wannan ba babbar matsala bace ba, kawai ki mata snatching just shot your short, Amma kamin Nan ki fara tabbatar da cewar ba Soyayya suke ba tukunna" Cikin damuwa ta maraice fuska Tace "Tayaya Kenan zanyi hakan? Guy d'in Nan fa haryanzu ba wani sake min yayi ba bare har na sa ran samun soyayyar sa" "hmm Qawata Kennan, sai kace ba mace ba ai kiransa kawai zakiyi cikin dabara irin Tamu ta mata Zaki tambaye sa" "Shikenan zan kirasa zuwa anjima insha Allah" "Yauwa ko kefe, idan Kuma bamu samu yanda muke so ba sai mu had'a shi da malamai su mana maganin sa" Wata shu'umin dariya sukayi suka tafa Aysha Tace "Shegur Qawata shiyasa nake yinki ta hannun damana" Dariya mardiya tayi Tace "Sa wasa ni d'in ai ba daga Nan ba" "Tabbas Ni shaidace" Mardiya Tace "Ya labarin mutuminki?" "Wa Kenan fa?" "Wa kuwa banda Abdul" Doguwar tsaki tayi tace "Please spare me wa ke ta tashi Yanzu?" "Hahahaha Qawata ba ji,kice Haisam ke ruling yanzu" "ai fad'a ma 'batawa,shi Yana ruling anan" ta nuna kirjin ta,ta d'aura da fad'in "Shi kuma

Chapter 5 of 24