da Mamy keyi ya sanyi shi ya yatsar da addan dake hannun sa jiki na rawa yace "A a Mamy ni Wallahi banyi niyar kashe su ba, kawai inaso ne na rau nata su"
Sunusi ne yayi kansu murya na rawa yace "Suna motsi Basu mutu ba mu Kai su asibiti" Nan suka Shiga Sanya musu kaya, Basu tsaya 'bata lokaci ba sai medical center suka kaisu ,a A&E (accident & emergency) aka ajiye su, likitoci na ganin su suka ce baza su tab'a su har sai hukuma sun sa hannu, babu yanda basuyi dasu ba Akan su basu taimakon gaggawa in yaso zasu je suyi report Amma suka ki sabida Haka law yake, Faisal da Sunusi ne suka nufi motar da suka Zo dashi suka wuce Police station.
Bayan sun Isa police station d'in sukayi narrating abinda ya faru Nan take aka Kama Faisal, hankalin Sunusi yayi mugun tashi ganin ansa d'an uwan say cell.
Police d'aya aka sa suka Dawo asibitin tare da Sunusi, sai da police d'in yasa hannu kana aka Shiga basu taimakon gaggawa, Mamy Jin an Kama d'an ta tayi ta kuka, ita kuka su Ayrah kuka Sunusi ne ke ta aikin rarrashin su.
"To ya zanyi Meerah, na amince na aure Amma Wallahi gangar jikina da zuciyar ta bata aminta dashi ba har yanzu"
"Yau 5 days da bakin ku Amma na Jinjina wa Ma'aruf ya kwanta dake a gado d'aya ba tare da ya tab'a ki ba?"
" Mtsww ni Nace miki muna kwana tare? A parlor yake kwana"
" Isha kin bani kunya wallahi Sam bata tunaniin zakiyi hakan ba, tunda kin San baza ki aminta dashi ba ai da baki aure shi ba"
" Na d'auka Zan iya ne shiyasa na amince da hakan, bazan iya ce miki bana son Ma'aruf ba kuma bazan iya ce miki ina kin sa ba , I don't know what the problem is"
"Dallah malama Kar ki 'bata min Rai mu bar maganar please don wallahi ji nake kamar na daka ki wallahi"
"Ban fahimce ki ba Isha kina nufin baki bashi hakkiin sa ba, kinsan Allah na fushi da ke ko?"
Ganin tayi shiru yasa tace "Nasan kin San abinda Kika aikata ba dai dai bane Kuma wallahi sai Allah ya tambaye ki, tunda kin San bakya son sa ai da baki bari an d'aura auren ba"
" Ni nace miki bana son sa?" Cikin Muryar tuhuma
" Baki ce ba Amma actions speaks louder than words"
"To ina son sa shiyasa ma na aure sa kin gane ko? So mu bar maganar ya wurin aikin?"
"kalau" a gajarce ta bata amsa.
"Yau fa almost a week banje Naga ya Haisam ba, Wallahi Duk na Shiga damuwa"
"Laa kin tuna min ma, kin San me ya Faru?"
"A'a tell me"
" Kina nufin baki ji labarin da yake ta yawo a gari ba?"
"Umm umm banji ba, tunfa da aka kawo ni gidan Nan ko waje ban leka ba, in takaita miki ma part d'in mom kawai nake zuwa shima baifi sau uku naje ba"
"To Kar kad'a kunnen ki ki Sha labari" ta karasa maganar tana Murmushi.
Gyara zama tayi tana kallon ta a kage tace "Tell me, me ya Faru"
"Malam hassan na kwance a asibiti Rai a hannun Allah" ta karasa maganar cikin Murya kamar zatayi dariya, zaro ido Isha tayi Tace "Wani malam Hassan d'in?"
"Malam Hassan dai Wanda Kika sani"
"Tooooh me ya same shi"
"Wai Yan Mata ya Kawo har cikin gidan sa"
" Ban gane Yan mata ba?"
"To bara na fito miki a Mutum karuwai ya Kawo har cikin gidan sa, shi Kuma d'an sa ya fusata ya sassare su da Adda, yanzun Nan da nake gaya miki Yan matan sun mutu shi Kuma yaji mummunan rauni" ta karasa maganar tana dariya, Isha Tace "Meerah baki da hankali Wallahi, yanzu me abin dariya anan?"
"Komai ma, this called for a celebration Wallahi"
"Bai Kamata ace Musulmi ya Shiga tashin hankali ba Kuma kice ki tsaya kina murna"
"Wai ko baki gane maganar wa nake bane Kam?"
" Na gane mana ba mahaifin Ayrah ba, Baffan Haisam,har naji tausayin su wallahi?"
"uhmnn lallai shine har kike cewa kina tausayin su?"
" Uhmn gara ke" mikewa tayi ta d'aura da fad'in "Ni Zan wuce gida"
Itama Isha mikewa tayi ta amsa da "muje na taka miki"
Ma'aruf da tun d'azu ya shigo Yana tsaye a bakin kofa yana Jin maganar da suke musamman ma maganar sa yasa shi ya kasa Shiga d'akin yana jin suna kokarin fita yayi saurin komawa parlor ya zauna, Yana danna wayar sa.
________________________
Please comment and share
Mihaat Ce
Yar Terawa
61&62
'''Continuation.......''' cike da mamaki suke kallon sa, murya chan ciko Isha Tace "Yaushe ka Dawo?"
'dago kansa yayi ya Kuma maida kansa Kan wayar sa kana yace "Yanzun Nan shigowa na"
Meerah cikin tsigar tsokana Tace "Ango Ango kasha kamshi"
Yar karamar dariya yayi yace "Meerah manyan gari ashe kina Nan gaba ki d'aya kin kimu"
"Aaaaahhh wane ni kawai dai na baku lokacine kuci amarcin ku da kyau, Amma har sai kun gaji dani"
" Baza mu gaji ba gaskiya, so ya aikin dai?"
"Alhamdulillah, Amma ba Dad'i Wallahi aminiyata bata Nan so wurin ya Zama min so boring,ya Kamata ka bar min ita haka ta Dawo bakin aiki"
Murmushi yayi yace "Zata Dawo ai da zaharan hutun ta ya kare"
"To Shikenan, Allah ya nuna Mana"
Ya amsa da amiin, Tace "Sai anjima"
Ya amsa da "A gaida gida"
" Gida zaiji"
Tayi gaba Isha Tace "Bari na rakata"
Yace "Alright"
Har wurin mota ta rakata, sai da taga fitar ta kana ta Shigo cikin gida, ta iske shi Yana zaune a inda ya bar shi, Zama tayi yace "Ba Zama zakiyi ba ki d'auki mayafin ki, zamu fita" magana yake ba tare da ya kalli inda take ba
Tace "Ina zamu?"
'dago kai yayi kalle ta kana yace "Sayar da ke zanyi" sai ya ki cigaba da danna wayan sa.
Tab'e baki tayi ta mike ta shige ciki, bata d'auki lokaci mao tsawo ba ta dawo jikinta sanye yake da hijab, d'ago kansa yayi ya kalle ta, Murmushi yayi kana yace "Kinyi kyau "
Murmushi tayi Tace "Thanks"
Mikewa yayi yace "Mu tafi ko?" Yayi gaba bai tsaya jin abinda zata ce ba, kallon sa tayi ta girgiza kai kana ta bi Bayan sa.
Motar sa ya Shiga baka sidik Mercedes Benz sai sheko take, ganin ta nufo shi ne yayi saurin fita ya zaga ya bud'e mata kofar motar ta Shiga, ya maida ya rufe zagayawa ya kuma yi kana ya Shiga, Yana Shiga bai Tsaya 'bata lokaci ba ya sa wa motar key, tun Kan ya Isa yayi wa Mai gadi horn, da sauri ya wangale kofan Yana musu a Dawo Lafiya, suka fice daga gidan.
Kallon ta yayi kana ya maida Kan sa Akan tukin da yake, yace "Isha" cikin wani irin low voice , kallon sa tayi had'e da fad'in "Na'am"
"Kina so na kuwa?"
"Uhmn Haba Ya ma'aruf wanann wace irin tambaya ce?"
"Don't feel bad kawai akwai abinda nake so na fahimta ne"
"Uhmnn ina sonka Mana , idan bana son ka me zai sa na aure ka?"
Wani dogon ajiyar zuciya yayi bai ce mata komai ba ya cigaba da tukin sa itama ganin bai da niyar magana tayi shiru abin ta.
Ganin sun doshi hanyar FTH ne hakan yasa Tace "Kar dai yaji maganar da muke d'azu da meerah?" A zuciyar ta take ayyana hakan.
A bayyane kuma Tace "Me Kuma zamuyi a anan?"
"Gani nayi kin kwana biyu baki ga Yayan ki ba"
Kallon sa kawai tayi tana mamakin Hali irin na Ma'aruf "shi ko irin kishin Nan baya yi Kuma yasan irin soyyayar da nake yi wa Haisam?"
Muryar sa taji yana Fad'in "Nasan zakiyi tunaniin ko bana sonki ko Kuma bana kishin ki, Isha Ina son ki Kuma ina kaunar ka babban burina shine na ganki cikin farin ciki da kwanciyar hankali, n aure kine a ganina zan iya Zama wani 'bangaren rayuwar ki Amma Naga alaman hakan bazaiyu ba"
A dai dai Nan suka Shiga cikin asibitin sai da yayi parking kana ya kwantar da kansa a Kan kujera yace
"Isha" d'ago Kai tayi ta kalle sa kana yace "ko yau d'in nan Haisam ya farka in dai zai karb'i soyyayar ki sannan ya soki kamar yadda kike son sa a shirye nake da na sake ki"
zaro Ido tayi tana kallon sa, hannun yasa ya share mata hawayen da ya ke gangarowa daga fuskan ta Wanda ita kanta bata San sun zubo ba kirkirerren murya yayi "Isha I can sacrifice anything for you in this world har da ni kaina"
bud'e marfin motar yayi ya fita ya Fara tafiya, ganin ta kasa fita daga motar ne ya dawo da baya ya bud'e mata marfin motar, kallon sa ta tsayayi ya zaro idanun sa had'e da mata gwalo yace "Rankashidad'e am a I safe?" Bata amsa mishi ba sai shesshekar kukan da take, ganin bata da niyar fita hakan yasa ya riko hannun ta suka bar wajen.
ICU suka nufa, Zama yayi a waje yana jiran ta, itako Isha tafiya take kamar kwai ya fashe Mata a ciki.
Bata dad'e a ciki kamar yadda ta Saba ba, ta fito ta hango shi Yana zaune Yana latsar wayar sa, Kallon sa ta tsayayi a zuciyar ta ce "Ya Allah me nake aikatawa ne haka, Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Ma'aruf mutumin kirkii ne mai yasa ni bana son sa, gashi kyakkyawa son kowa kin Wanda ya rasa ,Astagfirullah ya Allah ka yafe min"
Ma'aruf na d'ago kansa ya hango ta tana kallon sa murmushi yayi ganin irin kallon da take Masa hakan ya nuna hankalin ta baya jikin ta, mikewa yayi cikin tafiyar a nitse ya karaso inda take, ganin bata ma San ya karaso inda take ba yayi tafi, a razane ta kalle shi yace "Kina Lafiya kuwa?"
Fashewa tayi da kuka, ta Fad'a jikin sa, rungumar ta yayi sai ta tsinci kanta da shigewa jikin sa, sai faman kuka take tana chusa jikin ta a nasa, Ma'aruf kuwa rikice wa yayi shi a ganin sa wani abunne ya sami Haisam d'in a gigice yake tambayar ta "Isha tell me what happened?" The more yana tambayar ta the more shi cries.
" Isha please tell me what happened, me ya faru ne kike kuka haka?" 'dago kanta tayi ta Kalli fuskan sa kana ta Kara rugumar sa tana kuka, "Ya Salam" Ma'aruf yace.
Ganin attention d'in Mutane ya faro dawo wa kansu ya janye ta daga jikin sa, hannun ta ya rike suka nufi motar sa, sata yayi a mota kana ya zaga ya Shiga haryanzu bata daina kukan ba.
Iska ya hura murya kamar Fad'a yace "Oh My God , could please stop crying, Isha bana jin dad'in ganin ki a haka ki Fad'a min abinda ke damin ki Mana" ta tsorata da yanayin da ta gansa hakan yasa tayi shiru tana kukan kasa kasa, ganin Bata da niyar magana ya sa wa motar key.
Kai tsaye gida suka nufa, a parking lot yayi parking, cire key d'in yayi ya shige cikin gida rai a 'bace da sauri tabi bayan sa , ganin yana kokarin haurawa bedroom da sauri ta nufi inda yake ta rungume shi ta baya, tana kuka mai tsuma zuciya, tsayawa yayi chak ya kasa motsi, Yana Jin kukan ta har cikin ransa shima hawayen ya fara zubarwa yana cizan leb'en sa.
Cikin Muryar kuka Tace "Am sorry, am sorry Dan Allah ka yafe min" rike hannunta yayi had'e da juyawa yana fuskantar ta yace "Isha Ni fa babu abinda Kika min ki daina kukan Nan haka please" Yana mai share mata hawaye Tace "Bazan daina kuka ba har sai ka yafe min"
"Sai na yafe Miki?" Cike da rashin fahimta ya mata tambayar.
'dago kanta yayi yace "Look at me Isha babi abinda Kika min ko da ma kin min to Wallahi na yafe miki duniya da lahira" fashewa Tayi da kuka tana fad'in "Ina son ka mijina Dan Allah ka yafe min, na kasan ce ba mace ta gari ba a gare ka, na kasa sauken hakki ka dake kaina"
Shima rungumeta yayi Yana juya ta tamkar suna rawa , Murmushi yayi Mai d'an sauti yace "Wannan shine yasa kike kuka" Kai ta d'aga alamun eh, yace "Kar ki damu when ever you're ready ina Nan ina jiran ki, ban damu ba by The way bamu fa Kai sati ba so take your time Nasan abinda kike ji"
Janye ta yayi daga jikinsa yana kallon fuskan ta jaaan hancin ta yayi yace "Cry cry baby Duk kin tada min hankali na d'auka wani abune ya Faru"
Cikin shesshekar kuka Tace "Yanzu Dan Allah baka fushi dani?"
Murmushi yayi yace "ko kad'an"
Kallon kallon suka shigayiwa junan su, ko wannnen su da abinda yake rayawa a ransa.
A hankali yake kusanto fuskar shi da na nata, had'e kansu yayi wuri guda suna jin numfashin shin junnan su sun d'auki tsawon dakika 6 a haka, tsintan Kan su sukayi suna sumbatar junan su, a hankali suke Shan bakin junan su, sun dad'e a haka, a tare Kuma suka janye bakin su suna wani irin numfashi yanda kasan sunyi gudu ne.
Hannun ta ya rike suka shige bedroom d'insu, a Kan gado ya zaunar da ita, ya shige bathroom yayi wanka, Bayan ya fitone itama ta shuga, Bayan ta fito ne ta hango shi Yana ki shin gid'e a Kan gado daga shi sai Vest da gajeren wando, d'ago Kai yayi ya kalle ta, jikinta ya ke bi da kallo daga ita sai towel, zumbur ya mike ya nufe, Sa hannu yayi ya raba ta da towel d'in jikin ta, rintse ido tayi, Murmushi yayi ya sa hannu ya d'auke ta kamar wata Yar Baby, Akan gado ya dirar da ita Nan ya Shiga raba kansa da kayan dake jikinsa, niko ina ganin hakan nayi saurin barin d'akin na ja musu kofa, Nace bari na leka asibiti Naga a wani hali su malam Hassan suke. asha Amarci Lafiya.
"Sister nifa gaskiya na gaji da yawon asibitin nan kullum Kenan mu muna hanyar asibiti, gashi Yan iskan Nan sun hana mu komawa makaranta wai strike"
Murmushi Ayrah tayi Tace "Sunusi Kenan to yanzun me kake nufi? Zuwa asibitin ne baka so ko Kuma haushin ASSU kake ji?"
" Duka" yace a takaice, Nabila Tace "Ni kaina na gaji Wallahi, kullum asibiti kullum asibiti"
"To ai rashin Jin Faisal ne ya ja mana hakan, gashi Nan Yana chan a tsare na tabbata ba sake shi zasuyi Nan kusa ba"
Nabila Tace "Nifa yamin dai dai Wallahi"
Sunusi yace "To yanzu wa gari ya waya? Kin San dai hukunci Wanda ya kashe shine a kashe shi ko?"
Cikin Muryar kuka Ayrah Tace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un wannan masifa dame tayi Kama?"
Sunusi girgiza kai yayi ya fice abinsa , Nabila ganin Ayrah ta Shiga tashin hankali sosai Tace "Sister ya labarin Adnan ne Kam?"
Hannun tasa ta share hawayen dake fuskan ta kana Tace "Yana Nan, kin San tun lokacin da yaji labarin aurena da Haisam ya rikice babu yanda baiyi dani ba Akan Kar na Masa hakan, na so na Fad'a Masa plan ne Amma na kasa gudun karya tarwastsa Mana shiri"
" To yanzu ya ake ciki?"
" Ya daina kulani babu yanda banyi dashi ba Amma yaki kulanai shiyasa na hakura Amma to my surprise jiya ya turo min da wani sakon da ya tsorata ni"
Zaro wayar ta tayi a d'an karamin purse d'in dake hannun ta ta Shiga text d'in ta Mika wa Nabila ta fara karanta shi kamar haka.
"Na tabbata kina cikin tashin hankali Sabida iftila'in da ya dirin muku a gida, Allah Kenan baki ga komai ba this is just the beginning"
Nabila kallon ta tayi kana Tace "Me yake nufi da hakan?"
Tab'e bako tayi Tace "I don't know Wallahi, and I love this guy so much"
Muryar Mamy taji tana fad'in "Kwarai kuwa baki ga komai ba ko ince bamu ga komai ba, Ai Allah ba azzalumin bawan sa bane ba, sai Wanda ya zalunci kansa bare Kuma Kun tab'a maraya, yau tsawon shekara nawa haisam yake kwance rai a hannun Allah, ai naso da yana Raye yaga halin da mahaifin ki ya shiga kuma Wallahi masifa da bala'i yanzu kuka Fara gani, gashi chan Faisal shima taurin Kan Nasa abinda ya jaa wa kansa"
Nabila Tace "Haba Mamy maganganun ki sunyi tsauri dayawa Kar ki manta fa ke uwace, Mamy idan uwa tana yawan sawa d'anta Albarka tab'arbarewa yake bare kuma kin Masa mugun fata Dan Allah, Mamy ki Mana addu'a Allah ya Kawo Mana d'auki"
" Ni bazanyi musu mugun baki ba, Sannan ni bazan musu addu'a ba" tana kaina ta fice daga gun, ta shige d'akin Malam Hassan, hawaye ne ke gangarowa daga idanun sa kallon sa tayi ta jaa wani uban tsaki Tace "Nasan maganar da mukayi ne da yaran Nan yasa kake kuka to Wallahi baka ga komai ba, Duk Wanda yaci Amana to ba Makawa amanar Allah zata ci shi." Ta jaa kujera ta zauna ta d'aura kafa d'aya akan d'aya ta Shiga danna wayar ta.
Malam Hassan kuwa tunda wannan abin ya same shi ya daina magana, sai dai Ido kawai.
Tun daga Wannan ranar Isha da Ma'aruf wani soyyaya mai karfi ya shiga tsakanin su kullum a like suke da juna idan kaga sun rabu to ya fita office ne, a haka har suka gama cin amarcin su, har ta koma bakin aikin ta, sannan lokaci zuwa lokaci ta kan je gidan Umma ko kuma gidan Mummy wasu lokutan Kuma tare da Ma'aruf d'in suke zuwa.
Mardiya kuwa,tun ranar da ta kai musi abinci bata sake Shiga part d'insu ba,idan sun had'u a gun Mom sukan gaisa, kawancen nata da Ayrah tayi baya sosai ba kamar da ba kasantuwar Ayrah idan bata gun aiki to tana gun mahaifin ta, Itace Kad'ai take kula dashi Mamy kuwa da ta gaji da jinya gidan su ta koma, Ni ko Nace Anya Mamy bata d'auki zafi dayawa ba kuwa?
*AFTER SOME MONTHS*
Meerah ce ta Kawo wa Isha ziyara , Bayan sun gama hirar su ne suka fito tare har gun motar ta ta rakata, suna tsaye suka hango motar Ma'aruf parking yayi ya fice a motar yazo inda suke, Bayan sun gaisa ne ya ce "Barina na shiga part d'insu mom Dad ne ya dawo"
"okay Nima gani Nan shigowa yanzu"
"Okay ya shige ciki"
Yana wasa da key d'in motar dake hannun sa,Isha binsa tayi da Kallo tana Murmushi , Meerah Tace "Wannan kallon fa?"
"Hmm Bangane ba mijina ne fa"
"Oh sai yanzu Kika San cewa mijin kine ko?"
" Tun da dad'ewa Nasan da hakan"
"Uhmnn manyan Mata, Amma naji Dad'i Gaskiya da Kika kwantar da hankalin ki no wonder Mana Naga sai Fresh kike kina kyau, Anya ma ciki kike dashi ba?"
"Dallah malama bana son sa Ido...... " Motar Mardiya ce ta shigo ta faka, Bayan ta fito wurin su ta nufa, Isa wurin su ke da wuya suka jiyo wani uban Kara, juyawan da zasuyi suka hangi part d'insu Mom ne yake ci da wuta ga Warin gas ya maimaye gun gaba ki d'aya.
Dukkanin su babu Wanda ya Isa mosawa a gun, suna Tsaye suna kallon ikon Allah, Mai gadi be ta fito daga ban d'aki hannun sa rike yake da buta yana kokarin d'aure mazargin wandon sa, Yana fad'in "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, ba kowa a ciki ko?"
Nan ne fa Isha ta d'aura hannu a kai ta kwarma wani uban ihu, ta yanke jiki ta Fad'i , Mardiya kuwa suman tsaye tayi daga bisani ta Fad'i sumammiya, Meerah kuka ta shigayi tana nemon taimako.
________________________
Rashin comment d'inkune yasa jikina Duk ya mutu da typing d'in,Dan Allah ku bani had'in kai Nasan Kuma Kun kosa da kuji yadda labarin zai kasance
Please Comment and share
Milhaat ce
Yar Terawa
63&64
'''Continuation.....''' da gudu Mai gadi ya nufo su, Yana ta ambaton Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, Nan da Nan jama'ar unguwa suka Fara shigowa cikin gidan kowanne da abinda yake tufawa.
Fire service aka Kira ,basu d'au wani lokaci Mai tsawo ba suka iso , suka Shiga kashe wutan, Isha da Mardiya kuwa a motar Meerah aka sasu sai asibiti.
Bayan wutan ya d'a tsagaita suka Shiga ciki don duba 'barnan da wutan yayi, Mutum uku suka gani a parlor, Mutum biyu suna zaune a kujera Wanda Mom da Dad ne, yayin da d'ayan Yana kwance a kasa shine Ma'aruf. Nan aka Shiga fitar da gawakin su a waje kowa ya jinjina al'amarin cike da tausayi suke ta kallon su,yayin da masu saurin kuka Kuma sai kuka suke suna yabon hayyyan su musamman ma Dad da Ma'aruf.
Bayan sun Isa asibiti, taimakon gaggawa aka Basu, yayin da Meerah ta Kira Dad ta Sanar dashi abinda ya faru, anyi sa'a Yana gari, a lokacin suna gidan Umma shi da Mummy, a razane ya mike zufa na keto Masa, mummy da Umma a tsorace suke tambayar sa abinda ke faruwa, Daddy kallon Abba yayi kana yace "Zo muje" ya fice Abba kuwa yabi Bayan sa ba tare da yaji inda zasuje ba, bin Bayan su sukayi suna tambayar ko Lafiya.
Daddy waigo yayi cikin Murya kamar Fad'a yace "Ku koma ciki" Jin yanda yayi maganar Umma ta riko hannun Mummy suka koma ciki, motar daddy suka Shiga.
Daddy ne yake jaan motar, a hanyar ne yake Sanar dashi abinda ya faru, Banda ambaton sunan Allah babu Abinda yake har suka isa asibitin dasu Isha suke, suna dosan d'akin da Isha take suka jiyo ihun ta cikin Muryar kuka take fad'in "Dan Allah ku sake Ni, Meerah Ma'aruf fa wayyo na Shiga uku" Meerah itama kukan take Amma bata sake ta ba, da taimakon wata nurse suka rirrike ta, Isha na ganin su Abba da Daddy da dukkanin karfinta ture su ta nufi inda suke cikin kuka Mai sautin gaske, tana fad'in "Daddy Mijina na Shiga uku" ta maida kallon ta ga Abba tana fad'in "Abba ya mutu ko? Shikenan Shikenan na shiga uku, yanzun Nan fa mukayi magana dashi, Innalillahi wa ilaihirraji'un"
Daddy ne ya rungume ta Yana fad'in "Ya isa Isha ki daina kukan hakan"
Amma kamar cewa yayi ta Kara kukan ne, Abba waje ya fita yace su Umma suzo asibitin, Amma bai Fad'a musu dalilin kiran suba.
Isha tafi Mintuna talatin tana kuka, Abba da Daddy suna rarrashin ta, Meerah kuwa ta rakub'e a gefe itama kukan take sosai, Su Mummy suna shigowa suka halin da take ciki, cike da rashin fahimta suke kallon su.
Abba ne ya Sanar dasu abinda ya faru, mummy fashewa tayi da kuka da zaran ta kalli Isha sai ta fashe da kuka, Umma ma kukan take, Isha mikewa tayi ta rungumi Umma tana kuka.
Meerah fita tayi bata dad'e ba ta dawo hannun ta rike yake da goran ruwa Tace "Umma ki bata tasha, ko zata d'an ji sanyi" tayi maganar cikin sanyin Murya da jin tausayin kawar ta.
Dakyar da makyar kyasa Isha ta Karb'a tasha, bata d'auki mintuna biyar ba ta fara Jin jiri, Umma na ganin hakan tayi saurin kaita Kan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 24