blindly did what he ask to do"
Nabila Tace "Sunusi didn't you heard the story since from the beginning? Bata fa San komai akai ba, and ni ina blaming Mamy ma for not telling her the truth since from day one"
Sunusi yace "Uhhh here you go again look sis Nabila Mamy bata da laifi had it been lokacin da Dad ya Fad'a mata abinda zatayi ta Sanar da Mamy ai da zata hanata Amma ta boye mata gaskiya"
Faisal yace "Ya Isa please this is not the solution here, fad'in wa yake da laifi ko baiyi da laifi duk bai taso ba, sabida bazai amfane mu da komai let the bygones be gone please" ya karasa maganar yana hard'e Hannayen sa alamun roko.
Shiru Sukayi na d'an wasu lokutan Babu Wanda yace komai sai kukan Ayrah dake tashi a d'akin Faisal ne ya matso kusa da ita ta durkusa, handkerchief ya ciro daga aljihun sa ya Mika mata had'e da fad'in "Please ki daina kuka hakan ya Isa Dan Allah karfa ki ja wa kanki wani matsala"
Cikin shesshekar kuka tace "Faisal idan banyi kuka ba mezanyi kaina ya kulle duk duniyar bata yimin Dad'i"
Yace "Ki fawwala wa Allah komai Insha Allah komai zai dai daita"
Ciza le'be Sunusi yayi yace "Wato a cikin Haram aka Haife mu haryanzu kuma muna cikin ta Allah ya isan mu Wallahi......." kallon da Faisal yayi masane yasa ya shiru.
Mardiya na Isa gida da murna ta Shiga d'akin Yayanta ta Sanar dashi cewar zancen auren sa da isha na nan yace "Idan na Kira ta naji akasin hakan fa?"
Shiru tayi na d'an wasu sakonni kana tace "Ka d'auki Duk matakin da ya Dace"
Yace "Okay" had'e kiran Layin Isha,duka biyu ta d'aga da sallama ajiyar zuciya yayi yace "Na d'auka na rasaki"
"Uhmn baka rasani ba,Ina mardiya ta Isa gida kalau?" Kallon mardiya yayi kana yace "Eh kalau gata Nan ma muna tare"
"Okay ka gaida min ita"
Ya amsa da " tana amsawa" Nan ya fara Jan ta da Hira tun bata kulashi har ta saki jikin ta Sukayi ta Hira.
Da Yamma
Ma'aruf ne zaune da Mummyn sa da Daddyn sa suna ta shirye shirye Don a yau suke so sukai kayan lefe,Daddy tace "Yauwa Babana Nikam ya batun gidan naka ne an gama had'a komai ko?"
"eh dad an gama had'a komai"
Mummy Tace "Dan Allah yallab'ai ka bar min su anan tunda ka chan part d'aya ba kowa su zauna in yaso daga baya su zauna a Chan"
"in dai ya amince da hakan ai bani da matsala"
Kallon Ma'aruf yayi Yar karamar dariya yayi yace "mummy irin wannan Kallo haka?"
"Eh so nake naji ta bakin kane ko bakaji maganar da muke bane?"
"naji Mummy yanda kikace Haka za'a yi"
Murmushi kawai tayi suka cigaba da abinda suke.
Lefe ya had'u iya had'uwa in tsaya muku bayanin sa 'bata lokaci ne sabida haka just imagine it in your imagination,su Umma ne Kan gaba an karb'i baki yanda ya dace sai dai muce Allah ya nuna mana ranar biki.
*WASHE GARI*
Ma'isha tun da ta farka tayi sallah Bata Koma ta kwanta ba, had'a kayan ta tashigayi har sai da gari ya soma haske ta gama ban d'aki ta fad'a tayi wanka a gurguje sabida karfe 8 na safe jirgin su zai tashi, bayan ta gama shirine ta sauko kasa hannun ta rike yake da handbag d'inta d'ayan Kuma d'an madaidaicin akwatin ta take jaa, Driver da tun d'azu ya kai kayan Mummy mota yayi saurin zuwa ya karb'i akwatin natan yasa a jaka.
Mummy da Daddy da hango suna saukowa daga stairs ya rungume ta a jikin sa suna tafiya suna Hira had'e da dariya gyaran murya Isha tayi kana ta sunkuyar da kanta a kasa.
Murmushi daddy yayi had'e da fad'in "Har kin fito?"
Ba tare da kalle sa ba ta amsa da "Eh Daddy Good morning"
Ya amsa da "Morning" kallon Mummy yayi yace "Naso na kaiku Airport da kaina Amma Kuma zamuyi baki Kuma 8 ne yakamata mu had'u"
" Bakomai Alhaji gaba da yawa fatan mu shine mu Isa Lafiya kawai"
" To Hajiya Allah ya kaiku Lafiya ya Dawo daku Lafiya"
Ta amsa da "Ameen"
Ta d'aura da fad'in "Muje ko Isha? Driver na jiran mu dafan ba kiyi mantuwa ba?"
"Eh mummy banyi mantuwa ba, Amma ina Umman take ban ganta ba ko zamu biya mu d'auke ta ne?"
" A'a Umman Ku baza taje ba"
'dan Turo baki tayi Tace "To Amma mummy mai yasa haka bayan tafiyar Nan da ita aka shirya?"
" Gashi Nan ki tambaye shi da Abban kune suka Hana" tana nuna Abba had'e da tab'e baki.
Turo baki Isha tayi had'e da d'an buga kafa tace "Daddy why?" Ta karasa maganar kamar zatayi kuka.
Yar karamar dariya yayi yace "wato Hajiya so kike ki had'a min wuri ko? Daughter idan Umman ku ta tafi wa zai kula da yaran? Abban ku baya nan Kinga bazai yu a bar su da masu aiki bako?"
"But daddy 2 days fa kawai zamuyi"
"Yeah I know kawai kuje da mummyn naku, kinji kiyi hakuri"
Ba don tasa ba tayi shiru bubbuga kafa ta Shiga yi had'e da fita waje, motar ta fad'a, ta zauna had'e da rungume hannun ta sai faman Turo baki take, Mummy a gefen ta tazaun, Driver ya kunna wa motar wuta kai tsaye airport suka nufa, Basu dad'e da isa ba jirgin su ya Lula a sararin samaniya Nigeria to Turkey.
Bayan sun Isa ne a ranar hutawa sukayi basu fita ba sai washe gari suka fita, tun da suka fita basu dawo ba sai yamma liss, washe gari ma hakan Sukayi a takaice dai kwanaki uku sukayi sabida basu samu damar gama sayayyar tasu ba, sai a rana ta hud'u suka koma gida.
Yau saura 3 days biki shiri ake both families, sosai suke shiri ba kakkautawa, Isha dai sunan zatayi aure ne amma Sam bata farin ciki da auren babu abinda tayi na gyara jikin, Umma ce ta zage dantse wurin ganin ta gyara yar ta.
A yaune dubannin Mutane suka shaida Auren Ma'aruf da Ma'isha, Bayan an d'aure aure walima akayi a gidan su Amarya, karfe 8 na dare aka kaita d'akin mahaifin ta nasiha ya mata sosai mai Shiga jiki da fatan Allah ya basu zaman Lafiya, mummy Kam kasa magana tayi tana kuka Isha na Kuka rungumar ta tayi tana fad'in "Daba don aure ba babu abinda zai rabani da ke 'yata Allah ya miki Albarka ya baku zaman Lafiya" karar motoci suka fara ji alamun an Zo d'aukan Amarya Nan take sautin kukan Isha ya Karu mummy na taya ta Umma ma Saida ta zubar da kwalla, dakyar ta 'ban'bari Isha a jikin Mummy aka sata a mota , Mummy,qawayen Mummy Guda biyu,da Meerah da kawayen Isha guda biyu na wurin Aikin sune suka Rakata har gidan ta.
Umma nasiha ta Kuma mata tana mata fad'a akan tabi Mijinta sau da kafa, wani sabon babin kuka ta bud'e ganin Umma zasu tafi su bar ta, Dakyar ta bari suka fita aka barta da ga ita sai kawayen ta.
Karfe goma da Yan Mintuna Ango ya shigo tare da abokanan sa bakin su d'auke da sallama suka amsa ba 'bata lokaci sukayi duk wani abinda al'ada ya tanadar kana suka fice, Ma'aruf raka su yayi har gun motar su, Cikin kawayen ta babu wacce ta fito da motar ta hakan yasa Dole sai sun Kai su gida.
Sai da yaga fitar su kana ya shige part d'insu, Zama yayi kusa da ita a hankali ya d'aga mayafinta, wani ajiyar zuciya ya sauke had'e da fad'in "Alhamdulillah Allah na gode ma ka da ka mallakamin wannan kyakkyawar baiwa taka" Isha lokaci guda ta tsinci kanta da jin haushin sa, surutan sa yayi tayi bata tanka Masa ba, ganin bata da niyar kulashi sai yayi tunanin ko kunyar sa take ji, hakan yasa umurce ta da taje tayi alwala bata Musa ba ta Mike ta shige ban d'aki ta d'auro alwala bayan ta fita shima ya Shiga Bai dad'e ba ya fito sallaya ya shimfida musu Sannan ya jaa su sallah bayan sun idar da sallan ne ya dad'e yana roka musu zaman Lafiya a gun mahaliccin su sannan ya mata Duk wani tambayar da ya kamata Ango yayi wa Amaryar sa a, dukkannin tambayar da ya mata ta bashi amsar su dai dai yadda ya Dace hakan yasa yaji ta Kara Shiga ransa.
Ledan kajin da suka shigo dashi ya janyo ya ajiye a gaban ta mikewa yayi ya nufi kitchen bai dad'e ba ya shigo hannun sa d'auke yake da plate sai Kuma glass cup, da kanshi ya fara bata abincin Duk da taso tayi masa rigima, sai da ta koshi kana ya tsiyaya mats yogurt ya bata tasha kana shima ya sakar wa cikin sa shima.
Plate d'in ya mayar kitchen parlor ya nufa ya sa key kana ya dawo d'akin ganin ta yayi har ta kwanta, Canza kayan jikin sa yayi ya Sanya jallabiyar sa shima ya haura Kan gadon, hannunta ya rike kana yace "A haka zaki kwanta?"
Tace "Eh" a takaice
"Amma kayan Nan basu miki nauyi ba?"
"Basu yi ba"
" A a dai bari na rage miki su" hannu yasa zai tab'a ta da saurin Gaske ta Dirko daga Kan gadon tana kallon sa, cikin rashin fahimta yace "Isha Lafiya?"
Cikin Muryar kamar fad'a Tace "Me kake shirin aikatawa ne?"
Murmushi yayi kana yace "Babu komai kwanta abinki babu abinda zan Miki"
Gani kawai yayi ta d'auki Pillow da bargo ta nufi hanyar fita da sauri yasha gaban ta had'e da fad'in "ina kuma Zaki?"
"Zan bar maka d'akin ne, don ni gaskiya bazan iya had'a jiki da Kai ba"
Cikin sanyin Murya yace " Amma meyasa Isha Kar ki manta fa ni mijin ki ne ina da iko Akanki"
Fashewa tayi da Kuka Tace "Dan Allah kayi hakuri ban shirya ba"
"Kar ki damu ni bazan miki Dole ba, Kuma Dama ba dalilin da yasa na auri ki ba Kennan soyyayar da nake miki yasa na aure ki zan iya jiran ki har zuwa ranar da Kika shirya" sa hannu yayi karb'i pillow da bargon dake hannun ta yace "Je ki kwanta ni zan kwana a parlor" Yana Kai Nan ya fice abinsa.
Isha jikinta ne yayi sanyi tabbasa tasan bata kyauta masa ba, tunda Yana da hakki akanta Amma fa alkawari ta d'auka wa kanta babu wani mahalukin da zata bashi kanta in ba Yayan ta ba, da wannan tunanin ta kulle kofar ta koma ta kwanta abinta.
Ma'aruf kwance yake Akan kushin ransa Duk ba Dad'i a bayyane yace "Yau fa ranar da na dad'e ina jira Kenan Amma a parlor zan kwana, hmm bazan miki Dole ba Isha sabida nasan halin da kike ciki" tunani kala da iri yayi tayi har dare ya raba ya kasa bacci, ji yayi bazai iya hakura ba, mikewa yayi ya nufi d'akin da Isha take Wanda shine d'akin su Tura kofar yayi yaji ta a rufe Murmushin takaici yayi kana ya juya ya koma ya kwanta a haka bacci 'barawo yayi awun gaba dashi.
_________________________
Masu tambayar complete book d'in Nan Babu pls sabon book ne
Milhaat ce
Yar Terawa
https://www.wattpad.com/1248497695?utm_source=android&utm_medium=link&utm_content=share_published&wp_pageb=create_on_publish&wp_uname=Milhaat&wp_originator=yyYOiPWOf9d70htdRqg7I1%2F4ucy6HsOlgByapt3Dnb2JGUd5QVGMPXeC%2Bp0YdiBDdt6TP4swRtJhg2tXkbgWfc9O3T2b4yf1jRUCMIvqFOmhE71dThk0eS8%2FT5G%2F00JG
🍃 *DANGIN UBANA*🍃
Story & Written
By
Milhart
Na zo muku da littafi Mai ban tausayi,cike da abun al'ajabi,wannan salon na daban ne.
*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
*M. W. A*
*Wannan labarin kirkirarren labarine ban yarda a chanza min labari ba Wanda ya chanza bamu yafe ba.*
Ina alfahari da rubutu,sabida alkalami yafi takobi🗡️🗡️🗡️
*BISMILLAHIR RAHAMANIN RAHIM*
Page
59&60
_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._
*WASHE GARI*
Alarm d'insa ne ya fara bugawa mikewa yayi ya kashe, d'akin su ya nufa ya Shiga babbuga mata kofa, zumbur ta mike a d'an tsorace, bedside lamp ta kunna kallon d'akin ta shigayi tana mamakin a wani d'aki take, sunan ta da taji ya Kira ne kamar rad'a yasa ta kalli kofan shiru Bata komai ba, a karo na biyu ya Kuma cewa "Isha!!!
Cikin Muryar bacci Tace "Na'am"
"d'an bud'e kofar asuba tayi"
Mikewa tayi jiki ba karfi ta bud'e Masa kofar,Kan gado ta koma ta zauna shi Kuma ya Shiga ban d'aki,alwala yayi Bayan ya gama ne ya fito ya wuce Masallaci ba tare da yace Mata uffan ba.
Itama mikewa tayi ta Shiga ban d'aki tayi alwala ta shimfid'a sallah ya Shiga yin sallah,Bayan ta idar ta zauna Akan sallayar tana azkar.
Ma'aruf Kuma bai dawo cikin gidan ba har sai da gari ya fara haske,ya Shigo har cikin d'akin bakin sa d'auke yake da sallama,tana zaune akan sallaya, d'ago kanta tayi ta kalle shi suna had'a ido ta kawar da kanta a hankali, amsa sallamar sa tayi had'e da fad'in "Ina kwana"
Ya amsa da "Lafiya how was your night?"
Tace "Alhamdulillah" had'e mikewa,sallayan ta nad'e kana ta Shiga ban d'aki, Jin saukar ruwa a shower ne yasa ya fice daga d'akin,Bayan ta gama ne ta leko taga baya d'akin fita tayi cikin sauri ta nufi kofar ta sa key.
Gaban Mirror ta nufa ta zauna,kallon kanta tayi a mirror ko me ta tuna Naga ta girgiza kai had'e da Yar karamar dariya mai d'an sauti,Mai ta Shiga shafawa a jikin ta Bayan ta gama ne ta ciro kayan da zata sa, Riga da skirt d'in atamfa ta sanya a jikin ta, ba tayi wani kwalliya ba powder ta shafa sai kwallin da ta saka a idon ta sai lip glow.
Fita tayi daga d'akin, parlor ta nufa kallon d'akin ta tsaya yi tana ganin kokarin iyayen nata had'e da sa musu Albarka, komai na d'akin Royal Blue ne da Sky blue ya haska d'akin sosai ga wani uban kamshi da d'akin keyi.
Motsin da taji ne yasa tayi saurin maida kallon gun, a hankali take ta fiya har ta Isa kofar da take jin karar,a hankali ta Turo kofar had'e da kusa kanta ciki, kallon kitchen d'in ta tsaya yi tana Murmushi,ta shagala da kallon kitchen d'in har ta manta dalilin da yasa ta Shigo.
Ido hud'u sukayi,kallon kallon suka Shiga yi wa juna,wani irin kallon yake binta dashi ganin yanda tayi matukar kyau Duk da ba wani cika take dashi sosai ba kayan yabi jikin ta,kamar a jikinta aka d'inka shi.
Ganin kallon da yake mata yayi yawane yasa tayi sauri juyawa da niyar fita cikin Murya mai sanyi yace "Isha!!!
A hankali ta juya tana kallon sa murmushi yayi kana yace "Kinyi kyau" Murmushi itama tayi had'e da fad'in "Thanks" ta juya zata fita yace "Hold on mana" ajiye spoon d'in dake hannun sa yayi ya nufe inda take hannun ta ya riko ya jaa ta izuwa gun gas cooker da yake girki da ita.
Marfin tukunyar ya bud'e yace "Look Waifa gwanin ta zan miki Kuma sai naga baiyi yanda nake gani idan Mama tayi ba"
Isha kusa dariya ta Shiga yi Tace " Me ne wannan d'in?"
"Bakya gani Irish potatoes ne"
"Eh na gani ina nufin me kake son girkawa?"
"Chips Mana ai tunda kwanaki ka ka fad'a min kina son chips sosai sai na kudiri aniyar yi miki shi da kaina"
Dariya take yi sosai shi Kuma ya rungume hannun sa yana kallon ta cikin Muryar dariya Tace "chips fa kace" ya ama da "Eh Mana"
Dariya ta kumayi Tace "ba dai chips ba sai dai pourage" yace "Pourage Kuma gwate kenan fa?"
"eh Mana ina ka tab'a ganin chips haka,ai da ka dage ka koya Kan irin ranar Nan tazo"
" Uhmn Gaskiyar ki,ai ni yanzu ma gani nake kamar mafarki nake" Jin abinda yace ne yasa ta daina dariya kamar anyi ruwa an d'auke Tace "Ban gane kamar mafarki ba?"
"Umm na d'auka bazan tab'a samun ki ba Isha" Murmushi tayi Tace "Kasan mene ne?"
Yace "A a sai kin fad'a"
Sauke tukunyan tayi kana Tace "bari na nuna naka yanda akeyin chips sabida gaba" Kai ya d'aga had'e da fad'in "to"
Nan ta Shiga fere Irish d'in shima wani wukan ta d'auko Yana Taya ta ,sai ta fere biyar bai fere d'aya ba tayi ta dariyar su sunayi suna Hira sama sama,Bayan sun gama ta soye shi had'e da soya kwai ta d'aura a gefe, a tare suka kai abincin dinning,zama yayi tayi serving d'insu suka fara ci.
Bayan sun gama cin abincin a tare suka kai kitchen, a parlor ta zauna da niyar Kallo taji yace "d'auko mayafin ki mu shiga mu gaida su Mom"
Mikewa tayi had'e da fad'in to, d'aki ta shiga ta d'auko hijab dinta har kasa, tana fitowa suka wuce part d'in su Mom, da sallama suka shiga mom ce na gani a tsaye ita da Mardiya.
Baki a bud'e take kallon su Tace "Har kun tashi? Yanzu fa na ke cewa yarinyar Nan ta kai muku breakfast"
Neman wuri yayi ya zauna had'e da fad'in "ai mun karya"
"Shine kasa 'yata girki daga zuwan ta?"
"A a ni nayi girkin fa"
Mom kallon Ma'isha tayi Tace "Wai hakane?"
Murmushi tayi kana Tace "Na daiyi Mom"
"Yauwa nasan za'a Rina"
Kama baki yayi yace "Lallai bakya tsoron Allah ina laifin ma kice mata tare mukayi?" Dariya kawai tayi Bata ce masa komai ba, mom Tace "Sai ka nemi wuri ka zauna ka bar ta a tsaye"
Gyara Zama yayi kana yace "Yan zun Nan fa Kika ce Yar kice meaning ba sai ance Mata ta zauna ba tunda a gidan su take ko?"
Tab'e baki Mom tayi, zuwa tayi ta riko hannun Isha ta zaunar da ita, Ma'aruf kallon Mardiya yayi cikin Murya kamar fad'a yace "Ke baki iya gaisuwa bane? Ko baki ga Mutane bane?"
"Uhmn Yaya Kenan ai gani nake kamar Duk Kun manta dani shiysa, ina kwana?"
Ya amsa da "lafiya"
Maida kallon ta ga Isha tayi taace "Ina kwana Aunty Isha" Murmushi tayi had'e da fad'in " lafiya Lau kin tashi lafiya?"
" Lafiya ya Amarci?" Murmushi kawai tayi bata ce Mata komai ba, kallon da Ma'aruf ya mata ne yasa ta ajiye food flask d'in dake hannun ta , had'e da kokarin barin gun.
Mom ce Tace Mata "Ya haka Kuma anan Zaki bar min abincin? 'dauka ki Kai musu part d'in su"
Cikin sauri ta d'auka ra fita.
Ma'isha har kasa ta durkusa Tace "Mom ina kwana?"
Cike da fara'a ta amsa da "Lafiya Lau ya kwanan bakonta?"
Murmushi tayi had'e da fad'in "Alhamdulillah"
Ma'aruf ma gaishe ta yayi Bayan sun gama gaisawa yace " Dad ya fita ne?" Ta amsa "Yana d'akin sa , ku shiga ku gaishe shi" mikewa yayi had'e da kallon Ma'isha yace "Zo muje" mikewa tayi Sim sim tana binsa a baya, d'akin Dad suka nufa Bayan sun gaishe shi ya musu nasiha da fatan Allah ya basu zaman Lafiya Mai d'aurewa, Nan suka tashi suka koma part d'insu kasantuwar Mom bata parlor d'in.
"Mamy yanzu haka zamu zuba Ido muna kallon Daddy yana abinda ya ga dama a gidan Nan ki duba kiga yau ma ya shigo da mace" Faisal ke wannan maganar.
Sunusi yace "Mata dai ai su biyune yau Kam"
Faisal yace "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un, that's it Wallahi yau d'in Nan zan yi maganin Yan iska" ya mike Yana huci yayi d'akin sa.
Mamy kallon sa kawai tayi ta kawar da kanta, Sunusi yace "Mamy Wai baza kice wani abu bane ba?"
"To me zance muku tunda ku kuka Haife Ni bani ce na haife kuba na fad'a muku ba sau d'aya ba ba sau biyu ba Akan Ku bar zancen Nan Amma kunki, ina guje muku fushin uban kune, Duk lalacin sa fa shine mahiaifin ku ya Kamata ku San da wannan"
"Amma Mamy........ " Wani irin ihu sukaji ya d'auki cikin gidan Duk su biyun a razane suka mike, Ayrah da Nabila ko wacce da gudu ta fito daga d'akin su suna son ganin mene ne ke faruwa.
Sunusi yace "Mamy kamar ihu na ji ko?"
"Eh Nima naji"
Wani ihun suka Kuma ji wannan karon Muryar mace ne take kuka had'e da ihu, Ayrah Tace "Kamar daga d'akin Daddy ne" Nabila Tace "Eh daga d'akin sane"
Mamy ce ta haura da saurin Gaske Suma suka bi Bayan ta,Kai tsaye d'akin ta fad'a ba tsuman tsaye tayi tana kallon sa.
Faisal Ne hannun sa rike da Adda jikin sa duk jini sannan malam hassan da Yan matan Nan Guda biyu suna cikin jini,dukkanin su tsirara,wani Kara Ayrah ta sake, Nabila Kuma ta fashe da kuka.
Mamy Zama tayi da d'an karfi a kasa tana kallon su cikin jini, d'ago kanta tayi ta Kalli Faisal dake huci cikin Murya Mai sanyi Tace "What have you done Faisal? What have you done"
Cikin d'aga murya yace "Abinda ya Dace dasu Mamy ya Isa Haka na gaji da ganin ki Cikin kunci da tashin hankali"
"Faisal ka kisa? Faisal ka kashe su, ka kashe har Mutum uku"
Jin maganar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 24