gida da turaren wuta, saikace a novel? Aljanar inace nida Zan yi wannan aikin kullum? 🤣
To kaga ni gaskya ko agaban iyayena Babu me takuramin ehe! "
Tana fadar haka tajuya takoma cikin dakinta, jagwab Adam Yazauna akan kujera tareda dafe kansa 🤦🏻♂️maryam zata haukatashi
Yadade azaune sannan yatashi yatattare hannun rigarsa yadauki tsintsiya yafara share gidan, takan dakinsa yafara sannan kitchen, sai kuma falo, mopper yadauko ya goge falon tas, sannan ya goge kayan kallan yadauko qur'ani adaki yadawo falon yana karantawa
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Tunda taga ya Fawaz har gida yake shigowa da kayan maye yasaka acikin fridge ta shiga damuwa, ya Fawaz koshi ba dan'uwanta bane yakamata tafara nuna masa abinda yake ba daidai bane, balle ma shidin mijinta ne, haqqin kula dashi yana kanta
Jiya tatuno saida yagama qarewa fuskarta kallo sannan wai ta d'agashi tunda dama tasaba 🤣
Ahankali tatashi tashige cikin dakinsa, ta gyara masa dakin tas, ta lailaye masa gadon tsaf, fridge din dakin tabude kwalaben maganin maye dana mura gasunan birjik, shiru tayi tana tunani, tarasa mafita Dan haka tadau wayarta takira yayarta, bugu daya ta dauka tace "Diyana kinga dakin ya Fawaz nake gyara wa bakiga kayan maye ba, nikuma banaso yanasha wallahi, Yaya zanyi dasu ne?"
Diyana tace "um lalle Dida agaisheki, ke har gyaran dakinsa ma kike, tab!"
Dida tace "toya zanyi Diyana, mijina ne ko mahaukaci ne shi dole Zan kula dashi ahaka"
Batare da tunanin komai ba Diyana tace "kidebesu kizubar kawai"
Dida tace "to shikkenan nagode Diyana" daga haka takashe wayar, takwashe duka magungunan tafitar dasu waje ta tsiyayar dasu sannan tayi watsi da kwalaben
Tadawo ta goge fridge din, ta dauko lemuka a kitchen da ruwa tazuba masa su sannan tafuto daga dakin
Abinci taje tadafa musu bayan tagama tayi wanka tadawo falon tazauna tana game a wayarta
Ta dade azaune awajan sannan yashigo gidan, yau yayi mata sallama, cikin ladabi ta amsa masa, tace "a kawo ma abinci ne?"
Yatsina fuska yayi "no kibarshi kawai, ke kidena dafa abinci Ma Dani, kiyi rayuwarki kawai"
Batare data ce masa komai ba ta kwanta taci gaba da abin datake
Yana shiga dakin ya ganshi yasha gyara sai qamshi yake, zama yayi agefen gadon afili yace "wannan yarinyar da naci take wallahi"
Fridge dinsa yabude nan yaga Babu komai, cikin bacin rai yace "kan ubannan!!!"
Belt din jikinsa ya cire yafuto falon afusace, Dida tanayin game kawai sai Saukar belt din taji a jikinta, cikin sauri tatashi tana sosa wajan, be tausaya mata ba yaci gaba da dukanta, tatashi tana kuka sosai tana bashi hakuri, yana binta da duka tanayin baya har sukaje bangon falon ta tsugunna aqasa tana kuka sosai, cikin hucin bacin rai yace "ke Dan uwarki nizaki renawa hankali eh ? Okey wato saboda na sakar miki fuska acikin gidannan kina abinda kikaga dama shine zaki nemi ki takurawa rayuwa ta ko?, to bari kiji duk lokacin dana sake ajiye kayana cikin fridge tsautsayi yasa kika dauke min, saikin yabawa aya zaqin ta "
Yayi wulli da belt din awajan ya koma dakinsa, Dida kuwa kanta yana cikin qafafunta tana kuka, Dagowa tayi ta kalli jikinta, gefen hannunta harya shata
(Allah karabamu da mazaje masu dukan iyalinsu 🙏🏻)
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Nihla karatu yayi nisa, alhmdlh tafara kwantar da hankalinta, saide damuwarta daya ya Abba, yana nan daram acikin ranta, amma alqawarin data daukar wa kanta yana nan Babu shi Babu ita,fatanta daya tasamu miji nagari Wanda zai nuna mata soyaiyar dazatasa ta Manta da Abba kwata-kwata, tana fatan samun wannan mijin
Gefe daya kuma shaquwa Mai qarfi tashiga tsakaninta da abdallah, kullum suna tare, tana karatun ta cikin kwanciyar hankali, abdallah yazame mata tamkar aboki, gashi yanada abin dariya, idan suna tare dole nema saiya bata dariya, shiyasa take ganinsa Kamar qawanta, gashi duk abinda bata ganeba yana temaka sosai harsai tagane, fatarta kadai zaka kalla a yanzu kasan cewa lalle tasamu canji, Anty Nadiya tayi mata komai a rayuwa
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Bayan tagama gasa jikinta tabawa megadi kudi yasiyo mata magani tasha sannan ta kwanta, amma hawaye take sharewa, kanta har ciwo yake saboda kuka, yakamata tabarwa yaya Fawaz gidansa, Tun ranar da aka kawota gidan nan tafara cin karo da mari, to tunda yafara duka bazai dainaba gara tafara tunanin barin gidan Tun wuri,kuma yazo ya kwanta a jikinta yace itace, bayan duka ga sharri, inaaaa! Da sake
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Yau agajiye yadawo gida,gashi ya Manta bai siyo abinci ba awaje, tsaki yasaki yafara qwala mata kira "Ilham"
Daga kitchen tafuto, ya kalleta daga ita sai wata qaramar riga da bata wuce gwiwarta ba
Ya Girgiza kai, yarinyar nan bazata dena halin ta ba, batada kunya, batasan shigar kamala 🤣
Yace "jeki kawomin abinci"
Babu musu tajuya takoma kitchen, Aslam yabita da kallan mamaki, yau shine yace wa Ilham tabashi abinci Babu musu Babu rashin kunya tajuya zata kawo masa? Lalle yau za'ayi ruwa da qanqara
Ilham kuwa tana shiga kitchen tazuba masa Abincin, sannan tad'ebo gishiri Mai uban yawa tazuba masa aciki, tasa spoon ta jujjuya Sanna tadauko takawo masa, zuciyarsa daya yadebi Abincin yakai bakinsa, lokaci daya ya yatsina fuska, gaba daya gishiri yahade masa baki, daqyar ya iya hadiyewa, yadauko Abincin yakawo mata gabanta ya ajiye, tadago kai ta kalleshi dariya ta nasan kamata, cikin fishi yace "Ashe ke zero ce bansaniba?"
Ran Ilham yabaci, ita ya Aslam zai kalla yace mata zero? Itama cikin bacin rai tace masa "To sannu 1"
Tas kakeji yadauketa da mari, yace "Ilham idan kinaji da rashin kunyar ki kiyi abinki ke kadai, tayaya Zan kashe kudi na kawo miki abinci gida na ajiye, banda damar dazaki dafamin, Sannan yanzu nace kikawo min abinci zaki zuba min gishiri aciki?to gashinan zauna tas saikin cinye shi"
Hawaye ne yazubo mata, tasa hannu tashare tana magana cikin kuka "Allah bazanci Abincin nanba"
Yace "nikuma kika sakamin naci namutu, baki damuba, zauna saikin cinye Abincin nan"
Haka Ilham tasa hannu acikin Abincin nan tanaci tana hawaye, fakar idonsa tayi tatafi dakinta dagudu tana kuka, Kallanta yayi yafara fada cikin ransa, haba yarinya sai Jan magana da rashin kunya, in banda yana mata kallan qanwar budurwarsa yau dasai ta cinye Abincin nan tas
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Futowa tayi tatafi dakinsa kanta tsaye, shi kansa yayi mamakin ganinta a dakin, saboda ba kulashi takeba, agefen gadon tazauna "yaya Adam inason kudi zanyi amfani dashi, banda kudi"
Kallanta yayi yace "banda shi"
"yanzu yaya Adam kaine zakace bakada kudi? Idan ban tambayeka kudi ba wazan tambaya?"
Yace "Allah masani"
Tace "Ok to sata zanje inyi insamu kenan?"
Yace "maryam koma menene kije kiyi, amma nide bazan dauki kudina nabaki kitafi yawon banza ba, kokuma kisa kati ki kira samari, qarya haram!"
"Ok haka kace?"
"yes haka nace maryam, kije kiyi duk abinda kikaga dama"
Tashi tayi tafuto tabar masa dakinsa
Tunani tafara maranta ciwo yake, A'ina zata samu kudin dazata siyo pad, shikuma besiyo mataba sannan yahanata kudin, haka takoma daki ta kwanta ga ciwo da takeji sosai, Tun tanaji kadan-kadan harta faraji dayawa, daga qarshe ma zazzabi me zafi Yarufe ta
Washe gari dasafe ya shirya zai tafi makaranta saboda yanada lacture, yayi kyau sosai cikin farin yadi sai qamshi yake
Har zai shiga Mota ya tuna yarinyar nanfa Tun jiya beji motsinta ba, Dan haka ya koma ciki kai tsaye yashiga dakinta, tozali yayi da ita akan gado tana cikin blanket amma karkarwar sanyi take
Cikin sauri ya qarasa wajanta yace "subhanallah... Maryam!"
Bargon ya janye saiga Diyana tana kuka sosai, yace "bakida lafiya ne?"
Bata iya bashi amsa ba sai kuka, dagota yayi yatasheta zaune sai riyamm tafada jikinsa, kanta yana kan qirjinsa amma tana iya jiyo bugun zuciyarsa,wannan shine karo na farko da mace tahada jiki dashi, sai yaji abin wani iri, goshinta ya shafa yaji zafi sosai, lokaci daya yashiga damuwa, yace "Sannu, sannu kinji, bari nahada miki ruwa kiyi wanka sai Muje asbiti"
Dagota yafara yi daga jikin sa amma taqi tashi, ya sassauta muryar sa cikin sigar lallashi yace "kiyi hakuri, zaki denajin zazzabin insha Allah, kinji ko?"
Ahankali ya maida ta ya kwantar da ita, Sannan yashige toilet dinta yahada mata ruwa, yadawo yakamata zai tasheta, ta miqe kenan taji zuciyarta tana tashi, lokaci daya taji amai, cikin sauri zata shige toilet yatareta zai kamata suje, aikuwa sai amai ajikinsa, farar rigar yadin daya saka ya kalla, gaba daya tabata su da amai, tayi tunanin zataji Saukar duka, amma abin mamaki sai yace mata "Sannu, sannu kinji,"
Daga masa kai tayi, yadaga hannunsa ya cire rigar jikinsa, yadawo daga vest sai dogon wandon jikinsa
Kamata yayi suka shige toilet din, sannan yafuto yabarta aciki, dakin ya gyara tsaf, yasake gyara mata gadon, sannan yabude kayan ta yana dubawa kozaiga Mai Dan sauqin sakawa, amma gaba daya da riga da wanduna yayi ar'ba
Wata atamfa yagani yajanyota, ya ajiye mata akan gadon, shikuma ya juya ya koma dakinsa yasake shirya wa sannan yadawo dakin nata
Bude toilet din tayi tafuto, taganshi yasaka qananun kaya, cikin ranta tace ashe yana saka qananun kaya,kayan kuwa sun karbi jikinsa, Kallanta yayi sau daya yakawar da kansa cikin sauri, yace "ga kaya nan kisa, saimu tafi asbiti yanzu"
Yadauki wayarsa yayi kira "hello monitor ki fadawa kowa cewa bazan samu damar zuwaba, matata batajin dadi"
Dasauri Diyana ta kalleshi, yanzu saboda ita yaya Adam zai fasa zuwa wajan aikinsa?
Fita zaiyi daga dakin tace "ya Adam"
Juyowa yayi Bece da ita komai ba tace "banda pad, kuma inaso zanyi amfani dashi"
"idan mun fita sai asiyo" yana fadar haka yafice daga dakin, yaga alamar Diyana batasan cewa bayasan ya zauna da ita Awannan halin datake ba, kokuma kallan dutse take masa waya sani, ita kuwa ko a jikinta
Kalau ta shirya suka tafi asbitin aka dubata aka bata magunguna Sannan sukaje suka siyo pad din, suka dawo gida
A sauqaqe yadafa mata indomie da dafaffan qwai 😃saboda bazai iya soyawa ba, yadoro spoon akai tareda gorar ruwa, sai ganinsa tayi yashigo dakin da abinci, karon farko da taji Tausayinsa ya kamata, meyasa take masa Wulaqanci? Tabbas sai kana jinya zaka zaka gane masoyinka na gaskiya
Zama yayi akusa da'ita, yace "maryam tashi kici abinci kisha magani saiki kwanta"
Ahankali tatashi tasa hannu zata karbi flet din, yace "A a, ai naga jikin naki Babu qarfi, kibari nabaki"
Ta Girgiza kanta tace "zan'iya ci ya Adam"
"maryam banason musu fa"
Shiru tayi, takasa yimasa gardama, ahankali ya matsa kusada ita har jikinshi na gugar nata, yafara bata indomie din abaki, saida yaga ta qoshi sannan yabata maganin tasha, yace "ki kwanta kihuta, Allah yasawaqe"
Tace "amin" idonta akansa, tashi yayi daga kan gadon Yazauna akan bedside drower yayi shiru, itama haka Babu me magana acikinsu, saide cikin ranta tabbas ta Jinjina wa ya Adam, saika zauna da mutum sannan zakasan halinsa 🤣
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Yau Tun safe ya shirya yabi jirgi zuwa Abuja, yakamata yaude yaje yaga Nadiya yaji A'ina suka tsaya akan maganar aurensu, yanaso kawai yaturo iyayen sa agama maganar komai
Baisha wahala ba daga Airport kai tsaye wani abokinsa dayake tuqin jirgi amma bangaren state, yadauko shi a motarsa suka qaraso gidan nasu Nadiya,akofar gidan sukai Parking ,suka futo daga cikin motar yakira wayarta nan take tashiga
Tana dauka cikin muryar sa Mai cikeda aji yace "Nadiya gani agidan ku"
Cikin mamaki tace "gidanmu kuma?"
"eh, nazo ne muyi magana dake Mai muhimmanci, koda yaushe kina tambayata yaushe zanzo yaushe zanzo, banda lokacin ki, banida kirki, to yaude gani"
Tace "ayya, gashi kuma wallahi bana nan, naje lagos gidan Antynmu, munata shirin biki"
Be tambayeta bikin waba, sannan Beyi tunanin komai ba yace "okey, to shikkenan idan kindawo saiki sanar Dani, lokacin dana samu dama sainazo, but yanzu Zan turo miki 50k sai kiyi anko dashi"
Tace "to shikkenan Sadiq nagode"
Suna ajiye waya yatura mata kudin, sannan yadubi abokinsa yace "kaji batanan taje lagos, next time kawai"
Maigadi yaji dirin Mota abakin get kuma yaji shiru baiji ance yabudeba, Dan haka ya leqo, yana futowa yaga su Abba, nan take yagane shi
Cikin farin ciki yace "a a yallabai ashe kune kuke tafe, toku qaraso ciki mana"
Abba yace "A a sammani kada kadamu, ai munyi magana da ita ma yanzu tace taje lagos ko?"
Sammani maigadi yace "eh wannan gaskiya ne yallabai, ya hakuri kuma?"
Cikin mamaki Abba yace "wanne irin haquri kenan sammani?"
Yace "to yallabai Wanda yarasa mace Kamar Nadiya ai yayi Babban rashi dole a jajanta masa, ai lagos din data tafima sunje hado kayan lefenta ne itada mijinda zata aura 😳,
bikinma yanzu haka saura sati uku" 🙆🏻♀️
Lokaci daya kansa yasara, cikin tsananin mamaki yace "sammani me kace?"
Sammani maigadi yace" wallahi gaskiyar kenan yallabai "
Lokaci daya yafara karanta kalmar Innalillahi wa inna ilaihir raju'un abaiyane, da abokinsa da sammani maigadi basu zataba kawai sai ganin Abba sukai aqasa🙆🏻♀️
Cikin sauri sukayi kansa suna kira, abokinsa yana cewa "Abba! Abba!!"
Shikuwa sammani yana kira "yallabai! Innalillahi..."
Daqyar suka cacimeshi suka saka amota, sannan abokin yaja cikin sauri, sukabar kofar gidan
Asbiti yakaishi, anan doctor yake tabbatar wa da abokin cewa kawai yaji abinda ya razanashi ne shiyasa ya suma, allura akayi masa, ba'a dauki lokaci Mai tsawo ba yafarka, amma yakasa cewa komai, abokin nasa yabashi hakuri, amma Abba bai iya cewa komai ba, daga qarshe ma tashi yayi ya cewa abokin yagode amma yanaso yabar garin yanzun nan, duk yanda abokin yaso hanashi tafiya abin ya gagara, dole sai Airport yakaishi yabi jirgin dazai tashi zuwa kano
Ikon Allah ne kawai yakai Abba gida, Momy tana zaune afalo sai ganin shigowar Abba tayi yana tafiya yana layi Kamar d'an maye, baima kalli Inda takeba yashige dakinsa da alama baima lura da'itaba
Fadawa yayi akan gadonsa, Baqin ciki yazame masa goma da ashirin, kenan kudin ankon aurenta yatura mata? 🤔
Lokaci daya yaji hawaye yana zubo masa, ga wani zazzabi dayakeji me mugun zafi, blanket dinsa yaja yashige ciki yana kuka, tabbas Nadiya taci amanar soyaiya
Momy taturo kofar dakin tashigo, ganinsa cikin bargo yasa ta qarasa da sauri tazauna a gefensa tace "subhanallah... Abba na lafiyarka kuwa?"
Dasauri yatashi yadora kansa a cinyar Momy cikin kuka yace "Momy Dan Allah kiyi hakuri, kuyafemin keda Daddy, bazan sake ba Momy"
Gaban Momy yafadi, bafa qaramin abu ne yakesa Abba kuka ba, anya kuwa kalau yake? Cikin tashin hankali tace "Abba meyake faruwa ne? Me kayi kake bada hakuri? Kayimin bayani"
Kuka yake harda Jan zuciya, yakasa fadawa Momy abinda yake faruwa, tayaya zai fada mata cewa yarinyar dayaso bijire musu, yaso Yaqi yi musu biyaiya akanta ta yaudareshi zata auri wani? Tayaya?dole ne yanemi yafiyar iyayen sa akan qin biyaiya dayaso ya musu
Momy tace "to shikkenan bari nafadawa Daddynka tunda ni bazaka fadamin ba"
Nan take takira Daddy, yana dauka tace "Alhaji takwaranka fa Babu lafiya, gashinan yazo yanata kuka wai nayi hakuri"
Daddy yace gashinan zuwa, Momy ta kalli Abba taga ko alamar dena kuka bayayi tace "to inaga addu'ah zanyi ma Abba, meyiwa gamo kayi" 🤣
Alokacin Daddy yashigo dakin, Abba yana jin shigowar Daddy yace "Daddy Dan Allah kayi hakuri, natuba Daddy wallahi bazan sakeba"
{Allah sarki Abba,😢Dani kabawa kudin ankon ma wallahi 🤣 🤣}
El Yaqoub ✍️
[6/24, 11:52 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Dedicated to DANGI DAYA GROUP 😃
Like my page On facebook 👇
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
25&26
Daddy yadubi Abba yace "yanzu Abubakar da girman ka kasamu agaba kana kuka kamar mace!, sannan mun tambayeka abinda yake damunka kayi shiru, sai hakuri kake bamu, to hakuri akan me?"
Shiru Abba yayi Bece dasu komai ba, shi ya'isa yafada musu gaskiya? Ai kaf family dinnan sai sunyi masa dariya wasu ma suce Allah yaqara
Dan haka yayi shiru yaqyalesu
Momy tace" Alhaji Abba fa ba magana zaiyi ba, nikam kaga tafiya ta "tasa hannu tadauke kan Abba dayake cinyarta tafuto daga dakin 😃
Shima Daddy yace" to ai shikkenan tunda haka kazaba "
Yafuto daga dakin, yaje wajan Momy yace"ko menene yake damunsa? Amma miskikanci ya hanashi magana?"
Momy tayi Murmushi tace "to awajan wa yadauko halin"
Shima murmushi kawai yayi, yashige dakinsa
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Tun bayan dukan dayayi mata ta tattara shi ta watsar, gaba daya tadena shiga sabgarsa, idan taji yashigo gidan ma tana falo cikin sauri take shigewa dakinta Tun kafin yashigo falon, abinci kuwa zatayi tabarshi anan, idan yaci shikkenan idan baici ba kansa yayiwa itade tasan cewa batada haqqin kowa akanta, koda rasuwa tayi tasan tafita haqqin sa saide nata haqqin dayake kansa
Tunanin abin datasa aranta yasa duk tafara ramewa, idanunta duk sun futo
Yauma shi kadai ne azaune afalon, Tun safe baije ko'inaba amma baiga futowarta ba, Kamar wasa saigata tafuto daga daki zataje kitchen, ta kalleshi ta watsar ko gaisuwa Babu, taje ta dauko ruwa tasake komawa dakin
Shikuwa Fawaz Yana binta da ido kawai
Yayi ajiyar zuciya yatashi yabita cikin dakin, yaune karon farko daya taba shigowa dakinnata, yanemi waje Yazauna yana Kallanta tanashan ruwa, saida tagama sannan yace "meyake damunki kika lalace haka?"
Shiru tayi masa, Dan renin hankali kawai, yagama dukanta yadawo yana Tambayar me yake damunta, idanunta sukai rau-rau zatayi kuka
Sassauta murya yayi yace "bazaki fadamin ba?"
Duk yanda Dida taso boye hawayen ta saida suka zubo, tasa hannu tashare tace "banasan abinda kake aikatawa ya Fawaz, kana dukana, kanashan kayan maye, nikuma banaso"
Tana qarasawa tasake fashewa da kuka
Fawaz yayi shiru yana tunani, Wato yau sabodashi ake kuka, yau saboda andamu da abinda yake aikatawa ake kuka yadena,nan take yarinyar tabashi tausayi
Kallanta yayi yace "to kiyi hakuri, dena kuka, insha Allah daga yau nadena"
Cikin mamaki ta kalleshi ido duk hawaye tace "da gaske?"
"yes da gaske nake"
"harda dukanma?"
Yasake cemata "nace miki nadena, kema saiki daina kukan ko? "
Aikuwa nan take tashare hawayen idonta
Yatashi tsaye yace "Zan fita, but banaso kina zaman dakinnan, kifuto falo ki zauna, kici Gaba da abinda kikeso kinji ko?"
Cikin murna Dida tace "to"
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Tunda Diyana tafara rashin lafiya Adam yake kula da'ita, kokadan baya barin ta tayi aikin komai
Yauma shida kansa yakawo mata abinci har daki, ya tarar tana gyara dakin, yace "maryam ga abinci"
Tace "ya Adam aina warke ma, nagode sosai da temakon dakamin, yau nice yakamata nadafa ma Abincin" 😳
Adam yayi Murmushi yace "nagode, amma ba yanzu ba,kici Abincin kishirya zamuje gida"
Cikin farin ciki Diyana ta rungumeshi tace "yawwa nagode ya Adam"
Cak jijiyoyin jikin Adam suka tsaya, yarinyar nanfa kada tasa yakasa aiwatar da abinda yayi niyya, cikin wata irin slow voice yace "Diyanaaah" yaja sunan nata
Ahankali tadago daga jikinsa ta kalleshi yaune karon farko data tabaji yakirata da wannan sunan, koda yaushe maryam yake cewa, gashi yanda yakira sunan nata ma kadai ya'isa yasaka mutum cikin wani hali, ya'iya kiran sunan, tana gama wannan tunanin tayi fari da idonta tace "na'am"
Yace "kije kishirya mana, university nakesan wucewa daga gidan"
Murmushi tayi tace "to"
Sannan tasakeshi tashige toilet
Sai a lokacin yasaki wata irin ajiyar zuciya sannan yafuto daga dakin yadawo falo, abinda yake shirin yi shine daidai, dole zai nunawa Diyana kuskurenta, idan akaci gaba da zama ahaka to akwai matsala
Bata dauki Tsawon lokaci ba tafuto, ko hijabi bata sakaba kawai wani yalulun mayafi tayafa suka futo, shima Bece da ita komai ba, suna tafiya ahanya yana driving qira'ah tana tashi acikin motar
Har sukazo bakin get din gidan nasu Babu Wanda yace da dan'uwansa komai, amma Diyana tunanin Adam ne fal acikin zuciyarta, ashe haka yake da kirki? Babu ruwansa duk abinda take masa ko ajikinsa
Tsayawa ya kalleta yace "kishiga ciki, nizan wuce makaranta"
Cikin mamaki ta kalleshi tace "Kamar ya nashiga ciki, kai bazaka shigo ku gaisa ba?"
Fuskarsa Babu alamun wasa yace "kema ba gaisuwa nakawoki ba, gaba daya nadawo dake gida, kije saina nemeki"
Gaban Diyana yafadi, cikin rawar murya tace "ya.. ya.. Adam"
Cikin tsawa yace "yes abinda kikaji hakane, Maryam kitashi kifice min daga Mota kitafi gida saina nemeki"
Wani irin kuka ne yazo mata, Dasauri tabude motar tafuto da gudu tana kuka tayi cikin gidan
Kansa yadora akan sitiyarin motar idonsa yayi jajir, cikin kwana kin nan datayi batada lafiya tabbas yasan cewa yakamu dason yarinyar, saide bazai taba nuna mata hakanba, saita gane kuskuren data aikata abaya, shi aure ko wanne iri ne ba abin wasa bane
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Damuwa tayi masa yawa, gashi abin acikin ransa yarasa wazai fadawa yaji dadi aransa
Wayarsa ya janyo yakira Aslam "hello Aslam idan kasamu lokaci kazo gida inason ganinka, banda lafiya wallahi" 🤣
Aslam yace "subhanallah, to gani nan zuwa Abba"
Dama yana kan hanyar zuwa gida ne, Dan haka ya juya kan motarsa zuwa family house dinsu
Kai tsaye part dinsu Abba yaje, suka gaisa da Momy yashige dakin nasa
Akwance ya ganshi yana danna waya Yazauna yace "Abba da alama ka warke, tunda gashi wayace a hannunka"
Ajiye wayar yayi bayan yagama goge pictures din Nadiya da numbers dinta 🤣
Yace "banasan tunani yamin yawa ne''
Aslam yace" menene yake damunka? "
Abba shiru yana tunani, kode yafadawa Aslam ne? Kaiii wallahi Aslam ma sai yafi kowa yimasa dariya, Dan haka yace" kawai banajin dadin jikina ne "
" to Abba kaima kayi aure kaqi, ka zauna agaban Momy tuzuru dakai "🤣
" Aslam bana tunanin yin aure yanzu "😳🙆🏻♀️
"meyasa?" inji Aslam
Abba yace "haka nan, banda ra'ayin auren yanzu" 🤣
Ajiyar zuciya Aslam yayi "to shikkenan Allah yakaimu lokacin, daga campany nakefa kakirani, mungama tattara list din ma'aikatan da za'a dauka, yanzu kawai ina jiran kiran wayarsu ne, sunce zasu saka mana date din dasuke ganin shine yadace da bude campanyn, wallahi Abba banasan komawa gida, Ilham tacika rigima, yarinyar nan jiya gishiri tazuba min acikin abinci na, batajin magana "
Ran Abba yabaci " meyasa zaka tsaya yarinya ta raina ka haka Aslam? "
Aslam yace" to Abba ba dole raini yashiga tsakanin muba, tunda taga tashigo dakina taganni haka "
Murmushi Abba yayi yace " Aslam ni aganina zancen boye boye yaqare atsakaninku, why not ka koya mata hankali sau daya, daga ranar zata dinga yima biyaiya, shikkenan anwuce wajan "
Dariya Aslam yayi yace" kai Abba, akwai shawara, toshknn Zan wuce gida, inaso nahuta kafin Baqin sukira wayata "
" to Aslam "
Aslam yafuto yatafi gida yana mamakin yanda suka shaqu da Abba, kowa yana fadawa kowa damuwar sa, gashi de bayasan magana amma inde da Aslam ne tofa zakaji maganar sa
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Da gudu ta qaraso part din nasu, cikin kuka tafada jikin mahaifiyarta tace "Mom ya Adam ya tsaneni"
Hajiya Farida ta dagota tace "ke kiyi shiru kimin bayani, meyake faruwa?"
Hawaye ta share tace "Mom cewa yayi natafi gida saiya nemeni, Allah Mom bazan zauna ba"
Hajiya Farida tafara salati "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un... Diyana ki fadamin gaskiya me kika yi masa?"
"Allah Mom banyi masa komai ba, kuma saida yaga na haqura Zan zauna dashi zaice natafi gidanmu, Dan Allah Mom kibashi hakuri" 🤣
Hajiya Farida tace "yi shiru bari nakira babanku awaya,"
Alhaji habib takira, ta sanar dashi komai, nan take yazo gidan, yadubi Diyana datake zaune aqasa yace "ke maryam, fadamin gaskiya, me kika yimasa?"
Tace "Allah banyi masa komai ba, saide in wayar dayaji inayi da wasu maza ne yan ajinmu, kuma ni wallahi yan ajinmu ne, da rannan dana tafi biki ban fada masaba"
Alhaji habib yace "to ai kinji, haba maryam, da hankalin ki da girman ki tayaya zaki dinga waya da maza bayan da auren ki, ko qanwarki Dida bazata yi hakaba, ai shikkenan tunda kin kaso auren naki, saiki zo muzauna agida"
Cikin sauri tace "dan Allah, kubashi hakuri Mom Allah nadena, wallahi Zan dinga yimasa komai har girkin ma"
Zaro ido hajiya Farida tayi 😳"yanzu Diyana kina nufin har girki ma bakya yiwa wannan bawan Allah? Diyana me kikeso ki zama?"
Alhaji habib yace "to nide yaron nan yana ganina da mutunci, idan yaganni har qasa yake tsugunnawa ya gaishe ni, Dan haka ba zanje nabashi hakuri daga baya ki qara yin wani laifin yadena ganin girma naba"
Yatashi yafice daga falon nasu
Hajiya Farida tace "toke kinji, saiki haqura ki zauna, idan ya huce yazo yace kifuto kutafi saiki koma, tunda yace saiya nemeki"
Diyana tatashi tayafa mayafin ta tace "Allah Mom bazan zauna ba" daga nan tafice daga part din nasu tatafi part dinsu Adam wajan hajiya Na'ila🤣
Hajiya na zaune tanacin abinci taga Diyana tashigo tana kuka, Abincin hannunta ta ajiye tace "subhanallah, ke Diyana lafiya kike kuka? Me aka miki? Ko wani abu ne yasamu Adam din?" 🤣
Zama tayi akan kujera tace "Hajiya wai cewa yayi natafi gidanmu saiya nemeni"
Hajiya na'ila tahau salati "shi Adam dinne me yanke wannan hukuncin?" 🤔
Diyana ta daga kanta
"to kiyi hakuri, kidena kuka, zama na mutum biyu dole kowa yanada laifi, Zan kirashi gaba dayanku nayi muku fada, tashi kije daki ki zauna akawo miki abinci"
Diyana tatashi tana share hawayen
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 24