ciki yace "a a Kamar Nihlan Diddi"
Daria sukayi, Nihla tace "nice wallahi"
"A a masha Allah, sannu da zuwa"
Tace "yawwa"
Fita yayi daga falon, basu jimaba suma suka fice, Ilham tace "wannan shine yaya Adam,duk Mazawaje family shine ustazi, idan kina neman alaramma kikazo wajansa to kingama samu🤣, lacturer ne, yana koyarwa a yusuf maitama, Wato northwerst, yayansa yana germany shida yaya Abba Wato Aslam, su biyu ne a part dinsu
Nihla tace "Allah sarki, aikuwa Babu ruwansa bawan Allah" 🤣
Part din qarshe sukaje kafin su shiga Ilham tace "wannan shine part dinsu Diyana da Dida, maman su tana auren dan'uwanmu ne na family shiyasa taci gaba da zama agidan nan, basu bar family house ba, tana son yaranta sosai, batasan abinda zai tabasu
Kuma ayanda ummah take fada mana hajiya Farida Maman su Dida tana shiri da baban ki sosai"
Nihla tace "hakane kam, nima nasani Ilham"
Part din suka shiga, nanma Babu laifi sunsha fira da Dida, Dan Diyana bata nan 🤣, sannan suka futo kowa ya koma part dinsu
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Watan ta d'aya agidan tafara sakewa, kuma tagama gane halin kowa, nacinda Ilham take mata ne yasa suka saba da ita sosai, Dida da Diyana ma suna zuwa, saide Dida tafita zuwa saboda Diyana kullum tana wajan yawo, yawon ma bada yan'uwanta mata ba, maza!
Su yaya Usman da Aliyu fa farouq sosai suke nuna mata gata, Aliyu yakai ta anyi mata dinku na masu kyau amma kullum tana cikin hijabi, da wahala ka ganta tazauna haka Babu hijabi, haka yaya farouq yakai ta shopping tasiyo kayan kwalliya ta jeresu agaban mirrow din dakin nata, Yaya Usman kuwa Sabuwar waya yasiya mata qirar iphone Mai tsadar gaske.
Rayuwar ta take hankali kwance, saide tunda Diddi tarasu wata nutsuwa tasake shigar ta, abu dayane yake damunta, tunda tabar jigawa kullum takira wayar Baba baya dauka, tarasa dalili, lafiya lafiya zata kira yan'uwansa su gaisa da ita amma shi idan takira baya dauka, idan tayi masa text baya reply, amma tasan koma menene zai iya neman ta daga baya, tasan Baba da wahala yayi fishi da ita Babu dalili.
Hisnul Muslim din hannunta datake karantawa ta ajiye tafuto falo, babu kowa da alama Momy ma tana daki, zama tayi acikin kujerun falon tana kallan tashar aljazeera
Wayar Momy dake gefenta ce tafara qara, Ahankali takai hannu tadauki wayar, sunan dake yawo a screen din wayar ta kallah taga ansa Abba nah, haka kawai ta tsinci kanta da faduwar gaba, cikin ranta ta furta "Yaya Abba"
Wayar tana gab da katsewa tayi picking call din tace "Hello"
Shiru yayi anasa bangaren, Idanunsa a lumshe, yana kwance akan katifar robar nan ta cikin ruwa, acikin swimming pool din gidansu, babu riga ajikinsa dagashi sai gajeren wando, gashi Mai yawa kwance akan qirjinsa, cikin ransa ya furta "Sweet Voice"
Shirun dataji anyi ne yasa tasake cewa "Hello" still aka sake yin shiru, hakan yasa takashe wayar ta ajiye ta
Sake qara wayar tayi akaro na biyu, adede lokacin kuma Momy tazo falon tazauna tareda amsa wayar "Abba nah"
"Momy shikkenan ni duk kinmanta Dani ko nemana bakyayi, babu wanda yake missing dina"
ya qarasa maganar cikin shagwaba
Murmushi tayi "Abba kacika rigima wallahi, idan nakiraka kuna aiki kace baka kusa, idan naqi kira kace bana nemanka"
Shiru yayi Bece mata komai ba, baisan mezai cemata ba,itama tasan hali Dan haka tace "yaya aiki, ina Aslam?"
"Momy Aslam baya nan yaje Indonesia,"
"haka kuka iya dai, yau wannan qasa gobe wannan, amma banda Nigeria"
Yasan sarai abinda take nufi Wato sunqi dawowa gida, Dan haka yayi Murmushi cikin aji yace "Momy toki shirya next week zamu dawo"
Cikin farin ciki tace "Alhamdulillah, Allah abin godia, da gaske Abba nah?"
"yes serious Momy, i will call you back" dif ya kashe wayar batare daya tambyeta wadda ta d'aga wayar tasa da farko ba
pls Karku Manta da Comments da sharhi 🙏🏻
Amnah El Yaqoub ✍️[6/18, 12:36 AM] El Yaqoub: ❣️ DANGI 'DAYA❣️
{Romance &Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Like my page On facebook 👇
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
11&12
"Anty dawowa zaiyi?"
Nihla tayiwa Momy wannan Tambayar
Zama Momy tayi cikin farin ciki "Nihla Abba zai dawo next week"
Lokaci daya farin ciki yakamata, finally yaya Abba zai dawo, cikin murna tace "Tome za'a shirya na tarbar su Anty? Medame yaya Abba yafiso?"
Hannayenta Momy takama Kamar qawarta 🤣tace "Yanzu de kije daki ki dauko memo saimu zauna narubuta miki abubuwan da zamu iya buqata, sai kuje keda driver kusiyo, abinci za'a hada Mai yawa yanda zai ishi kowa nacikin gidan nan"
Cikin murna tatafi dakin tadawo dauke da memo da biro tazauna kusa Momy, nan take Momy tafara rubuta mata abubuwan dasuke buqata, duk irin kalar Abincin da Abba yafiso saida Momy ta zayyanewa Nihla tas🤣
"to Anty naje nayi wanka saimu tafi?"
"A a kibari sai gobe, sai kuje gobe da safe kidawo da wuri"
"to Anty"
Murmushi Momy tayi Wanda yayi kama da yaqe tatashi tace"zanje sauran part din na sanar dasu "
Hankalinta ya koma kan tv, Dan haka ta cewa Momy" to Anty "
Fita Momy tayi cikin sanyin jiki, sai yaushe ne yarinyar nan zata dinga kiranta da Momy Kamar kowa? Anya kuwa Nihla tasan yanda take jinta aranta kuwa? Yanzu idan tayi baqi tana murna ta nuna musu ita cewa ga 'yarta kai tsaye sukaji takirata da Anty zataji dadi? Me zatayi wa Nihla danta dauke ta amatsayin uwa?
Da wannan tunanin tafara zuwa part din hajiya Na'ila, da sallama ta shiga, hajiya na zaune itada Adam da Alqur'ani a hannunsa yana dubawa🤣
Gaisawa sukayi, shima ya gaida ta ciki girmama wa
Ta kalli hajiya Na'ila, "Hajiya munyi waya da Abba yanzu, yacemin suna nan zuwa Next week insha Allah"
Hajiya Na'ila tayi farin ciki, amma meyasa ita nata Dan bai kirata yafada mataba sai abakin facala zataji? Dama a family ana rad'e rad'in cewa angama shanye mata yaro, andauke mata shi ankai shi wata uwa duniya da sunan karatu gashinan Yaqi dawowa, nan take ta nuna bacin rai a fuskarta, Murya ciki ciki ta dubi Momy, "Allah yakawo su lafiya, nagode"
Jikin Momy yayi sanyi, tatashi tace "to sai anjima"
Tana fita Adam ya dubeta, "haba Dan Allah mama, meyasa kike hakane?" mutanan nafa sunyi mana komai, mijinta yayi muku kara yatura dansa da danki karatu, gashi nima nagama karatu na ina aiki na mallaki komai, to menene yayi saura awajan ki bayan godiyar Allah mama? "
" aikai dama ba dan agida na haifeka ba Adam to tabbas zan'iya cewa ansauya min kaine, da anfara magana zaka fara kawo aya da hadisi, Allah yace, annabi yace, tashi kabani waje, d'an kare me macacciyar zuciya Kamar ta ubansa "🙊
Tashi Adam yayi yace" nina tafi masallaci "🤣
Tsaki tasaki tace" haka de"
Washe gari Nihla ta shirya sukaje kasuwa itada driver da Dida, lafiya sukaje suka siyo komai suka dawo, saboda Dida Babu laifi akwai nutsuwa sosai duk family kowa yayi mata wannan shedar
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Bayan kwana bakwai wannan family ya haukace da hidima, kowa kaganshi yana cikin farin ciki sosai, part din Momy yacika da qamshi anata girke girke, Nihla da kanta ta shiga kitchen tace Momy tayi zamanta itace zata yiwa yaya Abba girki, Momy taji dadi sosai, Dan haka tatafi wajan ma'aikatan gidan domin ta sanar dasu suje su gyara wa Abba dakinsa, a bangaren hajiya Na'ila itama tanacan tana ta hidima
Diyana da Ilham da Dida ne suka shigo part din, dukansu kitchen din suka shige suka kama mata aikin
Sosai Nihla taji dadin zuwan su
Ilham tace "Nihla duk kinyi kaca-kaca a kitchen gaskiya kinaji da yaya Abba"
Nihla tace "ke kuwa qawana guda zai dawo ba dole ba"
Diyana taja kujera ta zauna "nikam nagaji wallahi, kugama nazuba naci" 🤣
Ta kalli Nihla tace "Kekuma Nihla yaya Abba ne qawanki?, lalle baki samu qawaba wallahi,aini dakika ganni nan gabana faduwa yake da dawowar su, saboda takura tadawo, harna fara blocking numbers din gayu, saboda idan sukazo gida Babu shakka wataran koshi ko yaya Aslam wani zai iya dukana"
Ilham tayi Murmushi tace "baki Manta marinda yaya Abba yayi mikiba ashe"
Nihla tace "au shi yaya Abban haka ya koma? Meyasa toni be taba nunamin ba?"
Diyana tace"inaaa ai zama ne beyi zamaba Nihla,😃 shiyasa, amma kowa yasan halin yaya Abba a family dinnan, babu wasa, kwata kwata bayasan raini dagashi har yaya Aslam, shiyasa ma jinin su yafi haduwa"
Jinjina kai Nihla tayi, wadannan karfa su saka mata tsoronsa
Dida ta wanke hannun ta yace"nikam duk family dinnan ko wallahi yaya Adam ne yake birgeni, babu ruwansa shiru shiru dashi, gashi kyakykyawa inason manyan idonsa wallahi irinna hajiya Na'ila "🤣
Daria sukasa gaba dayansu Diyana tadubi qanwar tata" toke dama ai bakisan luv ba, yanda kike shiru shiru ai dole kiso alaramma, to bari kiji kokin aure shi wallahi nasiha kawai zaki samu, ko kiss bazai mikiba, kirasa wazakiso sai ustaz tirr"🤦🏻♀️ta qarasa maganar tana dafe kanta🤣
Ajiyar zuciya Ilham tayi "gaskiya de Dida kinyi kokari, ni banga laifin yaya Adam ba amma gaskiya banason maman su, hajiya Na'ila masifarta tayi yawa, danni da ace ita suruka tace ko, wallahi saide ayita taqare bazan raga mataba" 🙆🏻♀️
Nihla tace "inama ace yaya adam din yazo yace yanason ki Ilham, muga yanda zaku kwashe keda hajiya Na'ila 🤣,"
Dasauri Ilham tace "wa? Allah yasawaqe, Dida ce take sonsa,danni kona aure shi idan mamansa tamin ramawa zanyi saide yasake ni aranar, shiyasa duk family dinnan Babu Wanda nakeso, gara kowa yayi harkar sa karma mufara soyaiya kayimin fada in rama azo ana cewa nacika rashin kunya"
Dariya Diyana tayi "aini yaya fawaz yana birgeni, akwai hutu da gayu, danni duk Inda gayu yake ina nan" 🤣
Ilham ta kalleta da mamaki tace "kirasa wazakiso sai Mashayi?" 😳
Nihla tace "Ilham yayan naki kike cewa Mashayi?"
"to Nihla kowa yasan yaya fawaz mashayi ne, Dan qwaya, Dan yana yayana sainaqi fadar gaskya?shiyasa ai ake ganin laifi na ace inada rashin kunya, bayan gaskiya nafada"
Diyana tace "keni can ta matse muku, anata zancen aure aure inma Allah yakawo mazajan auren yazo haka za'ayi shi sulu, wannan tsohuwar dukta hana komai" 🤦🏻♀️
Dariya suka saka dukansu, suna wannan firar suna aiki ahaka suka gama suka adana komai Inda yadace sannan suka dawo falo suna kallo, Momy ce tazo tabawa Nihla key "Nihla riqe wannan key din na dakin Abba ne,nasa masu aiki sun gyara, amma kije kiduba kigani idan akwai abinda baiyiba saiki gyara" karbar key din Nihla tayi, ita kuma Momy tayi ciki
Dida tace "Allah sarki Momy, dukta hana kanta sukuni saboda Dan autanta zai dawo"
Ilham tace "ai yanzu saide yayi hakuri dan Nihla ta qwace kujerar" 🤣
Tana fadar haka tamiqe tace "natafi nayi wanka na shirya, berage awa dayaba jirginsu yasauka"
Suma su Dida da Diyana tafiya sukai domin shirya wa, ita kuma Nihla tawuce dakin da'aka nuna mata tun farkon zuwan ta gidan cewar na Abba ne, key tasaka tabude dakin, ahankali ta tura ta shiga
Qamshin Air freshner ne yadaki hancinta, ta lumshe idonta sanan tabude, shigewa tayi ciki, dakin yayi kyau komai yaji, daga kan labulen dakin har komai da Komai naciki duk launin blue ne, gadon da aka lailaye ta kalla tasaki murmushi tareda fadawa kai, juyawa tayi tana kare wa dakin kallo, anan taga pictures dinsa manya manya guda biyu, cikin sauri tatashi ta qarasa wajan photon, zuba masa ido tayi, haka yaya Abba yakoma? Photon yayi kyau sosaai, daya ya dauka da qananun kaya, sun karbi jikinsa sosai, shagala tayi da kallan pictures din tanajin wani irin dadi da batasan dalilin sa ba, gyara zamanta tayi awajan kawai tana qare masa kallo, kira Momy ta qwala mata hakan yasa tatashi Dasauri ta gyara gadon sannan tafuto
"kin gama ganin komai yayi? ''
" eh Anty komai yayi "
" to shikkenan kije kiyi wanka kishirya, su Alhaji sun tafi su dauko su"
Cikin murna tace "to Anty" sannan tayi cikin daki
Wanka tashige, tana qalqale jikinta Kamar ba gobe, ta dade tana wankan sannan tafuto
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Acan filin jirgin Aminu kano kuwa, zaratan samarin gidanne sukaje dauko 'yan'uwansu
Usman, farouq, Aliyu, Fawaz, da kuma Adam
Basu dauki lokaci wajan jiran su ba, jiriginsu yasauka
Farouq ne yafara hango su yace "yawwa gasu nan" nan yafara daga musu hannu
Gaba dayansu hankalinsu suka maida wajansu, Sunqara kyau, fatarsu ta goge, kana ganin jikinsu kasan hutu Yazauna
Suna qarasowa wajansu suka saki ihun murna duk suka rungumesu, hankalin mutane yadawo kansu gaba daya, mutanan wajan suka fara kallansu
Usman ya kallesu yace "Aliyu, yarafa sun girma, babu abinda zamu jira saide kowa yakawo matar dayake so, musha biki"
Cikin aji Abba yadubi Usman "Aure kuma yaya?"
Dasauri farouq yace "aikai banda kai, nadade da yima mata, yanzu saura Aslam da, Fawaz, dakuma Adam"
Daria Fawaz yayi, shida arayuwarsa mace ma bata gabansa, harkar qwayarsa kawai yasa agaba, yaushe zaiyi wani aure, ahankali yace "Aure, Aure tab"
Aslam ya kalleshi yace "Guy yatake ne? Kaida nayi tunanin ma kafin mudawo har anwuce wajan?"
Kafin Fawaz yabashi amsa Adam yace "kun Manta da wasiyyar kaka kenan, ba taron biki ba taron suna" 🤣
Daria suka sake sakawa gaba dayansu, Aliyu yace "tome muke jira? Muje gida kawai"
Motocin dasuka zo dasu guda biyu suka bude suka shiga, har sukaje gida suna ta surutu da raha a motar, bakin Abba nede gim baya tofa albarkacin bakinsa
Suna qarasawa gida kuwa sukaga komai ya canja, anqara gyara gidan Kamar ba gidansu ba, gaba daya 'yangidan suna tsaye a compound kowa yana jira sufuto amma banda Nihla,
Aikuwa suna futowa waje yakaure da ihun murna, Abba yana ganin Momy yaje ya rungumeta, cikin shagwaba yace "Momy i miss you"
Daria suka fara yimasa, Momy tace "gidanku Abba, bakasan ka girma bane yanzu?"
Dariya akeyi musu, Daddy yanata farinciki yayi gaba, sannan kowa yayi part dinsa cikin murna
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Hayaniyar dataji afalo ne yasa gabanta yafadi, kode har sun zo? Kafin tasamu amsar ta Tajuyo muryar yaya Usman yana cewa "Pilot, Pilot Shagwaba de tana nan "
"to waye kuma pilot?" ta tambayi kanta, kafada ta daga taci gaba da kwalliya
Gaba dayansu dining suka wuce, Daddy, Momy, Usman, Aliyu, farouq, Abba, abinci zasu faraci, Usman yace "Momy banga 'yarki ba, ko ita muke jira?"
Daddy yayi Murmushi yace "ai tunda tayi 'ya takafa mana doka agidan bazamu ci abinci ba kome take sai anjirata"
Aliyu yayi Murmushi "gaskiya ne Abba zaiyi kishi an qwace masa fadar sa"
Duk maganganun dasuke yana jinsu, Wacece suke magana akanta? Shida yadawo daga wata qasa ba'a jirashi ba sai ita, Wacece ita?
Tunanin sane ya tsaya jin Momy ta daga murya tace "Nihla! Nihla!!
Cikin zazzakar muryarta tace "na'am Anty, gani zuwa"
"Nihla" ya furta hakan cikin ransa, lokaci daya ya zubawa kofar dakin dayake tunanin daga ciki zata futo ido
Usman yazuba masa ido yanaso yagano yanayin sa, yayinda Aliyu yake murmushi
Ahankali tafuto daga cikin dakin, tana sanye da doguwar riga ta atamfa, daya daga cikin dinkin da ya Aliyu yayi mata, tayi kyau sosai acikin kayan, daurin dankwalin datayi ya baiyanar da dogon gashin kanta, dukda ta daureshi , yan madedetan Breast dinta shape dinsu yafuto sosai ta cikin breast cup din rigar
Dashi tafara tozali, numfashinta ne yakusa tsayawa cak, saboda wani irin mugun kyau daya qara, ya girma yazama Babban mutum, ga fatarsa taqara wani gogewa
Shima a nasa bangaren hakan take, idanu yazuba mata yana qare mata kallo,
Cikin ransa ya furta "tad'an girma kad'an, but still yarinya ce qarama "
"oyoyo ya Abba"
Maganar ta ce tadawo dashi daga tunanin daya tafi,
Usman yagama kallansa tsaf yasaki murmushi
Kai tsaye wajansa tanufa, taja kujerar datake gefensa ta zauna ta kalleshi dakyau
" Ya Abba sannu da zuwa, mekake cine haka, kaga yanda ka sauya kayi fari ka qara kyau kuwa?"
Murmushin kefen baki yasakar mata "kema haka"
Abinda yace kenan
Murmushi tayi "haba de ya Abba wace ni? Gashinan kana nema ka kamoni fari"
tafadi haka tana matso da hannunta me dauke da dogayen yatsu kusa da nashi hannun, Dan yagani ya ban bance
Bin farar fatar hannun nata yayi da kallo, d'an siriri dashi, Wanda yake tunanin idan yayi mata kyakykyawan riqo zai iya karya ta 😳🙆🏻♀️
Kafin yace mata wani abu, Daddy yayi gyaran murya ganin suna nema su Manta dasu awajan "Am yata zuba mana Abincin ko?"🤣
Tashi tayi tabude Abincin, babu kunya tafara Jan flet din gaban Abba tazuba masa, sannan tadauki na Daddy😃
farouq, Usman, da Aliyu gaba daya suka koma yan kallo awajan, Aliyu cikin ransa yace anya idan Nihla da Abba suka fara soyaiya Momy zata iya bude idonta? 🤔
Saida tagama zuba musu sanan tazuba nata Dan kadan, sannan kowa yafaraci
abinci takeci amma hankalinta yana kansa, tana kallan yanda yake cin Abincin cikeda nutsuwa, Miqewa tayi tsaye Ahankali, tadauki just din dake gaban ya Usman ta tsiyaya a glass cup sannan ta tura wa ya Abba agabansa, takoma tazauna tanaci gaba da cin abinci, Aliyu da farouq suka hada ido tareda Jinjina kai 🤣
Gaba daya Babu wata damuwa aranta take nuna masa kulawa, sai tarairayarsa take Kamar Dan qaramin Baby
Tsawon lokaci suka dauka kafin su Gama, falo suka dawo suna kallo, su Usman sai tsokanarta suke suna janta da fira, ahankali yatashi ya kalli Momy "Momy zanje nayi wanka nahuta"
"to Abba nah,"
Wani irin kallo yayiwa Nihla Wanda ni kaina nakasa fassara shi, amma tabbas za'a sami matsala idan aka yiwa mutumin daya dade yana cikin soyaiyar ka "ina Diddi? Why bakizo da itaba?"
Gaba daya falon shiru sukayi, kowa yakasa bashi amsa
Shikuma ya tsareta da Idanunsa, dago kanta tayi ta kalle shi takasa magana, karkata kansa yayi alamun yana jiran amsa yace "uhm inajin ki"
Idanunta ne suka cika da qwallah, Ahankali ta dago kanta ta dubeshi "Diddi tarasu ya Abba"
"what?"
Dasauri ya kalli Momy yace "Momy, me yarinyar nan take fada haka?"
Jijjiga kai Momy tayi, alamun da gaske ne, Lokaci daya mutuwar Diddi ta dawowa Nihla sabuwa, da gudu tatafi daki tana kuka 😭
Lokaci daya jikinsa yayi sanyi "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, Diddi tarasu, Momy meyasa baku fadamin ba? Haba Momy, meyasa? Innalillah..."
Yadafe kansa da hannunsa🤦🏻♂️ya koma kan kujera Yazauna jagwab
Dafashi Momy tayi "kayi hakuri Abba, Aisha ta rasu Sanadin zazzabi na kwana daya, Daddynku ne yace kada afada muku, hankalin ka zai tashi, addu'ah take buqata idan kuka dawo sai kuyi mata"
"Momy yanzu Diddi tarasu?ashe ganin qarshe nayi mata?"
Su Aliyu dake zaune jiki a sanyaye, sune suka fara bashi hakuri, sannan ita kuma Momy tabi bayan Nihla daki
Zuwa dare ta ware, tadan kwantar da hankalin ta tadena kuka a dalilin nasihar Momy, tana kwance agadon dakinta tana daddana wayarta, yauma takira ya yusif yafi sau biyar amma wayar taqi shiga, ko a wanne hali yake?
ta duba Agogon dakin karfe tara da arba'in da bakwai, Dasauri ta furta "kaiiii goma saura"
Dasauri taduro daga gadon tafuto falo, kitchen tashige tafara hada coffee Mai Dan karan dadi
Momy ce taji motsinta, ta furta alhmdlh aranta, tunda tasaki ranta harta futo falo
Kitchen din ta shiga taganta tana aiki "Nihla me kike hada mana ne da wannan daren?"
"Anty bafa mu nake hadawa ba, Ya Abba nake hadawa coffee, nasan zaiji dadinsa"
ha'ba Momy ta riqe, "to Allah ya temaka, nima kallo zanyi shine naji motsinki na futo"
Tana fadar haka tajuya zuwa falo
Itama Nihla tana gama hadawa tadauka adan qaramin tire, tazo tawuce tagaban Momy tashige dakin nasa, saura kadan tasaki farantin dake hannunta, saboda yanda taganshi dagashi sai gajeren wando 😳, babu riga ajikinsa,gashi kwance a qirjinsa, yana kwance yana waya qasa qasa, batasan dawa yake wayar ba
Qamewa tayi a tsaye, takasa qaraso wa ciki, tayi dana sanin shigowa dakin nan nasa batare da nocking ba
shi kansa baiyi tunanin shigowar taba, futowarsa kenan daga wanka yasaka Dan gajeren wandon, ko shirya wa baiyi ba aka kira wayarsa shine yad'an kishingid'a yana wayar
cikin ransa ya furta "yasalam! Yarinyar nan kada ta raina shi fa" ahankali yatashi zaune tareda zubo qafafunsa zuwa qasa
Ya tsareta da ido Bece mata komai ba, hannunta ne yafara rawa, duk ta rikice, wanne irin qirji ne dashi haka me fadi? Duk Ta diririce tarasa me zatayi
Shima ya lura da yanayin data shiga, ko menene ya tsoratata take karkarwa haka? 🤔 🤣
Ya tambayi kansa.
Cikin in-ina tafara magana "Am dama... dama coffee..."
"zoki ajiye"
Abinda yace da ita kenan
Ahankali ta taka ta qarasa wajansa, sai kawar dakai take, takasa kallansa, ta tsugunna ta ajiye masa agabansa tafuto da sauri
Binta yayi da kallo, to menene abin tsoro ajikinsa ? To kodan ta ganshi haka ne dukta tsorata? Tabe bakinsa yayi, sannan ya kalli wayar tasa yaga anma kashe, shima bai sake kiraba yayi wulli da wayar yadauki coffee din data kawo masa
Tana futowa daga dakin tazauna afalo kusa da Momy suna kallo, amma gaba daya hankalinta bayakan kallan, 🤣
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Tsawon satin su biyu da zuwansu , koda yaushe da irin kulawar da Nihla takewa Abba, zuwan yanzu kam, kowa yasan cewa Nihla nason Abba, Shidinne de suka rasa gane Inda yadosa
Alhaji ne yashigo falon nasu dawowar sa kenan daga wata tafiya dayayi, Momy tanayi masa sannu da zuwa, ya amsa mata, yana zama akan kujera, "ina ya rannan ne?"
"Nihla bata nan taje wajan Ilham, Abba kuma ni Tun safe ma banganshi ba "
Wayarsa yadauka ya kira Abban
" kazo kaida Aslam ku sameni agida yanzu, kokuma ka turomin shi "
Yana fada masa haka ya kashe wayar
Basuda dauki lokaci ba sai gasu sun shigo shida Aslam din, cikin ladabi suka tsugunna agabansa bayan sun gaida shi,Alhaji ya dubesu " Aslam inaso ka shirya kaje India ka dauko Aisha daga makaranta, munyi magana da abokina cewa harma tarafa university, to Zan turoma adress din gidan, saika shirya kaje kutaho tare "
Momy ta kalleshi tace " Amma Alhaji lafiya kuwa? "
" lafiya kalau Alhamdulillah, kawai de lokacin karanta wasiyyar hajiya ne yayi, tunda Allah yayi mana Tsawon rai, gara intara kan kowa na family a karanta wasiyyar agabansa "
Momy ta Jinjina kai, tace" hakane, Allah Mai iko, kwanci tashi kenan "
Beyi mata magana ba, yadubi Aslam din yace " shine kiran dama, ka shirya katafi, ka tabbatar kun dawo akan lokaci "
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
" gaskiya Ilham akwai matsala "
" matsala kuma Nihla? Allah yarabamu da matsala, 🤣
Meyake faruwa? "
" Ilham ina tunanin son yaya Abba nake wallahi, shikuma naga Kamar hankalinsa baya kaina, ina yawan tunanin sa, sannan ni Tun ina qarama nakasa mantashi a raina, Ilham ina tsoro kar yaya Abba Yaqi saurara ta "
" soyaiya Nihla? Kuma ma da yaya Abba? Anya baki debo da zafi ba Nihla? "
" nima abinda nake tsoro kenan Ilham, bansan ya zanyi ba wallahi "
" kinga ki kwantar da hankalin ki, shima nasan Babu yanda za'ai yaganki amma baiji aransa cewa yana sonki ba,Nihla Allah yamiki kyau, sannan kuma ke dashi duka DANGI 'DAYA ne, bazai qikiba, dan'uwanki ne, tunda duk cikin mu Babu Wanda yake sakewa da'ita Kamar ke, amma idan zaki iya to kiyi masa maganar mana "
Kai tsaye tace" bazan iyaba Ilham, yanamin mugun kwarjini wallahi, kullum naganshi agabana ma gabana tsananta faduwa yake, sannan yana cikamin ido, koba wannan bama bazan iya tunkarar namiji da wannan maganar ba "
Ilham tayi ajiyar zuciya," hakane kam,gaskiya gara shiya fara furta miki, amma mezai hana cikin siyasa kifara nuna masa? "
" to ta wacce hanya kenan Ilham? "
" kulawa, kidinga bashi kulawa yanda yadace "
" Ilham duk Wanda Yazauna a part dinmu zaisan cewa ina bawa ya Abba kulawa ta gaske, saboda haka kicire kulawa a lissafi"
Girgiza kanta tayi tace "gaskiya ne wannan, nima shedace, ke kinga mudena bata lokacinmu akan wannan tunanin, duk miskilancinsa qarya yake ya juyawa mace Kamar ki baya Nihla"
tace" da gaske kike Ilham? "
Girgizakai Ilham tayi," da gaske nake "
Cikin farin ciki ta rungume Ilham
(to ko yaya zata kasance?ko yaya bayanin wasiyya? Fatana kuci gaba da kasancewa Dani)
Kada amanta da sharhi da Comments 🙏🏻
Amnah El Yaqoub ✍️
[6/19, 12:52 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️
{Romance & Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Like my page On facebook 👇
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
13&14
Bayan kwana biyu Aslam ya shirya yatafi India domin tahowa da Aisha, yaso sutafi tareda Abba amma sai Abban Yaqi
Yana sauka a Airport yakira number da Daddy ne yaturo masa amma wayar taqi shiga, haka yadinga tsaki shi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 24