yasa taja blanket din kan gadon tadora a jikinta
Bai tsaya a ko'inaba saida yazo saitin qafafunta, yazuba gwiwar sa aqasa har kafarta tana gogar gwiwar tasa
Shiru yayi yazuba mata ido yana Kallanta, Bece da ita komai ba
Nihla sai kallan mamaki take masa tace "lafiya ne?"
Ahankali, cikin sigar rada yace "kiyi hakuri"
banda dare ne kuma su kadai ne a dakin Babu abinda zai hana takasa jin Mai yace
Tace "for what"
"for Everything, please kiyafemin, nakasa bacci, hankali na yakasa kwanciya, meyasa bazaki yafe minba Nihlaaaa" ya qarasa maganar yanajan sunanta
Shiru tayi masa batace komai ba, Yakalleta yaci gaba da cewa "nasa ranki yabaci saboda nafasa miki wayarki, kiyi hakuri, insha Allah bazan sakeba, but kidena waya agabana, raina yana zafi, idan kikaci gaba dayi zan'iya fasa gaba dayan wayoyin hannunki, Allah ne yasakamin kishin ki acikin zuciyata, bazan dena ba kuma saboda ina qaunar ki, Nihlaaa! kidubi girman Allah kiyafemin, kisoni"
Kallansa tayi, mamaki ya kamata, lalle ya Abba
Ahankali tace "idan kagama inaso Zan kwanta, a tunani na mun dade da gama wannan maganar, babu abinda yayi saura bayan wannan"
Tana fadar haka takwanta, tajuya masa baya sannan taja blanket dinta tarufe jikinta dashi gaba daya
Bayanta ya kalla, yau shi Nihla take juyawa baya, shine yasa kafarsa aqasa yana neman yafiyarta amma taqi, yau shida Nihla takeso shine takasa bashi soyaiyar ta akaro na biyu
Dumin dayaji akan kumatunsa ne yasa yagane hawaye ne suka zubo masa, ahankali yasa hannu ya share, yamiqe yafuto daga dakin tareda ja mata kofar dakin
Yadade awajan ya tsaye idonsa arufe, tsayuwa ma neman gagararsa take, cikin damuwa ya juya yana tafiya ahankali Kamar zai fadi, yayi hanyar dakinsa
Momy ta duba gefenta taga Alhaji yayi bacci, ahankali ta sauko daga kan gadon tafuto daga dakin nasa, Allah nagani bazata iya runtsawa batare dataga halinda yaranta suke ciki ba, dakin Nihla tafara zuwa taganta tana bacci amma wutar dakin akunne, tasa hannu ta kashe mata wutar sannan tajuya, Nihla tana jinta, saboda ba bacci takeba
Dakin Abba tanufa, tana budewa taganshi azaune atsakiyar gadonsa yana kuka wiwi
Gaban Momy yafadi, cikin sauri ta qarasa wajansa tana fadin "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un... Abba!!"
Tana qaraso wa wajansa yafada jikinta, kansa tashafa tace "me yafaru?"
Ahankali yazame yadora kansa akan cinyarta, cikin kuka yace "Momy bata sona, naje wajanta yanzu taqi kulani, Momy zuciyata zafi take min, rannan ma nabata hakuri taqi kulani Momy, yanzu ma haka,Momy ya zanyi? Wallahi ina sonta, kowa Yaqi bani goyon baya, shikkenan ni Kowama ya tsaneni..." hannu tasa tarufe masa baki
Ahankali tace" kayi hakuri Abba, kadinga maimaita kalmar Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, insha Allah zakaji sanyi aranka "
Beyi musu ba haka yafara fada cikin ransa, Momy tana shafa kansa, tunani fal ranta, ahaka sukai bacci, Momy de baccinta ragagge ne, amma shi ya danyi kadan
Kiran sallar farko ne yatashe su, taji jikinsa da zafi, tabashi magani yasha sannan yatafi masallacin gidan, ita kuma ta nufi dakin Daddy
Bayan an idar da sallar asuba Momy bata koma bacci ba, addu'ah taci gaba dayi har gari yawaye tashiga kitchen da kanta tafara hada musu break fast
Karfe tara da minti uku tagama komai, takai musu kan dining, har lokacin Nihla bata futoba da alama bata tashi ba, Abba ma haka
Hanyar dakinta tanufa zataje ta watsa ruwa wayarta tayi qara, duba me kiran tayi mamaki ya kamata, afili tace "Mai hakuri!"
Sannan tadaga wayar, bayan sun gama gaisawa baba yace "hajiya dama maganar yar taki ne"
Tace "to Allah yasa de bamuyi laifi ba,"
"A a bakuyi laifin komai ba, jiya de munzauna da mahaifin Yusif dakuma yan'uwana dasuke yalleman, anyanke ranar bikin yartaki nanda wata biyu masu zuwa insha Allah, saiki fada mata, sannan kuma idan ansamu lokaci Zan turo muku da naku goron saka ranar saiki rabawa mutanan gidan "
Jikin Momy yayi sanyi sosai, cikin sanyin jiki tace" to shikkenan Ibrahim, mungode sosai, Allah yasa ayi damu, insha Allah zan sanar mata itama idan tatashi, yanzu tana bacci "
Yace" to shikkenan hajiya, ki gaida mutanan gidan "
Daga nan sukai sallama, Momy ta zubawa wayar ido tana kallo, wannan al'amari yafara bata tsoro fa, qamshin turaren daya saka ne yasa tadago kanta da sauri ta kalleshi, sanye yake cikin qananun kaya dasuka karbi jikinsa, ta kalli fuskarsa tayi fayau, kana ganinsa zaka hango tsananin damuwa a tattare dashi, tace "Abba na katashi?"
"yes natashi Momy, good morning"
Bata kula da gaisuwar dayake mata ba tajashi har dining tace "zoka zauna nabaka abinci, duk idonka yafada, kacire damuwa aranka fa"
"A a, Momy, bazan iyacin komai ba, kibarshi kawai, inaso zanje saudia, may be nadawo after 3 day's, Momy nasan Daddy yana fishi dani, Kibashi hakuri, kifada masa naje saudia"
Tausayinsa ya kamata, duba yanda yashiga damuwa ahaka ma baida labarin saka mata rana, ahankali tace "saika dawo, zan sanar dashi, amma kayimin alqawarin zaka kula da kanka"
Badan yaso ba ya qaqaro Murmushi yace "insha Allah Momy"
Ahankali yatashi yafita daga falon Momy tabishi da kallo jiki a sanyaye
Sharhi please 🙏
Amnah El Yaqoub ✍️
[7/11, 11:52 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Like my page On facebook 👇
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
49&50
Tasan cewa ba komai ne zai kaishi saudia ba saidon saboda damuwar dayake ciki
Kuma hakan ma tunani ne Mai kyau, domin kuwa addu'ah ita kadai ce mafita Awannan halin da yake ciki, ta Inda yake birgeta kenan, kokadan baya Manta Allah acikin dukkanin al'amuransa
Dakin Daddy tawuce domin sanar dashi yanda sukai damai hakuri
Tana shiga taganshi yafuto daga wanka yana shirya wa
Waje tasamu tazauna agefen gadon tace "Alhaji barka da tashi"
"yawwa Rahma"
Tasake dubansa tace "Alhaji kana nunawa al'amarin yaron nan Kamar bai dameka ba, kuma yana cikin matsala sosai fa, jiya kasa bacci yayi, ita Nihla taqi amince wa dashi, kai yazo da maganar ka koreshi, yanzu haka jikinsa Babu dadi yatafi saudia nasan kuma saboda hakan yatafi, dazu Mai hakuri yakirani yace ansawa Nihla rana nanda wata biyu bikin "
" daidai kenan "
Cikin sauri ta kalleshi tace" Alhaji,yakamata aduba wannan al'amarin, bazai iyu nasamu yarinyar nan da batun taso danaba, Kamar na tursasata ne, tunda batayi niyya ba"
"kinsan da hakan kikazo kikemin magana, ni mezan iyayi akai?"
"Alhaji kaine kuwa zaka iyayin komai, tunda idan kafada tazauna"
"ba kuma zan fada dinba bare tazauna, angama break fast ne?"
Momy ta kalleshi cikin mamaki, Annabi yayi gaskiya dayace abu uwa har sau uku, sannan yace uba 🤣
Tace "angama"
Sannan tashige toilet domin yin wanka
Zaune suke a dining Sunayin break su uku, Momy ta kalli Nihla cikeda kulawa tace "Dazu munyi waya da Mai hakuri yace zai aiko mana namu goron"
Dago kanta tayi "Momy goron me?"
Cikin farin-ciki Momy tace "nasaka ranar yata nanda wata biyu"
Cikin kunya tasa hannu ta rufe idonta
Daddy yayi Murmushi ya kalleta yace "saiki Rubutamin list din abinda kike buqata kije daki ki dauki atm dina kuje keda yayanki kusiyo, abinda Babu kuma saiki shirya kuje Dubai keda momynki kusiyo Acan"
Kanta aqasa cikeda kunya tace "nagode Daddy"
Momy ma tayi Murmushi cikin ranta tana Jinjina irin yanda Allah yasaka musu qaunar yarinyar aransu baki daya
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Tunda yaje saudia baije ko'inaba, yana zaune cikin harami yana addu'ah, ya kashe wayoyin hannunsa, bai nemi kowaba, kuma bayason a nemeshi adede wannan ranakun
Addu'ah yake Allah yakawo masa mafita akan wannan al'amari, idan har Nihla matarsace to Allah yahuci zuciyarta ta soshi, idan kuma ba matar sa bace Allah yabashi hakuri da juriya akan rashin ta, Allah kuma yasa hakane yafi alkhaairi a gareshi
Sosai yaduqufa wajan neman zabin Allah, yana kaiwa Allah kukansa saboda shine Mai kowa Mai komai,kowa ya juya masa baya, banda 'yan'uwansa da Aslam Babu Wanda yake sonsa da Nihla, sai kuma Momy datake tausaya masa, abinci ma ba sosai yake cinsa ba, gaba daya ya rame cikin kwana kin, ya lalace, ga qirjinsa dayake masa zafi sosai idan yatuno da cewa Nihla tayiwa baban ta maganar Yusif, jiyake Kamar ana zuba masa barkono acikin qirjinsa
Allah shine gatansa a yanzu, bashida wani gata daya wuce yakai kukansa wajan mahaliccinmu
Daren juma'ah kuwa yayi addu'ah sosai, yayi kuka yayi kuka harya gaji, sannan cikin dare yabiyo jirgi yadawo gida, su kansu su Momy basusan yadawo ba, saboda Saukar cikin dare yayi
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Zaune yake afalon shi kadai, yana sanye da three quater, da wata riga marar hannu, computer ce agabansa yana ta typing cikin sauri, gaba daya hankalinsa ya tattara shi akan abinda yakeyi
Momy ce tafuto falon sai ganinsa tayi, ta tsaya tayi turus, tace "Abba na yaushe kadawo Babu sanarwa?"
Dagowa yayi daga typing din dayake yadubeta "Momy cikin dare nasauka, bansan na tasheku ne shiyasa banje dakin ki ba"
"to sannu da zuwa, duk wayoyinka akashe, ina kabarsu ne?"
"Momy kashe su nayi wallahi, ina Daddy?"
Zama tayi a gefensa tace "yana dakinsa, yanzu zai futo shima"
Yace "Ok" sannan yaci gaba da abinda yake
Futowa tayi daga dakinta tayi kyau sosai cikin wani Material,qamshin ta dayaji ne yasa Ahankali yadago kansa ya kalleta, karaf idonsu yahadu, itace tafara janye nata idon, shikuwa Kallanta yayi yana mamakin canjawar datayi cikin kwanaki hudu, jikinta yayi lumai, sai wani qara cika takeyi, hankalin ta kwance
, sauke kansa yayi yaci gaba da abinda yake
Momy ta kalleta tace "wannan gyaran jikin nasu gaskiya sun iya sosai, idan aka miki na 3week ma ya'isa, saiki zauna agida kidena fita ko'ina, saiki sanar awajan service din naku ma"
Tace "to Momy"
Ta kalli Abba dake zaune yana typing amma tunani ne da tambaya fal ransa, gyaran jikin me ake mata? Ko bikin qawarta za'ayi? 🤔
Bai samu amsar Tambayar tasaba yaji tace "Ya Abba ina kwana"
Wani irin sanyi yaji aransa, koba komai yana jin dadin yanda take kiran sunansa, gaba daya jiyake Kamar tafi kowa iya fada
Idanunsa har wani lumshe wa suke yadago yazuba mata wani irin kallo Mai karya garkuwar jikin yanmata 🤣
Cikin kulawa yace "lafiya"
Daga haka bata sake cemasa komai ba, Momy ma taji dadin yanda Nihla koda wasa bata raina yayun nataba, gashi de Abba bawani shiri sukeba, ba qaunar sa takeba, amma tana bashi girman sa yanda yadace
Momy tace "Nihla jeki kitchen kidaukomin wannan garon, saiki kaiwa maqota"
Ahankali tatashi, yana jin tashin ta yadaga kansa yabita da kallo, ba komai ne yafi daukar hankalinsa ba irin hips dinta, Momy ta kalli Abba taga inda hankalinsa yake ta girgiza kai 🤣
Saida yaga tashige sannan yasaki wata ajiyar zuciya Mai nauyi, yamaida hankalinsa ga abinda yake
Murmushi Momy tayi cikin ranta tace oh Abba, babu ta ido, inaga mantawa yake da kowa idan Nihla tana waje, agefe daya kuma tausayin dannata yana damunta
Goron takawo da alawa Momy tafara yimata bayani "kikai duka gidajen Dan Allah, idan an tambayeki na menene kifada musu, idan kuma bazaki iyaba kice su kirani awaya"
Tace "to Momy"
Kasancewar unguwar Babu mutane sosai yasa tasaka hannu ta kunce Babban dankwalin kanta, gashin kanta yazubo gafen fuskarta, tasa hannu ta maida shi baya sannan tayafa dankwalin a jikinta kasancewar da girman sa, tadauki goron tanufi hanyar fita
Cikin sauri yatashi yasha gabanta yaje bakin kofar falon ya tsaya, daga Momy har Nihla mamakin yanda yayi tsalle yaje bakin kofar dakin ya tsaya suke 🤣
Shikuwa ko ajikinsa yace "haba Momy Dan Allah, ya za'ayi kibarta tafita ahaka, haka kawai taje tadauko mana magana"
Momy ta girgiza kanta "Abba kabata hanya tawuce mana, menene haka"
Cikin shagwaba yace "gaskiya Momy a a"
Momy ta dubi Nihla tace "dawo ki zauna Nihla, bani goron"
Babu musu tadawo tazauna tareda bata goron
Momy ta kalleshi tace "to tunda ka hanata kaiwa, gashi saikazo kakai"
Yace "wai goron menene ma Momy, saikace masu shirin taro"🙆🏻♀️
Momy kanta tsaye tace "goron saka ranar qanwar ka ne, na saka ranar auren Nihla ne"
Wani dummm! Yafara ji akansa, gabansa yafara faduwa, numfashinsa yafara yin sama, daqyar ya'iya cewa "Momy saka rana kuma?"
Momy data fara tsorata da yanayin sa yace "emana, menene?"
Hannu yasa yadafe kansa dake masa mugun ciwo, qirjinsa ya riqe numfashi yana neman gagararsa, ahankali yadora dayan hannunsa akan qirjinsa, Idanunsa suka fara rufewa, yafara ganin duhu-duhu har suka rufe gaba daya yadena gani dajin komai, nan take ya sulale awajan yafadi
Cikin sauri Momy tayi kansa tana fadin "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un.... Abba!"
Girgiza shi tafara yi amma Babu alamar numfashi awajan Abba, gaba daya Momy ta rikice sai jijjigashi take, hasbunallah wani'imal wakil... Abinda take guje musu kenan dama, nan take hawaye ya balle mata
Ta kalli Nihla cikin kuka tace" yi sauri ki kira Daddynku mutafi asbiti"
Da gudu tajuya zuwa dakin Daddy yana zaune yana duba jarida, ganin yanda tashigo dakin hankali tashe yasa yatashi tsaye da sauri yace "lafiya?"
"Daddy kazo inji Momy"
Cikin sauri yafuto itama Nihla ta biyo bayansa, yana qarasa wa wajanda Abba ke kwance ya tsugunna yana taba fuskarsa yace "meyasa meshi ne Rahma?"
Cikin kuka tace "Alhaji kaga abinda nake fadama ko? Kaga irinta ko? Babu abinda aka masa, kawai dagajin ansa ranar Nihla shine yayanke jiki yafadi"
Daddy yace "subhanallah... Kamamin shi Muje asbiti"
Daqyar suka dagashi, suka tafi asbiti baki dayansu, sai adala kawai aka bari agidan
Zuwan su asbiti keda wuya likitoci suka karbe shi cikin gaggawa, suka shiga bashi temakon gaggawa, Daddy da Momy kam kasa zama sukai, sai Nihla ce take bawa Momy hakuri akan tadena kukan datake amma ina! Hawaye Yaqi tsayawa a idanun Momy
Sun kusa awa daya da zuwa asibitin sannan likitocin suka futo, cikin sauri suka nufesu suna tambaya
Babban cikin su yace "kuyi hakuri Alhaji, ku kwantar da hankalin ku, amma Dan Allah ku kiyaye fadar abinda zai dinga tsorata mutum lokaci daya, yanzu haka danku yaji abinda ya tsorata shi ne sosai, shiyasa yasuma, kuma dama bugun numfashin sa ba normal yake fitaba sakamakon ciwon da zuciyar sa take son kamuwa dashi "
Daga Momy har Daddy hada baki sukai wajan fadin
" ciwon zuciya Doc.?
Kai tsaye yace "qwarai kuwa, amma tunda kunzo asbiti insha Allah zamuyi kokarin ganin yasamu lafiya, yanzu za'a futo dashi a sauya masa daki"
daga haka ya juya yabasu waje
Momy kasa magana tayi daga nan, kawai de tana goge hawayen idonta, kuma har zuwa yanzu kokadan batajin haushin Nihla, fatanta daya, Allah yabawa danta lafiya
Daddy yakira Alhaji Basiru da Alhaji Baqir ya sanar dasu abinda yake faruwa, nan take suma suka Garzayo asbitin
Cikin lokaci qanqani jinyar Abba tacika family din Mazawaje
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Aslam yafi kowa shiga cikin tashin hankali, musanman daya tambayi Momy menene yake faruwa tafada masa komai bata boye masa ba, haka Yazauna yana tunanin mafita
Nihla ya hango tareda Ilham azaune agefe, tana riqeda lil Abba a hannunta
Ahankali yataka yaje wajansu Yazauna, yadubi Nihla tareda miqa mata wayarsa yace "qanwata temakamin da number Angon namu mana"
Murmushi tayi kadan, ta karbi wayar tasa tasaka masa number ya Yusuf aciki, sannan tabashi, ya karba yayi godia
Wayarta ce tahau qara, tana dubawa taga ya Yusuf ne, tadauka
Ilham da Aslam suka kalleta, cikin zazzakar muryarta yace "hello ya Yusuf , yakake yagida"
"lafiya amarya ta, nashigo kano fa, zanzo naganki inaso naji shirye shiryen dakika tsara, saina wuce daga nan"
"Ayya ya Yusuf ai bana gida, munzo asbiti ne, saide nayima kwatancen wajan saimu hadu anan, kaga sai Muje gidama nahadama wani abin kaci"
Be tambayeta waye baida lafiya ba yace "toki turomin adress din Inda kike yanzu"
Sunan asbitin kawai tafada masa yace yana kusa, tace to zata futo waje bakin titi Inda zai ganta
Wayar ta kashe tadubi Ilham tace "zanje waje nadubo ya Yusuf "
Ilham tace "to shikkenan"
Ahankali ta miqe tafuto, Aslam ya kalli Ilham yace "kibita mana, kidan bata shawara ko zata saurareki"
Kallan mijin nata tayi, duk yashiga damuwa, tarasa wacce irin soyaiya sukewa tsakanin su shida ya Abba, tace "to" sannan ta biyo bayan Nihla
Daga murya tayi ta kirata, Nihla ta tsaya ta, sannan ta qaraso sukaci gaba da tafiya
Ilham tace "ya Aslam ne yace nazo naraka ki"
Nihla tace "Allah sarki, kinga salihin miji, wallahi idan ya Abba ne bazai bar matar saba"
Murmushi tayi tace "nikam Nihla nabaki shawara mana"
"inajinki" cewar Nihla
Shiru Ilham tayi, saida suka qaraso bakin titi suna jiran ya Yusuf ya qaraso sannan tace "Nihla Dan Allah meyasa bazaki tausaya wa ya Abba ki aure shiba?"
Cikin sauri ta dago kanta ta kalli Ilham tace "aure fa kikace Ilham"
Hannunta Ilham takama hannunta ta riqe tace "eh, aure nace Nihla, to menene aciki idan kin aure shi? Nihla wacce irin zuciya gareki?yaushe kika koma haka? Mutumin nan yayi miki laifi kuma yabaki hakuri, babu wanda baya aikata kuskure acikin Rayuwar sa Nihla, saide na wani yafi na wani,kidinga tunawa ya Abba dan'uwana ne da'aka bar wasiyya cewa kuyi aure, Nihla ubangijin daya haliccemu ma muna aikata masa laifi muroqeshi gafara yayafe mana, haba Nihla, yanzu ashe bazaki iya tausayawa yaron Momy ba? Bazaki iya ceto yaron Daddy daga halin da yake ciki ba? Nihla wannan shine sakayyar dazaki nunawa Momy kenan? matar da tasoki Tun kina qarama kina gaban mahaifiyarki? Duk cikin yaran Momy Babu Wanda ya qyamaceki Nihla, kowa kokari yake yaga yafaranta ranki, Momy tana qaunar ki Nihla, Inda wata uwarce da tuni ta sauya miki, suna qaunar dansu fa, soyaiyar dasuke miki ce tasa bazasu iya nuna miki komai ba, idan kina tuna laifin dayayi miki bazaki taba yafe masaba, kuma bashi zaki dubaba, a a, iyayen sa zaki duba, kinji de abinda likita yace, zuciyarsa tana gab da kamuwa da ciwo, kuma komai yana hannun ki, idan kinso zaki iya ceto Rayuwar Dan mutanan dasuke kaunarki Kamar yarsu ta cikin su, idan kuma kinso zaki iya barin sa, amma kiyi tunani akai "
Tana gama fada mata tayi shiru tareda sakin hannunta
Zuciyarta fal da tunanin maganganun Ilham, tabbas maganar ta Babu ta yarwa aciki, Momy uwace abar alfahri ako'ina, to amma baban ta fa? Tayaya zata iya nusar dashi? Tayaya zata fuskanci ya Yusuf da wannan maganar? adede lokacin yaqaraso wajansu, suka gaisa cikin kulawa, ahankali suka qarasa cikin asbitin
Ya kalleta yace" yanaga jikinki yayi sanyi ne? Waye baida lafiya? "
Murmushi tayi tace" lafiya ta kalau ya Yusuf , ya Abba ne baida lafiya, dukanmu ma muna ciki, ko zaka qarasa ku gaisa da Momy duk suma suna ciki "
Yace" why not "
Ahankali suka qaraso cikin asbitin, cikeda kulawa Yusuf ya gaisa da kowa, sosai Momy ta ware suka gaisa dashi Kamar Babu abinda yake damunta
Suma su Daddy sun yaba da halin sa sosai, kowa dayake wajan yayaba da tarbiyarsa, babu laifi yanada nutsuwa
Likita ne yazo yace zasu iya shiga su ganshi yanzu, gaba dayansu kuwa suka nufi dakin
Yana kwance hancinsa sanye da oxygen, ga kuma na'ura agefen kansa tana aiki, dakuma wadda take nuna yanayin hawa da Saukar numfashin sa
Cikin sauri Momy ta qarasa wajansa, ta dora kanta agefen gadon tasaki wani irin kuka, tama kasa magana sai kuka datake sosai
Hajiya Farida ce tazo ta janye ta tana bata baki, gaba daya dakin Babu Wanda bai tausayawa Abba ba, ajikin hajiya Faridanma bata dena kukan ba, tari yafara Ahankali, duk hankalinsu saiya dawo kansa, Tun yana tari Ahankali harya dawo yanayi sosai, Aliyu yayi sauri yakira likita, likitan na zuwa yace Dan Allah su fita daga dakin, gaba dayansu suka futo
Aslam yaja Yusuf gefe suna magana, wadda Babu Wanda yasan akan me suke tattaunawa saboda sunyi nesa da mutane
Saida suka gama magana sannan Yusuf yakira Nihla, suka tafi zata rakashi wajan motarsa, har tana mamakin wacce iri magana ya Aslam yayi masa? Kuma menene dalilin karbar number sa awajan ta?
Har gaban motarsa sukaje yashiga Yazauna amma bai rufe motar ba, ta kalleshi tace " banji kace komai ba, akan maganar da mukai waya"
Memakon yabata amsa sai yace "Wancen gayen yacemin sunansa Aslam, yayi min magana akan ki, yace ma ya karbi number ta awajan ki zai kirani kuma sai akai sa'ah nazo, yafadamin saboda ke Abba yake rashin lafiya, kece maganin damuwar sa, yayi min bayani sosai akan hakan, kuma na gamsu da bayanin sa, Nihla why not muhaqura ki auri Abba?"
Mutara zuwa gobe insha Allah 🙏🏻
Sharhi please
Amnah El Yaqoub ✍🏻[7/12, 9:57 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Like my page On facebook 👇
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
51&52
Lokaci daya idanunta suka cicciko da qwallah, ta dubeshi muryarta na rawa tace "ya Yusuf... Mekake fada hakane? Meyasa zaka qini saboda shi?"
"ba saboda shi nafadi wannan maganar ba Nihla, kinsani ina son ki, tunda kina qarama, Tun bansan menene so ba nake tare dake acikin zuciyata, halin da suke ciki shida iyayen sa zaki duba, mutanan nan sun karbeni hannu bibbiyu Babu Wanda ya nunamin komai ko akan fuska, sunada karamci Nihla "
" yanzu me kake nufi kenan?"
" ki auri Abba Nihla"
Batare daya shiryaba hawaye yazubo masa yasaka hannu ya goge cikin sauri sannan Yarufe motar tareda dora kansa akan sitiyarin motar yana kuka
Kallansa tayi tasaki wani irin kuka tareda juyawa ciki aguje tana kuka
Usman dake zaune gefensu Daddy yace "yanzu Daddy ai sai a fadawa su baba Ibrahim adaga wannan aure na Nihla, mu dangin mahaifiyarta bamu shirya ba, saboda Abba bashida lafiya"
Alhaji Baqir yayi Murmushi yace "naga alama de Usman bakason wannan auren ko"
Kansa ya sosa yace "A a kawu, danaga wai hankali ba'a kwance yakeba"
Murmushi yasake yi, amma Daddy de yayi shiru baice komai ba, zuwa yanzu kam kodan ceto Rayuwar dansa yakamata yaje su Gana shida Ibrahim Mai hakuri, yakamata su shirya suje su sameshi
Cikin kuka tashigo wajansu, gaba daya hankalinsu yadawo kanta, Nihla kuwa bata zarce ko'inaba sai wajan Momy, fadawa tayi jikinta tana kuka sosai, Momy tace "me yake faruwa Nihla?keda waye?"
Shiru tayi takasa bata amsa, mezatace mata? Saboda ance na auri danki nake kuka kome? Dan haka tayi shiru, Momy tasa hannu tafara bubbuga bayanta alamar rarrashi, haka tayi shiru amma cikin ranta wani kukan takeji tanaso tayi, Ilham tataso tace" kitashi mukoma can "
Babu musu tabi Ilham suka koma gefe sai Jan zuciya take, Ilham bata tambayeta dalilin kukan ba, tabarta tagama hucewa tukunna
Nihla tayi shiru tana tunani, ita kuma tata qaddarar kenan, sai anzo auren ta afasa, yanzu gashi shima yace ta auri Abba, hakan yana nufin za'a sake fasawa kenan akaro na biyu
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Washe gari Alhaji Basiru da Alhaji Baqir dakuma Daddy da Alhaji habib mijin hajiya Farida suka shirya sassafe suka nufi Abuja
Saukarsu keda wuya Alhaji Isma'iel da baba sukayi musu masauqi acikin falon nasu, baba sai mamaki yake irin wannan zuwan nasu
Saida suka gama gaishe gaishe sannan Daddy yadubi ma hakuri yace "Ibrahim wajan ka mukazo gaba dayanmu nan da qoqon bararmu, haqiqa munyi maka laifi abaya, kuma muna qara neman kuskure, ba kuma komai ne yasa nina aikata hakaba saidon kaunar yar'uwata Aisha dakuma abinda kuka haifa, Awannan lokacin kokadan banaso nayima magana akan Zan dauki Nihla natafi da ita, saboda nasan yanda kake jin mutuwar Aisha kaima bazaka so karabu da yarka ba, nikuma ina qaunar yarinyar, hakanne yasa nadauke ta muka tafi, maganar aure kuma da bamu sanar makaba wannan ma mun dauki laifin mu, amma maganar gaskiya itace banine nayanke wannan hukuncin ba, iyayen mune, bawai ikona bane hakan, amma kayi hakuri "
Baba yayi Murmushi yace"haba Alhaji, ai Babu komai, komai yariga yawuce, rannan ma kuwa Shima Abubakar yazo shida Aslam"
Mamaki yakama su Daddy, ashe su Abba sunyi hankali, Alhaji Baqir mahaifin Aslam yayi Murmushi cikin ransa yace shikkenan ma sun rage mana hanya, yadubi baba yace "ai Abubakar dinma bashida lafiya, yana kwance a asbiti yanzu haka, zuciya ce takeson yimasa ciwo, amma batakai ga farawar ba"
Alhaji Isma'iel yace "subhanallah... Subhnllh, kode shine yaron da Yusuf yake fadamin bashida lafiya?"
Baba yadubi Alhaji Isma'iel yace "A a yaushe Yusuf din yaje kano?"
Alhaji Isma'iel yace "toni jiya yazo yake min kuka waishi afada maka sun hakura da aure shida Nihla, saboda akwai wani dan'uwanta dayake rashin lafiya akanta, wai kada ya mutu a dalilin su, toni kuma ban dauki zancen nasa serious ba, tayaya kuna tareda yarinya zakace kunfasa, ban yarda da maganar tasaba, shiyasa ma ban yiwa mai hakuri maganar ba "
Alhaji Baqir yayi Murmushinsu na manya yace" wallahi shine, ai mungaisa dashi jiya, Yusuf kenan, Yusufa yaron kirki "🤣
Alhaji Basiru yayi gyaran murya yace" ai jikin nasama da sauqi, har yanzu de bai farfadoba,"
Baba ya Jinjina kansa yace " inafa lafiya kana cewa yaro har yanzu bai farfado ba "🤣
Alhaji Isma'iel Yace"Allah sarki, Allah yabashi lafiya, to amma ina ganin tunda yara sun fahimci juna harshi Yusuf din yayi jihadi, to ina ganin kawai ayi hakuri gaba daya tunda kowa ya fahimci kowa yanzu, sai adaura musu aurensu kawai, idan Allah yabashi lafiya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 24