dashi wani lokacin, sunada yara hudu, Usman shine babba, sai Aliyu,Sai farouq, Sannan Abubakar Wanda yaci sunan kakansa suna kiransa da Abba,
Alhaji Baqir kuwa yaransa biyu, Aslam da kuma Adam
Sai Alhaji Basiru, yanada yara uku, Fawaz shine dansa na farko, bayajin magana kokadan, ga kula abokan banza, sai Aisha qanwarsa wadda aka saka mata sunan Diddi, tanada hankali da nutsuwa, sannan ta fannin kamanni suna kamada Nihla sosai Kamar yan gida daya, sai qaramar Ilham, ita kuma ilham rashin kunya, kowa yasan batada kunya yarinyar
Sai hajiya Farida Mai yara biyu Dida, dakuma Diyana
Qa'idar familyn nasu shine tunda suke Babu wani Wanda yake auren bare, saide ka nema a family ka aura, kowa yabi wannan dokar, kwatsam sai Alhaji Basiru yagano wata wadda bata cikin family yace ita yakeso zai aura, adede lokacin itama Aisha Wato Diddi tace tanada saurayi wani bafulatanin yalleman dake jihar jigawa, tace shi takeso, al'amarin yakawo rigima sosai a tsakanin wannan family, har hakan ya haifar musu da rabuwar kai, wasu suna ganin aiba laifi bane hakan tunda ba haramun bane, wasu kuwa suna ganin cewa bedace ba, tunda dokace ta family, cikin su kuwa harda Abubakar, saida aka kai ruwa rana sannan aka rabu dasu sukai auren, da sharadin duk abinda yabiyo baya su sukaja amma kada su nemi kowa
Babu Wanda yakai Abubakar bacin rai akan hakan, ganin idon qanwarsa Yarufe akan soyaiya, hakanne yasa ya tattara ta yawatsar, yadena shiga cikin al'amarin ta, amma cikin qasan ransa yana qaunar qanwarsa, ita kuma matar Basiru hajiya Abida tunda tashigo family din taga basa sonta saita shanye mijin nata da kissa iri iri, idan tasa doka bai isa ya qetare ba, haka kawai kuma Allah yadora mata kaunar Diddi aranta, tana son Aisha sosai, shiyasa tana haifar yarta qanwar fawaz tace Aisha za'a sakawa yarinyar, babu musu mijin nata yayarda🤣
Aisha Wato Diddi tana zaune lafiya da mijinta Mai Suna Ibrahim, amma ana kiransa da Mai hakuri kasancewar mutum ne shi Mai mugun hakuri, dukda halin rashin dayake dashi bata taba nuna masa ba, haihuwar ta ta farko tahaifi mace Mai kama da babanta sak, suka sakawa yarinyar suna fatima, Wato sunan kakarta, amma suna kiranta da Nihla (kyauta)
Wannan shine labarin Mazawaje family
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
"Diddi tunda su yaya Abba suka tafi ko, kullum sai nayi mafarkin su"
Dasauri ta kalli yarta ta taga hankalinta yana kan wasa ma Kamar ba itace tayi magana ba, "suwa kike mafarki Nihla?"
Kallanta tayi cikeda qosawa tace "Diddi nace miki su yaya Abba, nayi mafarki shima munata wasa dashi"
Diddi tace "shi Abban ne ya koma yaya Abba?"
"eh Diddi, ai shine yace nadena cemasa Abba, saide yaya Abba"
Diddi ta Jinjina kanta tace "to suma sauran ai yayunki ne, dukansu haka zaki dinga fada musu"
Tace "to Diddi, yaushe zamuje wajansu?"
Daria Diddi tayi tace "kinason zuwa wajansu ne?"
"eh inaso naje, wai a wanne garin suke Diddi?"
"Suna kano, Nihla, kibari idan akai muku hutu saina kaiki, kiga qawayenki su Aisha, da ilham, da Dida, su Diyana"
"Diddi duk agidan suke suma?"
Diddi tace "duk suna gidan Nihla, idan mukaje zaki gani, gidane babba sosai, kowa aciki yake, amma kowa yana part dinsa, kuma akwai nisa atsakani, amma duk gidanmu daya dasu"
Cikin murna tace "to yaushe zamu tafi Diddi?"
Cikin sauri qosawa da maganar ta tace "nace miki idan anyi muku hutu"
Tace "to Diddi"
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Haka Rayuwar taci gaba da tafiya, yara naqara girma, kuma har zuwa wannan lokacin Diddi bataje gidaba, kuma bata taba kai Nihla cikin yan'uwanta sun gantaba, kullum tayi mata maganar Abba saita shashantar da zancen
Zuwa wannan lokacin Abba yayi candy, Har Alhaji Abubakar yafitar dasu qasar Germany karatu shida Aslam, Dan gidan Alhaji Baqir, tunda yalura hankalin yaron ya karkata akan jirgi 🤣, shiyasa yadage yanaso yacika wa dansa burinsa na ganin yazama cikakken pilot
Yayinda Aslam hankalinsa yafi karkata kan harkar kasuwanci
Bayan shekara biyu Allah yayiwa hajiya rasuwa, mutuwar tataba kowa, wannan family sun shiga damuwa sosai, kowa kaga fuskarsa zaka ganshi dauke da damuwa, Su Abba sunso suzo, amma Alhaji Baqir mahaifin Aslam yahanasu zuwa, yace kawai suyi mata addu'ah, Momy ce takira Diddi tafada mata, a lokacin Nihla tana makaranta, bata jira dawowar ta ba tatafi, shikuma Ibrahim Mai hakuri yace bazai iyu su tafi dukansu subar Nihla ba, idan tadawo ranar uku shi sai yaje
Kowa yaganta a family din yasan ta rame, shi kansa yayan nata daya ganta, saida jikinsa yayi sanyi, gaba daya ta sauya Kamar ba itaba
Bayan angama sutura suka koma part din su Momy, anan takejin labarin tafiyar Abba da Aslam karatu germany, duk yaran gidan sunzo sun gaishe ta, Aisha ce kawai bata ganiba, anan Momy take fada mata cewa tana India tana karatu agidan wani abokin Alhaji, saboda ita tadage bazatai karatu anan ba 🤣
Murmushi kawai Diddi tayi, tace "Allah ya kyauta," suna wannan firar Alhaji yashigo, shima zama yayi, Diddi tasake gaida shi, a mamakinta saitaga ya amsa mata cikin sakin fuska, yana murmushi yace "meyasa baki Taho da mamana ba, Tun tana qarama ban sake ganinta ba"
Diddi tace "Nihla tana makaranta yaya, yanzu ma batasan nataho ba, ashe su Abba suntafi germany"
"wallahi su Abba suntafi, shekarar su biyu kenan, sunaso suzo gida ma nahanasu, nace su bari sai sun gama komai tukunna, aide kuna zaune lafiya ko?"
Mamaki yagama kashe Diddi, tace "yaya lafiya kalau,"
"to alhmdlh, idan kin koma sai kiyi harama hajjin bana dake za'a tafi insha Allah, daga nan sai Rahma tarakaki Dubai kisiyo kayaiyaki kifara business ko"
Saboda murna Diddi harda kukan ta, takasa cewa komai, ahankali shima yatashi ya shige ciki, yanaji kukan ta yana taba ransa, to yaya zaiyi tunda auren de bazata rabu dashi ba, gashi harda Rabon yarinya a tsakani, gara yayi hakuri yaja qanwarsa jikinsa
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
After 8 year's
Da gudu tashigo gidansu cikin murna tace "Diddiyyy"
Sannan tafada jikinta ta rungumeta
"Nihla ke kadai ma zaki karyani kihuta"
"to Diddi ai ina murna ne, kinga result din nawa"
Karba Diddi tayi cikeda murna tace "a a masha Allah, Allah yamiki albarka Nihla, Allah ya albarkaci ilminki, neco tayi kyau waec tayi kyau, saura jamb insha Allah"
Fari tayi da idonta tace"Diddi, wannan karan da kinaso, da bakyaso Diddi sainaje kano, inaso naga su Anty "
" A a Nihla kede kice kinaso kiga Abba, to ai Abban bai dawoba, saide kije kiga su Antyn Kamar yanda kika min qarya daga farko "🤣
Ajiyar zuciya tasauke, ta cire dogon hijabin jikinta, kanta Babu dankwali qananun kalbar da akayi mata tazubo agadon bayanta, ta zubawa waje daya ido tana kallo batare data cewa Diddi komai ba
Kallanta Diddin tayi cikin murmushi" to yanmatan Diddi, me kuma ake tunani? "
" Diddi, Yaya Abba yana germany har yanzu bai dawoba, Yaya yusif yatafi china shima Yaqi yadawo, duk qawayena basa nan, basusan nayi Candy ba, dama suna nan Diddi, shi yaya Yusif naje umma tabani number sa amma kullum na kirashi bata shiga, saura yaya Abba Dan Allah Diddi kicewa Anty taturo miki number sa na kirashi "
Diddi tace" a a babu ruwana, keda kikace zakije kanon da kanki? Idan kinje sai Antyn tabaki "
" shikkenan Diddi, idan naje Zan dauki wayarta da kaina na dauki number sa na kirashi "
Diddi tace" keni kin dameni da zancen wannan mutanan naki 😂, tashi kije kisiyomin maganin zazzabi, zazzabi nakeji "
"to Diddi"
Kudin tadauka agefenta tafice daga gidan
Gidansu Nihla kenan, Diddi ta manyan ta, bakinta manne da haqorin makkah, Nihla taqara girma, kyanta yana nan sai abinda yaqaru, tazama budurwa, idan ka kalleta saika sake kallonta, surutun ta yana nan yanda yake
Maganin takawo mata tasha, da yamma tagyara gidan tsaf, tayi wanka ta shirya cikin riga da siket, hips dinta yafuto acikinsu siket din sosai, 'yan madedetan breast dinta ma haka, dukda basu cika girma sosai ba, amma kana kallansu zaka tabbatar a tsaye suke sosai
Kusada Diddi tadawo tazauna tace "Diddi ko zazzabin ne? Naga kinyi shiru kina tunani"
Ajiyar zuciya tasauke tace "tashi kidaukomin wayata inkira yaya na,"
Saida tayi daria sannan tadauko mata wayar tana cewa "hajiya Diddi kinaji da wannan yayan naki,kuma ni Diddi banga alamun ma yanada Fara'ah ba wallahi"
"zakici ubanki Nihla, yayan nawa kike fadawa haka?"
Shiru Nihla tayi tana daria, Diddi takira yayan nata, bugu yadauka "Aisha kina lafiya ko"
"lafiya kalau yaya, Ya wajansu Abba kuwa? Sai yaushe zasu dawo ne yaya?"
Cikin mamaki yace "Abba sun kusa dawowa, amma Lafiya Aisha?"
"lafiya kalau yaya, kawai na matsu yadawo ne naganshi,"
Saida yayi Murmushi Wanda saika dade kafin ka ganshi yayi sannan yace "Zai dawo insha Allah, idan zai dawo ai zanturo driver yazo yadauke ki insha Allah"
"to yaya Allah yakaimu, Tokai yaushe zakazo yaya?"
Cikin mamaki yace "Aisha wai kalau kike kuwa?"
Saida tayi Murmushi tace "yaya lafiya ta kalau fa, kawai inaso naganka ne"
Jikinsa ne yayi sanyi, me yarinyar nan take nufi ne? Anya kalau take kuwa? Haka yake ta fada cikin ransa afili sai yace mata "inde nine Zan shirya gobe nazo kiganni Aisha, shikkenan?"
"eh yaya shikkenan, ka gaida Anty Rahma, ga Nihla ma tana gaishe ka,"
Yace "toki shafa min kanta" sannan ya kashe wayar, Diddi kuwa maganarsa dariya tabata, wai ashafa masa kanta Kamar wata 'yar yarinya
Da magrib baba yadawo daga kasuwa, suna zaune sunata fira, zazzabin datake ji ma Babu yatafi, sallama akayi akofar gidan, baba yace su shigo, samari ne guda uku suka shigo da kaya niqi-niqi ahannu, kwalin taliya da macaroni sai doya Mai yawa, sukace Alhaji isma'eeil mahaifin Yusif ne yace akawo musu yayi zakkah ne
Godia sukayi musu, baba yanata yabon kirkin mutumin, duk unguwar kowa yana yana yabonsa
Har dare yayi suna zaune suna fira, sannan sukaje suka kwanta, Diddi yau a dakin Nihla ta kwanta, Nihla ta dade dayin bacci, ahankali Diddi ta matsa kusada ita ta rungumeta a jikinta, sannan tayi musu addu'ah itama ta kwanta
Da asuba Nihla ce tafara tashi, kallan Diddi tayi agefenta tace "Diddi asuba tayi"
Bata jira amsarta ba tatashi taje tayi alwala tazo tatada sallah, harta idar Diddi bata tashi ba
Addu'ah tashafa, takama kafarta tace "Diddi asubafa tayi"
Taji shiru, hijabin jikinta ta cire tace "a a Diddi lafiya kuwa?"
Takoma kanta tana tashin ta, amma Diddi ko motsi batayi ba, gabanta ne yayi muguwar faduwa, tafara ja da baya Ahankali, harta futo tsakar gidansu, adede lokacin baba yadawo daga masallaci hannunsa dauke da carbi yanaja
Cikin tashin hankali tafara nuna masa d'akin da hannun ta, tace "Baba Diddi!"
Yace "Diddi kuma? Me yasameta? Ko zazzabin ne?"
Bata iya bashi amsaba, duk jikinta rawa yake kawai tana nuna masa dakin da hannu, Dasauri yashiga, itama ta doru abayansa
Yana zuwa yasa hannu ya tallafo Diddi jikinsa yace
"Aisha!"
Yaji shiru, gabansa ne yafadi yaduddubata, lokaci daya jikinsa yayi sanyi baisan lokacin daya zauna ba
"Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, Aisha, haba Aisha, meyasa zaki tafi kibamu, me.. Yas..sa Aisha" ya qarasa maganar yana kuka wiwi, sake rungumeta yayi yana fadin "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, yanzu Aisha dama tafiya zakiyi kibarmu?"
Cikeda tashin hankali tafara girgiza kanta "A a baba, Diddi bata mutuba, lafiya fa muka kwanta, baba Diddi na bata mutu ba kadena cewa tamutu baba"
Cikin kuka Kamar ba babanta ba yadago kansa ya kalleta yace "Nihla Aisha tamutu, Aisha tatafi ta barmu"😭
(sannu sannu bata hana zuwa saide adade ba'a jeba, dafatan kun gane)
Amnah El Yaqoub ✍️
[6/16, 11:52 PM] El Yaqoub: ❣️ DANGI 'DAYA❣️
{Romance & Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Like my page On facebook 👇🏻
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493/
9&10
Kuka take sosai Kamar ranta zai fita, wai gawar Diddi ce a gabanta Akwance haka, akan idonta makotansu da wasu daga cikin yan'uwan babanta sukayi mata wanka, bata taba tunanin zataci gaba da rayuwa batare da Diddi ba, babu me iya bata hakuri saboda kowa yasan yanda tashaqu da mahaifiyarta, gara abarta tayi kukan ko zataji sassauci
Dole saida aka jinkirta jana'izarta har saida yan kano suka qaraso, dirin motar da sukaji ne ya tabbatar musu da cewa sun qaraso, gaba dayansu sunzo yara da manya, Momy tana kuka tashigo gidan, duk hankalin mutane ya koma kanta, cikin dakin tashige, tana ganin Diddi Akwance anrufeta da farin mayafi tasake sakin kuka tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, Allah yaji qanki Aisha"
Nihla ta kalla datake zaune agefe idonta ya kumbura gashi sunyi jajir, Dasauri ta rungumeta, tana bubbuga bayanta "Nihla kidena kuka kinji, kidena kuka bakiyi rashin uwaba, kina damu kinji yata, kidena kuka"
Duk dakin saida suka sakasu kuka, Alhaji ne yashigo Wato yayan Diddi taredasu Alhaji Baqir gaba dayansu, tsugunnawa yayi agaban gawar, yasaka hannu yabude fuskarta, duk jajircewa irinta Alhaji, saida yayi kuka, yasaka dayan hannunsa Yarufe fuskarsa yana kuka sosai, yakasa magana, yadade yana tsugunne a gabanta, Alhaji Baqir da Alhaji Basiru suka jashi, suka fita dashi, sannan sukayi mata addu'ah, aka qarasa shirya ta, ana daukanta za'a fita da ita waje domin sallah Nihla tasaka kuka ta qanqame Momy tace "Anty zasu tafi da ita"
Kasa magana Momy tayi,domin itama wani irin d'aci takeji aranta
Babu yanda suka iya, haka aka sallaci Diddi aka kaita gidanta na gaskiya, saide muce idan tamu tazo Allah yasa mucika da imani
Ranar da akai sadakar uku data bakwai, da yamma lis yan kano sukai shirin tafiya gida, Momy tana zaune da carbi ahannun ta, wayarta ce tayi qara, wayar tana ajiye kusada Nihla, daukar wayar tayi taga ansa Daddyn Abba hakan ya tabbatar da cewa yayan Diddi ne yake kira, meqa mata wayar tayi tace "Anty Daddy yana kiranki"
Karbar wayar Momy tayi, Cikin ranta tace Daddy.., taji dadin yanda Nihla tace Daddy, amma ita Anty 🤦🏻♀️, batasan meyasa Nihla take kiranta da Anty ba, kokuma har yanzu bata bata matsayin uwa bane a gareta?
Kawar da tunanin tayi aranta tadauki wayar "ki dauko Nihla kufuto mutafi"
Abinda yace da ita kenan, tace "to" tareda kashe wayar, farin ciki yakamata, ta kalli Nihla tace "Nihla tashi ki sauya hijabi mutafi, tare dake zamu wuce"
Batayi tunanin komai ba ta shiga daki ta sauya hijabin jikinta, sannan tadauki wasu kayan acikin jaka sukayi sallama da sauran yan'uwan babanta suka futo
Motoci uku suna jere akofar gidan, suka nufi daya daga ciki, hannunta yana cikin na Momy, Daddy yatashi yayiwa sauran mutanan wajan sallama, amma kokadan baiyiwa Baba magana akan Nihla ba, kawai de yace musu su suntafi, baba yakasa magana, yayi shiru yana kallansu har suka shiga Mota, akan idonsa aka tafi da Nihla, amma bai nuna komai ko akan fuskarsa ba
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Sai dare suka qarasa kano, agate din gidan sukai Parking gaba dayan motocin, zubawa gate din ido tayi, shi kadai ma abin kallone
Ana bude musu gate suka shiga gidan
Anan taga Inda duniya take, Kamar gidan turawa,part hudu ne manya manya agidan, saide akwai nisa sosai a tsakanin kowanne parta, ga kuma Parking space dayake cikeda manyan motoci
Futowa sukai daga motar, kowa yanufi hanyar part dinsa, Alhaji Basiru yace "Nihla sai gobe yan'uwan ki zasuzo ki gansu kinji?"
Daga masa kai kawai tayi, Momy taja hannunta suka nufi nasu part din, suna shiga taga falon yahadu, komai ya tsaru yanda yakamata
Zama sukai dukansu afalon,Usman ya kalleta yanaso yaja hankalinta tadan sake tadena tunani yace "to yar'qauye tazo birni sai kalle kalle take, Momy wannan yarinyar fa sakina rufe mata ido wani lokacin" 🤣
Murmushi Momy tayi "eh lalle Usman bakason auren naga alama, karfa kazo kana kuka nabaka ita"
Daria sukasa gaba dayansu harda Nihla, Aliyu yace "haba Momy, kirasa wazaki bawa sai yaya Usman? Ai yayi mana tsufa Momy"
Dasauri farouq yace "eh dama ai kasan Nihla tawace, ni Momy zata bawa ko Momy?" ya qarasa maganar yana kallan Momy
Tace "duk ba Wanda Zan bawa, ni mijin yata saiya kasance Mai tsananin sonta kunji ko, bazan badata a araha ba"
Alhaji ne yashigo dauke da sallama, dukansu lokaci daya suka nutsu, yakalli Momy yace "Hajiya nina shiga daki, akula da wannan yarinyar"
Saida Momy tayi Murmushi sannan tace "to Alhaji"
Farouq yace"momy nizan wuce gida, nagaji sosai "
Aliyu yace" yes amarya tana jira "
Daria yayi yace" bakada dama yaya Aliyu, "yakalli Nihla yace" my Sister Zan gudu gida, kinsan momynki ta dade da bawa wata ni, idan kin gama hutawa sosai agidan, ki dauki wayar Momy kisaka number ta, ki kirani Muje nakaiki yawo kiga gari, sannan muyi shopping kinji ko? "
Saida tayi Murmushi Mai kyau dimple dinta suka futo sannan tace" to yaya farouq "
Usman yace" eh lalle farouq da alama wani zaiyi kishi dakai idan yadawo "🤣
Nihla bata fahimci komai ba akan maganar Usman, Momy de ta fahimta Dan haka tayi Murmushi
Aliyu ma yayi daria yace" saide ayi Yaqi, ba zamu qi kyautatawa yar qanwar mu ba, "
Yamaida kallansa ga Nihla yace" Nihla kina jina ko?, nima idan kin gama hutawa ki kirani nazo da kaina nadauke ki Muje wajan telan mata ta yayi dinki masu kyau "
Usman yace" to nikam Babu ruwana, zanyi rabiya a tsakani, kada naje nashiga ciki wataran Pilot Yaqi ragemin hanya zuwa Saudia "🤣
Momy tace" Usman baka isaba, bawani rabiya da zakayi, nagane ka, Wato wayo ko? "
Yace " Momy kinsan de halin mutumin naki ko,?amma shikkenan nima idan tagama hutawa zanzo gidan sai abinda tace tanaso da kanta insha Allah "
Momy tace" eh naji "
Daga nan sukai musu sallama kowa yatafi gidansa, Momy tana qara jin dadin yanda kan yaranta yahadu sosai, kuma tasan ba komai yasa sukewa Nihla wannan wasan ba sai don tasake dasu ne ta kuma kwantar da hankalin ta.
Kallan Momy tayi tace" Anty wai duk sunyi aure ne? "
" sunyi aure Nihla, ni kadai ce agidan yanzu, saikuma ke dakika dawo, shi Abba yadade da gama karatu harma yafara aiki, shida Aslam, basu saka ranar dawowa bane, yanzu haka Alhaji yahana afada musu wannan mutuwar amma da yanzu kin ganshi "
Tace" to Anty Allah yabasu zaman lafiya "
" Amin Nihla, tashi Muje kiyi wanka kici abinci saiki kwanta ko? "
Babu musu tatashi, kai tsaye dakin Momy suka tafi, tayi wanka sannan taci abinci, Momy tasa ta ta kwanta, ta qara mata karfin esi sannan takashe mata wutar dakin tafita zuwa wajan Daddy
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Washe gari daqyar tasamu taci abinci, idan tatuna Diddi saitaji wani irin abu yatokare mata maqoshi, daqyar taci kadan ahakan ma saboda Momy ta tsareta ne
Cikin murna tashigo part din nasu da gudu tana kwalawa Momy kira "Momy! Momy!! Momy!!!"
Cikin sauri Momy ta kalli wadda tashigo part din nasu, kafin tayi mata magana yarinyar tace "Jiya Ummah tah tace Nihla tazo, Momy tana ina?"
Murmushi Momy tayi "ilham, Nihla tana dakina, jeki sameta"
Dasauri tashige dakin Momy, a lokacin Nihla tana kwance tana tunanin Diddi, sai jin mutum tayi a jikinta, Dasauri ta kalli wadda tashigo din, kyakykyawa ce sosai wadda ake kira da choculate beauty, ahankali tatashi zaune tana cewa "wash Allah, zaki karyani"
Cikin murna dayar tace "to murna nake ance kinzo, duk bamu sanki ba, kema baki sanmu ba, nide sunana ilham, dama ummah na tana cewa kina kama da yayata Aisha, me sunan Diddi, kuma yau nagani, wallahi kina kama sosai da ita"
Murmushi Nihla tayi "dama kece ilham? Ai duk Diddi tana bani labarin ku, ina Aishan take?"
"tana India, amma ta kusa dawowa, meyasa kika zauna a daki ke kadai bakya tsoron kiyi tunani?,"
Ajiyar zuciya tasaki "nayi karatu ne kuma nagaji, shine nake Dan hutawa, ya karatu?"
Fari ilham tayi da idonta "ai nayi candy, ke dukanmu munyi candy, saide tagaba insha Allah"
"nima nayi candy har na karbi result dina,"
Kafin ilham tayi magana Momy tashigo dakin tace "Nihla tunda ga ilham tazo kuje ta tayaki ki gyara dakin naki ko?"
Ilham tace "eh wallahi zomuje"
Dakin dayaji furnitures da Komai launin green suka fara gyara wa, ilham tafara wanke mata toilet, sannan suka goge kayan dakin, tareda yin moppinga, Nihla tanata yabon halin ilham cikin ranta, babu ruwanta faram faram
Dasuka gama gyara wa zama sukai anan kowa tadau wayarta suka hau Xender suna tura abubuwa
Sallama sukayi suka shigo dakin susu biyu, kana ganin su kasan gidansu daya saboda kama dasuke da juna, daya tana sanye da riga da wando dasuka kamata sosai, gata da uban hips masha Allah,dayar kuwa norml kayane a jikinta, kana ganinta kasan silent ce, me riga da wandon ce ta d'akawa Ilham duka abaya
Sannan tazauna
Ilham tace "haba Diyana, irin wannan daukan ai saiki budamin qirjina"
Zama sukayi suma akan gadon, wadda aka kira da Diyana ta kalli Nihla "haba haba Nihla, wannan hijabin fa, Kamar bakyajin zafin duniyar nan? Kinci wani uban hijabi Kamar matar liman haba be wise mana"
Murmushi nihila tayi tana kallanta, yanda taci wannan riga da wando aidole tayi fada akan hijabi 🤣
Wadda batayi maganar ba tace "Nihla sannu da zuwa kinji, kirabu da Diyana, idan kina neman mace Mai shegen son maza to Diyana ce" 🙆🏻♀️
Kallanta Diyana tayi "to Dida idan banso maza ba mata zanso?🤣
Dida tace "kide rage wallahi, ai a yimaka shedar arziki ma abu ne Mai kyau"
Tashi tayi tsaye, batama kalli yar'uwar tata datayi mata magana ba, tace "Nihla, natafi, saina sake dawowa kokuma inkin shigo, ai zaki zo ko?"
Nihla tace "Zan shigo Diyana, nagode "
Ilham ta kalleta, "sai ina kenan?"
Kai tsaye batare da tantamaba tace "wallahi unguwa zamuje nida wani cika 🙆🏻♀️, yanaso zaiyi birthday zamuje mufara shirin komai, danya takura ne ma wallahi banso zuwaba"
Nihla ta kalleta cikeda mamaki anya kuwa Diyana kalau take? 🤔
Dida tace "ke dince zakice antakuraki? Keda yawo? To idan baki bishi ba ina zakije?"
Babu alamun damuwa tacewa qanwar tata "Dida nadade kema kinsan dadade banje nigh Club ba 😳, wallahi nan nakeso naje"
Wannan karan kam Nihla daria tasaka 🤣
Al'amarin Diyana akwai kallo, kuma duk maganar datake yi hankalin ta kwance, zuciyarta daya take magana
"Ilham tace" to saikin dawo, idan Nihla zatazo Zan rakota masha fira "
Tace musu " ok" sannan tafice
Dida ta kalli Nihla tace "haka take wallahi, Karki yi mamaki 🤣, mune yaran Anty Farida, itace babba ninake binta, kuma wallahi Mom dinmu tasani amma tazuba mata ido, tana zama idan ta tsarata shikkenan sai kiji shiru"
Murmushi Nihla tayi, tace "Diyana kenan" sannan sukaci gaba sa firarsu gwanin sha'awa
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Washe gari Ilham ce tasake dawowa taja Nihla zasuje ta nuna mata kowanne part na gidan, part dinsu suka fara zuwa
Hajiya Abida tana ganinta ta karbeta hannu bibiyu, tana tausayin yarinyar sosai, taso Aisha Wato Diddi, hakanne yasa ta sakawa yarta suna Aisha, kuma ganin Nihla tana kama da Aishanta saitaji dadi, sai nan nan take da ita, sun dade sannan suka futo
Ji tayi taci karo da mutum, Dasauri tadago kanta taganshi a tsaye abakin kofar part din shima zai shigo, dogo ne fari, saide bakinsa dayayi baqi, alamun yana shan wani abun🤔,yaraba gashin kansa biyu yasakawa Rabin colour Mai launin yallow, dayan gefen kuma yabarshi yanda yake, hatta Dan gemun daya tara irinna samari yan gayu shima yasaka masa kala,ga wani uban bluetooth daya toshe kunnuwansa dashi, da alama waqa yakeji, kana ganinsa kaga tantiri na gaske, ahankali tace masa "ina wuni?"
Yace "normal ne, Nihla ko?"
Tanajin irin Tambayar dayayi mata jikinta yayi sanyi, ahankali ta daga masa kai kawai
Yace "okey kihuta"
Yana fadar haka ya shige ciki 🤣
Ilham taja hannun ta suka futo ta kalleta sannan tace "wannan shine yaya fawaz, shine Babban yayanmu, dagashi sai Aisha saini, Tun suna yara yake kula abokan banza har suka koya masa shaye-shaye, babu irin qwayar da baya sha, Tun su ummah suna fada har sun gaji sunyi shiru
Nikuma kinga banaso naga abinda akeyi nayi shiru, kokuma ban shiga sabgarka ba ka shiga tawa, to Zan rama ne, shiyasa Tun muna qanana ake cewa nafi kowa rashin kunya.
Nihla tace "kai wannan gida kuna abinda kukeso wallahi" 🤣
Part dinsu Alhaji Baqir sukaje "hajiya na'ila ta amsa musu cikin sakin fuska, amma aboye hararar Ilham take, saboda yarinyar batayi mata ba kwata kwata 😎
Daga cikin dakin hajiyan yafuto da car key ahannun sa, yana sanye da manyan kaya riga da wando na wani yadi, ya kalli hajiyan yace" mama zanje school inada lacture da yamma "
Tace" to adam saika dawo "
Ilham tace" yaya adam ina wuni"
Sai lokacin yakula dasu, cikin farin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 24