Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
takeso, shine ma yafi" Cikin damuwa Abba yace "zobe, sarqa, kokuma kayan ciye-ciye ai duk sun zama gama gari Aslam" Aslam ya kalleshi cikin mamaki, lalle Abba yashiga dayawa 🤣 Yace "tome kake gani za'a bata?" "why not asiya mata Mota? Kamar zatayi murna da'ita" Aslam yayi dariya yace "gaskiya Abokina Nihla tayima Babban kamu, irin wannan soyaiya haka aiko Nadiya ba'a nunawa itaba" Memakon yabawa Aslam amsa sai yace "please ka bincika min yanzu, inaso akawota yanzun nan" Aslam yace "okey" sannan yadauki wayarsa yafara dube-dube, yadago yadubi Abba yace "wacce irin qira kake buqata?" Kai tsaye yace "Camry" Aslam yace "angama" ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Suna tsaka da aiki iliya maigadi yashigo yace tanada baqo, cikin mamaki tafuto anan taga Baqon fuska, suka gaisa dashi faram faram, gift din hannunsa yabata yace "gashi daga Abuja, inji ogana, yace kiyi hakuri shima yakusa zuwa" Murmushi tayi jin daga Inda saqon yake, tasan ya Yusif ne, tace "a a babu komai wallahi, zamuyi waya dashi, qaraso mana ciki kasha ruwa" Yace "a a Hajiya, inakan hanya ne wallahi, babu damuwa" Nihla tace "to shikkenan nagode" daga nan takoma ciki Tana zuwa tabawa Momy gift din nata tace "Momy, ya Yusif ne ya aikomin da birthday gift" Jikin Momy yayi sanyi, amma dukda haka saida ta nuna murnar ta afili, tace "masha Allah, Allah yasaka da alkhaairi, da alama ko menene aciki zaiyi kyau Kamar kyakykyawar 'yata" Murmushi tayi tafara kokarin budewa tace "Momy bari mu bude mugani" Cikin sauri Momy ta riqe hannunta "a a, kibari idan mungama aiki, kinyi wanka, me makeup tazo tazo tayi miki kungama bikin birthday dinku lafiya saiki bude abinki atsinake" Tace "to Momy," Sannan tayi hanyar dakinta da kyautar tata Dawowa tayi sukaci gaba da aiki, Momy tana ganin tsantsar baiwar da Allah yabawa Nihla, kek din ta cire daga cikin oven tafara yaiyenke gefensa,sannan tadauko wifed cream na ruwa, ta ajiye, tafara neman sauran kayaiyakin buqata Kallan Momy tayi tace "Momy, wai yaushe Daddy zai dawo ne?" "kinyi missing dinsa kenan, gobe zai dawo insha Allah," Cikin murna tace "to Allah yakaimu" Momy taga yanda Nihla take murna saitaji dadi, amma itama kanta tana murna da dawowar da Daddy zaiyi saboda tanaso tayi masa maganar matsalar Abba, gara su zauna dashi suyi masa magana akan Budurwar sa Nadiya, yaushe zasuje anema masa auren nata, bazai iyu suci gaba da zama dashi hakaba Iliyane yasake shigowa cikin part din, fuskarsa dauke da murna, yafara kiranta Dasauri ta kashe oven din suka futo daga kitchen itada Momy, Momy ta zauna akujera tace "dama ni duk kin gajiyar dani, bari nadan huta" Nihla ta kalli iliya tace "iliya danme qarfi lafiya kuwa?" Yace "hajiya kinada wani Baqon ne, gashinan yashigo har ciki, yana compound" Cikin mamaki tafuto harabar gidan, da wata hadaddiyar mota tayi tozali Ash color, qirar CAMRY, na cikin motar da yaga tafuto yabude shima yafuto, yagaidata tareda miqa mata wats takarda da key din motar yace "gashi inji yallabai" Jikin Nihla yayi sanyi, yallabai kuma? Waye hakan? Cikin mamaki ta kalleshi tace "please waye ya aikoka?" Yace "daga campany ne" Daga nan ya juya yatafi, batare daya sake cemata komai ba Motar ta qarewa kallo, tayi masifar yin kyau na qarshe, amma waye wannan dazai aiko mata da Mota? Cikin sanyin jiki tajuya cikin falon su, Momy tace"yanaganki haka jiki a sanyaye, menene? " Zama tayi kusa da Momy ta miqa mata car key din tace "Momy Mota aka aikomin dashi" Momy tace "Mota kuma?" Daga kai Nihla tayi, Momy cikin sauri tatashi ta leqa taga motar Sabuwa ce dal sai daukan ido take, dole nema ta birge Wanda aka mallaka wa ita Tadawo wajan Nihla tace "waye ya aiko miki?" "nima bansaniba Momy, amma gashi harda takarda bari nagani" Momy tace "duba kam" 🤣 Nihla tabude 'yar qaramar takardar da aka hado da'ita tafara karantawa : { _Ina tunanin Babu Wanda_ _ya taba sanar da ke cewa__ _murmushin ki abin so ne ga_ _kowa,duk lokacin da kike yin_ _murmushi yana mayar da fuskar ki tamkar wata_ _fitila mai hasken gaske, You're Beautiful, shiyasa_ _akoda yaushe qwaqwalwata take_ _zana mini kyakkyawar_ _fuskar ki a cikin zuciyata, wadda ta zamo_ _abar kallo a gare ni a_ _duk lokacin da nake_ _zaune ni daya cikin kadaici_ , _murnar qarin shekara._ *ABBA* } Gabanta ne yahau luguden faduwa bayan tagama karantawa, cikin ranta tace ya Abba! Momy dake zaune ta kalleta cikin matsuwa tace "waye ya aiko miki"? Gaskiya banda bakin godewa masu yimin sharhi akan wannan littafin, saide nace Allah yabarmu tare yabar zumunci, inajin dadin yanda kuke sharhi akan DANGI DAYA nagode 🙏🏻 Amnah El Yaqoub ✍️[7/7, 2:00 AM] El Yaqoub: ❣️ DANGI DAYA❣️ {Romance&Friendship luv} Writing by Amnah El Yaqoub Like my page On facebook 👇 https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 41&42 Gabanta sai faduwa yake, yayinda jikinta yayi mugun sanyi tadubi Momy tace "Ya Abba ne" Ita kanta Momy saida tayi mugun mamaki, Abba kuma? Wannan yaron kuwa yasan meyake shirin janyo musu? Aqasan ranta tabbas tayi murna sosai yar'uwa da siyan motar, koba komai Kamar kansu yafara haduwa ne, amma ganin yanda Nihla tayi tsaye jikinta asanyaye yasa tayi Murmushi tace "Ah masha Allah, gaskiya Abba na ya kyauta, to menene kuma kikai shiru banga kina murna ba?" Murmushin yaqe tayi "Momy ya Abba fa nace miki " " aina jiki Nihla, naji abinda kika fada, to menene kuma Dan yayanki yasai miki Mota? Dama ai acikinsu shine baiyi miki Babbar kyauta ba tunda kika zo gidannan, kisaki ranki kije kici Gaba da aikin ki, idan yazo sai kiyi masa godiya" Sai yanzu tayi wata irin ajiyar zuciya tace "to Momy" "kin fadawa su Ilham kuwa?" "eh Momy nafada musu, harsu ya Usman ma" "to shikkenan, kije kici Gaba da aikin ki kiyi sauri Dan Allah" Nihla na wucewa Momy ta kalli key din motar dake hannunta, Innalillahi wa inna ilaihir raju'un... ta dade tana zargin Abba nason Nihla, gashi yau ta qara gani da idonta, kome ya rubuta mata ajikin takardar? 🤔 Su suka sani, abinda tasani de shine itace mace ta farko dazata ziga Nihla akan karta kuskura ta amince wa Abba dukda shine danta mafi soyuwa acikin zuciyarta, Alhamdulillah da Daddy zai dawo gobe. Tana aiki a kitchen amma zuciyarta tana wajan wannan kyauta (ina tunanin Babu Wanda ya taba sanar da ke cewa murmushin ki abin so ne ga kowa...) Kalamansa suka fado mata arai, ta tsaya da aikin tayi shiru, yanzu shi ya Abbanne yaturo mata da wannan kalaman?To idan kyautar Mota Momy tace bawani abu bane, shikuma wannan kalaman fa? Amatsayin me zata daukesu? Kanta datafe tace "kaiii ya Allah!" sannan taci gaba da aikin, tsaf ta shirya kek din yayi mutuqar kyau, Babban kek ne sosai data hada wiped cream fari da ja, tayi adon dasu, ta yankashi daga tsakiya tasaka cream din Wanda tadan disa jar color aciki, Sannan tasake rabashi tasaka farin kawai batare datasa komai ba, yanda idan ka yankashi zakaga cikin kek din yayi kaloli hawa biyu, sama fari, qasa ja Momy tashigo kitchen din tana yin tozali da kek din tace "kai kai kai, masha Allah, amma gaskiya wannan kek din yayi kyau sosai yata, babu wanda zaigani yace kece kika yi" Nihla tayi Murmushi kawai Momy tace "yabaki rubuta sunaba? Ki rubuta sunanku ajiki, amma kifara saka naki sunan, sannan na Abba" "to Momy" Sauran cream din ta dauka ta rubuta Happy birthday Nihla & Abba Momy tace "yawwa kinga saiya qarayin kyau sosai, kije kiyi wanka wadda zata miki kwalliya tana hanya" Hannunta ta wanke tace "to Momy," sannan tafice daga kitchen din, Momy kuma ta kira Adala akan shirya abincin dazasuci anjima ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Wanka tashiga tayi, tafuto daure da towel tana goge jiqaqqen gashin kanta Momy tashigo ta leda a hanunta tace "to gashi inji farouq yace ga tasa kyautar nan" Cikin murna ta karba tabude ledar wani kwali ne Mai kyau babba, tabude taga riga me bala'in kyau ta bayyana, me launin pink,rigar daga qasan ta abaje take sosai gawani uban stone da taji , cikin murna ta rungume Momy, tace "Momy kiga rigar wallahi tayi kyau" Momy tayi daria "yau kam aini ina ganin ikon Allah awajan wannan yan'uwan naki, kingani ko, wannan ne abinda nake fada miki dangane da kyautar da Abba yayi miki, shiyasa nace ki saki ranki" Nihla cikin ranta tace Momy kenan Dan baki karanta abinda yake cikin takardar bane Cikin sauri tashafa Mai da turere sannan tazura rigar, tajuya bayanta tace "Momy zugemin zip din" Momy tarufe mata,rigar ta karbi jikinta sosai, breast dinnan sun futo sosai masha Allah Momy tace "rigar kuwa tayi miki daidai Kamar danke akayi" Zama tayi tafara gyara gashin kanta tace "wallahi Momy tayi kyau sosai" Momy tafuto daga dakin, itama tana gama gyara kanta tafuto tasamu wata Babbar Cardboard paper ta yanki dede yanda takeso sannan ta rubuta Happy Birthday Nihla da biro sannan tadinga bin wajan biro din tana liqa stone's ajiki fari da baqi, dakuma ja, sai rubutun biro din yabuya sai stone din kawai kake gani Tafuto farkon kofar dazata kawoka cikin falon ta manna anan, Momy de tazama yar kallo sai bin Nihla take da kallo Mai kwalliya ce tashigo tareda temakon iliya, nan suka baje afalo tafara yimata kwalliyar tagani tafada, tunma kafin agama Momy tayaba, da aka gama kuwa ita kanta maiyin makeup din saida tayi mata picture, gawani irin Style datayi mata na gyaran gashi, Momy kawai masha Allah take fada aranta, tabbas Abba ya cucesu, Inda ya aure ta ko banza wata rana zata haifa musu yara kamarta Momy ta biya Mai kwalliyar kudi masu yawa sannan tasa driver yamaidata, ita kanta tasan yau tayiwa yar gata kwalliya ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Da yamma su yaya Usman sukazo,gaba dayansu zaune suke afalo, ankawo musu abinci kowa yanaci Futowa tayi suka gaisa gaba dayansu kuwa Babu Wanda bai yababa, Usman yana murmushi cikin ransa yana yiwa qaninsa fatan samun Nihla Momy tasa Adala ta shirya falon da kek din dakomai, sannan ta shirya lemuka agefe, falon yaqara tsaruwa yayi kyau sosai Direban Ilham ne yakai ta gidan Dida da Diyana suka daukosu suka Taho gidan gaba dayansu, zuwansu ne yasa Nihla tatashi sukai cikin dakinta dasu Aliyu yace "Momy karfe biyar saurafa, me take jirane?ta yanka kek din mana muwuce ko" Momy tace "lalle Aliyu yazama dole acika tara, kamanta da birthday din Abba kenan" Aliyu yace "yasalam!, wallahi Momy namanta, yanzu kam nasan Wanda muke jira" Usman yace "ni dama ban Manta ba, nasan yau Abba yake birthday, saikuma da Nihla takirani ta sanar Dani cewa itama tana birthday" Farouq yace "um yau zamu ga yanda d'an miskilin Momy zai yanka kek, ko zai bawa Nihla,? Momy kina ganin bata kiwa?" Tace "kaifa farouq haka kake dajan magana, saikace abokinka?" Dariya yayi yace "Momy kinsan me, wallahi rannan nakama Abba yanata kallan pictures din Nihla, Kamar fa yana ciki" Usman yace "nifa na dade da ganewa, kune de baku fahimta ba amma yanda yake kallanta ma ai ya'isa mutum yagane akwai wani abu" Ajiyar zuciya tayi "Usman Nikaina nasan Abba yanason Nihla, amma bazan yi masa magana ba, zan zuba masa ido naga gudun ruwansa, ban qara tabbatar wa yana sonta sosai ba, sai yau daya aiko mata da Mota wai shine gift dinsa" Gaba dayansu suka kwashe da dariya, Aliyu yace "lalle Abba, ko'itace wannan Sabuwar motar damuka gani a compound?" Momy tace "itace Aliyu, kuma shi kansa yasan cewa abinda yake shirin yi bazai taba iyuba" Usman yace "Momy saboda me? Meyasa zakice haka? Abba yanason ta" "Usman ka Manta abinda Abba yayiwa Nihla ne?" Yace "nasani Momy, abinda yafaru abaya yariga yafaru Momy, Abba da Nihla duka yaranki ne, Kibashi dama yanemi yafiyarta suyi aurensu" "aure fa kace Usman, Hmm to ai ko Nihla ta amince saina zigata tarabu dashi, waye yayi wasa da damar sa?" Farouq yace "Amma Momy munason kasancewar ta acikin mu ne shiyasa" Shima Aliyu yace "Momy ni ina ganin abarshi da yarinyar yanemi yafiyarta yafi, ubangijin daya haliccemu ma muna masa laifi yayafe mana, ke kanki zakiji dadi ace Nihla ce matar Abba, akan yadauko wata yakawo miki, haba Momy kiduba mana" Cikin fishi Momy tace "toku hademin kai saboda qaninku, yayi mata laifi kuma saiya gane kuskuren abinda ya aikata mata" Usman baice da'ita komai ba yatashi yafuto daga falon yana kiran wayar Abba, ya sanar dashi cewa sutaho gida yana nemansa, bai fada masa cewa shi suke jira yazo a yanka kek ba ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Diyana ta kalleta "Nihla gaskiya kinyi kyau sosai masha Allah, Kamar amarya" Cikin sauri tace "agidan ya Yusif ba, bari na kawo muku lemo, babu komai a fridge dina" fita tayi tabarsu Ilham ta kalli Dida da Diyana tace "wallahi akwai abinda nake zargi, kunsan Allah ya Abba naga alama yanason Nihla, bakuga abinda yamata ba rannan" Nan take ta basu labarin komai Adede lokacin Nihla takawo musu lemuka ta ajiye sannan tazauna Diyana tace "aini Ilham haka nakeso, ya Abba ya haukace akan Nihla, yanda zataji dadin juya shi son ranta" Ta kalli Nihla tace "wallahi idan nice ke ko, riga da wando zanyi ta sakawa a gidannan tunda momy ba magana zata mikiba, kidinga daukan hankalinsa" Girgiza kanta tayi "bazan iyaba Diyana, dane da kaina yake rawa nake iya yimasa komai, amma yanzu ni, bazan iyaba, ina fata de yasoni,shima ya dandana abinda naji a raina, yaji irin quncin danaji a lokacin daya qini, nikuma daga baya sainayi aure na" Dida tace " gaskiya Nihla Kamar be kamata ba, tunda kowa yafara fahimtar yana sonka kibarshi da wannan ma ya'isa, meyasa zakike masa fatan yaqara sonki duk dan yaji abinda kikaji kuma daga qarshe ki auri wani bashi ba? Nihla tace "Dida kenan, bakisan abinda naji bane, bakisan wahalar da zuciyata ta fuskanta ba, to wallahi rannan har kuka nayi, saboda taqaici na daya zaije wajan wata zance, hakan yana nufin bayasona kenan, nikuma nafiso yasoni ta yanda Zan nuna masa kuskurensa, sannan daga qarshe na auri ya Yusif, Kamar yanda shima yaqini yace zai Auro wata,da kam naso ya Abba Kamar hauka,kuma naji dadin yanda kukace yafara sona saboda lokaci yayi da zanqi shi na auri bare, Kamar yanda yaqini abaya yaso bare, amma a yanzu soyaiya ta kacokam takoma kan ya Yusif, shi nakeso, kuma shi Zan aura insha Allah" Ajiyar zuciya Ilham tayi "to munji, komai de Yusif Yusif, to munji, saura kuma anjima kikasa bashi kek din" 😏 Diyana tace "shikkenan Nihla, ni dama bazan miki dole akan ya Abba ba, saboda naji ciwon abinda yamiki nima, amma yanzu de tunda taro ne yahadamu anan, Dan Allah kiyi hakuri Karki bamu kunya, kiyi hakuri farin ciki ne yahadamu, kuma shi muke fata yarabamu, Kibashi kek dinnan a baki please " "abakifa kikace Diyana, saikace wani ya Yusif" Dida tace "ai roqonki mukayi, please" Shiru tayi musu kawai, domin kuwa bata tunanin zata iya abinda suka nema Ilham tace "zamu ga kyautar da ya Abba zai miki" Nihla tace "Hmm gatacan kun ganta awaje" Gaba dayansu sukace "Kamar ya" Tace "Sabuwar motar datake compound shine ya aikomin dazu" Gaba dayansu suka hada baki wajan fadin "Mota!" Dida tace "um Ilham nayarda da maganar ki" Diyana ma tayi daria tace "gaskiya nima nayarda yanzu, tab Mota! saikace Wanda kika kai masa budurci lafiya" 🤣 Nihla tace "Diyana banason Wulaqanci, ni wallahi da niyata nabashi key dinsa, amma wai sai Momy tace idan yazo namasa godia, ni kuwa ya Abba mezai fadamin" Ahankali Momy taturo kofar dakin tashigo tace "toku kowa yazo ku ake jira" Fita sukai gaba dayansu zuwa falon, sai fira suke cikin farin ciki Da niyya Diyana ta kalli su ya Usman tace "ya Usman ba yanzu zata yanka bane?" Kafin Usman din yabata amsa farouq yace "sai Abba yazo, suna hanya, yana zuwa zasu yanka tare" Dariya ta kamata, Wato ta lura yaran Momy ma gaba dayansu jona Nihla da Abba sukeyi, tatashi tsaye tace "to mufara yin picture kafin yazo" ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Daga cikin motar suka futo shida Aslam, suna tafiya ahankali cikin aji, hannunsa daya yana cikin aljihun wandon suit dinsa,dayan hannun kuma yana riqeda wayarsa da kuma jacket dinsa Ya kalli Aslam yace "kana ganin wannan kyautar kuwa zata birgeta?" Aslam yace "sosai ma kuwa, kasan mata da Mota, sannan motar tayi kyau sosai, dole zatayi mata kyau Idan tahau" Jinjina kansa yay"to amma wannan kalaman fa?" Murmushi Aslam yayi" haba Abba, ai wannan ma nasan zasufi birgeta fiyeda motar, zasu tsaya aranta nake fadama, haba paper nawa muka 'bata akan tsara kalaman? "🤣 Murmushi yayi shima Bece komai ba, cikin ransa yana fatan hakan, qarasowarsu part din keda wuya sukaci karo da rubutun da Nihla ta liqa awajan Aslam yace" wow wow, Abba waye yayi mata wannan abun? " Murmushi yayi"bansan waye yayi ba, batare nake dakai ba" Aslam yace "a a, Abba kenan, Abba na Nihla" Dariya sukayi suka qaraso cikin falon, ba sukai ga shigowa ba kuwa ya farouq ya kashe wutar falon baki daya Ahankali Abba yace "subhanallah" Kunnawa yayi haske ya gauraye falon, da'ita yafara yin tozali, cikin ransa yace " Beautiful" Itama ana kunna wutar falon idonta yasauka akansa, kalamansa suka fara dawo mata, nan take tayi gaggawar janye nata idon, tayi watsi da kalamansa daga qwaqwalwarta gaba dayansu suka hada baki suna fadin " Happy birthday to you, happy birthday to you, happy birthday happy birthday happy birthday to you... Suna qarasawa suka fara tafi kowa yana daria Qamewa Abba yayi awajan yakasa motsi, ashe shirin da ake musu kenan shiyasa ya Usman yace yataho gida? Ya Aliyu yace "to bamuda lokaci, azo ayanka kek, wannan yaron duk ya bata mana lokaci" Dariya sukai gaba dayansu, Nihla de kanta yana qasa bata cewa komai Ya Usman ya kalleshi yace "to Abba a qarasa mana, Aslam farouq Muje da Allah" Cikin aji ya qaraso gaban kek din, mamaki duk yagama kamashi, Diyana ta janyo Nihla ta kawota kusa dashi, ita kuma ta tsaya daga hannun hagun ta Sunkuyawa tayi zata yanka kek dinta, ya Usman yace "Nihla ya haka,? tsaya ayi pictures tukun" Ya kalli farouq yace "farouq ayi musu pictures" Ya farouq yafara daukan su pictures, gaba dayansu sunyi bala'in birge kowa, danma Babu wani Fara'ah da Nihlan take Nihla kuwa jinta akusa dashi yasa duk ta takura, gashi sai binta yake dawani mayan kallo Aliyu yace "Nihla ku yanka kek din mana, me ake jira" Ahankali ta sunkuya zata dauki wuqar yanka kek din, adede lokacin shima ya sunkuya, yakai hannu takai hannu saijin Saukar hannunsa tayi akan nata hannun, gashi duk sun sunkuya hakan yasa dogon gashinta zubowa ta dede fuskarta, kallan hannunsu yayi, sannan ya juya ya kalleta, itama kallansa tayi tana masa nuni da idonta akan yadauke hannunsa amma saiya shareta Kamar bai ganeba Hasken camera kuwa sai aiki yake awajan, saboda Babu Wanda basu birgeba, kowa zaiyi tunanin wasu shahararrun masoya ne Ahankali ta motsa hannunta suka yanka kek din tare, sannan ta dago, shima yamiqe tsaye Ahankali Bakinta zatakai kek din, Diyana tataka kafarta alamun tabashi amma sai tayi mursisi da'ita, takai kek din cikin bakinta Aslam daya harde hannu aqirji yana Kallansu cikeda birgewa sai lokacin yayi magana yace "no!, Nihla Kibashi mana" Cak ta tsaya da hannunta, ita bataci ba, ita bata bashi ba, ahankali ta juya tana fuskantar sa, tadaga kanta ta kalleshi saboda yamata tsawo, gani tayi idonsa akanta ko kunyar jama'ar wajan bayaji Ahankali tadaga hannun Kamar bataso ta nufi bakinsa dashi, shikuma ganin Kamar zata bashi kunya agaban qannansa su Diyana yasa cikin aji yadora duka hannunsa biyu akan nata, wani irin zirrrr yaji ajikinsa sakamakon laushin dayaji hannunta yana dashi Ahankali yakai hannunta bakinsa yakaryi kek din Dan kadan yaci, sannan yasake kai hannunta bakinsa yayi kissing bayan hannun nata,sannan yasaki hannun Farouq dayaga pictures bazai yi ba saiya koma yimusu vedio kawai 🤣 Diyana datake ziga Nihla akan tabawa ya Abba kek abaki sai tayi shiru tana ganin ikon Allah, tana ganin yanda ake bawa masoyi kek, ita tana ganin idan an bashi abakin ma yayi, ashe shi nasa salon ya dame nasu Shikuwa bejira komai ba ya yanko wani kek din Dan qarami yanufi bakinta dashi, qin bude bakin tayi, yazuba mata ido yana kallan Dan qaramin bakinta yace "Open your mouth" Ahankali tabude bakinta yasaka mata kek din, gaba daya jikinta yayi sanyi,maganar su Ilham de tazama gaskiya Yana saka mata duk falon aka hau tafi, sannan kowa yazo yayanki yanda yakeso, jiki a sanyaye Nihla ta zauna akujera, ta kalli ya farooq tace "ya farouq katuramin pic din ta WhatsApp gaba dayansu, harda Wanda nayi rannan a wayarka" Cikin mamaki yace "wayata? No awayar Abba kikayi, yaturo miki" Shiru tayi bata sake cewa komai ba Momy tafuto daga daki tace "a a, har angama kenan naga kowa ya yanka yanaci" Dariya sukai dukansu, cikin shagwaba Nihla tace "Momy shine kikaqi zuwa" "in banda abinki Nihla abinku na yara mezai kawoni, fatana nide Allah yarayamin ku" Gaba dayansu sukace amin Abba ya kalleta,"Momy thank you, kek din yayi dadi sosai" Murmushi Momy tayi tace "ai Nihla ce tayi da kanta, ita zakayi wa godia" Wani irin dadi yaji acikin ransa, ya juya Yakalleta Bece da'ita komai ba, Sannan yatashi yace "nagaji" yakalli Aslam yayi cikin dakinsa, shima Aslam din yagane nufin sa danhaka yabi bayansa cikin dakin hannunsa dauke da Lil Abba Saida su Dida sukaci sukasha sannan sukai shirin tafiya, amma ko waccensu da magana a bakinta, sai dariya sukewa Nihla ita kuwa ta sharesu Saida sukai sallah sannan suka tafi, suma su ya Aliyu kowa yatafi, Momy tasa Adala tafara gyara wajan, ita kuwa Nihla dakinta tashige tazauna agefen gadon ta tana tuna abinda ya Abba yayi mata, idan tatuno yanda yayi kissing hannunta saitaji gaba daya tsikar jikinta tatashi Haka tashiga wanka tafuto tayi sallah, tasaka kayan bacci masu kauri, sannan tazauna atsakiyar gadon tatafi duniyar tunani, yakamata ace ya Yusif yazo ko yaya ne taganshi, zamanta agidan nan tana hango yar qaramar qura, kowa cewa yake ya Abba yana sonta, Shin idan Momy da Daddy sukaji wannan batun yaya zasu dauki maganar? Su Ilham ma dasuke DANGI DAYA dashi suna bashi goyon baya to inaga iyauensa? Tasan cewa suma sai sunfi kowa murna, kuma da kunya tana zaune acikin gidansu taqi dansu na cikin su,abinda kunya, saide kuma yanda takeji aranta ko duniya da abinda yake cikinta ya Abba zai bata bazata iya auren saba kwata kwata, baba kansa yasan cewa ya Abba baya sonta, amma ya Yusif yayi mata komai, yaso ta a lokacin da Abba yagujeta Saboda haka Tun ana yad'a jita jita a family gara tayi maganin abun Tun kafin ya furta mata kalmar soyaiya Hannunta tadaga sama tayiwa Allah godia daya saka soyaiyar ta acikin zuciyar Abba, ko banza zaiji abinda taji abaya Gift din ya Yusif tafara budewa Bude ledar keda wuya kwalin Sabuwar waya qirar iphone ya baiyana Murmushi tayi tace "Allah sarki ya Yusif" Lokacin dazai siya mata waya tatuna, ya tambyeta wacce takeso tace iphone amma a lokacin kishi ya hanashi siya mata, shine sai yanzu kenan yasiyo mata Kwalin wayar ta dauke anan taga wani kati Dan qarami Mai kyau sai sheqi yake, saikuma rafar kudi yan dari biyar guda daya, Wanda ta tattabar da cewa rafar dubu hamsin ne Katin tabude taga rubutu aciki Mai kyau, nan take tafara karantawa : _Alkawari ne na dauka, ba zan taba barin damuwa ta wanzu_ _a cikin zuciyar ki ba matukar muna a tare da_ _juna, ina fatan nan da dan wani lokaci kadan zaki_ _tabbatar da hakan bayan kin zamo mallakina kuma mata_ _a gare ni, ke kadai zuciyata ta amincewa Nihla,naso_ _nazo naciyar da mata ta kek da kaina amma aiki yamin_ _yawa, dafatan zakimin uzuri, Happy birthday_ Tana gama karantawa tayi kissing katin, tace "i luv u ya Yusif" Wayarta tadauka ta kirashi, ringing din farko yadaga, cikin farin-ciki tace "ya Yusif, irin wannan gift haka, gaskiya naji dadi nagode sosai, i luv u so much dear" Murmushi yayi tareda lumshe idonsa "saqona ya'iso gareki kenan" "yes, yazo, kuma wayar tamin kyau sosai, naji dadi" "da gaske kinji dadi?" "emana ya Yusif, naji dadi sosai" Yace "to tayaya Zan gane hakan?" "mekakeso nayima Wanda zaka gane?" Yace "um think about it" Fari tayi da idonta Kamar yana ganinta tace "to idan kasamu time kasamu baba kayi masa magana akan soyaiyar mu, kaga shikkenan dana gama service sai bikinmu " Sosai Yusif yayi mamakin kalaman ta, Murmushi yayi yace "Really?" Tace "yeah" Murmushi yasaki har tana jiyoshi sannan yace "gaskiya naji dadi, nagode sweethrt,kuma zan sameshi a gobe muyi maganar, zan fadawa Abbana ma, but yanzu yaya taron?" "Alhamdulillah ya Yusif, komai yayi daidai, rashin daidai dinsa shine baka nan" "to kiyi hakuri, tuba nake, idan nasamu

Chapter 16 of 24