Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya duddubashi tareda yimasa yan tambayoyi sannan yace yaci gaba da shan magunguna zuwa jibi za'a warware masa hannun nasa, sannan yafita Ilham kuwa sai murna take bakinta Yaqi rufuwa, kujerar datake kai takoma ta zauna, ta dora hannunta akan goshinsa tace "ya Aslam sannu, ahadama Tea kasha ko?" Dayan hannunsa da Babu ciwo yasa yakawar hannunta dake kansa yace "kidena tabani banaso, ai shikkenan tunda hankalinki ya kwanta, ba haka kike so kiganni ba" Wani irin kuka ne yazo mata maicin rai, batasan lokacin data fada kansa ta rungumeshi ba, tana kuka, hawayenta yana d'isa agefen wuyansa, cikin kukan tace "ya Aslam Dan Allah kayi hakuri Allah nadena" Aslam kuwa baisan lokacin daya lumshe idonsa ba jin nashanunta masu laushi akan qirjinsa, dama gwadat yake yaga tadena rashin kunyar kokuma de tarkonsa yakama shima tafara sonsa🤪 Adede lokacin Adam yashigo dakin, hannunsa dauke da ledojin fruits, murna yafara ganin idon dan'uwansa biyu yaude yafarka, adaya bangaren kuma kunya ce ta kamashi ganin yanda Ilham ta rungumeshi tana wani kuka qasa-qasa 🤣 Aslam yace "Adam sannu da zuwa" Ya kalli Ilham dako niyyar tashi batayi yayi qasa da murya yace "qanina fa yashigo, zakisa ya renani" 🤣 Ahankali tatashi tana goge hawayen idonta tace" ya Adam sannu da zuwa, ina wunin " Adam yayi ajiyar zuciya yace" lafiya Ilham, ashe maigida ya miqe " Murmushi tayi masa kawai, takama hannun Aslam din tariqe Kamar wani zai qwace mata shi. Hajiya Na'ila ce tashigo dakin Diyana tana gefenta da abinci a hannunta Da Adam tafara tozali acikin dakin, yana sanye da qananun kaya, saiyayi mata mugun kyau, ahankali tasauke idonta kasa, shikuwa Kallanta yake yana magana cikin ransa, Wato maryam dayace taje gida saiya nemeta wajansa mahaifiyarsa tatafi kenan 🤣, dama ai matsalar ka auri wadda kuke DANGI 'DAYA da'ita kenan, yanzu Inda bare ya aura ko hanyar gidansu bazata nemaba, Dan Allah kalli wannan shegen kayan data saka duk ya kamata hips dinta awaje, kuma mama tana gani shine suka futo ahaka Cikin nutsuwa Diyana tace "ya Aslam ya jiki?" Yace "jiki Dasauqi Diyana" Ta kalli Adam dinma tace "ya Adam ina wuni ya aiki" 🤣 Shiru Adam yayi be amsa mata ba, haushi yakamata, Hmm zata rama ne Hajiya Na'ila tace "kema de dabata yawun bakinki kike, kina gaidashi yana wani hura hanci, ajiye musu Abincin mutafi gida" 🤣 Diyana ta ajiye Abincin tafice daga dakin, hajiya ta kalli Adam tace "kasan abinda ka aikata ai, shiyasa idan na nemeka baka dagaba, to kazo gida ka sameni ina nemanka" tana fadar haka tafice daga dakin Aslam yace "Adam kayi hakuri, kasan sha'anin mata sai Ahankali, dole sai kakai zuciyarka nesa, da niyya ma zasu dinga qin yiwa mutum biyaiya kasan... Su" Maganar sace ta katse saboda mintsininsa da Ilham tayi ahannu🤣 Adam yayi Murmushi, shikam sun birgeshi, inama maryam zatazo ta koyi yanda ake kula da miji anan, yace "to insha Allah, nizan tafi, sai gobe idan Allah yakaimu" Aslam yace "to shikkenan kakira Abba kafada masa natashi please" Yace "okey" Daga nan yaja musu kofar, Ilham tayi masa hararar wasa cikin shagwaba tace "shine zakake fada masa laifi na ko?" Murmushi yayi yana Kallanta Kamar ba'itaba, Kamar an sauya masa qanwar budurwarsa🤣 Yace "ya jikinki? Yanzu de Babu kuka kin warke sosai ko?" Kunya takama Ilham, tasa hannu ta rufe idonta tace "dan Allah ya Aslam katashi Muje kayi wanka" 🙈 Murmushi yayi, sannan yafara kokarin tashi, yana jin dayan hannun yana masa ciwon kadan-kadan ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Jikinsa a sanyaye yadawo gida yana tunanin mutuwa, kai tsaye dakinsa yawuce yabude kayansa duk wata qwaya datake ciki saida ya dauko ta, nacikin fridge ma yadauko su yazuba acikin wani kwali yanufi dakin Dida dasu, yanaso ya tabbatar mata cewa yau yadena shan komai, yanaso yafara tabbatar wa matar sa cewa daga yau Babu me sake kiransa da Mashayi Amma me, yana bude dakin yaga bata nan, qarasa shiga yayi yaga kofar toilet dinta abude, afili yace "a a, to ina yarinyar nan tatafi ne? Nasan duk Inda zataje tana tambayata ai" Cikin sauri yafuto yadawo kitchen bata nan, yaduba compound bata nan, kwalin dake hannunsa yasaki yafadi qasa, yasake komawa cikin gidan da gudu, karon farko daya fara ambatar sunanta "Dida! Dida!! Dida!!!, ina kike ne?" Wasa-wasa saida Fawaz yagama duba gidan tas yaga bata nan, Kamar mahaukaci haka ya koma dakinta ya kalli Inda akwatunanta suke yaga sunragu, anya kuwa Dida ba guduwa tayi tabarshi ba? Kode taganshi ne dazu bayan yasha maganin mayen nan? Tabbas yarinyar nan taganshi, awajan ya sulale yazube akan gwiwar sa tareda dafe kansa 🤦🏻‍♂️, ya zata masa haka? Dasauri yatashi yafuto daga dakin yashige motarsa bai zarce ko'inaba sai gida Kai tsaye part dinsu yatafi, hajiya Abida tana zaune tana kallo sai ganinsa tayi yashigo Kamar mahaukaci Tace "subhanallah Fawaz lafiya?" Yana daga tsaye yace "umma Dida batazo nan ba?" Tace "Dida kuma? Aini rabona da Dida Tun bikinku Fawaz, kai baka taba hankalin dauko ta ka kawomin ita ko wuni ne muyi ba, itama batazo ba" Gabansa ne yafadi, Yazauna aqasa kafet din falon jagwab, Idanunsa suka kada sukai jajir yace "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un , Umma Dida tagudu tabarni" sai kuka 😭 Gaban hajiya Abida yafadi tace "kaini banason sakarci, yanzu Inda qannanka suna nanma haka zaka zauna kanamin kuka, kayi min bayani dalla-dalla meyake faruwa?" Cikin kuka yace "umma...gani...ganina..tayi nasha wani magani shine... Shine...tagudu" Tace "ahaf, ni nasan da walakin goro amiya, haba Fawaz, yarinyar nanfa tana kokari, aure kusan shekara biyu amma bata taba kawomin kararka ba, lokacin da akace anhadaka da'ita yarinyar nan ko uhm batace ba, duk family dinnan kowa yasan anfi qwararta akan sauran 'yan'uwanta, ai kai kamata yayi ma ace kayiwa yarinyar nan gata samada kowa acikin gidannan, kayi mata abinda takeso ka fifitata saboda ta rufama Asiri ta zauna dakai, yanzu ma dakace akan kasha wani magani tagudu bawani magani dazaka sha Fawaz bayan na maye " Cikin kuka Fawaz yace" to umma kuma saita gudu tabarni " Tace" a a, bamu bincikaba ba zamuce tagudu ba, tashi Muje wajan maigadi muji ko yaga shigowar ta gidan " Tashi yayi yana goge hawaye yabi bayanta, suna zuwa wajan maigadi ya tabbatar musu da cewa tabbas yaga Dida Tun rana tashigo gidan, shine ma yabude mata get Hajiya Abida tayi masa godia takoma part dinta, ta nemi kujera zata zauna kenan Fawaz yasa hannu yariqe rigarta yace "Ummah matata" 😭 Qwace rigarta tayi tazauna tace "tome Zan maka Fawaz? Bakaji da bakinka ance tazo gidaba? Ai kasan hanyar part dinsu" Zama yayi agefen qafafunta yana kuka Kamar mace yace "Ummah Allah nide adawomin da matata, ya za'ai naje part dinsu bayan nasan mamanta bata sona" 🤣 Hajiya Abida tace "kaga Fawaz karufe min baki, ya zakazo kasani agaba kanamin kuka? Lokacin daka mata laifin kayi shawara Dani? To bari kaji, tunda akai auren ku har yau Babu Wanda yace uffan akan zaman aurenku, Dan haka ba zanje part din hajiya Farida tafadamin magana inqyale taba, wallahi saide kaje" Bece da'ita komai ba, yatashi yafice daga part din, yayi nasu Dida, hankalin sa kwance yatura kofar falon, a lokacin kuwa Dida tana zaune itada Hajiya Farida suna kallo, kallo daya tayi masa tadauke kanta, cikin ransa yace tana nan kenan Hajiya Farida tace "a a Fawaz kaine atafe, sannu da zuwa, shigo ka zauna" Fawaz yanemi waje Yazauna yana mamakin yanda ta karbe shi hannu biyu, sai sunkuyarda kansa yake qasa dan karsu gano yasha kuka 🤣 Hajiya Farida ta miqe tsaye tace "Dida kawo masa ruwa mana" daga nan tayi cikin dakinta tabarsu su biyu, cikin ranta tace tasan bazai wuce biko Fawaz yazo ba, ita kuwa bada itaba, yaje su qarata atsakaninsu, tunda taga Dida tadawo gida tasan cewa qarshe yakai yarinyar shiyasa tayi fishi tataho gida, to ba zatayi mata dole akan takoma gidansa ba, Dan daga nanma zata iyayin wani gidan su nemeta su rasa, gara yanda tazo da qafarta, takoma da qafarta, amma bazata bakinta a sabgar yara ba Daga kan kujerar yasauko yadawo kusa da ita har tanajin yanda numfashinshi yake sauka akan fuskarta yace "Dida" Kallansa tayi, yaune karon farko data tabaji yakira sunanta, harara ta sakar masa tatashi ta nufi hanyar dakinsu, shima yatashi yabita, tana shiga dakin tarufo kofar, shikuma yakawo kansa zai shiga sai qumm tabige masa fuska Kadan yarage Fawaz yayi hauka agidan surukai 🤣, haka yafuto jikinsa duk yayi sanya, ko kallan part dinsu baiyi ba yaja motarsa ya koma gida ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Yau Tun safe hajiya Na'ila bataga futowar Diyana ba, Dan futowar datake ta yataya aiki ma yau shiru 🤣 Tace "to wannan yarinya ko lafiya?" tashi tayi ta nufi dakin nata, tana zuwa ta risketa tana kuka adaki, hajiya tace "subhanallah Diyana menene kuma yafaru?" Cikin kuka tace "Hajiya niso nake natafi gidanmu" Hajiya tanemi waje tazauna agefen Diyana tace "ai dole kice zaki tafi gida Diyana, tunda shi yazo ya ajiye ki baya tunanin zuwa ya dauke ki, bansan yaushe Adam yakoyi taurin kaiba, nace yazo gida ya sameni Yaqi zuwa, nakira wayarsa kuma yadena dauka ma yanzu, inde baso yake na yiwa babansu maganar ba bansan yaya zanyi ba, hada kayanki ina zuwa " Gyada kanta tayi, sannan tadauke komai nata na dakin itama ta shirya, hajiya ce tadawo dauke da cup ahannun ta da zuma aciki, tace "ki kalli abinda Zan hada miki kigani saiki dinga yi ," Diyana ta gyada kanta tana goge hawaye Hajiya tazauna tana 'bare gyadar miya da qwai agaban Diyana tanayi tana sababi🤣"ba dole maza su dinga renaku ba, yaran zamani idan anyi muku aure shikkenan saiku zauna dagaku sai i love you, bazaku tashi tsaye akan mazajenku ba, ko wacce mace tanada sirrin ta, kuma ita tasan abinda mijinta yakeso, Inda kin kamashi ahannun ki datun ranar dayace kidawo gida saiya nemeki toko sati daya bazai iyaba zaizo har Inda kike yadauke ki " Akan idon Diyana hajiya Na'ila tagama bare gyadar miya guda goma, da dafaffan qwai guda biyu sannan tazuba acikin cup din zuman nan tabata tace" karbi ki shanye duka " Diyana datayi kasaqe tana kallan ikon Allah takarba ta shanye, zaqin zuman yasa harda saka hannu ta lashe kofin tass🤣 Cikin ranta tana mamakin hajiya, ko da wadannan abubuwan take amfani shiyasa duk masifar ta mijinta yakasa rabuwa da ita? ('yar uwa wanna sirri ne Mai mutuqar kyau wallahi, ko gwada zaki tabbatar da magana ta, wadda bata taba yiba zata samu gyadar miya, irin me qamshin nan, bafa gyada wadda ake gyada amaro da'itaba, a a gyadar miya zaki samu guda goma, kibareta kidaka tadaku sosai, saiki bare dafaffan qwanki guda biyu, ki yaiyanka akan gyadar miyar dakika daka, saiki zuba zuma cokali biyu aciki kijuya sosai, saiki shanye gaba daya, idan kuma kin tabayi to qwai daya zaki yaiyanka Karki sake kisa guda biyu, sirri ne Mai kyau, matan aure zasuji da dinsa sosai, ki jarraba yar'uwa🙏🏻) Hajiya ta dubeta tace "to nan gaba saiki dinga saka qwai daya, kuma biyaiya kici Gaba dayi Diyana, yinayi bari nabari,kuma saikin ja ajinki dakyau, ki nuna masa kema kinada daraja, dan abubuwan Jan hankalin nan kidinga yimasa, yar kwalliyar nan ce duk ki masa" 🤣 Diyana tace "to hajiya, insha Allah" Daga nan hajiya tace tasaka mayafin ta sutafi, aikuwa cikin sauri Diyana tasaka suka futo, ahanya ma fada take qara mata, tana dada wayar mata da kai akan zaman aure har sukaje gidan nasa 🤣 Sabon maigadi suka gani azaune abakin get din, nan hajiya tafada masa kosu waye, aikuwa cikin ladabi yabarsu suka shiga, acikin ma saida hajiya tasake yimata fada sannan tayi mata sallama tatafi, hajiya na tafiya Diyana tatashi tahau gyaran gidan, dakinta tafara gyara wa da toilet Sanna tashige dakinsa, duk gadon nasa a hargitse, haka tahau gyaran dakin tasaka masa Air freshner, duk kayansa daya ajiye a'inda bai daceba ta gyara masa su, takardun dalibai yan jami'ah data gani Kamar ma text ne suma ta tattara masa su waje daya, sannan tafuto ta gyara falon, bata zauna ba tashige kitchen tahada masa abinci Sabon maigadi suka gani azaune abakin get din, nan hajiya tafada masa kosu waye, aikuwa cikin ladabi yabarsu suka shiga, acikin ma saida hajiya tasake yimata fada sannan tayi mata sallama tatafi, hajiya na tafiya Diyana tatashi tahau gyaran gidan, dakinta tafara gyara wa da toilet Sanna tashige dakinsa, duk gadon nasa a hargitse, haka tahau gyaran dakin tasaka masa Air freshner, duk kayansa daya ajiye a'inda bai daceba ta gyara masa su, takardun dalibai yan jami'ah data gani Kamar ma text ne suma ta tattara masa su waje daya, sannan tafuto ta gyara falon, bata zauna ba tashige kitchen tahada masa abinci Sabon maigadi suka gani azaune abakin get din, nan hajiya tafada masa kosu waye, aikuwa cikin ladabi yabarsu suka shiga, acikin ma saida hajiya tasake yimata fada sannan tayi mata sallama tatafi, hajiya na tafiya Diyana tatashi tahau gyaran gidan, dakinta tafara gyara wa da toilet Sanna tashige dakinsa, duk gadon nasa a hargitse, haka tahau gyaran dakin tasaka masa Air freshner, duk kayansa daya ajiye a'inda bai daceba ta gyara masa su, takardun dalibai yan jami'ah data gani Kamar ma text ne suma ta tattara masa su waje daya, sannan tafuto ta gyara falon, bata zauna ba tashige kitchen tahada masa abinci, wainar shinkafa da miyar egusi da kuma lemon danyar citta, tasaka shi a fridge yana daukan sanyi (yau Diyana anzama matar novel 🙊😀) Wanka taje ta sheqo, ta shirya cikin wata 'yar bingilar riga, rigar batazo gwiwar taba, amma saura kadan ta qaraso gwiwar ta ,babu hannu ajikin rigar hakanne yasa lafiyaiyar fatar jikinta ta baiyana, Sanna tazo takunna tv tana sauraren karatun qur'ani Tadauki wayarta tariqe ta, dora kafa daya kan daya tana jira yashigo taji dame yazo inyaso ayita taqare Taurari: D-Diyana A-Abba N-Nihla G-guy (Fawaz) I-Ilham D-Dida A-Aslam Y-Yusif A-Adam (idan naga Comments dayawa zan'iya yin Wanda yafi wannan yawa gobe, idan ban ganiba kuma gaskiya.... 🤒) Amnah El Yaqoub ✍️ [7/1, 12:54 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI DAYA❣️ {Romance&Friendship luv} Writing by Amnah El Yaqoub Like my page On facebook 👇 https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 29&30 Tun daga bakin get maigadi ya sanar masa cewa su hajiya sunzo, yana jin haka yasan cewa may be tare suke da Diyana, Parking yayi yafuto daga cikin motar, yana nufi cikin gidan yana magana cikin zuciyarsa, shida yace taje gida saiya nemeta meyasa zata dawo masa gida, kuma yasan sarai aikin mama ne Yana dosar kofar falon yaji qamshin girki yana tashi, yace ikon Allah, sannan yatura yashiga,falon yabi da kallo yanda ya sauya kama Kamar bashi ba, ga wani qamshi dayake tashi, hakanne yasa ya lumshe idonsa. Tana ganin shigowarsa falon ta miqe sai rangwada takeyi, taje kusa dashi da niyya ta matsa jikinsa sosai tace "Sannu da zuwa" Dasauri yabude idonsa, sai ganinta yayi agabansa, kafin yabata amsa tasa hannu ta karbi Briefcase dinsa, shima da niyya tahana da hannunsa wajan karbar Briefcase din, tace "kawo jakar" Babu musu yasakar mata,yana sakin ajiyar zuciya, sarai tajishi, tajuya tayi gaba da niyya take wata irin tafiya me daukan hankali, tayi cikin dakinsa da jakar Shikuwa Adam sai satar Kallanta yakeyi, Yaqi yadago kansa ya kalleta sosai, saide ta qasan ido yake qare mata kallo, yanzu dama maryam ta'iya wannan gyaran gidan shine bata taba yiba? Acikin kujerun falon Yazauna, yasake lumshe idonsa yana sauraron karatun qur'anin dayake tashi, ga wannan qamshin girkin yacika masa hanci, tabbas zaiso yaji dandanonsa Yana nan zaune tafuto daga dakin, takalleshi taga yanda ya lumshe ido, tatuno yanda ya shareta a hospital, qasa qasa tace ai saina rama ne, qarasawa tayi tazauna ahannun kujerar dayake zaune, taja hannunsa guda daya tace "ya Adam Muje kayi wanka kaci abinci" Cikin basarwa yace "no kibarshi kawai, nagode" Wata irin harara ta zuba masa irin ta baka isa dinnan ba, ta qara jan hannunsa har wajan breast dinta, yanajin yanda hannunsa yake gogar breast dinta cikin ransa yace Innalillah...meyake damun maryam ne, Kallanta yayi, yaga sai sake tura hannunsa take awajan yace "shikkenan sakeni zanje nayi" Murmushi tayi tasakar masa hannun, sannan yashige dakinsa, bata bishi dakin ba tayi kitchen tana kokarin hada masa Abincin, yau kam tasa aranta saitasa ya Adam yadau charge, barema hajiya tagama yimata huduba ai batada damuwa 🤣 Bayan yayi wankan tsaf ya shirya yafuto falon anan yaga irin girkin data hada masa, kokadan besaki fuskar saba, sai wani basarwa yake, yanemi kujera Yazauna yana sauya tasha, ta kalleshi tace zakayi bayani ne, afili tace "ya Adam ga abinci, ka sauko kaci" Batare dayace komai ba yasakko Yazauna aqasan shima, yafara kokarin zuba Abincin da kansa, cikin sauri ta riqe masa hannu tace "kabari mana, yau nice zanyi feeding dinka, Kamar yanda kamin lokacin da banda lafiya" Yace "Am maryam dakin bar..." Dasauri katseshi, tace "shiiiii" Nan take yayi shiru, ta matsa kusadashi tazuba masa Abincin sannan tasa spoon tafara bashi, daqyar Adam yake cin Abincin saboda gaba daya tashige jikinsa, yanajin yanda take goga masa kirjinta ajikinsa, duk yarasa yaya zaiyi da ita, shi yana ganin Ilham da Aslam suna soyaiya a asbiti ashe idan Diyana ce saide arufe ido? Ko yaya yayi motsi saiya gogi kirjinta, gashi ita abin nata masha Allah ba kadan ba, Danya rabata da jikinsa yasa yayi dabara cikin shagaggiyar murya yace "ke bazakici bane?" Diyana tanajin yanda yayi mata maganar tasan cewa lalle tarkon ta yakama, cikin qasa-qasa da murya tace "um um, nafison kaide kafara qoshi tukunna" Jiyayi jijiyoyin kansa suna nema su fara aiki, haka yayi shiru yakasa cemata komai, gaba daya saiya zame mata Kamar wani dolo, haka tadinga bashi Abincin shide sai santi yake aransa, domin kuwa ba qaramin dadi yamasa ba Saida tagama bashi, sannan taci Dan kadan, yazuba mata ido yana Kallanta yanata mamaki, gaskiya duk Wanda ba'a zauna lafiya a gidansa ba to mata basu bashi hadin kai bane, amma inde mata sun bashi hadin kai, to za'a zauna lafiya, kalli de maryam, da ya'isa yayi mata maganar girki ma, amma yanzu shine ake bashi abinci abaki, yaji dadi sosai aransa, kuma yadena fishin shi ya dade da janyewa🤣 Ajiyar zuciya yayi, yace "Maryam girkin yayi dadi sosai" Ajiye spoon din hannunta tayi tace "da gaske ya Adam yamaka dadi?" Jinjina kansa yayi alamun qwarai kuwa Beyi aune ba yaji takai masa wata irin runguma, tace"thnk you ya Adam " Ahankali Adam yace " yasalammm!" Besan cewa sarai Diyana tajishi ba, itama sai tayi fuska Kamar bataji ba, tasake shi tace, "nima naqoshi, bari nakai kayan kitchen" Adam yana ganin shigar ta kitchen ya lallaba yashige dakinsa, Dan idan yaci gaba da zama anan, maryam zata haukatashi da salonta Bayan tafuto daga kitchen taga baya nan tayi Murmushi tace "ko'ina yakai fishin dayake oho?" 🤔 ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Cikin nutsuwa take shirya musu kayansu, yau likita ya sallamesu, shikuwa Aslam yana kwance yana aikin Kallanta, har yau mamakin Ilham yakeyi, kulawar datake bashi ne yasa yaji bayason subar asbitin, duk'da gidan nasu ma su kadai ne, amma saiyake ganin Kamar idan sun koma gida zata dena, tsaf tagama shirya kayan Tajuyo ta kamashi yana Kallanta, yatsina fuska yayi alamun ciwo yace "wash Allah na" Cikin sauri ta qaraso wajansa tace "Sannu ya Aslam, ko wani waje ne yakema ciwo?" Yace "kad'an kad'an nakeji" Jikinsa tafara tabawa tana cewa "ka tabbatar deko?bakajin komai" Qirjinsa ya nuna masa yace "sai nan dina, setin zuciyata yana dan min ciwo kadan" Wajan tasa hannunta tana shafa wa tace "Sannu ya Aslam, ze daina yima ciwon kaji" Lumshe idonsa yayi, yanaji Kamar karta dauke hannunta awajan Ahankali yabude idonsa yace "bafa nan baneba" Cikin mamaki ta kalleshi tace "to'inane? Kode ma kira Doc.?" Cikin sauri yace "um um, kinga irin nan ne fa" Yakai hannunsa kan qirjinta yana shafa wa, wani irin zirrrr taji a jikinta, numfashinta yana sauya wa, gaba daya taji wani irin yanayi yana ziyartar ta, kuma takasa hanashi abinda yake, ganin saqon nasa yasamu karbuwa yasa ya janyota jikinsa gaba daya, babu musu ta dora kanta a Kirjinsa, shikuwa yatura hannunsa cikin rigarta, yana abinda yakeso, kansa yadora akan wuyanta yana kissing wajan, lokaci d'aya Ilham ta lumshe idonta, gaba dayansu nema suke su fita haiyacinsu Ahankali tadago kanta tace "Ya Aslam muna asbiti nefa, katashi mutafi" Ajiyar zuciya yasauke yana Kallanta, sannan yakira number Abba, ko minti talatin basuyi ba kuwa yazo yadauke su, Ilham tana baya tanajin su suna firar kamfaninsu da zasuyi bikin budeshi gobe, ya Abba Babu wasa bayason raini, ko saka Ilham bayayi acikin maganar tasu, saide Aslam yanayi yana juyowa yana Kallanta ahaka har sukaje gida sannan ya juya, sukuma sukai ciki ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Wasa-wasa saida Fawaz yayi zarya awajan Dida harya gaji amma Dida ko kallansa batayi, gaba daya ya lalace, idan ya koma gida Babu abinda yake sai aikin tunanin ta, a yanzu kam shi kansa yasan cewa yana qaunar Dida, saide anata bangaren yanada tabbacin cewa Dida bata sonsa. Abangaren Abba kuwa aiki yataru yayi masa yawa, ganasa aikin da yakeyi, ga kuma aikin campanynsu dasuka bude Wanda yake sarrafa kayaiyakin Furnitures, kuma Abban ne yake jagorantar komai tunda Aslam yana gida yana shan Honeymoon, shiyasa koda yaushe baya zama ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ "kiyi hakuri mana, kukan ya'isa haka" Cikin shagwaba tace "toba saida nace ma akwai zafi ba, amma kai kullum saika dinga qyaleni" ta qarasa maganar cikin kuka Jikinsa ya janyo ta, ya bubbuga bayanta yace "Ilham, toyi shiru mana hajiya ta, kiyi hakuri insha Allah zaki daina jin zafi, Nikaina nayi mamaki ace kusan wata daya kenan amma har yanzu kinajin zafi, but kiyi hakuri zaki dainaji kinji?" ya qarasa maganar cikin sigar sigar lallashi Daga masa kai tayi, kafin tayi magana wani irin amai yataho mata, cikin sauri tatashi da gudu tayi cikin toilet, Aslam yabita da kallan mamaki ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Idan lissafin sa yayi daidai to yau watan Dida daya kenan agida, yau kam saide ayi Wacce za'ayi, amma inde yaje Babu Inda zai dawo saida matar sa, tsaf ya shirya yatafi gidan yaje kofar part dinsu Dida Yazauna, hajiya Farida tafuto falo zatayi kallo saitaga Kamar mutum awaje, tadaga labulen falon nasu kawai sai ganin Fawaz tayi azaune, Dasauri tasaki labulen Tun kafin yaganta, juyowa tayi tadawo cikin falon jikinta asanyaye, wannan yaro yanashan zarya, amma taga alamun Dida ko'ajikinta, Tun bata tausayin yaron harda dawo tana tausaya masa, gaba daya ya lalace wannan Jan lips nasa duk sun bushe 🤣 Haka tayi shiru tana fatan Allah ya hade kan yaran nasu gaba daya Tun la'asar yake wajan, har magrib baije ko'inaba, saide idan ankira sallah yaje masallacin dayake cikin gidan yayi sallah yadawo, itama Dida da magrib din tafuto falo akan idonta yadawo daga masallaci yaci gaba da zama awajan Amma saita nuna batasan ma yana wajan ba, hajiya Farida tana hankalce da'ita, tayi shiru tana kallan ikon Allah Har karfe goma na dare Fawaz Yana wajan, kawai jira yake babanta yadawo yaje ya sameshi suyi magana abashi matarsa, adede lokacin kuma hadari Mai yawa yahadu, sai cida akeyi da walqiya alamun ana gab da yin Ruwan sama. Iska aka fara amma Fawaz Yana zaune, har wajan shadaya na dare sannan ne aka fara sheqa ruwa kamar da bakin qwarya, Fawaz Yana nan zaune ruwa yana dukansa sai karkarwar sanyi yake, kayan jikinsa ya jiqe jalaf Amma tsabar taurin kai yana wajan azaune, daga qarshe ma tashi yayi tsaye ya zubawa part din nasu ido yana kallo Dida na cikin dakinta tana karanta littafi harta sauya kaya zuwa doguwar riga ta bacci, sai dan qaramin mayafi data daure kanta dashi, cikin ranta tace su Fawaz anace, Tun la'asar anzo an zaune, ai yanzu nasan dole yatafi, danni kam bazan koma gidansa yaci gaba da dukana Kamar yasamu jaka ba, littafin ta ajiye tatashi ta zuge window din dakinta taleqa, gabanta ne yafadi ganin Fawaz Acan gefe a tsaye yana karkarwar sanyi, ruwa sai dukansa yake, cikin tsananin mamaki tace "Innalillahi... Ya Fawaz" Dasauri tafuto daga dakin zuwa falo, hajiya Farida taji alamun gudu, tace to Dida ko lafiya? Dida kuwa kofar falon tabude tafuto wajansa tace "mekake yi hakane eh? Sai mura takamaka ko?, kawuce katafi gida" Fawaz yanajinta yayi shiru, kuma still yana tsaye awajan bai motsa ba, Kamar marar gaskiya haka ta kalli gabas ta kalli yamma taga Babu kowa awajan saisu kadai, Sannan tafuto cikin Ruwan itama ta nufeshi, jikinsa tashiga girgizawa tana cewa "ya Fawaz katafi gida, kar zazzabi ya kamaka" Wani irin dadi ne yakama Fawaz, ko banza yau Dida ta kula dashi, cikin sauri ya fusgota jikinsa ya rungumeta tareda hade bakinsu waje daya, tureshi

Chapter 11 of 24