Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tafuto daga cikin dakinta zuwa compound din gidan, tunda aka kawota gidan yaune kawai Adam yaganta da atamfa a jikinta dinkin riga da Zani, kuma sai kayan yayi mata kyau sosai Tana ganin mazan tasaki murmushi tace" guy's, ya garin? Yakuka tsaya daga nan? " Murmushi sukayi, atare sukace" zamu dawo, Karki damu zamu dawo next time "daga nan suka fice da sauri Itama tajuya cikin gidan ko kallan Adam batayi ba, shikuwa binta yayi da kallo yace" Allah ya shirye ki " ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Da yamma suna zaune afalo shida ita, kanta ko dankwali Babu dana daddana wayarta, shikuma yana can kujerar qarshe yana cike wasu takardu daya karbo awajan Abba Tun safe rabonsa da abinci, Dan haka yana gama cike takardun yadago kansa ya kalleta Besan meyasa yarinyar nan take san zama kai Babu dankwali ba, amatsayinsa na saurayin yayarta ai yadace ace tana shiga ta kamala, amma kullum kai Babu dankwali, wani lokacin ma shigar da zatayi idan yaganta daqyar zai dauke idonsa akanta 🙈 Badan yana ganinta amatsayin qanwar budurwar sa ba ai zata iya saka shi awani hali Ajiyar zuciya yayi yadaga murya yanda zata jiyoshi, saboda basa zama waje daya yace "ke tashi kikawomin abinci" Hankalinta yana kan waya tace "banajin yunwa banyi abinci ba" Yace "Wato Ilham na lura kanki yana rawa acikin gidannan, rashin kunyar ki tafara kaini bango, Karki qureni kuma" "to yanzu yaya Aslam girki akace nazo nayi kome? Ni wallahi bazan iyaba, saikace wata jaka" Yace "okey Wato nida nake nemowa na kawo gidan na ajiye nine jaki, 🤣 To bari kiji Dan Allah ki yarda nasake yimiki maganar abinci acikin gidannan" Yana fada mata haka yatashi yafice ransa abace, wannan qaddararran auren yafara isarsa, haba! ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ "A'a, yanmatan Yusif, kece atafe kenan" Ajiyar zuciya tayi "wallahi nice Anty Nadiya, mamy tafita unguwa, saini kadai agidan shiru, shine nace bari nataho wajan ki kawai" cewar Nihla Nadiya tace "hakane kam, kin kyauta masha fira, gashi saurayin naki ma yagudu china" Murmushi Nihla tayi "wai yaya Yusif, aiba saurayina bane Anty Nadiya, Yaya Yusif yaya nane, yayi min abinda dan'uwana yakasa min, inajin sa a raina tamkar yayana da muka futo ciki daya" Gyara zama Nadiya tayi tace "waye dan'uwan naki?" Kai tsaye tace "yaya Abba" "yaya Abba kuma? Kifuto fili kimin bayani Nihla, NI DAKE, munzama Kamar yaya da qanwa, yakamata kibani labarin ki, menene yake yawan sakaki tunani, har kike bige mutum ahanya batare dakin saniba?" 🤣 Nihla tace "Anty Nadiya, labarins yana cike da abin tausayi, nida iyayena natashi, mahaifina ne qaramin qarfi ne, bayan na girma mamana ta rasu, nakoma gidan yayanta da zama har Allah yadawo dashi daga qasar waje" Nadiya tace "wakenan? Kici Gaba mana" Hawaye ne yataru a'idonta, tace "yaya Abba, Tun muna yara nasaba dashi, har na girma da tunanin sa acikin qwaqwalwata,ganin irin sabon damukai dashi muna yara yasa ya daya dawo daga qasar waje nake kula dashi, yanda nake masa zaki dauka ansaka mana ranar aure ne, ashe shi ba haka bane acikin ransa, yanada budurwa, ranar da akace anhadamu aure acikin mutane yace bayasona, akwai wadda yakeso, ahaka iyayen sa zasuyi mana auren bayan an lallabashi ya amince, sai ranar auren babana yaje yadauko ni, muka Taho nan garin ta dalilin baban yaya Yusif, wannan dalilin ne yasa naje ganinsa Kamar yayana uwa daya uba daya, Yaya Yusif yamin abinda yaya Abba yakasa min shi "tana gama bata labari tashare hawayen idonta taci gaba da cewa" bansani ba ko bankai yasonin bane kokuma banida abin dazai gani a wajena yasoni " Kai tsaye Nadiya tace" qwarai kuwa bakidashi Nihla " Da sauri Nihla ta kalli Nadiya cikeda mamaki Nadiya tace"Nihla Dafarko ki kalli Hijabin dayake jikinki, ki kalli irin atamfar datake jikinki, wallahi idan ni kika bawa wannan atamfar taki saina tambayeki dalili, saina zaunar dake nace Dan Allah meyasa kika bani wannan kayan? A a kin renamin hankali ne kokuma tsabar kin maidani yar qauye ne yasa kika banisu? 🤣🤣 Nihla samarin wannan zamanin fa saida dabara, na farko namiji yanason mace Mai aji, Nihla kinje kina zubda ajinki agabansa abanza, wasu mazan zakiga duk wata mace Mai yi musu biyyaiya to zakiga hankalinsu baya kanta, idonsu yanacan wani waje, Nihla tunda nake dake bantaba ganinki Babu hijabi ba, kullum kina cikin hijabi, tayaya zaiga kwalliyarki har wani abu yaja hankalinsa yaji yana sonki? 🤔 ni macece 'yar'uwar ki amma tabbas na yabawa kyanki, kinada kyau Dan kyau, amma awajan wani na mijin hankalinsa bayakan kyau kokadan, hankalinsa yafi karkata kan abubuwan more rayuwa, kuma ke bakidasu" Nihla tayi shiru tanajin maganganun Nadiya, acikin maganar ta Babu ta qarya Nadiya ta dafata tace " babanki yamiki gata daya dauko ki,saboda dakin aure shi ma wahala kawai zakisha, sannan kuma ki godewa Allah dakika hadu Dani, domin kuwa komai yazo qarshe, zan temaka miki, kishigo gari Kamar ko wacce budurwa da takeji da kanta, ta yanda Abba kikace kowa? Bashi kadai ba kowanne namiji ma idan yaganki, saiya sake kallan ki, amma bazai iyuba saikin kwantar da hankalin ki, kin cire shi aranki " Nihla ta kalli Nadiya tace " gaskiya Anty Nadiya inason ya Abba "🤣 Murmushi Nadiya tayi tace" matsalar ku kenan yara, saiku dauki soyaiya kusa aranku Tun bakuje ko'inaba, kinganni nan Nihla, babu na mijin dazan zauna ya renamin hankali, Idan naga take takenka agu Zan tattaraka na ajiye agefe, akwai wani saurayina SADIQ MAZAWAJE, naje germany karatu anan muka hadu, shida kansa ya nuna yana sona kuma na amince, sai daga baya nagane cewa nayi kuskure danake saurarensa, na farko bayamin kalaman soyaiya, sannan bayasan kirana nice nake ta kiransa, ke qarshe ma kwanaki dana kirashi muna waya kawai naji yana magana da wata mace agefe, naji yana cewa zoki ajiye anan, wallahi Nihla tunda nakashe wayata ban sake nemansa ba sai rannan, amma ni Inda yake birgeni akwai riqe alqawari, munyi alqawari dashi zamuyi aure, amma gaskiya Nihla nagaji, ko wacce mace tanason kulawa, amma ni bana samu awajansa, aikinsa kawai yasa agaba,tunda nagane haka saina saka shi awani bangaren daban na ajiye, naci gaba da kula samarina masu bani kulawa, (😳) To kinga ko rabuwa mukai dashi bazanji wani haushi ba, bari kiga pic dinsa " Wayarta tadauka tadubo pic dinsa, tadorawa Nihla data zama mutum mutumi wayar akan cinya, tace "bari in shiga toilet na futo" Batare data lura da yanayin Nihla ba tashige toilet dak! dak! Gaban Nihla yake faduwa, cikin ranta ta furta yaya Abba!!! Gaskya ne, Sadiq yana nufin Abubakar kenan, yanzu dama yaya Abba shine saurayin Anty Nadiya? Saboda Anty Nadiya yaqita? Kallan pic din tayi, karon farko data taba ganinsa cikin kakinsu na pilot Mai launin fari da baqi, yayi bala'in yin kyau a pic din, yana zaune akan kujera wajan da'ake tuqa jirgi Wato ita da yakeso harta samu pic dinsa, amma ita batakai wannan matsayin ba Jikinta har rawa yafara saboda tsananin firgita, abin yabata mamaki sosai, dole dole tasan abinyi Nadiya ce tafuto daga toilet tace "kin ganshi?" Cikin in'ina tace "eh na.. naganshi Anty Nadiya, amma yayi kyau" Nadiya tace "ke rabu da wannan kyan yarinya, kyau Babu kulawa ina wani kyau, idan na aure shi kyan zanci ko kulawar zanfi buqata, shareshi kawai" 🤣 Hausawa sukace naka nakane, hakanan taji bataji dadin furucin Nadiya ba, meyasa zata fadawa dan'uwanta haka? Nadiya tace, kishirya gobe zamuje kasuwa akwai abubuwan dazamu siyo, sannan kincemin akwai atamfofin da Yusif yasiyo miki basuda dinki, zamuje wajan telana ya gwada ki yayi miki dinki nagani nafada, Sanna wannan kan naki zamuje wajan saloon awanke shi, wani satin kuma sai Muje wajan gyaran jiki ayi miki, sonake qanwata ta sauya ta yanda Babu wani na mijin dazai qara rena miki hankali " Murmushin yaqe Nihla tayi" tace " to Anty Nadiya, Allah yakaimu, dama akwai kudin dayamin saura irin Wanda ya Yusif yake bani, saimu hada dashi" Nadiya tace "Karki damu nima akwai kudi a wajena," Washe gari Tun safe suka yiwa many sallama suka tafi wajan tela, Nadiya ce ta karbi tif din da kanta ta aunata, kuma itace tabasu irin Style din datake so ayi mata, daga nan kasuwa suka wuce suka sai : Alkama Shinkafa Gyada Ridi Dawa Hulba Gero Aya Zogale Kanumfari Waken soya Sannan suka dawo gida,Nadiya tace" Sai gobe kuma zamuje wajan saloon,da wankin qafa, " Nihla tayi shiru ta kalli kayan dasuka siyo tace" yanzu Anty Nadiya me za'ayi da wannan hadin? " Murmushi tayi tace" kece zaki dinga sha kullum safe, da dare, idan zaki iyama har rana, zakisa ka ruwa kadan ya tafasa saiki debi garin wannan maganin kidamashi a cup dadan kauri, saiki zuba acikin Ruwan zafin nan nakan wuta kina juyawa har yayi kauri saiki juye kidinga sha da madara ko nono kindirmo, Nihla nabaki wata uku cikakke qirjinki zai qara cikowa sosai, Sannan hips dinki ma zasu sake budewa " (yanmata masu buqata da matan aure zaku iya gwadawa yanayi sosai, shine de ake zuba mukushi aroba azo asiyar muku shi dubu uku uku, dukansu zaki hadesu waje daya ki soya su sama-sama, saiki kai aniqa miki, ki tankade kidinga damawa kinasha 🙏🏻) Jikin Nihla yayi sanyi, jiki a sanyaye tayi mata godia ta tafi gida dashi,da daddare tana zaune agadon ta har sha biyu na dare takasa bacci, tunanin Nadiya kawai take, dame zata sakawa Anty Nadiya? Yazama dole ta cire ya Abba daga cikin zuciyarta kodan Anty Nadiya,dole zata dage da addu'ah akan Allah ya yaye mata, afili ta furta " insha daga yau nahakura dakai ya Abba, koda sanka zaimin illa insha Allah daga ranar yau, nahakura da kai, saide yamin illlar" (kunga laifin Nihla? 🤔) Ina godia sosai da sosai masoyana, yan group din DANGI DAYA kuna sani nishadi, wallahi sharhinku yana bani dariya 😃 oh Abba ma yaga takansa 😚 Amnah El Yaqoub ✍️[6/22, 11:41 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️ {Romance&Friendship luv} Writing by Amnah El Yaqoub Like my page On facebook 👇 https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 21&22 Tunani taci gaba dayi, mahaifin ta bashi dashi Mai qaramin qarfi ne, meyasa ma Tun farko hankalinta Yaqi karkata kan karatu? Wata zuciyar tace saboda soyaiyar Abba Juyi tasakeyi, gashi wadda yaqita saboda itanma bawani sonsa takeba, ita kuma yafuto bainar jama'ah yace baya sonta, gara ta hakura itama dashi, idan taci gaba da sonsa har Anty Nadiya tagano gaskiya haqiqa zatace ta munafurceta, to gara Tun wuri ta tsaida Rayuwar ta waje daya, itama ta haqura dashi dukda tasan abune Mai wahala amma dole zata kamanta , tsaki tasaki afili, tayi juyi tareda addu'ah tarufe idonta Washe gari suka tafi wajan saloon bayan tadawo daga makaranta,ba Nadiya kadai ba, hatta masu shagon tsayawa sukai ganin yanda gashinta yaqara tsawo, gashi Kamar ba 'yar hausawa ba, ita kanta wata irin iska takeji tana shigar ta Duk lokacin data ga Anty Nadiya saita tuno da ya Abba, amma tana kokarin kawar da tunanin sa acikin zuciyarta Sati na zagayowa sukaje wajan gyaran jiki, Nihla saita koma Kamar wata amarya, mamy de tanata Kallanta tana wannan bidiri, saide tayi Murmushi kawai, taga take taken Nihla qarfi dayaji sotake ta sauya Sosai ta maida hankalinta akan karatu, babu ruwanta da kowa a makarantar, kawai karatun ta tasa agaba,dinkunanta da sukaje suka karbo shi tafara sakawa, babu meyi mata kallan raini, bata shiga harkar kowa bama bare ta fuskanci wani bacin rai Kamar yauma tana zaune awaje daya cikin makarantar, littafi ne a hannunta tana dubawa, taji anyi mata sallama, dago kanta tayi ta dubeshi, batare data ce komai ba, shima yayi Murmushi Yazauna dab da ita yace "baki ganeni ba ko?" Tace "eh, bangane kaba" Yayi Murmushi yace "qanin Anty Nadiya nefa Abdallah, anan makarantar nake nima, tacemin kullum kina shigowa shine taturo min number ki tace nanemeki, to nakira taqi shiga sai ita nakira tafadamin Inda zan sameki" Lokaci daya tayi Murmushi tace "ashe kaine, ai inajin labarin ka awajanta,amma ban taba ganinka ba, ya gari?" "wallahi ina wajan friend dinane, kawo natayaki karatun" Yaja littafin ta yana gani, itama da taga yanada kokari saita fara Tambayar sa abinda bata saniba ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Yau Tun safe take shiri zataje wajan biki, wanka ta dauka taci kwalliya Kamar me, sannan ta shirya tsaf tafice batare data kalli ko Inda dakinsa yakeba, shima daya shirya yafuto zai tafi makaranta bai gantaba, kuma beyi tunanin neman Inda tatafiba, Yarufe gidan yayi tafiyar sa Tun azahar yagama abinda yake amma saiya zauna baidawoba sai yamma, daya dawo gidanma abin mamaki bata nan, yayi shiru yana tunani, yarinyar nan tunda akai aurensu gaisuwa ma bata Hadashi da ita, ga mu'amula datake da samari awaje duk yana sane da ita, me zaiyi mata ne yaja hankalin ta ta daina abinda take? Dariyar dayaji ne yasa yadago kansa da sauri ya kalleta, wani shegen mayafi tayafa ga kayan datasa dinkin irin dede da itan nanne, ta kalleshi taci gaba da wayarta tana cewa "ashe pictures sunyi kyau, kaima kagani ashe," Ta saki dariya tashige dakinta Adam yabita da kallo, yanzu idan Diyana zata fita bekai tafada masa Inda zataje ba? Anya yarinyar nan kuwa tasan me ake nufi da aure? 🤔 Binta yayi cikin dakin tana zaune tana cire Dan kunnanta, yace" daga ina kike? " Hankali kwance tace "daga gidan bikin wata qawata" "ke ba'a isa da keba kenan, kindauki qyale qyalen duniya kinsa aranki, maza suna kawo miki ziyara, kinada aure akanki kina waya da wasu qartin banza, to Karki Manta de da aure na akanki, kuma duk abinda kika aikata zunubi kike kwasa akanki" Kallansa tayi tace "zunubi?" Takaici yakama Adam, tabbas idan yaci gaba da kula yarinyar nan, zai iya yimata dukan tsiya, kuma yasan hakan a addinance Babu kyau, cikin bacin rai yafice yayi dakinsa ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Kalau yadawo gidan yau yana cikin nutsuwarsa,yana sanye da qananun kaya sunyi masa kyau sosai, kayan kallo take gogewa tadago taganshi taci gaba da abinda take, beyi mata sallama ba yaqaraso falon Yazauna yana ganin yanda take komai cikin nutsuwa, itama ko kallan Inda yake batayiba, harta gama tashige kitchen Bayanta yabi da kallo kenan shi yarinyar nan saboda bata daukeshi a mijiba ko gaida shi ba zatayi ba bare sannu da zuwa Ajiyar zuciya yasaki yatashi ya shige d'akinsa, Dan qaramin fridge din dakin nasa yabude yadauko magungunan maye ya ajiyesu a gefensa, Yazauna agefen gadon yabude kowanne yasha, sannan ya koma gadon ya kwanta yana lumshe idonsa Acan kitchen kuwa Dida lemon Kankana tahada Mai dadi tahada da Abincin datayi tazuba masa sannan tafuto zata kawo masa, tana zuwa falon taga baya nan, Dan haka kai tsaye tashige dakin da Abincin Tana zuwa gabanta yafadi ganin uban kwalaben dake gabansa shikuma gashinan Akwance yana bacci ko takalma bai cire ba Girgiza kai tayi ta ajiye Abincin agefe ta tsugunna tadauke kwalaben, karantawa tayi, afili ta furta "Benalyn, Codein,Emzolynn, 🙆🏻‍♀️tabdi harda su Emzolynn acikin kayan mayen?" Karaf maganar ta shiga kunnansa, a lokacin bacci yafara fizgarsa Dida kuwa kwashe shu tayi, ta ajiye masa agefe,kafarsa takama tafara kokarin cire masa takalmin, tana cirewa ta zubawa kafarsa ido tana gani, kafar me kyau kuwa, saide Mai kafar bashida kyan hali, ahankali tatashi zatabar wajan yasa kafarsa yabigeta, lokaci daya ta'iyo kansa tafada Kirjinsa, sai jin mutum yayi akan Kirjinsa, Dasauri yabude idonsa yazuba mata ido yana Kallanta Dida kuwa idonta yana kan bakinsa, meyasa yana shan kayan maye amma lips dinsa beyi baqi ba? ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Kasancewar yasan Babu me shigo masa daki yasa daya futo daga wanka yana daure da towel iya qugunsa yanufi cikin kayansa yadauko manyan kaya, saboda baqi dazasu gani shida Abba akan shirye shiryen bude campany nsu. Kayan yadauko ya ajiye sannan yagama shafe shafensa yadawo zai saka kayan, gajeren wando yadauko, ya cire towel din ya wulllashi kan gado, zai saka kenan sai gata taturo kofar dakin tashigo 🙆🏻‍♀️ Tana ganinsa haka tasaki qara tafuto aguje, gabanta sai faduwa yake, Innalillahi..😳,meyakaita dakin yaya Aslam? Shikuwa Aslam yana jin qaranta ya tabbatar yarinyar taganshi, qarasa saka wandon yayi Yazauna agefen gadon yadafe kansa 🤦🏻‍♂️, shikkenan girmansa yazube a'idon qanwar budurwarsa, zance yaqare taga komai Haka yatashi ransa abace yagama shirya wa yafuto, tana ganinsa futowarsa takwasa aguje tayi dakinta, shikuwa Aslam ko Kallanta beyiba yawuce zai fice daga falon, ta kalli bayansa tasaka dariya, tashige dakinta Sarai yana jinta yayi fuska ya shareta, toba dole tayi masa dariya ba, duk yanda yake kare mutuncinsa saida yarinyar nan taga komai, wallahi yanda yakeji aransa idan ta kuskura yadawo tayi masa dariya wallahi sai jikinta yayi tsami 😃 Bayan sun gama ganawa da baqin harma suntafi, sun tsaida ranar dazasu shirya bude campany, Aslam yayi shiru yana tunani, Abba ya kalleshi yace "meke damunka" Ajiyar zuciya yayi yace "wallahi Abba akwai damuwa" "wacce irin damuwa?" "Abba kaga tunda akai auren nan, yarinyar nan ko abinci bata min, kullum ina wajan cin abinci, idan na yi mata magana tafadamin ba dadi" "Aslam wannan ne dalilin dayasa nake fada muku kudena kula qananun yara, amma bakwa ganewa," Ajiyar zuciya yayi yace "yanzu de abinda nake fadama yarinyar nan fa taga komai, koda nayi mata fada bama lalle taji ni ba" Abba yace "Kamar ya, mekake nufi" Cikin haushi Aslam yace "kagane mana, saina futo fili nama bayani ne" Dariya takama Abba, sosai yake dariya yana kallan Aslam Aslam yace "tomiye kuma abin dariya, miye hakan, wallahi Zan huce akanka" Abba yace "maida wuqar abokina, kaima saika rama abinda tama, kaga shikkenan kunyi 50 50, babu wanda zaiyi wa wani dariya" Kallan Abba yayi yace "Kamar ya Abba? Ma kake nufi?" Abba yakama Kunnan Aslam yayi masa rada Lokaci daya sukasa dariya, Aslam yace "kai Abba wallahi bakada dama, natafi, yanzu yanzu zanje nasiyo, sai munyi waya" Daga nan kowa yayi gida Aslam bai zarce ko'inaba sai wani super market da ake saida kayaiyakin wasan yara, daga nan yayi gida, lokacin yamma liss, yana shiga falon yaji qamshin abinci yadaki hancinsa, ahankali yaleqa kitchen yaganta tana girki tana waqa hankali kwance, cikin sand'a yadawo da baya yashige cikin dakinta, yabude toilet dinta yadauko lizard cikin aljihunsa yasaka mata shi dede Inda yaga tana shanya panties dinta, cikin sauri yafuto Yarufe dakin Ahankali ya koma falon Yazauna yadora kafa daya kan daya yana jijjigata Agabansa tafuto daga kitchen din, ta kalleshi tayi Murmushi, tazauna tazuba Abincin ta ita kadai tanaci tana murmushi Kallanta yayi yasan sarai dashi take, sotake yamata magana tafada masa marar dadi, Dan haka yayi shiru yaqyaleta, suna zaune ana kallan kallo har dare yayi, bega tatashi ta shiga dakiba, shikuwa sallah yake zuwa yadawo falon Yazauna, daga qarshe ma bayan sallar ishsha'i wanka yayi yadawo falon Yazauna yana kallo, abin harya fara bata mamaki, yatsina fuska tayi tashige daki, zuciyarta daya tazage ta shiga wanka, cikin nishadi tasha wankan ta tas, ta janyo towel zata daura kenan tayi ido biyu da qadangare, tsaro ido tayi😳 Cikin faduwar gaba tace " Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, nashiga uku me yakawomin masifa cikin toilet" dagudu tafuto towel ahannu Shikuwa yana zaune yana kallo yana shan lemo, yana jin salati yace "lokaci yayi kenan" 🤣 Ahankali yatashi yayi hanyar dakin, yana zuwa bakin qofa sukai karo, jikinta yana karkarwa ta kamashi ta riqe, cikin tsoro tace "yaya Aslam qadangare a toilet dina, wallahi yana ciki, Muje ka ganshi" Aslam kuwa gunki yazama a tsaye, magana take masa amma yadade da shagala yana kallan surar jikinta, ashe haka yarinyar nan take? Jijjigashi tayi tace "yaya Aslam!!!" Firgigit yadawo cikin duniyar mu 🤪 Yanayin sa yadan sauya kadan, ya kwashe da dariya yace "to daura towel din" Sai a lokacin talura da towel din dayake hannunta, kunya ta kamata, cikin sauri taja tarufe jikinta, amma takasa kallan idonsa 🙈 Futowa yayi yabarmata dakin, tabiyo bayansa, yana dauke kafa tana maidawa, yajuyo ya kalleta yace "wai menene?" Cikin shagwaba tace "to Muje kacire min shi mana, haka kawai saika tafi kabarni" Banza yayi da ita ya kashe kayan kallo yadauki wayarsa yayi hanyar dakinsa, itama ta doru abayansa 🤣 Dakinsa yashiga, yafara cire kayansa,cikin sauri tajuya masa baya, Kallanta yayi yanda tajuya bata kalleshi ba, ya zubawa cinyarta ido daga baya, yadauki jallabiya yasaka, yahau gadon ya kwanta Tanajin ya kwanta tataho kansa ta tsaya tana share hawaye, yanajinta ya qyaleta, ita kuwa daga ta haka saita qara gunjin kuka, tsaki yayi yatashi yafuto yabar mata dakin, itama tasake futowa, cikin ransa yace yau naga ta kaina 🤣 Hanyar fita daga falon yanufa tabiyoshi, yajuyo ya kalleta "ina zakije ahaka?" Cikin kuka tace "Allah bazaka fita kabarni ba" Yace "abinci nakeso naje nasiyo, banaso dare yamin" Tace "to baga abinci can a kitchen ba, basai kaje kaciba" Cikin sauri yace "ni? A a riqe abinki, Abincin da ba'abanishi Dan dadi ba saidon wuya?" Yana fadin haka ya juya zai fice, tasa hannu ta riqe gefen jallabiyarsa Yuyowa yayi ya kalleta ya girgiza kai sannan yadawo falon Yazauna, itama tadawo tazauna akusa da qafafunsa 🤣 ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Computer datake gabansa Yarufe ya ajiye ta agefe, sannan yadauki coffee din da Adala Sabuwar Mai aikin Momy takawo masa Yana kai coffee din bakinsa ya runtse idonsa, zaqi yayi yawa, shikuma bayason zaqi, ga shi kansa coffee din har wani d'aci-d'aci yakeyi Tsaki yaja, yadauko cup din yafuto falo yana kwalawa Momy kira "Momy! Momy!!" Momy dake kallo afalo tadago idonta ta kalleshi, tace "Abba nah menene?" Cikin damuwa yace "Momy waye yahada wannan coffee din?" Tace "waye zai hadama coffee Abba bayan Adalaiye? " Tamkar qaramin yaro haka yafara yimata shagwaba "Momy wallahi Babu dadi, zaqi yayi yawa, kuma ni kwata kwata ma bayamin dadi abakina Kamar yanda yarinyar nan take min, duk Babu teste" Momy tayi shiru tana kallansa, Wato Nihla ce bazai fad'aba saide yarinyar nan,ai already Nihla tagama bata Abba da wannan shegen coffee Kamar qa'ida, Tun bayan barinta gidan komai yaci yadinga mita kenan shi Babu dadi 🤔 ajiyar zuciya tayi afili tace "Abba Tun yanzu?" Ko'ina masu lizard zasu kwana yau? 🤔 Oga me coffee ko yaya abin zaici gaba da kasancewa🤣? Amnah El Yaqoub ✍️ [6/23, 11:31 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️ {Romance&Friendship luv} Writing by Amnah El Yaqoub Like my page On facebook 👇 https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 Wannan page din na'yan la'be ne🤪 kawai sonake yau kuma ku futo kuce wani abu 23&24 Yace "Momy me kike nufi?" "A a, babu komai Abba, zanyi mata magana saita gyara" Ajiye cup din yayi "no kibarta Momy, kawai de daga yau karta sake min" Haka ya juya cikin dakinsa ransa duk ajagule, zama yayi yadauki wayarsa yafara kiran number Nadiya, but number busy, cikeda mamaki yakalli agogo "to Dawa take waya Awannan lokacin ?" Babu me bashi amsa, Dan haka yayi wulli da wayar ya kwanta ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Har sha biyu suna zaune jugum jugum afalo, Aslam sai hamma yake yanaso yaje ya kwanta, gashi wannan yarinya ta hanashi sakat, tazo tasa shi agaba da wannan shegen towel din nata Wanda dashi ma gara Babu Ahankali yatashi yayi dakinsa, tatashi tabishi, Bece mata komai ba yahaye gadonsa ya kwanta, kujerar datake dakin nasa tahau ta kwanta itama, saide atakure take Yakalleta yace "kitashi kibarmin dakina" Ilham kuwa tana jinsa tayi banza ta qyaleshi Wai akan masifa ta sameta yake korarta, Hmm zata rama ne, da haka tayi addu'ah sannan tayi bacci, shikuwa kasa baccin yayi yazuba mata ido yana Kallanta dukda ta juya masa baya, daqyar yasamu yayi bacci bayan fama da juye juye dayake, idan Yarufe idonsa, surarta kawai yake gani Tun kafin tatashi daga bacci asubar fari yatashi yaje toilet dinta ya cire lizard din sannan yatafi masallaci ❣️❣️❣️ ❣️ ❣️ ❣️ Yau daga makaranta gida yawuce, yadade agida sannan yakamo hanyar gidansa Tun kafin yasako qafarsa cikin falon ya ganshi kaca-kaca, yariqe qugu ya tsaya yana qarewa falon kallo, fillow's din dake kan kujera duk wasu aqasa, matsawa yayi yaje wajan kayan kallo yasaka hannu yataba, yana duba hannunsa yaga qura Daga murya yayi yafara qwala mata kira "maryam! Maryam!!" Cikin sauri tafuto daga dakinta,fuskarta cikeda kwalliya, riga da wando ne a jikinta, rigar nan takamata kyam ajiki, wandon kuwa tacika abin ta, Dan qaramin mayafi ne a hannunta tana kokarin nad'ashi akanta tace "gani" "yanzu maryam abinda kike acikin gidannan yadace kenan? Bakisan mukwana dake acikin gidannan kibudi baki kice Dani ina kwana ba, idan zaki fita unguwa bankai matsayin dazaki tambayeni ba,bakisan kidafawa mijinki abinci ba, now kalli gidannan, kina nema kibar min gida ya lalace, kalli, kalli Dan Allah cikin falon nan " Yaqarasa magana yana nuna mata cikin falon Kallansa tayi " yanzu ya Adam duk kokarin danake dannaga na zauna dakai lafiya baka gani? Auren nanfa baso nake ba, sannan kana maganar abinci aikai malami ne kasani, haqqinka ne kaci Dani sannan kashayar Dani, ni bazan iyaba!, bazan iyaba!! Bazan takura kaina ba, in tashi dasafe, inyi wanka, inyi kwalliya, inyi kokarin hadawa kaina abinci, sannan kuma inzo ingyarama gida, na maka girki, saboda samu ma inyi mopping,inturara

Chapter 8 of 24