Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
duk wata bidi'ah da za'ayi suyi daga baya " Farin ciki yakama Daddy, da kansa yasauko daga kan kujerar dasuke kai yafara yiwa Alhaji Isma'iel godia, Alhaji Isma'iel yace " Babu komai ai matar mutum kabarinsa " Alhaji Baqir yace" toni ina ganin, tunda abin yazo da haka, memakon Muje musake dawowa, kawai asiyo goro yanzu adaura, shikkenan anhuta " Alhaji Isma'iel yace" A a akwai goro, Muje masallaci anemi liman yadaura musu auren, ni Zan zama waliyin Nihla " Baba yakasa magana ganin irin karamcin da Alhaji Isma'iel yayi masa, haqiqa samun irinsu a yanzu sai antona Gaba dayansu kuwa suka futo, kai tsaye masallacin unguwar sukaje aka kira liman, da maqocin Alhaji Isma'iel Wato baban Nadiya, Alhaji Baqir yaje banki da kansa yaciro kudi, yace shine zaiyi wa Abba waliyi, nan take kuwa aka daura musu aure akan sadaki nera dubu dari, aka danqawa baban ta sadakin, kowa aka bashi goro, suka yiwa limamin ihsani, sannan suka futo kowa zuciyarsa fes Daga nan su Daddy sukayi wa su Alhaji Isma'iel godia, suka nufi Airport Mamy da taji labarin abinda yafaru ta tausayawa Abba, saide wani bangaren na zuciyarta yana jimamin rabuwarta da Nihla, taso ace danta Yusuf yasameta, amma yaya za'ayi, matar mutum kabarinsa ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Zuwan su kenan asbitin itada Dida da Ilham, Diyana bata zoba tana fama da cikin ta, Ilham sai fada take mata "kintashi kinsaka wa kanki damuwa ina dalili? Tunda shine yace zaiyi hakuri yaya zakiyi dashi, amma Tun jiya kidinga kuka,Yaya zakiyi da qaddarar da Allah yadora miki, kokuma zuwa zakiyi wajan Yusuf din kijashi ta qarfi, kuma Momy tayi miki Tambayar duniya kinqi bata amsa, yanzu idan taji saboda Yusuf yace yafasa aurenne saboda danta ya warke kike kuka ai ba zataji dadi ba, menene amfanin rashin mantuwa da ruqo Nihla " Itama Dida tace"wallahi de kam, idan ma kina tunawa da lokacin da yace baya son ki ne agaban family ai yakamata ace zuwa yanzu kisan cewa saboda ke dinne ya kwanta jinya, idan mutane kowa da kowa yaji ya Abba yace baya sonki to yanzu kowa ya shaida ya Abba yadawo yana sonki, kuma gashi Akwance baisan wake kansa ba saboda ke, duk cikin mu waye yasamu irin wannan soyaiyar? Yakamata ki godewa Allah Nihla " Nihla tayi shiru tana jin maganganun yan'uwanta, ahaka suka qaraso cikin asbitin da hannunsu dauke da abinci, kasancewar ba'a barin kowa yashiga dakin dayake shiyasa suka nemi waje suka zauna, sai Momy ce kawai acikin dakin nasa Daddy ne yashigo asbitin fuskarsa dauke da farin-ciki Kamar ba dansa ne baida lafiya ba Su Ilham suka gaida shi, sannan Nihla takira wayar Momy tafuto daga cikin dakin Gaisawa sukai dasu Ilham suka qara yimata, yamai jiki sannan suka bata Abincin, Momy taji dadi sosai tayi musu godia sannan sukai mata sallama suka tafi, sukabar Nihla awajan Tazauna tana duba wayar hannunta, Momy dake gefe itada Daddy tace "Alhaji yanaga kanata Fara'ah ne? Allah yasa lafiya" Murmushi yayi yace "daga Abuja muke" "Abuja kuma Alhaji, meyake faruwa" Hannu yasa a aljihunsa yadauko goro yace "riqe wannan goron" Momy ta karba tace "na menene Alhaji?" Yace "goron daurin auren Takwarana ne shida yarki" Momy ta zaro ido tare saka hannu abaki cikin mamaki, takai Kallanta wajan Nihla taga hankalinta yanakan waya Tace "Alhaji da gaske kake?" "da gaske nake, ga shaida nan kingani, shikkenan Abba sai hankali ya kwanta" Momy tasaki ajiyar zuciya tace "Alhamdulillah... Allah nagode ma, to Alhaji binka zanyi mutafi gida nayi wanka nahuta nima, tunda ga matar sa nan ita saita zauna ta dora daga ina na tsaya" Daddy yayi Murmushi yace "to zo mutafi" Abincin hannunta takai wa Nihla tace "Nihla riqe wannan Abincin, idan Allah yasa yau yafarka shikkenan sai kuci, akwai kayan Tea aciki, idan kuma bai farkaba sai kici, ni natafi gida sai munyi waya" Mamaki yakama Nihla, tace "Momy gida kuma? Ba anan zaki kwana ba?" Momy tace "a a, aina dena wannan zaman Nihla, yanzu kam saike" 🤣 Jikinta yayi wani iri, tayaya Momy zatace tazauna da ya Abba bayan tasan hakan bai kamata ba? Tace "to Momy kuma...." Cikin sauri Momy ta katseta, "Nihla bafa Zan zauna ba, yau kema ki d'ana" Tadubi Daddy tace "Alhaji Muje" Har sun fara tafiya Tajuyo tace "yawwa Nihla Karki Manta likita yace kullum dasafe ana goge masa jikinsa da ruwa Mai Dan dumi, duk abinda kike buqata yana cikin dakin, idan baki ganiba saiki kirani" Nihla ta kalli Momy takasa cewa komai, wai me Momy take nufi ne, ya za'ayi takama taba jikinsa bare har dasu goge jiki? 🤔 Momy kuwa bata jira amsar taba, suka tafi itada Daddy Kuyi hakuri da wannan ba yawa Sharhi please 🙏 Amnah El Yaqoub ✍🏻 [7/14, 2:19 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️ {Romance&Friendship luv} Writing by Amnah El Yaqoub Like my page On facebook 👇 https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 53&54 Jiki a sanyaye tajuya cikin dakin, ahankali ta tura kofar dakin tashiga, idonta yasauka akansa, babu oxygen din ancire masa, amma fuskarsa tayi wani irin fari, Dan qaramin lips dinsa ta kalla duk yafara bushewa, gashin idonsa sun kwanta gwanin sha'awa Kujerar dake gefen kansa tazauna ta ajiye Abincin, sannan tayi shiru tana tunanin irin wannan zaman jinya, ko yaushe zai farka? 🤔 Ya Yusuf ne yafado mata, Allah sarki, tunda sukai maganar rabuwa dashi basu sake waya ba, tana mamakin yanda lokaci daya yace zai sadaukar da soyaiyar ta ga ya Abba, bayan tasan ya Abba da kishi idan shine ba lalle ya'iya hakura da itaba Haka tazauna shiru ita kadai a dakin, lalle idan hakane Momy tayi kokari, amma tarasa Inda Momy tasa gaba, tayaya zasu barta daki daya da ya Abba? Ajiyar zuciya tayi tajuya ta kalleshi, saikuma ta dauke kanta cikin sauri Kamar tana tsoro karya kamata ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Mutanan gida kam, kowa labari ya sameshi, saboda su Alhaji Baqir kowa daya koma gida yafadawa iyalansa, Aslam Kamar yayi me saboda murna, Ilham kuwa bakinta Yaqi rufuwa, haka tadinga d'aga lil Abba sama tanayi masa wasa Yaron kuwa sai dariya yake shima Kamar yasan abinda ake Aslam Yazauna yanemi number Yusuf domin su tattauna kuma yaqara yimasa godia amma kiran duniya ya Yusuf bai dagaba, haka ya hakura, ya shirya da daddare domin suje asbitin shida Ilham, Ilham tazuba musu abinci, sannan tahada wa Nihla wani maganin mata, tatafi mata dashi, cikin ranta tana cewa gara tafara bawa qawar tata Dan abubuwan nan tanasha, tunda auren yazo a qurarran lokaci, kuma tasan halin Nihla yanda batason ya Abba yanzu tsaf zataqi sha, Dan haka gara tana zuwa dashi tana bata tanasha a gabanta Zuwan su asibitin kenan suka kira wayarta tafuto, fuskarta Babu yabo Babu fallasa, ya Aslam sai Fara'ah yake yace "Amarya kinsha qamshi" Nihla bata kawo komai ba, tunda kowa yasan ansa mata rana Dan haka tace "na'am ya Aslam" Yace "yaya marar lafiyar naki kuma" "ya Aslam namu de" Yayi Murmushi yace "A a, mun barmiki, keda dan'uwanki, kinga ai yanzu yazama naki" "duk da haka de ya Aslam, kaima ai dan'uwanka ne" Ilham ce tajata gefe tace "ke rabu dashi, zomu zauna" Tabashi Abincin tace "ga Abincin nasu, ka shiga musu dashi ciki tunda zakaga jikin nasa" Abincin ya karba yawuce cikin dakin Yau Tun safe ransa fari tas, Baqin cikin sa daya yanda Abba yake kwance bai farkaba, yaso ace shine mutum na farko dazai fara bawa Abba labarin aurensa da Nihla , amma yaya zaiyi? Wayarsa yafara dubawa yaga batanan, da alamun agida akabar masa wayoyin, yar drower din gefen gadon yafara dubawa cikin sa'ah yaga biro da wani littafi, cikin sauri yayagi qaramar paper yayi rubutu aciki, sannan ya linke takardar yaqaraso gaban gadon na Abba yana dube duben Inda zai saka takardar ko Allah zaisa Abba yagani batare da Nihla ta lura ba, hannunsa ya kalla, yadaga hannun yasaka masa takardar aqasa hannunsa, yasan ma Nihla zata gani, amma duk da hakade yana fatan karta gani din Awaje kuwa Ilham ta dubi Nihla tace "amarya, amarya, ah ah, kaga amarya kinsha qamshi"🤣 Tsaki taja tace "keni ba wannan ne yake damuna ba, Ilham yanzu Dan Allah tayaya Momy zata tafi gida ta barni tareda ya Abba, bayan tasan surutun wannan family din yanzu sai kiji ankasamu a faranti ana qananun maganganu akan mu" Ilham tace "Babu wani maganar da za'ayi, to waye ma ya'isa yace muku wani abu?" 🤣 "Ilham bazaki ganeba, bafa muharrami na bane sannan wai Momy harda cewa wai...." shiru tayi takasa qarasa wa Ilham tayi Murmushi tace "kinga, ki kwantar da hankalin ki Nihla, babu abinda zai faru, tome zai miki shida bashida lafiya? Kisaki jikinki kiware ki kula da dan'uwanki, karkiji komai tunda su Momy sunsan kina tare dashi, kifa saki jikinki dashi" 🤣 Cikin sanyin jiki tace "to Ilham, amma de.." Ilham tace "kinga, karbi wannan hadin kisha, kinga yanzu bawani zaman gida zakiyi ba bare Momy tadinga baki kina sha, kuma mazan yanzu saida gyara, ke masu gyaran ma yaya aka qare dasu, Dan haka gara kije gidan mijinki tsaf" Babu musu takarba tace "to Ilham nagode" Dariya sai cin Ilham take, Nihla kuwa bata kulaba Fira sukaci gaba dayi har ya Aslam yafuto sannan sukai mata sallama suka tafi, ita kuma tajuya cikin dakin Wajan shadaya na dare likita yazo ya dubashi yace "idan akwai matsala zaki iya kiranmu" Tace "to" Likitan nafita tadauki wayarta tafara kiran ya Yusuf amma baya dauka, Tun tana yin na marmari harta gaji da tadena, sai message ta tura masa Tashi tayi tadauro alwala tazo ta shimfida sallaya tatada sallah, data idarma addu'ah kawai tayi tayi sannan tatashi ta linke sallayar takoma kan kujera tazauna, zuba masa ido tayi, gaskiya ya Abba qarshe ne, yahadu iya haduwa, halin sa ne bai haduba, ajiyar zuciya tasaki ta kalli girarsa datake kama da tata girar, Allah de yabashi lafiya tadena wannan zaman shirun Tun tana kallansa tana tunani harta gaji tadan dora kanta agefen gadon nan take bacci ya kwasheta ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ "Rahma sai murna kike Tun safe" Momy ta kalli Daddy tace "Alhaji ai dole nayi farin ciki, yau Abba na yasamu abinda yakeso, koda na mutu nasan yarana dukansu sun samu mata nagari" Jinjina kansa yayi yace "hakane, Allah yabasu zaman lafiya" "Amin Alhaji, ni dama nasan Dan bakasa baki bane, amma inde an fahimci juna ai komai Mai sauqi ne" "hakane, yabata min raine yaron, haba yaro sai taurin kai" "Hmm Alhaji kenan, kowa yasan de halin Abba gaba daya naka yadauko, kuma kaga laifin yaro?, amma Alhaji yanzu ai sai afara gyara musu gidansu, idan komai ya kammala saisu koma can" Daddy yace "Haba Rahma, korar yaran nawa kuma kike? me zaisa sukoma wani waje Rahma? Da badamu suke zaune ba? Yanzu ma ai sai suyi zaman su" Cikin sauri Momy tace "um um Alhaji, kayi hakuri da wannan maganar, ba zaman gidan kake bane shiyasa, amma nida nake zaune dasu nasan abinda yake faruwa, Abba bashida kunya gara su tafi kawai" Murmushi Daddy yayi yace "to bansan de mekika ganiba, amma tunda kince haka, idan angama gyare gyaren komai saisu koma ai" Tace "yawwa yanzu naji batu" Asuba tagari Daddyn Momy 🙏🏻 ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Karfe hudu da rabi na dare yaji kansa yasara, Ahankali Ahankali yafara bude idonsa Hasken dayagani adakinne yasa yasake runtse idonsa sannan yasake budesu Ahankali, Nihla kuwa bacci yayi bacci kanta yanakan dantsan hannunsa tayi fillo dashi Kallan kansa yayi anan ya tabbatar da asbiti aka kawoshi, ahankali yafara tariyo abinda yafaru dashi harya tuna komai, yana gama tunowa yaji wani irin Baqin ciki aransa ga kansa dayake masa ciwo,qirjinsa nauyi idan yanajan numfashi, jin alamun mutum akan hannunsa dakuma gashinta daya bazu akan hannun nasa shiyasa yakai dubansa ga hannun damansa anan yayi tozali da dogon gashin kanta, babu dankwalin yazame yafadi qasa Gabansa yafadi,meyakawota nan? Ahankali yafara motsawa zai tashi yaji hannunsa na hagu akan takarda, komawa yayi ya kwanta sannan yadauki takardar Ahankali baiyi tunanin komai ba yabude, mamaki ya kamashi, wannan ai rubutun Aslam ne Ahankali yafara karantawa : _Ango mijin amarya, congratulation_ _Abokina, Allah yasa kada wani_ _yarigani sanar dakai cewa_ _Nihla tazama mallakinka_ , _but ka kiyaye batasan komai ba "_ Cikin sauri yatashi zaune Kamar ba marar lafiya ba, sai yaji yana nema yanemi ciwon kan nasa yarasa, ita kuwa Nihla jin kanta ya koma kan katifa yasa ta danyi motsi, sannan tasake gyara kwanciyar ta tajuya taci gaba da bacci Dube dube yafara yana neman wayarsa amma bai gantaba, wasiqar yasake karantawa, ya karanta ta yakai sau biyar Yajuya yasake Kallanta tana bacci hankalinta kwance, Hawaye ne suka zubo masa, yasaka hannunsa duka biyun ya share, sannan yadaga hannunsa sama yana yiwa Allah godia, domin kuwa yasan cewa banda addu'ah Babu abinda zaisa yasamu Nihla cikin sauqi Alerm din wayarta ne yafara qara, Ahankali ya koma ya kwanta Yarufe idonsa Kamar me bacci, nan take masallatai suka dauki kiran sallah Saida Alerm din yaqare yasake bugawa sannan tabude idonta, bacci takeji sosai Kallan kanta tayi Babu dankwali tace "subhanallah," tadauko shi aqasa ta daura dankwalin ta sannan ta kalleshi, tasaka hannu ta gyara masa fillo din da kansa yake kai sannan tashige toilet, yana jin alamun shigar ta toilet yabude idonsa yatashi zaune yana daga hannu yana ta murna 🤣 Haka yaita murna saida yaji zata futo sannan ya koma ya kwanta, harta idar da sallah duk yana jinta, wayarta tafara qara, tadauka yaji tace "Hello Momy" "Nihla kuna lafiya deko?" "lafiya kalau Momy, yanzu na idar da sallah ma" "toya jikin nasa" "gashinan nan de Momy, har yanzu shiru" "to Allah yasawaqe, Karki Manta da goge masa jikinsa de anjima, akwai Ruwan zafi a flask, anjima za'a kawo muku abinci" "to Momy sai anjima" Tayi shiru tana azkar, har gari yafara haske, ganin idonsa biyu kuma ga lokacin sallah yana wucewa shiyasa yafara bude idonsa Ahankali, ya kalleta da gefen ido yaga tayi tagumi tanajan carbi Ahankali yafara cewa "Momy!, Momy!! Momy kaina" Cikin sauri ta zabura tayi kansa "ya Abba! Katashi? Sannu, bari akira Doc." Tajuya tafice daga dakin cikin sauri Wani irin murmushi yasaki, yana jin wani masifar dadi aransa yabi bayanta da kallo, wai yau shine Nihla take nuna masa wannan kulawar, aikuwa in hakane Babu shi Babu warkewa🤣 Tare suka dawo da likitan, ya dubashi, yasake kallansa yace "abin mamaki, ya akai ciwon naka yaragu haka sosai?" Maida kansa yayi majinyacin sosai, ya langabe yace "qirjina yana min ciwo kadan, kuma ko'ina ma ciwo yake min na jikina" Doc. Yayi Murmushi yace "insha Allah Ahankali zaka dena ji" ya kalli Nihla yace "please ki goge masa jikinsa idan zai iya saiyayi sallah ma, idan ma zai iya wanka saiyayi ko zaiji qarfin jikinsa" Jikinta a sanyaye tadaga masa kai, yafice daga dakin yarage saisu biyu Kallansa tayi, cikin sauri takawar da kanta tafara linke sallayar datake kai Shikuwa sai binta yake da wani irin kallon soyaiya , badan kada ya to nawa kansa Asiri ba da Babu abinda zai hana tajita ajikinsa Toilet tashiga tahada masa ruwa, sannan tafuto tazo wajansa tana kallansa qasa qasa tace "Anhada Ruwan wankan ko zaka shiga kayi?" "Ai bazan iyaba, saide nagoge jikina" Cikin sauri tace "to" sannan tahada Ruwan zafin agabansa, tadauko qaramin towel takai masa gabansa ta ajiye tace "gashinan ankawo" Kallanta yayi har yana lumshe idonsa alamun jin jiki yace "bazan... Iyaba fa" Shiru tayi, tarasa meyake mata dadi, shikuma yana Kallanta yanaso yaga yaya zatayi Ajiyar zuciya tasaki ta qarasa wajansa ta matsar da Ruwan gefe, ta kalli rigar jikinsa tace "to dan gyara" Sarai yagane nufin ta sai yace "jikina ne Babu qarfi, bazan iyaba" Wannan karon kam kawarda kanta tayi gefe, itade wannan zama baiyi mata ba kokadan, sai hura hanci take, takasa yin komai 🤣 Kamar wadda aka tsikara Tajuyo takama rigar jikinsa Ahankali tafara yin sama da ita, babu musu yadaga mata hannunsa ta cire masa rigar duka, gabanta yafadi ganin yanda hannunsa yake a murde, ga gashi daya kwanta akan qirjin nasa,lokaci d'aya yacika idonta yayi mata masifar kwarjini, fat... fat... fat... takejin bugun zuciyarta nayi, ta ajiye rigar sannan tadauko towel din dake cikin Ruwan ta matse, tadora shi akan qirjinsa Zirrr yaji wani irin abu acikin jikinsa, cikin sauri ya lumshe idonsa yanajan wani irin numfashi Satar kallansa tayi taga idonsa arufe, dan haka tafara goge masa cikin sauri, shikuma wani irin dadi yakeji Kamar karta daina abinda takeyi, bayaso yadena jin abinda yakeji din Ita kuwa sai kawarda kanta takeyi, har wajan wuyansa saida ta goge masa, sannan ta ajiye tace "nagama" Ahankali yabude idonsa yasauke su akanta, meyasa Nihla ta kasance damuwar sa dakuma maganin damuwar tasa? Meyasa yakejinsa Kamar ba marar lafiya ba? Tabbas dole ne yayi azumi domin nuna godiyar sa ga Allah Gari kam har yayi haske sosai, ahankali yafara kokarin tashi yadubeta tareda miqa mata hannu cikin shagwaba yace "kikamani natashi" Kallansa tayi, tadauke kanta, inaga yamanta itace atare dashi ba Momy ba shiyasa yake mata wannan shagwabar Ahankali ta dora hannunta cikin nasa, yanajin haka yariqe ta sosai, saboda yanda yaji hannun nata da taushi, yatashi tsaye yadora kansa akan kafadarta, yasaka dayan hannun yariqe waist dinta Yanayin yadda ya tura saqon nasa kuwa ya karbu, nan take tayi taga zatayi baya, amma saiya sake riqe waist dinnata sosai, cikin shagwaba yace "Uhm... Uhmm.... Nifa bazan iyayin wankan ba" 😳Zaro idonta tayi, sannan tazare jikinta Ahankali, ta kalleshi tace "tome kake nufi? Ban fahimta ba?" Saura kadan tasaka shi dariya, amma saiyayi Dan murmushi yakawar da fuskar sa, yadafa bangon dakin harya shige cikin toilet din Ahankali Wata irin nannauyar ajiyar zuciya tasauke sannan takoma kan gadon ta zauna tareda dafe kanta🤦🏻‍♀️ Inda yariqe mata dinnan wani iri takeji "Zoki gani" Ta tsinci muryar ya Abba yana kiranta Dak.. Dak.. Gabanta yafara faduwa, Innalillahi.... mekuma zataje tagani? 🤔 Abba dake toilet yaji shiru, yasaki yar qaramar dariya yasake cewa "Kizo kigani" Nihla kuwa mayafin ta tayafa, tana jiran likita yashigo tagudu gida, sarai tana jinsa tayi shiru, da yasan zai iyayin wankan amma shine zaisata wahalar goge jiki Masu cewa naqara yawan typing suma su qara yawan Comments, dama nafada more Comments more typing 👌🏻 Amnah El Yaqoub ✍🏻 [7/15, 12:34 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️ {Romance&Friendship luv} Writing by Amnah El Yaqoub Like my page On facebook 👇 https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 55&56 Jin bata amsa masa ba yasa yayi Murmushi yafara wankan sa, yasan cewa sarai tana jinsa Bai dauki lokaci Mai tsawo ba yafuto, yana sanye da kayan jikinsa, Nihla tana jinsa yafuto amma bata daga kai ta kalleshi ba, idonta aqasa, ya kalleta yayi Murmushi yasaka hannu yadauki sallaya sannan Yazauna abakin gadon yayi qasa da muryar sa Kamar Wanda yake rada yace "please yaushe mukazo asbiti?" Yatsun hannun ta take wasa dasu batare data dago ta kalleshi ba tace "Shekaran jiya" "kwana biyu kenan?" yasake yimata Tambayar Kanta tadaga masa alamun hakane Kansa ya Jinjina alamun gamsuwa sannan yatashi yatada kabbarar sallah Yasha addu'ah sosai acikin sallar tasa, yana qara yiwa Allah godia, bayan ya idar ya ajiye abin sallar sannan yafara kokarin hawa gadon Cikin sauri tatashi takoma kujera tazauna, Sam taqi yarda suhada ido dashi Shikuma kwanciyar ta isheshi, haka Yazauna yasata agaba yana Kallanta, tanaji a jikinta ana Kallanta Dan haka koda wasa taqi yarda suhada ido dashi Wayarta tadauka takira Momy, Momy na dagawa cikin shagwaba tace "Momy yaushe zakizo" Momy tace "Nihla me zaisa nazo asbiti bayan gaki nan? Menene yake faruwa?" "Momy Babu komai" "A a ki sanar Dani idan akwai abinda yake faruwa" "Babu komai Momy, dama ya farka ne" Momy tace "to Alhamdulillah, Allah mungode ma, yana ina Abban?" Satar kallan Abba tayi daya zubawa lips dinta ido yana kallo tace "gashinan" "to bashi wayar" Ahankali ta miqa masa wayar, memakon ya karbi wayar kadai sai da yahada da hannunta yariqe sannan yazare wayar yayi qasa da murya yace "Momy...." "Abba na ashe jiki yayi sauqi, to Alhamdulillah bari mu shirya muzo" "A a Momy, kiyi zaman ki, banajin ciwon sosai, sonake ma yasallame mu" "to shikkenan idan kana buqatar wani abu de karka yi shiru ga Nihla nan" Murmushi yayi yace "to Momy" Wayar ya ajiye gefensa, a lokacin likitan dayake aiki da safe yadawo yadubashi,shima yayi mamakin yanda Abban ya warke Abba yace "Doc. Ai ina ganin ma dazaka temaka daka sallamemu, saboda banajin komai yanzu, inajin karfi ajikina banajin ciwon komai" Likitan yace "ka tabbatar?" "da gaske nake Doc." Yace "to shikkenan, zaku iya hada kayan ku, zanje nadawo yanzu" Yana ganin Fitar likitan ya kalleta yace "madam kira min Abokina mana" Kallansa tayi, taga wayar tana gefensa, tace "gata nan awajan ka" "eh nasani, kinsan wayar yanmata, saisu" Ahankali tamiqo hannunta zata dauki wayar yabi hannunta da kallo gwanin sha'awa dogaye dasu Tadauki wayar tadannawa ya Aslam kira Ringing din farko kuwa yadauka, batayi magana ba tabashi wayar Cikin aji yace "Abokina" Cikin murna Aslam yace "kaga Ango, Ango kasha qamshi, kace kanajin qamshin amaryar taka kamiqe" Murmushi yayi kawai yace "naga saqon ka ai" "Hmm ai addu'ah nayi tayi kada Nihla tagani, amma yanzu de jikin da sauqi ko" "babu komai, na warke" Aslam yasaka dariya yace "toganinan zuwa" Daga nan sukai sallama, doc. Yazo yabasu takardar sallama, sannan Nihla tafara hada musu kayansu, ko minti goma ba'aiba Aslam yazo, suka tafi, sun shiga cikin Mota su agaba ita kadai abaya, wayarta tafara qara, tana dubawa taga baban tane, cikin ladabi tadauka "Baba ina kwana" "lafiya Nihlan Diddi, Yaya su hajiya" "suna nan kalau baba, inasu mamy" "mamy tana nan lafiya, bakya wani abune yanzu ko" "eh baba" Gyaran murya yayi yace "to abinda nakeso dake shine ki saurari abinda Zan fada miki,jiya su Alhaji Abubakar sunzo andaura miki aure da Dansa Abubakar" Gabanta yafadi, cikin sauri tadafa qirjinta tace "Aure kuma baba" Abba da Aslam dake gaban Mota suna jinta, Aslam aransa yace to fada mata ake kenan Abba kuwa shiru yayi yana jinta Daga daya bangaren baba yace "eh aure, Yusuf da kansa shiya fara yiwa mahaifin sa magana akan ya hakura, saide bai yarda ba, saida sukazo jiya muka sake tabbatar wa, ga sadakinki ahannu na dubu dari cif,kiyiwa mijinki biyaiya sannan kiyiwa Yusufa addu'ah Allah yabashi mace tagari, mahaifin sane ya tsaya akai komai aka gama, sannan Alhaji Abubakar yanemi yafiyata da kansa, Dan haka banason wani tone tone, kiyi hakuri Allah yabaku zaman lafiya " Hawaye suka silalo daga idonta, muryarta ta sauya tace" to baba " " yawwa Allah yayi miki albarka " "amin baba" Daga nan sukai sallama, tayi shiru tana goge hawayen idonta, yanzu ashe dama shiyasa Momy ta barta awajan ya Abba, wani hawayen yasake zubo mata, Allah sarki ya Yusuf, haqiqa tayi rashin masoyi, yasha wahala akanta, tasa hannu tashare hawayen Ahankali Abba yadubi Aslam yace "dan tsaya Aslam" Babu musu kuwa ya tsaya, yabude gaban motar yafuto yadawo baya wajan ta Yazauna, Aslam yayi Murmushi yadauke kansa yaci gaba da driving Sake matsawa yayi jikinta, tanajin yanda jikinta yake gogar nasa, yasaka hannunsa ta bayanta ya rungumota jikinsa, batada zabin daya wuce ta dora kanta akan faffadan qirjinsa Bayanta yafara bubbugawa Ahankali, yasunkuyo da kansa dede kunnanta cikin rada yace "kiyi hakuri kidena kuka kinji, kukan ki yana tabamin zuciyata, kiyi shiru, kinji?" Ahankali tadaga masa kanta, wani irin dadi Abba yaji, yanda yaga lokaci daya taji maganarsa Cikin kunnanta yadora bakinsa yace "kin hakura?" Wani irin abu taji yana yawo a jikinta, kode ya Abba ya Manta da ya Aslam ne, ahankali ta janye jikinta daga nasa Shima sai murmushi dayayi, yamatso kusa da Aslam yace "Abokina ina Abba nah" Aslam yayi Murmushin waskewa yace "kaiko, Hmm" Dahaka suka qarasa cikin gida, suna zuwa tabude motar tafuto jikinta asanyaye, tayi part dinsu Momy da Daddy na zaune afalo, Adala tana gefen Momy tanayi mata lissafin abubuwan dazata siyo mata, haka Nihla tazo ta samesu, cikin ladabi ta gaishe su tareda zama aqasa Momy tace "a a, yana ganki yanzu, yanxun nanfa nake cewa Alhaji yatashi mutafi" "Momy ai an sallamemu, yace yawarke" Daddy yayi Murmushi, a lokacin suka shigo falon shida Aslam, suma gaida su sukai suka zauna aqasa Daddy yace "Abba ashe jiki yayi sauqi" Lallausar sumar kansa ya shafa yace "eh Daddy" Yace "to Alhamdulillah, Dafarko de kayiwa Allah godia, sannan ka godewa Aslam,idan da hali ma kayi masa Babbar kyauta 😃sannan kaida Aslam din Idan jikinka yagama warware wa kushirya kuje can Abuja kuyiwa yaron nan Yusuf godia, yayi mutuqar kokari kuma yayi maka halacci, sannan dazu mahaifiyarka tayi waya da Ibrahim ta sanar dasu ka farka, sunce asaka musu lokacin da za'ayi biki yan'uwan mahaifin ta zasuzo daga jigawa ahadu anan, na Abuja ma zasu so gaba dayansu duk ayi komai anan, nikuma nafada musu nasaka sati daya, saboda haka sai kayi kokari zuwa next week din kagama shirya komai, saiku tare a gidanku " Cikin farin-ciki yadan sosai qeyarsa yace" to Daddy insha Allah" Sannan yakalli Nihla yace "kinji abinda yafaru ko?" Tace "naji Daddy" "to kiyi hakuri, ki qara akan Wanda kikai abaya, Allah yabaku zaman lafiya" Tace "amin

Chapter 20 of 24