tafuto daga dakinta tana saka wayarta acikin jaka, sanye take da riga da wando na kayan bautar qasa, kayan anyi masa shape sosai, wandon nan tacika abinta Dam, rigar ma tabi jikinta, sai jacket din kayan data dora asama, tasaka Dan qaramin hijabi daya tsaya mata iya qirji, idonta sanye da glass
Qamshin turaren dasukaji ya bigesu ne yasa dukansu suka daga kansu suka kalleta
Itama kallansu tayi tace "ya Aslam ina kwana"
Murmushi yayi yace "lafiya Nihla, ya service"
Tace "Alhamdulillah" sannan takama hanya zata fice
"ke koma kicire wannan kayan"
Ta tsinci muryar Abba yana mata magana
Cak ta tsaya awajan, Sanna Tajuyo ta kalleshi fuskarta Babu yabo Babu fallasa "makaranta fa zanje, kuma kowa da uniform dinsa yake zuwa"
"nace kikoma kicire wannan kayan bazaki fita dasu ki janyo mana magana ba"
Aslam daya ga za'ayi drama agabansa saiyayi gyaran murya yace "haba Abba"
Sannan yadubi Nihla yace "Nihla jeki"
Babu musu kuwa tajuya tafice daga falon
Aslam ya kalleshi yaga fuskar nan ahade tace "meyasa zakayi mata magana Abba? Bayan kasan waje dayawa doka ne coppers suje batare da uniform ba"
"kalli shigar ta mana Aslam, tayaya yarinya 'yar musulmai zata fita da wannan kayan ana ganin komai nata"
Murmushi Aslam yayi yadubi abokin nasa "Abba kana kishin Nihla, kode sonta kakeyi ne?"
Cikin sauri yace "Babu wani so"
Aslam yace "Abba banason rainin wayo, baka sonta tayaya zaka dinga wannan masifar akan zata fita da wannan kayan? Ni nayi mata magana ne? Malam ko kanaso ko bakaso, ina tabbatar ma kakamu dason Nihla"
Hannunsa yadaga masa "dakata Aslam, Dan Allah kadena min wannan maganar, meyasa bazaka fahimce niba ne?"
Haushi yakama Aslam yace "Ok fahimta ko? Nafahimceka"
Daga nan ya tattara takardun gabansa yafice daga part din, aikin da ba'a qarasaba kenan 🤣
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Cikin farin-ciki ya kalleta, yana goge jikinsa da dan qaramin towel, "Baby Dida Tun dazu kike wannan kukan, bayan kuma kece kikace nayi, cemin kikai kinajin dadi nayi"
Hawayen idonta ta goge tace "to aiba wannan nace kayi ba, kuma saida nacema kabari amma tsabar mugun ta ka qyaleni"
Murmushi yayi, yau Babu Wanda yakai shi murna ya angonce, gaskiya masu aure sunji dadinsu, yasan hakane ai da tuni an wuce wajan yace "toki hakuri, ai daga yau nadena, wajan yadena ciwo?"
Jan zuciya tayi tace "akwai zafi sosai, rad'ad'i nakeji sosai, kuma zazzabi ma nakeji"
Yace "subhanallah, bari nagani"
Batayi masa musu ba, haka tabarshi yabude kafarta yaga wajan, yasa bakinsa yahura mata iska kadan aciki, jiyayi Kamar ya qara, amma dole hakura zaiyi Tun kafin ya ballowa kansa ruwa, tasa shi agaba tana kuka
Rufewa yayi yace "shikkenan to kiyi hakuri, zai daina insha Allah"
Ahankali ta daga masa kanta, yasaka hannu yana shafa kanta
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Washe gari da yamma yana kwance a dakinsa, tunanin maganar Aslam yakeyi, yanzu idan maganar Aslam ta tabbata gaskiya yaya zaiyi? Gabansa yafara faduwa, idan hakane kuwa ai yashiga ukunsa, tayaya zai iya fuskantar yarinyar dayace bayaso cikin bainar jama'ah yace yana sonta yanzu? Anya kuwa su Momy zasu bashi goyon baya akan hakan? Innalillah...
Sumar kansa ya hargitsa, yana tuno lokacin da Momy take ce masa tana gujemasa ranar dazaiyi DANA SANI (my first novel)
Kai, bazai iyu bama, tayaya zai fara son Nihla? To amma meyasa yakejin kishinta aransa? Meyasa ranar sunan takwaransa yakasa kwantar da hankalin sa akan dadewa datayi bata dawo gida ba? Meyasa yakejin haushi idon yaga tana wa yan'uwansa Fara'ah bashi ba? Meyasa? Meyasa duk yakejin hakan?
Wannan alamomin duk sun nuna cewa tabbas yanason Nihla, Innalillahi wa inna ilaihir raju'un..., Idanunsa ne suka cika da qwallah, yasan cewa Babu me fuskantarsa
To amma yasan Nihla, yasan cewa Nihla tana sonsa, yasan cewa koda kowa zai juya masa baya banda ita, amma yanda yake ganin tsanarsa a'idonta yasan cewa abinda wahala, amma tayaya zai gane cewa tana sonsa? Ta wacce hanya?
Wata dabara ce tafado masa, lokaci daya yadanji sanyi aransa, haka yatashi yashiga toilet yayi wanka, wata shadda yadauko yasaka Mai launin Ash, yasaka hula tareda Agogon sa qirar gucci, yayi masifar yin kyau, idan ka kalleshi Babu qarya saiya birgeka
Falon yafuto yanata zuba qamshi, Nihla tana kwance da waya a hannunta tana chatting, Momy tana zaune agefe, gaba dayansu kallansa sukayi, yayi mutuqar kyau Kamar bashi ba
Momy takasa yin shiru tace "Masha Allah, Abba wannan wankan sai ina?"
Murmushi yayi Wanda yaqara wa fuskarsa kyau, yasaci kallan Nihla, Sanna yace "Momy zanje wajan zance"
Momy tayi dariya tace "Alhamdulillah, gara da kayiwa kanka fada ai"
Haushi yakama Nihla, tayi shiru batace komai ba, Abba kuwa ya juya zai fita daga falon
yaje dede kofar falon ya tsinci maganarta tace "ya Abba"
Cak yaja ya tsaya awajan, shi yasan cewa Nihla tana sonsa, wani farin-ciki ya kamashi, finally yau de takira sunansa, cikin murmushin da yaqara masa kyau ya juya yana Kallanta yace "na'am"
Budar bakinta saitace "idan kaje ka gaishe ta" 🤣
Be'iya cemata komai ba saide Jinjina kansa dayayi kawai tareda ficewa daga falon
Yana fita itama tatashi tashige cikin dakinta, Momy tabita da kallo amma bataga komai akan fuskarta ba
Tana zuwa dakin tafada kan gadon ta tasaki wani irin kuka Mai cin rai, ita kanta tarasa dalilin yin kukan, haushin ta daya, yanda tadage ta gyara kanta, take Jan ajinta, duk Dan yaso ta tayi amfani da wannan damar wajan nuna masa kuskuren daya aikata abaya, yanzu komai yatashi abanza kenan, ashe duk wannan dauke kan datake abanza, ashe hankalinsa yanacan kan wata daban, Wato harda yimata Fara'ah yana amsawa Dan zaije wajan wata, to tunda hankalinsa yana kan wata, tayaya zata iya rama abinda yamata?
Haka tasha kukanta sannan tashige toilet ta wanke fuskarta tadawo falon tazauna
Yana futowa daga falon nasu yake ganin duhu-duhu a'idonsa, duk hasken dayake wajan Abba baya gani, duhu kawai yake gani, baisan Inda yake saka qafarsa ba,lokaci daya Idanunsa Yarufe ruf yadena ganin komai sai jinsa yayi yafada jikin mutum Wanda baisan ko waye ba
Daqyar Aslam da Allah yakawo shi gidan yanzu, yakawo Abba cikin falon
Momy da Nihla cikin tashin hankali sukai kansu, Momy tana cewa "subhanallah, Aslam lafiya? Menene ya sameshi? Yanzu yanzu fa yafita"
"Momy wallahi shigowa ta kenan nima naci karo dashi"
Momy ta kamashi suka qarasa cikin dakin Abban, akan gado suka kwantar dashi, Nihla tabude fridge din dakin tabawa Momy ruwa tace "Momy ga ruwa" jikinta sai rawa yake
Momy ta kalleta taga yanda duk ta rude, ta karbi Ruwan aka shafa masa a fuska, Allah ya temakesu yafarka, yana bude idonsa yasauke su akanta, kallo daya tayi masa tace "Sannu"
Yadaga mata kai, daga nan tafice daga dakin
Momy tace "meyake damun kane Abba na, naga lafiya kafita"
Ahankali yace "Momy kaina ke ciwo"
Tace "to Allah yasawaqe, bari ajima idan bakaji sauqi ba sai akira Doc"
Bece da ita komai, domin kuwa abinda yakeji yafi ciwon kan yawa, Inda ace ciwon kai ne Toda sauqi 🤣
Momy na fita Aslam yace "Abokina meyake faruwa ne? Meke damunka?"
Cikin damuwa yace "Aslam kayi Gaskiya, kafini gaskiya Aslam, ina sonta, Nikaina yanzu na tabbatar ina sonta" ya qarasa maganar tareda fashewa da kuka
Gaban Aslam yafadi, bade maganar datake ransa hakace take shirin kasancewa ba, kallan Abba yayi yace "Wacece?"
Kai tsaye yace "Nihla"
Aslam yayi shiru Tsawon second talatin,zaka dade kafin kaga Abba yana kuka Kamar haka, yasan cewa tabbas tunda haka ta faru toba qaramin so yakewa yarinyar ba, haka yasa hannu yayi tagumi hannu bibbiyu,
gaskiya Abba yadauko musu Babban aiki, kallansa yayi yace
"Gaskiya Abba akwai damuwa,ka janyo mana Babban aiki a gabanmu, maganar gaskiya itace kana ruwa tsundum kusada kada"
Cikin masifa Kamar bame kukaba yace "Dan Allah Aslam idan bazaka bani goyon bayaba to kamin shiru kawai, meyasa bazaka fahimci abinda nakeji bane?"
Cikin damuwa shima Aslam din yace "Abba aini nafi kowa fahimtar ka" 🤣
"dan Allah Aslam tashi kafita kabarni da abinda nakeji" yasa hannu ya goge hawayen idonsa
Sharhi please
Amnah El Yaqoub ✍️
[7/5, 10:18 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Like my page On facebook 👇
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
39&40
Aslam yatashi yafuto daga dakin jikinsa a sanyaye, domin kuwa yasan abokin nasa yana cikin damuwa yanzu, maganar aikin data kawoshi ma baiyi ba.
Fitar Aslam keda wuya Abba ya danna kansa cikin fillo yana hawaye, to Aslam ma dayake makusancin abokinsa yakasa fahimtarsa inaga sauran jama'ar gida? 🤔
Har dare yayi sosai Abba bai sake futowa daga dakinsa ba, saide Momy tana zuwa tana dubashi akai akai
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Karfe goma na safe ma agida tayi mata, babu part din da batajeba cikin family house din nasu, tana zuwa part dinsu Nihla taji shiru Kamar Babu kowa, kai tsaye dakin Nihla tashiga taganta kwance tana bacci fillo rungume a qirjinta
Batare data tasheta ba, ta'ajiye mata lil Abba agefenta, yaron kuwa idonsa akan fan din dakin dake juyawa Ahankali
Fita tayi daga dakin tashiga kitchen din tanaso ta hadawa kanta Tea Dan taga Momy da Nihla harkar gayu suke ji ita kuwa tana goyon yaro bazata iya wannan zaman ba
Cikin baccinta taji yaron yana wasa, bude idonta tayi ta kalleshi, shi kadai, sai tsotsar hannu yake, murmushi tayi tatashi zaune tareda daukar sa tace "Wato mamanka tazo shine ta ajiye min kai tagudu danka tashen a bacci"
Kissing dinsa tayi, suka futo falo, anan taga taga Ilham zaune tana shan Tea da uban Bread a gabanta, Momy tana zaune da alama itama yanzu tatashi
Qarasowa tayi ta ajiye yaron tace "ashe kinzo, yau kece agida kenan"
Kafin Ilham tace wani abu momy tace "nima yanzu na futo naganta"
Ilham tace "Momy Tun dazu ya Aslam ya kawomu yawuce wajan aiki, ina zuwa wajan umma nace ko Abincin ta ba zanci ba wajan Nihla Zan tafi, shine na tarar da ita tana bacci, nabar mata Yayanta a dakin na futo"
Momy tace "Ah kin kyauta wallahi, gashinan ya warware,"
Daukansa Momy tayi tace "Abba nah, mekakeci ne?"
Daga nan tayi cikin dakinta dashi tabarsu anan suna fira
Har yamma Ilham tana wajan Nihla suna ta firarsu, yaron ta kuwa yana hannun Momy saide idan yayi kuka takawo mata shi, yanzu ma nono tagama bashi Nihla ta karbe shi tana masa wasa, sai dariya yake
Tace "Ilham wannan yaron Kamar ku sai sake futowa yake"
Miqewa tsaye tayi tadauki towel dinsa ta goyashi taci gaba da magana "gashi sai dariya yake gwanin sha'awa wallahi ba Kamar me sunansa ba, kullum fuska adaure ko murmushi Babu" 🤣
Karaf maganar ta sauka a Kunnan Abba daya shigo cikin falon yanzu, Tun safe yaje company sai yanzu yadawo, Wato shine kullum fuska adaure, Ilham de taga shigowarsa, danhaka sai tayi shiru 🤣
Ita kuwa Nihla data bawa kofa baya ko'ajikinta, taga de Ilham din tayi mata shiru kawai kuma sai qifta mata ido take 😃, amma bata gane komai ba, yaron taci gaba da jijjigawa a bayanta ko zaiyi bacci, amma memakon bacci ma saiya fara kuka
Ahankali ya qaraso cikin falon, cikin ladabi Ilham tace "ya Abba sannu da zuwa"
Saida yadan saki fuskarsa sannan yace "yawwa, ya Baby"
Tace "gashinan Alhamdulillah"
Shiru Nihla tayi, kode yaji maganar data fada ne, shiyasa Ilham take qifta mata idanu? 🤔
Abba kuwa bai sake cewa komai ba yanufi Nihla fuskarsa adaure ko alamun wasa Babu, muryar sa yarage cikin fada yace "bani yaron nan, saboda rashin hankali kina goyo"
Mamaki yakama Nihla, menene abin rashin hankali a goyo? Batare data ce masa komai ba tafara kokarin kunce yaron, saura kadan yaron ya qwace daga hannunta garin sauko dashi, aikuwa yakama gaban rigarta ya riqe, karon farko da kunya takama Nihla ganin ga ya Abba a tsaye, Sannan wannan yaro yakama riga yariqe har hakan yasa ana hango albarkatun qirjinta
Batayi auneba taji ya Abba yasaka hannunsa awajan ya cire hannun yaron, sannan ya juya zai tafi dashi
Ilham tana zaune tazama yar kallo, duk abinda ake akan idonta, saide bataji abinda ya Abba ya cewa Nihla ba, tayi Murmushi tace "lalle Nihla kin iya goyo, kema da yanzu danaki Babyn"
Abba yana kokarin shiga dakinsa yaji wannan maganar ta Ilham, Wato da ace anyi musu aure a wancan lokacin da yanzu itama da nata yaron, ko juyowa beyiba yashige cikin dakinsa
Nihla kuwa tana qame a tsaye, Ilham tace "kitaho ki zauna mana, kin daskare a tsaye, shiyasa nake ta qyafta miki ido, amma inaaaa gulma ta rufe miki ido bakisan yashigo ba sai zuba kike" 🤣
Nihla ta kalleta "niba wannan ne yasa na tsaya ba, bakiga abinda d'anki yamin bane?" tayi qwafa tadawo tazauna akujerar tana kumburi
Ilham tayi dariya tace "nagani mana, jiyake rigar mamansa yariqe, besan takwaransa ya budewa abubuwa yana ganiba" 🤣
"kuma basai ya tsaya nacire yaron nabashi ba, amma haka kawai saiya wani sakamin hannu a qirji"
Dariya Ilham tayi "kiyi hakuri, ganide ba tabawa bane, kuma gani yayi zaki yarda takwaransa, shiyasa yakawo muku temakon gaggawa" 🤣
Nihla tayi shiru batace komai ba, al'amarin Abba kullum qara tsamari yake, da yana zama agefenta yanzu kuma yafara kawo mata hannu, nan gaba kuma ai batasan mezai faruba
Ilham tace "wai Dan Allah meyake cemiki ne naji yayi qasa da murya yana magana"
"cemin yayi nabashi yaron, saboda rashin hankali ina goyo, menene abin rashin hankali agoyo"
Ilham tace "eto da gaskiyarsa, may be bayaso abubuwan sa suzube ne"
"mekike nufi Ilham?"
"Nihla kinsan goyo yanasa nonon wasu matan yazube, inaga shiyasa, inba hakaba ai bazai ce kina goyo ba"
Nihla tadafe kanta 🤦♀️ tace "Innalillahi.... Wallahi gayen nan yagama dani gaba daya"
Ilham tace "kema ai kinga ma dashi, Dan wallahi nide abinda na fahimta ko, ya Abba sonki yake, kigafa yanda yawani matsa gab dake Kamar zaisaku ajikinsa keda Babyn kawai saboda zai karbe shi, Nihla kiyi tunani mana"
"Ilham kenan, babu wata soyaiya, rannan ma sallama ya mana nida Momy yace yatafi zance"
Ilham tace "to nide abinda idona yagani aishi Zan fada"
Haka sukaci gaba da firarsu har hudu da rabi tayi, hajiya Na'ila takira wayar Ilham din tace tazo kafin tatafi gida, tashi tayi tafara shirya wa, Momy takawo mata wani turaren wuta Dan Sudan Mai qamshi, ta karba tana godia
Momy ta kalleta tace "Nihla karbo mata yaronta awajan Abba, zasu tafi"
Tashi tayi ta nufi dakin nasa, Ilham tanayi mata dariya qasa-qasa, ahankali ta tura dakin tashiga, taganshi yana kwance yadora yaron akansa yana masa wasa
Cikin ranta tace ashe yana yiwa yara wasa, sallama tayi ta qaraso, tunda tashigo idonsa akanta Ahankali shima ya amsa sallamar tata
Gabansa ta qarasa, ganinsa dagashi sai ita yasa taji duk yayi mata kwarjini, tana jan yatsun hannunta tace "Momy tace akawo shi zasu tafi"
Da idonsa ya nuna mata yaron yace "gashi nan daukeshi mana"
Wai yaro akan qirjinsa bazai bata shiba saide tasa hannu tadauka, zuciyarta daya kuwa tasaka hannu tadauki yaron
Jin hannunta yadan taba Kirjinsa hakan yasa ya lumshe idonsa, gaskiya yanzu kam yaqara tabbatar wa kansa cewa soyaiyar yarinyar tayi masa mugun kamu
Nihla bata lura da yanayin sa ba tafuto daga dakin, bayansu yabi da kallo itada Babyn, sai yaji dama basu tafiba, dama tazauna yasaka su agaba yana kallansu itada babyn
Bayan sun futo daga part din Momy Nihla tawuce part din umman Ilham itada Yaron, ita kuma Ilham tawuce part din hajiya Na'ila
Ta dade a part din hajiya Na'ila kome take bata oho 🤔 sannan tataho part din ummanta wajan Nihla, takira ya Aslam yazo yadauketa suka tafi, Nihla taji dadin ziyarar da Ilham takawo musu, Ilham tana sonta sosai, tazo gida amma bata wuni awajan sirikarta da ummanta ba, sai awajanta tawuni
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Wanka yashiga ita kuma tana gyara masa dakin nasa, wayarsa ce tafara qara, tanufi wayar taduba taga number ce take kira
Zuciyarta daya tadaga wayar, sai taji muryar mace tace "Malam Adam yau zaka shigo makaranta kuwa?"
Gaban Diyana yafadi, cikin masifa tace "Wacece ke? Menene hadin ki da mijina?"
Alokacin yafuto daga wanka yayi gaban mirrow zai shirya, yana ganin wayarsa ahannun Diyana sai masifa take amma ko Kallanta beyiba, shide yasan yanada gaskiya, kuma Babu wata mace daza dauke hankalinsa daga kan Diyana a yanzu,yanda yakeji da amarcin nan ai Babu me rabashi da maryam
Diyana kuwa sai masifa take, amma wadda takira wayar bata qara cewa komai ba Tun maganar ta ta farko, daga qarshe ma saita yanke wayar
Diyana Tajuyo ta kalleshi tace "ashe yanmatan university har kiranka suke kuna waya bansani ba"
Kayansa yake sakawa cikin sauri saboda yayi latti dayawa, yace "to menene abin damuwa maryam, tunda kece Mai ni"
"wata yar'iska takira ka awaya da wannan safiyar kacemin menene abin damuwa? Amma yanzu idan nice wani yakirani da yanzu kafara fada ko"
Hularsa yasaka yajuyo yana Kallanta, kishi qarara yagani akan fuskarta, Bece da ita komai ba yadauki key din motarsa yana kokarin fita
Itama cikin haushi tafice daga dakin, da wayar tasa a hannunta
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Wayar Dida ce a hannunsa yana sending pictures dinta zuwa tashi wayar, gyaran falo take, yana ganinta tagama ta goge sauran kayan kallo, sai aikin take da jikinta Kamar batasan ciwon jikinta ba
Kitchen ta wuce yatashi yabi bayanta, yana mata wani irin mayen kallo, "wai har yanzu aikin bai qare bane?"
Kallansa tayi "bai qareba, abinci ma zanyi mana"
"kibar Abincin nan Dan Allah, basai naje nasiyo mana ba, ke kullum bakya hutawa"
Wani irin kallan soyaiya tayi masa "menene abin gajiya acikin girkin mutum biyu"
Ajiyar zuciya yayi yatako yazo bayanta ya rungumeta, yayi qasa da muryar sa yace "please kibarshi"
"ya Fawaz Dan Allah kabarni nayi aikina, sokake kahanani kai kuma ka bata kudin ka, menene amfani na da zakaje siyo mana abinci"
Kissing din wuyanta yayi, yasake qasa da muryar sa yace "wai wajan nan har yanzu bai warke bane?"
Zaro ido tayi, takwace jikinta Dasauri "wallahi be warke ba, bari naje daki akwai abinda zanyi" cikin sauri tafice daga kitchen din tabarshi anan
Murmushi yayi ya shafa kansa sannan yadawo falo Yazauna, yana ganinta takoma kitchen din tana aikinta, harta gama tazo tazuba musu cikin flet daya, cikin nutsuwa suka gama cin Abincin, sannan ta maida komai kitchen, kafin tafuto daga kitchen ya kwanta atsakiyar kafet din falon yafara murqususun qarya Kamar gaske, Dasauri Dida ta qaraso wajansa "ya Fawaz menene? Lafiya kake kuwa?"
Idanunsa a runtse yace "Dida cikina ciwo yake min, bayan kinsan meyake damuna, kuma gashi kince wajan bai warke ba"
Gabanta yafadi, cikin in-ina tace "emana, be warke bafa da gaske dane, sannu insha Allah zai daina"
Yace "shikkenan Babu komai idan na mutu ma shikkenan"
Dasauri tace "mutuwa! A a ba yanzu ba insha Allah,"
Yace "yanda nakeji Kamar mutuwa zanyi Dida"
Cikin shagwaba tace "to shikkenan kazo kayi amma Dan kadan gaskiya, kuma idan nace ya'isa to katsaya ahaka"
Dadi yakama Fawaz, sai yau yaqara tabbatar wa Dida yarinya ce, yace "eh nayarda"
Lokaci daya yatashi ya janyo ta jikinsa, dayake yarinya ce kwata kwata bata ganoshi ba, yanda yamiqe lokaci daya Babu wani alamar ciwo, anan falo yafara nuna mata yanda yayi missing dinta, daga baya sukai ciki
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Zaune take akan kujera har yanzu dube dube take cikin wayar tasa, amma bataci karo da number mace ko dayaba, koda yake tayaya zaiyi saving numbers din yanmatansa a wayarsa, haka nan ranta yake mata zafi Tun safe
Shigowa yayi da sallama ta amsa masa batare data kalleshi ba, yayi Murmushi yana zama agefenta, yace "wash Allah, nagaji wallahi"
Tanaci tayi banza dashi
Hannu yamiqa mata yace "bani wayata, dazu na Manta ban dauka ba"
Asheqe tamiqo masa wayar, ya karba yace "Maryam ina abinci"
"Dining"
Abida tace masa kenan, yatashi tsaye yace "wai saboda wata takira wayata shine kike wannan fishin? Ni nayi tunanin ma kin huce, ai shikkenan, yau bazan samu damar da za'a kaini inci Abincin bama, to zanje na Auro wadda takirani awayar, saitazo tadinga bani, tunda naga alama nema kike ki rainani"
Nanma banza tayi dashi, shima yaje yaci Abincin sa hankali kwance, yana gamawa yakara wayarsa akunne Kamar yayi kira yafara cewa "hello hajiya ta, kiyi hakuri dazun wata qanwata ce tadauki wayar wallahi, kinaji na.. Kinsan me za'ayi yanzu....?
Diyana bataji qarshan wayar ba saboda shigewa dakinsa dayayi yarufo kofa, Baqin ciki yakamata, dama ai tasan matar cushe bata daraja, wani kukane yazomata Mai cin rai, tatashi cikin kuka ta nufi dakinsa, duk kayan ta dasuke dakin tafara hadawa tana hawaye
Dariya takama Adam, yayi fuska, sannan yatashi yazo bayanta ya tsaya yace "mekike shirin yi haka maryam? Ina zakije kike daukan kaya haka"
"gidanmu Zan tafi, bazan zauna bakin cikin wata yadameni ba"
"saboda nace Zan qara aure kike kuka? To aikuwa ki shirya, Dan uku suna nan zuwa, Allah yabani damar dazan ajiye mata har hudu acikin gidannan, kuma ni banyi miki alqawarin cewa Zan zauna dake kekadai ba, garama kisa aranki kishiya tana nan zuwa"
Hannunta ta dora akanta tafashe da kuka, ta tsugunna awajan tana kuka bilhaqqi
Adam baisan lokacin da dariya ta kwace masaba, Yazauna agefen gadon yanata dariya yace "maryam, yanzu saboda kishiya kike wannnna kukan?ashe kina sona haka? To kinga ni wasa nake miki"
Kallansa tayi cikin harara, tatashi zata fice daga dakin
Cikin sauri yatashi yariqota, tafara fizge-fizge "nika cikani natafi gidanmu tunda dama baka kaunar ganina"
Yace "maryam nifa wasa nake miki"
"Babu wani wasa, bayan gashinan kashigo daki kana waya da'ita, kacika...... Bata qarasa maganar tataba yahade bakinsu waje daya, diff kakeji Diyana tayi shiru
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Itada Momy ne a kitchen sunata aiki kayaiyakin yin kek ne agabansu Nihla tana hadawa
Adede lokacin yafuto daga dakinsa yana daura agogo a hannunsa, yana sanye cikin suit,sunyi mutuqar yimasa kyau, amma baisaka jacket dinba, a hannunsa ya riqeta, ko wajan Momy bai nufa ba yafita Dasauri, zai qarasa campany wajan Aslam
A kitchen din kuwa Momy ta kalleta "Nihla idan kinsan bazaki iya yin kek dinnan ba Tun wuri nasa ayi muku oder"
Murmushi tayi "Momy kenan, kede zuba ido kisha kallo, da kaina zanyi kek din"
Momy tace "shikam Abba da alama ma ya Manta cewa yau yake birthday, ke kuwa gashi baki Manta nakiba Tun safe kin hana kanki sukuni, nima kin hanani zama saboda wannan bikin birthday ganaki Gana Abba"
Murmushi tayi tace "Momy ai abune na rana daya, idan tawuce shikken"
"hakane, to Allah yabada sa'ah, guda daya zakiyi muku ne ke dashi kokuma daban daban zakiyi?"
Kai tsaye tace "Momy da nawa Zan farayi, idan yanaso shima sai ayi masa"
"wacce irin magana ce wannan Nihla? Nafada miki Abba ya Manta yau yake birthday, ya za'ai kuna gida daya keda yayanki kuma ranar birthday dinku daya aje ana rabe raben wani kek, kiyi muku babba guda daya keda shi, sannan idan masu kayan Decoration din sun kawo kishirya muku komai tare "
Jikinta ne yayi sanyi tace" to Momy "
Momy tafita daga kitchen din, ita kuma tayi shiru tana tunani, Allah yasa ta dinga control din kanta agaban Momy karta ga tana tsanar danta qiri-qiri
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Cikin motarsa qirar Rang rover yafuto daga gidan, adede lokacin wani matashi yafaka motarsa, yafuto hannunsa dauke da Wata leda anyi rapping dinta, cikin sauri ya Dakatar dashi yace "yallabai Dan Allah nanne family house na Mazawaje ko?"
Yace "lafiya?"
Matashin saurayin yace "a a babu komai dama maigida nane ya aikoni daga Abuja wajan hajiya Nihla, gift din birthday dinta ne yace ayyuka sunyi masa yawa bazai samu damar zuwaba, amma very soon yana hanya"
Cikin mamaki yafara magana aransa Birthday? dama yau take yin birthday?to ai shima yaune nasa, Waye wannan daya aiko mata da gift daga Abuja? Haushi ne ya kamashi, yaji wani irin kishi aransa
Kallan matashin yayi yace "i don't no, ka tambayi wasu"
Daga nan yaja motarsa yayi gaba, matashin yayi sa qare yana kallan motar Abba, ikon Allah, shikuma wannan daga tambaya? 🤣
Cikin gidan yanufa yaga maigadi anan yafara tambayarsa
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
"kaga Abba idan muka saka hannun jarinmu Awannan campany zamu samu riba sosai, saboda shima Babban campany ne ansan shi sosai"
Yana jiran yaji Abba yabashi amsa sai yaji shiru, cikin mamaki ya kalleshi "Abokina mekake tunani ne?"
Nanma yaji shiru, ta'bashi yayi yace "Abba!!"
Cikin sauri yadawo daga duniyar tunanin daya lula, ya kalleshi "Aslam ya akayi?"
Dan qaramin murmushi Aslam yayi "kana nufin kacemin duk wannan maganganun danayi baka jina?"
Kallansa yayi yadaga masa kai alamar hakane
Wani murmushin Aslam yasake yi "meyake damunka haka Abba? Tunanin me kake? Yanzu fadamin menene matsalar?"
Ajiyar zuciya yayi "yanzu Aslam misali idan mace tana Birthday me kake ganin za'a bata amatsayin gift?"
Aslam yayi Murmushi, sai yanzu yagano Inda tunanin Abba yadosa
Yakalleshi yace "um nide aganina za'a iya bata kyautar sarqa idan ranar birthday din tazo saika saka mata, kokuma zobe kakama hannunta kasaka mata, kokuma ka tambayeta abinda
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 24