Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta, wayarta tadauko zata kira Momy, kawai saita fasa, gara tayi mata surprice kawai Ko awa daya basuyi ba, jirginsu yayi landing, tana futowa daga Airport din mutane suke ta Kallanta, daga ita sai yar qaramar truly dinta tanaja, tayi mutuqar birge kowa, Mai taxi ta tare tashiga tafada masa Inda zai kaita, acikin motar ma kafa daya ta dora kan daya, tana daddana waya, har sukazo bakin get din family house din Mazawaje Sallamarsa tayi, ta tsaya ta qarewa Babban get din gidan kallo, duk an sassauya abubuwa dayawa, yau gata a Mazawaje family akaro na biyu Tura get din tayi tashiga, iliya Maigadi yana zaune yanajin radio, taga ya kalleta yayi shiru Kamar besanta ba, cikin mamaki tace "iliya d'anmai qarfi baka ganeni bane?" Kallanta yasake yi, yaji sunansa radau abakinta yace "Wacece? Bangane kiba wallahi, baquwa mukayi ne?" Murmushi tayi ta cire glass din idonta tace "iliya nice Nihla fa" Cikin sauri yatashi tsaye yace "kai kai kai, wai Nihla kece? Aini jinake wata balarabiyar ce wallahi, a a a a, masha Allah, sannu da zuwa, sannu sannu, kice yau munada manyan baqi agidan namu, kawo jakar taki, kawo, kawo" Nihla tayi Murmushi tace "iliya kenan," Sannan tabashi jakar, suka nufi part din Momy, saida yakai mata jakar har cikin falo sannan yajuyo yana qara yimata sannu da zuwa, Nihla ta zube akan sabun kujerun falon da aka sake tace "wash Allah nah, gajiya" Sannan tadaga murya tace "Momy!!! To futo 'yarki tazo"🤣 Kamar almara Momy Tajuyo Kamar muryar Nihla, amma sai taqi gaskatawa, mezai kawo Nihla kano yanzu? Kawai de kunnanta ne Nihla tasake cewa "Momy!, koba kowane agidan?" Dasauri Momy tafuto falon, taga Nihla kwance akan kujera ga jakar tanan agefe, qaraso wa tayi cikeda tsananin mamaki, Nihla na ganinta tatashi ta gudu taje ta rungumeta cikeda murna Momy tadagota daga jikinta tana Kallanta tace " Nihla 'yata, yanzu Allah kece kika qara girma haka? Gaba daya kin sauya kamar ba Nihla ta tadaba" Dariya tayi tace "Momy nice mana, wai meyasa kowa yake cewa na sauya ne? Momy girma naqara ne?" "girman ma Nihla, kin qara kyau, Kamar balarabiya, mezakici adafa miki yanzu?" Saida tayi farrrr da idonta sannan tace "Momy yanzu banajin yunwa, saide da daddare, but idan akwai cornflakes zansha kadan" Momy ta lakace mata hanci, tace "Wato bakyason cin abinci Kamar da ko? Ni narasa ya'akayi ma kikai bul-bul dake masha Allah Babu wata rama Kamar da" Dariya tayi, cikin ranta tace Anty Nadiya ce sirrin, afili kuwa sai tace "Momy bari nakai kayana daki" Momy tace "a a Barshi, Adala zatazo takai miki, tashi Muje ki gaisa da sauran yan gidan" Hannunta Nihla ta riqe Kamar wasu qawaye suka futo, kowanne part saida sukaje ta gaida kowa, kuma kowa sai nan-nan yake da'ita, kowa yayi murna da dawowar Nihla, saita zama wata abar sha'awa kowa Kallanta yake yanda ta sauya,Hajiya Farida maman su Diyana kuwa tana ganin Nihla taji tausayin Abba ya kamata 😢 🤣 Haka suka dawo part din Momy, Nihla ta dora kanta akan cinyar Momy tana bata labarin makaranta dakuma service din da aka turota Suna wannan firar har la'asar tayi, Tatashi taje tayi wanka, tasaka riga da wando na jesy, (kayan ball) na mata, amma nata dogon wando ne Mai launin dark blue, Momy ce da kanta tahado mata cornflakes din, tace "to yata taso kisha, yauda kaina Zan baki" Murmushi tayi tatashi, suka zauna a kafet din, Momy tafara bata, ita kuwa sai surutu take mata, Momy cikin ranta sai mamakin yanda Nihla ta sauya takeyi, kanta Babu dankwali hakan yasa dogon gashinta dayasha gyara kwanciya a bayanta Adede lokacin yaturo falon nasu yashigo, yau kwanansa takwas baya qasar ma baki daya, saukarsa kenan da dogon gashinta yafara tozali, kasancewar tabashi baya baiga fuskar ko Wacece ba, mamakin hakan yasa yaqame a tsaye abakin kofa, Wacece wannan Kamar ba 'yar hausawa ba kuma Momy tana feeding dinta? Momy ce ta lura dashi takalleshi cikin murmushi tace "a a Abba, shigo mana" Jin an ambaci sunansa yasa bugun zuciyarta ya sauya, ahankali tajuya ta kalli bakin kofar itama, lokaci d'aya Idanunsu yahade dana juna, cikin abinda baifi second ashirin ba tagama qare masa kallo, yau ne karon farko daga taba ganinsa azahiri sanye cikin kakinsu na Pilot Mai launin fari da baqi banda pic dinsa data gani awayar Anty Nadiya sanye da kayan , sosai kayan sukayi bala'in karbar jikinsa, yaqara girma, yaqara yin kyau Kamar ba shiba yasake zama babba tamkar wani cikakken magidanci, kawarda idonta tayi,ta karbi spoon din hannun Momy ta cigaba dashan cornflakes din ta, shikuwa kasa dauke idonsa yayi akanta, shin anya kuwa ita dince de agabansa? Inda ace baiyi mata kyakykyawan saniba Babu abinda zai hana yakasa ganeta, but ya'akai takoma haka? Dogon gashinta yasake kalla Kamar ba gashin bahaushiya ba, ahankali yaqaraso cikin falon cikin takun izza Momy tace "Nihla ga yayanki yashigo fa, shima baya qasar yanzu yanzu yadawo, yaude ina cikin farin-ciki yarana duk sun dawo gabana" Hankalin Nihla yana kan cup din gabanta, ko dago kanta batayi ba, bare yasaka ran zata kalleshi, kanta aqasa Kamar anyi mata dole tace "ina yini" Ataqaice yace "lafiya" Sannan yayi gaba, yajuyo yasake kallanta waiko zaiga ta kalleshi amma yaga gaba daya hankalinta ma baya kansa, shi wannan yarinyar zata gaisar asheqe Kamar ta samu sa'anta? Momy kuwa tayi mamaki guda daya, mamakin daya kamata shine yanda Nihla taqi ambatar ko sunan Abba, da tasaba tanaji yarinyar tana ya Abba kaza, ya Abba kaza, duk da yana shareta bata fasa fadar sunansa ba, Kamar a bakinta aka rada mata sunan ya Abba, amma yau taga gaisuwar ma daqyar tayi 🤔 Dakinsa yashige yafada kan gado yana tunani, inaaa! Bazai iyuba, Sam bayason raini, Dan haka bazai dauki wannan ba, lumshe Idanunsa yayi, meyasa yake jin farin-ciki ne awani bangare na zuciyarsa? (ko a film fad'an boss shine qarshe 🤪dafatan za'a min Comments 🙏🏻) Amnah El Yaqoub ✍️ [7/3, 12:43 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI DAYA❣️ {Romance&Friendship luv} Writing by Amnah El Yaqoub Like my page On facebook 👇 https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 33&34 Nihla ta kalli Momy "Momy kibani wayarki nakira su Ilham, banda number kowa acikinsu" Momy tace "wayarki tada tana nan a dakin naki, ki kunna saiki dauka, ai Babu wadda ta sauya number acikinsu, nima Bari nakira Daddynku dasu Usman nafada musu zuwanki" Tace "to Momy" sannan tashige dakinta Da daddare kuwa su ya Usman sukazo dukansu, dama Momy tasa Adala ta shirya musu abinci Mai kyau Alokacin Nihla tasake wanka tasaka riga da siket na atamfa Mai launin Jan duhu, dinkin yayi mutuqar yimata kyau, siket din kuwa hips dinta yacikashi dam, daurin dankwali nede tayishi simple amma gashinta awaje yake daga baya Babu Wanda bai rude ba, lokacin dasuka ganta, gaba dayansu suna zaune acikin qayatattun kujerun dakin, Adala kuma tana dauko abinci daga kitchen zuwa kan dining, firarsu suke cikeda farin-ciki but Abba kam baya saka musu baki, baya cewa um bare um um, asali ma waya ce ahannun sa yana danne-danne, yayinda yadora kafa daya kan daya Farouq yace "Momy, yarki fa tagama rikicewa, gaba daya ta sauya kamar ba ita ba, ni sai yanzu nema nakejin naqara matowa, inba itaba sai rijiya" 🤪 Ahankali yadago kansa ya kalli farouq, amma Bece masa komai ba Murmushi Nihla tayi, har dimple dinta yana lotsawa, tace "ya farouq bakada dama, aina fadama dakai za'ayi, tunda kaji sharadin" Wannan karon ma tana fara magana Abba yadauke idonsa daga kan farouq yadawo dashi kanta, har yanzu de wannan dimple din nata yana nan, yayi tunanin zata kalleshi amma kwata kwata saiyaga ko kujerar dayake kai bata kalla ba Aliyu yace "ai farouq, bazan baka qanwata ba, mijinda Nihla zata aura ai sai Wanda duniya tasan dashi" Usman yace "Kamar ni kenan" 🤣 Gaba dayansu sukasa daria, Momy tace "Dinner is ready kutashi Muje kowa yaci abinci" Usman da farouq da Aliyu gaba dayansu ajere suka zauna, Momy ma tazauna akusa da Usman, kujeru biyun dasukai saura kuwa na Abba ne da Nihla, hankalin ta kwance taja kujerar tazauna sannan tafara cin Abincin ta, shima Abba daya qaraso wajan yaga saura kujera daya ta kusa da Nihla, haka yaja Yazauna, idonsa akan wayarta data ajiye a gabanta, yana zama wani irin sihirtaccen qamshi yabugeshi, baisan lokacin daya lumshe idonsa ba yabude, kowa shiru yayi yana cin abinci, wayar Nihla tafara qara, kowa yazuba mata ido yana Kallanta, Abba yakai dubansa kan screen din wayar yaga ansa ❤my Yusif❤ harda alamar hert ajikin sunan, Nihla tasa hannu tasaka wayar a silent, idonsa ne yasauka akan kyawawan yatsun hannunta, dogaye gwanin sha'awa, janye idonsa yayi, Nihla kuwa ko a jikinta taci gaba dacin Abincin ta, ana jimawa ya Yusif yasake kira, tasake sakata a silent, akaro na uku ma yasake kira, ahankali ta miqe tsaye tace "Excuse me, zan amsa waya" Tana fadar haka ta nufi hanyar dakinta, Hips dinta Abba yabi da kallo, anya kuwa yarinyar nan itace bawani abu take sakawa a jikinta ba? gashi sai yawo take tana fitarda gashinta waje kowa yana kallo, amma Momy tana gani ko magana bata taba yiba Har suka gama cin Abincin Nihla tanacan tana waya, da dade tana shan wayarta dashi sannan tafuto sukai sallama dasu ya Aliyu ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ "ku shikkenan idan akace anyi muku aure, ankai muku amarya daki saiku rasa control dinku gaba daya, tayaya za'ayi daren farko kace zaka shigi mace gaba daya, shiyasa mutanan da sukafi mazan yanzu iya zama da mata, da kanku kukesa matanku suna tsoron ku, yanzu saboda Allah wannan dame yayi kama? Kaja anyiwa yarinya dinki, tayaya kake tunanin zata sake yarda dakai akaro na biyu? " Adam yayi shiru kansa aqasa, ko yayiwa doctor bayani bazata ganeba, gara yayi shiru tagama fadanta kawai, ahankali yadago kansa ya kalleta, matar kam babba ce zata iya haifansa, shiyasa Babu kunya baro baro take masa fada, yace" insha Allah Zan kiyaye gaba likita " Fuska a cukune tace" to dade yafi muku, narubuta muku magunguna kasata agaba tadinga sha, sannan karka sake zuwa wajanta sai nanda yan kwanaki " Kansa aqasa yace" to insha Allah " Daga nan yafuto daga office din nata yaje wajan Diyana daya tarar tana bacci, baiyi kokarin tashinta ba, yabarta tagama baccinta sannan tatashi Dan kanta, yakamo hannunta da kafadarta suka futo daga asbitin, saida yasai magungunan da aka rubuta musu sannan suka wuce gida Dakinta tashige ta kwanta tana tunani, dama haka daren farko yake? Ahakan wasu suke cewa sunason daren farko? Wannan aiba abin dadi bane abin wahala ne kawai, har akan wannan abun wasu matan suke fada? Har wasu sukai kansu ga aikata zina, tabdi, ita kam, itada ya Adam danba qara Dakin yaturo yashigo yakalli fuskarta tayi fayau, zama yayi agefenta yace "maryam kiyi hakuri, insha Allah hakan bazata sake faruwa ba" Shiru tayi masa batare datayi magana ba, ahankali ya miqe yafara cire kayan jikinsa, gaban Diyana yafadi, me kuma zai sake yi? 😳 Tsaf ya cire komai dagashi da boxer yahau kan gadon, cikin faduwa gaba tace "dan Allah kayi hakuri ya Adam,"hawaye ya silalo daga idonta " ohhh Diyana, niba wani abu Zan miki ba, kawai inaso najiki ajikina ne " Yana fadar haka yasa hannu yadaga mata hannayenta ya cire rigar jikinta, daga ita sai breziya ya janyo ta jikinsa ya rungumeta tsam, sannan cikin rarrashi yace "muyi bacci ko?" ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Tunda suka dawo normal shida ita yakasa yimata komai, yasan cewa Dida mace ce Mai matuqar kunya bazata taba kawo kanta gareshi ba, to shi kuma kunya yakeji da girman sa yaje gun yarinyar mutane da sunan neman haqqin sa, amma azahiri yana matuqar buqatar matar sa, saide zaici gaba da haquri kawai har Allah ya yaye masa abinda yakeji, saboda yakusa sati kullum da ciwon mara yake kwana, amma be nuna mata cewa yanayi bama bare ta daga hankalinta Magun gunansa suna hannunta, kullum itace take bashi saboda tana tsoro karta je Yaqi sha, idan lokacin shan maganin yayi saiyaje tabashi yasha Yauma da azahar yashigo gidan, kai tsaye dakinta yashiga, a lokacin tafuto daga wanka tana zaune gaban mirrow tana kwalliya daga ita sai Dan qaramin towel Gabanta yaje ya tsaya yana Kallanta, duk kuma saita rikice tarasa mezataci gaba dayi, ta kalleshi tace "Sannu da zuwa ya Fawaz" "yawwa sannu da kwalliya Baby Dida " Murmushi tayi, ahankali tafara kokarin tashi zata nufi wajan kayan ta, Miqewar da zatayi towel din ya kunce yayi qasa 🙆🏻‍♀️ Ganinta haka Babu komai yasa cikin sauri Fawaz ya runtse idonsa, bugun zuciyarsa yafara sauyawa, ita kuwa Dida tsugunna wa tayi ta rarumi towel dinta ta daura 🤣 Tayi tunanin zata riskeshi yana kare mata kallo amma abun mamaki tana kallansa taga idonsa a runtse, mamaki ya kamata, to kode ya Fawaz baida lafiya ne? Miqewa tayi tsaye tace "ya Fawaz Zan shirya, kaje Zan futo ma da maganin" Babu musu yace "to" sannan yafuto, Dida tabishi da kallan mamaki, mum tace mata masu shaye-shaye basa kula mata, to amma ita ai matar sa ce, menene zaisa ya runtse idonsa Kamar yaga abinda ba halal din saba? Haka ta shirya tafuto falon tabashi maganin yasha, anan falon suka zauna suna kallo, amma Babu fira, maganar sai de kadan kadan 🤣, ita Dida tana tunanin hali irinna Fawaz, shikuma idan ya kalleta saiya tuna dazu da towel yafadi, dama haka wannan abin na qirjinsu yake? Dama bata tsugunna ba, meyasa ma ya runtse idonsa ne? Ahankali yatashi ya kalleta yace "zanje daki nadan huta, anjima Zan futo" Cikin ladabi tace masa "to" Dakinsa yashige yafada kan gado, ya janyo fillo ya rungume yana tunanin Dida, gara yazo daki ya kwanta yanda zaifi jin dadin tunanin nata, ahankali yaji yanayin sa yana sauyawa, Tun yana jin dadin tunanin harya dawo yana jin mararsa tana masa ciwo kadan kadan, sai qara matse fillo yake a qirjinsa Shiru shiru har bayan sallar ishsha'i Dida bataga Fawaz yafuto ba,dakinsa tabishi anan taganshi akan gado yahada uban gumi, yatakure kansa waje daya, Dasauri ta qarasa wajansa "Innalillahi, ya Fawaz, menene yake damunka? Meyasa baka kirani ba?" Kasa magana yayi, sai runtse idonsa yake, Dida tasa hannu ajikinsa tana jijjigashi, "ya Fawaz, kafadamin meyake damunka? Zaka iya tashi Muje asbiti?" Girgiza mata kai yayi, ahankali yakamo hannunta yajashi jikinsa, batayi aune ba taji yadora hannunta akan mararsa, gabanta yafadi, Dasauri tafara kokarin dauke hannunta, amma Fawaz yariqe hannun yana qara tura matashi can qasan mararsa, cikin sauri ta fizge hannunta tana fadin "nashiga uku na, tsaya ya Fawaz ina zuwa"🤣 Falo tafuto takira wayar likitan daya dora Fawaz din akan magani, cikin tashin hankali tace "doctor, ya Fawaz baida lafiya, cikin sa yana ciwo, kuma bazai iya tashi mutaho hospital ba, Dan Allah ko zaka temaka kazo ka dubashi?" Doctor yayi jimmm, yasan de ciwon cikin namiji baya wuce qarfin sha'awa ne kawai, Fawaz Yana buqatar matar sa ne, ajiyar zuciya yayi yace" keba matar sa bace? Kibashi haqqin sa" "doctor kamarya? Mekake nufi?" "ina nufin mijinki Fawaz Yana buqatar mace atare dashi, Inda baida aure sainazo na kawo masa maganin dazaisha, amma yanada iyali, menene amfanin ki? Kibashi haqqin sa kawai Tun kafin mijinki yaje yakai kansa wajan wata, Allah yakiyaye hakan" Gaban Dida sai faduwa yake, kai tsaye tace "gaskiya Doc bazan iyaba" Yace "to shikkenan, ai zaki iya biyawa mijinki buqata ta wata hanyar, amma de Karki Barshi haka,ke mace ce, kinsan hanyar dazakibi kisamawa mijinki nutsuwa basai nafada miki ba, sai anjima" Doc. Ya kashe wayarsa yabar Dida da waya akunne, tunani takeyi tayaya zata iya cire kunya tayiwa yaya Fawaz wani abu? To amma kuma Doc yace zai iya kai kansa wajan wasu matan, yanzu yaya zatayi? Diyana ce tafado mata, Dan haka ta dannawa 'yar'uwar tata kira, a lokacin suna can suna bacci, Adam ya qwaqumeta ajikinsa, sama sama taji wayarta tana ringing, tameqa hannu ta dauka taga Dida ce me kiran, cikin sanyin murya tace "Dida ya' akayi? "Diyana kinga ya Fawaz ne baida lafiya, cikin shi yana masa ciwo sosai, bakiga yanda yake hada gumi ba, tona kira Doc. Sai yacemin wai matar sa yake buqata, kokuma wai namasa wata dabarar, narasa ya zanmasa Diyana, Kibashi shawara Dan Allah ya zanyi? Abinda nauyi Diyana " Diyana tayi shiru tana tuno irin azabar da tasha ahannun Adam, tace " karkiyi masa komai kirabu dashi yamutu "😳🙆🏻‍♀️ Cikin sauri Dida tace" narabu dashi yamutu fa kikace Diyana, haqqin sa yana kaina ya za'ayi nabarshi ya mutu? " Diyana tace" to Dida Karki bari yamutu, ke saiki tsaya ya kasheki ai " Qit takashe wayarta tana masifa, yarinya ana nuna miki annabi kina runtse ido, nace kirabu dashi zaki fara min wa'azi wani haqqi haqqi ai sai kije, lokacin dazakiban labari Babu wani haqqi dazaki tuna Adam kuwa yana jinta yayi shiru Kamar bacci yake, sai dariya yake qasa-qasa 🤣 Haka Dida takoma cikin dakin nasa tazauna agefen gadon tayi tagumi, tarasa shawarar wazata dauka, Doc. Kokuma abokiyar shawararta Diyana, tajuya ta kalli Fawaz taga gaba daya ya rikice mata ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Tunda tadawo daga camp taci gaba da harkar gabanta agidan, kuma har zuwa wannan lokacin magana bata qara Hadata Da Abba ba, idan taganshi afalo ma bata futowa, idan tafuto kuwa ko gaida shi batayi take harkar gabanta, abin yana masa mugun ciwo, yarasa yaushe yarinyar nan takoyi rashin kunya Yauda yamma taci kwalliya cikin riga irin readmade dinnan, Mai launin green, rigar tayi mata mugun kyau, kuma tayi daidai da jikinta shape din cikinta daya kwanta yafuto sosai, hakan yasa qirjinta Dagowa, daga qasan rigar kuma abaje take, sai farin mayafi data nad'a akanta, tafitar da gashinta waje Falo tafuto hankalinta yana ka waya tana daddannawa,a lokacin Abba yana zaune da system agabansa yana serch wasu abubuwa, wando ne ajikinsa three quater, sai riga irin body hock dinnan, takama jikinsa rigar, hakan yasa muscle dinsa 💪🏻bayyana, sarai taganshi azaune amma ta dauke kanta, tazo tawuce ta gabansa ta zauna awata kujera ta gefensa, harda dora kafa daya kan daya, tadauki remote tana sauya tasha, wayarta ce tayi qara ta duba taga Ilham ce, cikin murmushi tadauka "meciki" Ilham tace "mekikeci nabaka na zuba, abinda bai zoba bai wuce ba" Wani irin dariya tayi me daukan hankali tace "um um aide baizo dinba, ke kuwa yazo, yakike yagida" "lafiya Nihla, kinqi kizo, kewai karkizo ki takura mana kuma wallahi Babu wata takura, ya Aslam dinma baicika zama ba wallahi" "kwantar da hankalinki insha Allah zansa rana dukanku nazo muku" Ilham tace "to shikkenan, bari naje Zan aiki direba kasuwa, wani sabon direba ya Aslam yakawomin waiko Zan buqaci wani abu, wallahi yacika shirme dayawa" Murmushi Nihla tayi tace "Toda ke waye yafada miki direbobi basuda shirme? Ai kowanne irin direba dakike gani duk haka suke" 🙆🏻‍♀️😳 System din gabansa ya janye yajuyo yana Kallanta, me yarinyar nan take nufi? Bade shi take fadawa magana ba, Wato kowanne direba mashirmaci ne, to Allah yasa tace harda Direban jirgi, wallahi dasai taga qarshen rashin kunya yau🤣 Momy ce tashigo falon, tayi Murmushi tayi matuqar jin dadin ganinsu atare , tayi tunanin masu zaman falon zaman arziqi suke, tace "a a, ashe duk kuna nan kuna kallo" Abba Bece da ita komaiba yadauki computer dinsa da wayoyi yanaso yatashi daga wajan, Nihla ta kalli wani mujalla agefenta tabude taga pictures din kayan daki dasu kujeru masu mugun kyau, haka take bude shafi shafi tana gani, gaskiya kayan sunyi kyau sosai, sun birgeta, bangon farko takoma tagani, anan taga amsa A&A FURNITURES Ta kalli Momy tace "Momy wannan kayan sunyi kyau sosai gaskiya, inane wannan A&A din?" Momy tace "laaa campany yayunki nefa, Abba da Aslam ne suka bude, nayi tunanin ma kinsani ai" Girgiza kanta tayi, tace "bansani ba" Cikin ransa yace yawwa tunda batamin magana yanzu ai dole tatayani murnar bude campany... Kafin ma yagama tunanin sa yaji tace "idan nasamu lokaci zanje nayiwa ya Aslam din murna" 🤣 Cikin ransa yace Aslam... It means banda Abba, cikin bacin rai yatashi fuuuuu yashige cikin dakinsa Babu Wanda yalura da yanayin sa, saboda shi dama koda yaushe fuskarsa adaure take Yana zuwa yafada kan gadon yana tunani cikin damuwa, tunda yarinyar nan tazo gidannan baitaba ji takira sunansa ko sau dayaba,yalura kallan arziki ma baya samu awajanta, to meyasa hakan? Meyasa? Nan take ya tsinci kansa cikin damuwa a dalilin hakan More Comments more typing, idan akai Comments dayawa nima inyi typing dayawa, idan akai Comments kadan nima inyi typing kadan, babu zafi 👌🏻 Amnah El Yaqoub ✍️ [7/4, 12:34 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI DAYA❣️ {Romance&Friendship luv} Writing by Amnah El Yaqoub Like my page On facebook 👇 https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 Masu buqatar sa daga farko sunemi wannan number 09039066577, kokuma kai tsaye suje page dina suyi like saisu karanta 35&36 Furzar da iska yayi daga bakinsa tareda yin ajiyar zuciya, toshi menene ma zai dame shi?wata zuciyar tace saboda yar'uwar ka ce, sannan kaida ita DANGI DAYA ne, ba haka take wa su ya Usman, meyasa shi take rabuwa dashi? Koda yake, yasan ba komai ne yake damunta ba sai yarinta 🤣 Wataran idan tayi hankali zata dena, danhaka shi zai dinga yimata magana kawai Washe gari dasafe yana kwance akan doguwar kujera wayarsa na hannunsa yana danne-danne, Momy kuwa tana gefe tana waya da Daddy dayayi tafiya, Nihla ce tafuto daga dakinta kai tsaye wajan Momy tanufa ta dora kanta akan cinyar Momy, binta yayi da kallo, lokaci yayifa dazai fara yiwa yarinyar nan magana, to amma ta wacce hanya? Shi dama can bawata magana sukeba, mezece mata yanzun? Hakanan ya tsinci kansa cikin faduwar gaba, tome hakan yake nufi? Tsoron ta yakeji kokuma kwarjini take masa? 🤔 Daqyar yayi gyaran murya yadaga kansa yana Kallan gashinta dako dankwali Babu yace " Am Zan samu coffee?" Sarai tajishi amma saita shareshi, idan bazai kira sunanta ba yabari, babu wani coffee dazata hada Momy ta kalleshi taga idonsa akan Nihla yake, da alamun da'ita yake kenan, kuma taga alama itama Nihlan taji tayi masa banza, kai wannan yara tarasa ya zatayi dasu, ta lura kowa jinkansa yake, yanzu shi bazai bude baki yace Nihla tashi kihadamin coffee ba, saide ya yi mata magana Kamar yana magana da wata daban ba qanwarsa ba Ajiyar zuciya tayi tace "Nihla yayanki yana magana" Cikin shagwaba tace "Momy Allah nina gaji" Momy ta shafa gashin kanta tace "Nihla banason qiwa, maza tashi kije ki hada masa" Daqyar tatashi tana bubbuga qafa tayi hanyar kitchen din tana gunguni "Allah ni nagaji..." Yaja daga kwancen yagama qare mata kallo, ba qaramin birgeshi tayiba yanda take wannan shagwabar, shiyasa yace yarinta ce take damun yarinyar, kallan Momy yayi yace "Momy yanzu haka zakibar yarinyar nan tadinga yawo kanta Babu dankwali" Momy tace "Abba kaima fa qanwar ka ce, kanada iko akanta, kayi mata magana mana" Shiru yayi, besake magana ba, daga yin qorafi kuma sai ace shi yayi mata magana? Nihla kuwa da niyya taqi futowa daga kitchen din dawuri, saida tagama Jan ajinta sannan tafuto da iya cup daya jal a hannunta, ko akan tire bata dora ba, takawo gabansa ta direshi batare datace komai ba, sannan takoma wajan Momy, Kallanta yayi yanda ta ajiye masa coffee din Babu ladabi aciki, aikuwa karaf idonsu yahadu dana juna, fuskar nan tasa ahade, lokaci daya kowa yadauke idonsa cikeda basarwa ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Yau juma'ah, su ya Usman sun saba ko wacce juma'ah da an'idar da sallah gidan suke zuwa susha firarsu da yamma can saisu tafi Yauma zaune suke afalo suna kallo amma hankalinsu baya kan kallon ma, kawai firar duniya sukeyi, koda yaushe Momy ta kallesu wani irin dadi takeji yanda Allah ya hade mata kan yaranta waje daya. Bakinsa dauke da sallama yashigo falon, yau manyan kaya yasaka harda Babbar riga, kayan sunyi masa kyau sosai Kamar bashiba, kallo daya Nihla tayi masa ta dauke kanta, bata taba ganinsa cikin manyan kayan dasuka karbi jikinsa Kamar yau ba, koda yaushe saide qananun kaya, farouq ya kalleshi yace "saurayi mijin yanmata, baka gankaba Kamar sabon Ango" Murmushi yayi, Wanda ya qarawa fuskarsa kyau sosai, qaraso wa cikin falon yayi, duk kujerun dake falon bai zauna akowacce ba, sai wadda Nihla take zaune dayake a 2seater take zaune Yanda ya zauna akujerar dab da ita saika dauka matar sa ce, gabanta ne yafara luguden faduwa amma sai tayi fuska ta basar Kamar yanda yayi Aliyu yace "farouq bakada damuwa, shiyasa ko d'an yayan ne da qanne suke fadawa yayunsu Abba baya fada ma, kacika tsokana wallahi" Usman yadauki wayarsa Kamar yana dannawa amma saiya shige cikin camera ya cire flash din camerar yadauke su photo batareda kowa ya lura ba, pic din ya kalla sosai anan yaga tsantsar dacewar dasukayi, murmushi yayi yasaka wayarsa cikin aljihu yace "gaskiya farouq yafada, munada manya manyan biki a gabanmu nan gaba, Gana

Chapter 13 of 24