Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tasan cewa Momy ce, saboda ita kadai Nihla take cewa Anty Ta daga wayar tace "Momy Nihla tafita bakin get, wai babanta yazo" Kashe wayar Momy tayi tace "Innalillah... Yanzu Alhaji shikkenan Nihla tatafi? Inaji ina gani anrabani da 'yata..." Sai kuka Su farouq suka dawo gefenta suna bata hakuri, takalli Abba tace "duk abinda yafaru, laifin ka ne, Inda ace baka nunawa yarsa qiyayya ba, babu abinda zaisa Ibrahim yazo yatafi da ita, idan ma akan antaho da ita batare da sanin sabane to danaka laifin, na tabbatar labari yaj...j...ji" numfashi tane yafara sama Anan maganar ta tsaya, numfashinta yana qara yin sama, cikin tashin hankali Abba yataso yacire Babbar rigar jikinsa yayi wulli da ita 🤣 Ya cacimeta yana kiran "Momy! Momy!!," Amma inaaaa, numfashinta ne kawai yake sama, qirjinta sai Dagowa yake, lokaci daya kuma, jikinta yasaki Cak Abba yadauketa yadawo da ita kan gadon Daddy, farouq yadauko ruwa a fridge ya shafa mata, Usman kuma yafara kiran number family doctor nasu yace gashinan zuwa Saida tadauki lokaci kafin ta farfado, tana bude idonta tafara kuka, Daddy yanaga yashiga tashin hankali ashe duk abinda yakeji Rahma tafi shi 🤣 Mamaki yagama kashe Abba, yanzu duk saboda Nihla suke wannan abun? Lalle ba qaramin so suke mataba ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Sai yamma liss suka sauka, saboda Alhaji Isma'iel bayasan gudu, futowa sukai daga ciki motar, Yusif yasaki miqa yana fadin "wash Allah" idonsa akan Nihla Mami tace "Yusif banasan wannan san jikin fa, to yanmata de basason rago, oya bude boot ka dauki kaya mushiga" Yace "yanzu ni dinne rago?" Murmushi tayi, ta kalli Nihla data shagala wajan kallan hadadden gidan, yanzu itace zatayi rayuwa acikin wannan gidan? Duniya kenan Mami tace "Muje ciki Nihla" Fuskarta Babu yabo ba fallasa tace "bari nadauki wata jakar mami" Kusadashi taje ta tsaya, shi beyi mata magana ba itama haka, haushi yaqara kama Yusif, duk murnar dayake zaizo yaganta yaga yanda takoma amma shine tashareshi, 🤣 Cikin fishi yadauki jaka guda daya yamiqe zaiyi ciki Dasauri ta tareshi tareda miqa hannu zata karbi jakar tace masa "kawo jakar" Lokaci daya hannunsu yahadu dana juna, kallan hannunta yayi zanen qunshin da akayi mata yayi kyau sosai, Dasauri ya fizge jakar yace "no Barshi kawai" Daga haka yayi ciki, sai wata tadauka acikin boot din tabiyosu ciki Dakinda zata zauna mami ta nuna mata, sannan tashige ciki, anan taga babanta yana ciki, yana futo mata da kayaiyakinta na sakawa daga cikin jakarsa, cikin ranta tace dama de baba yagama shirya komai Jakar yadauka yatafi Inda akayi masa masauqi daga can baya Yana fita taga wayarsa ya mantata, Dasauri tadauka tasaka number Momy tafara kira Acan kano kuwa gida duk ya hargitse yanmata duk sun shiga damuwa saboda labarin tafiyar Nihla, Ilham tafi kowa Baqin ciki saboda Babu abokiyar shawara antafi, Dan dole ake saka su abu su yi, yanzu ma wanka akasa ko wacce tayi domin anjima kadan za'akai kowa dakin mijinta Apart din Momy kuwa kowa sai neman ta yake yarasa, tunda tashiga dakin Daddy bayan doctor yazo yagama dubata bata sake futowa ba, wayartace data Nihla a gefenta, adede lokacin wayarta tafara qara, Dasauri ta dauka tace "Ibrahim Dan Allah kayi hakuri, munsan munyi maka laifi amma kayi hakuri kadawo min da yarinyar nan" hawaye yazubo mata tasa hannu tashare Kuka Nihla tafara tace "Anty kidena kuka nice" Dasauri tace "Nihla kece? Kina ina, gida kuka koma?" "Anty gida baba yadawo Dani, amma yanzu muna Abuja, mun tafi Abuja gaba daya da zama Anty" Momy tace "Innalillah...Nihla banji dadi ba, banji dadin tafiyarki ba yata, kiyafemana kinji?" Tace "Anty kidena neman yafiyata ba kiyimin komaiba, kedin Kamar mahaifiyata ce" Momy tace "to ai kinji Nihla, kema kikace kama, ba kama nakeso nayi da mahaifiyar ki ba Nihla, sonake ki daukeni amatsayin mahaifiyar ki, ki kirani da Momy Kamar yanda 'ya'yan cikina suke fadamin, ke dasu bakuda banbanci a wajena" Jikin Nihla yayi sanyi sosai, bata taba sanin cewa Momy batasan Antyn datake fada mataba sai yau, ashe haka Momy take kaunarta? Wannan wacce irin soyaiya ce? Kasa magana tayi sai kuka datake sosai abaiyane Alokacin baba yashigo yadawo daga masallaci kenan, tana ganinsa takwashe wayar, idonta jajir, tana share hawaye Zama yayi agefenta ransa abace yafara magana "ke saboda rashin hankali, da hauka dayake damunki zaki zauna kinawa mutumin dabai damu dake ba kuka,? idan akayi muku auren waye zai wahala bayan ke? Anayi wa mace auren dole kuma tayi hakuri tazauna din, amma namiji karkiyi tunanin lokaci daya zai hakura Yazauna dake amatsayin matar sa, yaron yafuto yace bayasonki to kema ki cireshi aranki, sannan daga yau ko awaya ne ban yarda ki nemesuba, " Yana fadin haka yafice yabar mata dakin Innalillahi... Baba bai taba fishi irin wannan ba, dama ance ka kiyayi fishin mutum Mai hakuri Wai ita ta d'orawa kanta soyaiyar yaya Abba ne? Yaya zatayi da Rayuwar ta? Yanzu yaya Yusif yadawo amma ta gagara yimasa magana, ba kuma komai ne yasa hakanba sai tunanin datayi akan Abba, yadawo daga wata qasa tabi ta shishshige masa, daga qarshe ya Wulaqantata, tana tsoron shima tayi masa magana daga qarshe yayi mata Wulaqanci, itada shigewa maza har abada, ya Abba ya koya mata Hankali 🤣 ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Shadaya da rabi kowa ya watse daga gidan amare anbarsu su kadai, mayafin da'aka lullube mata kai dashi ta cire tayi wulli dashi tafara fada "ina dalili Zan takura kaina akan wannan malamin, kun wani rufeni da mayafi ai zafi sai yamin illa" 🤣 Saukowa tayi daga gadon, tafara cire kayan ta, daga ita sai under wear a jikinta, tadauki towel tashige wanka, da ruwa Mai Dan dumi tayi wankan saboda gajiyar biki Tana futowa daga wanka tadawo gaban mirrow tafara shafe jikinta da turare, ko kayan bacci bata nemaba ta kashe wutar dakin ta kwanta bacci 🤣 Shikuwa Ango Adam sai wajan sha biyu yashigo gidan, hakanan gabansa yake faduwa saboda baisan mezai tarar ba Falon yashigo da sallama, yaga Babu kowa, wucewa yayi zai shige dakinsa amma wata zuciyar tace yakamata kaje kaduba yarinyar nan, haqqinta yana kanka Dan qaramin tsaki yaja Kamar anyi masa dole, yakoma baya sannan yabude dakin nata yaga duhu, zuciyarsa daya yakunna wutar dakin, lokaci daya yayi arba da santala santalan cinyoyinta, baccinta take hankali kwance, magana yafara cikin ransa, to yanzu wannan tayaya zakai tunanin yimata maganar sallar da akeyi raka'a biyu ga sababbin aure? 🤔 Kallanta yasakeyi sosai, Diyana tanada komai da d'anamiji yakeso awajan mace but ba yarinyar kirki bace, kuma may be hakanne yasa take tallar jikinta awajan sauran maza Bata son haske inde tana bacci, ko yaya taga haske tofa zata farka, yanzu ma cikin magagin bacci tabude idonta taganshi a tsaye yana qare mata kallo 🙈 Cikin ranta tace jikinnan dai haka za'a ganshi abarmin kayana Tashi tayi zaune, har towel din yana kwance wa kana iya hango nashanunta takalleshi tace "Yawwa nace ba, idan kagama kallon ka kashe min wutar dakin please, banasan haske idan ina bacci" 🤣 Tana fadar haka tayi juyi ta rufe idonta, Adam kuwa kunya ce ta kamashi, karfa yarinyar nan tayi tunanin neman wani abu yazo wajan ta, tsaki yaja, yafice daga dakin ko kashe wutar baiyi ba ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Ilham kuwa tunanin Nihla take tayi, tayi shiru ita kadai agidan, gashi kowa yatafi Babu kowa, tashi tayi tarage kayan jikinta tafuto falo ta kunna kallo ko Allah zaisa ta daina tunanin, gashi tabar wayarta agida bare ta kirata Tana kwance akan kujera tana kallo har bacci yayi awon gaba da'ita Angon nata kuwa yana can awajan Abba Yaqi yataho gidan, daqyar yataho gida ganin karfe daya tana neman yi, harda ledar kaza a hannunsa 🤣 Yana shigowa falon yaji qaran tv, falon yakalla tsarin komai yayi masa yanda yadace Can yahangota tana bacci akan kujera, 'yan qananun kitson da aka mata yayi mata kyau kuma yafuto mata da goshinta, sai fuskarta tayi fayau Ahankali yataka yaje kanta ya tsaya, kayan baccin dake jikinta ya kallah kana iya hango yanda qirjinta yake azahiri, haushi ya kamashi, ya za'ai wannan yarinyar tasaka wannan kayan tazauna haka tsabar rashin kunya amatsayin sa na saurayin yayarta 🙆🏻‍♀️ Saida yasami dede cinyarta sannan ya d'aka mata duka, cikin firgita tatashi tace "subhanallah," Tabude idonta sosai taganshi a tsaye akanta, cikin bacin rai tace "ya Aslam lafiya zakamin irin wannan dukan Kamar agidan kurame? Kira daya idan kamin ai Zan tashi" "Ok ke saboda tsabar rashin kunya nizaki koyawa yanda Zan tasheki daga bacci?" Tayi shiru tana jinsa, sosai taji zafin dukan, ledar hannunsa ta kaza ya wullo mata jikinta yace "gashinan kici, idan kuma ba zakici ba shikkenan kinyi wa kanki" Hararar ledar daya wullo mata tayi, tawurgar da ita awajan tayi cikin dakinta tabarshi awajan a tsaye Shikuwa da kallo yabita yace "Dani kike zancen" ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ "mami bade kinfara bacci ba" "wallahi nafara bacci Yusif, ina ka tsaya ne baka dawoba?" "mami naje wani waje ne, ga Ice-cream nataho muku dashi ko zakusha" Dukda tana bacci hakan bai hanata murmushi ba, wai ga ice-cream yakawo musu, ita da girman ta ina ita ina wani ice-cream, kawai de yace ga ice-cream na kawowa Nihla 🤣 Kokarin tashi take tace "nikam na qoshi Yusif saide Nihla, bari nakai mata" Cikin sauri ya Dakatar da ita yace "a a a a, mami aikin fara bacci, kiyi baccinki bari nakai mata" Tace masa "to saida safe" Daga dakin yafuto kai tsaye yayi dakin da aka bawa Nihla, abin mamaki a zaune ya taddata tana kallan saman dakin tana hawaye, tana tausayawa Rayuwar ta sosai Kallanta yayi ya girgiza kansa, sannan yaqaraso cikin dakin Cikin sauri ta goge hawayen fuskarta tace "Sannu da zuwa yaya Yusif" Yaji dadin yanda takira sunansa Tsawon shekaru Zama yayi agefenta kan bedside drower, yakalli abinci agefenta alamun bataci komai ba Fuska Babu alamun wasa yace "sauko kici abinci" Babu musu ta sauko, tazauna aqasa, shikuwa be motsa daga Inda yakeba yazuba mata ido yana Kallanta Abincin ta dauka tafaraci amma wani irin daci takeji acikin ranta, daqyar take tura abincin, idonta yayi rau-rau Kamar zatayi kuka, kafin kace me tuni hawaye sun zubo mata, saikuma tasaki kuka sosai, daga qarshe ma saita saka kanta akan gwiwar ta taci gaba da kuka Ajiyar zuciya yasauke yadawo kusa da ita Yazauna har tana iya juyo hucin numfashinsa akusa da ita Haushi ya kamashi, yace "kuka kike akan mijin naki ne?" Cikin sauri tadago kanta ta kalleshi, sai ganinsa tayi dab da ita Kamar zai sakata cikin jikinsa, nan take yayi mata kwarjini, ta girgiza masa kai tace "a a Anty" Ajiyar zuciya yasauke, yace "to kici Abincin Karki zauna da yunwa" Abincin tafara ci amma hannunta sai karkarwa yake, gashi Yazauna dab da ita, duk atakure take tarasa yaya zatayi Shikuwa ganin haka yasa yakai hannunsa kan nata hannun yariqe, sannan yadauki spoon din da daya hannun yafara bata abaki, babu musu take karba tanaci, cikin zuciyar ta fal tunani, kulawar da dan'uwanta ya Abba yakamata yabata, bebataba amma gashi wani bare yanayi mata Saida ya tabbatar taqoshi sannan yabata ledar ice cream din daya shigo da ita yace "ga wannan, idan bazaki iyasha yanzu ba, ga fridge nan kisaka gobe sai kisha" Daga masa kai tayi, yatashi tsaye yace "saida safe" Daga nan yafice Yarufe mata dakin ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Tun tana jiran zuwan Ango harta daina tahaqura, girman gidan yasa takejin tsoro sosai, gashi bakajin qaran komai, shiru garin, haka tatakure waje daya afalo cikin kujera har bacci yadauketa Shikuwa fauwaz yanacan mashaya, da temakon Allah da temakon wani abokinsa da sukasha tare yadawo gida, dirin motar da taji ne yasa tatashi afirgice, Agogon falon ta kalla karfe biyu da rabi, tashi tayi tsaye cikeda tsoro Yana tangadi irinna yan maye yashigo cikin falon, gabanta yafadi, tunda take bata taba ganin mutum murararan cikin maye hakaba sai yau, gadan-gadan yataho wajanta tana ja da baya, har yazo gab da ita, cikin muryar maye yace "keeeee..uban waye yakawo ki nan eh?" Girgiza masa kai tafara tace "yaya Fawaz Dan Allah kayi hakuri" Idanunsa yake son budewa sosai amma yakasa, yayi tangal-tangal zai fadi qasa tayi sauri tariqeshi aikuwa saiya dawo kanta gaba dayansa, dagashi har ita sukai baya suka fada kan kujera, shine akanta ita kuma tana qasa, tureshi tafara kokarin yi amma yamata nauyi sosai, shikuwa jinshi Akwance yasa nan take yafara bacci, kansa ta kalla taga yadora shi akan qirjinta, nan tafara ture masa kansa, amma saiyayi juyi ma yaci gaba da baccin sa Haka ta hakura ta zubawa sarautar Allah ido, wai ita Dida itace qato Akwance akanta, wannan Baqin ciki da yawa yake 🤣 ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Da asubar fari yafarka daga baccin da yake, amma Idanunsa a lumshe bai budesuba, qamshin turaren dayake shaqa Mai dadi ne yasa cikin sauri yabude idonsa, da fuskarta yafara tozali, mamaki ya kamashi, laushin dayaji akansa ne yasa cikin zabura yadaga mata qirjinta Tashi yayi tsaye yana qarewa yarinyar kallo, gaba daya kunya ta kamashi, yaushe ya aikata hakan? Yarinyar nan shi tunda yake ko kallo bata isheshi ba ko a family house dinsu, amma tayaya zaizo cikin maye ya kwanta a qirjin yar mutane d'ame d'ame?😳 Cikin borin kunya ya wanka mata mari Azabure tatashi ta dafe kumatunta, qwallah tacika idonta, cikin tsananin mamaki tace "ya Fawaz menama?" Yace "ashe dama ke ana ganinki shiru shiru ke 'yar iska ce bansaniba? Ni zakizo ki kwantawa a jiki?" Hawaye ne suka zubo mata tace "ya Fawaz kaine fa kaz..." Kafin ta qarasa magana yace "waye yayan naki? Amma kuwa bakiyi sa'ar yaya ba, ki kirani guy, bawani fauwaz kingane ko?" cikin dakinsa ya shige fuuuuu, yana zuwa ya zauna akan gado yadafe kansa,🤦🏻‍♂️ Allah ya soshi ya qwaci kansa awajan yarinyar nan 🤣 ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ "Ibrahim tunda auren yarinyar nan bai iyuba ai bekamata tazauna hakaba ko, yakama ace takoma makaranta" Baba yadubi Alhaji Isma'iel "to Alhaji wacce makaranta zatayi, kawai tazauna haka har Allah yakawo mata miji tayi aure," "A a Ibrahim ba za'ayi hakaba, yarinya zata fara karatu idan Allah yakawo mijin sai tayi aure, akwai maqocina me wannan gidan na hannun damana, already nayi magana dashi, yana aiki a university, yanzu kaje ka dauko min takardun yarinyar Zan bashi, saiya nema mata admission takoma school kawai " Baba yayi shiruuu, sai can yace" Alhaji da wanne baki Zan gode maka? Alhaji kayimin kayiwa yata? " " kada kadamu Ibrahim, ai anzama daya " Alokacin baba yaje ya bincika kayansa yadauko takardun Nihla, yakawo masa, adede lokacin akayi wa Alhaji Isma'iel din kiran gaggawa daga office dinsa,Dan haka yakira wayar mamy yace taturo masa da Nihla, a lokacin suna kitchen suna aiki tare, har Nihla tafara sakin jiki da mamy saboda yanda take janta da fira Tana fadawa Nihla, tadauki hijabinta dogo tafuto compound din gidan wajansu Har qasa ta tsugunna tace "gani baba" Alhaji Isma'iel ya kalleta yace "yawwa yata, kije nan gidan kikaiwa matar gidan takardun ki kice inji ni, tabawa mijinta su" Cikin ladabi ta karbi takardun tafita Tana fita taga unguwar shiru Kamar Babu kowa, kowa yana gidansa yana sabgar gabansa Ilham ce tafad'o mata arai, cikin ranta tace Allah sarki Ilham ko ya take yanzu? "kaga Mazawaje, nagaji da wannan halin naka, saina dinga kiran wayarka amma kashareni?" karo sukayi da juna, har wayar dake hannun wadda take wayar tafadi qasa Matar tace "subhanallah, qanwata me kike tunani haka har kina bigeni? Bakya kallan gabanki ne?" Nihla de tayi shiru tana tunani, inde ba kunnuwanta ne suka jiye mata qarya ba, to tabbas taji wannan matar tace Mazawaje, to dawa take waya acikin family dinsu? Dawa take waya acikin samarin dake Mazawaje family? Koda yake may be da d'an wani family din take wayar Ganin matar ta girmeta yasa tace "kiyi hakuri Anty, wallahi ban kula bane" Ita kuma matar jin angirmama ta ance mata Anty yasa lokaci daya taji yarinyar ta shiga ranta Tayi murmushi, tadafata tace "kada ki damu qanwata, kema anan layin kike ne?" Nihla tace "eh, bamu dade da dawowa ba, kinga gidan mu can" Matar tace "laaa ai nasan gidanma, to dafatan de zamu dinga zumunci, menene sunanki?" Tace "sunana Nihla" Itama tace "ayya suna Mai dadi, nikuma sunana NADIYA"😳 tofa wata sabuwa, anya wannan zumunci zai dore kuwa? Shin Nihla ta gane Wacece Nadiya kuwa? Duk kuci gaba da bibiyata, nagode 🙏🏻 Amnah El Yaqoub ✍️ [6/22, 1:47 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️ {Romance&Friendship luv} Writing by Amnah El Yaqoub Like my page On facebook 👇 https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 19&20 Murmushi Nihla tayi "Allah sarki Anty Nadiya, nagode, bari inje an akenine" Gidan tawuce zata shiga Nadiya tace "to ai gidanmu ne, Dan haka tare zamu shiga" Daria sukayi gaba dayansu, sannan suka shige gidan Nadiya ta lura yarinyar akwai abinda yake damunta, tabbas akwai damuwa a atattare da ita, amma zata jata a jikinta har taji damuwarta, Dan ita kam haka kawai taji yarinyar ta kwanta mata, Kamar qanwarta kasancewar batada qanwa mace sai namiji Nihla tabawa maman su Nadiya takardun, cikin murmushi takarba tace idan yadawo zata bashi, daga nan Nihla tayi musu sallama tafuto, amma fafur Nadiya tahanata tafiya, qarshe ma dakinta tajata suna fira kadan kadan, Nihla ta lura Nadiya Babu ruwanta, gata da son mutane, Tun tana dari-dari da ita harta sake sukayi ta fira Kamar sun saba ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Zaune suke su uku Sunayin break fast, mamy tadubi Alhaji Isma'iel tace "Alhaji Nihla fa batada kayan sakawa sosai, sannan Babu waya ahannun ta irinta 'yanmata,kuma ace wannan kyakykyawar yartawa Babu waya Alhaji, yanzu idan tafita ta samomin siriki wacce number zata bashi?" Yusif yana jinta, ahankali ya kalleta, yamaida hankalinsa kan Abincin dayake ci Alhaji Isma'iel yayi Murmushi, yaga alama hajiya tanaso ta maida yarinyar tata Babbar yarinya yace"to hajiya ai ga yayanta nan, suje su siyo duk abinda takeso, idan sun kawo kinga akwai abinda babu saikiyimin magana asiyo mata " Dadi yakama Nihla ta kalleshi tace"Nagode Dad" "Babu godia a tsakanin mu Nihla, sannan ga albishir ki shirya zuwa next week zaki fara zuwa makaranta, saide kuma zaki bar mamynki da kewa" Daria sukayi gaba dayansu Suna gama cin Abincin suka tafi shopping ita dashi, suna tafiya ahanya Babu Wanda yakewa dan'uwansa magana, shi har yanzu maganar mamy ce take masa yawo a zuciya, wai saboda tabawa samari number Hmm Ita kuma Nihla ganin Yaqi bata fuska akan maganar yasa itama tayi shiru Har sukaje super market din ataqaice yace mata "Futo" Babu musu kuwa tafuto, sukayi ciki Dogayen riguna suka diba, masu shegen kyau, saida suka duba Wanda sukayi mata dai dai sannan suka dauka, inde yaga kalar riga zata karbi fatar jikinta saiya dauka yaqara musu, har mamaki yake bata Da sukaje wajan kayan kwalliya komai Set yake dauka Kallansa tayi "yaya Yusif sunyi yawa fa" Yace "zaki dade kina amfani dasu" Daga haka bata qara magana ba, suka koma wajan perfume dakuma inner wears, Kallanta yayi, yanzu kam bashida damar dazai zaba mata, yace "dauki mutafi" Kunya ce ta kamata, haka ta matsa taba zaba, da yaga tana kunyar sa saiya kauce yabar wajan Atamfofi kuwa sun kwashe su sosai, sannan suka tafi shagon saida wayoyi Anan ma Kallanta yayi yace "wacce iri kikeso?" Tace "irin tawa tada, iphone ce" Haka nan yaji zuciyarsa tana zargin cewa mijinda zata aura ada ne yasiyamata wayar, cikin kishi yace "dole sai irinta?" Itama da taga fuska ad'aure Babu alamun wasa sai tace "A a, ko wacce ma asiya inaso" 🤣 Babu musu yasiya mata Babbar waya Qirar Huawei Sannan suka dawo gida da kaya niqi-niqi Mamy suka samu afalo tana ganin su tare taji dadi, harga Allah tanason Yusif da Nihla, anan Nihla tabata kayan itama tana gani ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Cikin satin mahaifin Nadiya yanema mata admission a wata private university, Base university, yayan manya ne acikin makarantar kowa tanajin kanta ita watace, gayu kuwa ba'a magana, ko wacce mace tanaji da tata wayewar Direban gidan zai kaita yadawo da ita, saide kawai zuwa take, amma bata gane komai, damuwar datake ciki ma ta isheta, gashi babu wanda zatai sharing damuwarta dashi bare ta cire maganar datake ranta abata shawara ko zataji dadi baba yahanata kiran kowa na kano Ahankali sabon su da Nadiya yake qaruwa harta kai kowa yana ziyartar kowa acikinsu Yauma bayan tadawo daga makaranta tana daki tana duba hand out, Nadiya ta kirata awaya suka gaisa sannan sukai sallama, dena karatun tayi tafuto falo, anan taga mamy tana zuba danbun nama dayawa acikin wata roba, tace "mamy wannan ina za'a kai?" "Na yayanki ne, zai tafi dashi yanzu" "mamy ina yaya yusif din zaije?" Murmushi tayi, ganin yanda Nihla tayi mata Tambayar cikin sauri haka, tace "china zai tafi, akwai aikin dayake son yayi" Jikinta ne yayi sanyi, ahankali ta karba tace "to mamy kawo nazuba masa" Bar mata tayi, tazuba masa sannan tace "mamy bari nakai masa" Bata jira amsar mamynba tayi hanyar dakinsa, akaro na farko Tun zuwan su gidan Turawa tayi ta shiga dakin nasa da sallama, yana zaune yana hada kayansa acikin truly Ya amsa mata batare daya kalli Inda takeba, zama tayi akusa dashi tace "ya Yusif gashi inji mamy" "ajiye anan" abinda yace mata kenan Ta ajiye masa, zuciyarta tana karyewa Kamar zatayi kuka, duk sai shamata kunu yake tunda yadawo, wai ita ya sukeso tayi ne? Dauka yayi yasaka acikin jakar tasa sannan yatashi tsaye yace "idan kinsamu time kuje keda Nadiya abude miki account idan kina buqatar kudi saiki kirani ki fadamin, zan tafi yanzu, may be nadawo dawuri" Yana fada mata haka bakowa ne yafado mata araiba sai ya Abba, duk alamomi sai yanzu suke nuna mata cewa dama ya Abba baya santa, itace takasa gane hakan soyaiyar sa ta rufe mata ido, duk su ya Usman Babu abinda basuyi mata lokacin data dawo kano, kowa yana nan nan da ita, amma shi ya Abba itace take nan nan dashi, 😃 Gashi shima ya Yusif yadawo amma bata bashi kulawar komai ba sai shine yake hidimta mata, batasan lokacin da hawaye yazubo mataba, ahankali ta miqe tsaye tafada jikinsa tana sakin wani irin kuka abaiyane Qam Yusif yaqame a tsaye, shibe tureta ajikinsa ba, shikuma bai saka hannu ya rungumeta ba 🤔 Kuka take sosai har hawaye yana d'isa agaban rigarsa Wata irin ajiyar zuciya yasaki, sannan yasaka hannu ya rungumeta gaba daya, yana bubbuga bayanta, wani irin yanayi ya tsinci kansa aciki, Wanda bai tabajin irinsa ba, cikin kasalalliyar murya yace"kiyi hakuri mana kiyi shiru, menene na kukan? Me aka miki?kokuma Wanda zaki aura kika tuna? " Girgiza kanta tayi, tace" dan Allah kayi hakuri, kadena fishi " Yaga alama idan akaci gaba da tsaiwa ahaka to yarinyar nan zatasa yayi mata ba daidai ba, Dan haka ya janye tadaga jikinsa, yace" ya'isa to, ni bana fishi dake, kuma kece yakamata nabawa hakuri, tunda kina ganina kika share ni, saboda kin samu wani" Wasa tafara da yatsun hannunta tace "kayi hakuri, kuma ba kullum saina kiraka ba, amma wayar taqi shiga" Tafadi haka cikin shagwaba Murmushi yayi "to naji, komai yawuce, yanzu Muje ki raka yaya Yusif zai tafi kada yayi missing flight, but banda bawa samari number, kinji ko?" Daga masa kai tayi, tace "to" Sannan ta janyo masa jakar suka futo daga dakin, mamy bata falon, kai tsaye dakinta suka nufa domin yayi mata sallama ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Dawowar sa kenan daga makaranta duk yagaji, ga yunwa dayakeji yaji Kamar ana buga get din gidan Tsaki yaja sannan yatashi yafita, yana budewa yaga samari su uku dukansu yarane bazasu wuce 27 ba, gaba dayansu sun tsuke cikin qananun kaya, kallansu yayi dakyau yace "samari lafiya kuwa? Ko wani gida kuke nema?" Daya daga cikin su yace "dama munzo wajan qawarmu ne, munyi waya da ita, so tace mana tadawo nan gidan dazama" Cikin mamaki yace "qawarku kuma? Inaga kunyi batan hanya ne, ba nan bane" Na biyun yace "bawan Allah ya zakace mana ba nan bane, bayan nan gidan tayi mana kwatance?" Yace "Wacece qawar taku?" Na ukun yace "Diyana" Tsayuwarsa ya gyara yace "Ok ai sai yanzu nagane ku, ashe wajan aminiyarku kukazo, to bismillah, kushigo mana" Wanda yace wajan Diyana sukazo yakalli Adam dakyau, anya kuwa zai shiga? Da alama fa wannan yayan tane, karfa su shiga yamusu shegen duka 🤔 Saiya girgizakai yace "no, Barshi kawai," Ya kalli sauran yace "Baba kuzo mu ware kawai" 🤣 Sukuma biyun suka dage sai sun shigo, Adam yana tsaye cikin zuciyarsa yana addu'ah su shigo gidan, ysce"ku qaraso mana, tana ciki fa maryam din " Sunfara shigowa gidan kenan sai daya yalura da yanda Adam yake tattare hannun rigarsa aboye 🤣, sai yaja dan'uwansa ya tsaya Adam yajuyo ya gansu sun tsaya yace" me kuka tsaya yine? Rakaku zanyi " Adede lokacin

Chapter 7 of 24