Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ciki yahanata magana tama kasa Dagowa ta kalli idon kowa saboda abin kunyar da d'ansu ya aikata Hajiya Farida bataji dadin abinda akaiwa Nihla ba, yanda take shiri da Mai Hakuri bataso wannan abu yafaru akan yarsa ba, kowa yasan cewa yaran Babu Wanda yakeso, amma dukda haka ai basuyi magana ba Hajiya Abida mahaifiyar Ilham tayi shiru abun duniya yayi mata yawa, wannan abin takaici da yanzu harda Ayshanta za'ace baza'a iya aura ba Ran Daddy yayi mutuqar baci akan abinda Abba yayi, haqiqa ya kunya tasu agaban mutane, ya nuna musu cewa ba'a isa dashi ba Ahankali yadago kansa ya kalli al'umar dake gabansa yace "amatsayina na babba acikin wannan family daga ranar yau, na yankewa wannan yara ranar aure, nanda wata daya Mai zuwa" Ahankali Momy tatashi taja hannun Nihla suka futo daga cikon hall din, qafar Nihla sai hard'ewa take saboda yanda ake Kallanta Suna fita shima Usman yatashi yayi gaba ransa abace, Aliyu ma ya biyo bayansa, yayinda farouq shima yaga to zaman me zaiyi? Yatashi yabiyo bayan 'yan uwansa Sai ajiyar zuciya Nihla take ja saboda yanda taci kuka, ta kalli Momy tace "Anty inajin zazzabi" daga haka tashige cikin dakinta tafada kan gado tana sakin sabon kuka Momy ma ta doru abayanta,tana zuwa taganta tana kuka, tasa hannu tadagota ta rungumeta tana bubbuga bayanta alamar rarrashi, saida taji ta rage kukan sannan tadagota tana kallan idonta tace "Nihla, zaki iya rabuwa da Abba? Ki cireshi gaba daya daga cikin zuciyarki?" Hawaye ne yazubo mata tace "Anty inason ya Abba sosai, bazan iyaba Anty" Momy tace "zaki iya Nihla" Girgizakai tayi alamun a a, sannan ta koma kan gado tarufe idonta da fillo tana kuka Jikin Momy yayi sanyi, taso ace Nihla zata iya rabuwa da Abba, dasai ta nunawa Abba Dan hakin daka raina Shike tsone maka ido, to amma yaya zatayi tunda yarinyar ta dage akan tana sonshi? Dole shi zatayi wa dole akan saiya amince da wannan auren Tana gama wannan tunanin tafuto daga dakin domin zuwa wajan Abba, dasu Usman tafara cin karo afalon azaune, kowa ransa Babu dadi Batace dasu komai ba tashige dakin Abba, suma sukabi bayanta dukansu Suna shiga dakin suka sameshi yana zuba kayansa acikin jaka, Momy ta kalleshi tace "ina zakaje?" Fuskarsa atamke yace "Momy already hutu na yaqare Zan koma bakin aikina" Usman yace "Abba kanada hankali kuwa? Kasan abinda ka aikata zakayi dana sanin sa agaba ko?" "bana tunanin haka yaya Usman, wai meyasa kuka kasa fahimta tane? Saboda me Zan boye mata gaskiyar abinda yake raina?" Cikin zafi Aliyu yace "to Dan uwarka baka isaba, wacce yarinya kakeso dazaka Wulaqanta Nihla akanta? Wacece?" Kai tsaye yace "sunanta Nadiya, tana Abuja, tare mukai karatu da ita a germany" Momy tace "Abba,yarinyar nanfa marainiya ce, agabanka mahaifiyar ta tace idan ka girma da kanta zata samo maka matar aure, kana tunanin tanada wadda zata samo makane bayan Nihla? Ashe yanzu da ace Aisha tana raye a gabanta zaka watsawa yarta barkono a'ido? Banasan abinda zakazo kana dana Dani akansa nan gaba " Shiru yayi Bece komai ba, farouq kam me raguwar zuciya hawaye yake sharewa yakasa cewa komai tunda suka shigo dakin, sai yanzu yadago kansa cikin hawaye yace " Momy nizan aure ta" Kallansa Abba yayi jin irin furucin dayayi, yarasa meyasa duk suka damu kansu akan Nihla, shima yanaso yaga ya faranta ransu ta hanyar amince wa to amma Nadiya fa? Aliyu yace "farouq bazaka aure taba, shidin shine dai zai auri yarinyar, da yanaso da bayaso" Momy ta kallesu tace "ya'isa haka," Taci gaba da cewa "Abba idan na isa dakai, amatsayina na mahaifiyar ka to inama umarni akan ka auri Nihla, nide amatsayina na wadda tayi renon cikin ka Nihla tafi kwanta min a raina, idan kuma nima zaka nunamin ban'isa dakai bane shikkenan katafi kabar Mazawaje family din Kamar yanda mahaifin ka yace, su Usman ma sun isheni " Dasauri tafice daga cikin dakin saboda wani sabon kuka daya Taho mata Farouq ya kalleshi yace " danma kasamu yarinyar tana sonka, duk tarasa wazata so acikin mu saikai, kaje kayi tayi, kada Allah yasa ka amince, bazata rasa masoya ba" Yatashi yafice daga dakin, su Aliyu suka mara masa baya suka Barshi shi kadai a dakin Ahankali Yazauna yadafe kansa 🤦🏻‍♂️ Meyasa kowa yakasa fahimtar sane? ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Daddy tunda yadawo daga wajan taro Yazauna afalon nasa yayi shiru yana tunani, yanda Aisha tatafi tabarshi ai dole ya kyautatawa yarta, yanajin Nihla aransa sosai, duk lokacin daya bude ido yaganta yanajin dadi, bayasan abinda zai rabashi da yarinyar kokadan, Su Usman suna zaune afalon suma, ya kallesu fuskarsa Kamar Babu damuwa yace "kume kuke jira anan ne? Tunda angama ai yakamata kutafi gida ko?" Babu musu suka tashi, amma farouq kansa har ciwo yake saboda yanda yayi kuka Momy ce tafuto tafon taga Daddy azaune shi kadai, tazauna kusa dashi tace "Sannu da zuwa Alhaji" "yawwa Rahma sannu, ina wannan yarinyar take?" "tana daki, zazzabi ne yadan rufeta, amma na bata magani tasha, nabarta tahuta" Jinjina kansa yayi batare dayace komai ba, itace tasake kallansa tace "Alhaji nasamu Abba munyi magana dashi, ya amince da auren, yana cikin dakinsa baitafi ko'inaba, kayi hakuri akan abinda yafaru" Ajiyar zuciya yayi "ai nayi tunanin yatafi wajan wadda yakeso din, da saide yanemi wani uban, amma baniba" Itama Jinjina kanta tayi, tace "yana ciki, kayi hakuri Allah yahuci zuciyarka" Batare dayace mata komaiba yatashi yayi cikin dakinsa Awannan rana haka Nihla tawuni adaki ko falon bata futoba, gaba daya family din Babu mejin dadi aransa Acikin yammatan ma Babu wadda taje wajan kowa, ko wacce tana part dinsu tanaji da abinda yadameta Bayan sati biyu tana zaune a dakinta, yammatan suka zo wajan ta, kullum tana zaune adaki, abincima saide Momy takawo mata, kunyar ma hada ido take da Abba saboda yanda take shishishige masa amma yayi watsi da'ita Ilham ta kalleta tace "Nihla har yanzu kinqi sakin ranki, yakamata ki Manta da abinda yafaru fa, duk kin rame" Dida tace "wallahi kuwa, ni bazan d'orawa kaina ba, muma nan dukanmu hakuri mukayi, dama yaya Adam naso, kuma yanzu anbawa Diyana shi" Tsaki Diyana tayi tace "ni wallahi Dida kina qara ba tamin raina idan kina hadani da wannan mutumin, arasa Wanda za'a bani sai malami, ni kunyar fita ma nake wallahi, adinga nunaka ana ga matar Malam" 🤦🏻‍♀️ Ilham tace "nide bansan yaya Zan zauna da yaya Aslam ba, agabana Anty aysha take wayar soyaiya dashi amma wai ace shi Zan aura, haba aida kunya, amma Zan bashi girman sa yanda yakamata, renin hankali ne bazan daukaba, idan ya min wallahi ramawa zanyi, Dan dagashi har Hajiya Na'ila bazan dauki renin wayonsu ba " Ta kalli Dida tace" kekuma Dida wannan shiru shirun naki wallahi saikin Barshi, bar ganin yaya Fawaz yaya nane wallahi idan yamiki kicire kunya kirama " Ahankali tace" inani ina shi Ilham, bazan iya bama, kowa yayi sabgar gabansa " Diyana ta kalli Nihla tace" ke ya batun yaya Abba kuwa?" Tace" bansani ba Diyana, Tun lokacin da abin yafaru ban qara haduwa dashiba, banyi tunanin zaimin hakaba, abin takaicin ma shine yanda nakasa cireshi a raina, har yanzu ina nan ina jinsa acikin raina, abinda yake bani tsoro Diyana shine idan na kwanta bacci kullum sainayi mafarkin sa, dana kwanta dashi a raina daban kwanta dashi a raina ba " Gaba dayansu sun tausaya mata, Dida tace" kiyi hakuri Nihla, lokaci ne " ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Tsaye suke a compound din gidan shida Abba, Aslam ya dubeshi yace "Abba biki yanata matsowa bamu gayyaci kowaba" "nifa Aslam mantawa nake da wannan auren, babu wanda Zan gayyata, tunda sundage saina aure ta, ayi bikin kawai, naji haushin wasiyyar nan, akan wannan qullin nasu suka hana wannan family yin taron komai, wai saboda sun tanadar mana Babban taro agaba, mutsw " ya qarasa maganar dajan tsaki Aslam yace" to aikai Dasauqi Abba tunda Nihla zaka aura, amma nifa, qanwar budurwa ta fa, gata da rashin kunya yarinyar " " idan tayi maka rashin kunya ka zaneta kawai ka wullota waje karufe gidanka "🤣 Cewar Abba Ajiyar zuciya Aslam yayi" Abba duk cikin mu kaida Fawaz ne kukai sa'ah, Nihla tana sonka sosai " " So, so, so, maganar kenan dai, Aslam narasa gane meyasa qananun yara suke daukar kulawa amatsayin soyaiya, kaga mubar wannan maganar dai, na turawa wajan aikina takarda inaso su yimin transfer nadawo gida " " hakanma yayi Abba, kaga zamufi samun damar kammala abubuwan damuke buqata na company " ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ "my son, kacika rigima dayawa, idan kazo gidan me zakayi? Mami d'inka tana nan lafiya, saini nikuma kana ganina idan nazo" Shiru yayi yana sauraron yaron nasa, saida yagama jin abinda yace sannan yace "to shikkenan naji, idan kazo ma bazan barka ka kadede ba zaka koma, Allah yakaimu next week din, Yaya batun kayaiyakin da nace katuro? Katuro kuwa?" Cikin muryarsa Mai cikeda Aji yace "anturo su, zuwa jibi zasu qaraso" "Ok to, to, ba laifi, zan fadawa mami dinnaka zuwan ka" daga haka suka yanke wayar, yana juyowa bayansa yaga Ibrahim Mai hakuri, nan take ya fadada fara'arsa yace "a a mai hakuri, kace kana tafe" Baba yace "ina nan wallahi Alhaji, ai nazo na tarar kana waya, shine nace bari naqyaleka kagama tukunna" Cikin murmushi yace "eh wallahi ina waya da yusif ne Dan wajena, yadage yanaso nabarshi yazo gida yaga maminsa" Baba yayi Murmushi yace "to Alhaji abarshi mana, aiya dade yayi kokari ma, daga karatu anzarce harkar canji ai yaro yayi hankali saide muce Allah yaraya mana" Yace "hakane kam, Mai hakuri abinda yasa nakiraka shine dama nayanke shawara zamu koma Abuja da zama nida Mai dakina, saboda harkokin nawa sunfi yawa Acan, shine nakeso kaima ka shirya akwai wani aiki na canji danake so na doraka akai, idan Babu damuwa inason mutafi gaba dayanmu harkai, mu koma can gaba daya " Cikin tsananin murna baba yafara yiwa alhaji isma'eeil godia, Alhaji yace" Babu damuwa, sai ka fara shiri, wani satin idan Yarona yadawo, zamu wuce insha Allah " Cikin tsananin murna baba yace zai shirya, haka suka rabu da maqocinnasa cikin farin ciki Yana shiga gida yafara hada kayaiyakin gidan yanata farin-ciki, wayarsa ce tayi qara, yana dubawa yaga hajiya Farida ce mutuniyar tasa, cikin farin ciki yadaga wayar "Barka da wannan lokaci hajiya Farida" Itama anata bangaren "tace yawwa Mai hakuri, mu munata shirye shirye, amma banga yan yalleman sunzo ba" "shirin me kuke hajiya?" Tace "Ah Mai hakuri karka cemin bakasan ansawa yaranmu ranar aure ba? Kuma danaga harda Nihla shiyasa nace bari nakiraka naji yaushe zakuzo"🤣 Cikin mamaki yace "ranar aure kuma hajiya Farida?" "qwarai kuwa, wani satin ma aure idan Allah yakaimu" Yace "subhanallah wallahi bansaniba hajiya, banida labari, waye ne Nihla zata aura?" Tace "Abba aka bata, saboda anbi tsarin wasiyya ne da iyayen mu suka bari, shine sukace ahadata da Abba, abin takaicin ma shine yaron baya sonta, acikin bainan Nasi yafuto qarara yace bayaso" "subhanallah, subhnllh, banida labari hajiya, Allah yakiyaye gaba," Tace "amin Ibrahim to sai anjima" Shima yace mata "to hajiya Farida nagode sosai" Wayarta takashe tana tunani aranta, anya kuwa Mai hakuri Babu abinda yake damunsa? Afada maka wannan maganar amma kace Allah yakiyaye gaba,? lalle kuwa in hakane ya tabbata Mai hakuri 🤣 Shiru yayi yariqe wayar a hannunsa, me Alhaji Abubakar yakeji da shine? Za'ayi bikin yarsa ta cikin sa amma bashida ikon da za'a kirashi Afada masa amatsayin sa na ubanta? 🤔 Wannan wanne irin iko ne? ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Zaune suke a part dinsu, shida Momy, yasaka qananun kaya, farin wandon jeans, sai riga marar hannu, yana zaune afalon suna kallo shida Momy, gaba daya tamanta dashi awajan, harkar gabanta kawai takeyi, Dan wani irin haushi takeji aqasan ranta, yana Kallanta Tun dazu take ta hada wani abu da madara, daga gani zai yi dadi sosai 🤣 Nihla ce tafuto, jikinta sanye da kayan bacci amma ta dora Babban hijabi akai,dogo ne sosai Tsawon sa har qasa, daqyar kake gano qarshan wandon jikinta saboda tsayin hijabin 🤣 Tana ganinsa afalo tayi turus, nan da nan gabanta yafara faduwa, ahankali ta qaraso cikin falon itama tazauna, tunda akai meeting dinnan sai yau taganshi Tunda tafuto yake Kallanta, cikin ransa yake cewa kullum tana cikin hijabi, yarasa metake boye wa, yarinya qarama ta d'orawa kanta wahala 😂, kullum ka takura kanka acikin hijabi kome zata boye masa bayan yagama yimata wanka? 🤔 🤣 Ahankali ta dago kanta, karaf suka hada ido, cikin sauri yakawar da kansa gefe, Kamar ba shiba Ajiyar zuciya tayi tace "Ya Abba ina kwana?" Ataiqaice yace "lafiya" Haushi yakama Momy, taso ace Nihla tayi banza dashi wallahi, domin kawar da bacin ranta yasa tadau cup din maganin tsumin data hada mata tace "Nihla ungo wannan kisha" Dasauri ya kallesu, yayi tunanin shi zata bawa yasha ashe wannan yarinyar take hadawa? Kona menene oho musu Dauka tayi tafara sha, abin yanada dadi Dan haka Babu musu ta shanye shi tsaf Yana ganin ta shanye cikin ransa yace gaskiya ne, yanzu Momy bata sonsa 🤣, kowa dakowa Nihla Nihla Kamar abin sihiri 🤦🏻‍♂️ Kallanta yayi Babu ko d'ar yace mata "Am Zan'iya samun coffee?" Ba Nihla kadai ba, hatta Momy saida tayi mamakin qarfin halin Abba Batare da tace komai ba tatashi taje kitchen tahado takawo masa, daga nan tawuce daki, bata qara dawowa falon ba, Dan ganinsa ma zai iya qara mata wata soyaiyar tasa acikin zuciyarta ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ "umma Tun safe gashi har yamma tayi amma yaya Fawaz yana dakinsa yana bacci, saikace me baccin mutuwa" Hajiya Abida tace "Ilham kenan, zai wuce qwaya yasha ne? Jiya idona biyu har karfe biyu Fawaz bai dawo gidaba, sai wajan biyu da kwata yadawo shima ina Tambayar sa daga ina yake yafara min magana cikin maye alamun wajan abokansa yaje suka sha tare, nasan shine yasa har yanzu bai tashi ba" "to amma ummah meyasa yaya Fawaz bazai daina halinsa ba? Kayi ta bankawa cikinka kayan maye baka tsoro suma illa? Gashi ko sallah baiyi ba" "Hmm Ilham ni kaina al'amarin Fawaz yana bani mamaki, kinga babanku yayi masa maganar aiki yafara zuwa office amma Fawaz yayi biris, inajin haushin yanda ake kiran dana Mashayi, Allah ya shirya minshi kawai" "Ilham tace" amin ummah, gabana yana faduwa idan natuna da ranar bikin nan ummah " " kiyi hakuri, insha Allah komai zaizo da sauqi, kitashi kije gidan safara'u sister na, tamin maganar gyaran jiki " Haushi yakama Ilham, wai gyaran jiki, tarasa wa zata gyara wa jiki sai saurayin yayarta🤦🏻‍♀️ Suma su Dida haka hajiya Farida tasasu agaba tahada musu kaza kowa dai-dai, Diyana kuwa tafi bata maganin matsi, saboda ita kanta batasan adadin mazanda yarta takula ba🙆🏻‍♀️🤣 Haka akaci gaba da hidimar biki kowanne bangaren Babu maiso, har Allah yakawo satin biki ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Rana bata qarya, ayaune aketa hada-hadar daura aure, iyaye maza kowa ka kalli fuskarsa zaka ganshi yana farin ciki, amma iyaye mata kowa da abinda ya isheta Tun karfe goma mutane suke ta tururuwar zuwa wajan daurin auren, saboda iyayen maza sun sanar, su kuwa yaran a tsakanin su ko walima Babu Wanda yahada Angwaye kowa yayi kyau da fararen shaddodin da Alhaji Basiru ya dinka musu, Kamar ka sacesu ka gudu Kowa ya hallara acikin Babban masallacin unguwar domin daurin auren, liman ya gyara zama da nad'in rawanin kansa, yace "to Alhamdulillah , wanne za'a fara daurawa?" Alhaji Baqir yabashi sunayen yaran a rubuce kowa da matar sa agaban sunansa Adam -maryam(Diyana) Fawaz-Khadija (Dida) Aslam - Ilham Abubakar - Fatima (Nihla) ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Tun safe yafuto daga gida yanaso yaqaraso gidan amma matsalar go slow tasa ya makara, mutanan daya gani a masallacin unguwar ya tabbatar masa da cewa anan ake daurin auren, kai tsaye yatafi masallacin shima, Kutsawa yake cikin dandazon jama'ar wajan har ya qarasa cikin masallacin Adede lokacin liman yake cewa "yawwa Alhamdulillah saura na mutum daya kenan,"🤣 Ladan yace "eh saura na Abubakar da Nihla" Qarewa mutanan wajan kallo yayi, Alhaji Baqir, Daddy, Alhaji Basiru, da Alhaji habib mijin hajiya Farida, dakuma mazan family din baki dayansu su Usman dasu Aslam Wato Angwaye Dasauri yadaga hannu yace "A dakata!!" Gaba daya idanu suka dawo kansa, Daddy cikin ransa yace "Mai hakuri" Amma afili baice dashi komai ba, yazuba masa ido yana kallansa Baba ya kalli liman yace "ala gafarta Malam, nine mahaifin Nihla, amatsayina na ubanta ban yarda adaura wannan aure ba, yarinya ta kawai nazo dauka, ita nake buqata" Ko kallan Inda su Daddy suke baiyi ba, bare gaisuwa ta hada su, yajuyo yafice daga cikon masallacin, yanaji ta cikin Speaker anata salati 🤣🤣 Daga nan baba ya koma gidan,ya tsaya abakin get, yasa maigadi yashiga gidan yakira masa Nihla, ace inji babanta tazo Maigadi kai tsaye yatafi part din Momy, jama'a sun taru anata hidimar biki, gaba dayansu yanmatan suna zaune a dakin Nihla, Mai kwalliya tana tsantsara mata Diyana ce tafuto falo tana amsa wayar wani saurayinta 🤣 Maigadi yana ganinta yace "yawwa Diyana, kicewa Nihla babanta yana kiranta, yana can abakin get" Ta amsa masa sannan ta amsa wayarta tajuya dakin tace "Nihla babanki yana bakin get, yace kije" Yanda ta dade tana kiran wayarsa Yaqi ya amsa, tana tura masa saqo Yaqi yayi reply, hakanne yasa ta naji ance babanta tatashi tace "Baba nah!!!" Sannan ta kalli maiyin kwalliyar tace "ina zuwa, bari naje nashigo da babana ciki" Futowa tayi, Momy bata lura da ita ba tanata baqi Kai tsaye Nihla tafuto bakin get din ko mayafi Babu🤣 Tana zuwa taganshi fuska Babu Rahma tace "Baba!!!" "wuce mutafi gida" abinda yace da ita kenan Mamaki yakamata, bata taba ganin baba cikin fishi irin wannan ba, tace "Amma baba Anty...." "Kiwuce mutafi gida nace!!!" Yadaka mata tsawa Tace "To baba Babu ban dauko hijabi..." Kafin ta qarasa yaja hannunta, suka fara tafiya, sai dankwalin da aka nad'a mata akanta ta ware tayafa a jikinta 🤣 Suna zuwa bakin titi yatare musu adedeta suka shiga, gaba daya tarasa gane kan baban nata, tashar Mota sukaje, daga nan suka wuce jigawa Awa biyu ce ta kaisu gida, kuma har lokacin Bece da'ita uffan ba, suna zuwa kofar gida sukaci karo da motar Alhaji Isma'eeil qirar Range rover Alhaji Isma'eeil yace "Mai hakuri ina ka shiga Tun dazu angama zuba kaya amota kai muke jira?" Baba yace "Alhaji wallahi kano naje Tun safe, yarinya ta za'ayi wa aure batare da iznina ba, shine naje nadauko ta" Adede lokacin yafuto daga gidansu shida mami, karaf maganar tasauka acikin kunnansa, Dasauri yakai kallansa kan yarinyar da ake magana akai "Nihla my friend" yafadi sunan cikin ransa, fuskarta ya qarewa kallo har yanzu kyanta yana nan saima qaruwa dayayi Cikin mamaki yakalli baba yace "Baba wai wannan yarinyar za'ayi wa aure?" Ko a mafarki taji wannan muryar bazata taba mantawa da ita ba, kallansa tayi tafara magana cikin ranta "yaya Yusif! Innalillah.. Yaushe yadawo? 🤔 Alhaji isma'iel yayi Murmushi yace" Mai hakuri, hakuri yaqare kenan "🤣 Mami da baba sukai daria, Nihla tayi shiru, ga tashin hankalin rabuwarta da yan kano ga kuma mamakin ganin yaya Yusif Handbag din mami ce a hannunsa, ahankali ya matsa ya wullawa Nihla jakar yace "ke riqe wannan " Dasauri ta cafe jakar, saboda karta fadi qasa Alhaji isma'eeil yakalli Yusif yace "nasa Mai gadi yadauko kayan Mai hakuri ansaka amota, bani key naja motar da kaina, ban yarda da driving dinka ba na ganganci, idan kuka samu titi kuna gudu Kamar bakwa son ranku" 🤣 Sumar kansa ya sosa,sannan yabashi car key din Sai a lokacin Nihla tagaidasu, mami da Alhaji Isma'eeil suka amsa mata cikeda kulawa Alhaji ne yabude motar yashiga, shima baba yashiga gaba, mamy da Nihla suka shiga baya, sannan shima Yusif yashiga bayan daga daya bangaren, Yazauna agefen mamy Mamy ta kalli Nihla cikin kulawa tace "Nihla kinsha hanya sosai ko 'yata, nasan kin gaji, zoki kwanta kihuta" 🤣 Taja Nihla jikinta sannan ta dora kanta akan cinyarta tana bubbuga bayanta Kamar wata qaramar yarinya Shikuwa Kallanta yake, Wato bazatayi masa magana bako? It means batayi missing dinsa ba,koda yake yaushe zatayi masa magana tunda ta Manta dashi harta samu wani zata Aura (tofa🤔) Ahankali Alhaji isma'eeil yatada motar, suka dauki hanyar Abuja. To Alhamdulillah anan na kawo qarshen labarin DANGI DAYA, zan Dakatar da typing dinsa badan komai ba saidon Comments din readers da ban gamsu dashi ba, sharhi yayi qaranci, idan akwai wadda na batawa rai Sanadin wannan labari to tayi Hakuri 🙏🏻 WhatsApp readers banida bakin dazan gode muku, kunyi min komai akan wannan littafi masu yimin sharhi daga cikinku nayi saving number dinsu insha Allah zansakaku asabon group dina, mudinga gaisawa Yaya labarin Mazawaje family? Wanne hali Momy zata shiga dangane da tafiyar Nihla? Yaya Rayuwar Nihla zata kasance a Abuja? Ina labarin amare masu shirin shiga daka ciki?🤣 Amnah El Yaqoub ✍️ [6/21, 1:40 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️ {Romance&Friendship luv} Writing by Amnah El Yaqoub Like my page On facebook 👇 https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 Tabbas hakane, laifin wani baya shafar wani, amma kuma Babu dadi kayi rubutu a karanta ma bayan ansan kanason Comments a share ka, danku nake wannan rubutun, be kamata agani ayi shiru ba, masu kirana, masu min private text, masuyi min magana ta group, da Wanda suka min ta page d'ina, duk naji maganganunku, nagode da soyaiyar dakuke nunamin, insha Allah zanci gaba da typing, daga qarshe wannan page din na sadaukar dashi ga dukkanin masoyan Amnah El Yaqoub 💋 'yan labe ina kuke? 🤔 To Allah yasa ku d'ore dayin Comments ehe😚😚 17&18 Liman ya kalli Alhaji Abubakar kozaice wani abu tunda shi ne babba, amma tashin hankalin da Alhaji Baqir ya hango a fuskar Daddy ne yasa shi yayi magana dasu yace "ala gafarta Malam mungode, mungode sosai," Yadauko kudi a aljihunsa masu yawa ya ajiye musu, Sannan yakama hannun Daddy suka futo daga masallacin, Alhaji Kabeer kuma shine yake sanarwa da mutane ansoke daya daurin auren, daga nan yaci gaba da godia ga jama'ar dasuka gayyata Uban gayya kuwa fuskarsa Babu yabo Babu fallasa Wato Abba Angwaye dukda dama can suna cikin bacin rai, sai abin yasake qaruwa Usman yadafe kansa, meyasa baba Ibrahim zai musu haka? Amma aida yayi hakuri anbi komai Ahankali ko, amma abu acikin taron mutanen da sukazo daurin aure Dan haka yayiwa su Aliyu alama da ido, nan danan suka futo gaba dayansu sukabi bayan Daddy Su Daddy kuwa saida sukaje bakin get sannan Alhaji Baqir yasaki hannunsa yace "Alhaji kayi hakuri, nasan yanda kake ji acikin ranka, kayi hakuri" ya qarasa maganar yana bubbuga kafadarsa Su Usman ne suka qaraso, Aliyu yajashi hannun Daddy yace "Daddy Muje ciki" Alhaji Baqir yawuce part dinsa jiki a sanyaye Suma sukaja hannun Daddy suka tafi, mutane baqi anata hidima, dasuka shigo kowa sai gaida su yake amma su Usman ne masu amsawa, suna shiga dakin Daddy gaba dayansu suka zauna Babu me magana acikinsu, farouq yafuto daga dakin yayi wajan Momy Yana zuwa yakama hannun yace "Momy zokiji" Kallansa tayi tace "jarababbe, farouq Dan Allah kabarni nahuta yau ana bikinma bazaka rabu Dani kaima kaje wajan mutanan ku ba" Yace "Momy kitaho please" Fuskarsa ta kalla taga Babu wani wasa ko Fara'ah, mamaki ya kamata, Dan haka kai tsaye tabishi zuwa dakin Daddy Kujera ta nema tazauna, tace "yanaganku haka jiki a sanyaye? Meyake faruwa ne?" Daddy yayi shiru har lokacin Bece komai ba, Aliyu ne yafara magana "Momy Wallahi fa ansamu matsala, anfasa auren Nihla da Abba" Cikin mamaki tace "me kace Aliyu?" Usman yace "hakane Momy, baba Ibrahim yazo yadauketa, suntafi" Adede lokacin Abba yashigo dakin, yanemi waje Yazauna, duk Babu Wanda ya kulashi Momy ta kalli Daddy tace "to Alhaji meyasa zakayi shiru? Yanzu de ka kirashi kafada masa Dan Allah ni yadawo min da yarinya" 🤣 Ajiyar zuciya Daddy yayi, sai a lokacin yayi magana "Ibrahim ya nunamin yafini iko akan Nihla ne, yanda na nuna masa iko da farko, shine yazo har gida ya nunamin yafini iko akanta" Tace "mekake nufi Alhaji, bangane maganganun ka ba" Yace "Rahma bayan rasuwar Aisha nashiga tashin hankalin da ban taba fuskantaba, Nihla kadai Zan gani naji dadi, ita kadai Zan gani yarinyar inji Kamar Aisha tace akusa Dani, hakan yasa lokacin dazamu dawo gida kai tsaye nace ku fito mutafi, saboda ina tsoron inyiwa Mai hakuri magana yace bazai ban itaba, nasan shima yaji mutuwar Aysha, Awannan lokacin bazai taba yarda yarabu da 'yarsa ba, nikuma Rahma bazan iya tahowa nabar jinin Aisha Awannan wajan ba, shiyasa nadauko ta muka Taho batare da iznin mahaifin ta ba " Momy tace "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un," Dukda taji gaskiyar magana a bakinsu, wani bangaren na zuciyarta bai yardaba, wayarta tadauka takira layin Nihla, Adayan bangaren wayar tana hannun Dida tana ganin sunan Anty

Chapter 6 of 24