time zaki ganni verry soon"
"to shikkenan ya Yusif thnks"
Yace "yr wlcm"
Daga nan sukai sallama.
Momy ce taturo dakin tashigo, cikin murna Nihla tanuna mata abinda Yusif din ya aiko mata dashi
Murmushi Momy tayi, tazauna abakin gadon, saide wannan ne karon farko da taji tausayin Abba aranta, saboda yanda taga Nihla tana farin-ciki akan kyautar da saurayinta yayi mata, saide Babu yanda zatayi, dole sai Abba yagane laifin dayayi abaya, bazata biyewa son zuciya dason datake wa danta ba
cikin nutsuwa tace "nagani Nihla, Yusif yayi kokari sosai, amma dafatan de dashi za'ayi ko 'yar Momy?"
Ahankali tadagawa Momy kai cikin kunya
Momy tayi Murmushi "to shikkenan, idan kunyi waya dashi kifada masa momynki tana gaishe shi, sannan kifuto muci abinci, goma saura yanzu"
Ahankali tace "to Momy"
Falon suka futo itada Momy, yana zaune shi kadai a dining yana daddanna waya, tunani yake aransa meyasa har yanzu Nihla bata sakewa dashi tayi masa magana Kamar da? Bayan kuma tasan cewa shi bawata magana yakeba dama can
Yayi tunanin dazu da farouq yace pictures dinta suna wayarsa zatace yatura mata, amma sai yaji tayi shiru, yarasa me zaiyi mata tadinga sakewa dashi suna magana Kamar da
Zuwansu wajan ne yakatse masa tunanin dayake, Nihla ta kalleshi yana sanye da jallabiya fara qal wadda ta karbi jikinsa, sumar kansa ta kwanta luf tana sheqi gwanin sha'awa, hankalin sa yanakan waya
Zama sukai, Momy tace "Nihla zuba mana Abincin"
Tashi tayi tafara zuba musu, ahankali ya ajiye wayarsa yazuba mata ido yana Kallanta, rigar jikinnata tayi mata kyau,wadda ta kasance marar hannu,kyakykyawar fatarta ya kalla tayi luwai luwai da'alama zatayi laushi
Momy ta kalleshi taga ya zubawa Nihla ido, duk abinda take akan idonsa, tunani tafara to kode Abba ya Manta tana wajan ne yakebin 'yarta da wannan mayen kallon? 🤔
ahankali ta dauke kanta
Nihla tazuba wa kowa sannan tazauna kowa yafara cin Abincin
Suna tsaka dacin Abincin yadubeta yace "please inason Tea"
Dago daradaran idanunta tayi ta kalleshi batare da tace komai ba tatashi ta janyo flaks din dake gabansa tadauki cup tazuba suger kadan sannan tasaka madara
Momy ta kalleta, gaskiya ne Nihla ta karanci Abba tas, Inda wanine zai hada masa Tea dinnan da tuni yayi magana yace kar asaka suger dayawa, amma ita ko magana baiyi mata ba saboda yasan tasani
Ruwan zafin tafara tsiyayowa by mistek hannunta yazame Ruwan zafin yazubo ahannunta
Flask din ta ajiye dasauri tace "auch..." tafara yarfe hannunta tana runtse idonta
Spoon din hannunsa yasaki yatashi dasauri ya nufeta, yanda take girgiza hannun ne yasa qirjinta suke rawa Wanda batasaka musu ko 'yar breziya ba, numfashin sane yafara kokarin daukewa, badan tana cikin jin azabar zafi ba da Babu abinda zai hanata ganoshi, jiyake Kamar ya fuzgota jikinsa
Ahankali yadora hannunsa akan nata yariqe hannun data qone din, gaba daya damuwa ta baiyana a fuskarsa, hannun yakai bakinsa yafara hura mata iska awajan,runtse idonta tayi yace "wayyo Momy hannu na"
Kallanta yayi yaga idonta yacika da qwallah, yace "Sannu, kidena kuka"
Hannun yakalla dogayen yatsunta masu kyau sunyi jajir, yasake hura mata iska awajan
Cikin shagwaba tace "wash!"
Dago kansa yayi yazuba mata manyan idonsa, rakinta yana birgeshi, haka yatsira mata ido yana Kallanta ga hannunta yariqe cikin nasa
Momy tadena cin Abincin ta tsaya tana kallan ikon Allah 😱, kode sun Manta tana wajan ne? Lalle wannan Inda ace Nihla tana sonsa Kamar yanda yake sonta a yanzu, Toda Babu abinda zai hana su hanata zaman gidan mijinta, irin wannan rashin kunya a gabanta har ina!🤦🏻♀️Ita Nihla yanda take shagwabar saika rantse da Allah da niyya takeyi, shikuma gaba daya ya susuce akanta yasakata agaba Kamar zai maida ta cikin jikinsa
Gyaran murya tayi, Abba yajuyo ya kalleta batare daya cika hannun Nihlan ba, itama sai a lokacin tabude idonta ta kalli Momy
Momy tace "jeki saka qanqara akan hannun, zakiji yadena zafi, Allah yasawaqe"
Cikin sauri yace "bari a dauko"
Yasake kallan Nihla yace "Sannu" sannan yasaki hannun nata yawuce kitchen batare daya jira ta amsa masaba
Tausayinsa yad'an kama Momy yanda taga gaba daya ya rikice, to idan yaji akwai wanda Nihla take tare dashi yaya zaiyi kenan?
Tana tsaye sai turo baki take gaba yadauko qanqarar yadora mata ahannun sannan ta danji dama dama
Suka zauna kowa yayi shiru, Momy tadubeshi, taga ko kallan Tea din beyiba, magana tafara aranta, yasa yarinya tahada masa abu, a dalilin haka ta qone amma baima kula Tea dinba, tace "Abba kasha Tea din mana"
Bece da'ita komai ba, kawai de ya girgiza kansa 🤣
Ajiyar zuciya tayi tace "nikam na qoshi, saida safen ku,"
Ta kalli Nihla tace "idan hannun be daina zafi ba koda cikin dare ne kizo ki fadamin saina tasoshi yakaiki asibiti"
Abba yayi Dan qaramin murmushi saboda yasan sarai dashi take
Wajan yarage saisu biyu kawai,kowa yayi shiru Babu me magana, ta dago ta kalleshi ta kawar da kanta, shikam, zuba mata idanu yayi, wani irin dadi yakeji cikin ransa, besan cewa ya takura taba, dazai matsa da tafi cin Abincin yanda ya kamata, tunda shi baci zaiyi ba
Bata tsammata ba taji yace "kek yayi dadi"
Ahankali batare data kalleshi ba tace "thank you"
Daga nan tayi shiru, tana tunanin maganar Momy da tace idan yadawo tayi masa godia akan motar daya bata, tarasa tayaya zata gode masa, kwata kwata ma batasan tuno da maganar motar, saboda wannan takardar daya hado mata da'ita tarasa gane Inda yadosa, shi ya Yusif dasuke soyaiya tayi masa godia yanda ya kamata amma shifa ya Abba?
Ahankali tadago kanta ta kalleshi, karaf idonsu yahadu, tayi saurin janye nata idon tace "nima... Nagode sosai"
Murmushin yayi, zaiso ace taci gaba da magana saboda yana jin dadin yanda Dan qaramin lips dinta suke motsawa dan haka yace "for what?"
Kai tsaye tace "motar daka turomin"
Memakon yayi mata maganar motar saiya jefo mata tambaya "Can you drive?"
Tace " i can't, but yaya farouq saiya koyamin"
Shiru yayi na Tsawon mintuna, farouq, farouq, karfa tasa yafara kishi da yan'uwansa, ya kalleta yace"dole sai shi?"
Amnah El Yaqoub ✍️
[7/7, 11:07 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Like my page On facebook 👇
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
43&44
Kanta tsaye tace "ehmana"
Fuskarsa ta nuna alamun damuwa yace "no, kibarshi, zan koya miki"
Kallansa tayi, lalle ya Abba yasakko, ahankali tace "nagode, amma kabarshi"
Tsam ta miqe daga wajan, Dan taga alamun zancen yakeso, kawai yazo yasa ta agaba, hanyar dakinta tanufa batare data qara masa magana ba, shima binta yayi da kallo, saida yaga tashige dakinta sannan yasaki ajiyar zuciya
Shima dakinsa yatafi ya kwanta, tunani yafara akan tayaya zai shawo kanta? Har tausayin kansa yakeji wani lokacin, tana bashi irin wannan amsar tayaya zaiji qwarin gwiwar fada mata abinda yake ransa?
Har qarfe biyu da rabi yakasa bacci yana tunanin ta, yaji haushin kansa yafi a qirga, Inda ya amince da'ita Tun farko daduk haka bata faruba, ganin tunanin Babu Inda zai kaishi yasa yatashi yanufi toilet yadauro alwala yazo yafara fadawa Allah kukansa
Bayan ya idar ya kashe wutar dakin ya kwanta, bai taba barin wayarsa akunne ba idan zaiyi bacci, koda yaushe kashe ta yake idan zai kwanta, amma yau akunne yabarta, rigar jikinsa yazare dagashi sai boxer yaja fillo ya rungume a qirjinsa sannan yadau wayarsa yana kallan pictures dinta, ahaka bacci ya daukeshi.
Dadewar dayayi beyi bacci bane yasa daya koma bacci bayan sallar asuba, yajima yanayi, bai tashi ba sai wajan shadaya
Wanka yayi yafuto domin ya gaida Momy,ganin su yayi gaba dayansu zaune afalo,ga Daddy ga Momy ga kuma Nihla agefen Daddy tana sanye da Jan leshi Wanda akayi mata dinkin riga da siket amma wuyan rigar irin budaddan nan ne da'ake yi yanzu
Cikin murna ya qaraso Yazauna ya gaida Daddy da Momy
Itama Nihla fuskarta Babu yabo Babu fallasa ta gaida shi ya amsa cikeda kulawa
Daddy yace "Tun karfe takwas nadawo momyn ku tace baka tashiba"
"eh Daddy, ban kwanta da wuri bane shiyasa"
"to Alhmdlh, kuma bana nan sai qanwar ka tazo service harma kasiya mata Mota"
Shiru yayi Bece komai ba
Daddy yace "to Allah yasaka da alkhaairi, Allah yabar zumunci" 🤣
Ahankali yace "Amin"
Tashi Daddy yayi yakalli Momy yace "idan yagama break fast ki turomin shi"
Momy tace "to Alhaji"
Bayan yagama cin Abincin kuwa Momy ta turashi dakin Daddy, sannan itama tabi bayansa, Nihla kuwa kwanciya tayi tana daukan remote
Zaune yake agabansu kansa aqasa, yarasa dalilin wannan kira, Daddy yadubeshi yace "Abubakar Momynka ta sanar Dani rashin lafiyar dakayi kwanaki harma da abinda likita yace"
Abba najin haka cikin ransa yace Innalillah.., yayi shiru Kamar ruwa ya cinye shi
Daddy yaci gaba da fadin "nadade inama kallan marar lafiya ashe ba haka bane kalau kake tunda gashi har kana rashin lafiya akan haka, ina ita yarinyar dakace kanaso din take, inane gidansu sai Muje ayi magana guda daya, ka dade da sanar damu cewa kana sonta, amma maganar aure kayi shiru"
Shiru Abba yayi, idonsa yayi jajir, ga kunyar iyayen nasa dayakeji Ahankali yace "Daddy tayi aure"
Cikin sauri iyayen suka kalleshi, Daddy "to shikkenan Allah yakiyaye gaba, sai kayi kokari kasamo wata ka aura, bazai iyu kaci gaba da zama da rashin lafiya ba"
Jinjina kansa yayi yace "insha Allah Daddy"
"zaka iya tafiya"
Ahankali yatashi yafuto daga dakin, ta gabanta yazo yawuce yashige dakinsa, itade Nihla taga shigar sa daki Kamar yana cikin damuwa, tabe baki tayi taci gaba da kallonta
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Bayan sati daya tana kwance tana bacci da weekend kasancewar bazata ko'inaba
Wayarta ce tahau ruri cikin magagin bacci takai hannu tadauki wayar cikin sexy voice tace "Hello"
"Baby na kina bacci kenan"
Tace "Um"
Murmushi yayi "to albishirinki"
"goro ya Yusif"
"yau ina kan hanyar zuwa naganki, aide adress din dakika taba turomin kina nan ko?"
Bude idonta tayi "ya Yusif da gaske kake zakazo?"
"Yes, yau zanzo insha Allah, yanzu hakama wanka zanyi nabiyo jirgin dazai tashi 12"
"wayyo ya yusif, mekakeso na shirya ma?"
"Karki wahalar min da kanki, kiyi zaman ki kawai"
Murmushi tayi, amma Babu yanda za'ai zaizo takasa shirya masa wani abu
Daga nasa bangaren yace "me kikeso nataho miki dashi?"
"mamy ya Yusif, ita nakeso, nayi missing dinta"
Murmushi yayi yace "tunda zaki ganni ai Kamar zaki ganta ne"
"to shikkenan ya Yusif sai kazo"
Tashi tayi taje ta sanar da Momy, nan da nan kuwa Momy ta aiki Adala kasuwa tasiyo musu abubuwan buqata, Adala tana dawowa suka hau aiki itada Nihla,ko sau daya bataga Abba yafuto ba, may be baya gidan ne, aikin sukaci gaba dayi lokaci daya gida yadauki qamshin hadadden girki
Saida Nihla taga komai yayi normal sannan taje tashiga wanka
Karfe biyu saura yakirata yace yana bakin get
Kwalliyar datayi ta doguwar riga ta atamfa ya karbi jikinta, tayi mutuqar kyau sosai
Da kanta tafuto taje ta taryoshi daga bakin get,ta karbi key din motarsa tabawa Direban gidan tace yashigo masa da ita
Yusif sai Kallanta yake, kwalliyar tata tayi bala'in tafiya da imaninsa, ahankali suke ta kowa gwanin sha'awa har suka qaraso part din Momy, Nihla sai Fara'ah take, a falon suka zauna Momy tafuto suka gaisa, tayaba da Yusif din Babu laifi, cikin sakin fuska tace "yaka baro mutanan Abuja" yace "Alhamdulillah, suna lafiya wallahi"
"aaa masha Allah, ai kullum muna jin labarinka awajan Nihla"
Yusif yayi Murmushi cikin ransa yana yabon matar
Tashi tayi tace "bari akawo maka Dan ruwa, Alhaji yafita aida kun gaisa dashi "
tatafi tasa Adala takawo masa kayan motsa baki dakuma Abincin da aka shirya masa
Kallanta yayi yace "wannan ce Momy ko?"
"itace ya Yusif"
"tanada kirki gaskiya, idan naje gida saina fadawa baba cewa kina nan kalau wani kyau ma kike qarawa"
Murmushi tayi masa, tatashi tazuba masa Abincin, yafaraci, Dan kadan yaci yace ya'isa
Yakalleta yace "Nihla gaskiya bazan boye miki ba ina qaunar ki, kuma naji dadin yanda naganki hankalin ki kwance, fatana mu kasance inuwa daya amatsayin Ma'aurata nanda Dan wani lokaci qanqani"
Kallansa tayi "ina fatan hakan ya Yusif"
Fira sukaci gaba dayi har yamma tayi, yatashi yayi sallah suka dawo falon suka zauna, wayarta ce tayi ringing, cikin zolaya tace "bakada kirki yaron nan"
Daga daya bangaren akace "ninema yaron, gaskiya kin cuceni, koke aka kawomin yanzu tsaf Zan riqeki"
Dariya tayi "lalle ma Abdallah, aikuwa baza'a kawo makaba, yakake yagida, ya service"
"gida lafiya Nihla, dama nashigo kano ne shine zanzo mugaisa saina wuce"
"Ok to shikkenan abdallah saikazo, zan turoma adress din gidan yanzu"
Wayar ta katse ta kalli Yusif "ya Yusif abdallah ne yakirani, wai zaizo mugaisa"
Yace "Ok Abdallah qanin Nadiya qawarki"
"eh shi"
Yace "to saiyazo, ina pictures din birthday din naki baki turomin ba, nunamin nagani" 🙆🏻♀️
Hankalinta kwance tabashi wayarta tace "gashinan suna cika duba kagani"
Bude wayar yayi yashiga gallery anan yaga pictures din, lokaci daya yanayin fuskarsa ya sauya yace "ashe bake kadai kikai ba"
Jikinta ne yayi sanyi "eh nida ya Abba ne"
Tabe baki yayi yabata wayarta, sannan yatashi yace "toni Zan tafi"
Shagwaba tafara masa "haba ya Yusif, ya za'ai katafi Tun yanzu, karfe hudu nefa"
Jiyayi ta birgeshi, yace "karfe hudu nakeso nabi jirgi nakoma, bakina tareda wani masoyin nakiba, menene zaki damu?"
"saboda ina sonka, kuma kai zuciyata ta'aminda dashi shiyasa nabaka dama ka gabatar da soyaiyar mu awajan mahaifina"
Yaji dadin maganar ta, kuma ya gamsu sosai, danhaka shima ya lallabata yace bayason yayi missing flight ne, daqyar ta yarda, takira masa Momy sukai sallama sannan suka futo harabar gidan tare domin tayi masa rakiya
Awajan motarsa suka tsaya suka jingina da motar, sai kallan soyaiya suke sakarwa junansu, yabude bayan motar yabata wata leda cikeda coculate, ta karba tayi masa godia, yace "to Zan tafi, mezaki fadamin Wanda Zan dinga tunawa ina jin dadi"
Murmushi tasakar masa har dimple dinta suka futowa sosai, adede lokacin maigadi yabude wa Abba get yashigo ciki
Dasu yafara tozali, lokaci daya gabansa yayi mugun faduwa, jikinsa har rawa yake yana neman yakasa driving din, hakan yasa yafaka motar tasa a'inda bai kamata ba, waye wannan yake tareda Nihla? Wanne dan'iskanne yazo yasakata agaba ita kuma sai wani murmushi take masa?
Cikin sauri yabude motar yafuto, fuskarsa adaure, Dafarko yayi niyyar zuwa wajansu, amma saiyayi hakuri yarabu dasu yazo yawuce su ko kallan Yusif din baiyi ba
Yusif ya kalleta da mamaki "waye wannan?"
Tabe baki tayi sannan tace "ya Abba"
Nan take shima bacin rai ya wanzu a fuskarsa 🙆🏻♀️
Falon yashigo anan yaga kayaiyakin da'aka ajiye da alama wannan gayen aka sauka dasu, zama yayi akan kujera yadafe kansa🤦🏻♂️, lokaci daya idonsa yayi jajir, to zaman mema zaiyi anan? Meyasa zai zauna yanacin Baqin ciki ita kuma tanacan tareda wani? Lokaci daya wani irin kishi ya rufe masa ido, glass cup din da'aka kawowa Yusif domin shan lemo yasa qafa yayi ball dashi, lokaci daya cup din yahadu da bangon falon ya tarwatse awajan, cikin bacin rai yafuto daga falon yanufi wajan Nihla da Yusif
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Cikin kuka tace "mum wallahi Tun safe nakejin qaiqayin, Tun yanayi Dan kadan yadawo yanayi dayawa, idan nasosa ma sakeji nake"
Hajiya Farida tace "Dida, to kiyi shiru kidena kuka mana, ba komai gane sanyi ne yake damunki, kuma muddin kina dashi to shima Fawaz din zai iya samu, kina amfani da Ruwan zanyi ne?"
Tace "eh mum inayi"
Hajiya Farida tace"to ai kinji, Dida Tun kuna gida nake muku magana akan Ruwan sanyin nan, kidena tsarki da Ruwan sanyi, sannan idan kina period kwata kwata kidena shan Ruwan sanyin ma bare kiyi tsarki dashi ko wanka, kiyi shiru zansa akawo miki magani yanzu, shima Fawaz din saiki bashi yadinga sha "
Tashare hawayen ta tace" to mum, mungode "
Yana zaune agefenta yayi tagumi, yace" to yanzu kinsa itama hankalinta zai tashi, bayan nace Karki fada mata kinqi ji, tunda safe fa nakira ummah nima nafada mata, kuma tacemin zata kawo miki magani da kanta "
Zaro ido Dida tayi," nashiga uku ya Fawaz meyasa zaka fada mata, aida kunya "
Yace" keni bawata kunya, meyasa Dan muna cikin damuwa zamu kasa sanar da iyayen mu, sunefa suka haifemu Dida "
Shiru tayi masa tafara matse cinyoyinta, ya kalleta yace" qaiqayin kikeji ne? "
Ta daga masa kanta, ahankali yatashi yadawo gabanta ya tsugunna sannan yasaka hannu yadaga yar qaramar rigar dake jikinta bejira komai ba yatura hannunsa ciki 🙈
Cikin nutsuwa yafara sosa nata wajan yana Kallanta, yanayin sa ne yafara sauyawa cikin shaqaqqiyar murya yace "yana raguwa qaiqayin?"
Idanunta a lumshe tadaga masa kai, yasaka hannu yasake bude kafarta yaci gaba da sosa mata,daga susa sai aka zarce abinda yafi yafi susa, gaba dayansu sunyi shiru kowa da abinda yakeji
Sallamar da sukaji ana doka wa ne yasa suka dawo hayyacinsu, ahankali yatashi duk hankalinsa yatashi, yace "ga ummah nan," sannan yashige cikin daki
Hajiya Abida Maman Fawaz tashigo falon tace "Sannu Dida, ke kadai ce agidan ne?"
Cikin kunya tace "a a umma ya Fawaz din yana daki"
Zama tayi akan kujera ta cire mayafin ta tashiga kitchen din didan da kanta, tafuto da wani itace daga leda ta wanke shi sannan tasaka tafarnuwa aciki tazuba a tukunya tadafa mata shi
Saida ya dahu ta debo a cup takawo mata tace "karbi wannan kisha"
Adede lokacin Fawaz yafuto daga daki bayan yagama dedeta kansa 🤣
Hajiya Abida tace "Sassaqen Zogale ne wannan, shi zaku dinga sha dagake har shi, ga sauran can a kitchen nabar muku, kudinga sha kuna tsarki dashi, ina tabbatar miki koda sanyi Hajiya Farida ta haifeki to insha Allah saiya barki" 🤣
Dida da Fawaz sukai murmushi gaba dayansu, sannan hajiya Abida tayi musu sallama tatafi
(Yar'uwa kisamu Sassaqen Zogale, ina nufin jijiyar Zogale, za'a saro miki shi daga jikin bishiyar Zogalen, saiki qara daddatsa shi yayi Dan dede misali kisa shi a tukunya kidafa da tafarnuwa, kokuma kidafa da jar kanwa, idan ya dahu saiki dinga sha safe, rana, dare, daga lokacin zakiyi hannun riga keda cutar sanyi, Allah yasa anfahimta 🙏🏻)
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Hannunsa zube cikin aljihun wandonsa jeans Mai launin fari yaqaraso wajansu fuska daure, kana kallansa zaka hango tsananin kishi afuskar sa
Kallan Yusif yayi yace "Sannu ko"
Ya Yusif shima da kishi Yarufe masa ido yace "Sannu fa"
Kallan Nihla yayi "ina jiranki kizo Muje ki hada min abinci"
Kallan mamaki tabishi dashi, da'ita ce take hada masa abinci? Tace "abinci kuma?"
"eh abinci, kokuma da kaina zanje nahada? Bayan kinsan ban'iyaba?"
Tace "Abincin...." cikin sauri ya Yusif ya tare ta, ta hanyar daga mata hannu
Ya kalleshi yace "Abba ko?"
Fuskarsa Babu alamun wasa yace "Yeah"
Ya Yusif yace "kanata kishi kana bacin rai saboda kawai muna tare, to bakaga tana tareda mijin da zata aura bane?"
Haushi yaqara kama Abba, baice masa komai ba yakalli Nihla yace "banda lokacin batawa anan, zaki wuce mutafi kokuma saina daukeki nashiga dake?" 🙆🏻♀️
Cikin fishi Yusif yace "karka kuskura kafara tabamin mata, idan tana yarinya ka tureta narabu dakai to yanzu ko Dan yatsanta ka taba ranmu ne zai baci gaba daya"
(Lol dama kunsa ba 🤪)
Abba ya kalleshi, sai yanzu yagane komai, sai yanzu yagane shine meyi masa shishshigi akan qanwarsa Tun tana qarama, kuma shine silar dayasa yayi fishi da'ita kafin subaro qauyen na jigawa, meyasa har zuwa yanzu yake masa katsalandan acikin rayuwarsa ne? 🤦🏻♂️
Cikin fishi yakai Hannu zai fuzgota shima Yusif cikin sauri yasa hannu zai tareta, Nihla tana ganin ikon Allah tace "nashiga uku, ya Yusif Dan Allah kayi hakuri karabu dashi banaso kokadan ranka yabaci akansa, Muje kada kayi missing fligh"
Yusif yace "shikkenan my dear, idan nasauka Zan gaida su baba"
Abba jin tace Yusif yasake kallan gayen, ashe shi nede yake kiranta awaya, kuma shine Wanda ya aiko mata da gift daga Abuja, damuwa tataru tayi masa yawa
Adede wannan lokacin shima yaqaraso wajansu, Tun daga nesa ya gansu a tsaye cirko cirko da alama ba kalau ba, yana zuwa kuwa yayi musu sallama, Nihla da Yusif suka saki ransu, shikuwa Abba mamaki yake meya kawo Abdallah gidansu? "
Fuskantarsa yayi yace" kai meya kawoka gidannan? Mekazoyi? Mayaudaran banza Mayaudaran wofi, kafice kabar gidannan yanzu yanzu "
Nihla tarasa yanda zatayi, tace" Abdallah Dan Allah kayi hakuri "
Abdallah yace " Babu komai Nihla, sai munyi waya "
Yayiwa Yusif sallama ya juya yatafi ransa fal da tunani me yakawo Nihla gidansu ya Abba saurayin Anty Nadiya? Dama Ta sanshi ne?
Shima Yusif yayi mata sallama yatafi, Abba kuwa Be qara cemasa komai ba saima hanya daya nuna masa
Nihla ta kalleshi," haba ya Abba, meyasa kake min hakane? Sainayi baqi zakazo ka tozartani agabansu, me kake nufi danine? "
bata jira amsarsa ba tawuce tayi part dinsu cikin fishi
Wato duk abinda yake Tsawon wannan lokacin batasan ma meyake nufi ba, tunda gashi tana tambaya meyake nufi da'ita, bin bayanta yayi yace "dakata"
Tayi banza ta qyaleshi taci gaba da tafiya
"ki dakata nace"
Nanma tayi shiru ta qyaleshi harta qarasa cikin falon, sannan Tajuyo ta kalleshi cikin fishi, bacin raine yasa batasan lokacin data daga muryarta ba, takalleshi tace " inajin ka"
Momy tana daki Tun dazu tana sallah taji Kamar qaran fashewar kwalba, kuma data idar ma bata futo ba, tazauna tana lazimi, yanzu kuma tafara jiyo murya sama sama Kamar ana fada, ahankali tatashi tace "toba lafiya ba duk yanda akayi"
Hijabin jikinta ta cire tafuto daga dakin, turus tayi ta tsaya abakin kofar dakinta ganin Abba da Nihla a tsakiyar falon kowa ransa abace, gaba dayansu Babu Wanda ya lura da ita bacin rai Yarufe musu ido, itama kuma ta zuba musu ido tana kallansu daga nan kofar dakin nata, me wannan yaran sukeso su zama ne? Karfa wannan halin nasu yaci gaba da tafiya harkan yaransu, yanzun menene yake faruwa me yahada su?
Cikina fishi yakama hannun ta yariqe yace "dan me zaki dinga kawo maza barkatai kina saurarensu, kinje kin tsaya musu agaba kina bude baki kina musu dariya, sannan ina kiranki kinyi banza kin share ni kintafi kinbarni"
Hannunta ta fizge tace "dan Allah dakata ya Abba, dan me zaka shiga cikin rayuwa ta kanemi katakuramin, meyasa kai akoda yau...." maganar tace ta tsaya cak, sakamakon hade bakinsu dayayi waje daya 🙆🏻♀️
Momy dake kofar dakinta a tsaye tayi sauri ta runtse idonta
Lips dinta na qasa yakama yanasha Kamar yasamu sweet, laushin da lips dinnata yake da shine yasa ya lumshe idonsa
Gabanta yayanke yafadi, dukansa tafarayi tana kokarin fizge bakinta, amma saiyasa duka hannunsa biyu ya tallafe kanta dasu, gaba daya yanayin sa ya sauya jinsa awani irin yanayi dabai taba tsintar kansa aciki ba
Zuwa wannan lokacin hawaye yagama wankewa Nihla fuska
Saida yayi kissing dinta sosai sannan yazare bakinsa daga cikin nata, yakama hannayenta yariqe cikin nasa sannan yazuba gwiwar sa aqasa, yadaga kansa yana Kallanta yace "i love you NIHLA, ina qaunar ki sosai, please kiyafemin abinda na aikata miki abaya, Dan Allah na roqeki kiyafemin, kidena kula wasu mazan Dan Allah, sosai zuciyata tanamin zafi akan hakan, bazan juri ganinki tareda kowa ba, da gaske zuciyata zata iya samun matsala" yayi shiru yana Kallanta, hawaye kuwa wani nabin wani akan fuskarta
Fuskarsa yadora akan hannayenta dayake cikin nasa hannun yayi shiru, lokaci daya Nihla taji ruwa yana sauka akan hannunta, hakan ya tabbatar mata da cewa kuka yake
Momy dake kallansu lokaci daya taji qwallah tacika idonta ganin yanda Nihla take kuka shima ya tsugunna a gabanta yana mata kuka
Dago kansa yayi ya kalleta idonsa yayi jajir, ganin taqiyin magana yasa Ahankali yatashi tsaye, har lokacin kuma hannunta yana cikin nasa
Dora hannun nata yayi akan qirjinsa yace "zaki iya Rayuwar aure dawani batare daniba?"
Hannunta ta qwace daga kan qirjinsa, ta kalli idonsa tace "ya Abba, wacce irin magana kake min haka? Kasan abinda kake fada kuwa? Saboda banda gata ne yasa zaka nemi kayi wasa da rayuwa ta? Alokacin dana soka nunamin kayi baka qaunata, baka duba maraicin mahaifiyata danake tare dashiba Alokacin haka kace baka qaunata cikin bainar jama'ah, mutanan dakake cewa narabu dasu sune suka soni, suka qaunaceni Alokacin da dan'uwana ya nuna baya qaunata"
Hawaye yacika idonta, bata damu data goge ba taci gaba da cewa "Inda ace mahaifiyata tana raye, bazata taba bari hakan tafaru daniba, Tun banda wayo nasan cewa Diddi tasoka ya Abba, amma kai kaqi abinda tahaifa kaso Nadiya, to idan baka saniba Anty Nadiya itace tanusar dani nasan menene rayuwa, ta nunamin maisona da maqiyina, amma yau dan'uwanta yazo wajena kaci masa mutunci, da kaqini, sai yanzu da hankalina ya karkata wajan wani sannan zakace kana sona? ta yaya? Impossible! "
Tasa hannu tashare hawayen idonta sannan tawuce tabarshi awajan
Zuwa wannan lokacin kam Momy ma sun sata kuka, hawaye yacika fuskarta
Shikuwa Abba kansa ne yayi mugun sarawa,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 24