kadai
Daga qarshe saiya kira Daddy yafada masa, a lokacin Daddy yasa Alhaji Basiru yatura masa number Aisha
Aslam na ganin number nan take yakirata, amma yakira yakai sau hudu bata daga wayar ba, haka yasake kiran Daddy ya sanar masa, daga qarshe de sai Daddy ne yayi masa kwatancen gidan da kansa, shikuma yahau taxi suka tafi, daqyar ma me taxi din yagane abinda Aslam din yake nufi, saboda shi Babu turanci, shikuma Aslam Babu yaran hindi 🤣
Sunyi tafiya Mai nisa sannan yasauke Aslam ya nuna masa bus din dazai shiga, zata kaishi har kofar gida
Dole saida dala yayi amfani wajan sallamar me taxi din, sannan yafara jiran zuwan bus
Yanayin garin yake kalla da dan hadari kadan, Kamar wasa kuwa aka fara yayyafi, mutane dasukasan kan garinsu kowa sai yake baza lema, Aslam kuwa sai kare ruwa yake da hannu amma abin ba riba🤣
Ruwan yafara jiqa masa kayansa saiga bus din tazo ta tsaya awajan, gani yayi mutane suna shiga, shima yace ai ko ba ita bace wallahi shiga zaiyi, sukaishi koma ina ne 🤣
Duk kujerun motar ma sun cika, sai wata yarinya datake zaune gefenta akwai kujera daya, kallo daya yayi mata yagane cewa Babbar arniyace, shigar ta kadai zaka kalla kagane hakan
Riga da wando ne a jikinta kayan ya kamata sosai, sannan gashinta awaje sai Dan qaramin mayafi data dora akai Wanda dashi da Babu duk daya
Itama kallansa tayi, taganshi a tsaye yariqe karfen Mota, kayan jikinsa sunyi masa kyau sosai, da yaren India tace masa yazo yazauna, taga ko Kallanta ma baiyiba alamun baima san dashi takeba
Dan haka tace "hi"
Sai lokacin ya juyo
Tace "please come and sit"
Kallanta yasakeyi ya yatsina fuska, "no, thank you" yafada mata haka yana yatsina fuska
Hankalinta ta maida kan window bata qarabi ta kansa ba
Wayarsa yaciro yaciro daga Aljihun jeans d'insa yakira Abba, Abba yana dauka Aslam yafara zuba "Abokina kasan me? Wallahi gara da Allah yasa baka biyoni ba, gani nan muna tafe awata bus tana tafiya yanda kasan hawainiya, ni a tsaye ma nake narasa wajan zama"
Abba yace "Kamar ya?"
"to gashinan de kowa yana zaune, babu kujera sai guda daya, ita kuma wata qatuwar arniyace azaune nake fadama 🙊, inani ina zama kusa da manyan arna😳
Shegiya harda cewa wai in zauna, d'an iska neni, ina zama zata liqemin daga nan kuma ta addabi rayuwata"
Murmushi Abba yayi, yasan halin Aslam sarai, "to kayi hakuri mana, insha Allah zakuje lafiya"
Wani uban birki aka taka, hakan yasa Aslam yayi gaba yasake dawowa baya, nan take yakashe wayar yasake riqe karfen 🤣
Mutum uku ne suka fita, kujerar datake gaban yarinyar Babu kowa, nan yakoma Yazauna, yarinyar tanata kallansa
Kafin su qarasa Inda zaije motar ta lalace, kowa yafuto, wasu suka fara tare Mota, wasu kuma suka tsaya, kiran sallah yaji anayi awani masallaci, Dan haka yaje wani dan case agefen su yasiyo ruwa, yadawo wajan motar ya tsugunna yafara daura alwala
Yarinyar tana tsaye a gefensa, duk tana kallansa, ajiyar zuciya tayi, tataka Ahankali ta qaraso wajansa cikin yaren hausa tace masa "bawan Allah Dan Allah idan kayi sauran ruwan inaso nima zanyi sallah, kudin hannuna baida yawa bazai isheniba"🤣
Shiruuu Aslam yayi Kamar an kwada masa sanda🙆🏻♀️
Kasa Dagowa yayi, bare yahada ido da ita 🤣
Tasake cemasa "dan Allah, kaji"
Sai a lokacin yadago kansa, cikin kuskurin kunya yace "yanzu ke, dama kinsan kina jin hausa kika barni inata zuba?"
Murmushi tayi batare datayi magana ba, Ruwan ya miqa mata yace "gashi inde ruwa ne, ai ruwa baya had'a fad'a, shi musulmi ai dan'uwan musulmi ne" 🤣
Hannunta ta meqo zata karbi gorar Ruwan idonsa yasauka akan wani abun hannunta irin Wanda yan gayu suke daurawa maza da mata, amma nata anrubuta mata MAZAWAJE da manyan harufa 😃
Fasa bata Ruwan yayi, ya tsaya yakalli fuskarta dakyau, aishi sai yanzu nema yaga yarinyar tanayi masa kama da Nihla sosai, saide tafi Nihla cika dakuma 'yar qiba, yayi ajiyar zuciya yace "ke fadamin, Yaya sunanki?"
Murmushi tayi tace "Aysha Basiru Abubakar Mazawaje" 🙆🏻♀️
Cikin ransa yace tabd'i, dara tasake cin gida kenan, yatsunsa biyar ya nuna mata yace "uwaki" 🤣
Yaci gaba da cewa "to a qasar nan qafata qafarki dake Zan koma Nigeria, Aslam ne Dan gidan Alhaji Baqir yayan babanki"
Cikin sauri tace "yaya Aslam, Innalillah..., ya akai nakasa ganeka?"
"aikokin ganeni, ko baki ganeniba, daga nan, babu Inda zan barki kije,wuce Muje muhau wata motar kikaini gidan"
"toka bari muyi sallah mana, bani Ruwan nayi alwala ni"
"da wannan shigar zakiyi sallah? Haba, haba, wannan kam baki isaba, ina wayarki ina kira baki dagaba?"
Jakar hannunta ta duba tace "kaganta acikin jaka, niban saniba"
Yace "yayi kyau, to wuce Muje gidan" 🤣
Daga nan tajuya sukayi bakin titi domin tare wata motar
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Kallanta yayi idonsa akan manyan qirjinta yace "gaskiya naji dadin rawar nan, gashi gayu sunzo dayawa, club din yacika sosai, Ina alfahri dake Diyana kin iya rawa ba qarya"
Murmushi tayi tace "najjashi kenan, ai mutum ya mori yarintarsa, yayi amfani da lokacin sa kafin yaqure masa, nan gaba idan natara yara ai bazanyi ba"
Yace "wannan gaskiya, toga kazar taki, nasan kinason kaza shiyasa nasiyo miki ita, zakiji dadin ta"
Yafadi haka yana miqa mata ledar kaza
Hannu tasa ta karba tace "to najjashi nagode, kaga dare yayi, sha d'aya saura, Zan shiga gida"
Idanunsa ya lumshe sannan yabude su, ahankali yadora hannunsa akan qirjinta, kafin ta farga yafara murzawa,😳🙆🏻♀️
Cikin kasalalliyar murya yace"to yanzu ya za'ai kenan? "
Da qarfi kuma cikin fishi ta bige hannunsa, bacin rai ya baiyana akan fuskarta qarara, ta kalleshi dakyau tace" najjashi bude min Mota nafita kafin na tsinka maka mari anan, anfada maka ni 'yar' iska ce? Saboda ina yawo club club bashi yake nuna jikina nake kaiwa ana amfani da niba, "
Runtse idonta tayi cikin tsananin bacin rai taci gaba da fadin " najjashi nace kabudemin kofa kafin inbude idona "
Dariyar yaqe yayi, yayi tunanin zai samu abinda yakeso awajan ta, yayi tunanin itadin yar hannu ce,koda yaushe yanaso ya gwada sa'arsa akan Diyana ko zai dace, amma abin ya faskara,
cikin borin kunya yace " dama fa gwadaki zanyi, 🤣
Kuma kinci Interview"
Cikin fishi tace "uwar Interview, nace kabudemin kofa," ta qarasa maganar cikin tsawa, babu musu yabude mata kofa, tawullo masa ledar kazar tafice daga cikin motar
Adede lokacin Adam yadawo daga wajan meeting din dasukai a Makaranta, qare mata kallo yayi tana sanye da riga da wando, duk shape dinta yafuto, babu wani namiji Mai cikakkiyar lafiya dazai ganta ya qyaleta
Yakalli Agogon motar yaga shadaya saura, yana Kallanta tashige cikin gidan, sannan najjashi yaja motar sa yabar kofar gidan, shima Adam din yayi horn megadi yabude masa, cikin ransa yana fadin Allah ya shirya, yarinya kam tagama lalace wa saide addu'ah 😭, Dan nasiha bazata karbuba adede wannan lokacin 🤣
Tana zuwa part dinsu taga Babu kowa afalon danhaka tashige cikin dakin su itada Dida, tana shiga ta gansu azaune dukansu, Ilham, Nihla, da Dida
Zama tayi akan gadon tana sakin tsaki, dukansu suka kalleta, Nihla tace "meyake faruwa ne Diyana?"
Cikin bacin rai tace "wallahi daga club nake, wani gaye ya ajiye ni abakin gate d'an iska jiyake nima irinsa ce shine yasa hannu yana tabamin nono"
Gaba dayansu suka hada baki suna fadin "Nono" 😳
Kallansu tayi, "to miye abin hada baki anan? Ku daga anbaku labari zaku nemi ku ta rawa mutum jama'ah"
Nihla tace "tab, ai abinne da nauyi, kema Diyana kidena wannan yawon, wannan shigar dakike duk bai kamata ba"
Ilham ma tace "ato shikuwa gaye ina ruwansa yaga abubuwa asarari ai dole ya gwada ko zai dace" 🤣
Dida tace "gara de ku fada mata ko zataji," sannan ta maida Kallanta ga yayar tata tace "gara ma wallahi, gaba kya sake fita" 🤣
Diyana de tayi shiru tana jinsu, amma tabbas yaukam najjashi ya nuna mata cewa ita yar'qaramar 'yar club ce
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Aslam yasamu tarba sosai daga wajan abokin daddy, cikin kwana biyun dayayi a qasar ya fahimci halin Aysha, tanada nutsuwa sosai da sosai, bako Mai ne yake qara birgeshi da yarinyar ba sai Kallanta, duk lokacin data daga ido ta kalleshi sai yaji wani abu ya soki zuciyarsa
Haka nan ya tsinci kansa dajin dadin kasancewar su tare da yarinyar, kwata-kwata ya Manta da maganar Daddy dayace kada su dauki lokaci Mai tsawo basu dawoba
Yau kuwa Tun safe Daddy ya kirashi yace sukamo hanya su Taho gida, Dan haka washe gari sukai shiri suka Taho shida ita
Acikin jirgi ma tana gefensa, sau uku tana kamashi yana Kallanta
Tace "yaya Aslam lafiya kuwa?"
"akwai abinda yake damuna qanwata"
Kokarin saka belt take saboda sanarwar da ake cewa jirgi zai tashi
"meyake faruwa?, meyake damunka?"
Yace "kece, kece damuwata Aysha, narasa yanda zanyi da soyaiyar ki"
Sakin belt din Hannunta tayi ta rufe fuskarta cikeda kunya 🙈
Dab da ita ya matso yadauki belt din zai saka mata, tanajin sa akusa da ita, Kamar zai maida ta jikinsa
Harya saka mata belt din bata bude fuskarta ba
"kibude fuskar ki mana"
Cikin kunya tabude fuskar tata
Hannunsa yadora akan nata yariqe yace "Aysha kimin alqawari duk rintsi bazaki rabu da niba"
Wani iri takeji yanda yakama mata hannu, danta taqaita maganar tace masa "insha Allah yaya Aslam, nayima alqawari"
Ajiyar zuciya yasauke, sannan yasaki hannunta yana jin farin ciki naqara ratsashi
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Tsaye suke a Airport, Fawaz, Adam da Abba
Suna jiran jirginsu Aslam ya sauka, Fawaz yace "guy's kunsan menene, ni arayuwata kwata kwata mata basa gabana wallahi, amma tunda nayi karo da'ita take nema ta addabi nan d'ina"
Yaqarasa maganar yana dora hannunsa asetin zuciyarsa
Da mamaki Abba da Adam suka kalleshi, Adam yace "Wacece?"
Ahankali yace "Nihla"
Dasauri Abba ya kalleshi, haka nan yaji haushin maganar Fawaz din, yayi shiru baice komai ba, Adam yace "Babu laifi tanada hankali, yarinyar akwai Face, duk family dinnan idan kana neman kyau kazo wajanta kagama Alhaji"
Fawaz yace"no ni bawai kyanta ne yajani ba, ina tunanin idan na aure ta bazata damu da halaiyataba, zata barni insha abinda raina yakeso "
Wannan karon Abba kasa hakuri yayi yadubi Fawaz din yace masa "Nihla?"
Hankali kwance Fawaz yace "yes"
Adam yace "nikam gaskiya idan Zabi za'a bani ko to Zan Zabi Dida, najima ina son yarinyar but narasa yanda Zan fuskanceta in fada mata, bazan iya zuwa wajanta da girmana ina qaramar murya akan tasoni ba, amma gaskiya sosai nake sonta, dama inka dauke Nihla da Dida da Aysha, tofa sauran biyun sai Ahankali, Ilham rashin kunya, Diyana kuwa Hmm karma kasata acikin lissafi, Dan rannan ma wani gaye nagani yasauketa amota "🤣
" dan Allah kundameni da maganar wannan yaran, ku yanzu ko kunya bakwaji kuzauna kuna cewa qannan bayan ku kukeso? Ahaifi yaran agabanku amma kudinga wannan maganar? "
Cewar Abba
Fawaz yadafa kafadarsa
" zamu ga yarinyar da zaka Aura Abba "
Suna wannan maganar su Aslam suka futo, shine yake riqe da jakar ayshan, Tana ganin Fawaz ta qarasa ta rungumeshi tace
" yaya Fawaz "
Cikin farin ciki yace " Sannu da zuwa qanwata, "
Su Adam ta gaisar, gaba daya sun sauya mata, in akan hanya ta gansu ba lalle taganesu ba, shima Fawaz din dan kullum suna gaisawa dasu ne ta cht
Hannun ta yaja yabude mata Mota ta shiga, Adam ma yashiga, shikuma Aslam zasu tafi shida Abba
Ta glass din motar ya leqo kansa yace "my dear shikkenan sai munyi waya ko?"
Kunya ta kama Aysha, shi yaya Aslam ko kunyar qaninsa Adam dayake wajan bayayi zai yi mata wannan maganar?
Ahankali ta daga kanta, Fawaz ya kalli Adam suka hada ido 🤣
Basu cemusu komai ba, sukaja motar suka tafi
Shima Aslam ya shige ta Abba suka tafi
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Bayan dawowar Aysha da kwana biyu Aslam yazo part din su Abba, suna zaune agefen gado da takardu agabansu suna tsara yanda zasu gina wani sabon kamfanin dasuke son budewa tare
Suna gama tattaunawa Aslam ya ajiye file din a gefensa yakalli Abba "Abokina gaskiya inason yarinyar nan, Aysha tagama tafiya da nutsuwa ta, zan jira agama wannan meeting din da Daddy yace za'ayi bayan angama Zan sanar dasu kawai ayi mana aure, inyaso saita dawo nan taci gaba da karatun ta tunda yanzu tafara"
Kallansa Abba yayi "Aslam kuna bani mamaki yanda kuka dage akan wannan qananun yaran"
"Abba karka renamin hankali, haka kakeso muyi ta zama ne? Ko kana tunanin muna germany bana sane da irin juyin dakake cikin dare kakasa bacci?" 🤣
"Malam ni bana wani juyi cikin dare"cewar Abba
"qarya kake Abba, to lemon tsamin danake gani cikin dozbin fa?ni bazan kashe kaina ba, aure nakeso kawai"
"to karka min kuka" inji Abba
Adede lokacin taturo kofar dakin tashigo, bakinta dauke da sallama, tana riqeda flet me dauke da meat pie
Kallansa tayi "ya Abba ga meat pie nayima,"
Agajarce yace mata "Ok"
Ta kalli Aslam tace "Barka da wannan lokaci ya Aslam"
Cikin sakin fuska yace"yawwa Nihla, mungode sosai "
Murmushi tayi tajuya tafice daga dakin
Aslam na ganin fitarta ya kalli Abba "Abokina yarinyar nanfa nagama lura tana sonka, irin yanda take kula dakai zaisa kowa yagane hakan"
Kallan Aslam yayi "wacce irin magana kake haka Aslam? Yaushe Nihla ta girma dahar zatasan wani soyaiya? She's 17 year's fa"
"to menene aciki?"
Hannu yadaga masa "no, no, dakata Aslam, kafi kowa sanin nafisan na Auri mace babba, wadda ta waye, me ilmi, ta mallaki duk abinda nakeso ajikin mace, sannan me hankali, amma Nihla renonta kawai zanyi, Aslam nasan kaina inada tsananin sha'awa, kuma ni kadai nasan yanda nakeji, wannan yarinyar zan'iya kakkaryata Tun a daren farko idan ma ta nuna kenan, bare ma yanzu dabata nunaba "
" dan Allah ka dakata Abba, wannan yarinyar fa qanwar ka ce, menene aciki idan ka aure ta? Meka dauki mace Abba? Kana maganar nuna ai kaine zaka maida ta hakan "
" dan Allah kadena min wannan maganar Aslam, nafadama bazan iyaba, nafisan mace me tarin ilmi, wadda tahada komai, amma Nihla amatsayin qanwata nake ganinta "
Aslam yace" nasan dalilin dayasa kake wannan maganar, kuma kasan hakan ba qaramin kuskure bane idan ka aikata shi, ba kuma ranka ne kadai zai baci ba harda namu baki daya, inaso ka tuna halin da Diddi ta shiga itada baba Basiru akan hakan "
Yana fadar haka yayi wulli da file din dasukai magana akansa yafice daga dakin cikin fishi
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
"wayyo Allah ummah cikina ciwo, zan mutu ummah, ummah Dan Allah kiyafemin, kicewa Abbanmu shima yayafemin"
Hajiya abida tashare hawayen idonta "Aysha kidena maganar mutuwa, ba zaki mutu ba, 'yata bazaki tafi kibarni ba"
Ilham idanunta sunyi jajir tace "Anty Aysha kiyi shiru Dan Allah, bazaki mutuba, zaki tashi mu rayu tare"
Hannun Ilham ta riqe tace"ilham kicewa yaya Aslam ina sonsa, bazan tashi ba Ilham ni nasan yanda nakeji, nadade ina wannan ciwon cikin, amma nayau dabanne ilham "
Alhaji Basiru ne yasa hannu da kansa yadauketa suka futo daga cikin motar suka shiga cikin asibitin dasuka qaraso
Likitoci ne suka karbi aysha, nan take suka shiga bata temakon gaggawa, Alhaji Basiru Yazauna awajan yayi tagumi
Daga baya yan gidan gaba dayansu suka qaraso asbitin, Aslam yafi kowa shiga tashin hankali, Daddy ya kalli Alhaji Basiru yace "wai dama batada lafiya ne?"
"wallahi yaya Abubakar kwana mukai bamuyi bacci ba, cikin ta yana ciwo, bayan wani dan lokaci saiya lafa, shine muka Taho Asbiti yanzu"
Alhaji Baqir yace "subhanallah, Allah yabata lafiya"
Gaba dayansu sukace amin, haka suka zauna jugum jugum, babu wanda yankewa dan'uwansa magana, har likitocin suka futo
Gaba dayansu sukai kansu da tambaya, Likitan ya goge gumin fuskarsa yace "Alhaji saide kuyi hakuri, Allah yayi mata cikawa, munyi iya kokarin mu ganin mun ceto Rayuwar ta, amma hakan ya gagara sakamakon ciwon Hanta datake dauke dashi, hantarta tariga ta lalace, kuyi hakuri"
Ilham najin haka ta yanke jiki tafadi, yaran kuwa kowa kuka yake, Aslam ya sulale Yazauna aqasa yana maimaita kalmar Innalillahi wa inna ilaihir raju'un acikin ransa
Gaba daya waje ya kaure da koke koke, babu me lallashin wani, haka suka dauki gawar Aysha suka tafi gida, akai mata sutura aka kaita gidanta na gaskiya, Aslam kuka Kamar mace, duk yafita a hayyacinsa, saide muce Allah yaji qanta, idan tamu tazo Allah yasa mucika da imani
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Tunda akai wannan mutuwa gidan yadawo shiru, Diyana kuwa kullum tana cikin hijabi🤣
tunda taga aysha qiri-qiri tamutu da quruciyarta, sosai mutuwar tataba matasan gidan, saboda basu taba kawowa kowa mutuwa acikinsu ba
Ranar ukunta yayi daidai da ranar da Daddy ya sanar za'ai meeting, amma ganin anyi musu rashi yasa aka sanarwa kowa sai bayan sati biyu akwai gagarumin family meeting.
Hakan ce kuwa ta kasance,ranarda sati biyu tacika kowa yatafi Babban dakin taro nacikin gidan mata da maza manya da yara, Usman shida matar sa da yaransa biyu, sai Aliyu shima yazo da matar sa da dansa daya namiji, farouq kuwa matar sa ko haihuwa batayi ba
kowa yazo yanaso yaji abinda wannan wasiyya ta qunsa
Samarin ne awaje kawai basu shiga ciki ba suna jira saisu Daddy sun qaraso
Sunata fira kadan kadan amma Aslam baya magana, Adam kuwa gabansa ne yake ta faduwa harya kasa boyewa yace "nifa gaskiya meeting dinnan danya zama dole ne amma gaskiya da bazan zoba, yau inada lacture, sannan gabana faduwa yake narasa dalili"
Fawaz kallansa yayi bai tankaba, Abba ma shiru yayi, Aslam kuwa daja tunda aysha tarasu suka kasa gane kansa
Kallansu yayi yace"wai badaku nake bane duk kunmin shiru?" 🤔
Ajiyar zuciya Fawaz yasauke yace" kai sai yanzu kakeji,? ni Tun jiya gabana yake faduwa, Kamar akwai abinda yake san faruwa Dani, amma koma menene Allah yasa ya sameni ni kadai banda Nihla "🤣
Kallansa Aslam yayi cikin mamaki, to kode Fawaz nason Nihla ne? 🤔
Kafin wani yace wani abu su Daddy suka qaraso wajan, shida Alhaji Baqir da Alhaji Basiru
Dakin taron suka shiga, sannan suma samarin suka bisu abaya
Wajan meeting din yayi kyau an qawata shi da lemuka da ruwa domin baqi 😃
Nihla tana kusada Momy, yayinda Ilham ma take gaban ummanta hajiya abida, suma su Dida itada Diyana suna gaban maman su hajiya Farida
Su daddy suna zama hall din yayi shiru, Kamar ruwa ya cinyesu, megadin gidanne yaqaraso dauke da akwatin da aka rufe takardar wasiyya aciki ya ajiye yajuya yafita 🤣
Daddy dakansa yatashi yabude, kowa yazuba masa na mujiya, yadauko takardar Yazauna sannan ya'ajiyeta agabansa
Yakai dubansa wajan samarin sun zauna waje daya gaba dayansu, Adam ya kalla yace "Adam taso kabude mana taro da Addu'ah"
Babu musu yatashi yadinga kwararo musu addu'ah, sannan aka shafa
Daddy yayi gyaran murya, yafara magana "Alhamdulillah, muna qara yiwa Allah godia akan Tsawon rai dayayi mana har muka kawo wannan lokaci cikin kwanciyar hankali, wadanda suka rasu acikin wannan family Aisha, da takwararta Aysha, muna yi musu addu'ah Allah yaji qan su"
Gaba daya aka amsa masa da "Amin"
Sannan yaci gaba da fadin
"insha Allah yanzu zamuji dalilin daya taramu anan wajan "
hall yaqara yin tsit, Daddy yabude takardar yayi tozali da rubutun Ajami, yadaga kansa yasake duban Adam yace"da Ajami sukayi rubutun, Adam kaine malami zoka karanta mana"
Hajiya na'ila tafara karkad'a kafarta tana hura hanci , jin ansake kiran dannata akaro na biyu
Jikin Adam a sanyaye yaje gaban iyayen nasa ya karbi takardar yafara karanta wa :Assalamu alaikum jama'ar wannan dangi Mai albarka, ni Abubakar Mazawaje mun zauna tareda matana guda biyu mun rubuta wannan wasiyya badan komai ba saidon hadin kan wannan zuri'a,mun yanke shawarar hada jikokinmu aure domin zumunci yaqara qullu wa,...
Adam yana zuwa nan yaji gabansa yafadi, jikinsa yafara rawa, hannunsa sai karkarwa yake yaji maganar akansu ne Wato jikoki
Cikin daure fuska Alhaji Baqir ya kalleshi "kai menene haka? Cigaba mana"
Muryar Adam na rawa Kamar ba namiji ba yaci gaba da karatun
"Duk mazan da suke cikin wannan family an mallaka wa kowa filin dazai gina,duk Wanda yayi aure acikin wadannan yara dazamu ambata, to lalle lalle ya tabbatar yasake wani auren yacika namu Burin
munyanke shawara tareda umarnin cewa Ilham 'yar gidan Basiru zata auri Aslam Dan Alhaji Baqir
Dida yar gidan Farida zata auri Fawaz yaron Alhaji Basiru
sannan Adam yaron Alhaji Baqir zai auri Diyana, yarinyar hajiya Farida
saikuma na qarshe takwarana Abubakar Wato Abba, zai auri Aisha yar gidan Alhaji Basiru tareda Nihla yarinyar Aisha "
Wannan dalilin ne yasa mukayi muku hani akan duk wani taro acikin family, na suna kona aure, saboda gagarumin taron dazaku hada na auren jikokinmu, muna yiwa kowa fatan alkhaairi "
Takardar ya ajiye, saboda jiri-jiri dayake gani 😃
Cikin fishi hajiya Na'ila ta miqe tsaye tace "wallahi bazata sa'buba, kowa yasan kaf family dinan yarana sunada hankali, babu wanda yakai Adam sanin Allah yace, annabi yace, 😃
amma arasa yarinyar da za'a liqa masa sai Diyana, yarinyar dakowa yasan tagama tambad'ewa atiti, shikuma Aslam wai Ilham, da rashin kunyar ta zaiji koda aikin gabansa "
Hajiya Farida cikin sauri itama tatashi tsaye ta maida wa hajiya Na'ila martani,
" ke saurara hajiya Na'ila, dakike cewa 'yata tagama tambadewa ambawa danki jinake yata Dida aka hada da qungurumin Mashayi 🙆🏻♀️, ni nace wani abu ne? Saike me bakin magana?"
Hajiya abia tayi shiru, tabbas taji haushin furucinsu akan yayanta, sai yau take dana sani akan halin Fawaz na shaye shaye, ta kalli hajiya Farida tace
" Farida Karki sake danganta min dana da sunan shaye shaye, "
Hajiya Farida tace " besha bane? Jinake Tun yana yaro kika gama lalata masa tarbiya, antashi an Auro mana baragurbi cikin family"
Gaba daya hall din ya kaure da surutu, da hayania, Aslam yayi shiru yana tunani, tayaya zai iya Rayuwar aure da qanwar Aysha? Yanzu kenan da ace tana raye ma Abba zata aura? Innalillah...wannan wacce mahaukaciyar wasiyya ce?
Momy kuwa hamdala take cikin ranta, shikkenan Abbanta zai auri nihila
Adam kuwa me karanta wasiyya yana ganin Ance Diyana zai aura yatuna lokacin data futo daga motar wani qato
Shikuwa Fawaz tunani yafara wai A'ina yakejin Dida ne? 🤔 Wacece Dida ne acikin yaran?
Daddy yayi shiru yana kallan kowa, matan sai hayaniya suke, Alhaji Baqir ne yatashi yadaka musu tsawa sannan suka nutsu kowa takoma wajan zamanta tazauna
Cikin ransa yafara magana, mata biyu!! amma wad'annan tsofaffin sunfi kowa cimasa mutunci, to aishi guda d'ayanma bayajin zai iya zama da ita, Dan haka yadago kansa Ahankali ya kalli Daddy yace
" I'am sorry Daddy, amma i can't marry her, Daddy bazan iya auren taba, inada wadda nakeso"
Gaban Nihla yayanke yafadi, ita yaya Abba yake cewa bazai aura ba agaban jama'a?
Lokaci daya hawaye suka wanke mata fuska, babu wanda yafado mata sai Diddi, tabbas sai kayi rashin uwa zakasan wani bangaren na rayuwa
Momy ta kalli Abba da sauri tanaso ta gaskata abinda kunnanta sukaji, ba ita kadai ba hatta Usman, Aliyu, farouq, shi suke kallo cikin tsananin mamaki
Daddy kansa maganar Abba tadaki ransa, amma saiya basar bai nuna ba ya kalli Abban yace "Amma kasan cewa yanda 'ya'yan wasu sukabi umarni bazai iyu d'anda nahaifa acikina yaqibiba ko? Tunda kace baka sonta tokaje kanemo son aduk inda yake, idan kuma kanakan bakanka har yanzu to kasa aranka cewa, qin auren Nihla dede yake da fitarka daga cikin Mazawaje family,sannan ni kaina nacireka acikin 'ya'yana, Zabi na gareka, koka amince kokuma daga nan katashi kafita baka cikin Mazawaje family "
Hall yasakeyin tsit, maganar Daddy ta daki kowa, tabbas yanda yayanke wannan hukunci akan d'ansa nacikin sa tofa bazaiji kunyar yankewa Dan wani ba
Babu musu Abba yamiqe, yafuto daga cikin Hall din
Momy tafara kuka wiwi, tace" Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, meyake shirin faruwa damune?"
Ta kalli Abba dayake dab dabarin cikin hall din ta qwala masa kira tace "Abba!!!"
Amma ko juyowa baiyiba
(wai ina labarin yusif ne,?🤔Yaje China ya maqale)
(tab bari na fece kar masu dukan Abba sudawo kaina 🤪}
Mutara zuwa gobe🙏🏻
Kada ku Manta da sharhi, Comments, dakuma share, please
Amnah El Yaqoub ✍️
[6/19, 10:55 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️
{Romance & Friendship luv}
Writing by Amnah El Yaqoub
Like my page On facebook 👇
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493
15&16
Baqin ciki yakama Momy, batasan lokacin data rungume Nihla ba suna kuka tare, Nihla kukan abu uku takeyi, na farko yanda ta dauki Abba aranta, take jinsa na daban acikin zuciyarta Tun tana qarama, amma karshe ga irin abinda yamata, na biyu Diddi, ta tabbatar da ace tana raye, zataji Dan sauqi acikin zuciyarta, na uku mafi munin yanda yafadi kalmar baya sonta acikin bainar jama'ah
Momy kam Baqin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 24