Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Daddy" Momy ta miqe tace "Nihla taso Muje kitchen" Bayan Momy tabi abaya, suna zuwa kitchen Momy tabata wani magani tace "kisha wannan yanzu, sai kici abinci kishirya kitafi gidan gyaran jikin" Cikin ladabi tace "to Momy" tadauka tafara sha tana tunani aranta, Ilham tabata, Momy tana qara mata wani itakam yaya zatayi? Momy ta kalleta tanajin tausayin yarinyar, gani take Kamar ba'a kyauta mata ba, Allah yasa de taso Abban nata, koda yake tasan Abban ma da naci, zai rarrasheta Bayan tagama sha tawuce dakinta tazauna agefen gadon tana tunani, yanzu haka aure ne akanta fa, ashe yaya Abba yasani shiyasa yake min wasu irin abubuwa a asbiti, tatuno lokacin da ya Aslam yake cemata yaya marar lafiyarta, Hmm ashe duk sun sani, wayarta tadauka takira Anty Nadiya tabata labarin komai, nan take Nadiya tace zatazo bikin itama domin ta nemi yafiyar sadeek, tayi musu ala sanya alkhaairi, bayan sun kashe tatashi tashiga wanka, tafuto ta shirya tsaf taci abinci, sannan tayiwa Momy sallama tatafi driver yakai ta gidan ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Sai bayan sallar ishsha'i tadawo gida, zaune suke afalo su biyu shida Momy, Momy tana bashi coffee abaki, sallama tayi tashigo cikin falon idonsa yasauka akanta, doguwar riga ce a jikinta Mai godon hannu amma rigar abaje take sosai, ya dinta yanada santsi Kamar na abaya, da mayafin rigar tayi amfani tayafa akanta sauran kuma ta zuba shi baya, dukda fadin rigar hakan bai hana ka hango bajajjan hips dinta, yayinda cikakken qirjinta yadago ,hakan yasa cikinta shafewa, da yar qaramar jakar ta a hannunta Cikin ransa yafara magana ya'ilahi! Yanzu haka duk anganta ahaka, amma yaya zaiyi? Bazai iyamata magana ba tunda shine yake neman sulhu Zama tayi akujera kusa da Momy, tace "wash Allah Momy nadawo" Zaman datayi awajan kawai wani irin qamshi na daban yake tashi, ahankali ya lumshe idonsa sannan yabudesu Momy tace "Sannu Nihla, ai gara da Allah yakawo ki, zanje in dubawa Alhaji wasu takardu, karbi wannan coffee din kibashi" Baki taturo gaba alamar bataso, ita Momy batasan halin ya Abba ba, kawai shagwaba ce take damunsa, amma aiya warke Haka tasa hannu ta karba Momy tashige dakin Daddy tabarsu anan Gyara zaman sa yayi akan kujerar ya dauki fillo din kan kujera yadora a cinyarsa yazuba mata ido yana murmushi Gaskiya yaji dadin abinda Momy tayi, wani irin nishadi yakeji aduk lokacin dasuka kasance su biyu shida ita Kallanta yayi yace "zeyi sanyi fa" Dago idonta tayi ta kalleshi, ta janye idonta, sannan tamatso kusa dashi ta diba a Spoon din takai bakinsa, Dan qaramin bakinsa yabude tasaka masa Spoon din, yanasha ya lumshe idonsa, haka taci gaba da bashi yanasha harya qare tas, bedena bude mata bakin ba, ta kalleshi tace "yaqare" Murmushi yayi yace "bazan samu qari ba?" Tashi tayi tsaye kanta tsaye tace "eh" Cikin sauri yasauko daga kan kujerar yace "kawo nariqe miki jakar to Muje dakin" Babu musu tabashi handbag din nata , shikuma yabita abaya har cikin dakinta Abakin gado tazauna shikuma Yazauna aqasanta tareda dora mata jakar akan cinyar ta, bayan yadora mata jakar a cinya memakon yadauke hannayensa sai yabarshi akan cinyar tata, bayaso kokadan yadena jin wannan qamshin nata dake rinjayarsa Nihla tarasa yaya zatayi dashi, ahankali tace "inaso ne nashiga wanka" Yace "akwai maganar danake so muyi" Fuskarta Babu yabo Babu fallasa tace "to" Kallanta yayi yafara tunani, yarasa meyasa har yanzu taqi sakin jikinta dashi, idan yadubi qwayar idonta yana hango rashin sabo atattare da'ita, kokuma har yanzu bata yafe masa bane bai saniba Ajiyar zuciya yayi, cikin maganar sa Ahankali cikin sigar rada, Wanda dagashi sai itane zasuji yace "ina qara baki hakuri akan abubuwan dasuka faru abaya .... Nihlaaa! " Yaja sunan nata Sannan yaci gaba da cewa "Wallahi yawancin kowanne dare bana iya kwanciya harna samu nayi bacci saboda tunaninki, koda yaushe jinake inason ganin ki a kowanne lokaci, duk lokacin dana kasance tare dake inajin wani irin dadi acikin zuciyata, abaya nayi kuskure dana kasa bawa wadda nashaqu da'ita kulawa harta hakura dani,domin kuwa nagama ganewa shaquwa ce kawai tasa na furta mata kalmar soyaiya, amma soyaiya daya Tun ta yarinta ta kena bawa Nihla..... a yanzu nayi miki alqawarin Zan kula dake fiyeda yanda Zan kula da kaina, kiyi hakuri kiyafemin kisaki jikinki dani please " Shiru Nihla tayi bayan tagama jin duk bayanin sa, Kamar ba shiba wani lokacin idan Yazauna yana yimata wasu abubuwan Ganin tayi shiru ba tace komaiba yasa shi motsa hannunsa dake kan cinyar ta, ahankali yafara shafa cinyar ta, kasancewar rigar jikinta me santsi ce saitaba shi damar shafa cinyar tata dakyau Ta kalli fuskarta yace "kinji" Gaba daya yafara kashe mata jiki da salonsa, Cikin shagwaba tace "ya Abba nide kabari" Yace "to kin yafemin?" Ahankali tadaga masa kanta, sannan tace "Allah yayafe mana baki daya" Yayi Murmushi yace "Amin, kinga wani abu" Yabude wayarsa ya nuna mata wasu pictures Kanta ta matso tafara ganin pictures din, shima yaturo nasa kan domin su gani tare,tana gani tace "laaaa pictures dina" Murmushi yayi ya kalleta, yanda kansu yahadu ne yasa yaji Kamar yayi kissing Dan qaramin bakinta, musanman yanda ta bude shi dinnan tace laaaa, amma bazai yiba, gara yabi komai Ahankali Yace "yes, Tun lokacin da mukaje garinku nayi miki pictures din, kin tuna? Abakin ruwa, har ruwa yadakemu" Cikin murmushi tace "wallahi na tuna, bani na gansu gaba daya, waye yatura ma?" Dadi yafara kama Abba, yanda yaga tafara sakewa dashi, yace "ya Usman ne yatura min" Tace "wayyo,lokacin banda qiba wallahi" Kallan qasa qasa yayiwa cikakkun nashanunta yace "yanzu ai kinyi" 🤣 Nihla bata gane komaiba tace "wallahi sune, zaka tura min kuwa" Kallanta yake yanda take jin dadi sai yaji dadi shima, gashi shiba wani surutu ba, kuma bayaso firar taqare,bayaso yadena jin daddadan qamshin dake tashi a jikinta, bayaso yayi nesa da'ita, yarasa mezaice mata domin tasake jin dadi shikuma yaga farin ciki akan fuskarta, ya kalleta yace "nagoyaki?" Cikin sauri ta kalleshi, cikeda mamaki, wanne irin goyo kuma ana zaune lafiya? Saikace Wanda zai iya goyon, tasan kawai fada yayi, amma domin taga gudun ruwansa sai tace "eh" Cikin sauri yace "to zo ki hau" Yadauke hannunsa akan cinyar ta ya tsugunna a gabanta Mamaki yagama kashe Nihla, anya ya Abba ne kuwa wannan? Yau ya Abba ne zaice tahau bayansa ya goyata? Ta ajiye wayar tasa agefe sannan tafara tattare rigar jikinta, tad'ane bayansa, lokaci daya yamiqe tsaye, beji nauyin taba kokadan, hanyar kofar dakin yanufa da ita yace "muje nakaiki falo saina dawo dake?" Zaro ido tayi tafara girgiza kanta tace "laaaa a a babu ruwana" Ganin yanda ta tsorata yasa yayi Murmushi yace "Allah Muje" Riqeshi tayi sosai tace "dan Allah kar Muje" Lumshe idonsa yayi, numfashin sa yafara sauyawa, qarfin jikinsa yafara raguwa, kasala ta lullube shi sakamakon jin nashanunta agadon bayansa yanda tasa hannu ta rirriqeshi Nihla taji shiru, tayi tunanin bai haqura ba, tasake jijjigashi tace "dan Allah" Nan take yaqara daukan caji, yashiga cikin yanayi, yaji qafafunsa suna neman gaza daukarsu, sai gyara kafafunsa yake, ita kuma takasa gane komai Yana motsawa kuwa suka tafi kan gadon nata gaba dayansu suka fada kai Nihla tayi tunanin da niyya yayi hakan, batasan yanayi ne yasa ba 🤣 Nan take tafara dariya, yajuyo da kansa yana Kallanta, yajima rabon daya ga tana dariya Kamar haka, ahankali yadago hannunsa ya dora shi akan dimple dinta Sharhi, share please 🙏 Amnah El Yaqoub ✍🏻 [7/15, 11:04 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️ {Romance&Friendship luv} Writing by Amnah El Yaqoub Like my page On facebook 👇 https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 57&58 Juyowa tayi tana kallansa, cikin murmushi tace "Aidama nasan bazaka iya daukana ba, shiyasa nahau banyi ma musu ba, yanda nake d'innan" Ta qarasa maganar tana jijjiga jikinta Shima murmushin yayi mata "nayi tunanin zan'iya ne, bansan haka ake jiba" Nihla kwata kwata bata gane maganar dayayi ba, Dan haka tayi shiru, hannunsa dake kan dimple dinta yadauke yadawo dashi dede karan hancin ta, yace "kinada kyau" Cikin sauri ta kalleshi, tayi Murmushi sannan ta yunqura tatashi zaune, ta kalli Agogon dakin tace "kaiiii shadaya saura, ya'akai lokacin yayi gudu haka, bari de in shiga wanka" "to kitashi kishiga mana" "to ai baka fita ba" "idan kika shiga Zan fita, kona kaiki?" Cikin sauri tace "a a, tsaf zaka sake kayar dani" tashige toilet din da kayan ta a jikinta tareda rufo kofar Yana ganin shigarta ya lumshe idonsa tareda yin ajiyar zuciya, yatashi jiki a mace yafuto daga dakin nata, har lokacin Momy bata falon, ya kashe kayan kallo sannan yawuce dakinsa, cikeda begen matarsa ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Acikin satin su Abba sukaje Abuja suka yiwa Yusuf godia, Abba har kunyar sa yakeji akan abubuwan dasuka faru abaya Sosai suka fahimci juna Tundaga lokacin Nihla tadena zuwa wajan gyaran jiki, dede da falo Momy hanata futowa tayi saide dole, kullum tana cikin hijabi, hatta qafarta akwai safa, data zauna aqasa kuwa Momy zata sata tatashi takoma kan gado ko kujera duk saboda kada sanyi ya shige ta Magunguna kuwa Momy bata take iri-iri masu inganci, Nihla qwarai ta yaba irin sonda Momy take wa ya Abba, haka kuma duk cikin surukanta Nihla ta daban ce, dama Tun tana qarama soyaiyar Nihla take cikin Zuciyarta, kokadan Momy bata qyashin yiwa Nihla abubuwa, domin kuwa tayi alqawarin zata riqeta Kamar itace ta haifeta, shiyasa take mata duk wani abu da uwa zata yiwa 'yarta Abba da Aslam Babu zama, danma wani lokacin su Adam da Fawaz suna yin wani abun ta wani bangaren, gida kam komai yaji, sun qawata shi yanda yakamata da kayan kamfanin A&A Furnitures, yayinda Anty Salama matar ya Usman da hajiya Farida maman su Dida suka shirya sukaje Dubai suka hadowa amarya kayan lefenta Anty Firdaus kuwa matar ya Aliyu itace tashiga tafita wajan kawo anko, dayake abune na kudi nan take kowa yayi, duk Wanda kaduba yana cikin farin ciki, kuma doki yake wannan rana tazo, andade ba'ayi wani taro a wannan family ba, ko bikinsu Aslam da akayi Babu wani biki da akayi, kasancewar kowa yasan Babu Wanda yake son auren, kowa dole aka masa Ana sauran kwana biyu biki 'yan'uwa na nesa dana kusa duk sunzo, yan'uwan mahaifin ta duk sunzo, kuma family anhadu anyi musu kara duk Inda suka so anan suke kwana, yan Abuja ma duk sunzo, mamy kam wajan Momy ta sauka suka hadu suke gudanar da Komai Yusuf yana wajan angwaye, saide duk abinda yake yana kokarin danne zuciyarsa ne kawai, saboda kada yazobe ladansa, bayan badan komai yayi ba saidon Allah Ranar kamu kuwa kowa ya shirya, amarya tanata sauya shiga kala kala, Acan gidan sheik Adam kuwa Diyana kuka tasaka masa da qaton cikin ta na wata shida, gaba daya dinku nan sunyi mata kadan, haka tasa Adam agaba tana masa kuka, yarasa yaya zaiyi da'ita haka yadauko mata wasu kayan suka Taho gidan bikin, Dida kuwa normal take harkar ta, domin kuwa har yanzu batada komai 🤣 Washe gari da rana amare suna zaune a part dinsu Ilham, cikin tsohon dakin Ilham datake ciki kafin tayi aure, bayan angama yiwa amarya kwalliya, zuwa dare za'a tafi wajan dinner Diyana tana gefe, da ciki agaba tana karanta wani littafi, Nihla ta kalleta tace "meciki" Diyana tace "saura ke ai" "A a, aini ya Abba yana sona, saiya qara reno na, sannan" Gaba dayansu suka saki dariya, Dida tace "tab, ina Ruwan yaudaran kai" Dariyar dasuka sa ne yasa lil Abba kuka, Nihla tace "kai Innalillahi... Dan Allah Ilham ki dauke wannan yaron naki, gaba daya ya ishemu da kuka" Ilham tace "angonki nede, yanda kuka sashi kuka yasin kema lokaci yana zuwa saiya saki kuka" 🤣 "ni Ilham Dan Allah kidena min irin wannan maganar, Allah banaso" Wayarta ce tadauki qara, Dida tabata tace "ga Ango yana kira" Karbar wayar tayi, ashe yanada number ta, betaba kirantaba, rage murya tayi tace "Hello" Saida yaja wasu second sannan yace "Amarya bakya lefi kokin kashe Dan masu gida" "to waye Dan masu gidan?" Murmushi yasaki Mai aji yace "farouq mana" "Hmm kaiko, shiyasa kullum kuke fada ai" "muna gidan Aslam, kuma suna jin yunwa" "toooo, to saide Ilham din tadawo tadafa muku abinci" "A a, kece zaki kawo mana" "yanzu ya Abba fisabilillah tayaya Zan Taho ni kadai, idan Momy ta ganni ma zata hanani" Shagwaba yafara yi yace "uhm.. uhm.. Allah nide yunwa nakeji" 🤦🏻‍♀️Kanta da dafe da hannunta tace "to naji" qit takashe wayar sai mita take, mutum ana tabashi sai shagwaba, saikace shine autan duk duniya, nida nake wajan iyayena ni kadai banyiba saishi, haba ni wallahi nagaji 😔 Mesu Diyana zasuyi inba dariya ba, Dida tace "wai Dan Allah ya Abba ne yake miki shagwaba?" Tace "tab, ai saide in bamu zauna ba" Diyana tace "ya birgeni, yanzu ba kowanne namiji ne yake wa matarsa shagwaba ba, saide ke mace kullum ki daddage kiyi, duk saboda ki faranta musu, maganin mata ne, mata ne suke nema, maganin tsumi ne mata ne, shagwaba ce mata ne, ke mace kullum kede kina kokari kiga kinyi Dan ran mijinki yayi fari, amma Ba kowanne namiji ne zaisha magani ba, saboda matarsa taji dadi, komai de saimu, saboda haka idan yafara miki shagwaba kema ki masa, zai dinga tattalinki, Dan kowanne namiji dakike gani Babu Wanda zaice bayason yasamu mace wacce ta'iya shagwaba " Ilham tace" wallahi gaskiya ne kam " " salamu alaikum " Gaba dayansu suka juya suka kalli kofar dakin, baquwar fuska suka gani,yarinya ce qarama da alama zatakaisu shekaru, wata shegiyar gown ce a jikinta datahau jikin nata sosai, kallo daya zakayi mata kasan cewa lalle mace ce har mace, haka kana ganin hancin ta zaka tabbatar ita din bafulatana ce, duk yanda doguwar rigar ta baiyanar da hips dinta hakan baisa tasaka Babban mayafi ba, Dan qarami ne sai tayi rolling dashi ganin yanda suka zubo mata ido suna Kallanta yasa ta qarasa shigowa cikin dakin ta ajiye jakar kayanta, sannan tazauna agadon ta cire mayafin datayi rolling tana firfita dashi Tace "ku qaramana esin mana" 🤣 Ilham tana kallan ikon Allah tace "aqure yake ai" Tace "to inaga Dan daga rana nake ne shiyasa," Ta kalli Nihla tace "amarya, wai baki ganeni bane? Naga duk sai kallona kuke, naje wannan part ance bakwa nan, naje wannan ance bakwa nan, saida nazo nan nayi sa'ah akace kuna ciki, ina qawayen naki naga saiku hudu kawai?" Nihla tace "banfa gane kiba" Dida ma tace "amarya batada qawaye, qawayenta yan'uwanta, mune kuma" Itama tace "to gani naqaru, Rafi'ah cefa, yar gidan yayan baban ki Abdullahi na lagos" Nihla tace "kut, au Rafi'ah wai kece? To ina Zan gane ki, kinga yanda kika koma kuwa" Ta kalli su Ilham tace "cousin sister nace, yar gidan yayan babanmu ce, alagos suke dazama, babansu yana canji" Gaba dayansu sukai murna,Dida tace "to yanzu ai kinga kinsamu qawa yan'mata" Nihla tace "to Rafi'ah ko zaki kaiwa angwaye abinci, suna gidan Ilham" Rafi'ah tace "angwaye? Sunada yawa?" Ilham tace "gaskiya bazasu rasa yawa ba" Tace "a a toba lalle nashiga ba gaskiya, dade mu biyu ne,bari na gyara fuskata,nikam Nihla ina yusuf Dan unguwar ku? Kwanaki naji baba yana waya da baban ki naji yace kuna Abuja agidan su" Murmushi Nihla tayi "ya Yusuf, shima yana wajansu ai, idan kinje saiku gaisa dashi" Tashi Rafi'ah tayi tashige toilet taqara gyara fuskarta dakyau, sannan tafita wajan Momy domin karbar Abincin Tana fita Diyana tasaki ajiyar zuciya tace "kai duniya akwai kyawawan mata gaskiya, Wato Nihla wannan sister naki Babu qarya tahadu, kice muqara rike kazajenmu hannu bibbiyu" 🤣 Dukansu sukai dariya, " oh Diyana uwar kishi" cewar Ilham ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Suna zuwa gidan iliya driver ya tsaya, tafuto tace "ga Abincin kashiga kakai musu, ni ina jiranka anan" Iliya yayi dariya yace "ranki yadade aida Kinshiga" Tace "a a, idan kakai musu kace ana magana da yusuf" Iliya yaje yakai musu Abincin, yafadi saqonsa, yana fada kowa yafara yiwa Yusuf kallan kallo, Adam yace "iliya kace mace ce take sallama dashi?" Yace "eh, tare muke da'ita ai, itace tabani Abincin tace na kawo muku, budurwa ce" Dariya sukayi, Aslam yace "to kode munyi kamu ne" 🤣 Yusuf yayi Murmushi kawai ya cewa iliya "Muje" Suna futowa yaganta a tsaye daga nesa, begane taba, cikin ransa yace anya kuwa shi take nema? To Wacece wannan saikace aljana saboda qira? 🤔 Wajan ya qarasa, ta kalleshi cikin murmushi tace "baka gane niba ko?" Yace "gaskiya kam, kiyi hakuri bangane kiba" Tace "Rafi'ah cefa, yar garinku, Wanda suke lagos" Saida yayi jimmm sannan yace "okeyyyyy nagane ki yanzu, to Rafi'ah aikin girma ina Zan gane ki idan akan hanya ne?" Tayi Murmushi tace "na tambayi Nihla ina kake, kuma ance min a gidanku suke zaune a Abuja, shine dana tambayeta tacemin kaima kana nan gidan" "wallahi ina nan, Yaya school, meyasa baki shigoba kuma?" "ai ance min angwaye suna ciki, nasan kuma suna dayawa,gashi ni kadai ce, shiyasa nace idan yakai muku Abincin yaturo ka mugaisa " Yace "gaskiya kin kyauta, Allah yabar zumunci, zakije wajan dinner din ai anjima ko?" Tace "eh zamuje tareda amarya" "to shikkenan idan bamu wuceba saimu dauke ki mutafi" "to shikkenan nagode, sai anjima" Tajuya wajan iliya dake jikin Mota yana jiran su, tashiga suka tafi, Yusuf yabi bayan motar da kallo, ikon Allah, ashe yanzu ana samun yanmata masu sada zumunci haka, Wato ita haka kawai dansu gaisa ta kirashi, amatsayin sa na Dan garinsu Yayi ajiyar zuciya tareda komawa ciki, yana shiga kuwa duk suka bishi da kallo, Fawaz yace "Malam Yusuf irin wannan dadewa haka, kode kasuwa ta tabbata ne" Yayi Murmushi yace "yar garinmu cefa" Abba da tunda aka fara magana baisa bakiba yace "to menene ai ana auren yar gidama" 🤣 Aslam yace "Kamar yanda kayi ko" Adam yace "mukayi de" 🤣 ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Wajan dinner yayi kyau sosai, an qawata shi yanda ya kamata, kujerun da Amarya da Ango suka zauna sunacan sama, sauran mutane kuma anshirya musu nasu wajan zaman, iyaye mata duk sunzo, nan take aka fara gabatar da Komai bayan shigowar Ango da Amarya, gown din da tasa launin light green tayi masifar yimata iyau, yar qaramar posting din hannunta kadai ma abin kallo ce, yayinda Ango yasaka farin kaya yaci Babbar riga Kamar ba shiba, hannunta yana cikin nasa, mc yafara gabatar da mutane sannan aka umarci amarya da Ango sufuto su yanka kek Rafi'ah tana gefen Nihla sai tafi ake musu ga kida yana tashi, Dan qarami ta yanko tasaka masa saikawar dakai take taqi yarda suhada ido, waje yadauki ihun murna, shikuwa daya yanko nasa saida yasa hannunsa yariqe waist dinta sannan yamatso da bakinsa dab da nata Kamar zaiyi kissing dinta yace "haa" Murmushi tayi, takai masa dukan wasa a qirjinsa "sannan tabude baki yasaka mata" Su Momy suna ganin haka, suka miqe daya bayan daya suna barin wajan, akabar iya yaran su kadai 🤣 Ana kiran mutane suna fita suna rawa, Diyana tayi tagumi tanajin haushi, taso tayi rawar amma Babu hali,saboda cikin ta 🤣 Nihla tana zaune awajan dasuke ta hango ya Yusuf da Rafi'ah suna Selfie, taji dadin yanda Rafi'ah take kulashi, ko banza hakan zaisa tarage masa wata damuwar, ita har yau Yaqi bata dama ma suyi magana, amma tunda yakula yar'uwarta ma taji dadi sosai Hadari ya gangamo agari amma kasancewar suna ciki ga qaran kida shiyasa basuji ba, sai wajan goma da rabi aka tashi, hannun Nihla yana cikin na mamy, mahaifiyar Yusuf suka futo kai tsaye aka wuce da Amarya gidan ta 'yan'uwa kowa ya yaba da gidan amarya, ganin Hadari yasa kowa yatafi gida dawuri akabar amarya ita kadai, bayan fama da akai da'ita akan tayi hakuri ta daina kuka ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Shadaya da rabi suka qaraso gidan shida Aslam, ruwa ake sheqawa Kamar da bakin qwarya, ahankali motar take tafiya kasancewar ana ruwa, har suka qaraso cikin harabar gidan, Aslam yayi Parking Abba yafara kokarin fita Dasauri Aslam yariqe shi "haba Abba, haba, irin wannan saurin fa? Kagafa ruwa ake, kabari yadan ragu mana" "Aslam yazan zauna anan matata tana ciki ita kadai" 🤣 "Abba wallahi de kabi 'yar mutane Ahankali, idan kana nan ana ruwa ai itama tana ciki, mezai sameta? Katsaya Dan Allah" Dawowa yayi Yazauna yace "gaskiya kana takuramin wallahi, kabarni naje wajan amarya ta kawai" Aslam yayi Murmushi yace "bade acikin Ruwan nanba, kayi hakuri kawai, inkuma ana ruwan zakayi naka amarcin ga hanya nan" "Hmm Aslam waidan Allah meka daukeni ne? Kace nabi yarinya Ahankali, kace zanyi amarci acikin Ruwan sama, haba, yarinyar da ko gama sakewa dani batayi ba" Dariya Aslam yayi yace "ai gaskiya ne, hali nasani" Wayar Aslam tafara qara, yana ganin sunan matar sa yadauka, tace "ya Aslam dagani sai Abba fa a gidannan har yanzu baka dawoba, baku gama siyan bakin bane?"🤔 Yace "ruwa ne yatareni, amma ganinan zuwa, bari nataho" yakashe wayar Abba yace "tab, tosu dasuke su biyu ma takira ka awaya, amma ni kahanani tafiya" yana gama fadar haka yabude motar yafuto Aslam yana dariya yadaga murya yace "ledar, kamanta ledar taka" 🤣 Dasauri yadawo ya karba yayi ciki, duk yanda yake sauri saida Ruwan yadakeshi,yashigo cikin falon sannan Yarufe, kai tsaye dakinta yashige, tanajin shigowar sa ta kalleshi ta cikin mayafin da'aka rufe mata kanta dashi Mai shara-shara, tana ganin yanda yajiqe tayi Murmushi Ledar hannunsa ya ajiye, yafara cire Babbar rigarsa ya ajiye, sannan ya kalleta yace "amarya, angon naki duk yajiqe saboda yana zumudin son ganinki" Nihla tayi shiru batace komai ba Ahankali yataka yazo gaban gadon ya tsugunna, sannan yasaka hannu ya janye rigarta data rufe kafarta aciki, Jan lalle da Baqin da akayi mata ya baiyana, cikin ransa yace wow! Shafa wa yayi ahankali Cikin sauri ta janye kafarta batare datace uffan ba Kallanta yayi, sannan yasaki wani irin murmushi, wacce irin godia zaiyi wa ubangijinsa daya mallaka masa Nihla? Hannun nasa yasake maidawa ya janyo kafar tata, yakama yatsun kafar yanajansu daya baya dayan,qunshin da'aka yi musu yayi mutuqar kyau, kokarin janye kafar take, amma sai Yaqi bata damar hakan, daga qarshe ma saiya dora bakinsa akan Dan yatsanta guda daya yana sha Wani irin abu taji yana mata yawo a jikinta, takasa gaskata wa kanta cewa Shin ya Abba ne kokuma wanine daban, sunkuyarda kanta tayi tadorashi akan gwiwar ta tanajin wani irin yanayi yana shigar ta Saida yakai kusan minti uku yanasha sannan yazare bakinsa, muryar sa harta fara disashewa yace "please ko zaki temakamin incire kayana, duk sun jiqe" Sharhi please Amnah El Yaqoub ✍🏻 [7/17, 1:57 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️ {Romance&Friendship luv} Writing by Amnah El Yaqoub Like my page On facebook 👇 https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 59&60 Nihla tayi shiru tana jinsa batace komai ba, ahankali yatashi yahau gadon tareda yaye mayafin nata, cikin sauri tasa hannu biyu tarufe fuskarta, yayi Murmushi yace "masha Allah," Yasa hannu ya shafi fuskarta yace "kinyi kyau sosai," Tayi Murmushi kadan batare data kalleshi ba, yace "kunya ta kikeji kuma? Toki dena, tashi mana, tashi kitayani mana" Ahankali tace "saikace wani Yaro" "yes, ai qaramin Baby ne awajan ki" Nanma batace komai ba, yafara kokarin tashi yana mata wasa "amarya amarya, kisaki jikinki fa" 🤣 Nihla de tana jinsa tayi shiru, tasan cewa yau me rabata da ya Abba sai Allah, yanda yake wannan rawar kafar Allah ne yasan yanda zasu kwashe dashi Agabanta yafara cire kayan jikinsa, cikin sauri ta runtse idonta, ya kalleta yayi Murmushi, kunyar Nihla tana birgeshi sosai, yadawo dagashi sai gajeren wando yadubeta yace "zanje nayi wanka, yakamata kema kiyi shirin kwanciya, nasan kin gaji" Ahankali ta daga masa kanta, shikuma yafice daga dakin da kayansa Bai wani dade ba a wankan yadawo dakin nata yana sanye da kayan bacci,dakuma jallabiya a hannunsa, a lokacin harta kwanta da kayan ta a jikinta 🤣 Wata yar qaramar dariya yasaki yace "kisakko muci abinci" Girgiza kanta tayi tace "naqoshi" "mene? Banason musu, sauko kawai, kuma wannan kayan najikinki aida kin ciresu, damunki zasuyi idan kina bacci" 🤣 Kokarin tasowa take daga kan gadon tace "Babu komai, bazai dameni ba" Ajiyar zuciya yayi yace "kozakiyi alwala mufara yin sallah?" Tace "to" sannan tayi hanyar toilet dinta dake cikin dakin, yabi bayanta dawani irin mayen kallo Tare suka gabatar da sallah,bayan sun idar yadinga kwararo musu addu'ar zama lafiya dakuma samun zuri'ah tagari, bayan sun shafa ne yabude musu ledar dayazo da ita, kaza ce aciki babba saikuma fresh milk, shida kansa yafara bata taci taqoshi sannan shima yaci, itace takai kayan kitchen har lokacin ana zabga Ruwan sama Dakin tadawo tarakube agefen gadon, shikuwa kwanciya yayi harda dora kansa akan fillo, yana riqe da wayarsa🤣 Yadago kansa yadubeta yayi Murmushi, yaga alama gaba dayan ta atsorace take dashi, idan kayi mata kyakykyawan tsawa zata iya zurawa da gudu 🤣 Yace "kizo ki kwanta mana" Ahankali tahau gadon can gefe ta kwanta tareda juya masa baya, tashi yayi ya kashe wutar dakin yadawo kan gadon kusada ita ya kwanta, gabanta yafara faduwa sosai Yace "Ruwan nan anayin sa dayawa yau, yayi albarka sosai, Allah yasa muma auren mu

Chapter 21 of 24