Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sannan tace "Muje na wanke miki to" "Diddi Zan wanke mata" Cikeda mamaki kowa yake kallansa, musanman Momy, cikin ranta tace tabd'i Amma a fili sai tace, "lalle Nihla kin ciri tuta" Diddi tayi daria tace"lalle yau haihuwa tanamin rana sosai" takai Kallanta ga Nihla tace " ke tashi kije yayanki ya wanke miki kanki " Babu musu tatashi ta cire kayan jikinta, daga ita sai pant tabishi suka futo tsakar gidan ta tsugunna, shima tsugunnawa yayi sannan yafara zuba mata ruwa akan, ba komai yasa yace zai wanke mata kanba, saidan yanaso yataba gashin yaji, omon yad'auka yazuba mata akan sannan yafara wankewa yana dirzawa da duka hannunsa biyu Momy dasuke zaune a rumfa kallansu take tanajin d'ad'i aranta, ashe Abban nata ya'iya wankin kai,🤣 shikuwa Usman hannu yasa a aljihun jeans d'insa yad'auko wayarsa yana musu photo Kannata yafita sosaai amma haka yaita wasa da gashin sannan yadena zuba mata Ruwan, ya kalleta Ahankali yace "kicire wandon nayi miki wanka" Hannu tasa ta goge Ruwan daya zubo mata a fuskarta ta d'aga murya tace "Diddi wai yamin wanka?" Cikin rashin damuwa tace "Eh yayi miki mana" Ahankali tatashi ta cire wandon sannan ta tsugunna, babu bata lokaci yafara yimata wankan, saida ya wanke mata jikinta tass sannan yacemata "tashi kije" Bata damu da yanda yayi mata maganar Kamar bayaso ba, tatashi tatafi d'aki da gudu Da yamma Usman da Aliyu da Farouq suka fice yawo ganin gari Nihla kuwa tunda Abba yayi mata wanka ta shiga d'aki tasaka wata 'yar qaramar riga marar hannu tashan iska, ta kwanta tana wasa tana surutun ta ita kad'ai anan bacci ya dauke ta Diddi ta kalli Abba da Idanunsa suke lumshe wa tace"me sunan yaya nah, kai ba zakaje yawon kaga gari ba? " Hamma yayi yace" Diddi bacci nakeji " " to tashi ka shiga d'aki mana, jeka kwanta kahuta, dama ai akwai gajiya kunsha hanya " Yana shiga d'aki yaga Nihla na bacci, katifar tanada girma sosai, shima ya kwanta agefenta, nan da nan kuwa yayi bacci Saida Momy ta leqo d'akin taga sunyi bacci dukansu sannan ta kalli Diddi tace" Aisha kin tambayeni kowa amma baki tambayi yayanki ba, " Lokaci d'aya yanayin Diddi ya sauya," Anty Rahma yaya bayasona yanzu, wannan shine dalilin dayasa bazan iya baki Nihla ba, qiyaiyar dayakemin bakan kowa zata komaba sai kan 'yata,nikuma ina son yata, banasan wani abu yasameta, yanzu haka tsoron irin amsar dazaki bani ne yasa ban tambayeki shiba, saboda nasan ba zanji amsa Mai d'ad'i ba " hawaye ne suka zubo mata, wasa wasa Tun ta nayi marar sauti harta dawo tana kuka sosai Kamar qaramar yarinya Ajiyar zuciya Momy tayi, ta dafata "Aisha yayanki baya fishi dake yanzu, idan ma yanayi to kad'anne,kisaki ranki kidena damuwa, wai Aisha ke kadai kikai wannan laifin ne? Baga Basiru nanba, ganin yarane yasa banyi miki fada ba, ki kalli jikin ki aisha kin kasa kwantar da hankalin ki duk kin rame, meyasa hakan Aisha " Cikin kuka tace" dole zanyi kuka Anty Rahma, ki kalli irin Rayuwar danake nida 'yata, Yaya yana dashi bazai tallafamin ba, uwarmu d'aya ubanmu d'aya, wacce irin qiyaiya ce wannan? " "Aisha idan kika sake zancen qiyaiyar nan tsakanin keda yayanki ranki zai baci yanzun nan, yanzu haka yayanki ne ya shirya mana wannan tafiyar, kiyi hakuri ki kwantar da hankalin ki, watarana komai zaizo qarshe" Jakarta ta bude tadauko kudi masu yawa ta miqa mata, Diddi tasa hannu takarba,sannan tasake dauko mata wata sarqa ta gold tabata, sannan tace "ki ajiye wannan sarqar awajan ki, dakaina nasiyo miki ita, tanada tsada, duk lokacin dakika buqaci kudi idan babu ahannun ki kije kasuwa kisiyar kiyi amfani da kudin, shikuma wannan kudin dubu hamsin ne,yayanki yace akawo miki" Hawaye masu d'umi suka zubo wa Diddi, taji dadin kyautar amma wani bangare na zuciyarta ya kasa yarda cewa yayanta ne ya aiko mata da kudin, ta kalli Momy tace "nagode sosai Anty Rahma, Allah yasaka da alkhaairi" Momy ba tace komaiba tajata jikinta tana bubbuga bayanta alamar rarrashi, saida taga ta daina kukan tasaki ranta, sannan suka tashi suka fara shirye-shiryen had'a Abincin dare ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Cikin bacci taji anajan gashin girarta, zafi taji, lokaci d'aya tabude idonta, dashi tafara yin tozali yana kwance agefenta yazuba mata ido, tace "kai meyasa kakejamin girata, Allah Zan fadawa Diddi" "to sai bacci kike kitashi mana, tashi natayaki wasa" Kafada ta maqale masa "bazanyi wasa dakai ba,saboda d'azu kaine kaqi rakani shago nasiyo omo" Kansa ya nuna da hannunsa yace "nid'in? bana wanke miki kanki ba?" Daria tasaka, gefen kumatunta duka biyun suka lotsa, ahankali ya d'ora hannunsa awajan, itama hannunta tasaka ta janye nasa hannun daga fuskarta tace "eh natuna, kamin wanka, to mun shirya, meyasa kai baka magana? Anty tace baka magana" "inayi mana, gashi ina magana dake" Gyara kwanciyar ta tayi Tajuyo tana fuskantarsa, kusancin yayi kusanci Kamar zata shige jikinsa, tace"meyasa to kakeyi Dani?" " because You're my friend " Girgiza kanta tayi tace " niban gane me kace ba" "Zan fad'amiki" "yaran Momy kun tashi daga baccin kenan" Dagowa sukai dukansu suka kalleta, Dasauri Nihla tace "yawwa Anty, me You're my friend take nufi?" "Nihla Anty, Anty, nahanaki cewa Antyn nan kinqi ji, to zamu bata dake, kutashi ku futo kuyi shirin sallah, magrib takusa," tana fadar haka tafice daga d'akin, itama Nihla tashi tayi tafice tabar Abba shi kad'ai ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Da daddare dukansu suka baje a tsakar gidan akan tabarma, Nihla ta liqewa Usman tana ganin game a wayarsa, gama cin Abincin su kenan, sai lemuka dasuke ajiye agefe Wanda suka sha sukabar sauran Baba ya kalli Momy yace "Amma hajiya ai zakuyi mana sati d'aya ko" Momy tace "sati Ibrahim! Haba Mai hakuri, sati ai yayi yawa, jibi jibin nan zamu tafi insha Allah, kwana biyu zamuyi muku, saboda yara suna zuwa school, yanzu ma saida muka sanar a makaranta sannan muka Taho dasu" Yace "to hajiya, ai hakanma kunyi kokari sosai, su Alhajin de duk suna lafiya ko?" "lafiya kalau alhmdlh" "to yaya wajan su hajiya Farida da yaran nata su Dida da Diyana?" Wannan karan saida Momy tayi Murmushi, saboda tasan duk cikin mazawaje family baya shiri da kowa Kamar hajiya Farida, tace masa "suma suna nan kalau" Yace "to madallah, Allah yasaka da alkhaairi Hajiya, Aisha duk ta nunamin abin arziqi" Murmushi Momy tayi ba tace komaiba, suna nan zaune suna taba hira har dare yayi, suka nemi makwanci, Usman da Aliyu da farouq sukabi baba d'akinsa, Momy da Diddi da Abba da Nihla suka tafi dayan d'akin suma, Momy ce ta gyara musu shimfida daga nan taja Nihla jikinta suka kwanta, yanda tasata a gabanta Kamar wani zai qwace mata ita, har Diddi nayi musu daria ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Washe gari bayan sallar asuba yaran duk bacci suka koma, sai Diddi da Momy ne kawai suke fira sama-sama, gari nayin haske suka fara had'a abin karya wa, zuwa tayi d'aki tataso Nihla tashiryata tsaf sannan tabata nera ashirin tace ta tatafi makaranta Yauma tana fita kofar gida taga gate din gidansu abude,direban gidan yana goge Mota, shikuma yana tsaye da lunch box ahannun sa, lokaci d'aya farin ciki ya kamata, yau itace da kanta tafara d'aga masa hannu, cikin sauri ya ajiye Abincin nasa aqasa yafuto da gudu, direban yana kiransa amma ko waiwayowa baiyi ba, qyaleshi yayi amma de yabishi da kallo yanaso yaga Inda zaije Kusa da ita yaje ya kalleta "meyasa jiya ban ganki ahanya ba da aka tashi daga school?" Zaro ido tayi "laaaa ashe kaima kana nemana, nima inata kallan hanya banganka ba" Zuba mata ido yayi yace "yaya sunanki?" Tace "Nihla Ibrahim Mai hakuri, kaifa?" Cikin farin ciki yace "Yusif Isma'eeil," Hannun ta yaja yafara tafiya "zomuje direba yakaimu school tare" Qwace hannunta tayi tace "um um Babu ruwana Diddi zata dakeni, tace karna tsaya ako'ina" Tana fadar haka taqwace hannunta tatafi da gudu, shima Kallanta yake yana daria, sannan ya juya ya koma cikin gidansu Da azahar ana tashinsu daga makaranta bata tsaya wasaba tataho gida, tana hanya bataga motarsu ba, saida ta kusa qarasawa gida sannan ta hangi motarsu suna shiga gida Bayan sallar la'asar dukansu suna zaune suna fira, Nihla tana kwance akan tabarma Momy tajata ta d'ora mata kanta akan cinyarta 🤣 Sukuma mazan suna buga ball Ahankali kasancewar gidan akwai d'an fad'i kad'an yau harda Abba akeyi, yana sanye da qananun kaya riga me Jan duhu da wandon jeans amma ya tattare wandon daga qasa ya maidashi Kamar three quater Saida sukayi suka gaji sannan kowa Yazauna, wayar Usman Abba ya karba yafara game, Nihla tanajin qaran game tatashi takoma wajansa tana gani, qasa-qasa tayi muryarta tace masa "zomuje yawo" Shiru yayi ya qyaleta, tasake cewa "kaji" Kallanta yayi becemata komaiba ya kashe game din yasaka wayar a aljihunsa yatashi yace mata "Muje" Daria tayi itama tatashi, takama hannunsa suka fara tafiya ya kalle Momy yace "Momy munfita" Cikin farin-ciki tace "to Abba na, amma Karku d'ad'e naga garin akwai hadari" Basuce mata komaiba suka fice daga gidan ita kuwa Nihla takama hannunsa ta riqe sosai Suna fita suka dinga zaga garin, sai surutu take masa amma amsar datake samu kad'ance daga wajansa Kallanta yayi "ina zamuje?" Tace "zakaje rafi innuna ma ruwa dayawa muyi wasa saimu dawo?" "akwai ruwa sosai?" Tace "eh akwai sosai baka ganiba harda kwale-kwale" Yace "to Muje mu" Tafiya sukayi me nisa sosai, Yakalleta yana haki yace "kewai bamuzo bane?" "to idan munzo ai zakaga Ruwan ko? Kaide kataho kawai" Bece da'ita komaiba suka cigaba da tafiya har sukazo wajan, hannunsa tasaki tatafi wajan Ruwan da gudu tana daria, abaki bakin Ruwan ta tsaya, sannan tasaka hannunta tad'ebo Ruwan ta watsa masa Firgigit yayi, yadawo hankalinsa daga kallan yawan Ruwan wajan, yace "kika jiqani?" Kafin tabashi amsa ya qaraso wajan shima yad'iba ya watsa mata, bata damuba, dariya ma tayi tasake diban wani tajiqashi, shima yasake ramawa, haka duk suka jiqa jikinsu shima ya biyemata sai daria suke cikin farin-ciki Hijabin jikinta ta cire tana wullashi sama, tana cafewa, sai tsalle take tanata farin ciki, wayar Usman yadauko acikin aljihun wandon sa ya tsaya yanayi mata photo, gani tayi yana binta da waya ta tsaya tace "photo kakemin?" "eh" shine kawai amsar daya bata Tace "to tsaya na gyara" Tsayuwa ta gyara, yanata yimata photon iri iri, ya shagala yanayi mata pictures din, ta tsugunna ta d'ebi yashin dayake wajan ta zuba masa ajikinsa Wandonsa ya kalla yanda tazuba masa yashi,memakon ransa yabaci saiyayi murmushi yabiyota da gudu, tana gudu tana waiwayensa har tazo wajanda aka tara wani yashin da yawa, tana zuwa wajan tafad'i Shima yana qarasowa wajan yariqe gashin kanta yace "wana kama?" Daria tayi tace "nadena, Allah nadena" Rabuwa yayi da ita ya kwanta anan gefenta akan yashin, sai haki suke maidawa kowa yana kallan Dan'uwansa, wayar hannunsa yadaga yayi musu pic suna daga kwancen 'Dis taji an d'iso mata ruwa, Dasauri tatashi duk yashi yabata mata gashin kanta tace,"ABBA ruwa" Hannunta ya fizgo tadawo ta kwanta yanda take da, yace "me kikace?" "Abba" tabashi amsa kai tsaye Girgiza kansa yayi yace "Yaya Abba zakice" Daga masa kai tayi, kafin tace wani abu sukaji Saukar ruwa akansu, cikin sauri suka tashi, tadauki hijabinta, yariqe hannunta suka tafi qasan wata bishiya da gudu, suka tsaya anan, Tun ana yayyafi aka dawo ana shara ruwa da karfi, duk tsoro yakamata, ta rikice, shikuwa Babu wani tsoro atare dashi, iskar da akeyi ne yasa bishiyar dasuke qasanta kad'awa, nan take ruwa yajiqe musu jikinsu jagab,kallan gashin kanta yayi, gaba d'aya yajiqe ya kwanta sosai yana sheqi Kamar Wanda ake saka masa Mai, hijabin jikinta ya karba Yarufe mata Kannata dashi, sannan yajata yasakata ajikinsa yace "kidena tsoro" Bata iya cemasa komaiba, ahaka suka tsaya har aka qare Ruwan tas, Inda Allah yarufa Asiri ba'a dauki lokaci ana Ruwan ba Ana gama Ruwan yasaketa, cikin tsoro tace "mutafi gida" Bece mata komai ba yariqe hannun ta suka fara tafiya, mutane kowa yafuto yanata harkar gabansa Sunzo wucewa ta wata bishiya su kaga mutane suna gudu ana cewa Zuma! Zuma!! Zuma!!! Kallansa tayi tace "la'ila, wallahi mugudu karya cijemu" Nan take suka fara gudu duk yanda sukaso kaucewa saida zuman yacijeshi awuyansa, kafin ya farga wani yashiga cikin hancinsa, lokaci d'aya ya rikice ya tsaya yadena gudun, hannunta yasaki, yarasa yaya zaiyi yafitar, wani me machine ne yazo wucewa ya gansu, ita yagane yace "subhanallah Nihla, me yakawo ku nan wajan?" Kafin tace wani abu yacacimi Abba yasakashi akan machine din, ita kuma yasakata agaba, be tsaya ko'inaba sai Dan qaramin asbitin garin (Nuhu Alfa Hospital) Saida ya danqasu ahannun likita, yaga sun fara duba Abba sannan yace musu zaije gidansu yasanar ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Acan gida kuwa duk sun fito kofar gida, gaba dayansu har mahaifin Nihla, sunyi neman duniya sun rasa Abba da Nihla 😂 Me machine yana zuwa kofar gidan yafaka, suka gaisa da mahaifin Nihla, nan take ya sanar dasu komai, cikin tashin hankali suka nufi asbitin baki d'ayansu Waye yusif? Menene yake tsakanin Aisha da yayanta Abubakar? Wacce irin wasiyya iyayen su suka rubuta? Duk Ku biyoni Sharhi please 🙏 Mrs Usman ce ✍️ [6/14, 10:40 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI DAYA❣️ { Romance & Friendship luv} Writing by Amnah El Yaqoub Like my page On facebook https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 5&6 Suna zuwa asbitin sukaga Abba Akwance Idanunsa yayi jajir, Nihla tana zaune agadon kusada qafafunsa, sai likitan daya dubashi a tsaye Momy tace "subhanallah, sannu Abba," Sannan ta kalli likitan tace "doctor Babu dai wata matsala ko?" "Babu komai hajiya, ai anyi masa allura ma, zaku iya tafiya, saide a kiyaye gaba" Diddi tace "insha Allah likita, yanzu ma nemansu mukai muka rasa, amma insha Allah za'a kiyaye" Takai Kallanta ga Abba tace "Sannu Abba, kanajin zafi yanzu?" Girgiza mata kai yayi, Bece komai ba Momy tasa hannu ta kamashi yasauko daga gadon, su Usman suka riqoshi suka futo daga asibitin Suna hanya yadaga kai yakalli momy yace "Momy" Kallansa tayi, "na'am Abba" Yace "Momy nasha wahala bazan sake dawowa garin nanba" Murmushi Momy tayi "a a Abba karka ce haka mana, kaida nakeso duk wata kana zuwa kana duba Nihla" 🤣 Nihla ta kalleshi tasaka daria, shima Kallanta yayi yadauke kansa, amma baiyi mata ko murmushi ba Suna zuwa kofar gidansu Nihla tasake saka daria, Abba yajuyo ya kalleta, su kuwa su Momy da Diddi rabuwa sukai dasu suka shige gida Yace "me kikewa daria?" Saida tasake yimasa daria sannan ta kwaikwayi maganarsa tace "Momy nasha wahala bazan sake dawowa garin nanba" Haushi tabashi sosai,beyi wata wataba yasa hannu ya tureta tafadi aqasa Da gudu ya qaraso wajan, tun daga nesa yake kallansu, shima yana qaraso wa yasa hannu yabige Abba yace "me tayima zaka bigeta?" Cikin bacin rai Abba yace "menene ya shafeka? Qanwarkace ko qanwata?" "bansaniba, amma idan kasake tureta, saina rama mata" yana fadar haka ya tsugunnawa yadaga Nihla tatashi tsaye Cikin fishi Abba yasa hannu ya fizge hannunta yace "cika mata hannu!" Shima dayan cikin tsawa yace "bazan cika ba!" Lokaci daya ransa yaqara baci, ya kalli Nihla batare dayace mata komaiba ya shige gida Itama dayan ta kalla tace "yusif..." Kafin taqarasa maganar da zatayi yace "karkiyi kuka, idan yadakeki ki fadamin Zan rama miki kinji?" Daga masa kai tayi, sannan tashige gida Tana shiga taga Diddi tana ha'bo, Abba yana zuba mata ruwa abuta, bata wani damuba saboda tasaba ganinta ta nayi, rana d'ai'dai ne Diddi bazatai ha'bo ba, Dan haka hauka irinna yarinta dakuma gani yauda kullum yasa bata damu sosai ba, wajan Momy ta nufa tafada jikinta tace "Antyyy" 🤣Girgiza kai Momy tayi, har cikin ranta bataso antyn nan da Nihla take fada, sotake tadinga kiranta Momy Kamar yanda sauran yaranta suke fada, har zatayi mata magana saita fasa Diddi nagama wanke fuskarta suka dawo tabarma suka zauna, Abba yace "Sannu Diddi, idan na girma Zan kaiki asbiti" Daria Momy tayi, "wannan girma wannan girma, zamu gani dai, ga umara ga hajji, yau kuma anqara da asbiti 🤣" Diddi na goge fuskarta da gefen zaninta tace "kuma insha Allahu duk saiya cikasu" Momy tayi daria tace "muma haka mukeso aisha, wai dama har yanzu kina wannan ha'bon naki? Aisha yakamata kije asibiti fa kiga Babban likita akan haka, kina zubar da jini dayawa" Murmushi Diddi tayi "Anty Rahma kenan, to Tun muna yara mukeyi nida yaya, saide ni nafishi yi, kuma Tun umman mu tanada rai muke zuwa asibiti, maganin dai dayane ake bamu, kuma anan ma inashan irinsa, amma bandainaba, shiyasa nake yanka albasa ina shaqar qamshin nata, shima yana maganin ha'bo sosai" Farouq najin haka yace "to Diddi bari na yanka miki yanzu ma, yatashi yadauki wuqa yanufi wajan da take ajiye albasa" Nihla ta kwaikwayi Abba tace "Sannu Diddi" 🤣 Kallanta yayi yasakar mata harara, yadauke kansa, Momy tana kallansa, cikin ranta tace to da alama sunyi fada 😃 Saita kalli Diddi tace "to Allah yasawaqe aisha, amma Zan sake yiwa yayanki maganar gaskiya,abin yayi yawa" Babu musu Diddi tace to, Dan itama abin yana damunta, wani lokacin tana bacci zataji jini yana futowa daga hancin ta Har dare, Abba Yaqi kula Nihla, da niyya take tsokanar sa amma saiya shareta, idan ya tuna abinda yafaru dazu a kofar gida shida wannan gayan sai yaji haushi ya kamashi 🙊 Shiyasa itama yarabu da ita, da daddare ma ko kallan Inda take baiyiba, ita kuwa bata fasa tsokanar saba, har sukayi bacci Washe gari da yamma sunata shirin tafiya, Nihla duk tayi shiru bataso sutafi, har direba yazo yagama zuba musu komai nasu amota, kowa yayi wanka ya shirya, dukansu qananun kaya suka saka Momy ta kalli Diddi, "to Aisha zamu tafi" "to Anty Rahma Allah yakaiku lafiya, idan kinje ki gaida kowa," Momy tace "to yayanki fa?" Daria Diddi tayi, "harda shi Anty Rahma, ki qara yimasa godia, ki gaishe shi sosai" Tace "to zaiji, yanzu Aisha Allah bazaki bani Nihla ba?" "Anty Rahma rigima, sokike na zauna nikadai agidan de" 🤣 Momy da taga alamar Aisha bazata iya rabuwa da Nihla ba, sai tayi shiru kawai, suka futo, har kofar gida suka rakosu itada Nihla, suka tsaya daga bakin kofa suna kallansu Yaran kowa yashiga Mota, Nihla tanata kallan Abba, shima ita yake kallo, lokaci daya idonta yayi rau-rau, tasaka kuka tace "Diddi zasu tafi" Hannu Diddi tasa tashare mata hawaye, jikin Abba ne yayi sanyi, Dasauri yabude motar yafuto, duk 'yan uwansa suna kallansa, har gaban Diddi yaje, ya tsugunna agaban Nihla yace" kiyi shiru, kefa qawata ce, You're my friend " Kallansa tayi ta daga masa kai alamun to Saida ya kalli Diddi, sanan yamatso da fuskarsa daidai tata, yasakar mata kiss akumatu Zaro ido 😳Nihla tayi tana kallonshi, kafin tayi magana yajuya ya shige motarsu da gudu Qamewa Diddi tayi a tsaye, Abba datake ganinsa shiru shiru shine yayiwa Nihla haka? 🤔 Momy kuwa murmushi tayi, tace "Allah ya kyauta" 🤣 Sannan tayiwa direba umarni yaja motar sutafi Cikin gida Diddi tajuya tashige, tana tunanin wani abu aranta Nihla kuwa qin shiga gidan tayi, tazauna akofar gidansu tana wasa, Kamar daga sama taji maganarsa "Nihla, mekike yi anan kinyi shiru?" Kallansa tayi, lokaci daya tasaki murmushi, "yayunane suka tafi, nikuma banaso sutafi " "haba? Yaushe suka tafi? Kinsan garin da suka tafi?" Girgiza kai tayi, "nima bansan garin su ba" Hannunta yariqe yace "zomuje gidanmu muyi wasa" Gidan dayake kallan nasu gidan ta kalla, hadaddan gida ne daya gama haduwa, harda beni, tace "to Muje" Janta yayi suka shige cikin gidan, har falonsu suka shiga Nihla sai kalle kalle take, mamansa tana zaune tana kallo, falon ya tsaru iya tsaruwa Kamannin Ibrahim Mai hakuri da tagani a fuskar yarinyar hakan ya tabbatar mata da cewa yarinyar Diddi ce Wajan ta suka qarasa yace"Ummah kinga qawata, sunanta Nihla, Acan gidan take naje na kirata zamuyi wasa " Murmushi tayi, tashafa kan Nihla tace" a a masha Allah yanmata, to kuje kuyi wasan, banda fada kunji ko " Dakinsa yakai ta, nan taga kayaiyakin wasa iri iri, nan take suka fara wasansu, yana koya mata abinda bata iyaba ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Har bayan sallar isha'i Nihla bata dawo gidaba, Diddi tayi neman ta harta gaji, haka ta tsaya akofar gida tana Tambayar duk Wanda taga yazo wucewa ko yaga Nihla, amma Babu Wanda yace yaganta Umman yusif tazo rufe window tana daga saman beni, hango Diddi a tsaye akofar gida Saukowa tayi tafuto wajan ta sameta, Diddi tace "a a Hajiya, ina gajiya," Tace "lafiya kalau, da alama de Nihla kike nema" Dasauri Diddi tace"wallahi ita nake nema hajiya, Tun yamma ban ganta ba, " Murmushi tayi tace" ai tana gidana, sunata wasa da yusif Yarona, yanzu kam nayi musu shimfida ma sunyi bacci " " to bari naje nadauko ta hajiya, kar babanta yadawo begantaba " " haba Diddin, ki barta mana, dasafe sai akawo ta " Murmushi Diddi tayi, cikin ranta tace nagode Allah, kowa yana qaunar 'yata, afili tace" Hajiya ai wataran zata kwana, ina Ruwan yara "🤣 Badan tasoba, suka shiga gidan, Diddi tanata yaba haduwar gidan, Dan bashiga takeba, amma gashi yau wannan yarinya takawo ta Baccinsu suke hankali kwance, ga esi nan yana sanyaya musu jiki, haka Diddi tasa hannu tadauketa, suka tafi gida, tanata yiwa Maman yusif din godia (idan naga ana Comments Zan qara yawan page d'in) WhatsApp readers, ina qara godia sosai yanda kuka bani hadin kai, kuka bani lokacin ku wajan karatu da kuma sharhi, ana mugun tare🤪 Amnah El Yaqoub ✍️ [6/15, 2:27 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️ {Romance & Friendship luv} Writing by Amnah El Yaqoub Like my page On facebook https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 7&8 Zaune suke acikin Babban falonsa dayake tarbar baqi, Babban falo ne daya hada komai da Komai najin dadin rayuwa, tsaki yasaki yakalli Agogon hannunsa fuskarsa Babu alamun wasa yace "me Basiru yakeyi ne har yanzu baizoba, bayan Tun jiya nasanar dashi da kaina cewa akwai meeting karfe tara nasafe" Kafin sauran biyun su bashi amsa aka turo kofar falon aka shigo, kana ganinsa kaga cikakken magidanci, fuskarsa adaure yadubeshi "mekake yi bakazo a lokacin dana sanar dakai ba?" Yace "yaya Abubakar ai lokacin yayi, gani kuma nazo akan lokaci" 🤣 Kai tsaye yace dashi "duba agogo karfe nawa?" Kallan Agogon dakin yayi "goma da rabi" Fuskarsa adaure yace "kuma karfe nawa nace kazo?" "karfe tara kace, aini to inajin agogo nane yasamu matsala, karfe tara ya nunamin wallahi, inajin matsala yasamu, duba kagani" ya qarasa maganar yana nuna masa hannunsa Harara ya watsa masa yace "lusari, Wanda mace tagama shanye shi" Shiru falon yasakeyi, ba qaramin girma suke bawa Babban yayan nasuba, hakan yasa Wanda aka kira da lusari baice komai ba, yanemi waje Yazauna Gyaran murya yayi yace "munyi magana da hajiya dangane da wani abu Mai girma Wanda ni kaina bansan menene ba,...." nan take ya sanar dasu yanda sukai, sannan yaqara cewa "nasanar daku ne saboda nima korai zaiyi halin sa," Hajiya Farida datake zaune, wadda ita kadai ce mace acikinsu tace "Amma yaya Abubakar meyasa ba'a fadawa Aisha ba? Itama fa tanada 'ya, kuma 'yarta tana daya daga cikin wannan family, Kamar yanda Iyayenmu suka bada wasiyyar dabamusan kota mecece ba akan yaranmu, ai yakamata ace tasani" Kallanta yayi fuskarsa adaure "da Aisha da abin data haifa duk suna qarqashin iko nane," Jinjina kanta tayi, sannan tasake cewa "to amma yaya ai yakamata ace munjata ajikin mu, Kamar yanda aka fadawa yaya Basiru itama..." Kafin ta qarasa magana yadaga mata hannu tareda fadin "Farida!!!" Lokaci d'aya ta nutsu Kamar ba itace take zuba surutu ba, kallansu yayi yace "daga yanzu kuma daga rana irinta yau, doka zata fara," yana fada musu haka yatashi yafice, yabar kowa da tarin tambayoyi, Alhaji Baqir yatashi yana gyara Babbar rigar jikinsa yace "koma menene bazai wuce maganar rabon gado ba, ni wannan bata gabana," shima yafice daga falon 🤣 Hajiya Farida ta kalli Agogon hannun Basiru dayake zaune kusada ita batare daya saniba, taga karfe tara da kwata, ta kalli Agogon dake manne afalon taga goma da arba'in da biyar, tasaki daria tasan sarai aikin matar sa ne wannan, wadda ya Auro musu ita tazame musu baragurbi acikin family, Kallanta yayi "me kikewa dariya?" Tace "yaya Basiru Babu komai, nina wuce gida sai anjima" 🤣 Daganan shima yatashi yadoru a bayanta yana darurar sanar da matar sa abinda yaya Abubakar yace ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Labarinsu Mazawaje family Babban family ne dayake da tarin mutane dayawa, Abubakar shine jigo na wannan family yanada mata biyu Hauwa'u dakuma Fatima Hajiya fatima itace babba, tanada yara biyu, Babban danta shine Yaci sunan babansa Wato Abubakar, sai qanwarsa Aisha, sun taso sunasan junansu sosai da sasai Sai Hajiya Hauwa'u, wadda suke kira da hajiya sak, tana da yara uku, Baqir shine Babban danta, sai Basiru da kuma qaramar su Farida Abubakar yayi aure ya auri daya daga cikin family dinsa na uwa, maisuna Rahma, suna zaune lafiya saide murdaddan halin sa datake hakuri

Chapter 2 of 24