Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yazube awajan yana fadin" Innalillahi wa inna ilaihir raju'un... " 🤔Um jama'ah rikicin Mazawaje family naga alama ba qarewa zaiyi ba saide mu taqaita, nagaji wallahi, yakamata mu huta haka, kuma zaku Dan huta da Comments, Mutara zuwa jibi ko gata insha Allah, nagode 🙏🏻 Amnah El Yaqoub ✍️ [7/10, 1:36 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI DAYA❣️ {Romance&Friendship luv} Writing by Amnah El Yaqoub Like my page On facebook 👇 https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-10548777110149 45&46 'Da uwa sai Allah, tausayin Abba yakama Momy, ta kowa tafarayi Ahankali zataje wajansa, saikuma ta fasa tajuya cikin dakinta itama saboda bataso yaran su fahimci cewa tasan abinda yafaru atsakaninsu Agefen gadon ta tazauna tafada duniyar tunani, ada kam abinda tasa aranta shine koda Nihla ta amincewa Abba itada kanta zatasa karta amince, to ashe awajan Nihla itama hakanne, ashe bata son Abban a yanzu, ashe tunanin ta qarya yake bata,da gaske yarinyar bata qaunar Abba, amma yaya zatayi? Tanajin Nihla acikin ranta Tun tana qarama, tanajin ta Kamar yarta ta cikinta, ba zatayi mata dole akan Abba ba, dole zasu bata haqqinta, tazabi Wanda ranta yakeso, hakan shine adalci, amma Abba Babu kunya yakama yarinya yana mata kiss? 🤔 Baya tsoron tazo wajan ko Daddy Nihla nashiga daki tashare hawayen idonta, tafara cire kayan jikinta domin ta watsa ruwa,akan gado tazubar da kayan nata, daga ita sai towel tashige wankan, kokadan bataji tausayin ya Abba ba, koma menene shine yajawa kansa acewarta Abangaren Abba kuwa awajan Yazauna yadafe kansa, idonsa sunyi jajir tsabar kuka, bai taba tunanin cewa watan watarana zaiyi kuka akan soyaiya ba, amma gashi na farko yayi kukan Baqin ciki akan Nadiya, yanzu gashi yana kuka na biyu shikuma kukan nadama akan Nihla, ahankali yatashi tsaye jiri yana dibansa, yashige cikin dakinsa, akan gado yafada yadauki wayarsa yakira Aslam, bugun farko Aslam yadaga yace "Abba yane" Cikin muryar kuka yace "komai yaqare Aslam..., komai yazo qarshe, tace bata sona" Aslam yayi shiru Kamar an doka masa sanda Yasaki ajiyar zuciya yace "Abba wannan shine abinda nake gujema Tun farko, meyasa zakayi magana Awannan lokacin? Yanke hukunci cikin fishi banaka bane, a lokacin Abba Kowama yana jin abinda kake ji, duk cikin mu Babu Wanda yake son wannan hadin da akayi mana, amma haka mukai shiru, amma yanzu de kayi hakuri, nasan cewa Nihla zata soka" "bazata soniba Aslam, yarinyar nan har tsugunna mata nayi nabata hakuri, amma taqi yafemin, saima laifukan dana aikata mata abaya tasake maimaita min, Aslam tayaya zata yafemin idan tana tuna abinda nayi mata? Yanzu shikkenan mutum bazai iyayin kuskure ba a rayuwa kuma yadawo ya gyara? " " Abba!!, kaima fa abinda kayiwa yarinyar nan bashida dadi, dole zata tuna, saide Ahankali ta Manta " Cikin hawaye yace" kuma sai tace bazai iyu tasoni ba " " kayi hakuri Abba, amma ka denayin kukan nan, insha Allah nima Zan tayaka addu'ah zata soka, mu miqa lamuranmu ga Allah, shine kawai mafita " " Aslam bazata soni ba, tsanata nake gani qarara akan idonta, wallahi idan taqi aure na Allah saina saceta "🙆🏻‍♀️ 😳Zaro ido Aslam yayi" a a Abba ba za'ayi hakaba, babu maganar sata, mubi komai Ahankali " " wani fa takawo gidan Aslam, agabana take masa murmushi, Allah idan yasake zuwa wajan ta saide ayi biyu Babu, zan kasheshi nima nakashe kaina tunda haka takeso " Aslam yayi Murmushi, Abba da kishi sai Allah, afili yace" Abba, kayi hakuri, kaci gaba da bata haquri, amma kasan abinda zamuyi yanzu? Mufara gyara sama tukunna, Abuja zaka shirya Muje munemi mahaifin ta mufara bashi hakuri, sai aci gaba daga inda aka tsaya "🤣 Jan zuciya yayi yace" shikkenan " qit ya kashe wayar Ilham ta dafa Aslam tace" meyake faruwa ne? " " nida Abokina ne, yanason qawarki sosai amma tana bashi wahala, yayi laifi yanaso ya gyara laifukan dayayi mata amma taqi bashi damar hakan, yanzu abnda yake fadamin har tsugunna wa yayi a gabanta yabata hakuri amma taqi yarda " Ilham ta zaro idonta cikeda mamaki tace" ya Abban? " " shikuwa, ai soyaiyar Nihla nema take tahaukatashi Kamar yanda taki ta haukatani, kika hanani kallan ko wacce mace " Murmushi tayi tace " ya Aslam kenan, amma ina tausayin ya Abba gaskiya, Dan Nihla koda yaushe muka hadu sai munyi mata maganar sa, amma sai takawo maganar saurayinta " Cikin damuwa Aslam yace" akwai damuwa de gaskiya, Allah yashiga cikin lamarin kawai" "amin" cewar Ilham ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ After one week Kwance suke akan gado, ta dora kanta akan qirjinsa, yayinda hannunsa yake kanta yana shafa mata, yace "Baby Dida kinga maganin nan na ummah wallahi yayi kyau sosai, gashi yanxu shiru kake ji Babu kowacce damuwa" Idanunta a lumshe tace "Um, Allah yakiyaye gaba, amma ai zamuci gaba da sha" Yace "to, duk yanda kikace haka za'ayi" Kanta ya daina shafawa yatura hannunsa cikin blanket din dasuke ciki yana shafa qirjinta, rabuwa tayi dashi yana abnda yakeso, amma da aka jima taga abinnasa bana qare bane, kawai saita fara masa kukan shagwaba "ya Fawaz yanzu fa kagama, nide Dan Allah muhuta..." "Baby Dida kadanfa Zan qara, bazan dadeba kinji" "naji, amma gaskiya daga wannan shikkenan ko" Murmushi yayi yace "um inajin" Itama Murmushin tayi masa daganan suka lula duniyar Ma'aurata ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Zaune suke afalo itada Momy, wayarta tayi qara, tana dubawa taga baba ne, cikin girmama wa tadaga suka gaisa yace "Yusif yazomin da wata magana yace kece kika bashi dama yazo muyi magana ko?" "eh baba nice nace yayima magana" "to yamin magana, amma kuma yace kinfada masa wai saikin kammala service tukunna, menene abin jira Nihla, tunda Allah yakawo miji kawai ayi aure, auren ki na farko matsala ce tasa ba'aiba, amma yanzu tunda gashi kinsamu ilmi ai Babu abinda zamu jira, amma mahaifin Yusif din baya nan, idan yadawo daga tafiyar dayayi zamuyi magana akan hakan insha Allah, idan ma aurenne sai ayi, inyaso saiki qarasa service din agidan mijinki " " to shikkenan baba, Allah yasa hakane yafi alkhaairi, " " amin, Allah yayi miki albarka ki gaida su hajiyan " " to baba zasuji " Tana kashewa ta kalli Momy tace" Momy nida baba ne, yana gaishe ki, maganar Auren ya yusif yayi min, Momy nida nafiso saina gama service dina, amma shi baba yace wai basai nagama ba kawai zasuyi magana da babansa, su tsaida magana daya " Tun lokacin da al'amarin Nihla da Abba yafara wakana, Momy bata taba Jin faduwar gaba irinna yauba, jikinta yayi sanyi, Nihla de da gaske take tarabu da Abba Yusif din takeso Murmushi ta qaqaro tace" Alhamdulillah, to Nihla ai hakan yafi, menene amfanin jira yata, abinda Mai hakuri yafada gaskya ne, aide kina sonsa ko? " Momy tayi Tambayar tana zubawa Nihla ido ko zataga yanayin ta ya sauya amma saitaga Babu damuwar komai akan fuskarta Saima kanta data daga alamar eh tanaso Murmushi tasakeyi, kafin tayi magana yaturo kofar dakinsa yafuto yayi mutuqar cikin suit kalar ash, qaraso wa yayi Yazauna akan hannun kujerar da Nihla take zaune 🤣 Yasa hannu yadauki Ruwan da yagani ansha, yazuba a cup yafara sha Ahankali, Nihla sai matsawa take gefe, tarasa wannan abu na ya Abba, duk kujerun falon sai akusa da'ita zai zauna, wayarta tabude tashiga chatting tanayi Shikuwa yana shan ruwa hankalinsa yana kan wayar tata, jikinta ne yabata ana kallonta, danhaka tashiga cikin chat dinta itada ya Yusif tayi sallama daganan bata jira komai ba tafara tura masa da kiss💋💋💋 Wani irin qullutun Baqin ciki ya tokarewa Abba wuya, ahankali yaji Ruwan dayake sha yafita daga ransa Yusif kuwa baya rufe datar sa, yana ganin saqon Nihla yadoko mata kira Nanma akan idon Abba kiran yasake shigowa, murmushi tasaki sannan tayi cikin dakinta tana amsawa wayar Abba yabita da kallo ransa abace, Momy ta kalli yanayin sa, tace "Abba na sai ina?" "Momy zamuje Abuja ne nida Aslam" "Abuja kuma? Wajan wa? Me akeyi?" "Momy wajan baba Ibrahim zamuje mugaidashi" Tausayinsa yakama Momy, tasan duk saboda Nihla zaiyi hakan, taji dadi aranta tunda yau Abba zai gyara kuskuren daya aikata, tace "to sai kundawo" Daga nan tatashi, tsaye tayi hanyar dakinta, Abba ya kalleta dakyau yaga jikinta yayi sanyi, Kamar akwai abinda yake damunta yace "Momy bakyajin dadi ne?" Juyowa tayi "lafiya ta kalau Abba, kaina ne yake ciwo kadan" "Momy ko mutafi asbiti?" "A a Abba na, karka damu ai Nihla tana nan" Yace"To shikkenan Momy, Allah yasawaqe " Momy tashige dakinta tafada duniyar tunani, tunda Nihla tayi mata magana akan sunyi maganar Yusif da babanta shikkenan ta saddaqar Nihla bazata auri Abba ba, bazata auri danta ba, ahankali tatashi tasha magani, sannan ta kwanta Abba kuwa dakinsa ya koma yadauko wayoyinsa, yana futowa daga dakin yaga wayar Nihla akan kujera, mamaki ya kamashi, yaushe tadawo falon? Hanyar kitchen yanufa yaleqa kansa yaganta a kitchen tana kokarin kunna gas Bece da'ita komaiba, ya koma falon yadauki wayar tata batare da tunanin komai ba yahadata da bangon falon ya doka, nan take wayar tafashe tayi raga-raga🙆🏻‍♀️ Yajuya yafice daga falon, yahau Mota yanufi gidan Aslam ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ "congratulation Adam, matarka tana dauke da juna biyu Tsawon wata uku" Adam yasaki murmushi yace "Doc da gaske kake?" "qwarai kuwa, haka bincikenmu ya nuna, sannan wannan zazzabin datake fama dashi da amai, insha Allah zata denaji, karkuma kuyi wasa da bata magungunan da aka rubuta muku" "insha Allah Doc. Nagode sosai" Kallan Diyana yayi da aka yiwa qarin ruwa, tana bacci, saida Ruwan yaqare sannan yakira Doc aka cire mata, sukayi shirin tafiya gida Kamota yayi ya rirriqe yana ta mata sannu, ta kalleshi tace "ya Adam sai farin-ciki kake, bayan kuma kasan banda lafiya" "aidole nayi farin ciki maryam, kinsan me Doc yace kuwa?" Shiru tayi masa, Dan a tunanin ta baidamu da rashin lafiyar tata bane, Motar tabude tashiga, shima yashiga sannan tace "ina Zan sani saika fada" Cikin murna yace "to cemin yayi matata maryam tana dauke da Baby na acikinta na wata uku" Cikin sauri ta kalleshi tace "da gaske?" "sosai ma kuwa, bari mu koma gida nakira su Aslam da mama nafada musu" "yanzu ni ahakan ciki ne dani?"🤔 "maryam kenan kina mamaki kenan, aike yanzu kin zama sarauniya maryama sai abinda kikace" Shiru tayi masa tazuba masa ido tana kallan yanda yake farin ciki, Allah sarki ya Adam, rayuwa kenan ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Kasancewar jirgi suka biyo ko awa daya basu yiba suka sauka,baba yayi mamakin zuwan su Tun lokacin dasuka kirashi awaya Afalon gidan aka saukesu, mamy takawo musu abin motsa baki suka gaisa dasu, sannan ta basu waje Sosai suka gaisa da baba, Inda suka sake bashi hakuri akan abinda yafaru abaya, baba ya nuna musu Babu komai dama basune sukai masa laifin ba, amma komai yawuce insha Allah Yusif ne yashigo falon yayi kyau cikin qananun kaya Baqin wando da farar riga an rubuta handsome agaban rigar Ido biyu sukai shida Abba, kowa ya kawar da kansa Tunani Abba yafara, kenan gida daya take rayuwa da wannan gayen, shima Yusif din anasa bangaren tunani yake menene yakawo wadannan gidansu Ahankali yaqaraso wajansu yamiqa wa Aslam hannu suka gaisa Sannan yabawa Abba hannu yana kawarda kansa gefe Shima Abban kansa ya kawar gefe sukai musabaha ahaka 🤣 Baba yayi shiru yana kallon su, gaisawa suke amma kowa fuska adaure, kuma kowa ya kawar da kansa basa kallan junansu To tabbas da wani abu aqasa, duk yanda akai yarannan sunsan juna, sannan shi Yusif yayi masa maganar Nihla, ga kuma Abba shima yazo domin gyara laifin dayayi abaya, da alama shima da wani abu a tsakaninsa da yarinyar, to daga nanfa baba yafara tunanin akwai matsala Suna gaisawa dasu yawuce dakinsa, suma su Abba basu jimaba suka dauki hanyar Airport domin komawa kano ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Azaune take aqasan kafet din dake malale acikin qayataccecn falon na Momy datafe kanta da hannunta guda daya tana kuka, dayan hannun kuma ta riqe fashshiyar wayarta dashi, ba fashewar wayar ce tasa ta kukaba, Information dinta dayake ciki takewa kuka, saboda idan waya ce akwai Sabuwar da ya Yusif yakawo mata, kuma akwai tsohuwar wayarta ta farko duk suna nan Allah ne yakawo su Usman gidan gaba dayansu Ya Aliyu ya kalleta yace "Momy me aka yiwa wannan yarinyar ne take kuka?" "wallahi Aliyu futowa mukai falon nida ita shine mugaka wayarta afashe, shine take kuka" Ya Usman yace "subhanallah... To garin yaya ta fashe Momy?" "yaya ma za'ai kayimin wannan Tambayar Usman, Abba zai fasa mata wayar nina sani" Farouq yace "haba Momy, ya za'ai yafasa mata waya, Abba bazai yi hakaba, da hankalin sa dakomai yazaiyi yafasa mata waya" Momy tace "a a Farouq rabu da shiru-shiru, rabu da shiru-shiru farouq, dukanku nice na haifeku Babu Wanda bansan halinsa ba acikinku, nafada muku Abba ne yafasa wannan wayar" Suna wannan zancen yashigo cikin falon, yayun nasa yagaisar sannan yace "Momy nadawo" Momy tace "naganka ai Abba" 🤣 Ya Usman yace "Abba meyasa kafasa wa yarinyar nan wayarta, saboda me haka kawai zaka fasa waya?" Juyawa yayi ya kalli Nihla datake goge hawayen idonta, haushi ya kamashi, saboda yafasa wayar da saurayinta yake kira shine take wannan uban kukan Yamaida kallansa ga Usman yace "ya Usman ni ban fasa mata waya ba" yanemi waje Yazauna yana cire jacket din saman suit din jikinsa Momy tace "Abba, nasan halin ka sarai, idan bakaine ka fasa mata wayaba waye zai fasa? Adala bata nan, dagani saikai sai ita dakuma Daddynku, mune zamu fasa wayar kenan?" Cikin kishi dakuma wata irin murya Kamar zaiyi kuka yace "to Momy meyasa zata dinga waya dawani can, bana fada mata banaso ba" Hawaye suka zubowa Nihla ta kalli Momy tace "Momy ai kinji shi ko? Allah saiya biyamin wayata" Tashi yayi tsaye ya kalleta, ya girgiza kansa, sannan ya sunkuya yadauki wayarsa da jacket dinsa daya cire yayi hanyar dakinsa To,ko Alhaji Abubakar zaibawa Ibrahim hakuri akan abinda yafaru abaya? Yaya labarin abdallah qanin Nadiya ne? Anya kuwa zai iyayin shiru akan abinda yagani dangane da Abba da Nihla? More Comments more typing....👌🏻 Mrs Usman ce ✍️ [7/11, 12:19 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️ {Romance&Friendship luv} Writing by Amnah El Yaqoub Like my page On facebook 👇 https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493 47&48 Momy tayi zuru da ido tana Kallonsa, gaskiya ne karabu da miskilin mutum, ka kalleshi kawai, kagama yiwa yarinya kuka ka matseta kayi kissing dinta amma kaduba kaga Kamar bashi ba, kome yataka oho? Usman yace "Nihla kiyi hakuri kidena kuka kinji, zanyi masa magana saiya nemo miki waya wayar, kiyi shiru" Ahankali yatashi yabi bayan Abba, zaune ya sameshi yayi tagumi hannu bibbiyu, zama yayi a gefensa "Abba!, meyasa zaka fasa mata waya, tayaya zata soka ahaka Abba?" Kallan yayan nasa yayi, qwallah tacika idonsa, bai iya boye waba danhaka yabasu damar zubowa, jikin ya Usman yafada, cikin hawaye yace "yaya ashe kowa yagane halinda nake ciki? Yaya zanyi da soyaiyar ta yaya?" Usman ya shafa kansa "kadena kuka mana" "dama wannan shine abinda muke gujema tunda farko" Aliyu daya shigo dakin yafada Gaba dayansu suka daga kansu suka kalleshi, farouq ma yashigo dakin sannan Yarufe Zama sukai duk su hudun, Aliyu ya cigaba da cewa "yanzu wa gari ya waya? Kai taurin kai gareka Abba, yarinyar nan kowa yasan tasoka, amma ka Qita, tayaya zata soka yanzu?" Hawaye suka zubo daga idanun Abba, Usman yace "Abba na hanaka kukan nan, kuka bazai kawo mafita ba" Cikin hawaye yace "ya Usman kabarni nayi kukana, cewafa tayi batasona, kuma bata barni hakaba saita dinga kula wasu" Dariya takama farouq, bai boye ba yasaki dariyarsa 😃 Wani irin haushi yakama Abba, yazuba masa ido yana kallansa batare dayayi magana ba Saida farouq yagama dariyarsa yace "wallahi banga laifin Nihla ba, gara ta gwaraka ka gwaru" Cikin haushi yace "Aidama nadade da sanin sonta kakeyi, ai shikkenan" Farouq yayi Murmushi yace "ahhh ina son Nihla,wayace ka Qita? Lokacin dakace baka sonta nace Zan aure ta kaji haushi nane? Sai yanzu dakake sonta ne zakace ai dama kasan ina sonta, a a ina auren ta" "dan Allah kuyi mana shiru munemo kanmu mafita" cewar Aliyu Gaba dayansu kuwa sukai shiru, ya Usman ya kalli Abba yace "Abba kishi banaka bane, ka lallabata kagane? Kabata kulawa, kuma ka sameta kasake bata hakuri, kai Abba inta kama ma saika tsugunna a gabanta ne, to kayi inde hakan zaisa tahuce" "ya Usman har hakan fa nayi mata taqi yarda" Aliyu da farouq suka saki murmushi, lalle Abba da gaske yake Shima ya Usman din murmushin yayi yace "naji, kaci gaba da bata hakuri, insha Allah wani lokacin zata hakura" Aliyu ma yace "yawwa kuma naga Kamar Momy ma tanabin bayanta, yakamata kasamesu itada Daddy kuyi magana, amma wannan fishin naka akan ankirata awaya Babu Inda zai kaika" Haka yan'uwan nasa suka sakashi agaba sunayi masa huduba, dakuma shawara akan abinda zai kawo musu mafita ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Zaune yake agaban iyayen sa,acikin dakin Daddy, kansa aqasa, Momy tana zaune agefen Daddy, yayinda hankalin Daddy yake kan news din da akeyi Saida aka gama sannan ya kashe, yajuyo ya kalli Abba yace "Abubakar muna jinka, kazo kace akwai maganar dakake so muyi, amma kayi shiru" Gabansa ne yafara faduwa, yarasa ta Inda zaiyi wa iyayen nasa bayani Momy tace "kayi shiru Abba" Ahankali yadago kansa ya kallesu sannan yasauke idonsa cikin sauri,"Am.. Daddy dama.... dama inaso ne infada muku inason yin aure" Murmushi ya baiyana a fuskar Daddy, amma Momy kuwa Kallonsa tace, tanaso taji yafadi abinda ta dade dasani Daddy yace "wacce Abba? Alhmdllh ashe de kaji fadan damukai ma" Ahankali yadaga kansa alamar yaji Momy tace "to Wacece? Ko wata yar Abujan kasamu?" Kallanta yayi ya girgiza kansa alamun a a Daddy yakalli Momy yace "ikon Allah, kinga yau Abba kunyar mu yakeji" Momy tayi Murmushi batace komai ba Daddy yace "to a wanne garin take? Saina tura su Alhaji Baqir suje su nema ma auren ta, Wacece?" Karon farko da Abba yaji tsoron mahaifin sa, gabansa sai faduwa yake, jikinsa yayi mugun sanyi, har wata irin karkarwa yakeyi Ahankali yadago kansa ya kalli Daddy yace "Nihla ce Daddy" Lokaci daya, annurin fuskar Daddy ya dauke Yamiqe tsaye yace "zancen banza, zancen wofi, Abubakar ashe bakada hankali bansani ba?" Yasake maida kallansa wajan Momy yace "toke Rahma idan kin gama sauraren abinda yake fada, saiku tattara kufita, nima zanje daki nahuta" yana fadar haka yafara takawa zai tafi dakinsa Caraf yasa hannu yariqe kafar mahaifin nasa, kansa aqasa, amma yakasa Dagowa, Daddy jin anriqe masa kafa yasa ya tsaya cak, hawaye ne yake disowa daga Idanunsa, numfashin sa yafara sama sama Kamar Mai Asma, yasaka hannunsa daya ya goge, yayinda dayan hannun yake riqe da qafar Daddy Ahankali yadago kansa ya kalli Daddy yace "Daddy please, Dan girman Allah Daddy kayi hakuri kuyafemin irin laifin danayi abaya, Daddy ka tausayamin wallahi ina sonta...." ya qarasa maganar yana sakin wani irin kuka Mai cin rai Daddy yajuyo ya kalleshi yace "Abba!, kalleni nan, niba mutumin banza bane, kuma niba qaramin yaro bane dazaka raina wa hankali, saida kasa natara mutane agabansu ka nunamin ban isa dakai ba, yarinyar nan akan ka aure ta kazabi karbar Mazawaje family, sai yanzu zakazo min da wata irin magana, kaga da Allah, tashi kafice kabarmin dakin nan indena ganinka " Ahankali yamiqe yadafe kansa dayake masa muguwar sarawa, yakalli Momy da jikinta yayi sanyi yace" Momy, Dan Allah Kibashi hakuri, kuyi hakuri Momy wallahi zuciyata zafi takemin, Momy inason Nihla " Momy tace" Abba ai lokaci yaqure ma, Nihla akwai wanda takeso, sannan mahaifin ta yayi magana da ita akan hakan, kaine ka janyo koma menene, katashi kafice kawai, banason maganar banza " Hawaye yasake zubowa Abba, shikkenan Babu wani Mai goyon bayansa kuma, tunda Momy ma tace haka to Babu Wanda bazai iya juya masa baya ba Duhu duhu yafara gani, ahankali yafara takawa sai jiri ne yake dibansa, hannunsa yana dafe da kansa, haka yatafi yabar falon na Daddy yana tafiya yana hada hanya Hawaye ya zubowa Momy, tana tausayin Abba sosai amma dole zataso yagane dai dai da abinda ba dai dai ba Cikin sauri tatashi zatabi bayansa Daddy yace "Karki kuskura kije Inda yake, kinji nafada miki" Yana fadar haka ya juya yashige dakinsa ransa duk abace Momy ta zube akan kujera tana sakin wani irin kuka Mai ciwo Jikin bango yakebi yana tafiya Kamar Mai koyon tafiya, sakamakon duhun dayake gani acikin idonsa, da haka ya qarasa dakinsa yazube akan gado yana sakin kuka sosai abaiyane, nan take wani irin zazzabi Mai zafi ya rufeshi ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ "Abdallah yakirani awaya yafadamin komai, meyasa kika boyemin gaskiyar ke Wacece Nihla?" "Anty Nadiya... Dan Allah kiyi hakuri, wallahi bansan ta yanda za'ai nayi miki bayani ba, Anty Nadiya ya Abba ke yakeso, kuma a lokacin dana hadu dake kuna tare da juna, yana sonki kina sonsa, meyasa Zan rusa muku soyaiyar ku, bazan iyaba, shiyasa nayi shiru ban fada miki alaqa ta dashi ba, duk family dinmu kowa Abba yake cemasa, nahadu dake naji kince sadiq Mazawaje, banyi tunanin shi bane saida kika nunamin pic dinsa, kuma daga lokacin nake sporting dinsa awajan ki, harga Allah banso kikaqi auren saba, saboda banji dadi ba kokadan Anty Nadiya, koma meyayi min shidin dan'uwana ne,nida shi munkance cikin DANGI DAYA, duk da yayi min laifi wallahi banso kika Barshi ba, amma kiyi hakuri Anty Nadiya akan rashin sanar dake dabanyi ba " Ajiyar zuciya Nadiya tayi" nafahimceki Nihla, sai da abdallah yafadamin komai nasan cewa bakida laifi, Sadiq yahadu Nihla Nikaina nasan da haka,ashe ba banza ba kika rikice, Nikaina rashin kulawar sa ce tasa narabu dashi, amma Abdallah yacemin yaga soyaiyar ki sosai acikin idonsa, hakane? " " hakane Anty Nadiya, yafadamin ma, kawai de bazan iya sauraron sa bane, kuma nafada masa " " eto yakamata de yasan darajar ki gaskiya, sai kiyi addu'ah Allah yazaba miki mafi alkhaairi, idan ansa ranar bikin saiki sanar Dani " " munyi maganar ya Yusif da baba ma Anty Nadiya, insha Allah idan ansa Zan sanar dake " " to shikkenan qanwata Mai yan samari, sai munyi waya, kicewa sadiq Nadiya tana gaishe shi "🤣 Murmushi Nihla tayi tace" Babu ruwana Anty Nadiya, kunfi kusa kedashi " Da haka sukai sallama ❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️ Sanye take da atamfa Mai launin pink da brown, dinkin riga da siket ne amma Yazauna a jikinta sosai, mayafi tayafa dan qarami iya gefen kafadarta daya, yayinda data riqe hand bag dinta tafuto daga cikin dakinta, da alama unguwa zataje, adede lokacin shima yafuto idonsa yasauka akanta, tayi mutuqar yimasa kyau sosai, kasa dauke idonsa yayi akanta harta qaraso ta gabansa zata wuce shi batare data kalli Inda yakeba, hannu yasa ya fuzgota, lokaci daya tafada jikinsa, bai jira komai ba yasaka ta cikin qirjinsa ya rungumeta sosai Tudun nashanunta dayakejinsu akan qirjinsa ne yasa ya lumshe idonsa, sannan yaqara matseta tsam ajikinsa, jijiyoyin jikinsa suka fara karbar wani irin saqo, wani irin zirrr yakeji tundaga tafin qafarsa har zuwa kansa, kansa yasake turawa cikin wuyanta yana shaqar wani sihirtaccen qamshi dake tashi a jikinta, bayaso yadena jin abinda yakeji ajikinsa, baiqi ace su dauwama ahaka ba, ahankali yadago bakinsa, yadora Dan qaramin lips dinsa akan kunnanta yana gatsawa Ahankali Wani irin numfashi Nihla tasaki, gabobin jikinta suka saki lokaci daya Motsi tafara tanaso taraba jikinta danasa, cikin shagwaba tace "ya Abba please kasake ni mana, Momy fa zata iya zuwa" Wata irin murya yayi magana da'ita, wadda tunda take dashi bata taba Jin muryar sa hakaba, cikin shagwaba yace "to kice kin yafemin mana please " Ahankali ta zare jikinta daga nasa ta kalleshi tace "ya Abba kenan, kada kadamu, nayafe maka, komai yawuce kaji ya Abba na, duba kaga yanda ka rame, Pls kasaki ranka kaji?" Yace "da gaske kike kin yafemin?" Tace "ya Abba, nace nayafe ma, komai yawuce fa, Muje ka rakani unguwa...." Cikin sauri yafarka daga mafarkin dayake 🤣🤪 Sakamakon qaran wayarsa data tashe shi, a dalilin wani abokin aikinsa dayake kira Kansa yadafe da hannunsa duka biyu ya furta kalmar "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un..." 🤦🏻‍♂️ Jikinsa yataba yaji zafi sosai, ga kansa dake sara masa, zuciyarsa ce yaji tana tashi, cikin sauri yasauko daga gadon yanufi toilet yafara kwara amai, babu komai acikinsa sai riqe cikin sa yake ga ciwon kai, ga zazzabi, haka yadawo ya kwanta agadon, yanzu duk abinda yafaru dama mafarki yake? Ya Allah! Saida yaji dama dama sannan ya koma toilet din yayi wanka, yadauro alwala yafuto, jallabiyar sa yasaka fara qal da ita, sannan yatada kabbarar sallah, yadade yana sallah sannan yadaga kansa ya kalli agogo yaga sha biyu da kwata Ahankali yamiqe, yafuto daga dakin nasa, kai tsaye dakin Nihla yanufa, wannan shine karon farko daya fara shiga dakinta Ahankali yatura kansa cikin dakin, tana kwance agado wayarta da ya yusif ya aiko mata take gani, tana sanye da riga da wando na bacci, wandon ko gwiwar ta baizoba, rigar ma batada tsawo hakan yasa fararen cinyoyinta suka fara futowa Ganin mutum kawai tayi akanta, cikin sauri tatashi zaune tace "subhanallah... Ya Abba lafiya?" Ahankali yake ta kowa har yazo gabanta, ganin yana nufota

Chapter 18 of 24