zata tafi meeting ɗin nasu zai fara 10am. Jidda na kallon Leena tace "je ki fara shirya wa nima barin shirya though zan riga ki fita amma ina so naga wankan ki, Leena ta wuce ciki har Jiddah ta gama ta fito parlor Leena bata fito ba ganin agogo tayi hakan yasa ta karasa bakin kofar ɗakin tayi knocking Leena tace "abuɗe yake" Jiddah ta tsaya kallon ta from head to toe tace "Ma shaa Allah, kin yi kyau a maroon Abayan nan kamar wata bakarabiya" Leena na Murmushi tace "thank youu" Jidda tace "da fah makeup zan Miki amma sai naga hakan ma zaki fi kyau, kar a ɗauka makeup ɗinne ya kara Miki kyau" Ita dai bata ce mata komai ba Jidda tace "toh yanzu zaki tafi ko sai ɗan anjima" Leena ta kalli agogo dake nuni da pass 9am tace "zan bari sai 10am kawai zan fita Jiddah tace "ina ne ma venue ɗin" Leena ta buɗe watan ta tana kallo tace "transcorp Hilton, Abujs" Jidda na gƴada kai tace "iyyee, manya" ta karasa tana murmushi daga haka sukayi sallama Jidda ta fita ta bar Leena da take ta rehearsal ɗin poetry performance ɗin ta. Goma nayi bolt ɗinta ya iso ta fita ta kulle ma jidda gida ta shiga bolt ɗin a daidai bakin Transcorp Hilton Abuja ya sauke ta tun daga bakin gate ɗin take ganin tsaruwan wajan Ma shaa Allah ta furta Manyan motoci ne na gani na faɗa ke parke a layin wasu kuma ta jikin gate ɗin Hilton ɗin wasu kuma a ciki akayi parking Babban banner dake bakin gate ɗin ta kalla wanda yake ɗauke da wannan rubutun *Event Name:* "Abuja Economic and Cultural Summit" (AECS)
*Event Type:* Annual economic and cultural summit featuring keynote speakers, panel discussions, and performances.
*Venue:* Transcorp Hilton Abuja.
Sojojin dake bakin gate ta gaisar da su dayan na mata wani kallo yace "Do you have a gate pass?" ta girgiza masa kai tace "I don't have one. I'm here to perform a poem. I'm from kaduna, state" sojan yace "Let me see your invitation card" ta ciro wayan ta a jakkan hannun ta ta buɗe ta ciro IV card ɗin da aka buga da hoton ta ajikin ta mika masa yana kallo ya gƴada kai dayan sojan ya kalli IV card ɗin ya mika mata wayan yace "No wonder I saw your face so familiar! I just saw your picture on the banner inside the hall" suka buɗe mata gate ta shiga kowa da take kallo a wajan ba kananun mutane ne bane basu kudi ne na gaske ta gagara shiga ball ɗin ta kira numbern da suka yi inviting ɗinta kamar da 5 minutes sai ga wani mutum ya fito yana mata sannu da zuwa yace "Bismillah mu shiga" to her surprise tana shiga ball ɗin she was greeted by a massive banner with her picture, name, and details about her upcoming performance. The banner read: 'Leena, 18 yrs, from Kaduna state, Performing 'Voices of the Future' at the Abuja Economic and Cultural Summit'. Kawai taji wani honored bata san sanda ta rufe ido ta buɗe ba kowa kallon ta yake a hall ɗin ita dai gaban ta kawai take kallo take bin Mutumin daya shigo da ita wani kujera ya nuna mata wanda taga sunan ta a manne a jikin kujeran da lakanin special guest, ta zauna kai tana ganin kayan alatu da aka tara mata. Event nata gudana wajan da awa daya da rabi aka kira ta kan stage sunan Allah ta fara kira a ranta saboda duk taron da take zuwa tayi performing bai kai wannan da komai ba ta haura kan stage da Bismillah ta daidaita tsayuwar ta ta gama addu'o'in da zata yi a ranta sannan ta ɗauki mic a natse ta fara magana wanda yasa hall ɗin yayi tsit gidajen rediyo da BBC da duk wani kafafen sada labarai suka yi kanta suna ɗaukan ta, tayi delivered a powerful poetry performance on 'Voices of the Future,' captivating the audience of governors, business leaders, and dignitaries with her words on Nigeria's potential and the aspirations of its people. Hall ɗin kafa ya ɗau sautin tafukan hannaye kawai cos Leena tayi magana cike da kwarewa kuma a tsare, ta kusan karasa Last stanza ɗin idon ta ya faɗa cikin na shi sai da taji gaban ta ya faɗi ta ɗauke kai ta karasa tace "Thank you" ta sauka zata karasa gun zaman ta, aka dinga karɓan Acc details ɗin ta. Ana gama program wasu kafafen sada zumunci suka yi caa akan Leena ana mata video manyan mutane suka dinga cewa a musu hoto da Leena, ta tsaya kenan za'a mata hoto da kaduna's Governor yana proud ai daga state ɗin sa take Leena ta hango sa daga nesa yana taho wa ta ɗauke kanta tana ci gaba da pictures ɗin da Za'a fara mata da president taji an ja hannun ta juyawa tayi da sauri tana kallon sa tace "What is the meaning of this Yaya sadeeq?" be ko kalle ta ba shi de ya ci-gaba da jan ta suna tafiya, ganin zata iya calling attention din mutane yasa ta hakura ta biye masa take binsa amma tayi tayi ta kwace hannun ta a nashi ta gagara har suka isa inda yayi parking motar sa ya buɗe front seat ya jefa ta ciki ya kulle sannan ya xaga ya shiga driver seat ya tada motar tace "Meye hakan ina zaka kai Ni?" wani kallo ya juya ya wasa mata sai da ta tsorata taja bakin ta tayi shiru, addu'a kawai take gani wani irin tukin da yake yi kamar irin yana so su mutu wani waje da ba kowa ya tsaya ya juya yana kallon ta ya mata tsawa hakan yasa ta fara hawaye yace "So kike ki buɗe ido tun kina karamar ki ko?" Ta girgiza masa kai yace "shut up, kin wani tsaya kina hotuna da mutane ke har kin san kizo Abuja performing while kin san maza sun fi yawa a ciki, da ace taron mata ne akwai wanda zai Miki magana?" Leena da zuciyar ta yake bugawa ga wani tsoron sa daya dira mata yasa da sauri ta girgiza masa kai tace "I'm sorry na daina daga yau" kallon ta yake baya ko kiftawa...
I think you'd like this story: "AGOLA (Behind the palace walls)" by jiddatulkhayr on Wattpad https://www.wattpad.com/story/394027716?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp.w4b&utm_content=share_writing&wp_page=create&wp_uname=jiddatulkhayr
*AGOLA (Behind the palace walls)*
_By Jiddatul-khayr writes
Chapter 12
Thank you so much, my dear readers, for reading my book🫂🫧! I'm grateful to those who've added my novel to their reading list📖💕. May Allah bless you abundantly and provide for your needs, so you can keep enjoying my stories without any distractions (like running out of data 😊)! 🙏📚❤️
Gudun hauka yake kamar wanda ya ke son kashe su, ga shi Leena abinda ta tsana a rayuwar ta kenan hakan yasa ta tsorata matuka, a quarters ɗin su yayi parking kusa da block 1 yace "Get out" Leena jiki na bari ta buɗe kofar motar ta sauka ta karasa gidan da yake kallon inda yayi parking tayi knocking sau biyu sannan taji muryan wani yace "Who is it?" tace "It's Leena" wani saurayi ne ya karaso kofar ya buɗe yana kallon ta sai sannan ya matsa mata gefe yace "Come on through" ita duk tunanin ta may be wani ɗan uwan su Jidda ne ta fara shiga taji mutumin yace "thanks for coming to check on him. He's feeling a bit better now. The doctor even gave him an injection, and he's actually sleeping right now" sai sannan Leena ta ɗaga kai da sauri tana kallon sa sannan tabi cikin parlorn da kallo ganin ba na Jiddah bane za tayi magana taji yace " If you can wait for him, you're welcome to. I need to head back home for something important, so if he wakes up, please call me and I'll come back" ya karasa maganar yana mika mata hannu alamar ta basa wayan ta ya sa mata numbern sa da sauri tana girgiza masa kai tace "I'm so sorry, I think I'm mistaking. This isn't my sister's house. I think it's the next block" bata jira cewar sa ba ta buɗe kofar parlorn ta fita da sauri Mutumin ya tsaya kallon ta da mamaki and her face looks familiar to him, ko da ta fita bata ga motar sadeeq ba next block ta bi duk da taga mota kusa da shi amma still tana hoping shine tayi knocking Fortunately ashe gidan ne, Jidda tazo ta buɗe Leena na shiga ta fashe da kuka Jidda da take kan kallon Videon Leena da aka gama watsa wa a media tana murmushi ganin yadda Leena ke performing well shine taji anyi knocking kuma ta buɗe taga Leena to her surprise tho me ma yasa Leena kuka kuma tana tsaye bakin kofar har Leena ta karasa cikin parlorn sai kuma da sauri ta kulle kofar tabi Leena hankali tashe tace "Meya faru Leena? Kuma lafiya kuma?, ki daina kuka kimin bayani" Leena tana share hawayen ta tace "Amty Jidda, it's uncle sadeeq" Jidda tace "Uncle sadeeq? wani uncle sadeeq ɗin? Me yayi Miki toh?" Jidda na sheshshekan kuka tace "He went to where I was performing my poem and grabbed my hand, pulled me out of the hall, and forced me into his car. I didn't even get to say goodbye to the people who invited me, and the governor even wanted to take a picture with me, but he just dragged me away. He drove so fast, I was scared. I kept apologizing, but he wouldn't listen, just shouting at me. He brought me here and dropped me off" Jidda ta sake baki tana kallon Leena da mamaki Leena na sheshshekan saboda tsorata da tayi ta ci-gaba "I'm still shaken, Anty Jidda, I'm worried about how those people will feel, especially since I didn't even get to thank them or say goodbye" Jidda bata fasa kallon Leena ba sai kuma ta fashe da dariya Leena ta tsaya tana kallon ta sai kuma ta tashi ta wuce ɗakin da ta sauka aranta tana mamakin what was funny here, sai kuma taji haushin Jidda toilet ta wuce tayi Alwala sannan ta fito ta shinfiɗa sallaya, Jidda ita kadai ta ringa dariya a parlorn ta jawo wayan ta ta kira Sadeeq har ya katse be ɗauka ba ta kuma kira ya ɗauka a tsawa ce yace "Why are you calling me? Are you owing me? Stop calling me with this nonsense! It's all your fault for letting her go there alone to perform that so-called poem. Do you want her to be exposed to all those men? Can't you see most of the people there are males? What kind of aunt are you?" Duk maganganun nan be bata damar magana ba, tana ta kunshe dariyan da take ji yana gama magana ya kashe wayar sannan Jiddah ta fashe da dariya ita duk abinda taji a muryan sa tsantsan kishi ne bayan ga haka bata ga komai ba, tashi tayi ta koma ɗakin da Leena take ciki taga Leena ta idar da Sallah amma bata tashi akan dadduma ba ta zauna gefen ta ta kama hannayen ta tace "I'm sorry Leena! Ba wai dariya nake Miki ba, but to be sincere wallahi abinda na gane a cikin wannan lamarin Ya Sadeeq yana matukar kaunar ki Leena" da sauri Leena ta ɗaga kanta tana kallon Jidda, Jidda ta gyaɗa mata kai tace "Dagaske nake Leena, ko ƙaffara bazan yi ba Ya Sadeeq yana so ki, idan har ba haka bane ba yadda zaiyi wannan abun da yayi, na san Ya Sadeeq fiye da kowa bayi shiga harkan da be shafe shi ba, toh ki sani son da yake miki ne yasa ya Miki wannan Abunda yayi" har ta gama magana Jiddah girgiza mata kai take yi tace "Dan Allah ki daina faɗin haka Anty Jidda and I don't want to believe it" Jidda tayi dariya tace "ajuri zuwa rafi" Leena tace "in shaa Allah hakan ma bazai taɓa yiwa ba, he is so wicked" Jiddah tace "Wallahi Leena kin ma Sadeeq mummunar fassara, he is so nice yadda baki tunani kawai dai saboda baku saba bane" Leena ta ɗauke kanta tana kallon wani wajan Jidda ta mike tace "barin barki ki huta daga haka ta fice "Leena ta jawo wayan ta Mutumin da ya shiga da ita cikin hall ɗazu ta tura masa voice note da ya tura mata da videos ɗin da aka ɗauka. Rayyan har wani dishi dishi yake gani da kyar ya samu yayi parking, yana sauka part ɗin Hajiya ya wuce ya same ta tana shan fura da nono ya zauna yace "yanzu Hajiya idan har Daddy da ita Ammin basu hana Leena zuwa Abujan nan ba ke ba zakiyi magana ba?" Hajiya tace "Yo Ni nawa a me? ɗazu ma yaron nan Ayaan yana ta murna wai yaga Yayar sa a Tv ni na ɗauka ma karya ne can kuwa ina cikin kallon labarai naga an saka ta sai turancin nan take yi kamar baturiya" Rayyan yace "Hajiya dan Allah na roke ki, kiyi ma Daddy magana kar ya sake yarda Leena ta cigaba da wannan abun" Hajiya ta kwalo ido tace "A'a wallahi ba ruwana Nikam, so kake mu taru mu tsana yarinya diflashon ya kama ta? Da acikin gidan nan kai kaɗai kake mata magana toh kai ma yanzu ka tsane ta, a tunanin ka ban san abinda yake faruwa bane dan kawai na zuba ido, toh Abunda yake sata farin ciki bazan zama sillar ruguza mata ba" Rayyan ya dafa kansa dake sara masa yayi kusan 2minutes a haka Hajiya ta harare sa sannan ta cigaba da shan furan ta, ya ɗanga jajayen idon sa ya kalli Hajiya da su wanda hakan sai da ya ba ma Hajiya tsoro tace "Lafiya Rayyan?" Ga Mamakin ta hawaye ta gani a idon sa tashi yayi ya fice a parlorn nata tana kiran sa amma ko tsayawa be yi ba, yana shiga parlorn su yaga Mummy da Hajiya Fatima suna magana ko kallon inda Hajiya Fatima take beyi ba balle ya gaishe ta ya wuce ɗakin sa Fatima ta sake baki tana kallon sa har ya shige sai sannan ta mayar da duban ta gun Mummy tace "iyyee, shi kuma yaushe Rayyan ɗin ya zama haka?" Mummy tace "is like akwai Abunda yake damun sa" daga haka ta tashe ta bishi har ɗakin sa to her surprise ta burɗa handle ɗin kofar taji shi a rufe, ta bubbuga tayi magana still Rayyan be amsa ba ta koma ta zauna a parlorn amma hankalin ta ya tashi Fatima ta taɓe tace "kila yaga yadda yau ake ta posting Agolan nan ne shine zai wani shigo kan mutane haka?" Mummy ta girgiza kai tace "bana tunanin haka ne" tayi shiru tace "Nikam anya shegiyar matan nan bata asirce min ɗa ba yaro fah yanzu shekara da shekaru ya gagara zama yadda yake da ko fah walwala bayi da shi, Abunda yafi damu na yanzu shine ko maganar aure baya so a mishi" Fatima tace "Tabbacin da baki ɗauki wannan shawaran raba su ɗin ba da yanzu kila har ya aure ta" Mummy tace "ai wallahi ko bayan raina Rayyan ya auri ƴar nan ban yafe masa ba". Leena da ke video call da Ayaan, Ammi na sa musu baki lokaci zuwa lokaci tace "see you later" daga haka ta kashe wayan, Maganganun Jidda ne yake ta yawo mata a kai ita kaɗai ta fara Magana tace "How?" Sai kuma ta kyabe baki, ɗaukan hijab tayi ta saka sannan ta fito parlor ta tarar da Jiddah dake jiran ta har ta gaji ta fara game tana kallon ta tace "Anty Jidda gani" fita su kayi. Bayan sun gama sayyayan su, bolt yayi dropping ɗinsu a bakin Quarters ɗin, suka sauka su ka fara taka wa zasu karasa block ɗin Jidda wani mota ne ya shige su Leena na bawa Jidda labarin ɗazu ai ta shiga wani gida daidai inda ɗazu akayi parking nan yanzu ma mutumin yayi parking ya sauka ganin su Leena yasa ya tsaya be shiga cikin gidan ba ya jingina da motar sa Leena nata kallon sa ganin kamar ta san fuskar sa sai sannan ta tuna shine mutumin da ɗazu tayi mistake ta shiga gidan da yake ta ɗauke kanta suka cigaba da labari sai da suka iso daff sannan ya karasa inda suke yayi sallama Jiddah kaɗai ta amsa yace "Excuse me Ma'am, idan ba damuwa ina son zanyi magana da sistern ki" Jidda murmushi tace "It's Okayy" Leena ta girgiza mata kai ita ba zata tsaya ba Jidda a hankali ta mata magana me haka Leena zaki sa ya raina mu" Leena ta kamata gam idan Jiddah ta fara tafiya itama sai ta bita idan ta tsaya itama sai ta tsaya, Jiddah tace "ke me haka? Ki tsaya kiji me zai ce Miki" daga haka ta karɓe Ledan hannun Leena tayi gaba da sauri shi kuma ya samu daman shan gaban Leena, Leena ta ɓata fuska kamar zata yi kuka amma hakan bata bari ya nuna a fuskar ta ba yace "Leena right?" Bata ce masa komai ba ji take kamar ta kwashe a guje ta shige gida yace "I'm sorry na tsayar da ke kuma kamar you're not comfortable" to her surprise ya karɓe watan hannun ta ta saya sakeke tana kallon sa yace "Your passcode?" ji tayi kawai ta faɗa sannan tayi realizing ashe faɗa masa tayi, sakake tana kallon sa ya gama sa numbern sa sannan yayi dialing tana ji wayan sa yayi ringing a aljihun sa sai ya kashe sannan ya mika mata wayan yana murmushi yace "Thank you so much" ta karɓa watan tana jin haushin Jidda ta wuce sa, tana shiga Jiddah ta kwashe da dariya tace "Leena me kike yi kamar wata gwaɓuwa? Kinga reaction ɗinki kuwa? Haba zaki sa maza su raina ki wallahi" Leena tayi shiru tana kallon Jidda ita yau gaɓa ɗaya ta rasa me yasa ta zama wani iri ne ko dan Abunda Sadeeq ya mata ne Oho, ita dakyar ta bari aga hawayen ta balle aga gazawan ta tana cikin wannan tunanin taji Muryan Sadeeq na sallama da sauri ta ɗaga kai ta kalli jidda kan kace me ta tashi da gudu ta wuce cikin dakin. Strickly yana kallon Jiddah yace "yaushe zata koma?" tace "Dama kwana uku zata yi, jibi kenan zata koma" yace "tell her ta shirya kayan ta gobe zata koma" Jidda ta wani kalle sa tace "akan me Ya Sadeeq?" yace "saboda gobe zan koma itama dole ta koma gobe" Jiddah tace "toh dan zaka koma gobe sai ya zama na lalle itama goben zata goma? Toh tare ma kuka zo ne?" yace "wannan kuma ku kuka sani, dan na gama magana" Jiddah na masa wani kallo tace "Ni ban gane takuratan nan da kake yi ba, idan ma wani abun ne a ran ka gwara ka faɗa dan wannan ba solution bane" ya watsa mata wani kallo ta ɗauke kanta tana kunshe dariyar da ya taso mata. Sai bayan Magrib Sadeeq ya bar gidan kuma har ya koma be haɗu da Leena ba da gangan taki fitowa sai da taji tafiyar sa sannan ta fito ta ɗauki some snacks ɗin da suka tsaya ɗazu ta haɗa tea tana sha ta kalli wayan ta jin yana ringing taga numbern wannan mutumin ɗazun ne toh ita me zata ce Idan ta ɗauka, stranger ne fah a haka har ya katse kuma tun ɗazu yake addaban ta da kira, Jidda ta shigo da sallama Leena ta amsa ta karasa ta zauna kusa da Leena tana kallon ta tace "Leena meyasa baki fito kun gaisa da Ya Sadeeq ba?" Leena ta turo baki taki cewa komai tace "Har yanzu kina nan a Leenan ki na baya sai dai wancan ba ta da saurin kuka ita ɗin jarumai ce" Leena tayi murmushi bata ce komai ba duk sukayi shiru sai can Jiddarh tace "Leena Uncle ɗinki fa ɗazu da yazo fah yayi booking muku flight Leena ta kalle ta sai kuma ta tsunkuyar da kai kasa tace "I'm sorry Leena haka yayi requesting toh ba zai saurare Ni ba sai sa kawai na basa info" Leena that was speechless kawai wani wajan take kallo Jiddah ta kamo hannaun ta tace "I'm sorry dear, beside yana son ki samu enough time ɗin rubuta WAEC ɗinki ne" Leena tace "Allah sa hakan shi ya fi alkhairi". Leena ta kwanta amma kwata kwata bacci yaki ɗaukan ta, ta jawo wayan ta Whatsapp ta shiga nan taga messages ɗin wannan mutumin har guda 10 kamar tayi skipping sai kuma ta buɗe ta shiga tana ta kallon message ɗin da ya mata kamar haka "Hello Leena, you're my long-time crush! I've been watching your videos on Instagram. My name is Muhammad Faisal Arab, I'm 35 years old, living in Maitama, Plot 12, Street 5. I work with NNPC. I graduated from the University of California, Los Angeles (UCLA) with a degree in Petroleum Engineering. I did my master's degree in Energy Policy from Stanford University. And, I completed my PhD in Renewable Energy from the Indian Institute of Technology (IIT) Delhi.
I want to be honest with you; I'm not here to play games with your heart. Sincerely, I love you so much and I want to marry you. I'd love the opportunity to get to know you better and show you my feelings. If you're willing, could you tell me a little about yourself, where you live, and a bit more about your life?" Tayi ta kallon hoton sa kamar tana son gano wani abu, kawai ganin kiran sa tayi ya shigo tayi picking takai kunnen ta.....
*AGOLA (Behind the palace walls)*🫧
_By Jiddatul-khayr
Chapter 13
Thank you so much, my dear readers, for reading my book🫂🫧! I'm grateful to those who've added my novel to their reading list📖💕. May Allah bless you abundantly and provide for your needs, so you can keep enjoying my stories without any distractions (like running out of data 😊)! 🙏📚❤️
Around 8am Leena ta fito duk jikin ta amace ta samu Jidda already tana kan breakfast ta karasa ta zauna Jidda ta kalle ta tace "Dalla ki sake ranki, idan kina haka ne Ya Sadeeq zai ci-gaba da miki abinda ba baki so" ta turo baki Jidda tayi dariya ta haɗa mata tea ta zuba mata chips ɗin a plate Leena ta fara ci kenan akayi knocking zata tashi Jidda ta rike ta tace "Ke dalla ki daina wannan shashanci, ki daina abu kamar kina tsoro" Leena ta koma ta zauna Jidda tace "who is it" yace "Malama idan zaki zo ki buɗe, kizo ki buɗe" tayi dariya tace "har yanzu be sauka ba kenan" ta karasa ta buɗe masa ta matsa masa sai daya shiga sannan tace "ina kwana Ya Sadeeq" yace "Fine" ya karasa cikin parlorn ya zauna akan kujera Jidda ta karasa inda suke karyawa ta zauna Leena Satan kallon sa tayi suna haɗa ido tace "Good morning" yace "Morning!" daga haka ya cigaba da dannan wayan sa sai kuma yace "Look! Kina wasting mana time fah" sai sannan ta kalle sa Jidda tace "Leena be quick" ta gyaɗa mata kai ta tashi tace "I'm done" Jiddah ta shiga ɗaki ta fito mata da jakkan ta, Bolt ɗin da sukayi order ya karaso duk suka fito Jidda ta raka su har waje Sadeeq ya shige gaban motar, ita Jiddah ta buɗe mata bayan motar ta mata raɗa a kunne Leena tayi murmushi. Bayan sun isa Sadeeq ya ɗauki jakkan sa dana Leena suka karasa cikin airport tun da sukayi magana a gidan Jidda har yanzu ba wanda yace da ɗan uwan sa uffan, suna zaune suna jiran a kira su, Leena taji watan ta yana ringing ta ciro wayan a jakka gannin Muhammad ne ke kiran ta yasa ta ɗan saci kallon Sadeeq taga ita yake kallo tayi silencing wayan ta mayar jakka. Bayan jirgi ya tashi Leena ta fara jin bacci saboda rashin bacci da bata
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 50