Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wani ba yaji tausayin sa har cikin ransa kamar yau da yayi wa Leena aiki, dan har sai da ya zubda hawaye ganin yadda take wahala, har sannan yana rike da Babyn a hannun sa, sauran Nurses matan kuma suka gama dressing ɗin ta, Rayyan ya duka a gabanta ya sakar mata murmushi yace "Sorry lil sis, Allah baki lafiya?" Kallon Babyn hannun nasa kawai take yi ba tare da ta basa amsa ba ganin haka ya ajiye mata Baby a jikin ta nan da nan yaga hawaye ya fara sauka a idon ta da sauri ya daga Babyn yana kallon ta yace "Be strong please, ke fah jaruma ce" bata ce masa komai ba, bayan wata Nurse mace ta mata allura, ta rufe idon ta Rayyan ya gyara mata kwanciyar ta sannan ya mike, buɗe kofar yayi kana ganin Ammi sai ka tausaya mata yadda ta koma, duk suka daga kai jin an buɗe kofar dakin ganin Rayyan rike da Babyn yasa duk suka yo kansa, Rayyan ya mika wa Ammi, Ammi bata karbi Babyn ba tace "Leenan fah Rayyan?" yace "Ta samu bacci itama, amma zata zauna a asibiti for 7days" Ammi tace "Jikin nata fah" yace "Alhamdulillah" Hajiya tasa hannu ta karbi ɗan tana kallon sa, Anty Binta ma ɗan take kallo a hankali ta furta "Ma Shaa Allah" tana kallon hadaddan kayan Babyn da Rayyan yasa wata Nurse ta saya, dan babu wani kayan haihuwa da suka zo da shi asibiti. Ganin wayan sa na ringing ya daga da sauri yace "Luxurious accommodation kuma?" ya kalli Mami sai kuma yace "Alright, thank you" daga haka ya katse kiran  kafin yayi magana Mami ta riga sa tace "A can Sadeeq ɗin su ke ko?" Kai kawai ya gyaɗa mata tace "Toh shi a wani rashin hankali zai dauki mata da tsohon ciki ya kaita can" daga haka ta ɗauki keyn motar ta, Sultan ya kalle ta sai kuma yace "Mami ki bari Zanje da kaina, no need ki tafi kina bukatar hutu" wani kallo ta masa tace "kana tunanin zai ji maganar ka ne har ya biyo ka gida?" daga haka tayi kofa Jiddah ta mike yace "Ki zauna dear, kina bukatar hutu" ya sakar mata murmushi ka mayar masa daga haka ya bi bayan Mami da sauri, ya samu har ta shiga motar ta yace "Barin kaimu Mami" ta fita ta zaga zuwa dayan side ɗin motar ya tada motar sai kuma ya dauki wayar sa ya kira mutanan da suke basa info yana daga wa Sultan yace "ina son genuine details pls" daga haka ya katse kiran sai da suka yi tafiya mai nisa sosai sannan suka isa Luxurious accommodation, bayan yayi parking a compound ɗin ya Ciro wayan sa yana duba detail da aka turo masa just of recently, sannan suka kama shiga hanyar reception. Wani matsakaicin gidan ne mai dauke da ɗa karamin ciki da parlor sai kuma wani dan karamin dakin a gefe, gaka ganin gidan kasan kawai wadatar zuci gare su, dan basu da komai wanda zai nuna suna da hali, gaba ɗaya sun yi depending akan ɗan su ɗaya tilo, wanda shima inda yake aiki albashin nasa bai wuce dubu ishirin ba, rayuwar su suke cikin kwanciyar hankali da kaunar juna, dan basu da wata damuwa sun gama sallame lamarukan su ga Ubangijin, wata Dattijiwa ce dake kwashe abinci a tsakar gidan dan ko kitchen babu gare su, bayan ta gama kwashe abinci ta ɗauka ta kai nan parlorn, na mai gidan ta kuma ta shigar da shi dakin dake cikin parlorn ta sake komawa cikin ɗan karamin compound ɗin na su, dakin dake gefe ta karasa tana cewa "Wai ko baka da Lafiya ne Malik?" Malik dake kwance a kan dan karamar gadon sa ya mike zaune yace "Umma lafiya ta fah" ta daga labulen dake makale a kofar tana kallon sa tace "Naga kabar wajan aikin naka da wuri kuma har sannan baka sa komai a cikin ka ba, ga dukkan alama kana cikin wata damuwa" ya mike ya fito daga dakin yana kallon Umman nasa yace "A'a Umma, kawai dai bana ɗan jin daɗi ne" Umma ta harare sa tace "Ko dai kun samu matsala ne da surkar tawa" bai kuma ce mata komai ba yana biya da ita har ta shimfida tabarma a nan compound ɗin bayan ya zauna ta ajiye masa kwanan abincin a gaban sa, tana kallon sa tace "Menene damuwar ka?" yayi shiru kamar ba zai yi magana ba sai kuma yace "ina wannan yarinyar da nace miki mutane suna cewa muna kama?" Nan da nan Umma ta hada rai saboda tun day one daya bata labarin Leena taji ta tsane ta har cikin ran ta, ganin shirun da tayi yasa yace "Umma!" ta kalle sa sai kuma tace "Me?" yayi shiru yana kallon ta sai kuma yace "naga kin bata rai ne" tace "kawai dai kai na ne ya fara ciwo amma ba komai" yace "Toh Allah sauwake" daga haka ya fara cin abincin gaban sa ba tare da ya sake ce mata komai ba. Knocking suke a hankali ya daga kansa yana kallon kofar da ake ta knocking for almost 5 minutes kenan tunanin ko ma'aikatan hotel ɗin ne yasa ya mike a hankali dan gaba ɗaya wani zazzaɓi yake ji da kyar ya karasa jikin kofar ya buɗe with shock yake kallon su Mami, Mami ta karasa buɗe kofar ta shiga cikin dakin Sultan na biye da ita bin dakin tayi da kallo tace "Toh ina Leena?" Sadeeq ya durkusa nan kasa ya kifa kansa da bango duk suka bi shi da kallo, Mami tace "tambayar ka fa nake yi" Sultan ya durkusa a inda yake yace "Brother!" ga mamakin sa hawaye yaga Sadeeq yake yi ya juya yana kallon Mami ya mata alama da kuka fa Sadeeq yake yi, Mami ta karasa wajan da sauri ta daga kan Sadeeq tana kallon hawayen dake sauka a kuncin sa, tace "Sadeeq!" ya lumshe idon sa sai kuma ya faɗa jikin Mami yana zubda hawaye Mami hankalin ta yayi mummunan tashi tace "Menene? Ka buda baki kamin bayani mana" a hankali kamar me raɗa yace "Mami can you imagine na sake Leena" Mami bata san sanda ta zabura ta mike ba tana kallon sa Sultan ya duka inda yake zaune yace "can you here yourself, please? Kasan me kake cewa kuwa?" Har sannan Mami tana kallon sa with shock yace "Ban san what comes over me ba, nasan kawai idan na sake ta zan samu nutsuwa, ban san wani hali zata shiga yanzu ba" kawai ya fashe wa Mami da kuka kamar yaro karami ya kama kafafun ta, Mami na girgiza kai tace "Sadeeq kasan kuwa me kake cewa?" Ya daga kai a karo na farko yace "Mami na sani, amma believe me bansan me ta min ba na tsane ta, ban san me tamin ba na sake ta, i can still remembered her last words" Mami tayi ta maimaita innalillahi wa'inna ilahi raji'un' she's very disappointed on him kuma har sannan ta gagara kwakwaran motsi, Mami tace "ina Leenan take yanzu?" yace "ban san inda ta tafi ba, nasan tana rokana akan na taimaka mata" Mami ta rasa me zata yi ta kamaimai. Hajiya ta dinga masifa ganin har sun wuni a asibiti amma Daddy ko lekan su be yi ba, wato ma ko a jikin sa tunda ba 'yar sa bace, Rayyan ne ya shiga dakin da aka mayar da Leena after tayi 5hours acan duk kuma suna dakin, kuma har sannan Leena na bacci, Rayyan ne yayi sallama duk suka amsa masa bayan ya shiga ya gaida su, Sannan ya ajiye sayyayan abubuwan da yasan zasu buka ta, Ammi tace "Mun gode da ɗawainiya Rayyan, Allah Ubangijin ya maka Albarka" yayi murmushi yace "Haba Ammi, ai Leena kanwa ta ce, so, mention not" Hajiya tace "ai mun gode Allah da baka yi hali irin na uwar ka ba" Rayyan be kuma cewa komai ba Leena ne ta farka tana bin su da ido tana hada ido da Rayyan ya sake mata murmushi ta ɗauke kanta Hajiya ta mike ta karasa wajan ta tana mata sannu, Anty Binta ma haka Ammi kuma ganin Hajiya yasa ta kasa magana amma tana kallon 'yar nata da cike da tausayawa, Rayyan yace "make damun ki yanzu?" ta ce "ciki na" yace "Sorry zai daina" Leena na kallon anty Binta a hankali tace "Anty Binta ina son ganin Babyn" Anty Binta ta kalli Hajiya da har ta koma ta zauna ta karasa wajan ta tace "Hajiya bari a nuna mata abun da ta samu dan har sannan bata san me ta haifa ba" Hajiya ta rike haba tace "ikon Allah, wato yaran zamani ba kunya fa gare ku ba" Anty Binta bata bi takan Hajiya ba ta karbi ɗan ta kaima Leena da Rayyan ya gyara mata zaman ta, Leena ta dinga kallon fuskar yaron nan da nan ta fashe da kuka duk kallon ta suke Hajiya tace "ji wani iskanci kuma, kila saboda uban ɗan kika fara mana kuka halan" Rayyan yace "Ai dole ne Hajiya, gwara tayi kukan da ta rike abin zai fi damun ta" Hajiya ta juya a fusace ta fara balbale sa Leena a hankali ta kai hannu tana shafa fuskar dan, Hajiya ta sake baki tana kallon Leena Rayyan bai san sanda ya fashe da dariya ba ganin reaction din Hajiya, Leena ta turo baki ganin kallo da Hajiya ke mata, Anty Binta tace "toh karbi ɗan mana" Leena ta girgiza kai a hankali tace "ina tsoro". Jiddah da har bacci ya ɗauke ta tajiyo muryan su Mami a parlorn gidan, ta mike a hankali dan gaba ɗaya ba lafiya gare ta ba, ta sauka ta buɗe kofar sannan ta karasa cikin parlorn tana binsu da kallon a hankali tace "Ina Leenan?" Kana gadin su kasan duk hankalin su a tashe, kawai dai ga su nan ne, ta kalli Mami da ta jinginar da kanta tana kallon waje guda, Jiddah ta kalli Sultan tace "What is exactly happening here?" In briefly Sultan ya mata bayanin komai with shock take kallon Sadeeq tace "Ya Sadeeq!" bai ko kalle ta ba" tace "Mami ina Leenan toh?" Mami tace "ina muka sani Jiddah, ko baki ji ance a daren ta bar gidan ba" Jiddah ta mike tace "inaa, wannan ba yin kan sa bane" Mami tayi murmushin takaici tace "Ai da Leena nan ta zo akan ta je wani wajan, yanzu ta ya zamu fara hada ido da ahalin ta" Jiddah tace "ina zuwa" daga haka ta wuce daki ta dauki hijab ɗinta ta fito, Mami tace "ina zaki?" tace "zan je gidan nasu ne, ya kamata ace munyi confirming" kafin Mami tace wani abu har Jiddah ta fita. Sai da ta isa kofar gidan su Leena sannan ta tsaya ta fara tunanin me zata ce musu, dakyar tayi gathering courage tayi knocking gate ɗin Baba mai gadi yazo ya buɗe mata gate ta gaishe shi sannan ta wuce sashin su Leena ta dinga Sallama sai taji shiru ta wuce part ɗin Hajiya duk da yadda zuciyar ta ke bugawa amma bata damu ba, dan tasan Hajiya ba lalle su wanye kalau ba, tana isa ta samu part ɗin nata a kulle kawai tayi bakin gate tana kallon mai gadi tace "Dan Allah Baba ko kasan inda mutanen gidan suke?, ina nufin Hajiya da mahaifiyar Leena" yace "Oh Ayyah ai tun juya da daddare suka kwana a asibiti saboda Leenan kamar nakuda take yi" wani irin bugawa zuciyan Jiddah yayi taji kamar ba zata iya tsayuwa ba tace "Nakuda kuma Baba?" yace "Eh" daga haka ta fita da sauri taci karo da Binta da ta dawo gida zata haɗa musu dinner, Binta ta ɗan bata rai Jiddah bata damu da hakan ba ta gaishe ta bayan sun gaisa tace "yanzu nake jin wai Leena na asibiti" atakaice "Eh" Jiddah tace "Ya jikin nata?" tace "Alhamdulillah, Allah yasa an mata aiki cikin aminci, ta haifi dan ta namiji" Jiddah taji garin na juya mata, ta fara salati ba tare da ta shirya ba Anty Binta tace "shikenan tambayoyin naki? Ina sauri ne saboda abinci zan girka musu" inaa Jiddah ta faɗa tunanin da itama kanta bata san da shi ba, Anty Binta ta rabe ta ta wuce cikin gidan ba tare da ta sake bi ta kanta ba. Dakyar ta iya karasa har cikin gidan su, bayan ta shiga parlorn duk kallon ta suke suna jiran jin me take tafe da shi dakyar tace "Mami Leena ta haihu" Mami tayi shiru tana kallon ta sai sannan Sadeeq ya daga kan sa yana kallon ta Sultan yace "aina kika ji?" tace "daga gidan su nake yanzu haka suna asibiti ko sallamar su ba'a yi ba, kamar ma aiki aka mata" Sadeeq ya mike ba tare da ya sake kallon wani a parlorn ba ya fara haurawa sama, a hankali Jiddah tana kallon Sultan tace "Shikenan kuma yanzu ba matar sa bace?" Sultan bai bata amsar tambayar ta ba. Bayan yayi parking mashin ɗin sa ya sauka yayi knocking gate din gatekeeper ya buɗe kofar bayan sun gaisa Malik yace "an sallamo su kuwa?" yace "A'a, har yanzu basu dawo gida ba, kuma naji kamar kanwar mahaifiyar nata tace ba yau zasu dawo ba, dan ta haihu" ya gyada kai yace "Okay, Allah raya mana, ita kuma Allah bata lafiya, dama nazo naji ya jikin nata ne" Baba mai gadi yace "Ayyah, toh dai har sannan basu dawo ba" daga haka ya koma, sai sannan ma ya fara tunanin ace suna nan me ma zai ce ya kawo sa. Hajiya tayi ƙwafa tace "wallahi ni nasan maganin sa, daga shi har ita shegiyar matar nasa" sai maganganu take ba tare da ta damu cewa Rayyan na wajan ba, tana girgiza kafa tace "Allah maida mu gida, duk abinda zai faru ban damu ba" Anty Binta ta gyara zaman ta tace "amma toh ko Hajiya nace Daddyn bai san muna nan bane?" Hajiya ta fara masifa Ammi ta kalli Binta dan tasan da gangan ta sake tabo Hajiya, "kamar ya bai sani ba, baki da baki na masa magana amma yayi burus da Ni, saboda gani 'yar banza, wallahi daga shi har matar nasa su jira komawa ta gida" Rayyan ya sauke kansa kasa, Hajiya tace "Duk abin zai faru sai na barbade gidan da hayaki idan yaso duk abinda zai faru bai dame Ni ba" Rayyan ya mike Hajiya na kallon sa tace amma fah ba'a ma yaron hudu ba ba fah" Idan naga reaction da dayawa zamu cigaba da samu update sau biyu a rana, amma idan naga babu reaction hakan na nuni cewa baku jin dadin labarin ne. Jiddatul-khayr 08110615256 https://chat.whatsapp.com/K7dFXrl6zm1IG82QJyPjuV?mode=ac_c *AGOLA (Behind the palace walls)*🫧 Wattpad © Jiddatulkhayr YOUNG TALENTED WRITER'S ASSOCIATION Chapter 45 ___Rayyan ya da kata daga fitan da yayi niyya yana kallon Hajiya, Hajiya tace "Toh ai sai ka masa hudu ba ko Malam? tunda naga daga Sadik ɗin har uban naka ba mutunci suka gada ba" Rayyan ya tako har inda Hajiya ke zaune ya duka ya karbi Babyn yace "toh ai bansa sunan da za'a sa masa ba" Hajiya ta juya tana kallon Ammi dan jin me zata ce Leena tayi saurin cewa a sa masa "Abubakar" Rayyan ya tsaya kallon ta, Hajiya da Anty Binta suka sake baki suna kallon ta ta sauke kanta kasa, Hajiya tace"uban me shi Sadeeq din ya mike da kike son maida wa ɗan ki sunan sa?" Anty Binta tace "tun da kika zo kinji wani nasa ya zo ne, amma ke ga miji daɗi ko, duk wulakanci da ya miki baki daddara ba? Toh ki sani ba aure yanzu tsakanin ku, dan iddah ma kin fita" duk Ammi na kallon wani wajan amma bata tanka musu ba dan har sannan bata samu lokacin da tayi magana da 'yar nata ba, Leena tace "toh ai naga ba dan shi nace a sa masa sunan ba kawai dai I'm obsessed with the name" har sannan Rayyan idon sa na kan ta, Anty Binta tace "kar ki mayar da mu kanana mana, ya kamata ki cire sa a ranki dan yanzu kam babu wani abun da kika haɗa da shi" a hankali Leena dake juya tean gaban ta tace "Ni nasan har sannan ba yin kansa bane, dan ai tun daga farko ya nuna min so" tunawa da maganar Anty Binta na karshe wai yanzu ta fita a iddah kawai ta fara kuka duk kallon ta suke, su sun dauka saboda maganar sa masa Abubakar ɗin da tace ne ya sata kuka, Hajiya tace "kaga Rayyan sa masa Abubakar ɗin tunda kaga rashin kunya ƙarara take son nuna mana" Leena ta kifa kanta har sannan Rayyan na kallon ta a hankali yace "So kike ki jima kan ki wani ciwon?" Sai sannan Ammi tayi magana tace "Fama da kanta da take yi yanzu ai bai ishe ta ba sai kin kuma jin wani ciwon ko?" tayi shiru Rayyan yayi ma ɗan nata hudu ba duk da bai so ba ya mike ya kaiwa Hajiya Babyn daga haka ya fice, Hajiya ta kwantar da Babyn tayi tagumi tunani iri da kala ke yawa a zuciyan ta can ta daga kai ta kalli Leena da har bacci ya fara ɗaukan ta sai kuma ta sauke ajiyan zuciya. Mami dake kansa tun sanda suka kawo sa asibiti ita yanzu duk abin ya fara sata cikin ruɗani dan babu test da ba'a masa ba kuma ance lafiyar sa kalau, Jiddah ne ta kalli Mami tace "Ina ga fah kamata yayi kawai mu koma gida Mami, dan kinji duk result daya fito sai ace ba wani abun da ke damun sa" Mami ta sauke ajiyan zuciya tana kallon Sadeeq dake bacci. Layla bata tanka musu ba sai ma danna wayan ta da take yi, su kuma sai hira suke yi, Mummy sai maida zancen sakin da aka ma Leena take yi, Hajiya Fatima tace "Ai kadan suka fara gani" Niswa tace "Mummy ai baki ga yadda hankalin su ya tashi ba, daga gani har sannan yarinyar nan bata warke ba, shiyasa ko samun su na wuni a gida ba su yi" Hajiya Fatima da Mummy suka fara dariya sai sannan Layla ta sauke ganin ta daga kan wayan tana kallon Niswa tace "Toh ke yanzu uban wa yasa bakin ki a maganar su, kina yarinya sai shegen manyan ce, idan ke ce aka miki haka zaki ji dadi? ga dai aure gaban ki, ki natsune dai" Mummy ta sake baki tana kallon Layla Hajiya Fatima kuma tayi "Uhum, kai Layla" tana murmushi ta kare dan ita dama kamar tana shakkar 'yar nata ma, Mummy tace "Amma baki san wa ake magana akai ba ko Layla" ta mata magana in very calm way, Layla ta taɓe baki tace "Toh dama ku akwai wacca ta tsole muku ido ne bayan Leena?" Mummy tace "Toh ai itace wanda Rayyan ya kwallafa rai na hana sa nace ga ki nan sai an basa wata kuma" Niswa ta dinga hararan ta, Layla tace "Toh da kuka hana masa ita ya aure Ni, hakan yasa ya so Ni? Ba wannan bama yanzu a rashin tunani da kuka raba ta da auren ta ba hakan bane zai sa Rayyan ɗin yace zai koma mata a karo na biyu, ai wannan rashin tunani ne" daga Mummy har Maman ta shiru suka yi suna nazarin maganar ta, Layla har ranta bata so mutuwar auren Leena ba, Niwsa tace "kina magana da iyayen ki amma kamar kina magana da kannan ki fah?" Layla tace "Zo ki rufe min baki mara kunya" Hajiya Fatima tace "Haba Niswa, sai kace Layla sa'ar ki?" Mummy tana kallon Hajiya Fatima with shock, Hajiya Fatima ta kalli Mummy sai kuma tayi 'yar dariya tace "ina ga Layla na moody ne yau din" Niswa ta mike fuu tayi dakin su, dan bakin ciki Layla ta kama hanyar fita tana buɗe kofa taga Rayyan da saurin sa ya juya tace "Honey" jin muryan ta yasa ya jiyo yana kallon ta ta karasa wajan sa tace "shine rabon ka da gida tun jiya ko?" Kallon bayan ta yayi, yace "don't tell anyone kin ganni, anjima zan zo daukar ki, ki jira ni" ta gyada masa kai tana murmushi, daga haka ta kama hanyar garden, Rayyan har wani jiri yake ji, dakyar ya iya karasa gate yana tunani abin da ya gama ji, dakyar ya samu strength ɗin shiga Mota, how on earth could his mother be the one to cause a divorce? ya jingina da jikin motar yana jin zuciyar sa na kuna. Bayan sun dawo gida Mami dake zaune da wata sistern Baban su Sadeeq itama duk lamarin Sadeeq ya sata cikin ruɗani, Jiddah ce tayi Sallama, Mami ta daga kai tana kallon ta ta karasa cikin parlorn ta gaida Baabar ta sannan tana kallon Mami tace "Mami Ni da wani malami ne muka zo" Mami tace "ke da wani kuma?" ta gyada mata kai tace "zai shigo ne ya duba Ya Sadeeq" Mami tace "amma lafiya gare ki kuwa Jiddah?" Kanwar mahaifin su tace "Ai tayi tunani kuwa Mami" Sultan dake zaune a corridor ya fito yana kallon Jiddah yace "Yana ina, dear?" ta nuna masa waje ya karasa waje ya shigo da mutumin da yaki shiga da kyar dai ya samu ya lallaɓa sa, direct dakin da Sadeeq yake kwance suka wuce, Mami ta bi bayan su dan ita bata son irin haka, Malamin ya dinga kallon Sadeeq dake bacci ya juya yana kallon Sultan yace "Tabbas an masa illa, amma ba komai tunda lokaci bai kure ba, wannan rashin lafiyar ma kwantar da shi akayi" Jiddah tace "ya za ayi kenan?" Yace "Za'a warware komai, kawai dai an sa masa tsanar matar sa ne kamar yadda na fada miki tun kan mu zo, duk da ma yanzu wasu abubuwan sun warware kan su" Jiddah ta kalli Mami ta take bin sa da kallo, ya Ciro wasu haya ki da wasu itacuwa yana kallon Jiddah. Rayyan dake kwance a office ɗin sa har sannan bai daina tunanin da yake fama da shi ba, wayan sa ne ya fara ringing ya daga ganin Layla da kamar ba zai dauka ba sai kuma ya daga ya kai kunne tace "Honey, har Magrib ya gabato kuma baka zo ka ɗauke ni ba" sai sannan ya kalli agogon dake manne a office ɗin sa yace "Okay, on my way" ya katse kiran, sai daya fara biya ya duba Leena ya kuma tsaya musu abinda zasu bukata sannan, ya shiga dakin da Sallama Leena dake zaune ta ɗauke kanta ganin ya shigo bayan ya gashe su sannan Leena a hankali tace "ina wuni" yace "akwai wani abu dake damun ki" kai kawai ta girgiza masa yace "Kina kuka ko?" Hajiya tace "Ai dole ka tambaya, yanzu fah Shikenan bata da wani aiki face kuka wallahi ji nake kamar na daka shegiya" bai ce komai ba yace "barin tafi gida" Hajiya tace "Toh Ammi kina zaune ba zaki tashi ki bisa bane ko zaki tsaya jiran wannan motar hayan ne?" Ammi ta kalle sa tace "gida can zaka?" yace "Eh, Zanje daukan Layla" Ammi ta mike tana kallon Leena, Hajiya tayi saurin cewa yauwa Rayyan kama kanwar ka fada a matsayin ka na likita wai fa 'yar nan kafin ta bama jaririn nan Mama sai anyi da gaske, hakan ma tana yi kamar zata sake mana shi a kasa" Rayyan ya koma ciki dakin daga bakin kofar da yake yace "Leena, why don't you want to breastfeed your baby?" taki kallon sa kuma taki cewa komai yace "Don't you know how incredible good breast milk is for a baby?" ta ɗan bata rai ita fa kunyar sa take ji amma gani take kamar ba gane hakan yayi ba murmushi yayi yace "Please try your best to keep breastfeeding him, so he can grow up healthy and strong" daga haka ya ma su Hajiya sallama ya bawa Ammi waje ta fita sannan ya bi bayan ta. Hajiya Fatima tana kallon 'yar ta tace "ke ba

Chapter 29 of 50